SONE KO K’IYAYYA is a popular Hausa novel that tells the story of a young woman named Sone who falls in love with a man named K’iyaaya. However, their love is threatened by various obstacles, including family conflicts and societal expectations. In this blog post, we will provide information on how to download the complete PDF version of SONE KO K’IYAYYA Hausa Novel.
Akid’ime nafeesa ta mik’e tsaye tana fad’in tashi muje gida Allah yasa yaya Aliyu be dawo ba”In’am kasa mgn tayi ta mik’e tsaye tana gyara mayafinta” sady na kallonta tace”k’awata badai tafiya ba?”In’am tace”tafiya mana zamuyi har isha’i tayi bamu fargaba”kar muyi laifi Agida”to shikenan muje yaya farooq yamik’a munku gida ko?”shiru In’am tayi batace komaiba har suka fito haraban
gidan”farooq da
Abdul na zaune samqn wata jar mota”suna ganinsu suka diro”kasancewar ko ina da haske A gidan”sady na murmushi tace”yaya dan Allah ku mik’asu GRA nasssarawa”ta fad’a tana cika musu hannu ta musu godiya”In’am kuwa kamar tayi musun shiga motar”saita tuna yanzun idan sun fita kafin su sami nafef k’ilan 8 pm ta wuce”kushiga mana”cewar farooq yana bud’e musu back sit yana murmushi”sai kallon In’am yakeyi”bbu musu suka shiga”
Abdul yaza gaya yashiga gefen me zaman banza”farooq yaja motar cikin nutsuwa kafin yace” hjy in’am kunyi shiru keda nafeesa ko?”nima Abinda zance kenan Abokina”cewar Abdul”gaban In’am yafad’i tana mamakin ta yaya yasan sunanta?….kuna mamakin jin sunanku Abakina ko? hakane gaskiya munyi mamaki”cewar nafeesa”Abdul yayi y’ar dariya yace”to kucire mamakin”idan bbu damuwa muna son ku bamu contact naku”gaskiya bamuda waya kwanan nan dai zamuyita”In’am ke baza kiyi mgn ba?”cewar farooq”d’aure fuska tayi batace komaiba”duk yadda farooq yaso In’am tayi mgn k’in magana tayi har suka iso Anguwar GRA nassawa…..
yaya Aliyu na shigowa office yaja computer daya saita da CTV camera”yafara dube dube har yagano room d’in daya kai In’am jiya”Anan yaga yadda sukayi fad’an nasu itada nafeesa ajiya da dare” murmushi kawai yayi yana jin nafeesa na k’ara samun matsayi na y’an uwantaka Azuciyarsa”ya fahimci tana jin zafin Abinda In’am ke nunawa Akansa”yakuma lura In’am har yanzun k’uruciya na damunta”saidai ransa yabashi nan gaba harda nafeesa Acikin masu yimasa campaign d’in soyayyar sa awajen in’am….
yajima yana tunani har yafara duba patient”sai wajen 12 yatsaya yayi break fast sannan yaci gaba”be baro Asibitin ba sai
wajen 4:30 pm”sadda ya iso gida biyar saura”part nasa ya wuce yayi wanka yashirya cikin k’ananun kaya yanufo part d’in ummi sbd yayi lunch Acan” kuma yaga y’ar rigimar tasa”yasan dai yanzun ta dawo dg wajen lallen”yana wannan tunanin yashigo cikin parlourn ummi”mukhtar da Abokinsa Abdallah suna zaune suna kallo”cikin ladabi suka gaidashi ya zauna kan kujera yana danna waya yana satar kallon d’akin In’am”ina *maryam*?
Abinda yafad’a kenan Atak’aice”basu nan itada nafeesa”naji ummi tace”mommy ta Aikesu”shiru yaya Aliyu yayi bece komai ba…ummi ta fito dg cikin kitchen tana cewa”Aliyu kadawo ne?”Eh ummi miye kika girka?”Abinda kakeso ne”yana dining Area ko Aka maka Anan?? Ah ah ummi bara naje can”dato ta Amsa ta koma kitchen”yaya Aliyu yatashi tsaye yanufi dining area yaja kujera ya zauna”haka nan yaji zuciyarsa tak’i Aminta da fitar yaran….bayan yagama cin Abincin yafito yana duba time shidda saura”kan resting
chairs dake bakin k’ofar parlourn ummi Anan ya zauna har shidda ta ida Amma su in’am basu dawo ba”tashi yayi yafita dg gidan yashiga gidansu”kai tsaye part d’in mommy yanufa”yasameta zaune tana azkhar sai yaran zqinab da sukazo musu juma’a suna zaune sunata wasa”(Affan da Amrah)suna ganinsa suka nufesa suna fad’in Uncle! hannunsu yakama ya zaunar dasu Ajikinsa suna masa surutu” mommy dai na murmushi tace”kadawo ne Aliyu?”Eh ina nafeesa?bata nan, tana gidansu k’awar su mai suna sady wai tana bathday yau”shine har yanzun bata dawo ba mommy?meyasama Aka barta taje?”
wlh Aliyu magiya tamun bazatayi dare ba”kuma na mata warning k’arfe 6 ta dawo”to Ai harda maryam suka tafi sun
sanarwa ummi kece kika Aikesu….. innalillahi wa inna ilaihir raju’un! wato dan ubansu k’arya sukamin?”tashi tsaye yyi yana fad’in muddin magrib tayi suna waje jikinsu zai gaya musu”yana fad’in hakan yafita…
Bayan sallar isha’i yaya Aliyu ne zaune samqn farar kujera Awaje dg bakin get”kasancewar Akwai nefa Anguwar k’anyar take da haske”dayake Anguwar quarters ce bbu mutane sai motoci dake wucewa jefi jefi”fuskar yaya Aliyu Ad’aure take kamar hadarin gabas”yana sanye da milk d’in jallabiya”ya hard’e k’afafuwansa d’aya kan d’aya”yadad’e da bak’in tubarau”fuskarsa da Alamar no mutunci”sabon belt na fata na Ajiye Agefensa….yana danna waya yaji motsin wata mota yad’ago kansa yatsare motar da ido…..nafeesa ta zaro ido
A tsorace tana fad’in In’am wlh ga yaya can da Alama mu yake jira”karku damu bara na fita saina masa bayani cewar farooq”nafeesa tayi saurin cewa no ka barshi kawai zamu bashi hak’uri”dg haka taja hannun in’am suka fito dg cikin motar. Tunda suka fito daga cikin motar gaba d’ayan su jikinsu kirma yakeyi”Addu’ar In’am Allah yasa karya dakesu”gashi yadad’e da bak’in tubarau ba’a ganin idonsa…in’am kodai muje gidanku?
“wlh kinsan ummi tsab zata rikeni yadakeni kin sani kema”balle wannan mugun yaya sulaiman d’in shima yana nan”ta k’are maganar Adaidai lokacin dasu farooq ke barin wajen”jiki bbu lakka suka cigaba da doso get d’in gidansu dr Aliyu….tun lokacin da suka fito dg cikin motar yaya Aliyu yatsare In’am da ido k’irjinsa na wani irin bugawa”yana kallon dressing d’in datayi Ajikinta”dukda tun d’azun tayishi Amma ko Ayanzun ba
k’aramin kyau ta masa ba”waye yakawosu??”
ya tambayi kansa cikin tsananin jin zafi da b’acin rai”Atake yaji wani bak’in kishi yataso masa”yatabbatar idan yamik’e tsaye In’am zata iya guduwa”sai kawai ya zauna be tashiba yana ganin motar harta b’acewa ganinsa”kafin yamaida idonsa kan wayar dake hannunsa”kunnuwan sa najin sautin k’arar takalminsu…..yaya sannu da hutawa! cewar nafeesa”banza ya musu yana jin kamar ya fisgo nafeesa sbd itace babbar me laifi
Acikin su biyun”koda nafeesa taga yamata banza sai tayi shiru jiki na kirma suka tura get suka shiga”da hanzari yaya Aliyu ya mik’e tsaye ya d’auki belt d’in yana saka wayarsa Aljihu yashige ciki da sauri”K! ku tsaya”yafad’a cikin kakkausar muryanshi”saida Antar cikinsu ta kad’a”In’am kamar tasaki fitsari a wondo sbd tana masifar tsoron duka”cak suka tsaya basu juyoba….ku biyoni”iya Abinda yafad’a kenan yana yin hanyar part d’in hjy”Atsorace suka fara binsa In’am har tafara k’wallah”
Prince neh
SONE KO K’IYAYYA??
It’s rometic love story
Story & written
by mommyn fareesa
24…
kasancewar dg gidan da Akeyin lallen bbu nisa sosai da gidansu In’am”ko A k’afa zata iya komawa gida”wajen 10 am aka fara sai wajen 12 Aka gama”bata cireba sai k’arfe 3 sannan ta nufo gida”ummi na zaune A parlourn bayan ta gama cin Abincin rana”kasancewar tasan In’am na wajen lalle”saidai dataga ukku tayi bata dawoba ta fara tunanin tura Auwal gidan da Akeyin lallen yaga lafiya?….”
bata gama wannan tunanin ba nafeesa da in’am suka shigo cikin parlourn”ai nazata Acan zaki kwana?kai ummi kin sanfa Akwai zama”hakane kuma yayi kyau”cewar ummin tana kallon hannayen In’am da k’afafuwanta”Abinka da farar mace”sai yayi jajir gwanin ban sha’awa”nafeesa ta zauna ta gaida ummi tana kallon In’am tace”kije kiyi wanka da k’arfe 4 zamuje”ina zakuje?”mommy zata Aikemu”cewar In’am”dato ummi ta Amsa”nafeesa ta tashi ta fita”In’am kuwa dining area ta wuce ta zuba Abinci kad’an taci”sannan ta wuce d’akinta”sallah da wanka tayi kafin ta shirya cikin Riga da siket na lece blue”wanda
Aka musu iri d’aya itada nafeesa”bata d’aura d’an kwaliba” mayafi blue tasaka ta yane kanta dashi”sannan tazura takalmi masu tsini Ak’afar ta” ta rataye hand bag nata Agefen kafad’ar ta”tanata k’amshi tayi kyau har ta gaji”sbd harda make up tayi”bbu wani Aikensu da mommy zatayi wajen bathday d’in k’awarsu sady zasuje”(sit mate d’insu ce) wanda In’am itace tayi k’aryar mommy zata Aikesu”sady kuma d’azun tazo gidan In’am bata nan taka musu card na gayya “shine nafeesa ta sanarwa In’am data dawo…..fitowa in’am tayi har canza tafiya takeyi”Auwal da mahmood na zaune a parlourn suka bita da kallo”Auwal yayi dariya yana fad’in kinyi kyau badan halinkiba”ina zakije?”
ina ruwanka”waike yaya Aliyu yasan zama ki fita ne?”gaban in’am yafad’i”dan ita tama manta da wannan me tubarau d’in karyaji basu gida”Amma data tuna koya tambaya za’a ce mommy ta Aikesu”sai taji nutsuwa”ta shige bed room d’in ummi batare data kula su Auwal ba”bayan tayima ummi sallama ta fita”A waje suka had’u da nafeesa”itama irin kayan in’am ne Ajikinta”yauwa muje mu hau Adaidai ko?”cewar nafeesa”in’am na kallonta tace”kaddai muyi dare kinsan halin su yaya”haba zuwa 6:30 pm haka mundawo kafin magrib”ta fad’a suna tafiya” cikin sa’a suka sami Adaidai ta mik’a su Anguwar jan bulo”bayan sun sallami me nafef d’in suka nufi cikin wani had’add’en gida me farin get”lokacin da suka shigo ciki”wani guy na zaune kan resting chairs shida wani Abokinsa”tunda In’am ta doso wajen yakafeta da ido har suka wuce cikin babban parlourn gidan”
da sauri farooq ya mik’e tsaye yana kallon Abdul yace”Abokina naga matar aure gaskiya”wannan itace daidai dani”raina yabani k’ilan Acikin friends d’in sady suke y’an matan nan”Abdul yace”nidai black beauty d’in can tamun”farooq na murmushi yace”bara na bisu ciki ka jira Anan”yafad’a yana tafiya cikin nutsuwa…..farooq guy ne tun last year yakammala digree nasa yayi service”be wuce age mate d’in yaya sulaiman 30yrs”farooq ya had’u bbu laifi sbd yanada kyau ga kuma kud’i”mata da yawa na cewa suna sonsa yana yarfasu”Amma sai gashi yana ganin In’am duk ya rud’e….. Ahankali yatura k’ofar parlourn yashigo cikin nutsuwa”hannunsa guda yana rik’e da wayarsa kirar iphone 13″gudan hannunsa yana cikin Aljihun wondonsa”gaba d’aya parlourn hayaniya Akeyi sbd cike yake da
friends d’in sady”be kalli ko waceba ya nufi Inda sady take tsaye tana k’ok’arin had’a mp”yaya farooq ga friends d’ina sunzo tayani murnan bath day d’ina”kuma gashi tanimu be zoba balle yafara yi mana pics d’in”ta fad’a tana kallonsa”wasu dg cikin y’an matan suka gaishesa”Amma banda in’am da hankalinta na wajensu farida suna fira”Amsawa yayi yana d’an kallonsu sbd ko zaiga beauty d’in nan”Aikuwa cikin sa’a suka had’a ido da in’am”yadinga kallonta bbu ko k’iftawa”ta d’auke kanta da sauri”ya kalli sady yana fad’in zanje na kirashi ta waya sai yazo ya muku”ina mommy?”tana cikin d’akinta”okay zo muje na baki sak’o”dato ta Amsa ta biyosa”tasha gayunta cikin gownt An mata make up kamar Amarya”ga k’aton cake nata da drinks
Asaman wani table babba”suna fitowa dg cikin parlourn farooq yace”yasunan y’an matan nan guda 2 masu kaya iri d’aya??”d’an murmushi tayi tace”inaga MARYAM YAKUBU da NAFEESA IBRAHIM kake nufi”miye sunan farar?”maryam Anace mata In’am”gaskiya sady tamun babyn ina sonta wlh tunda na ganta”yafad’a yana lumshe ido”sady ta dinga murmushi tana fad’in oh yaya yau wace rana da kanka kace kana son budurwa??”gaskiya naji dad’i zan maka campaign”Amma saika cikamun jakata”karki damu muddin ta Amince nine kawai nasan meye zan baki”ita kuma gudar Abdul na ciki”yafad’a yana murmushi”sady tace”shikenan ta wuce ciki”batayiwa su in’am zancenba”suka cigaba da shewarsu da rawa dayin y’an ciye ciye”sosai In’am ta zage tanata rawa sbd wak’okin na music ne dana kuma Ado
gwanja”sai wajen k’arfe 6 pm Aka fara yimusu pics suda k’awayensu”kasancewar dama hutu Akeyi Anjima ba’a had’uba”gaba d’aya nafeesa da In’am sun shagala sun manta da zancen komawa gida”har Akayi magrib basu luraba”sai bayan Angama pics d’in wasu na cewa zasu tafi sannan in’am ta janye labule ta lek’a window taga dare yayi”gabanta yafad’i ta duba wrist watch d’inta k’arfe 7:45 pm”mun shiga ukku nafeesa! isha’i tayi… Akid’ime nafeesa ta mik’e tsaye tana fad’in tashi muje gida Allah yasa yaya Aliyu be dawo ba”In’am kasa mgn tayi ta mik’e tsaye tana gyara mayafinta”
Prince neh
How To Get Complete SONE KO K’IYAYYA
The most reliable and easiest way to obtain the complete SONE KO K’IYAYYAΒ isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.
You can get the complete SONE KO K’IYAYYAΒ in Portable Document Format (PDF) for just β¦1,000.
JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.
To get your own copy of the complete SONE KO K’IYAYYA booklet, follow these simple steps:
Step 1: Visit theΒ DOWNLOAD LINKΒ to make a payment.
Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.
Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.
Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.
DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE