Download Complete Triplet’s by Fateema Musa Romantic Hausa Novel PDF

TRIPLET’S

 FATEEMA MUSA
STAR LADY

Gargarɗi

Episode 32

Saƙabo ne ya wage wanna gabjejen bakin nasa ya fara ɓaɓɓaga dariya irin nasu na gunguma gunguman matsafa, nan take gidan ya ɗauka da karfin sautin dariyar tasa, juyawa sukayi, suka nufi hanyar da sukabi suka zo, da tsafi suka fara jan Rimsha tana bin su a baya daga kwance, Allah sarki jikin ta sai kukkujewa yake a kasa tana ihu kamar ranta zai fita.
Haka suka wuce da ita, duna yana ji yana gani dan kuwa babu abun da zai iya shima neman a kawo masa ɗauki yake.
A wanna yanayi su Barbushi suka shigo part ɗin suka same sa, kasan cewar mutumin sune kuma dole su taimaka masa saboda aikin da yake musu, cikin sauri suka ɗauke sa suka wuce da shi, dan suje su nema masa ruwan tsafi wajen Queen ko kafafun nasa zasu gyaru.
Su Ayla kuwa bayan tafiyar su Barbushi Mustapha ne ya taso yazo ya taimaka musu ya jasu zuwa ɗakin su, sanna ya mai da baba ma ɗakin sa, ya dawo ya zauna shiru ya buga uban tagumi sai haɗa zufar wahala yake, yau yaga abun daya kwance masa notikan kansa, duk sai yaji duniya ta isshe sa, ban da addu’a a ransa babu abun da yakewa Rimsha, shi kan shi baba addu’a kawai yake mata tare da tausaya mata da kuma su Ayla idan suka tashi ya zasu ji a ransu ace musu an kashe Rimsha.
Haka baba da Mustapha suka zauna jugum jugum suka buga uban tagumi kamar wasu marayu, suna yiwa Rimsha addu’a.
Wanna kenan mu leƙo Washington DC mu dawo
Sai sauri James yake ya sauko kasa daga saman bene, kamar wani mara gaskiya yana tafiya yana waigen bayan sa yana waya kasa kasa, jikin sa na sanye da suit ashe colar mai shegen kyau da tsada, kayan sun kara masa kyau sosai.
Dai dai tsakiyar palon yana waigen bayan sa bai ankara ba sukayi karo da wani bodyguard wadda ya ɗauko tray mai ɗauke da kyawawan glass cup wadda a ka cike su da drinks.
Gaba ɗaya drinks dake cikin cups ɗin nan suka kware a jikin James, zaro ido bodyguard nan yayi Allah sarki nan take jikin sa ya fara kerma, ya kasa magana saboda tsoro, James kuwa ransa ya ɓaci iya ɓaci, a fusace ya wanke wa bodyguard nan fuskar sa da wata mahaukaciyar mari, ji kake tass, dai dai lokacin Romeo ya sako kafar sa saman benen yana kokarin saukowa
Cikin jin haushi abun da James ɗin yayi rai a ɓace ya dakawa James tsawa “Are you mad James!!? Tsabar tsorata da bodyguard nan yayi na tsawar da Romeo ya daka sai da zuciyar sa ta buga a wajen ya yanke jiki ya faɗi kasa gawa, Allah sarki ya ɗauka shi Romeo ya dakawa wanna tsawar shiyasa ya tsorata haka har zuciyar sa ta buga ya mutu, dan dukka gidan idan Romeo yayi magana a hankali ma firgita su yake jikin su yayi ta kerma bare kuma tsawa ai sai mutuwa, criminals da dama tsawa Romeo ke daka musu zuciyar su ke bugawa saboda tsoro su mutu, dan duk wanda ya kwana ya tashi a Washington DC tofa yasan hukuncin GAR babu kyau, yasan GAR baya hukunci mai daɗi, mutuwar tsoron sa jama’a keyi, ganin face nashi yana cikin farinciki ma razanar da hantar manyan maza yake bare kuma in ya ɓata rai,
Subhanallah ba sai ya kai ga hukunta mutun ba tsawa kawai ya wada wa mutun zuciyar sa zata iya bugawa ya mutu, sai dai in mai sauran tsawon kwana.
Ganin bodyguard ɗin ya faɗi kasa yasa James yayi saurin tsugunnawa yana taɓa shi, ina rai yayi halin sa, ɗago ido James yayi a tsorace ya kalli Romeo dake tinkaro su
“He died” ya faɗa a razane, har cikin ransa Romeo bai ji daɗin mutuwar bodyguard ɗin ba, yasan dai jama’a da yawa a wajen suna tsoron tsawan sa, a wajen aikin su ma, wasu idan ya waro musu dara daran blue eyes na sa ya kalle su ma kawai suma suke, wasu criminals ɗin ma da ance musu GAR ne zan yanke musu irin hukuncin da ya dace da su, a wajen suke murɗe wuyar su su kashe kan su, dan a cewar su, da hukuncin GAR gwara mutuwa, da GAR ya kalleka da fusatacciyar fuskar sa kamar wani lion ɗin nan gara su mutu, bai taɓa tunanin bodyguard nasu na gida suna tsoron tsawar sa har haka ba, kasan cewar su bodyguard ɗin wajen dining table ba sojoji bane, su kawai an ajiye sune dan miƙa musu tissue paper da kuma ruwa da drinks sai serving nasu abinci.
Abun bai ma Romeo daɗi ba, wuce wa kawai yayi ya nufi hanyar fita daga palon ba tare da ya kara tanka James ɗin ba, yana fita ya turo jibga jibgan sojojin sa a kan suzo su ɗauki bodyguard ɗin su fitar da shi, aje a shirya sa zuwa mutuware,
Wanna ma ba cikin ɓacin rai Lion yayi wanna tsawar ba, da ransa a ɓace yayi ta ina ga da har shi kan shi James ɗin sai zuciyar sa ta buga.
Haka sojojin suka zo suka ɗauki gawar bodyguard ɗin suka fice da shi
Gaba ɗaya James yaji ba daɗi kuma ya ɗaura alhakin mutuwar bodyguard ɗin a kan sa, a cewar sa komai ya faru shine sila, da yayi hakuri bai mari bodyguard ɗin ba da Romeo ba zai yi wanna tsawar ba, zai zo ne kawai ya wuce su ya fice daga palon, amma gashi yanzu saboda nuna masa kuskuren sa da Romeo ke kokarin yi yasa zuciyar bodyguard ya buga.
Jiki ba kwari James ya wuce ya koma bedroom na sa dan sake wanka ya canza kayan jikin nasa.
After some hours
Shirye cikin wando jeans baki three quarter James ya fito da riga Turtle high blue, kai tsaye wannan fili na Romeo ya nufa, dan yana da tabbacin suna can.
Da excuse ɗauke a bakin sa, ya iso wajen, Romeo na zaune saman sofa daya saba zama yana latsa waya, while shi kuma Michael yana tsaye ya ɗaure wasu kwalaɓe wadda Romeo ke ɗaurewa sojojin sa idan suka masa laifi, sai ya ɗaure musu wayan nan kwalabe suna lilo ya ce su ja baya sosai su saita kwalaben da bindiga su harbe su dukka su fashe su, kuma kwalaben ba tsaye suke waje guda ba kaɗawa suke sosai suna lilo idan kayi missing na bullet ɗaya baka fasa kwalbar nan ba, to horo mai tsanani Romeo zai baka, a koi wani ruwa mai kankara, gaba ɗaya ruwan waje ice ne haka Romeo zai jefa ka ciki, ta kofar da yasa aka yiwa ice ɗin,
ka zauna cikin ice nan tsawon 3 hours kafin ya sa a fitar da kai ya sanya wasu sojojin su zane ka, kana rawan sanyi suna zane ka, idan suka maka kamar bulala hamsin sai a sake mai daka cikin ice ɗin na 3 hours again, duk wanna hukuncin na missing bullet ɗaya da kayi ne ba’a kai ga na laifin da kayi a ka kawo ka wajen harbin kwalaben bama tukun nan, wanna dalili yasa criminal da dama suke kashe kan su in dai suka san lion ne zai yanke musu irin hukuncin da za a musu, wanna ma idan yana farincikin kenan, duk wata kalar hukuncin mugun ta Romeo ya iya shi, gashi da zuciyar bala’i, ga kafiyar masifa idan yayi magana yayi ne ba wanda ya isa ya sanya shi ya sauya, baya mai mai ta magana idan yayi yayi ne, koda bakaji me yace ba to yazama dole kayi abun da yace dan ba zai mai mai ta maka ba idan kuma ba ka aikata abun da yace ɗin ba hukun taka zai yi, ga bala’i zafin rai kamar wuta, ga zafin kai, ba mai iya tankwara shi ya canza masa abun da yayi niyar yi, babu wanna mahalukin dan shi kaifi ɗaya ne, sannan miskiline na karshe, dan baya son magana, magana wahalan yi take masa, ga izzan bala’i idan ka masa magana sai ya dauki mintoci kafin ya amsa maka, bai son hayani, baya shiga tsabgar kowa, sannan bai yarda da kowa ba, sai Triplets na sa, da dad, su Uncle Herry, bayan su bai yarda da kowa ba, imma mace ko namiji.
Ɗaure kwalaben Michael yayi, sai famar harbin su yake da irin silent pistol gun ɗin nan, wayan nan kananan bindigun marasa karan nan.
Michael ya karan da bullet sau uku, yana kare wa yana kara wani amma ko kwalba ɗaya bai samu ya iya harba ba, saboda harbin wayan nan kwalabe ba wasa ba, sai wanda yaji training ya koshi, sai manyan jiga jigan sojoji masu saiti da kyau, Romeo na zaune yana ganin sa ta wutsiyar ido.
Wucewa James yayi har zai zauna kusa da Romeo, sai kuma ya fasa, ya nufi Michael tare da amsan gun ɗin, kwata kwata ya manta sai abun ya masa kamar wajen ta’addancin su yake, sai ta kwalaben yayi ya fara harɓi, tsabar iya saiti irin na James, kan kace me, ya fashe kwalaben nan dukkan, ba tare da yayi missing na bullet ko ɗaya ba, ba wani bullet da ya faɗi kasa ba tare da ya fasa kwalbar ba, sosai abun ya bawa Romeo mamaki,
dan kuwa wanna abun da James yayi kananan sojoji basu iya yin sa, horo ne mai wahala, dan ko Tga bai jima sosai da gama iya ire-iren wayan nan horon ba, abun ya ɗan bawa Romeo mamaki, kallon tsab yayiwa James yana tunanin, a iya sanin sa dai James ko yadda ake riƙe bindiga bai iya ba, dan bai koya musu ba, gara Michael ma daman shine mai karanbanin ɗaukan kananan bindiga yace zai koyi harɓi, amma James bai taɓa ɗaukan gun ba ko da sunan wasa to tayaya ya iya harbin wayan abubuwan, kuma yayi harbin ne cike da kwarewa da kwarin gwiwa, kamar wadda ya ɗauki 10 years yana karɓan horo.
Shi kuwa Michael rungume James yayi yana turo baki a shagwaɓe yace “Why to ni na kasa harbin ko ɗaya” raba jikin su James yayi yana faɗin “Baka mai da hankali ka sanya kan ka bane amma da zaka iya ai dan ba wahala” ya kai karshen maganar tare da wucewa zai zauna kusa da Romeo, sai lokacin idon sa ya sauka kan Romeo da ya tsare sa da dara daran blue eyes nasa yana kallon su da mamaki
Nan take James ya sha jinin jikin sa, dan kuwa yasan me Romeo ke wa mamaki, kwata kwata ya macen da ina yake shiyasa ya harbe kwalaben, kuma yasan wanna horo ne mai wahala, dan sai da yayi wata biyu yana koya kafin ya iya, dan ma yana da ƙwaƙwalwa da basira shiyasa yayi saurin iyawa.
Cikin sauri ya kawar da kan sa daga kallon Romeo ya fasa zaman da zai yi ma, dan dama yazo ne ya sanar da Romeo zai je party a New York kuma ba zai dawo ba sai gobe karsu neme sa, a zahirin gaskiya kuwa Meeting na su na criminals zai je.
A nitse ya sanar da Romeo zai je party, shiru Romeo ya masa har lokacin bai ɗauke blue eyes nasa daga kan James ɗin ba, ganin haka yasa James ya sauka daga wajen ya nufi hanyar fita daga wajen yana faɗin sai ya dawo, cikin sauri Michael yace “wait for me I want to go to White House so mu fita tare kawai” shi dai Romeo ido kawai ya zuba wa James yana kokarin fahimter wani abu, tunani yake ai na James ya iya wanan harbi haka
Kasan cewar baya yi musu tambayoyi a kan abun da ya shafe su, sai yayi shiru bai tambayi James ɗin ai na ya koyi har bi ba, idan ya ga wani abun da bai masa ba a tattare dasu bincike kawai yake da kan sa gani, baya tambayar su, har suka fice daga wajen bai dai na kallon suba.
Sai bayan sun tafi da jimawa sannan ya miƙe ya bar wajen shi ma, ya koma cikin gida.
Michael kuwa, suna fita kai tsaye white house ya wuce, dan yau yace bari ya kaiwa president ziyara, tun daga bakin gate bodyguard da sojojin dake tsaron white house suka fara sara masa, ko kallon in da suke bai yi ba, da wata Winter Sports Hat nasa da yansa a kan sa, saboda yawan gashin kan sa, sai hat ɗin tayi masa katuwa a kai.
Kai tsaye cikin ya wuce bai bi ta kan kowa ba, da fara’a President ya tare sa, sai turɓune fuska Micheal keyi kamar wadda aka sa shi zuwa dole, shiko president sai daɗi yake ji, saboda murna ya rasa ina zai sa Michael, saboda kaunar da yakewa GAR ne ya shafi su Michael, yana son family William jacop sosai, kasan cewar kakan su Romeo jacop Roshan babban ɗan siyasa ne kafin ya mutu, shiyasa suke da damar shiga ko ina a kasar ba wata shamaki sai ma girmamawa da suke samu daga manya manyan yan siyasa masu tasowa yanzu.
Wata dankareriyar diamond watch mai bala’i kyau da tsada president ya ɗauko ya bawa Michael kyauta, first time da Michael ya cire diamond watch na su na Triplets ba barci zai yi ko wanka ba, kuma ya cire ne dan ya sanya wanda president ya bashi, saboda ya nunawa president yaji daɗi.
Sosai president yaji daɗin abun da Michael ɗin ya masa, na cire diamond watch na su na Triplets da yayi ya sanya wadda ya ba shi, sosai agogon tayiwa Michael kyau kamar dan hannun sa a kayi ta, sanya diamond watch nasu na Triplets yayi a aljihun jacket nasa ya bar na president ɗaure a hannun sa, suka ci-gaba da hira kamar wasu friend, bayan kuma president ya kusa jika da Michael, amma saboda son da yake musu, sai ya zama kaman friend nasu idan suka zo wajen sa.
Shi kuwa James kai tsaye wajen taron su ya nufa, a in da zasu gudanar da taro cikin dajin palace, a nan zasuyi taron, manya manyan criminals uban nin gidan su James sun hallara, sun zauna sai hira suke suna jiran saukowar sauran jiga jigan ogannin nasu, sai a fara taron.
Shi kuwa Romeo yana kwance saman lallausan katafaren gadon sa, yayi kwanciyar rigingine ya tasa system a gaba yana bawa yaran sa dake shirin tafiya yaki umarni, sai faman lumshe dara daran blue eyes nasa yake kamar mai jin barci, ga daddaɗar kamshin air freshener da sanyin Ac dake ta faman tashi a bedroom ɗin nasa, gaba ɗaya wutar ɗakin nasa ya kashe farin wutar ya kunna sky blue, sky blue light ɗin ba karamin karawa ɗakin nasa kyau yayi ba, abun gwanin ban sha’awa da ɗaukar hankali.
A ɓangaren TGA kuwa, sosai wayan nan kwari suka masa illa, dan kuwa a kan gaban sa suka matsa wanna tsiyar, wajen ya kunbura sosai yayi jawur kamar jini ne a ciki, duk jarunta irin na soja sai da TGA yayi kuka, saboda ciwo a irin wanna waje ba karamin abu bane, yana da zafi sosai over, Allah sarki bawan Allah ko wando baya iya sawa saboda azaba, ga sanyi Ac amma duk da haka sai daddy ya kunna rechargeable fan ya kawo masa sai tin gaban nasa yana shan iska saboda azaba, shi kaɗai kwarin suka yiwa irin wanna lahani mai muni sosai haka, duk wannan hali da TGA ke ciki Romeo bashi da matsani dan yana can ya nitsa cikin aikin da yake.
Mu leƙa Jehan mu dawo
💞KATSINA💞
Yau ya kama Monday, tun 8 na safe a ka shiga da mum ɗakin da za’a mata aiki, while ita kuma Jehan ta shirya tsab cikin wata dakakkiyar atamfan ta super wax mai bala’i kyau ɗinkin riga da skit, kayan sun zauna a jikin ta sosai, sunbi shape ɗin coca colan ta sun mata ɗas, kasan cewar bata son ɗankwali ma bare hijabi hakan yasa ta ɗauki ɗan karamin Malaysian hijab ɗin ta pink color tare da takalmi pink color, ta ɗauko jakar ta suwaga shi ma pink color ta fito tsakar gida, ba karya duk da cewa fake face ne a fuskarta ba ƙaramin kyau tayi ba sai kamshin sauran perfume da ya rage mata take.
Kai tsaye kitchen ta nufa wajen maman Sadiq, suka gaisa sanna maman Sadiq ta mata addu’ar fatan fara aiki a Sa’a, yar murmushi tayi ta amsa da amin sanna ta fito daga kitchen ɗin da sauri saboda hayaki.
Tana fitowa sukayi karo da Sadiq yana kokarin shiga kitchen ɗin, ɗan baya kaɗan tayi tana faɗin “Good morning” zuba mata ido yayi yana kallon ta yana mai kara jin kaunar ta a ransa, tab lallai ita kuwa Jehan babu wani abu wai shi soyayya a ranta, bata san shi ba, kuma bata da wani ra’ayi a kan soyayya, ita da namiji da mace duk kallon abu guda take musu, namiji baya gaban ta, maza basu isshe ta kallo ba, kai har matan ma ita a wajen ta basu isshe ta kallo ba, bata taɓa kawo wani abu wai shi tunanin aure ma a rayuwar ta ba, a nata wautan har ta mutu dasu mum ɗin ta kawai zata yi rayuwa.
Share fisabilillah 👏

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.