Download Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 4 Hausa Novel PDF

BOOK ONE
PAGE 14 to 15.

Ayush tana kwance saman gadon Doctor Fatima tin sumar nan datayi bata farfad’o ba,
Abin duniya yabi ya ishi Doc. Fatima itama tana zaune a bakin gadon da Ayush take, tana dafe da goshinta Kai a sunkuye, “Allah yasa dai ba wani abu yaron nan yayiwa yarinyar ba” tana maganar zuci.

“Dodo, wayyo Dodo zai kamani, gashi nan idonsa wani iri, wayyo Allah na, Ku fitar dashi daga cikin gidan nan banason ganinsa”. Ayush ce ta farfad’o tana wannan sambatun

“Lafiya kuwa Ayush meyake damunki ne haka kodai kina tunowa da mahaifiyar ki ne?”. Ta rirri’keta domin taga niyyar ta so take ta gudu tsabar tsoro.

Ayush tana maida numfashi sama-sama kamar wacce tayi gudu
“Wayyo Alhamdulillah, mafarki nayi ashe” ta juyo tana kallon Doc. Fatima gumi duk ya ji’ke mata KO Ina kamar wacce ta fito daga wanka, duk A.C dake d’akin amma ko kad’an bata jin wannan sanyin AC.

Doc. Fatima itama amsa ta bata cewa “e fa mafarki kikayi, ki kwantar da hankalinki ba abunda zai sameki,
Yanzu dai tashi ki shiga toilet kiyi wanka sannan ki ci abinci saina kaiki d’akin da zaki zauna”

Mi’kewa Doc. Fatima tayi tare da nufan gurin da jerin kayanta suke tana fad’in “Bari na za6a miki kayan da zaki saka kafin gobe muje shopping”

Mi’kewa Ayush tayi ta tsaya cak, tana sa’ke- sa’ke a ranta!
Ji tayi ance go and enter mana.

“To inane Band’akin?”. Tayi maganar a shagwa6e.

Murmusawa Doc. Fatima tayi sannan tace “muje na nuna miki abubuwanda zakiyi using dasu”
Tare suka shiga toilet.
Ta bata Brush wanda zata wanke bakinta, ta nuna Mata yanda zatayi using da shower idan tana bu’katar tayi wanka da shi, idan kuma seat-B zatayi duk ta nuna mata, kafin nan ta fito, already ta fitar da kayanda Ayush zata sanya.

Falo ta nufa daga nan ta wuce side din Junaid Wanda tin lokacin da Ayush ta sume masa daga nan ya dafe goshin sa, kan sa ne yad’au zafi sai masifar ciwon da yake yi,
Daman duk lokacin da zai dawo hayyacinsa sai kayinsa da goshinsa sunyi ciwo kafin.
Alluran da Mom d’insa tayi masa da’ace ya juma da yin baccin zai iya tashi cikin hankalisa ba tare da ciwon Kai ba, domin kwakwkwalwarsa ce ta samu Hutu a wannan lokacin,
Ba haka kawai ya tashi daga baccin nan ba
Kwata-kwata bai dad’e da Fara baccin ba ya soma jin qamshin jini mai dad’in gaske da kuma ratsa zuciya,
A cikin baccin yake bud’a hanci yana shan-shane shan-shane, lokaci guda kuwa ya mi’ke daga baccin yana tafe a hankali yana bin wannan qamshin jinin nan kamar Karen da yake bin mushe.

READ ALSO:  Download Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 114 Hausa Novel PDF

Yana sau’ka a up stairs jikinsa ba ‘kwari ga dafin alluran da Doc. Fatima tayi mishi ga kuma qamshin jinin da ya ‘Kara kashe masa jiki,
Ido kuwa like tiger still bai washe ba.
A haka har ya iso daf da Ayush yana bibiyar jinin jikinta, ita kuwa flowers sun d’auke Mata hankali…………..

Tana sumewa a gurin kuwa nan take ya dawo hayyacinsa, ya dawo asalin JUNAID d’insa,
Yana dafe da goshinsa yake bin ko Ina da kallo, kamar komai na gidan ya dawo masa sabo, bai Lura da Ayush dake kwance a ‘kasi ba sai daya juya zai bar gurin sannan kyawawan idanunsa suka sau’ka akanta dai dain lokacin Sucuirity sun shigo falon jin ihun da sukaji itama sai ga Doctor Fatima ta nufo waran da gudu tana fad’in “lafiya kuwa mai yake faruwa a gidan”
Junaid binsu yake da kallo d’aya bayan d’aya still ya maida kallonsa kan Ayush tare da fad’in “Mom! Who’s dis girl?? Yayi tambaya tare da Kai idonsa kan Mom d’insa.

Security kuwa komawa sukayi tinda komai normal Tiger ya dawo Mutum.

Cikin ‘kik’kina Mom take fad’in “am daman marainiya ce, inaso ta zauna damu a gidan nan….
Bata ‘karisa maganar ba taji ya katseta da cewa
“Enough, enough Mom! you known bana son kasancewa cikin mutane, bana son hayaniya, bana son ko wani ‘kazamin mutum ki kawo shi gidan nan….
“Junaidddd!” Mom ce ta Kira sunansa cikin jaaa alamar dakatar da shi,
“Meyasa kake haka ne? Wannan Yarinya bafa house worker bace balle kayi tunanin haka, inason maye gurbin mahaifiyar ta data rasa ne”

Kama qugunsa yayi tare da jan dogon numfashi “koma meye ne, I don’t want her to stay wit us, ki San yanda zakiyi da ita ni dai tabar gidan nan kawai, inaso zanyi bacci”. Ya karasa maganar yana tafiya ya haura upstairs.

Cikin mamaki Mom ta Kira sunan sa “Junaid kana bani umarni ne? Shin Kai ka haifeni ko ni na haifeka?”

Juyowa Junaid yayi yana kallon Mom d’insa daga nesa “Ba Umarni nake baki ba, idan kinason taimaka mata ki tabbatar kin nesanta ta daga gareni saboda karai lafiyarta”.
Yana kai karshe ya kule room d’insa.

Mom girgiza kai kawai tayi domin ba yau ta saba jin haka daga gare shi ba,
Junaid asalin miskilin mutum ne marar son mutane, idan yace baya son abu to kuwa bazai ta6a son abun ba, ga tsirin tsira baya son raini, Mom tasha kawo house worker cikin gidan Junaid yana koransu,
Hakan yasa Ayyukan gidan suke yiwa mom yawa, Gashi tana zuwa hospital ta rasa yanda zatayi,
Junaid baya cin abincin kowa inba ta Mom d’insa ba…

READ ALSO:  Download Complete MAI BAKIN JINI Hausa Novel PDF

Haka Doc. Fatima ta cicci6i Ayush zuwa d’akinta………….

Continue.
Junaid yana a bakin gado da wata er glass table a gaban sa yanata pressing d’in computer yaji ana knocking
“yes coming” ya furta hakan ba tare da ya d’ago kansa ba.
Turo kofar akayi ta shugo ciki tare da mayar da kofar ta rufe ,
“my Son! anata business kenam sarkin danna computer fatan dai kayi sallar Isha’i?”
Tayi maganar a daidain lokacin da ta zauna a kusa da shi.
“Let me finish dis work be4”. Ya furta hakan yana cigaba da Danna computer!
Mom ce ta juya tana masa kallon ‘kurilla cike da mamaki tace “you finish what?? Junaid are you serious? A tunani na Sallah shine gaba da komai”

Download>>> Bakar Inuwa Complete Document

“Oh god! Mom nayi sauran sallolin only isha’i ne banyi ba, shi kuwa lokacinsa baya wuce wa da wuri, kinsan dai bana wasa da ibada na KO”

Jinjina kai Mom tayi “OK! I known that”
In short amsa ta bada.
Daga nan ta shiga nazari tayi shuru kamar mai yin tunanin wani Abu
Juyowa Junaid yayi yana kallon mom d’insa yasau murmushi sannan yace “let me go and pray, naga kamar ranki ya sosu KO?”
Yakai karshen maganarsa tare da mi’kewa ya nufi toilet.
Itama murmushin tayi jin abunda yace.

Ita daman tazo taga lafiyarsa ne da kuma ta bashi hakuri akan yabar Ayush ta zauna da su .

Tayi tunanin ta 6oye Ayush a cikin gidan yanda bazai ganta ba, sai dai duk lokacin da ya gano hakan bazai barta ba saiya hukunta ta, domin ba abunda ya tsana illa a munafurce shi da kuma ‘karya…

Zaman jiranshi tayi har yayi sallar sa ya had’a da lafuloli.
Daga bisani kuma yazo kusa da mominsa ya zaune yana fuskantar ta
“Is there any problem”. Ya furta hakan yana kallon ta.

Murmushi tayi sannan tace “Junaid kana son ganin farin ciki na?”

“Of course Mom” ya bata amsa a takaice!

“Idan kuwa hakane!
Inaso ka saurari abunda zance maka, Nan ta kwashe labarin Ayush ta gaya masa, ita marainiya ce daga asibiti bata San Ina zata nufa ba”
Ta dakatar anan tana kallonsa, so take taji abunda zaice,
Sai dai kuma bataga alamar tausayawa daga fuskar Junaid ba , hakan yasa Tasha jinin jikinta, tasan bazai bar yarinyar ta zauna a nan ba.

READ ALSO:  Download Complete Idan Ba Ke Chapter 1&2 By NimcyLuv Hausa Novel PDF

Download>>> Kadangaruwa Complete Document

‘Dan turo ‘karamin bakin shi Junaid yayi ya kalli mom d’insa ta wutsiryar ido yana yamutsa fuska yace
“Ni fa mom duk wannan tatsuniyar takin ban fahimce shi ba, naji labarin Kwata-kwata bai shafeni ba”

“Junaid please be patient and help her” murya a sanyaye mom take magana.

Juyowa yayi ya kalleta “how comes Zan iya temakan wanda ban Sani ba,
Mom don’t trust any body, yanzu mutane ba abun yadda bane, wani zai iya shugo rayuwarka domin ya cutar da kai, tin Ina yaro na fara ganin yanda rayuwar take, karki ga laifi na don Ina Koran house worker da kike kawowa because House worker ce tayi sanadiyar *MUTUWAR* *MAHAIFINA* mutumin kirki bai aikata komai ba! Wallahi Mom bazan bar kowa ya kusance mu ba, kuma har yanzu Ina kan bakata na d’aukar fansan mutuwar Mahaifina, idan ban d’au fansa akanta ba sai dai bata Raye to kuwa Zan d’au fansa akan *IYALANTA* har yanzu Ina kan bincike na kuma insha Allahu Zan samesu, hukunci na kuma kisa ne ko wa nasamu acikin familyn ta!
Hakan yasa na shiga Aikin *soja* ban damu da ciwon dake jikina ba, nasan Allah ne ya d’ora mun ciwon kuma Ina neman warakarsa”…….

Doctor Fatima ba abunda take sai kuka domin an fame Mata ciwon dake zuciyarta,

Shima kawar da fuskarsa yayi gefe yana ‘ko’karin share hawayen da ya zubo masa…………

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 4

The most reliable and easiest way to obtain the completeMatar Damisa Book 1 Chapter 5 isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Matar Damisa Book 1 Chapter 4 in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the completeMatar Damisa Book 1 Chapter 4booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.