Download Yarima Ashman Chapter 5 & 6 Hausa Novel Complete PDF

YARIMA ASHMAN

Story & written by mmn fareesa

Chapter 5 and 6

WANENE YARIMA ASHMAN?

Yarima Ashman saurayine matashi d’an kimanin shekara32 aduniya .

Yana tak’ama da ilimi,kud’i,saurauta had’e da k’asaiita”,bayason raini ko kad’an kuma bayason shishshigi,akwaisa dason girma.”gashi miskiline na karshe dan yanada girman kai haka jama’a ke cewa dan in yayi maka magana sau daya ko biyu bazaisake ba,kuma bayashiga abinda be shafesaba.

Barrister Ashman kenan ,lauyer ne mezaman kansa yakammala karatunsa na law a k’asar jodan. Ayanxun haka yazama cikakken barrister ,baya shigarma masu kud’i akan kara .”talakawa yake taimako kuma kyauta baya karbar ko sisinsu “,dan shi aganinsa bbu mai kudin daya isa yadaukesa lauyensa har yabiyasho,hakan yasa talakawa ke mugun sonsa suna kaunarsa”, ko guri zaibi ya wuce zakaga anatafi ana d’aga masa hannu hade da yima sa kirari.

” hakan yasa yyi suna sosai ko ina agarinsu ,kuma masu kud’i marasa tsoron ALLAH basa sonsa.”

Yarima mutumin kirkine don baya shaye shaye da Neman mata irin na samarin yanxun ga kuma uwa uba ilimin addini dayake dashi.

“Maimartaba isma’il khaleed sarkin bauchi shine mahaifinsa .”

Yanada mata2 hjy falmata da hjy rahama ,hjy falmatace uwar gida tanada yara5 lubna ,Ashman,Hanna,sadeeq,sa Auta salim.

Hjy rahama tanada yara3sameera ,sageer sai Maryam.”family ne dke zaune lfy cikin ganin mutuncin juna da girmama nagaba da mutum.”

Yarima iyayensa nasonsa da danginsa dan inkagansa gaban amminsa tana lallab’asa saikace shine Auta.yanada son yara sosai fan kanwarsa dke bimasa tanada yara twins munib da muniba ,yarima nason yaran sosai sun shak’u da yaran har shopping yake musu yaje gidansu yakai musu “, kowa yana mamakin sa dan inbada daliliba baya zuwa gidajen yan gidansu mata masu aure ba.”

Tun bayan yarima yafara aiki mai martaba yaso yyi aure amma sai yace ai yarinyar dazai aura bata ida karatuntaba .

Hakan yasa sarki yasharesa kafin yyi lokacinsa .

“Yarinyar da yarima keson ya aura wato salma “,yanason ya auretane sbd tana mugun sonsa dan ita ta tura kanta gunsa,ta dauki tsawon shekara tana binsa tana rokar soyayyarsa dg karshe yaga zata kashe wata yarinya sbd shi,daganan yaga zai iya aurenta tunda zata iya komai sbd shi,amma bawani sonta yakeba,tabbas ya yarda akwai so amma shi aganinsa yafi karfin zubda ajinsa yace yanason mace saidai ita tace tana sonsa.

READ ALSO:  Download Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 118 Hausa Novel PDF

” da kyar ya amince ma salma zai aureta amma yana mata wulakancin da yaga dama dan inba ita takirashiba baya kiranta ,kuma kota kira saiyagadama yad’aga kiran.”

Yahad’u da salma a akasar Jordan itama tazo karatu har ya kammala karatunsa yabarta yanxun saura shekara1tayi degree dinta tadawo Nigeria kuma itama yar bauchi ce.

“Tana mugun sonsa musammun a cikin kawayenta tana alfahari dashi,shikuwa yana juyata kamar bante,ko wani guri zata saita kirasa ta tambayesa ,inyace bazatajeba to ko iyayanta sunce taje bazata jeba.

” alokacin dasuke tare akasar Jordan yayimata alkawarin zai aureta hakan yasa ta nuna masa ko romancing juna surikayi,yanuna ma ah ah had’e da yin fushi sosai da ita dan nuna mata yyi zai iya rabuwama da ita akan hakan Dan yatsani mace marar tarbiya.kuma bawai dan bayada bukatar hakanba ah ah,saidai yana tsoran aikatawa da zunubin da zai daukarwa kansa.

Salma yarinyace yar kimanin25years tataso cikin gata dan iyayenta sun batata da kudi tana yadda take so.

Salma Nada wani boyayyen Hali danbakowa yasantadashiba ko yarima bai saniba.

“Y’ar lesbian ce ta bugawa ajarida ,inataga yarinya ta mata tofa duk yadda zatayi sai tayi tabiya bukatarta da ita,Wanda a Jordan ne ta lalace tazama yar lesbian gakuma shaye shaye tanayi.

” saidai bata taba bari yarima yaganeba.”

dan ita tana sonsane amatsayinsa na kyakkyawa kuma dan sarki amma bawai dan yabiya mata wata bukata ba in ya aureta.

WACECE YASMEEN?

Yasmeen yarinyace yar kimanin shekara 18,mahaifinta mlm ahmadu yarasu shekara2da suka wuce Wanda shiga akayi har gida aka kashesa amma ba’son kosuwa sukayi kisanba kasancewarsu talakawa.

READ ALSO:  Download Complete Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 111-115 Hausa Novel PDF

Mariya wato umman su yasmeen asalinsu yan yolane fulanin can fatauci yakawo mijinta da yayansa Kawu bala agarin bauchi har suka zauna da iyalansu.

“Yasmeen su biyune agun iyayansu daga yah Omar sai ita .”

Sunsha wahalar rayuwa bayan mutuwar ubansu.

“,Kawu bala mugune na karshe mai matuk’ar son abun duniya da had’ama ga ganin gari dan zai iyayin komai sbd kud’i”.

Yanada mata 1da yara 4bashir,Rukayya, saude sai Musa.

Bashir da’ake kira da bash tantirin marar mutuncine bayada aiki sai Neman mata dayiwa yara fyade ,askul d’aya suke da yasmeen tana 100level yana 400lavel.

Kawu bala bayan rasuwar mlm ahmadu wato mahaifin yasmeen duk Dan abinda yabarmusu Saida ya k’wace da karfi da yaji harda filing daya fara ginawa sukoma da iyalansada kasancewar gidan haya sukewasu tumaki5da shanu2dayake kiwo duk yakwace.

Umma mace mai hakuri da kawaici batace komaiba tabarsa ga ALLAH.

” hakan yasa suka tagaiyara ko abinda zasu ci gagararsu yake ,mai gidan dasu zaune yace su zauna kyauta yayafe musu kudin hayan.

Umma nayin wankau da surfe da haka suke cin abinci ga karatun yah Omar.

“Awahalce yah Omar yakamma NCE dinsa ,itakuwa yasmeen tana gama secondary skul tadakata da zuwa skul.

Cikin ikon ALLAH yah Omar yafara faskare yana siyarwa ALLAH yasa ma abun albarka jar yayi dan shago na langa langa yana siyarda kayan tireda,umma nayin cincin Nome ,aya ,anasiyarma ta ak’ofar gida gun da yah Omar keyin tired a.

” da haka har yamaida yasmeen a skul yanxun tana label 1 sannan yasayi fili yyi daki1da bayi suka tashi suka koma gaba daya yah Omar shine gatansu.dan shi bayata karatunshi burinshi shine yaga yasmeen takammala nata karatun dan mugun jida ita yake sosai.

AKawai wani Alh jamilu ,dan siyasane kuma ,mutane suna zargin dan mafiyane dan ba’asan meye sana arsaba.

Yakasance yana auri saki yanada matarsa uwar gidansa ,gidanta daban yake.

sannan yanada wani had’adden gida can yake auran yan mata yakai duk wadda ya aura batafin5or8month yake bata Jan kati ya auri wata dan barin kudi yake ma mata har su yadda su aureshi duk wadda ta yi shekara 1to ta Dade .

READ ALSO:  Dowload Abban Sojoji Hausa Novel: Complete Popular Book 1, 2 3 and Reviews

Anacikin haka yaga yasmeen xata skul abakin titi yaganta,duk yarufe ta tafi da imaninsa.

Cikin kwana2 yyi bincike akanta yagano komai har da mutuwar ubanta da cutarsu da Kawu bala yyi ,yajikuma Kawu bala Nada son kud’i,ai sai yaji dadi sosai.

Nan yaje har gida yafadamasa bukatarsa nan Kawu bala ido ga kud’i ya yarda ,had’e da cewa duk runtsi sai ya auri yasmeen ne bar gidanba Saida yana Kawu bala dubu Dari biyar yace wannan somun tabine.”

Shikuwa Kawu bala yagama shawara soyake kawai ya fidda rana yaje yasanar da umman yasmeen dan yagama yanke hukunci,Ammafa injisa.

Kuma sun yi da alh jamilu bayan kwana2yadawo yaji abinda ake ciki.

Cigaban labarin…

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Yarima Ashman Book

The most reliable and easiest way to obtain the complete Yarima Ashman book to purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Yarima Ashman in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete Yarima Ashman booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an emailcontaining the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.