Download Complete Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 111-115 Hausa Novel PDF

YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼
MATAFIYA

BOOK 2

111-115

Official

By
AsmaBaffa

SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN

GARKUWAR MATA

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na ‘Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace ‘yar gayu ce mace ‘yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci

Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki ‘Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da ‘boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan

wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau’in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata ‘Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni’ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai ‘Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

Page naku ne

Dukkan Makaranta wannan novel
‘YAR AIKIN KARUWAI

Kaka gidansa ya shiga tare da kulle ko Ina ya Kalli sakatar yace fatan kin kullu gam? ya sake taba kofar yaji gama gam yace yawwa ya shige cikin palon,ba kowa a ciki Kaka Yace har ta shige dakin jihadi ai shike nan ya kutsa Kai cikin bedroom din tare da sheka Sallama ,Mama anci lullubi cikin lafaya amsawa tayi a hankali,Kaka ya zauna a gefenta tare da furta barka da zuwa gidan abarka Amaryata,Mama ta gyara mayafinta ta amsa da yawwa barka da shigowa,Kaka ya sake nutsuwa shi a dole me Amarya,Mama ta tashi yace kinci sunanki

Zuwaira irin wannan zura kyau haka,Mama tana jinsa tayi dariya,hannunta ya riko yace haba matar Ambassador zo ki zauna, Ambassador nake har a kwanciyar aure,Mama ta zauna ya bude kayan makulalashensa suka ci,Mama tace zanyi wanka,wanne irin wanka yanzu ga babban wanka zamu yi nan da anjima ni fes kike kina wannan kamshi

Dan Allah kyale wankan nan ayi ta wanka sai kace Kwadi,Mama tayi dariya tace to ai harkar tafi Dadi,Kaka yace Ina a’a sai kace wasu Yara ki dinga tunawa shekaru sun ja kina matsawa kanki da ruwa ke da Mura Kuma Kun zama kawaye,notikan namu duk sun fara birgewa injina sunyi sakwa sakwa ki dinga adana tsufanki kina kiyaye lafiyarki,Mama ta zauna tace to Kai dai kace baka so ayi kawai,yace Ina laifin wanka biyu safe da dare ai yayi amma sai kace agwagwa.

Mama tace to Kai kayi ne? Kaka yace ai da zanzo nan nayi wanka fafes ko baki ga alama ba? tace na gani, mamaki Kaka yake bata ganin yanda ya birkice sai kace yaro Mama bata San Cele ce ta bawa Kaka tsumi ba,Kaka cewa yake muyi soyayyar mu ni Ambassador ne a soyayya, Mama ta Bude baki tana kallon Kaka,tace haka kake dama? Yace na wuce haka ma,ki Daina damuna da Surutu kamar kinci aku, kunya kake bani wlh,Kaka yace ke kika San sunanta ma wai kunya mece haka? Shi yasa fa ni bana son Saliha ana wani shuru shuru da kunya na fi son Yar duniya,Mama ta zaro Ido akan maganar Kaka,

Kaka kuwa aikin gabansa yake a jikin Mama,tun tana gani kamar wasa har ta biye masa, Kaka ya rungumi tanjama tanjaman boobs din Mama yace sharbila sunan wata,amma wannan bada su kika shayar da Sabreen ba? karya ne Madara kika bata ta sha ta girma wannan Abu aradu yayi girman kan Cele,Mama dariya take kamar ba gobe har suka tsunduma cikin harka Kaka yace Allah ya taimakeni na samu Location me kyau,ya dinga gwangwajewa ga karfin magani,sai da ya kure Mama ya goge mata hadda da tana rainashi,Mama ta zaci wani dan rubabben tsoho ne,Kaka a haka ma ba gajiya yayi ba,yace ke a saudiyya na koyo soyayya sabon salo,Mama tayi dariya tace gaskiya ka hadu,hakura yayi kar ta gaji,

da asuba yace Ina bazan iya Sallah ba sai da ya sake sannan ya samu nutsuwa maganin ya Dan sake shi,yace Allah ya kawo Cele in mata godiya ta musamman.

Mama tace Ina Raina ka ashe ba haka bane,kaka harda kuri yace lafiya ce Dani ki kiyayeni ba a wasa damu yanzu sai muyi maganin mace,tayi dariya yace yanzu Kam kiyi wankanki da hujja Zaki iya yini ma a cikin ruwa ba asarata,Mama tace haka kace ba komai.

Washe gari da wuri kuwa Cele tazo sai kace Yar iska,knocking tayi suna ta bacci Kaka Yana ji yasan Cele ce yaci gaba da baccinsa Cele sai gajiya tayi ta koma gidan Umma,wurin 11:30am ta dawo gidan Kaka ta bubbuga aka Bude,tabi Kaka da kallo ya sha jallabiya,Kaka ya kalleta yace wai baki zo da Mijinki bane?

Cele tace ka manta a can na barshi garin su Rabi fa,Kaka yace to shigo,Cele ta Kalli Kaka tana dariya Kasa kasa yace zan sa sanda na radeki, ke ko kunyata bakya ji sabo da Ina wasa dake ni bazan biki wata Saudiyya ba ku tafi da Mijinki Ina nan nayi abokiyar zama,Cele tace au baya zaka juya min Kaka sabo da ka samu mata,yace to Allah muna zuwa mu dawowa zamuyi bazan zauna a can ba indai zaman garin nan ne ni bana so sai dai da Ibada naje,Cele tace lallai kaka da nasan haka ne da bazan maka auren ba,ko da ke ko ba ke Allah yayi zan aureta baki ji kamshi ba girki ake shirya min inda kisan Dan Auta.

Cele tayi dariya tace lallai kaka wlh gashi nan kamshi har waje,ato ke ba sai ki zauna garari a hotel ba,Allah karki ji wasa bazan zauna a Saudiyya ba Kya dinga biya mana muna zuwa Ibada,Yanzu dai zan yarda mu tafi amma kafata kafar Zuwaira muna ganin komai normal zamu dawo, Cele tace shike nan ai Kaka yanzu ya batun gashin?

Sai dai ki gasa Zuwaira itace ta ji jiki ba ni ba,ni dai Ina fada Miki bazan zauna a garinku ba na samu location me kyau ni Kam,Cele tayi dariya sosai tace ba komai kaka me location,kawai ki Bude min shagona In Saka yaro ciki watarana Nima na dinga Dan zama Hakan ya isheni,Cele tace za ayi Hakan,kayan masarufi zaka siyar ko? Yace ae shi nake so,Mama ce ta fito daga kitchen tace a’a Cele kece a gidan? Cele tace ae wlh Ina kwana,suka gaisa, Cele a nan ta karya taci ta koshi ta tafi.

Bayan wata daya Auta Zaune yake cikin Palo sanye cikin 3quarter da Riga armless me hula farare, Salma ce ta fito cikin Dan guntun wando da kadan ya rufe mata mazaunai da Yar ficikar riga,Knocking suka ji taje ta Dan leka ta Yar kafa ta ga Rabi da yaronta a kafada bude kofar tayi tace ke kadai ce? Nace ae Nawwar ya saukeni ya wuce,yau yini nazo muku kune last gobe kauyenmu zanje wajen Dagaci,muka shiga na hade cikin wata shadda me tsada doguwar riga ce amma Dinkin na musamman ne,

Auta yace Hajiya Aunty yau kece a gidan namu? nace ae mana tunda kayi mata ka Daina zuwar mana Yar ziyarar ma ta gagara,Salma kitchen ta shiga ta kawo kayan motsa baki ta koma ta zauna a cinyar Auta,Nace ko kunya ta babu,Auta dariya yayi yace ke kunyar kike ji Aunty,Kuma ma Matata ce fa mene a ciki,Mami ce tazo gidan itama Salma ta mike ta leka tace Mami ce Allah, yau gidan namu yayi albarka ta dawo tare da haurawa sama ta dora doguwar Riga a saman kayan nata,Auta tashi yayi ya bude kofar,

Mami tayi Sallama Muka amsa,tace Rabi yaushe kika zo ne? Nace Nima yanzu nazo na durkusa na gaida ta,Salma ta fito tana gyara mayafinta itama ta duka ta gaida Mami,Auta kuwa hannu ya mikawa Mami yace Salam,Hannun nasa ta bige muka yi dariya ya duka ya gaisheta ya tashi ya jawo Hannun Mami ya zaunar da ita a inda ya tashi ya zauna a kasa gabanta yace kiyi hakuri banzo ba,Mami tace kaji da shi ace mutum daga an baka gidanka shike nan sai ayi sati ba a Ganshi ba,Salma ce ta kawo kayan motsa baki ga Mami tace kiyi hakuri Mami aiki ne ya sha Kansa,Aikin karya abinda sai yaga dama yake zuwa aikin,Auta yana dariya ya Sosa Kai yace Exam zamu fara,karya kake kullum haka kake cewa Exam zaku fara Karatu kake yi,nace wlh muma baya zuwa ba shi ba Salma ana magana zai ce school,Mami tace gashi nan ai kiba yake yi kullum,da Karatun yake ai da tuni ya rame

,Auta yace kawai dai ta iya girki ne matar tawa shi yasa nake kiba,Mami tace zaka gaji ne ka fito ai,Auta ya Kalli Salma suka hada Ido suka yi magana da Ido,Mami tana ganin abinda Auta yake ta mike tace dama unguwa zani na biyo ni na tafi,suka Rakata har mota ta tafi suka dawo muka ci gaba da hira,abinda nayi mamaki da rana sai naga Salma tace tana zuwa ta shige bedroom,Auta ya shiga kitchen yayi girki da komai sai da ya gama ta fito,nace Auta lafiya kuwa ita baza tayi girkin ba? Ido suka hada da Salma suka yi signa Salma tace wasu kaya na gyara watarana Kuma yana min girki, yace bana so ta dinga wahala da yawa kafin a samo me aikin shi yasa watarana nake tayata cewar Auta,nace Karku Raina min hankali wlh ciki ne da Salma gashi nan Ina ganinta na gane da haka take,Salma ta dinga dariya tace ciki Kuma Aunty har yaushe aka yi auren wata uku Ina yarinyata Auta yana yaronsa ai bai Isa haihuwa ba,

Dama Wise ta fada wlh tace ciki ne dake nace karya ne ashe da gaske ne to mene abin boyewa abin murna ne fa Yanzu zamu San Antena tana aiki,Salma tace laaaaa tana dariya,Auta yace rabu da su Aunty sun fiye gulma, ciki tun yanzu ai a zubar da shi ko amarcin yaushe naci,Salma har yamma banga taci komai ba ashe bata iya cin abinci sai kayan kwadayi shi yasa tunda ta fara Auta ya kaita asibiti aka ce ciki wata biyu da satikai.

Nawwar yana daukana nace wlh matar Auta ciki ne da ita,Nawwar yayi dariya yace shegen yaro bazan yi mamaki ba zata iya samu, nace shi yake girki fa yau abincin Auta naci ban taba ganin Auta ya dafa ko indomie ba sai yau,Nawwar yace ya iya girki yana taya mami ai,nace okay wai ya tallafin gidan marayun zaka Kai? Yace ae amma sai kin dawo daga bikin Gaji sai daga musu biki kike yi bayin Allah suna jiranki,Nace ai kasan kayan dakin fa sai da na siya mata me kyau Kuma ita da Mairo na siyawa,yace to kawai gwara na baki aiki a Office Dina na huta a miki salary wlh kin durfafi kudina,Dariya nayi nace har nawa naci a kudin naka? Nawwar yayi dariya yace ai bazan yi mamaki ba Idan kince haka ai macece ke kaza ci ki goge bakinki ko Mai aka muku zaku ce ba a taba Yi muku ba,tunda muka hadu dake a bariki kike min wasa da dukiyata duk kin karya min tattalin arziki,Dariya nayi sosai nace local government ta kaika ai mu kuwa ba daga kafa kudi muka sani,Allah bazan yi aiki ba Karatu dai zanyi Kaci gaba da Tara mana kudin,Yace ya zanyi ai Nima bana so ki fita gwara kullum kina gida kici me kyau ki huta ki kular min da kanki ni kuwa Ina huce gajiyata, hannu na Mika masa muka tafa nace Local government kuwa kullum tana jiranka kayi Jigi jigi a ciki muna dariya,

Muna komawa na shirya kayan tafiyata yace zan musu Allah Sanya Alkhairi bazan samu zuwa ba karki Kara kwana biyu kawai na baki,nace ai ko baka ce ba ma sabo da ni kaina bana son yin nesa da Antena uwar dadi har da juyawa na karkada kugu,Nawwar yace kinga Abdullah yana kallon ki tam,nace nifa yaro bazai takura min ba,yayi dariya yace irin rawar nan taku ce tasa kuka gigita min Auta ya rude,na sake girgizawa Ina bin kidan dake tashi a tv na Igbo,Nawwar yace har Kin tayar min da Antena,zo mu tafi wanka can zanyi aikin ya Jani,na Kwalawa Nanny Kira nace ki yiwa Abdullah wanka tace to ta dauke shi na bata kayansa muka yi ciki.

READ ALSO:  Download Complete Nurul Kalb By Matar Manya Hausa Novel PDF

Cele kuwa bata laulayi ita tana da ciki sai dai cin tsiya Idan ta samu ciki ta dinga cin abinci kamar jaka,tare da Cele da Umma,Abba,su Bilkisu dasu muka tafi bikin Gaji,Omaira sai ranar da yamma Omar dinta ya kawota a motarsa, Dagaci ya sake gyara gidansa ko Ina yaji tiles da paint,Omaira tana shigowa nace a’a’a irin wannan kiba haka Omaira,Cele tace wai wai wannan kyau haka ashe Ina da kanwa haka? Gaji suna ta dariya,Omaira tace ya ranku naji Antena kullum ana bani Vitamins ba dole ba,Aunty Bilkisu tace wlh Umma tana bakin kofa tana jinku,nace yo ai itama Abba yana bata mene,Cele tace ke Dan ma baki je ba kinga yanda take karrama Abba,Idan ya shigo fa haka Zaki ji tana ku tashi ku koma dakin can Abbanku zai shugo,

fisabilillahi Idan ya shugo me zaiyi nace Antena ce,Omaira tace ai ku dai wlh manyan banza ne na rantse ai sai ku fada min sirrin kuce Antena daga zafin ana zuwa wajen dadin sai ku barni a duhu,Nazifa tace Omaira dama kema haka kike? Omaira tace ba laifi na bane Aunty Antena ce ta jawo ba a iya shuru da baki,ni yanzu wa zai bani tafiyar kwana sai dole,Omar yanda ya iya soyayya gaskiya baku San shi ba,Baso kuke gani a Ido amma ni na Sanshi a Omar a zahiri,yanda yake ji dani kamar kwai wlh baya so yaga damuwata ko digo,yanzu shagwabar da nake ko Yar Auta baza tayi ba, Kuma biye min yake shopping duk sati biyu in fada muku,abinci ba abinda babu,ke maganin matan ma yace kar in dinga sha barkatai masu amfani na Yayan itatuwa ko mene siya min yake na hada da kaina wani,Wanda Kuma bazan iya ba Idan me kyau ne ya bani kudi na siya,kullum Idan zai fita sai ya bani kudin kashewa in ta tara abina.

Nazifa tace wai shegiya ga sababbin kayan harka ki siya wlh zai ji dadinsu,Nazira tace Allah ya shirye ku dai,Nace Ameen mufa baza mu fasa zancen Antena ba,Cele tace ke rabu dasu suma duk karya ce suna sonta sai an samu Miji aji luff,Bilkisu tace dan girman Allah ku kyale mu haka,Cele tace wlh baza mu daina ba,Omaira tace ai sai dai kuyi hakuri damu Antena gida gida ce ko Ina da ita,Gaji tace ai ba Shiri na tarko auren nan yo Ina zan iya rayuwa ba Antena,Mairo da yarta tayi girma sosai tace uhm Antena ai mu muka ga karshenta,

Omaira tace na lie har ki mutu baza kiga karshenta ba,nawa kike ma me kika sani a Antenar? Cele tayi dariya ta kwanta a saman gado tace ni dai ku bani abinci naci wlh bana jure yunwa yanzu,nace kin kunsa ai tace ai ciki tuni ya Kai wata biyu haka akace a asibiti,ranar mun sha yini anyi iya shege,Omaira a ranar ta koma,da zamu tafi ta gidanta muka sake biyawa sannan ni da Cele muka tafi,ba a Dade ba Cele, Ahsan,Kaka da Mama suka tattara suka tafi saudiyya.

Tafiyar su da kwana daya bayan ta mana waya sun sauka lafiya Wise ta fada nakuda sai labari naji an kaita asibiti,kafin muje ma ta haifo danta Namiji katon gaske,Papa sai murna Iyamami tana can ta saduda itace akan gaba duk Halin banzanta ta gaji ta Daina ita da Sabreen sun nutsu,Wise ras da ita Papa sai murna yake ya samu da Namiji ya Kara samu Yaya, Sabreen anyi Kani ana ta murna.
Tunda aka sallamota kullum sai munje,Iyamami ce ke kula da Jaririn da komai na wise ita da Mami har ranar suna tazo yaro yaci Sunan Nawwar sabo da Nawwar shine duk ya wuce gaba,junior muke ce masa,Auta anyi da tsohuwar budurwa ta haihu Gift ya kawo ta gani ta fada.

Kaka kuwa bayan sunyi Umrah dukkansu Cele tace suzo su wuce Riyad yace a Dan Jira yaje wajen abokansa na garin Makkah su gaisa,Cele tace kuyi sauri Kaka Dan Allah muna jiranku a masallaci harami, Kaka da Amarya Zuwaira Mama suka fito suna tafiya cikin nutsuwa Basu san wani kazamin kame ake yi ba,har gida gida ake bin ko wanne takari a kama su,gidan da Cele ta taba zama su Meenal har gida akaje duk an kamasu an kashe musu passport baza su sake shiga kasar ba an dawo dasu Nigeria sabo da haka ko sun dawo Makkah ana Shigar da passport dinsu computer zai nuna an dakatar da su daga shiga kasar,duk Wanda suka kama da laifi a kasar haka suka masa,sabo da haka takari da yawa duk an tsince su,Suna tafiya Kaka ya hango gungun askarawa shi ya San kwanan zancen

Mama ce dake bata taba takarci ba bata San komai ba,ya juya da gudu ya bar Mama sai da yayi nisa ya kwala mata Kira Zuwairaaaaaa tashi injin kafarki, bawa kafarki wuta ki taho a millionnnnnnn,Mama taga askarawa sun dumfarota gata da kiba sai gudu, tabi Kaka sukub sukub da kyar take gudu Allah yasa suka Dan buya a wani lungu sai da Askarawan suka koma sannan suka fito suka koma wajen su Cele suna basu labari,Kaka yace Zuwaira ga kiba inda kisan tana taka soson katifa sai ki rantse akan soson katifa take gudu sukuf sukuf,Cele da Ahsan suka dinga dariya,yace ai baza su kama ku ba da Kun nuna musu wannan abin,Kaka yace Kai rabu Dani haka kawai tsautsayi yasa ance masu shedar zama ma a kasar duk sun kame su,Ahsan yana ta dariya yace su tashi anzo daukansu,Driver Yazo da mota aka kaisu Airport suka wuce Riyad.

Download>>> Kadangaruwa Complete Document

Ahsan a gidansu ya fara sauka a dankareriyar farar mota driver na jansu daga airport,gidane hadadde Yan uwansa larabawa maza da mata suna ta murna ana tarensu,wasu a ciki Basu so ya auri ba Yar kasar ba wasu Kuma ba ruwansu,Cele tana rike a hannunsa suka shiga katon Palo ya gaji da tsaruwa,ga girki kala kala an shirya, masu son auren sai rungume Cele sukeyi da Ahsan suna musu pics,Bayan anyi gaisuwa irin ta larabawa Ahsan ya gabatar da Cele ya Basu labarin abinda duk ya faru tsakaninta da Maheerah har auren Cele,Wanda basu so aka auri Cele ba ma a nan suka narke suka koma Sonta,ya gabatar da kowa nasa a wajen Cele sannan aka ci aka sha duk da cewa Kaka,Mama da Cele ba komai suka iya ci ba,

Basu Saba ba suna haka sai ga Maheerah ta shigo tana balbala masifa anci Amanarta,Cele ta mike tsaye tace sai ma an Kore ki daga aiki Zaki San an ci amanarki ta fada da larabci,Maheerah tazo ta cakumi Cele,Cele ta kwasheta da gigitatten Mari ba shiri ta saketa,Larabawa sai Subhannallah Subhannallah suke furtawa,Ahsan yaji dadin hakan da Cele tayi,ya rike hannunta dama a tsaye take ta mike zasu tafi ya jata zasu shiga mota Maheerah tana kuka ta zube a kasa ta rike kafafun Ahsan tana bashi hakuri,Cele ta hankadeta suka shige mota da su kaka suka wuce gidan Ahsan sabon gidan da ya canja a wani layin daban na masu hannu da shuni,gidane na gasken gaske yaji kaya komai me tsada,Cele tana ta uban murna,yana shafa cikinta yace gidan yayi? tace komai perfect,sai me aiki Cele tace a’a ni zanyi komai da kaina Ina wani aiki a nan garin da ba kura, daukanta yayi suka wuce Bedroom suna soyewa,Cele tace Antena Dadi,yayi dariya sosai yace amma da kince zafi,Cele tace na tuba dama a farko ne nace yanzu na gane gaskiya na tuba ranki ya Dade karya nake wane mutum,Kaka kuwa yana bedroom din da Ahsan ya Basu shi da Mama yace da Mama azo a Adana ni,Mama tayi dariya yace amarci zanyi a Saudi yau sai na ajiye tarihi.

Bayan haihuwar Wise da wata Daya Star ta haifi yarta mace taci suna Nawwara wai sabo da Wise tayi Nawwar shine ta Saka Nawwara,Ba a dade ba Seraline ta haifi Namiji itama yaci suna Ahmad,Yar Zabil da Mandula kuwa sai bayan wata biyu Mandula ta haifo Mace taci Sunan mamanta Aisha suna ce mata Waheeda,Sai Yar Zabil bayan sati biyu da suna ta haifo Namiji itama aka Saka sunan babanta Usman suna ce masa Aabeed.

Salma kuwa cikinta yana ta girma sosai sai gani akayi ya fito a hakan ma boyewa take yi Idan zata je unguwa hijab har kasa kowa yasan da cikin amma sai boyo suke ita da Auta,Yau Auta yana wajen Mami tace Idan kun gaji da boyon ai cikin ya tsufa sai ka dawo da ita gida nan ta haihu,Auta yace wlh ni bazan iya barin Mamatata ta dawo nan ba,ni na karbi haihuwar,Mami ta kalle shi tace munga Rabi ma me boyon nono,Auta yayi dariya yace kawai a raba mutum da matarsa ayi ta gargajiya ni bazan yarda ba,Mami tace Karka dame ni Kuma kaje Allah ya bada sa’a yace Ameen .
Salma tana ta tiri tiri da ciki gashi ya tsufa sosai,Auta yace ya dai ya kalleta tana hawaye tace Allah cikin nan ya isheni wlh hakuri kawai nake yi,Auta ya fara lallashinta yace sorry Autana kin kusa ai Yana shafa cikin tayi Turus a zaune tare da mike kafafu.

Cele kuwa cikin yana shiga watan haihuwarsa cif cif sai gata sun dira a Nigeria ita da Mama da Kaka sai Ahsan,lokacin an gama musu hadadden gidansu na gagara,Kaka da Mama anyi kiba anyi jajir,Cele da Ahsan ma haka,Kaka suka sauka a Kaduna gidansu har Cele sai da suka zaga dangi sannan Ahsan ya dauketa suka dawo kudu a jirgi,Gidansu nasa Yan aikin sun gyara an zuba furniture da komai na haduwa an shirya musu kawai tarewa suka yi a gidansu abinsu.
Kusan kullum Ina ziyarar Cele sabo da cikin ya tsufa,nace gaskiya ya kamata Uwa tazo ta zauna da ku,Cele tace wacce Uwa ga Mama matar Kaka zasu taho gobe,nace Allah ya kaimu ai yafi Idan da manya,nace kinji Omaira tana da ciki Omar dinta ya Bude mata shagon boutique,Cele tace ta fada min.

Cele ta budewa Kaka shagon siyar da kayan Masarufi sannan ta sake gyara masa gidansa sosai,sai su Bilkisu ni da Cele mun hada kudi mun Basu jari babba suna juya abinsu, komai Alhmdllh kowa Yana zaune lafiya da yaransa Babu talauci kowa da rufin asirinsa dai dai gwargwado.
Mairo ta shirya bayan ta yaye yarta ita da Dagaci da Gwaggo da Gaji suka samu Iyayen Najib bayan sun gaisa suka ce yarku muka kawo,Najib aka Kira Yazo ganin Mairo da yarsa sai hawaye ya durkusa a gaban Mairo yace ki yafe min Dan Allah,Mairo tace ba komai na yafe maka Albarkacin yarka gata nan sunanta Madina,

Najib ya dauketa sannan ya fara rokon Mairo akan ta aure shi yace wlh Ina sonki Dan Allah ki aure ni,Dagaci ne yayi magana yace sai dai kayi mata gidanta daban sabo da gudun gorin kishiya,Baban Najib yace indai wannan ne ba matsala,Mairo dai haka ta amince gwara ma ta auri Najib din ta huta musamman sabo da yarta Madina.
Bayan sun koma gida ba a dade ba suka kawo komai na aure aka sha bikin Mairo itama aka kaita gidanta Dan madaidaici me kyau itama ni na mata kayan daki dukkan su sunci albarkacina Yar tsuntuwar da suka raina tayi musu rana a duniya

Maheerah kuwa asibitin da take aiki Ahsan yakai kararta suka koreta daga aiki gaba daya,tayi kuka tayi bakin ciki gashi Ahsan ko saurarta bai yi,kwarton nata ma sunyi fada gashi su can ba a samun Miji da wuri ta rasa Mijin aure sai gantali a gari kawai bata a tsuntsu bata a tarko,in Banda tarin nadama da Dana sani ba abinda take yi a rayuwarta.

Download>>> Silar FyaÉ—e Complete Novel Document

Yau cikin dare Salma tana kwance ta tashi ta zauna ta tashi Auta tace Auta ka tashi Dan Allah zan mutu kana ta bacci ai gwara na cika a gabanka,Auta ya tashi yace ko dai Nakudar ce ne? Salma tace itace gaskiya ni ban taba jin irin wannan ciwon ba,mu Dan Kara Jira ayi Sallah sai mu tafi asibiti,Salma ce ta sakko daga kan gadon tana rike mara tun tana Dan kokari har ta kasa tace Autaaaaaa da karfi yace na’am kamar abin arziki tace Auta ubanka,wayyo Nawaf zanci Ubanka,Auta yace ba lafiya mata ta zagi mijinta me Antenar ban girma, tashi mu tafi ya dauketa da tarkacen Salma da suka hada abinsu na haihuwa sai asibiti,Auta yaki fadawa kowa Kuma suna asibiti tun asuba har yayi Sallah rana ta fito Salma bata haihu ba,

READ ALSO:  Dowload Saseen Hausa Novel Complete PDF

Mami ta kirashi da hantsi amma bai fada ba yace lafiya suke,sai 12pm sannan Salma ta haifo yarta mace katuwar gaske kyakyawa,Sai da aka gyarata Auta ya shiga ya dauki yarsa yana ta jin Dadi yana uban murna ya rasa inda zai sa kansa,sai da Salma ta huta ya fita ya samo mata abinci take away taci ta koshi yamma karfe hudu aka sallame su,Auta yana zuwa ya hada mata ruwan zafi da kansa ta shiga tayi wanka,ta fito ta shirya cikin doguwar rigar material marar nauyi ya Mika mata turaruka yace shafa jego sai da turare tayi dariya,yace gashin nan iceko ya wanku fes tana taje gashin tace wlh bani da karfi komai karfin Hali nake yi kasusuwana sunyi rugu rugu,Auta yace a Kira Mami ko Zaki iya yiwa my Lovely Baby wanka?Salma tace na iya ya hada ruwan suka wanke yarsu mutum biyu akan jaririya daya Auta ya riketa Salma tana wanke ta,Auta yana cewa a hankali karki daye mata fata na shiga uku

Yar nan kamar raina haka nake jinta ki goga a hankali,a haka suka mata wanka harda mata ruwa biyu wai tafi fita,Auta ya zubar da ruwan ya sake wanke toilet din,Yazo ya gyaran gidan neat yayi wanke wanke sabo da tun dare suka tafi duk da ma gidan ba dirty sharp sharp ya gama komai yayi wanka ya fito ya shirya cikin jallabiya arsh yana kamshi,Salma ta shirya yarta harda hada garwashin wuta dama sun tanadi gawayinsu,

Auta ya dawo ya zauna yace ya kama gawayin? tace gashi yayi Jajir tana fifitawa da littafi,yace a gasa mata cibin,suna ta faman gashi ba ji ba gani Auta yace ayi mata sosai tayi sauri ta soye,kamar zasu kashe yarinya da gashi suna ta abu daya,Salma tace shi yasa nace a siyo gawayi kaga yayi amfani mun tanadi abun mu,Auta yace yaushe za a fara mata kwalliya,tun yanzu Kuma a barta ta kwana biyu tayi Kwari yace haka ne ya matsar da wutar gefe yace ko Zaki gasa local government dinne again?

Salma tace ta gasu ai dazu sai dare Kuma,Abu kadan sai budewa yarinya cibi a gasa a gasa a ajiye ta,cikin kaskon wuta Kuma na kasa a ciki suka zuba gawayinsu sai da suka Nemo abinsu tun cikin Bai girma ba,Auta ya zauna a gadon yace kamar kar a Kira kowa muyi ta kallon Yar mu,Salma tace ae wlh a bari sai dare a fada musu,Suka zauna suna ta kallon yarinya ba ji ba gani.

Auta yace wannan hancin nawa ne,Salma tace wlh nawa ne kana gani gashi nan daga karshe yayi tsini,yace bari dai a Kira Mami Dan darajar jaririyata suzo su tayamu murna,Auta ya Kira Mami yace Mami tace Naam,Yace albishirinki,tace goro Auta,yace to kinyi jika yarki Salma ta haihu,Mami harda guda tace Auta yaushe me aka Haifa? Yace Mace Mami tun 12pm ta haihu muna gida fa muna ta kallon Yar mu shi yasa santin Baby ya kwashe mu muka ce baza mu fada da wuri ba,Mami tace gani nan amma kuruciyarku tayi yawa Auta,ta zaci ma ba a yiwa yarinyar wanka ba,su Wise ta fadawa ta fadawa Iyamami,

Ina jikin Nawwar a kwance Auta ya Kira Nawwar ya daga,yace Yaya ku taho na haihu dazu tun 12pm,Nawwar yayi dariya yace Allah kace kaji jiki me ka Haifa? Yace wata zukekiyar mace ce da gani wannan sai Dan sarki Amma dai zan hakura ta auri Abdullah muyi manage,Nawwar yayi dariya kamar me,yace to gamu nan,Auta yace kuyi sauri kar ta huce ku kalleta da duminta,Ina jinsa Ina ta dariya nace to fa Auta yayi Baby mun shiga uku Kuma yanzu,

da Kansa duk ya Kira su Star ya fada musu,Ya kira su Umman mu ya fada musu,Baso ya Kira yace ta wajenka ta haihu,Baso yace akwai burar….a gidan nan sai munzo zan Kira Salma,Omaira tana ji tace Salma ce ta haihu? Baso yace ae fa ki shirya akwai suna ba yawaa,Omaira tace saura namu yace ba Yawaa zai zo inshallah, Allah yasa kar Nakuda ta miki ae yane kin gane,Auta Baffa ya sanarwa da Papa.

Mami ce ta fara zuwa ta shigo har bedroom din Salma ta iske Auta a zaune a tsakiyar gadon shi da Salma da Baby dinsu sun sata a tsakiya,Mami tace yayi masu ‘ya haka ake haihuwar ta ganganci baku San komai ba kuka ki fadawa mutane,Auta yace ga waya me takeyi a Nan muke browsing mu gani yanda ake yi,zo ki ganta Mami,Mami ta leka tace to a bani ita mana,yace bacci take yi ya daukota cikin kaya pink masu kyau ya mikawa Mami a cikin showel,Mami tace Masha Allah,Me jego boyon ciki Kuma ya kare yau gashi abinda ke ciki ya fito,

Salma harda jawo mayafi ta rufe fuskarta,Iyamami,Sabreen,Wise sune suka zo suma ana ta yiwa Salma tsiyar boye ciki,tayi shuru ko Allah ya raya bata iya amsawa wai ita kunya,Auta ne ya mata rada yace Idan ance Allah ya raya ki amsa a zuci,tace ai Ina amsawa a hankali cikin rada ganewa ne ba a yi,Mami tace ai kunyi kokari Auta wlh da kuka iya aikin nan,yace Yar tawa na kasa gyarata Ina bazan iya ba ai zagewa nayi Mami Ina kallon kan Yar ya fito daga local government,Kai Mami kunyi kokari ku duba Yar wannan kafar yaro guda ya taho,

Mami ta Kalli Auta tace wannan rashin kunya haka Auta wlh zaka bar dakin nan, Iyamami tace Dan bantan Uba marar kunya ka tashi ka fita Kaki fita yau naga jaraba,Baffa kuwa Auta ya ishe su da Kira wai ya akayi yaga shuru ne Basu zo ba,Baffa suka zo da Papa suka ga Baby suka tafi.

Mami tace to yanzu dai ai dole na zauna a gidan nan tunda ba Babba ko Iyamami ta zauna,Iyamami tace rabani da fitsararre amma tunda ke da Mijinki ki je gida na zauna haka Kuma wlh yaro ya min rashin kunya ubansa zan ci,Mami tace me za a kawo Salma na ci? tace wlh yunwa nake ji dama a kawo min tuwo ,Ina Shirin zuwa nida Nawwar na gama shirya girke girke na, Auta ya sake Kirana wai me kuke yi ne a gida ni ba’a son jinina Anki kulamin Yata,Nawwar yace gamu nan fa a hanya tunda Yar har an bawa Abdullah ai munyi suruka,Auta yace kar kuce Ina Neman Kai da Yata Idan bata sonsa bazan mata auren dole ba,haka muka tafi da Abdallah Wanda har tsaiwa yana yi.

Su Star dukkansu suna ciki Cele kuwa sai waya suke da Auta tayi nauyi,tace Auta Yaya Baby din? Shike nan ku Kun huta Inama nice Auta yace saura ke Kam munyi gaba mu,tace Allah sa na haifo Mace muyi takara da Kai wajen Neman auren Abdallah,Auta yayi dariya yace ai mu sai dai azo ace ana so,Muna shiga Auta ya dauki Abdallah yace Dan banza inye yaro yayi goshi tun yanzu sai farin jini yake ana ta son aurensa Allah yasa baka gaji babanka ba wajen Kaunar local government ka cuci Yata a banza,Star dariya harda bugar kafa tace Amma Auta anyi Dan Iskan yaro,Iyamami tace yaron nan ba ya jin kunyar kowa,Nawwar yayi dariya ya dauki Yar Auta ya mata Addua yace gata kuwa so cute,Auta yace mu ai ba na wasa bane kalleni Kalli uwarta,Salma ta gyara hancinta da hannu tace wallahi,Aka kwashe da dariya.

Muka zauna muka kafa dabar hirar Antena,Star tace ai ni sati biyu da haihuwa Ina samun lafiya da nayi wanka Abhulkhairi ya fara buga harka,Wise tace ni kuwa ai ni na Kai kaina Kun San ni ba hakuri, Seraline tace ni kuwa har yanzu,Mandula tace an barki a kwana yarinya,Yar Zabil tace bare ni ai tuni na Mika Kai,Iyamami sai Yar ta dauka ta bar dakin,

Salma kuwa sai labarin haihuwa take bamu muna Shan dariya tace ai na zaci mutuwa zanyi yau Auta yasha zagi ban San ma Ina zaginsa ba,sai dare sosai muka tafi abincin da na Kai shi Salma taci Auta ma haka da Iyamami tuwon shinkafa na mata miyar danyar kubewa sai farfesun naman kaza.
Da sassafe ma lafiyayyen Kari Wise ta kawo gidan,Iyamami ta Hana Auta kwana a dakin Salma itace take Hawa bed din dole bedroom dinsa ya koma amma kullum da shi ake yini ana karbar barka yana cikin mata.

Santana ma Yazo da Jamcy dinsa itama tana ja cikin ya tsufa.
Ana gobe suna Auta ya dauki Salma da Baby da Iyamami ya kaisu can gidan Baffa wai kar a bata musu gida, Baso Yazo tare da Omaira da Dan cikinta Kato,Baso ya ga jaririya yayi murna siyayyar da yayi me yawan gaske ya hadowa Salma kaya da nata dana Baby,ranar Suna Baby taci Sunan Mami Salamatu wato Salma Kuma sunan matar Auta uwar yarinya,Auta yace Baby za a dinga ce mata Babyna ce,,da yamma Auta hole ya kama me kyau muka dauki wankan Anko kamar ana party na biki haka Auta da Salma suka hade a high table ana cashewa anci an sha an cashe.
Bayan kwana uku da suna Ahsan Yazo yaga Babyn Auta ranar Kuma Auta ya dauke matarsa da Iyamami suka koma gidansa.

Bayan sati daya da Suna Kaka da Mama suna gidan Cele da Zama ta fara nakuda,Cele ce ta fito kamar an jefota tace Kaka ka taimakeni Kaka,bazan sake Shan maganin mata ba,har Umma na sawa a lemo na bawa Auta ya sha,Cele tana ta tonawa kanta Asiri Kaka yace ni maganin nan yayi min kici gaba da bani wlh ko ya kika ce Zuwaira? Zuwaira tace wlh wannan ai abin a siya ne, sun Saba Cele tana yawan siya musu kala kala suna shoshalewarsu,Mama Basu san Nakuda take ba sai da suka ji tana ta maganganu ita kadai kamar me Aljanu,tace Sanda na hadawa Salma mugunta na sawa Salma maganin sai muguntar ta dawo kaina ranar Ahsan yayi min ciki Allah Kaka,

Mama tace Kai ba lafiya ba ta Kira Ahsan yana daki ma yana bacci tace tashi Cele nakuda,bai gane da Hausa ba sai da zancen kurame Mama ta nuna masa yayi zumbur ya mike ya fito ya dauketa da gudu,Mama ta dakko kayan haihuwar,suka tafi driver ke Jan motar kaka yana gida shi Kam,Ahsan sai kuka yake ya rike Cele ,dama su akwai saurin kuka sai kuka yake yana Kiran Allah,ya Allah,yana yiwa Cele kiss a goshi Cele ta dirka masa duka a kirji Dan iska ka barni naji da kaina aikin banza kayi min ciki ka hanani sakewa ko wani zaka sake yi min yanzu to sake yi min na gani,kawai ba tausayi ba Imani kawai ka dawo kana min kiss Ina wani halin,

kiss din banza,Ahsan yace kiyi hakuri ciwo ne,tace bazan hakura ba wlh bazan hakura ba Mugu kawai,wayyo zan mutu Zuwaira zuwairaaaaaaaaa….uwarku gaba daya, Ahsan dan iska…..Koda suka je asibiti ma Cele cewa take likita uwarki,Likitar burar….ashar dazagi ba Wanda basu sha ba,wata nurse tace Kai wannan da bala’i take haba Babu Wanda bata zaga ba,a lokacin Kuma Santana an kawo Jamcy ta haihu harda dafe Kai yana ihun murna ,ya Kalli Ahsan yace sorry woo ta kaina nake yi nima, ya shige ciki abinsa.

Basu dade ba Cele ta haifo yarta mace kuwa,tana samun kanta tace a Kira Miracle,aka kirani na tafi asibitin duk muka Kira Yan uwa da abokan arziki sannan tace Kira min Auta ki fada masa kice tawa Abdullah zai aura jinin larabawa kalleta gaba daya Ahsan tayi wlh,Nace au ku yanzu akan Abdullah kuke takara da Auta nace Antenar yarona lafiya ku jawo min masifa ya girma da wuri wlh ku Daina wannan iskanci ke da Auta,

Cele tace to shi a dangin Uba ni a dangin Uwa naga Dan Iskan da zata auri Abdallah din,na dinga dariya nace Dan Allah ki koma ta auri dan gidan Wise wlh bazan hana Yar Auta Dana ba,Muna ta dariya akan Yara kanana muke wahalar da kanmu, da wuri aka sallamomu Ahsan ya ishishire Shima ba kunya ba komai kamar Auta yarinya tana hannunsa,gashi da taurin Kai, Mama tayi fadan har ta gaji,sai Cele ta masa magana ma da lallabawa sannan yake hakura,Cele tace Miracle Nima a tanadar min magani wlh planning zanyi Ahsan yace bai yarda ba shi Kam shi Yara yake so sai an haifar masa biyu ko uku Cele zata huta shi Sam bazai yuwu ba,Cele tace jaraba sai kayi ta yi ai indai local government ce gata nan zan gyarata ni naga irin wannan masifa haka.

Ranar Suna yarinya taci Noor Cele ta dinga masifa wai sunan yaso yayi kama da na Maheerah,Ahsan ya dinga dariya yace mene hadin Noor da Maheerah? ai da R a sunan kawai kace kana son tsohuwar matakarka shine zaka sawa Yata,haka ya gaji da masifar Cele ya kyaleta,Auta ya zama Abokin dabin Cele akan Abdullah kullum musunsu kenan kowa yace yarsa zai aura,Jamcy mun sha sunan danta Namiji Raheel,bayan sunan Cele da sati biyu ita da Ahsan suka tafi Saudiyya abinsu,kaka da Mama suka koma Kaduna.

READ ALSO:  Download Complete BINDIGAR KWALI By Nazir Adam Salih Hausa Novel PDF

Auta kuwa a ranar da yasan Salma ta fara Sallah bayan tayi arba’in ranar ya samu Iyamami a Palo tana shirya Yar Baby,Yace Iyamami My life ake shiryawa ne? tace ae yace da kyau ya kamata kema ki shirya kanki kiyi gida yau, Iyamami ta bude baki tace ba sannu ba na gode? Auta yace to Matata ta fara Sallah kar muzo mu cika Miki kunne da ihu mufa a ko Ina harka muke karki ce ban fada Miki ba ni ba tsayawa zanyi na jiraki ba Antena bata Jira Idan Kuma so kike ki kalla to,

Iyamami tace a’a me yayi zafi ungo yarka Auta ya karba yana dariya a boye ta kwaso kayanta,Auta yace muje na kaiki,Salma ta fito da kaya ta hadawa Iyamami sha tara ta arziki,Iyamami Auta yana sauketa ta fada wajen Mami tace sun Koro ni,wai Ina sa musu Ido,taje ta fadawa Baffa ma tace karshen duniya Yazo la’ilahaillallahu Auta ya gama fitsare kafafunsa har Kansa ya fitsare ba iya kafafu ba.

Auta yana dawowa ya samu Salmansa ta wani cakare cikin kana nan kaya shegu,Yace Salma Maman Salma ga surukarta Salma matar Auta,Autar Auta Kuma ga wata Autar,Salma tana dariya tace ai sai mun huta zamu sake ko? Auta yace Idan na Kalli yarinyar nan gaba na faduwa yake, da wuri zanyi suruki na shiga uku Auta da suruki yanzu yarinyar nan ranar data fara zance ya zanyi,Salma ta sheke da dariya,tace Kai dai bari ni kaina Ina hango abin nan,Auta yace gaskiya Kano zan dinga kaita gidan Baso can zata girma sabo da tafi yin hankali da tarbiyya,Salma tace Nima haka nace yafi Hakan a sata a can taci kwal ubanta da Islamiyya da boko,

Salma tace ae ai Hakan yafi mu kuwa muna nan muna harka da Antena,Auta yace ya zama dole shi yasa nifa bana son haihuwar nan a Kai a Kai gwara muyi da kadan kadan,wayyo yaran karshe sun shiga uku kafin a haifo su ai sai min dibi harka,Salma tace Kai tsaya kaji yanzu fa Autan mu yana nan a rubuce a wajen Allah,Auta yace muci gaba da gashi Allah bamu masu Albarka kiyi ta bani Oven suna ta zuwa mu ba ruwanmu akan dadi baza mu fasa ba,Salma tace for sure.

Salma ta mike tace muje Oven na kaiyayi Auta ya rike kugunta yace Ina da abin Susaaa…. Ina da abin Susaaaaa.. da Waka yake fada,tunawa sukayi sun bar Baby dinsu a Palo saman kujera suka dawo ya dauketa yace Allah sarki ba hankali Zaki ta jin ihun Daddy da Mummy amma ko kin girma baza ki sani ba sai dai ki ta ganin mutuncinmu nan kuwa Yan iskane mu iyayen naki,kita zare Ido a Dan gadonki muna ta iban harka baza ki sani ba,Yau ma Zaki fara jin ihun uwarki ba ruwan Auta wlh,Auta ya kwantar da Baby a gadonta yace kiyi bacci Yar nan baza ki gane komai ba,ko kuka kike ba daukanki zanyi ba Ina saman Mummy.

Salma suna ta dariya ta bawa Yar Nono ta fara bacci Auta yace kin samawa kanki Lafiya da kika yi bacci My love,suna kwantar da ita suka kashe light yarinya bata son duhu ta Farka ta shiga tsaga kuka,Auta ya daina latsa Salma ya kunna haske ta koma baccinta yarinya a haka suka ci gaba da gashi Auta kamar yau yake Ango haka ya zauce ya susuce,Salma ma haka sai I miss you take furtawa ta fada yafi cikin kwando.
A hankali a dangimu Nawwar ya biyawa wasu aikin hajji a Yan uwana mutu hudu Cele ma takai sauran suma Banda Omaira me tsohon ciki.

Watanni kadan Omaira tayi gadon Umma ta haifo Yan biyu manya da su mace da Namiji kyawawa,mun sha bidiri wajen Baso ya kashe kudi,Shekarar Yar Cele biyu tana yaye Noor ta samu wani cikin sai kuka take ita bata so amma Ahsan shi murna kamar ba gobe,ni kuwa da su Wise Salma duk mun dauki mataki Babu me yi da wuri,waya Cele ta min tana kuka tace yanzu Antenar ma baza kaji Dadinta ba kullum ciki haihuwa,Nace kiyi hakuri yace Zaki huta ai Idan kinyi biyu,da kyar Ahsan ya shawo kan Cele, sai da cikin ya girma ta dawo Nigeria tare da shi a gidansu.
Auta kuwa yarsu tayi wayo sosai wani wankan Swagga ake mata kullum kamar Yar turawa,kullum tana gidana wai an kawowa Abdullah budurwarsa,Yau ma Weekend Auta basu da school muma haka sai ga Auta da Babynsa an kaita Saloon an mata wani kitson style har Abdullah dinma shi yake zuwa ya Kai su tare duk kayan da ya siya mata sai an kawowa Abdallah na maza Shima,Yana kawota yace gata nan ga nononta a flask ki bata Idan ta nema,Salma ce me tatso nono a zuba a feeder a Saka cikin flask kar ya huce an kusa yayeta ma,nace to Autares yace yau Weekend shanawa zamu fita yawo zamu je gata nan ki

raineta karki bari Abdallah yayiwa Yata kiss tun yanzu nasan ku ya gado ba kunya zaiyi ba,Nawwar yana jinsa yace waye zai mata kiss din wannan yar taka marar kunya ai sai dai tayi masa, Karka isheni wai ni ni bani da aikin yi ne duk weekend sai ka tattaro yarinya ka kawo mana jego wa yace ka haifeta,Auta yace Allah ne,Cele ce tazo da yarta Noor tayi wayo itama kamar ta Auta wai gata nan Rabi zanje unguwa nace bafa gidan raino na Bude ba jiya jiya su wise suka buwayeni da Yara wlh kowa ta rike nata ni bana son Antenar ne da zaku dinga kawo min Yara,Cele tace kyaji da shi in Zaki raineta ki raineta da kika samu ma an yayeta tayi ficewarta,Nawwar yace Ina jin garin nan zamu bari kawai mu huta,Auta yace sai mu kawo

su hutu suyi watanni ya fita,Nace wlh kowa ya dinga kaiwa Mami da su Iyamami yaransa bana iya ba,a fake da son Abdallah ana cutata,Nawwar yayi dariya yace ga yarki nan tana Miki hannu,Yar gidan Auta tana ta Miko hannu tana dariya ta dafa cinyarta ta mike tana tafiya ,Na dauketa nace taho ni,na Tara musu kayan wasa da Abdallah suna ta fama,Abdallah ga mugunta duk ya bibbige Yan Yara suyi ta kuka,shi wasan ma bai iya ba sai duka.

Omaira wannan shekarar suka tafi aikin hajji ita da Baso ya biya musu,Nawwar na roka da kyar ya biyawa Dagaci da Gwaggo suma.
Cele ta haifi danta Namiji na biyu yaci Sunan Kaka Muhammad lokacin wise ta samu wani cikin da su Mandula amma ni da Star shuru munki,Ahsan ya bar Cele wannan karon ta huta.
A Karatu waec muka zana aka Saka mu a university gaba dayan mu muka ce mu kure karyar turanci muka fara karanta English abinmu,Cele ma a can Saudiyya ta fara karatun bokonta,Ahsan ya dawo da ita nan ya shiga Makarantar koyon turanci zalla ita Kuma ana mata lesson ta zana waec ta biyo sahun mu itama tace duk karyar turanci ake Dan ubanku duk mu karance shi,Auta da Salma suna gama Degree dinsu suka tafi aikin hajji daga nan suka wuce yawon shakatawa yarsu tana wajena sun bar min Nima na hada da Abdallah na kaiwa Mami can.

Gaskiya zaman mu yayi Dadi sai dai mu godewa Allah kowa muna zaune lafiya cikin fahimtar juna ba fada ba komai duk mun zama Daya kowa ya zama Dan uwan kowa,Sabreen ma ta haifi Namiji abinta,Gaji ta haifi Mace,Mairo ta haifi Namiji a gidan Najib dinta muna ta zumuncinmu da taimakon juna.

Lokaci zuwa lokaci muna kaiwa gidan marayu ziyara muna Kai taimako sannan har kwancen kaya muna Tarawa mu Kai har na Yara kanana,muna siyen gwanjo ma da yawan gaske mu Kai ayi ta rabawa marayu a gidan marayu daban daban ba sai sabon kaya ba har gwanjo da kwance duk ana kaiwa Dana Yara da na manyan ma.

Har Auta suka gama yawon su suka dawo sannan suka dauki yarsu abinsu lokacin na samu cikina karami Salma kuwa Auta yace su Yara ne ba yanzu ba.
Bayan wata tara na sake Haifo Namiji Nawwar yace na zama uban maza yace duk me son aure ya haifo Mace tazo ga Miji tayi,Auta Kuma sai ya dawo yace to Idan Baby bata samu Abdullah din ba ta auri kaninta me sunana,ya damu Nawwar sai an Saka sunansa haka aka Maida sunan Nawaf,Salma tazo ta dauke shi ta masa kiss tace Dana mijina nace dalla bani Dana ance Miki Auta ne Mijinki Zaki masa kiss,Cele tace jaraba bata danta,Star ta dinga cashe rawa tun kafin suna ma.
Yau ranar Suna kowa Yazo su Gaji,

Mairo,Yan uwana da kawaye,dangin Miji kowa muna ta Hira su Wise duk da Yaransu da suka sake Haifa munyi Hira anyi barin zance anyi rawa an cashe Kuma,da dare ya rage daga ni sai Nawwar,Auta,Salma da Babynsu,Cele da Ahsan muna ta hira nace wlh Salma ciki ne dake tana wannan boye boyen nata tace ba haka bane ita Babu,Auta yace na Kara jefa kwallo a raga wlh karya take na gaji da boyewa second goal na jefata tuni,Cele tace yeeeeeeeee an kure karya,Nawwar yayi dariya yace Allah ya shiryeka Auta,yace Ameen,Ahsan yana dariya Dan Shima yanzu yasan mene Antena da local government,Ahsan yayi magana da Yar hausarsa yace local government tayi biyayya ga Antena gashi nan tana da ciki muka kwashe da dariya,Nawwar dai rada yake min a kunne Ina dariya,Cele tace taho muyi radar mu muma ta wani cakumo kan Ahsan,Auta suna dariya yace kwayi Kwa gama zancen dai Antena ce ato mun San komai……..

ALHMDLLH

NAN NA KAWO KARSHEN NOVEL DINA YAR AIKIN KARUWAI 1&2

ALLAH YASA DARASIN DAKE CIKIN LITTAFIN YAYI MANA AMFANI DUNIYA DA LAHIRA,KUSKUREN CIKI ALLAH YA YAFE MANA

INA MIKA GODIYATA GA MASOYA WANNAN LITTAFI WANDA SUKA BATA LOKACINSU SUKA BIBIYE SHI SABO DA KAUNA,WASU NA SANSU WASU BAN SANSU BA,DA WANDA NA SANI DA WANDA BAN SANI BA INA GODIYA MATUKA ALLAH YA BAR KAUNA

WANDA SUKE MIN SHARHI NA GROUP DABAN DABAN INA GODIYA AKWAI WANDA BAN YIWA KYAUTAR PAGE BA KUMA SUNA MIN SHARHI KUYI HAKURI ABIN NE YAYI YAWA KUYI HAKURI NASO KO MASU CEWA TNX NA BASU PAGE AMMA HAKAN BAI SAMU BA AFWAN READERS.

MASU SHARHI KUNE KUKA TAIMAKA HAR NA SAMU KAMMALAWA LAFIYA INA MATUKAR GODIYA BAN SAN DA ME ZAN BIYA KU BA SAI DAI ADDUA ALLAH YA BIYA MUKU BUKATUNKU NA DUNIYA DA LAHIRA

ZANYI MISSING DINKU FANS AMMA ANA TARE AI INSHALLAH.

YAN GROUP DINA NA YAR AIKIN KARUWAI FAN INA JINJINA GAREKU DUK WANI JIN DADI NA GROUP KUNA BADA SHI SOSAI.

SAI MASU COMPLAIN GROUP AN FIYE MAGANA YANZU KAM AN GAMA WACCE TAGA DA TAKURA YANA CINYE MATA DATA ZATA IYA FITA
NA AMANATA NASAN MUNA NAN TARE BA GUDU BA JA DA BAYA HAR MU FARA SABON NOVEL IDAN DA RAI DA LAFIYA

SANNAN INA FATA MASU MAGANA DA HIRA A GROUP ZASU CI GABA,A SAMU NOVEL BANA KUDI BA MU DORA DA KARATU MUNA SHARHI MU RAYA GROUP, INSHALLAH NI ME GIRMA ADMIN INA NAN INDA RAI DA LAFIYA DANI ZA A DINGA SURUTUN DUNIYA.

INA GAISUWA TA MUSAMMAN ADMINS

AUTARESS
MRS CHIEF
NAJIDA ALIYU BICCA

JINJINA GA

BINTA UMAR ABBALE
HAUWA S ZARIA
AIDA MAMAN TASNIM

KUNA DA YAWA FA NA AMANATA DUK NA SANKU KUN SANNI INA GODIYA GA MASU ADDUA DA YABO NA ALLAH YA SAKA DA ALKHAIRI

SAI NA HUTA NA HUTA NA HUTA ZAKU SAKE JINA A SABON LITTAFI A ME ZAFI DA RADADI SHIMA ME DOGON ZANGO🤣

 

FAST DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Yar Aikin Karuwai Book 2

The most reliable and easiest way to obtain the complete Yar Aikin Karuwai Book 2 isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Yar Aikin Karuwai Book 2 in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete Yar Aikin Karuwai Book 2 booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.