Download Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 10 Romantic Hausa Novel PDF

Download Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 10 Romantic Hausa Novel PDF
{{Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu}}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

{{N W A}}

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

BOOK ONE
PAGE ➡️23 to 24.

Tana cikin nazarin duniya kamar wacce aka zabure ta tayi cikin falo da gudu kamar wanda taga abun tsoro, daga nan ta haura upstairs ta shige d’akin Junaid, da sauri taje gabansa ta tsaya tana ajiyar zuciya! Still a yanda ta barshi anan ta dawo ta same shi, lokaci guda taji wani irin tausayinsa ya kamata ta wani 6angaren kuma tarin tsanar sa ne acikin kwayar idanunta, bata kaunar ganin fuskar shi sunkuyar da kanta ‘kasi tayi tana tariyo lokacin da ya buge mata mahaifiya da kalar wulakancin da ya yi mata itama yaso ya rabata da duniyar a lokacin, zazzafar hawaye ne yake gangaro mata ta d’ago da manya- manyan idanuwanta wad’anda sukayi jawur lokaci guda, kallon tsana takeyi mishi tana maganar zuci “saboda mahaifiya ta zan taimakeka, ba don haka ba ba abunda zaisa na ceci rayuwarka a halin yanzu sai dai ka hallaka! Allah yasa ka mutu” a halin yanzu mutuwar Junaid shine farin cikin Ayushh.
Rufe idonta tayi sosai ta d’ago da hannayenta biyu zata jawo shi, wani irin murya ne mai ban tsoro ya daki dodon kunnen ta

“KEE AYUSH KADA KI KUSKURA KI TA6A SHI, UMARNI NAKE BAKI, KAR KI KARYA MUN DOKATA, YANA CIKIN HUQUBA TA” tan fa ta bara jin kukan namun daji dana mujiyoyi 🦉 cikin firgici da tsananin tsoro yasa ta rungumi Junaid ta ‘kan’kame shi cikin rashin sani,

(Ita da ake bata dokar kada ta ta6ashi amma tsananin tsoro yasa ta rungume shi gaba d’aya) dogon numfashi yajaa tare da d’ago kansa sama ya bud’e jajayen idanuwansa wad’anda suka canza launi tsabar azaba, wani irin sanyi yaji a cikin zuciyar shi kamar wanda aka watsa masa ruwan sanyi, sakin shi akayi daga sama ya tafo luuuu ya fad’a kan Ayush atare suka fad’o ‘kasan lallausar carpet ‘Kara Ayush tayi saboda jin yanda Junaid ya fad’o akan ta ga ciwon breast d’inta da ya fame mata shi!
Shi kuwa sai ‘Kara narkewa yake ya ‘kara ‘kan’kameta, shi yasan kalar nutsuwar dayake samu daga gareta ba tare da yasan ko ita wacece ba, haka yake maida numfashi sama-sama!

Guri kuwa yayi tsitt ba alamar motsi sai numfashin da suke ja a tare.
(Ayush itace samun nutsuwar Junaid, itace kuma samuwar warakar sa indai ta samu rauninsa wanda yake jikinta, in har ta kusanci yanda Junaid yake to babu wani abun cutarwar da zai sameshi, a yanzun mah itace ta ceceshi daga azabar da ake gana masa, domin suma kansu Aljanun tsoronta suke,
Ita d’in dai itace AYANAR JUNAID 🧚‍♀️🧚‍♀️ ).

Dakyarr Ayush ta tattaro iya ‘karfinta ta ture Junaid gefe tana mai da numfashi duk ya kashe mata jiki, ta d’ago zata mi’ke ta nufi yanda yake kwance da rarrafe ta Isa waro ido waje tayi tana ‘kare shi da kallo abun mamaki duk ciwon dake jikinsa babu shi, jikinsa ya koma normal kamar bashi ne wanda akaita azabtarwa ba babu tabo ko ‘kurzune d’aya sai tarin gargasar dake kwance saman kirjinsa,
Abun ba karamin bata mamaki yayi ba aranta take fad’in “Anya ba Aljani bane, nashiga uku nayi gamo” a tsorace taja da baya zata gudu yayi caraf ya ri’ke hannun ta, a hankali yake bud’e idanuwansa yana ganin Dishi-dishi har idon ya washe nan ya sau’ke kyawawan idanuwansa akan ta idon ya washe ya komo fari soll, a hankali yake lumshe ido still hannunsa yana ri’ke da nata a hankali yake motsa ‘karamin bakin shi murya Ciki-ciki yake fad’in “Wace ce ke?” Murya na kakkarwa tace “Ni ni ni ni” ta rasa mai zata ce tsabar tsoro kuma lokaci guda yayi mata kwarjini ga wani shakkar sa datake ji! Tana cikin motsa baki ba tare da yasan mai take fad’i ba ya katsar da ita “please can you carry me to go inside bathroom?”

READ ALSO:  Download Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 5 Hausa Novel PDF

Yayi maganar da harshen turanci, waro Manya-manyan idanuwanta tayi waje tana binsa da kallo, seriously taji abunda ya ce! Duk da batayi karatun boko ba amma ta iya turanci sosai ta koya agurin mahaifiyarta domin Umanta sai data zo Nigeria sannan ta koyi Hausa amma yarenta daga Ghananci sai turanci ta kuma iya yaren French, haka itama Ayush duk ta iya yaren sai dai yaren mahaifinta ne bata iya ba wato fulatanci…….

Ita dai bazata iya maida masa da amsa ba sai dai tayi magana da zuciyarta “How comes Zan iya d’agaka kana nam gardi da Kai, amma sai dai kyakykyawa ne mutumin” tana cikin maganar zuci taji ya ri’kota zai tashi ai tunin ta fad’a jikin shi ‘karfinsa ya ninka nata sau goma 😄
Shima komawa yayi ya kwanta yana binta da kallo, d’agowa tayi a hankali suna fuskantar juna, numfashin su yana dukan na juna, ido cikin ido suke kallon juna! Dakyar Ayush ta iya cewa “you’re a strong man, I can’t……. Kasa ‘karisa maganar tayi sakamakon Breast d’inta dake mata ciwo ga wani feeling da yake shirin kawo mata ziyara duk ya kashe mata jiki shi kuwa babu wani abunda yake ji babu sha’awa a ransa an gusar masa da shi,
Gaba d’aya jikinsa ne yake masa ciwo, shi bai San meya faru dashi ba a tunaninsa duk abunda ya faru dashi mafarki ne saboda ya duba jikinsa babu alamar ciwo…
“I need to bath, please d’agani mana ko na zama gadon kwanciyarki ne” yana magana ne a lokacin da yake shirin tashi…

A kunya ce Ayush ta tashi daga kansa, ita dalilin dayasa ta cigaba da kwanciya masa rad’ad’inda Nononta keyi mata ne yasa ta kifar da kanta saman kirjinsa hakan yasa yayi mata magana.

 

Tashi yayi yana tafiya a hankali zuciyarsa kuwa cike tam da tambayoyi “shin meya same ni haka bana jin dad’in jikina, and than who is dis girl? And what she her doing inside my room in dis midnight?? still ni da nake kwance on my bed meya kaini ‘kasa?”. Haka ya shige cikin toilet yana wannan tunanin!
Itama tashi tayi tana maganar zuci “tabbas wannan shine ya sha’ke mun wuya bayan ya buge mun mahaifiya da mota,

 

 

Anya kuwa yanada lafiya kuwa, Ina tantama akansa wannan ba mutum bane, na ganshi a wani mummunan hali yanzu kuma Gashi lafiyarsa klau ba ciwo a jikin shi Anya ba mafarki nake yi ba..? Shin meye silar faruwar haka..? A lokacin da ya raunana mun breast nabar d’akin normal amma kuma bayar faruwar haka meya faru..? Zanyi bincike akan wannan al’amarin……”
Nufan hanyar fita tayi taji an tsayar da ita “where are you going….?”

Waiwayowa tayi da sauri ta kalle shi fuskarsa a d’aure ba annuri yana d’aure da towel a kunkumin shi alamun ya watsa ruwa ne a jikinsa..
Nufan wurin da take tsaye yayi har sai da ‘karaso gurin da take GAF to GAF suna fuskantar juna ya ri’ke kunkumin sa yana mata kallon tuhuma,
Ganin kallon yayi yawa yasa ta sunkuyar da kanta ‘kasa tana kallon carpet, hannu yasa ya tallafo ha6arta suna fuskantar juna ya ce “who are you…?”
Shuru tayi batace komai ba sai siraran hawayen da ya gangaro mata.

READ ALSO:  Download Yarima Ashman Chapter 5 & 6 Hausa Novel Complete PDF

Sakin fuskarta yayi yana fad’in “can’t took to me..? Okay have a seat” ya nuna mata bakin gado, ya koma gaban mirrow yana Milka jikinsa da cream mai shegen ‘kamshi! Ayush zama tayi a bakin gadon kamar yanda ya umarce ta tana ta sa’ke-sa’ke a raanta cewa “yanzu kenam yana nufin ya manta da fuskata..? Ya manta da matar da ya d’auki raanta…?” Lokaci guda kuwa taji kamar ta sha’ke shi ta baya.. Tana bin duk surar jikinsa da kallo “gaskiya yana da ‘kirar jiki mai kyau, ga tsayi ga fad’i ga d’aurarran jiki ga kuma gargasa ta ko ina a kwance luff-luf gwanin sha’awa sai dai kuma shi baya yabon mace kamar yanda mace take yabonsa bcox baya ra’ayin mace kwata-kwata, bai ta6a jin son mace ko sha’awarta ba haka yake zaune daga gida sai gida ko aiki baya zuwa yanzu….
Ayush fah ta kafa idonta akan Junaid bata San lokacin da take sauwa murmushi ba,

Shi kuwa gaba d’aya ya tsargu da kallon da takeyi mishi , ransa a 6ace ya juyo gareta akaci rashin sa’a jikin mirrow ya Kama towel d’in dake d’aure dashi ya zame gashi bayan towel babu komai a jikinsa .
Ayush tana ganin haka ta zaro ido waje wani irin ihu tayi tabi saman gadon yaraff ta fad’i sumammiya taga abunda bata ta6a gani ba tinda uwatta ta haifeta……. Shi kuwa ihun datayi ne yasa ya bita da kallo bai bi takan towel d’in ba haka ya tsaya zigidirrr yana kallon Ayush wacce ta suma akan gadonsa……..

Su aunty hassana ne suka za6ar mata wadanda zata dinka,,ranar saida Tasha kuka da daddare dan sam ta tsani yah abdallah jininsu bai hadu ba.
Biki yana ta matsowa baifi saura kwana goma ba,Abba ya bawa abdallah wani gidan shi tsakaninsu ba wani nisa,,karamin gida ne mai dauke da falo sai bedroom guda biyu sai kitchen da bandaki a waje da store,,”gidan yayi kyau ba laifi yasha gyara sai kamshin sabon fenti yake da sumunti,ana sati da’ya biki akaje akayi jere shima baba yayi kokari sosai yayi mata kaya masu kyau…..
Falon yaci saitin kujeru,sai kayan kallo da dan karamin frige ,an shimfida center carpet a tsakiyar falon,Masha Allah komi yayi kyau, sai bedroom din guda da’ya aka jera gado da wardrobe da mirror da yake dakin da girmanshi ya cinye komi a wadace,kitchen ma da yake an buga kanta,anyi mata jerenta mai kyau komi dai yayi cikin rufin asiri saidai fatan zaman lpy ga ma’auratan,
Wae kuwa kaje kun tattauna da ummyna kan bikinnan??…ammi ta tambayi abdallah dake kwance kan doguwar kujera a dakinta yana danna waya ,shiru yayi ya rasa abinda zaice, ba da abdallah nake ba??…ta fada tana masa kallon tuhuma, eh ammi….ai zan…zanje,ya fada cikin in ina yana shafa kwantaccen sajenshi..,wai abdallah me yake samunka ne,? ynz badan nayi maka mgnr ba kilan bazaka jeba,wlh ka shiga hankalin ka tun kafin raina ya 6aci inyi maka abinda baka tsammani,zuwan farko ma saida nayi maka mgn saboda kai baka san abinda ya dace ba ko??…to yau din nan kaje kaji abinda take buqata na biki,in ba haka ba kuma wlh tamu ce dakai,kaji na fada maka,tashi tayi ta shige daki ,tana ta mita,,,,
Wayar ya ajiye kan cikin sa tare da lumshe idanu,..gaba da’ya ammin tashi ta canza masa akan wnn fitsararriyar yarinyar..mtss an kusa yin auren dai kowa ya huta kafin nima in nemo wadda nike so ya fada cikin ranshi yana miqewa tsaye,ya fice daga gidan..
READ ALSO:
READ ALSO:  Download Complete A SANADIN MAKWABTAKA Romantic Hausa Novel PDF
Da daddare yaje gidan,ranar ma baa wanye lpy ba gurin zancen😀,daya tambayeta abinda zatayi da bikin kai tsaye tace ai auren so ne akewa hidima ita ba abinda zatayi,, kudin daya bata tace bata so wurga mata yayi ya fice daga dakin yana fadin ta konasu ko ta zubar..wata muguwar harara tabi bayan shi da ita harda murguda baki ta dauki kudin ta shiga gida,,kai tsaye dakin umma ta shiga ta miqa mata kudin ,na menene?umma ta tambaya,, baki a dane ,tace,
“Bani yayi wai in da abinda zanyi, kar6a umma tayi tace to me zakuyi keda kawayenki??,nifa ba abinda zanyi umma,, ban gane ba abinda zakiyi ba??to umma ni me zanyi??… Kada Allah yasa kiyi,fice ki bani guri.
Toh duk abinda aka sawa rana to komi daren dadewa yana nan tafe ,yau ake kamun humaira gidan aunty ramla anan akayi kamun dan yafi kusa dasu sosai,, amarya humaira taci kwalliya,tayi kyau sosai saidai fuskar nan a cukule kadan take jira kamun ma saida aunty asiya taci mata dan da farko cewa tayi ba inda zataje fatima taje ta fadawa aunty asiya,, anyi lpy an tashi lpy.
Washegari akayi walima a wani kangon baba da bai dade da siyaba aka gyara shi sosai..malamai mata biyu su suka wa’azantar tare da fadakarwa kan zamantakewar aure,bayan an gama ne aka rarraba abubuwan da aka tanada na rabo….
Ana gobe daurin aure saqo yazo musu islamiyyar su ta hadawa ango da amarya wata walimar.
Cike filin makarantar yake da mutane,wajen maza daban mata ma daban,sai gefen hagu humaira ce da kawayenta sai daga gefen dama kuma abdallah ne da abokanshi,,sanye yake cikin shadda light ash color da hula kalar kayan sai farin space daya saka hakan ya kara fidda kyawunsa,ita kam sanye take cikin atampa sai akayi sa’a kalar atampar yazo da’ya da shaddarshi,,da kuma hijab din data saka fatima ce takai bakinta kusa da kunnen humaira tace,”kai kawata wlh ba karamin dacewa kukayi da yah sayyadi abdallah ba,ashe duk fadan nan da akeyi na luv ne,, tsaki taja tace a’ah na uban luv ne, dai2 nan suka hada ido dashi saqon harara ya aika mata dashi, ai kuwa batai kasa a gwiwa ba ta maida masa harda murguda baki,, kai ya kada alamun zata sani,,in ka kamani ka kasheni abinda yayi hasashen ta fada kenan.da haka taro ya tashi lpy.

 

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Matar Damisa Book 1

The most reliable and easiest way to obtain the complete Matar Damisa Book 1 isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Matar Damisa Book 1 in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete Matar Damisa Book 1 booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

 

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.