Download Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 114 Hausa Novel PDF

Kafin yaci gaba da cewa”Gaskiya duk wanda yayi silar jefa mu cikin wannan matsanancin tashin hankalin,Sae ya ɗanɗani kudarshi,sai yayi danasanin haihuwarshi da uwarshi tayi acikin duniyar nan,zanso nasan wanene wannan MASTER PLANNER ɗin”

Sannu da jiki suka ƙara Yi ma Abbansu kafin suka juya atare suka bar bedroom ɗin nashi,Matsawa Abba Yayi kusa da Junaid,Zuba mashi ido Yayi yana kallonshi cike da tsantsar so da ƙauna,Ji yake tamkar ya mayar dashi cikin cikinshi,tsananin tausayinshi ne ya kamashi,Rungumeshi yayi ajikinshi kamar jinjiri haka Ya koma,shafa sumar kanshi Abba Ya Soma yi a hankali har zuwa bayanshi,sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi,Jiya haka suka kwana a Asibiti manne da juna saboda firgitar da yake yi,kuma da zarar Abba ya janye jikinshi daga nashi sai ya dinga kiran sunanshi,har sai ya ji shi ajikinsa sannan yake rufe bakinshi,

Bayan fitarsu Sgr daga bedroom ɗin,direct suka wuce Babban Falon gidan Inda kowa Ya hallara Kamar yarda Ya Mu’allim Ya nemi alfarmar Yin magana dasu,A saman Sofa mai mazaunin mutun uku,Sgr tare da Marshal da kanal Yusuf,ɗayar Sofa ɗin itama mai 3 seat,dama 2 sofa sets ne a babban palourn,Ayyan da Jahan ne tare da Irfan suka zauna asamanta,Jabeer da khaleed suna a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu,Alexandra tare da Fawan suna zaune a saman same Sofa,Abusufyan na tare da Ya’ Mu’allim,gaba ɗayansu ne banda wanda suka kwana gidan,
Gyaran Murya Ya Mu’allim yayi tare da cewa”Idan ba damuwa,ina buƙatar ganin sauran da basu hallara ba,”
Miƙewa Fawan yayi dama shine messenger,Duk in wani aike ya tashi jiki na rawa zaka ga Ya miƙe,

Bedroom ɗinsu Sehrish Ya nufa,A ƙopar ɗakin ya tsaya tare da kwankwasa ƙopar,Almost 3 times Yana buga ƙopar,Sae sharar bacci suke yi sun baje saman gado,da yake sun tara gajiya kuma basuyi bacci da wuri ba,
Yana ƙoƙarin sake buga ƙopar yaji an buɗe ta,Tsayawa tayi ruƙe da qugu,fuskar nan a kumbure idanuwan sun ƙankance,Tunkafin yayi magana tace”Ya fawan wai lafiya irin wannan bugun ƙopar ɗakin haka,Sai kace zaka 6alle ƙopar,”
Sai da takai ƙarshen maganar,Ya wurga mata harara,don ya gane wacece acikinsu
“Rasa kunya 6eran tanka,aiko ni akayi,Ki shiga ciki ki sanar dasu cewa ana son ganin kowa a main palour,”

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Murguɗa mashi baki tayi,har ya ɗaga hannu zai make bakin,Sae ga Abu na ƙoƙarin fitowa Jikinta sanye da hijabi,da sauri Ya kawar da hannun,
“Ina kwana Aunty,”abu ta amsa mashi”Lafiya lou,fawan Ashe kun dawo,”
“Eh,bamu jima da dawowa ba,dama An aiko ni ne don in kira ku,Ana son ganin kowa da kowa ne a babban falo,”
“Allah yasa Lafiya,Bari na shiga ciki na tashi jahad,Yanzu zamu fito,”
Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta koma ciki,a lokacin Hosana ma ta shige ciki,
Ɗakin Azmee Ya nufa,Hannu yasa ya kwankwasa mata ƙopar ɗakin,bugun farko yajiyo muryarta tana magana daga cikin ɗakin
“Wanene”?
“Fawan ne Aunty azmee,”
Jim kaɗan ta buɗe mashi ƙopar ɗakin,Jallabiya ce ajikinta ta yafa babban mayafi,Hannunta na ruƙe da Cazbaha,
“Kun dawo kenan Ya jikin Abban naku,”
“Jikinshi da sauƙi Alhamdulliah,”
“Allah Ya tashi kafaɗunshi”
“Ameen,Dama Akwai baƙi a palour,naga baki fito ba,Ko abunsha ne ataimaka a haɗo masu”,
Jinjina kai tayi”badamuwa,gani nan zuwa,”tayi maganar tare da komawa cikin ɗakin,juyawa Fawan yayi a hanzarce Ya koma palourn,tare da samun wuri ya zauna,Shigarshi da minti Biyar,Abu ta fito tare da Jahad suka nufi palourn,Hosana kuma Oummansu ta aiketa Bedroom ɗin Abusufyan don ta kira su Sehrish,

A gefen Mommy,Oumma ta zauna,Jahad kuma A ƙasa ta zauna saman carpet,musayar gaisuwa suka shiga yi atsakaninsu,Bayan sun kammala gaisawa kowa Ya shiga natsuwarshi,
“Sun gama hallara ko akwai sauran wanda baya nan ne”?Ya Mu’allim Ya tambaya,don bayason wani yayi missing discussion ɗin da zasuyi,
“Akwai saura,Amma na aiki Hosana taje ta kirasu,”Abuce ta
bashi amsa,Lokacin da Hosana ta kutsa kai ɗakin,A baje ta samu Sehrish da Amrish suna bacci,saman gadon ta hau tare da sanya hannunta tana bubbuga ƙafafunsu”Wai bazaku tashi ba!”shiru ba wadda ta motsa acikinsu,

Bubbuga ƙafafun nasu ta kuma yi”wlh ko ku tashi,Ko in ɗebo ruwan sanyi in watsa maku,”jin wannan maganar yasa Sehrish ta buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci,koda tayi arba da fuskar hosana nan take ta ɗaure fuskarta,A ƙule tace”Lafiya’?
“Nima bansani ba,Oumma ne tace na kira mata ku,Ana son ganinku a palour,”
Takai ƙarshen maganar tare da saukowa daga saman gadon ta fice daga ɗakin tana ƙara jaddada masu akan su fito,

Atare da Amrish suka fito daga ɗakin hannunsu ruƙe dana juna,tunkan su ƙaraso Sehrish ta hango Sgr dake gefen Kanal Yusuf ya lumshe idanuwanshi,kamar mai jin bacci,da alama Jiyan nan baiyi bacci ba,ko bai samu isasshen bacci ba,

Ƙarasawa Cikin palourn su kayi,A nan saman Carpet gefen Jahad suka zauna suma tare da lankwashe ƙafafuwansu,

Ɗagowa Ya Mu’allim yayi tare da binsu da kallo,kafin yace”Akwai saura ko su kenan”?
“na kira Aunty Azmee,Yanzu zata zo itama,”Fawan ne ya bashi amsa,Duk sun ƙagara suji abunda Ya Mu’allim ke son sanar dasu,

Saukowa Azmee tayi daga 3 steps na fitowa daga Corridor ɗin ɗakunansu,bata nufi falon kaitsaye ba,kitchen ta nufa,after few minutes ta fito hannunta ruƙe da faffaɗan tray saman shi glass cups ne,Wanda ta shirya masu abunsha ciki,

Jin takun takalmanta ne Ya jawo hankalinsu,tana ƙarasowa wurin sofas ɗin da suke zaune,Kamar ance ta ɗago karaf Suka haɗa ido da Ya Mu’allim,A gigice Azmee ta saki tray ɗin hannunta Wani irin sauti suka bada ji kake fass fass tatass Glass Cups ɗin suka faffashe,ganin haka yasa kowa Ya shiga tambayarta Lafiya,kasa buɗe baki tayi don tayi magana,gaba ɗaya duk tabi ta firgice ta rasa natsuwarta,Da gudu ta juya zata bar wurin Ya Mu’allim Ya daka mata tsawa”Karki kuskura kice zaki bar wurin nan,idan har kika ƙara ɗaga ƙafarki a wurin nan,Saina sa6a maki,”Cak ta tsaya lokaci guda wata irin Zufa ta shiga wanke mata fuskarta,

Abun ya ɗaure masu kai,har suna haɗa baki wurin tambayarshi A ina yasan Azmee?,
Miƙewa tsaye Ya mu’allim yayi tare da nuna ta da yatsan hannunshi”Wannan itace Silar duk wani hali da kuka shiga acikin gidan nan!”
Saboda tsabar firgitar da su kayi gaba ɗaya suka miƙe suna kallonshi,
“Anya kasan me kake faɗa kuwa?Wannan fa Azmee ce,me aikin gidanmu,kusan Shekara Ashirin tana Yi mana aiki,”kanal Yusuf ne yayi maganar,

“Kodai tayi maka kama da wadda ka sani ne”?acewar Irfan,
A tsanake Ya mu’allim ya soma magana”Niko nasan Azmee farin sani!Ku ne baku santa ba,Wannan matar da kuke Gani,Mushirika ce ƴar qungiyar asiri”,
Hankali A matuƙar tashe Suke kallonshi,Duk basu kaiga yarda da maganarshi ba,
Azmee kuwa tuni ta ɗaura hannu asaman kanta,Tunda Ya Mu’allim Ya fallasa cewa ƴar gungiyar asiri ce ita,tasan cewa Alƙadarinta ya karye!A ƙa’idar ƙungiyarsu daga inda wani Yasan sirrinka shikenan ƙarfin sihirinka zai naƙasa…………”

Download>>> Miji Nagari Burin Ya Mace Complete Document

“Kinji haushin rayuwarki!Muguwa azzaluma,dama Alƙawarine na ɗaukarwa kaina saina Tona maki asiri,koda kuwa zakiyi silar mutuwata ne,balle kuma ke baki isa ki kawar dani ba,”

Kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu,Kowa yasha jinin Jikinshi,
Hankali atashe Mommy tace”Don Allah ka fahimtar damu,”

Cigaba da magana yayi”nasan ba lalle ne wasun ku su gane ni ba,Amma mahaifinku zai iya tuna fuskata,Ni ina ɗaya daga cikin malaman da aka ɗauko don su koyama Junaid karatu lokacin yana yaro,A lokacin Mahaifinku Ya faɗamun cewa duk malamin daya ɗauko don ya koya mashi karatu,tun arana ta farko idan Yazo bai ƙara dawowa,Abun Ya ɗaure mun kai,farkon haɗuwata dashi A masallaci ne,Ta dalilin yabona da mutane keyi ne ya jawo hankalinshi akaina,harya jani gefe yake sanar dani game da ɗanshi da yake son indinga zuwa ina koya mashi karatu,

A ranar dana fara zuwa gidan nan koya ma junaid karatu,A garden muka zauna dashi in ban manta ba,Saman darduma ne muke zaune dashi,Idan inayi mashi karatu sai ya ƙura mun ido yana kallon bakina kamar yana fahimtar abunda nake cewa,Ashe kwata kwata bai ganewa ne,Abun ba ƙaramin ƙona mashi rai yake yi ba,a ƙarshe sai ya fashe mun da kuka yana cewa shi baiso ana zuwa yi mashi karatu tunda ba ganewa yake yi ba,Wahalar dashi muke Yi,naji tausayinshi sosai a wannan lokacin,Na kuma Yi mamakin yarda bai gane karatun al’qur’ani,sanin cewa Ƙaramin yaro yafi ɗaukar karatu a lokacin ƙuruciyarshi,

Amma shi ko Bismillah wuyar faɗi take yi mashi,Idan na matsa mashi akan yayi karatu da zarar ya buɗe baki zai amsa karatun da nake biya mashi,kwatsam sai inga ya sanya hannu ya toshe kunnuwanshi,La66anshi na kerma,wani lokacin kuma sai inga yana ruƙe maƙoshinshi,tundaga nan na sanya ayar tambaya akanshi,bayan na koma gida,Yini nayi da tunanin Junaid,Saboda Yaron akwai shiga rai,Ya kwantamin araina sosai,a daren ranar,wuraren ƙarfe 1 na dare aka kira wayata Ana yi mun barazana akan karna kuskura na ƙara zuwa koya ma junaid karatu idan ba haka ba zan rasa raina ne,duk da haka ban daddara ba,A washe garin ranar na kuma dawowa koya mashi karatu hada ruwan Zam Zam na addu’a nazo mashi dashi don yasha,ruwan Addu’ar yana karya sihiri duk mun ƙarfinshi in akayi ma mutun in ba wani iko na Allah ba,Aranar nayi ƙoƙarin na bashi yasha ruwan addu’ar nan amma wani abun mamaki daga nayi yunƙurin kafa mashi ruwan a bakinshi don yasha Sai kawai inji an buge mun hannuna,tun daga nan na ƙara yarda cewa akwai sihirin ajikinshi,Sae na fara tunanin yin bincike akan Wanda ke sarrafa kwakwalwarshi,domin in taimakeshi,Akwai wata rana Da Azmee ta kawoshi da hannunta,A ranar na gane cewa itace ke sarrafa shi,Allah yayi mun baiwar gane mutun mai sihiri da zarar mun hada ido,ta kalle ni na kalleta,Bayan tafiyarta nake tambayarshi Wacece ita,ko mahaifiyarshi ce?Sai ce mun yayi Eh,Mamansu ce,banyarda da maganarshi ba a lokacin saboda sam babu kamanceceniya a tsakaninsu,Hasken yaron ba irin nata bane,ko irin kama ta jini babu atsakaninsu,da na tsare shi da tambaya sai yake cemun mamanshi bata nan,kuma bata sonshi ta tafi tabarshi,Sai tausayinshi ya kamani,Bayan na koma gida na shiga zurfin tunani akanshi,Abunda ya tsayamun araina shine meyasa mahaifiyarshi ta tafi tabarshi?Wacece wannan matar dake sarrafa kwakwalwarshi,Meyasa take son juye mashi tunani don karya gane karatu,Na nace akan son sanin dalilinta na yin hakan,Gashi bansan wa zan tambaya ya bani amsa ba,matasan gidan kuma ba gwanayen son magana bane,Gasu sojoji in nace zan tambayesu ba dole su fahimce ni ba,Zasu yi mun wata mummunar fahimtar ne,akwai wata rana da muka haɗu da mahaifinku a lokacin na kammala Koya mashi karatun ranar,Shi kuma ya dawo daga wurin aiki,Na ƙarasa muka shiga gaisawa dashi har yake ce mun in shigo daga cikin gidan muci abinci atare,Dayake mutun ne shi mai son jama’a,baida girman kai ko kaɗan,Yana da kyakkyawar zuciya,Banyi niyyar shiga cikin gidan cin abinci ba,Amma tunawa da binciken da nakeso nayi saina Yanke shawarar binshi,

READ ALSO:  Download Complete Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 91-95 By Asma Baffa Hausa Novel PDF

Download>>> Anya Baiwa Complete Document

Lafiyayyen Abinci Azmee ta shirya mana tare dashi,a lokacin in ban manta ba,Hada waɗannan tagwayen guda biyu,ko gaishe ni basuyi ba lokacin,Dama tunda na kallesu nagane cewa suna da girman kai,wani kallon ƙaskanci suke yi mun,Amma wani abu dana hasko shine,Hasken fatarsu irin na Junaid ne,Sai na fara tunanin kodai cikin Iyayensu akwai jinsin turawa ne?Saboda ƙwayar idon ɗaya daga cikinsu,muna cikin cin abincin Sai naji ɗaya na tambayar Abbansu,na kasa kunne ina sauraronshi,
“Abba,har yanzu Mommy bazata dawo ba”?Sai Abbanku Yace”bana tunanin zata dawo da zama Nigeria,
Sai naji yaja dogon tsoki yana cewa”Gaskiya batayi mana adalci ba,kodan saboda Junaid yakamata ta dawo taci gaba da kula dashi,Ni bana so Azmee taci gaba da rainonshi…..”bai kai ƙarshen maganarshi ba sai Abbanku yayi mashi tsawa,nan take yaja bakinshi yayi shiru,bayan mun kammala cin abincin,Na shirya tafiya mahaifinku yayi mun jagora a lokacin ko abun hawan kaina ban mallaka ba,A ƙafafuna nake yawo,ko in hau abun hawa,to a lokacin shima yana da wani uziri a waje,Sae yace mun in shiga motarshi su rage mun hanya,

Muka shiga motar atare,Driver ɗinshi Yaja motar muka fita,A cikin motar ne,na soma ƙoƙarin bugun cikinshi,
“Na lura kamar akwai damuwa akan fuskarka,”sai yayi ƙoƙarin 6oye damuwarshi yace mun bakomai,

Sai na canza maganar nace”Maganar Junaid Alhaji,Yau mahaifiyarshi data kawo mun shi daƙyar ya tsaya,Yana ta kuka sai ya bita,”Nayi mashi zancen junaid ne don na lura ba ƙaramin son Yaron yake yi ba,indai kanason kaga fara’arshi toh kayi mashi maganar Junaid,
Nan yake ce mun ae ba mahaifiyarshi bace,Mommynshi bata a ƙasar tun lokacin da ta haifeshi tabar ƙasar,Wannan matar dana gani mai aikin gidan ce,Itace ta shayar dashi,sun shaƙu sosai,Ya saba da ita baison rabuwa da ita,iya haka ya tsaya mun da bayani,Bai faɗamun dalilin dayasa Mahaifiyarshi tabar ƙasar nan ba,batare data ƙarasa shayar dashi ba,Ni kuma a wannan lokacin na samu abunda nakeso,bayan sun sauke ni a gida,Yinin ranar da tunanin maganganun mahaifinku na kwana,Saboda yarda nasa ma raina junaid har mafarkinshi nake yi,Dana zauna nayi nazari sosai,Sai na hasasho wani abu game da Azmee,tabbas akwai wata mummunar manufa dayasa take zaune a gidan,In ba haka ba meyasa zata Juye mashi kwakwalwarshi?Saboda yaron yana da kaifin basira!he’s genius,irin yaron nan ne masu wayon tsiya,Gifted Ne shi,ita kuma Azmee ita ke rainonshi dole zai iya kasancewa A ɗakinta yake kwana,koda yaushe yana manne da ita,duk wani surkulle da zatayi agabanshi take yi,Tanajin tsoron kada Ya tona mata asiri,that’s the reason Why Ta toshe mashi kwakwalwarshi Ta yarda bazai Iya gane komai ba……….”

Download>>> Sexxy Boss Lady Romantic And Comedian Novel Complete Document

Gaba ɗaya hankalinsu Ya tashi haikam,Musamman Sgr da Mommyn Junaid,Jikinsu har tsuma Yake yi,Su kanal Yusuf kuwa sun shiga ruɗani sosai,Abun yafi ƙarfin tunaninsu,Har yanzu basu samu ƙwaƙƙwarar hujjar da suke son samu ba,Farat ɗaya bazasu fara Accusing ɗinta ba,

Azmee kuwa tuni ido ya raina fata,Jikinta sae kerma yake yi,Ta gaza buɗe baki tayi magana,binsu kawai takeyi da ido,

Cigaba da magana Ya mu’allim yayi”A lokacin sai tafiya ta kamani zuwa ƙasar Egypt,scholarship na samu don ƙaro ilimin addini acan,ba don naso ba haka na kwasa nabar ƙasar nan,cike da tunanin Junaid,Tsorona kada kafin in dawo Nigeria,Azmee tayi silar mutuwarshi,tunda ta fara zautar dashi,

bayan tafiyata ƙasar egypt,duk da bana a nigeria,ina samun Labarin halin da Junaid ke ciki,Duk in mukayi waya da mahaifinku yana sanar dani,Har na samu labarin ciwon Shi daya tashi har akayi mashi aiki a ƙirjinshi,Lokacin nashiga damuwa sosai,Saboda ni nasan cewa Junaid baida ciwon asthma,Lafiyayyen mutunne shi,Wannan ciwon asthma ɗin duk aikin Azmee ne,itace ta sanya mashi ita,duk don saboda kada yayi Lafiya,domin kuwa lafiyarshi zai iya jaza mata matsala,ta ko’ina ta hanashi sakat,ta mayar dashi tamkar soko,Yanayin wasu abubuwan irin na mata bayan shi namiji ne,kuma tundaga kan Iyayenshi da yayyenshi babu wani rago acikinsu balle ace ya ɗauko wani daga cikinsu ne,kuskuren da kukayi shine,

Yarda da Azmee ta shayar dashi,Tabbas kun tafka babban kuskure na Yarda da ƴar aiki ta shayar maku da ƙaninku,Sauke ajiyar Zuciya Ya Mu’allim Yayi kafin ya ɗaura da cewa”Bayan wasu shekaru Allah yayi na dawo Nigeria,A lokacin bansan wani hali ahalinku suke ciki ba,Domin kuwa nadaina samun mahaifinku a waya sakamakon Rasa wayata da nayi wadda nake da saving ɗin Layinshi aciki,lokacin dana dawo mahaifinku Ya samu karin girma a wurin aiki,Na chief of army staffs,Hakan yasa gidanku Ya ƙara tsaro sosai kuma mahaifinku yayi wuyar gani,Har zuwa saida nayi amma Sojojin dake gadin gidan suka hanani shiga ciki,saboda banda shaidar da zasu Iya barina na wuce,kusan sau biyar ina zuwa amma bansamu shiga ciki ba,A ƙarshe na haƙura da zuwa gidan,

Ana haka,Na samu koyarwa,A makarantarsu wannan Yarinyar,Yayi maganar yana nuna Sehrish dake atsaye,
Kullum naje koya masu karatu sai inga yarinyar nan tana ta sharar bacci abunta,Sae kace ba karatu tazo ɗauka ba,Abun saiya ɗaure mun kaina har rannan na tanka sai yan ajin suka sanar dani haka take,duk in ana karatu sai tai ta bacci,jin haka yasa naje har seat ɗin da take zaune na tasheta daga bacci ta miƙe tana mutsuttsuka idanuwanta,Kallo guda nayi mata na gane cewar akwai matsala atattare da ita,Nace mata ta ɗago ta kalleni,Taƙi yarda mu haɗa ido,Ni kuma a lokacin inaso in gani idan akwai Jinnu ajikinta,Don naji ajikina cewa ba ita kaɗai bace,Dana tambayeta a wani gida take ne,Sae take sanar dani cewa ita Ƴar family ɗin SALAHUDDEEN HOSSEIN ce,Inajin hakan sai na gane cewa Ƴar uwar Junaid ce ita,tunda sunan mahaifinshi ne,kuma naga kamanninshi a fuskarta,

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

Tunda naji hakan sai na gane cewa Har lokacin Azmee na acikin Family ɗinku,Kuma ina tunanin itace ta shiga jikin Yarinyar tayi mata sihiri,ban tabbatar da zargina ba,Kawai na yanke shawarar in bata wannan ruwan addu’ar na zam zam,Ta hanyar ƙawarta Amrish gata nan a gefenta,Ita naba ruwan zam zam ɗin acikin robar ruwan donta ba Sehrish tasha,Har nace ta sanar da ita cewa idan bata sha ruwan ba,ƙusumbi zai fito mata abayanta ne,Nace haka ne don ta tsorata tasha ruwan,in ba haka ba nasan daƙyar ne tasha ruwan,To ni bansan tasha ruwan Addu’ar ba,ko bata sha ba……”ya dakata da maganar yana kallon Sehrish,hankali Ya koma kanta,.
Daƙyar ta iya buɗe baki tace”A’a bansha ba,Nazo dashi gida,Amma na neme shi na rasa,A lokacin nayi tunanin ko Junaid ne Ya ɗaukeshi saboda shikaɗai ne ke zuwa ɗakina,daga baya ban ƙara tada maganar ba,

Tunda ta soma magana Ayaan da Jahan ke kallon Juna,saboda sun gane cewa Wannan ruwan da suka sha ne,Har suka samu warakar Cutar dake damunsu,Na neman juna da suke yi,

Da sauri Ayaan yace”Ni na ɗauki Robar ruwan acikin fridge,bansan waya kaita ba,Amma nida Jahan ne muka sha ruwan…….’anan Ayaan ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar dasu,Bai 6oye masu komai ba game da homo sex ɗin da suke yi shi da Jahan,Saboda ƙwarin guiwar da suka samu ayanzu,
“Yanzu haka robar ruwan,Tana a hannun Jahan,Shiya 6oyeta saboda muyi bincike akan wanda ya kawota cikin gidanmu,Ashe Sehrish ce ta shigo da ita,”
Kallon Jahan Sgr yayi”inason ganin robar ruwan da kuka sha,”da sauri Jahan Ya nufi part ɗinsu,

READ ALSO:  Download Complete Furar Danko Chapter 4 By Billyn Abdul Hausa Novel PDF

Tashin hankalin da ba’a sama shi date,Gaba Ɗaya idanuwan ko wannansu na akan Azmee,Duk tasha Jinin jikinta,After some minutes Saiga Jahan ya dawo hannunshi ruƙe da bottle water ɗin,mai rubutun Larabci ajikinta,

Miƙa ma Sgr yayi,Bayan ya kar6i robar ya kalli Ya Mu’allim”Itace wannan”?
Jinjina kai Ya mu’allim yayi,”ƙwarai kuwa itace wannan,idan kana jin harshen larabci ka karanta rubutun dake ajikinta,Zakaga Bayanin da take ɗauke dashi na karya sihiri,”
A fili Sgr ya karanto musu Larabcin dake rubuce a jikin robar,kafin Yayi masu translation ɗinshi,kowa Yaji a kunnanshi,

Download>>> Doctor Eesah Complete Novel

“Tun daga ranar da muka sha ruwan nida Jahan bamu ƙara neman junanmu ba,mun samu sauƙi,dama kullum cikin fargaba muke,Allah shikaɗai yasan irin raɗaɗin da muke ji acikin zuciyoyinmu,Saboda munsan cewa aikata homo babban zunubi ne wanda ubangijinmu Allah Ya haramta yinshi,Ga kuma tsoron hukuncin da za’a yanke mana idan aka kamamu muna yinshi,”idanuwanshi cike tab da kwalla Yayi maganar,

Tuni guiwowinsu sun sage,Zuciyoyinsu sun karaya sosai,
Cikin sanyin murya Kanal Yusuf Ya soma Yi mata magana”Aunty Azmee dagaske ne duk wannan Abun da malamin nan Ya faɗa akanki?Amsarki kawai muke son ji,”
“Amma in har dagaske ne,Azmee kin gama da mu,Kin cuce mu,kin zalunce mu,Laifin me muka aikata Maki?da har kika shigo cikin rayuwarmu,Tsawon Shekara ashirin kina yi mana aiki,”Acewar Jabeer,

Ganin taƙi basu Amsa yasa Sgr Ya daka mata tsawa har saida ta firgita,
“Zaki buɗe baki kiyi magana!ko kuwa saina sa kinyi”?

Maimakon ta bashi amsa,Saita rufe idanuwanta ta soma karanto wasu zantuttuka cikin wani harshe mara daɗin ji,Zuba mata ido sukayi suna kallonta,Watsa hannuwanta tayi saman iska tana kaɗasu,

Murmushin takaici Ya Mu’allim Ya saki tare da cewa”Kada ki wahalar da kanki AZMEE,Domin kuwa Allah Ya rigada ya kamaki,Sihirinki bazaiyi aiki ba A yanzu,”

Buɗe idanuwanta tayi akan fuskarsu,Duk a tunaninta tayi masu layar zana,Basu ganinta hakan yasa ta saki murmushi tare da juyawa zata kama hanyar fita daga falon,Wani irin kukan Kura Alexandra tayi tabi bayanta da gudu ta damƙo wuyan Jallabiyar jikinta da ƙarfin gaske ta wurgota,A sukwane goshinta Ya daki ƙasan tiles,bugu ta shiga kai mata,shaƙo wuyan rigarta tayi”Bazaki buɗe baki kiyi magana ba,”rai a matuƙar 6ace Alex ke magana,
“Dama ni ban ta6a yarda dake ba AZMEE,I have been accusing you for a very long time,Nayi shiru ne saboda banda hujjar da zan kamaki,”
Daƙyar Abusufyan yashawo kan Mommy ta rabu da ita,
“Kodai kiyi mana jawabi da bakin ki ko kuma musa kiyi,”

Motsi ta soma yi da la66anta,Yayin da idanuwanta ke kallon fuskokin kowannansu,lokacin da suka haɗa ido da Sehrish saita fashe da kuka,ita kanta sehrish ɗin hawaye ne sharkaf akan fuskarta,
Hannu tasa tana goge jinin da Mommy ta fitar mata agefen bakinta,
Lokaci guda idanuwanta suka canza sosai,Suka yi jawur tamkar garwashin wuta,

Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel

Duk wannan abun dake faruwa akan idanuwan Abbansu,Wanda ya jima da fitowa,Bawan Allah ya girgiza da jin abunda suke tattaunawa,ƙarasowa Yayi wurinsu daƙyar yake jan jikinshi saboda rashin ƙarfin jikin da babu,
“Na kasa yarda da abunda kunnuwana suke jiye mun,Azmee dagaske kece kike son ɗaukar fansa akan ahalina?Laifin me suka yi maki?Me Junaid Yayi maki da kikeson kashe mun shi,Idan ma fansar ce zaki ɗauka meyasa ni baki kashe ni ba,Sai Ƴa’ƴana kawai”?fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yayi maganar,

Girgiza kai Azmee ta shiga yi kafin ta soma magana,
“Da ace inason kashe ɗaya daga cikin ƴa’ƴanka,Wlh da yanzu na jima da shafe Babinku a doron duniyar nan!Dama nawa na samu?Meyasa ban sanya guba acikin abincin gidan nan kowa yaci mutu ba?Tabbas Dama nasan wannan ranar zata zo,Nikaina na jima ina jiranta,Banzo gidan nan don inyi maku aiki ba,Nazo ne don in ɗauki fansar kashe mun Iyayena da kukayi da kuma Mijina,Kun jima kuna cin zalin danginmu amma bamu ta6a ɗaukar mataki ba,Kun tarwatsa mana farin cikin Zuri’armu Yayin da ku Kuma kuke rayuwarku cikin Farin ciki….,

Wacece Azmee?

Azmee cikakkiyar bafullatana Ce ƴar jihar Gombe state,asali garinsu daga ruga ya fara kafin a hankali ya zama gari,A tsakanin family ɗinsu da family ɗin Salahuddeen basu Shiri,faɗansu tun kaka da kakanni ne,Dama tsakanin family ɗin soja da family ɗin Masu tada ƙayar baya a kasa basa jituwa,faɗan nasu ya fara tun daga kan kakanninsu,Kaka wanda sunan kakansu ne kuma dashi ake yi masu inkiya amatsayin sunan family ɗinsu,Kaka Mugun mutunne wanda ya gagari kowa hakan yasa al’ummar dake kewaye dashi Ke tsananin tsoronshi,Matsafin gaskene a wurinshi duk suka gado wani tsaface tsafacen da suke Yi,Sun kasance wasu irin mutane marasa buri a rayuwarsu,Mugunta kawai sukasa a gaba,Kuma abunda zai baka mamaki Suna da ilumin addinin musulunci,Da yawansu Mahaddatan Alqur’ani ne,Suna Yin iliminne ba don komai ba,Sai don su kawar da idanun mutane daga kansu,Don Tafiyar da rayuwarsu batare da jama’a sun zargesu ba,Kuma suna yin amfani dashi wurin Gudanar da sihirinsu,Dama ance in mutun ya 6ace ya 6ace kenan,Sae wani iko na Ubangiji,Sun tsunduma tsulundum wurin aikata shirka,Zubda jinin al’umma da kuma Yin amfani da Mutane wurin yin tsaface tsafacensu,A zamanin kaka,Salahudeen shi ne Ya kawo ƙarshen tawagarsu ta matsafa,Sunyi nasara akansu wurin ruguza ƙungiyarsu,Tundaga wannan lokacin Suka zama abokanan gaba,Salahuddeen Ya kafa dokar duk inda akaga ɗaya daga cikinsu yana yawo nan take A yanke mashi hukuncin kisa,Suma haka su kaka suka sanarwa jama’arsu da zarar sunga Jinin Salahudeen Su kashe shi,Kisan wulakanci,ya kasance suna farautar junansu,A lokacin da su salahudeen sukayi nasara akansu,Saida suka ƙarar da rabi da kwata na jama’arsu,Kuma a wannan lokacin suka kashe Kaka har lahira,sunyi tunanin sun gama dasu ashe akwai sauran runa akaba,Kaka ya mutu yabar ƴa’ƴanshi,Wanda bayan mutuwarshi,su kuma suka tada ƙungiyar,suka cigaba da aikata munanan laifuka acikin ƙasa,Nan fa su salahudeen suka bazama neman inda suke shirya maƙarƙashiyarsu,Babban danshi ne ya amshi mukamin mahaifinsu kaka,Sunanshi Ubaid Hatsabibine harya fi Ubanshi kaka,Su biyu kaka Ya haifa dashi da ƙaninshi Wanda suke Kira Uba,Dukkansu Mugayene Basu da Imani ko misƙala zarratin,Shan jini ya zama ruwan dare a wannan lokacin,cire sassan jikin ƴa’ƴan mutane abun ba’a magana,Sai dai kawai a tsinci gangar jikin mutun an cire wasu Organs na jikinshi,Abun Ya tashi hankalin Al’umma,Zama baiga su salahudeen ba,Nan fa suka Bazama neman waɗannan hatsabiban guda biyu,Ubaid da Uba,Yadda kasan aljanu haka suke,Baka ta6a ganinsu cikin jama’a,Sai Lokacin Sallah,Ubaid ma Shike jan Sallah a babban masallacin Yankinsu,Babban limaminsu ne,kuma babban Malamin addini ne,Baka ta6a gane halinshi inba gani kayi ya aikata agabanka ba,Fuska biyu ne shi,A fuska musa azuci fir’auna,a yadda mutane suka sanshi,Mutumin kirki ne,Mai tausayi ga son jama’a,Yafi kowa Iya kiran sunan Allah,Idan Ya hau mumbari zaiyi wa’azi sai ka sha mamakin yarda yake kuka Yana kira ga mutane su Koma ga Allah,shu’umin mutunne mai wuyar sha’ani,Ƴa’ƴanshi Biyu Gali shi ne babban ɗanshi,Sai mai bi mashi mace ce Wadda suke kira da Saratu,Ƙanin mahaifinsu Uba shima Ƴa’ƴanshi Biyu,Babbar ƴarshi itace Azmee,Mai bi mata kuma Namiji ne,Wanda suke kira da Sayyad wato Ya sayyadi.

Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document

tundaga kan Iyayensu maza har matan Mugayen mutanene,Mushirikai,Tun daga kan kakanninsu ne abun Ya fara,Sai wanda Allah yaso acikin zuri’arsu yake zama na gari,kamar Azmee duk acikin ƴa’ƴansu itace bata ɗauko mugun hali ba irin na sauran,Hasalima batasan me iyayensu ke aikatawa ba,Mace ce mai tsananin son addini,Kamilar gaske,Tun tana da shekara goma sha Biyar a duniya ta haddace alqur’ani mai girma,Saratu kuwa ƴar wurin wan mahaifinsu jakkace,bata gane komai sai Iya mugunta,

Ana haka Azmee ta fara soyayya da wani bawan Allah,Wanda Ya ta6a taimakonta,akan hanyar dawowarta daga islamiyyar dare,Wasu ƴan iska suka biyota suna ƙoƙarin yi mata fyaɗe,A wannan lokacin wani matashin saurayi ƙakƙarfan gaske ya riƙesu sun kewayeta,Haɗa kawunansu yayi ya dinga bugu sai da yayi haɗa masu jini da majina,Sannan Yace ta sanya hijabinta suje ya rakata gidansu,A ƙopar gidansu yayi sallama da ita,Tunda ta koma gida ta kasa runtsawa saboda tunanin bawan Allahn nan daya taimaketa,tun adaren ranar ta kamu da tsananin sonshi,so bana wasa ba,

Saboda shi kullum sai taje islamiyar dare,tunda ta gane cewa hanyar dawowarshi ce,duk in suka haɗu saiya rakata har gidansu sai ya tsaya yaga shigarta kafin shima ya wuce gidansu,Soyayya mai ƙarfi ce ta shiga tsakaninsu,sam batasan asalinshi ba,Abu ɗaya kawai tasani akanshi yana da kyakkyawar Zuciya,

Tun tana 6oye ma Iyayenta soyayyarta dashi har suka fara lura da yadda Azmee ke yawan ambaton sunanshi Jabeer,ko bacci take yi sai ta dinga sambatu tana ambaton sunanshi,Sa6anin da in tana bacci karatun haddar da aka basu ne zaka ji tana biyawa a bakinta,

Da iyayensu maza suka gane cewa tana son wani bare ba danginsu ba,Sai suka gargaɗeta akan ta rabu dashi,In ba haka ba zata ja mashi ne,su sunfi son suyi mata auran zumunci dama kuma Family ɗin kaka basu auren bare,Yasu yasu ne,ita kuma ta tsani Wanda suke son su haɗa ta dashi,Ɗan wurin Ubaid ne yayan mahaifinta,Wato Ghali mugun mutunne kuma Arne ne shi,Sunan yana musulmi ne ko sallah baya yi,a lokacin taƙi jin maganarsu ta kangare,Aikuwa mahaifinta Uba yasa aka ɗauko mashi Jabeer,A wani kogon dutsi suka Rufe shi,Anan suke gana mashi azaba,duk don su raba ta dashi,kwana biyu da azmee bata sanya shi a idanuwanta,Ko abinci tadaina ci a ƙarshe ciwon zuciya yakusa kamata,ganin dagaske takeson Jabeer kuma zata Iya Kashe kanta akanshi gashi kuma Uba yafi Sonta cikin ƴa’ƴanshi,Sae ya yanke shawarar zai aura mata jabeer,ashe da wata mummunan manufa Ya amince zai aura mata shi,Saboda yayi bincike akanshi ya gano cewa Jinin Maƙiyansu ne,mutanan da suke hari,shi kanshi Jabeer ɗin baisan wanene shi ba,Yawo kawai yake yi acikin garinsu tun yana ƙarami ba’asan danginshi ba,Amma su dayake Shu’umaine da suka bi diddigi saida suka gano ainihin wanene shi…………

READ ALSO:  Download Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 118 Hausa Novel PDF

Karanta>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel – Aihausanovels

Cikin lokaci ƙanƙani aka ɗaura auren Azmee da Jabeer,Aranar Hamma Gali kamar Ya haɗiyi zuciya Ya mutu,Ya tsaneshi kamar mutuwarshi,Saboda Shi ke son Azmee,duk da ba son Allah da Annabi yake yi mata ba,Yasha yin kokarin Keta haddinta amma Allah bai bashi iko ba,

Bayan sun ɗaura auren Azmee da jabeer,Mahaifinta da kanshi Ya basu kyautar gidan da zasu zauna,Saboda Jabeer baida komai,Talaka ne shi gaba da baya,

A ranar da aka kai Azmee gidan Jabeer wani mummunan abu ya faru,lokacin da kowa yabar gidan Amarya Ya kasance su biyu ne acikin gidan,Bayan sunyi al’wala sun gabatar da sallah,jabeer ya ɗauketa zuwa saman gadonsu,sai da yafara karanta addu’ar saduwa da iyali kafin suka soma biyan buƙatar junansu,Ita dai a wannan lokacin tasan da jabeer suka kwanta,Amma a washe garin Ranar da ta farka cikin mawuyacin hali,Hamma gali ta gani kwance saman gadonta babu kaya ajikinshi,ta fasa wata irin gigitacciyar kara ta soma ƙoƙarin mayar da kayan jikinta,Da gudu ta shige bandaki tana kuka,Bata fito daga toilet ɗin ba har saida taji Muryar Jabeer yana ambaton sunanta,
Sannan ta fito tana kuka,A gefen gadonsu ta same shi zaune,Hawaye wasu na bin wasu akan fuskarshi,Jikinshi sai kerma yake yi,Zuƙunnawa tayi agabanshi tana kuka,
Cikin shessheƙar kuka take tambayar meya faru dasu a daren jiya?ina ya tafi yabarta har Hamma Gali ya shigo cikin ɗakinsu,ta rikice ta rasa gane waye ya kusanceta a cikinsu,A lokacin Jabeer Ya amsa mata da cewa shine ya kusance ta,Bata yarda da kalamanshi ba,Hakan yasa ta soma tambayarshi Idan har dagaske shi ya kusanceta meyasa da ta farka da safe bata ganshi ba,Sai dai Hamma Gali ta gani kwance Saman gadonsu,Sannan meyasa yake kuka?”ganin halin da ta shiga ne yasa bai sanar da ita ainihin abunda ya faru ba,Shi dai A iya saninshi a daren jiya bashi kaɗai ya kusanceta ba,An gusar mashi da hankalinshi,Ya mike a wani irin yanayi yabar ɗakin bai ƙara sanin inda kanshi yake ba,A wannan lokacinne Gali ya shiga ya ƙarasa aikin,shi kanshi kokwanto Yake yi Anya Shine ya kawar da budurcinta ko kuwa Gali ne?kamar yarda tace Gali ta gani kwance saman gadonsu,Allah kaɗai yasan Ƙuncin da jabeer yaji acikin Zuciyarshi,Iya cuta dai an cutar dasu,Hakanan ya daure Ya rungumi matarshi suka ci gaba da rayuwa da ita,

Ana haka,Azmee ta fara ganin sauyi atattare da jabeer,Ya canza mata sosai,kwata kwata babu kwanciyar hankali atare dashi,Ko magana baisan yi,abinci ma baya ci,idan dare Yayi baya bacci sai dai ta farka ta same shi saman darduma Yana sallah yana kuka,Duk in ta tambayeshi meke damunshi sai yace mata,tayi ma mahaifinta magana,Yadaina yi mashi abunda baiso,Ta rasa gane me jabeer ke nufi,ita dai a iya saninta Mahaifinta mutumin kirki ne,babban malamine shi,ko maiyasa jabeer ke ƙorafi akanshi,duk yarda taso ya sanar da ita,ainihin abunda Iyayenta keyi mashi amma Yaƙi sanar da ita,tun tana tambayarshi har ta gaji ta ƙyaleshi.

Download>>> Mijin Malama Complete Document

Wata ɗaya da yin auransu,Azmee ta fara laulayin samun ciki,A lokacinne suka shiga ruɗani ita da jabeer,Ga ciki Ya bayyana ajikinta,Amma basu da tabbacin Cikin Shi ne kona Hamma Gali,A wannan time ɗin Jabeer Ya bata kyakkyawar kulawa,ya rage nuna damuwarshi,don kawai farin cikinta,

Ranar da Azmee bazata ta6a mantawa ba,Shine ranar da cikinta Ya shiga wata Tara ta fara nakuda,Dayake ƙa’idar family ɗin kaka in mace zata haihu,a gida suke kar6ar haihuwarta,

Cikin ɗakin mahaifiyarsu Dije aka shigar da ita saman gadon karfe,Su biyu ne akanta zasu kar6i haihuwarta,Hada matar wan mahaifinsu Ubaid,mahaifiyarsu Gali,Inno bata da mutunci matar nan,Halinta sak ƴa’ƴanta suka biyo,Duk acikin gidan suke,Dayake babban gidane na iyali,zumuɗinta akan jaririn da za’a haifa ne saboda gali ya sanar da ita cewa ɗanshi ne,

Azmee bata haihu ba Sae daren Ranar Allah yayi zata haifi santalelen ɗanta Namiji,Ko wanke jikin jaririn ba’a kaiga Yi ba,Kwatsam Ba zato ba tsammani Sojoji Su kayi masu dirar Mikiya,A fusace sojojin nan suka shigo,Kuma sunci sa’a Gaba ɗaya family ɗin sun taru a gidan suna jiran Haihuwar Azmee,Bisa umarnin Salahuddeen A lokacin shine shugaban sojoji na Nigeria,Umarni aka basu kai tsaye su kashe duk wanda suka Gani acikin Family house ɗinsu,amma banda mata da ƙananun Yara,Nan fa sojojin nan suka buɗe masu wuta,ta ko’ina sautin bindigu kake ji,Sunga tashin hankalin da basu ta6a gani ba,Anan Suka kashe ubaid da kuma Uba,Daga ciki hada iyayensu mata,domin sunyi ƙoƙarin Ɗauko makamai a cikin ɗakunansu da niyyar su taimaki Mazajensu,wannan ya tabbatar masu da cewa suma matan suna da sa hannu a aikata ta’addanci tunda har sunsan suyi harbi da bindiga,aikuwa suka kashesu gaba ɗayansu,A ranar an zubda jini kamar kamar mi,Daga cikin waɗanda tsautsayi Ya ritsa dasu,Hada Jabeer bawan Allah baiji ba bai gani ba,Suka kashe shi,A lokacin yazo duba jikin Azmee yaga in ta sauka lafiya,Shigowarshi keda Wuya,Sojojin suka harbeshi saitin zuciyarshi,Anan Ya yanke jiki ya faɗi matacce,

A ƙarshe mutun uku suka tsira,Azmee data 6oye a ƙarkashin gadon mahaifiyarsu,hannunta ruke da jaririnta, itama Saratu Ta tsira a wannan Lokacin,Sae kuma Gali tare da Ya sayyadi da basa acikin gidan abun Ya faru.

Karanta>>> Matsi Ga Sabbin Amare Kafin Kije Gidan Miji.

Azmee bata tashi sanin Jabeer ya rasu ba,Sae a washe garin ranar,ta fito daga ƙarkashin gadon hannunta ruƙe da jaririnta,jini duk ajikinshi domin ba’ayi mashi wanka ba,haka ta fito dashi rungume a hannunta,ta tsorata da ganin yadda sojoji suka wanke gidan da jinin Iyayenta,Tasha kuka kamar ranta zai fita,A lokacin Allah ne kawai Yayi zata rayu,A nan tsakar gidan taga gawar Jabeer yashe a ƙasa,ga gawawwakin Sauran Ƴan uwanta,nan take ta yanke jiki ta faɗi kasa a sume,jaririn hannunta ma Ya faɗi wanwar yana ta tsala kuka,

Bayan wasu kwanaki da yin wannan Tashin tashinar,Azmee ta farka a gadon asibiti,bayan ta shafe sati biyu kwance bata acikin hayyacinta,

Tasha kuka kamar ranta zai fita,ita sam bata damu da iyayenta da aka kashe mata ba,Mijinta tafi ji,shi da baisan komai ba,Bai aikata laifin komai ba,Amma an haɗa dashi an kashe,

Hamma Ghali ne Ya kawo ta asibitin,Lokacin data farka tare da sayyadi da saratu tagani tsaye akanta,sune ke jinyarta tun daga wannan lokacin rayuwarsu ta tagayyara,mutane suka ƙyamace su,kowa gudunsu yake yi,saboda sanin Abunda iyayensu suka aikata,Idan suka biyo hanya har jifarsu akeyi da duwatsu ma,Dole suka daina shiga cikin jama’a,

Tundaga wannan Lokacinne,Hamma ghali Ya tunzurasu akan su ɗauki fansar kisan wulakancin da Family ɗin SALAHUDEEEN HOSSEIN suka Yi masu,Kunji silar shigar Azmee ƙungiyarsu,Wadda bayan Su salahuddeen sun ruguzata a karo na biyu,Ghali kuma Ya tada ƙungiyar ta hanyar wasu abokanan Iyayensu da suka rage ba’a kamasu ba,A lokacin ne kuma Salahuddeen yabar duniya,Saboda ɗaukar fansa Azmee ta jefa kanta cikin halaka,duk don saboda Mijinta da aka kashe,ko lokacin bataso shiga ƙungiyar ba,Hamma ghali ne Ya tunzurata sosai har saida ta amince Ta tsunduma tsulundum,Da ita da Ya Sayyadi da saratun dukkansu,Jinjirin da Azmee ta haifa ba kowa bane,Face Haroon shine ɗanta da take dashi ɗaya tilo,

Shiri na musamman sukayi domin ganin sun tarwatsa Family ɗin salahuddeen,Wannan yasa suka raba kansu,Ya sayyadi yabi Ta 6angaren Abusufyan dake zaune a kano,Da biyu ya shiga rayuwar abu saboda kawai Ya cimma burinshi na Ƙuntata rayuwar Abusufyan,Azmee kuma ta hanyar hajjaju ta biyo masu,Sai da tayi bincike sosai ta gano cewa hajjaju tana da kusanci sosai da mutanan gidan kuma itace ke kai masu ƴan aiki duk in suka buƙata,Wannan dalilin ne yasa taje har gidan hajjaju ta nemi da ta taimaka mata ta samo mata aiki a gidan Abban sojoji,
Ganin yarda take roƙonta,Ga ƙaramin yaro yasa hajjaju ta tausaya mata,har dai ta amince zata sama mata aiki a gidan,kuma cikin sa’a Batare da ta sha wahala ba,ta samu aiki agidan duk da dama sai da tayi ma hakan shiri……..”

*Masu cewa Basu son littafin abban sojoji na kuɗi bane,Littafina na kuɗi ne,Book one ne kawai nayi shi kyauta,Amma 2 da 3 Na kuɗi ne,Dukansu 300 ne duk maiso yayi mun magana kaitsaye Amma message ta whatsapp 08103884440*

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.