Download Complete The Governor’s Wife Book 1 Page 1 Hausa Novel PDF

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

*Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani iko da kuma damar fara  rubuta wannan labari. Ina addu’ar Allah ya sa yadda na fara lafiya na ƙare shi lafiya. Amin*

*wannan labari zai zo daga kashi na ɗaya zuwa kashi na uku Insha Allah. Na ɗaya zai zo a kyauta yayinda kashi na biyu da na uku zai zo na kuɗi. Zuwa gaba kaɗan zan sanar da farashin da za a same shi*

*wannan labari ƙirƙirarre ne, idan yayi kamaceceniya ta wani fanni da rayuwar wani, wata ko wassu to bisa kuskure ne, ba ayi dan cin zarafin kowa ba*

(CONGO STATE is a fictional state in Nigeria. Jahar Congo ƙirƙirrerren Jaha ce a Nigeria)

*MAFARI*

Da ƙyar kyakykyawar matashiyar budurwa da ke riƙe da hannun Mahaifiyarta  ke jan numfashi da dogon hancinta da ya zauna ɗas a tsakiyar fiskarta wanda ya ƙara ƙawata ma ta fiskar sosai. Iskar asibitin wanda ke gauraye da warin magunguna, allurai, jini, fitsari da sauran su shi ya ke yiwa mutum iso a duk lokacin da ya kusancin farfajiyar asibitin. Ansan Asibitoci da wari amma wannan warin na sa ya fita daban. Ko dan Asibitin ta gwamnati ce, oho. Rabonta da zuwa General Hospital Congo tun wani ciwo da Abba yai kusan shekaru biyar da su ka wuce.

Ba su jima da zama a wajen reception ba wata mata mai ɗauke da jaririya ta fito daga office ɗin Likita ta ce ” wai Zainabu Inusa ta shiga”

Budurwar nan ta kama hannun mahaifiyarta su ka shige ofishin Likitan.

Lokacin da su ka shigo Likitan yana ta cike-cike  a file ɗin su. Ba tareda ya ɗago ba ya ce “Malama Zainabu mi ya ke damunki?”

“Ciwon ciki”

Da sauri Likitan ya ɗago fiskarsa saboda yadda muryan budurwar ya shige shi, bama wannan ba, a file ɗinsu an rubuta Zainabu Inusa matar aure ce mai shekaru talatin da takwas wannan budurwa kuwa da ƙyar idan ta haura shekaru ashirin da ɗaya.

Lokacin da ya haɗa ido da budurwar sai da numfashin sa ya tsaya na ɗan wasu sakanni. Muryar da fiskar ba baƙon sa ba ne amma wannan ne karo na farko da ya ke ganin ta gaba da gaba.

“Mu ne wanda Dr Ubaydullah Gidaɗo ya turo” ta faɗa da siririyan muryarta me ratsa zuciyar mazaje.

“Masha Allah! ke ce ƙanwar mu kenan. ya jikin Umma?”

Sai da ta yi murmushi kafin ta amsa mi shi da cewa jikin Umma da sauƙi.

Duban Umma Dr Hassan yai ya ce “Umma tun yaushe kika fara jin ciwon cikin?”

Ido kawai Umman ta bishi da shi har ya gama maganar sannan ta maida dubanta ga ‘yarta wacce ta fara ma ta bayani da yaren kurame. Dr Hassan ya sake baki yana kallon ikon Allah, sai yanzu ya gane dalilinta na iya sign language na kurame dan watarana a wani rahoto da ta naɗa ta yi amfani da shi wajen yiwa wani kurma tambayoyi. Abin ya burge mutane da dama amma yanzu da ya ke ganinta tana yiwa mahaifiyarta tafintan (interpreting) duk abinda ya ke faɗa sai tausayinta ya kama shi. Bayan ya gama sauraron bayanen ta ya ma ta tambayoyi sai ya rubuta mu su takardar scanning ya ce su je su yi su kawo ma sa ya gani.

Ba su suka bar Asibitin ba tun takwas saura minti biyar da su ka shigo har sai ƙarfe shaɗaya da minti biyu.

Lokacin da su ka fito daga Asibitin Keke daban-daban su ka hau saboda sauri da budurwar ke yi dan ta je wajen aiki yayinda Ummanta ta wuce gida.

Da gudu-gudu sauri-sauri ta shigo cikin ma’aikatar ta su, kai tsaye studio na biyu ta wuce domin yau ne za ta fara gabatar da sabon shiri da za a fara a tashar  su. Ƙarfe shaɗaya da rabi saura minti huɗu ta gani lokacin da ta duba agogon hannun ta. Ta ja dogon numfashi kafin ta buɗe studio ta shiga.

Zaro ido waje ta yi ganin wanda ke zaune akan kujera tareda baƙon su na mako.

Gefen C Y ta tsaya wanda ke ta faman saita Camera dan fara ɗaukan shirin.

“C Y mi yake faruwa? ya na ga Iklimah a nan”

“Sorry Sweery, Oga ya chanja ki”

“Amma…”

“We are going live in one, two, three” C Y ya faɗa yana ɗagawa Iklimah hannu.

Iklimah ta yi wani fari da ido ta fara bayani kamar haka: ma su kallon mu kuna tareda gidan Talibijin na HILL TV, inda a dai-dai wannan lokaci mu ke gabatar mu ku da sabon shiri mai suna BAƘON MU wanda ni Iklimah Jibril zan gabatar. To a yau dai mun taho mu ku da babban baƙo.  Jajirtaccen Ɗan kasuwa wanda duniya ta ke damawa da shi. Baƙon na mu dai shine Alhaji Isa Madara…

Juyawa ta yi cike da ɓacin rai ta bar cikin studio ɗin. Wannan wani irin walaƙanci ne Oga ya ma ta haka.

Kai tsaye ta wuce sama inda office ɗin Ogan su ya ke.

Gaisawa ta yi da Sakatariyar sa wata mata wacce za ta iya kaiwa shekaru Arba’in zuwa Arba’in da biyar.

“Madam Deborah Oga na nan?”

“Yana ciki” ta amsa tana cigaba da latsa na’urar computer da ke gaban ta.

Wucewa ta yi ciki zuciyar ta cike da jin haushin Ogan na su.

Office ne da ya fi kowanne girma a cikin kamfanin. Mamallakin office ɗin na zaune kan kujera yana duba wa su takardu.

A ɗan ƙaramin katako da aka ajiye a tsakiyar table da ke gaban sa an rubuta *MD  Adamu Ribaɗo*

“Ina kwana Sir”

“Lafiya”

“Sir na ga Iklimah ta karɓi shirin BAƘON MU”

“Eh” ya faɗa ba tareda ya ɗago ya kalleta ba.

“Sir amma ni aka ba wa shirin nan, ranan Jummu’a kai da kan ka ka jaddada mini cewa ni zan fara shirin nan, ni na tsara tambayoyi, ni ne na kira Alhaji Isa Madara…”

“Kin zo da wuri?” Yai tambayar yana ɗago ma ta ƙananun idanun sa.

“Sir inada uzuri, na yiwa C Y text tun da sassafe, kuma na zo kafin lokaci ya cika”

“So?”

“Sir wannan ba adalci ba ne, kuma…”

“Fita” ya faɗa da ɗan ƙarfi.

Ranta a ɓace ta fice daga office ɗin da sauri. MD ya bi bayan ta da kallo yana ƙara yabawa da wannan halitta ta Asiya.

Kai tsaye office ɗin su ta wuce wanda su takwas ke amfani da shi. Mutum biyu ta tarar a wajen ta gaishe su kafin ta wuce kan madaidaicin desk ɗinta ta zauna, ta ajiye jaka  da wayoyin ta sannan ta kifa kan ta a kan desk ɗin.

Idan mutum ya ce yana son ka ka ƙi shi shikenan sai ya zama abin damuwa.  Tunda ta fara aiki a wannan waje MD ke takura ma ta.

“Da wani ƙaton tumbinsa a wajen” ta furta a fili tareda jan dogon tsaki…

Yinin ranan gaba ɗaya a hasale ta ke saboda abinda MD ya ma ta. Ita gani ta ke ma da gangan yai hakan, dama tun asali Iklimar ya ke so ta yi shirin ba ita ba. Dama ƙwalele ya ke son yi ma ta…

Kusan ƙarfe biyu na rana su ka fita ɗauko rahoto chan wani ƙauye. Faɗa ne ya ɓarke tsakanin manyan ƙabilu guda biyu da su ke wajen.

Sun samu sun tattara bayanai sannan sun yi hira da mutane da dama a ƙauyen kasancewa an ɗaura labarin ne life. Faɗa ne da ya faro daga ƙona gona guda ɗaya sai abin ya zamo rikicin ƙabilanci akayita ƙone-ƙone.

*”bayan Gwamnatin Jahar Congo ta turo jami’an tsaro zuwa wannan ƙauye, ƙura ta fara lafawa, yayinda iyayen da aka yi awun gaba da ‘ya’yan su su ke cikin Alhini. Na tambayi wani jami’in tsaro wanda ya tabbatar mini da zaran sun gama bincike sun tabbatar babu hannun yaran nan guda biyar a sakawa gonar Malam Bala wuta za su sako su wa iyayen su. Muna fata dai wannan abin da ya faru zai tsaya a iya haka domin zaman lafiya ya fi zama ɗan Sarki. Ta ku ASIYA-SHAHIDA FARUQ BABA, tashar Hill TV”* ta ƙarasa maganar tana murmushinta mai shiga rai.

Ajiyar zuciya ta sauke lokacin da C Y ya ce cut. Ba yau ta fara kawo rahoto ba amma yau tunda ta fara ta ke jin ƙirjinta na mata nauyi. Ko dan ranta a ɓace ya ke oho. Ta ɗan ɗaura hannunta a ƙirji tana jin yadda ya ke bugawa da ƙarfi. Ikon Allah! Ko ranan da ta fara tsayuwa gaban camera ta kawo rahoto shekara ɗaya da ya wuce bata ji irin wannan tsoron ba. Lokacin da ta ke kallon camera ta sani tana fiskantar duniya ne, amma yau ji ta ke kamar mutum ɗaya ta ke fuskanta, kamar wannan mutumin da ke kallonta koma wanene idonsa yana ma ta  nauyi, ya saka ma ta tsoro, ya kassara duk wani ƙwarin gwiwa da ta ke da shi.

 Za ka fahimci halin da ta shiga ne kawai idan har ka tuna yadda ka ke ji idan wani mutum da ka ke tsananin jin kunya ya zuba maka ido. Kana jin idon sa na yawo a ko’ina na jikin ka har hakan ya saka ma ka kasala har ma ka kasa iya aiwatar da komai, idan ma kana wani abu to ka dinga kuskure kenan.

To ko dai Ubayd yana kallon news ɗin nan ne? Ta tambayi kanta.

“You Ok?” C Y ya fargar da ita daga tunanin da ta ke yi

Ta gyaɗa ma sa kai tana murmushi.

“Ko dai saboda abinda MD ya miki ne? Yau gaba ɗaya kin yi wani iri. Babu wani spark lokacin da ki ke camera”

Yana maganar yana lanƙwasa doguwar tripod da aka ɗaura camera a kai.

“Ban san mi ya ke damuna ba, its like kamar mutumin da na ke jin kunya yana kallon program ɗin nan. I’m feeling his eyes all over me”

“Ba ma her ba, his eyes. Lallai Aseey, ko kin yi sabon crush ne” C Y ya faɗa yana dariya.

Ba yau Ubayd ya fara ganin report ɗinta ba. Infact akwai ranan da ya ke wajen ma ta ke ba da rahoto a gaban camera ɗin kuma bata taɓa jin irin haka ba. Idan ba Ubayd ba waye? Certainly not Umma da Abba saboda su kam tun ma kafin ta fara aikin sun kasance confidante ɗinta. Ta iya tuna ranan da aka ƙara mata matsayi ta zama field reporter sai da ta kira suka boosting confidence ɗinta kafin ta fara aikin.

Idan ba Ubayd ba idan ba Abba da Umma ba, to WAYE?  Ta faɗa tana kallon motar su da su C Y ke faman saka kayan aikin su ciki…

***

 GOVERNMENT OFFICE, CONGO STATE,

dif…dif…dif… ƙarar da yatsar sa ke bayarwa kenan lokacin da ya ke buga table ɗin gabansa da yatsarsa manuniya. Tunda aka fara rahoton ya ke kallo bai ɗauke idon sa ba sai da mai ba da rahoton ta faɗi sunan ta sannan aka ɗauke wajen zuwa announcer da ya ke chan studio yana ƙara commenting akan abinda ya faru a ƙauyen.

Ya bibiyi labarin ne saboda shine abu na farko mai mahimmanci  da ya aiwatar a wannan shekara wanda har an kusa cin rabi cikin ta.

Mutane dayawa kallon hoto su ke ma sa. It has being a challenge lokacin da aka kira shi da gaggawa aka sanar da shi faɗan daya taso a ƙauyen Kayal ɗin. Gwamna baya ƙasar dan haka shine ya ke da damar ba da umurni a aiwatar da duk abinda ya dace gameda matsalar.

Tuni ya rattaba hannu a takarda wajen  tura jami’an tsaro ƙauyen domin daidaiton lamurra a wajen.  Ya ji daɗi da reporter ɗin ta yabawa Gwamna duk da dai shi da yai aikin ba Gwamna ba ne, da alama ko dai ta manta cewa Gwamna baya gari ko kuma dai ta furta Gwamna ne a matsayinsa na wakilin Gwamna ɗin.

Gidan Talabijin na HILL TV ba ta Gwamnati ba ce shiyasa ya damu da ganin rahoton daga tashar maimakon CONGO NEWS wacce ta ke gidan Talabijin na gwamnati ba lallai a yaɓawa Gwamnati baƙin fenti ba idan har ba su yi abinda ya dace ba sai ma ayi ƙoƙarin kare su.

READ ALSO:  Download Complete Y'AN MATA RETURN by Hafsat Hisham Romantic Hausa Novel PDF

Bai ida wannan tunanin ba wayar sa ta hau ringing. Mr Governor ya gani ɓaro-ɓaro a screen ɗin. Da sallama ya amsa wayar cikin muryarsa mai sanyi.

Daga ɓangaren Gwamna kuwa ko amsa sallamar bai yi ba ya ce ma sa maganan Albashi da zai sa hannu akai ya bari sai ya dawo tukunna.

Deputy Governor  ya ce “Mr Governor nan da kwana shida fa kenan “

“To mutuwa za su yi kafin kwana shidan?”

Bai ce mishi komai ba har ya gama magana ya kashe kiran.

Yayi tunanin ya kira ne domin yai ma sa magana akan faɗan da aka yi a ƙauyen Kayal may be ma ya yaba ma sa akan ƙoƙarin da yai wajen daƙile faɗan da wuri amma shi damuwar shi kada ya saka hannu a bawa mutane Albashinsu har sai ya dawo. Yau Albashin ya shigo daga gwamnatin tarayya, kwanan wata ya kama ashirin da bakwai idan aka ƙara kwana shida zai zama uku ga wani watan kenan, mutane za su ji jiki.

Minene amfaninsa idan har a matsayinsa na mataimakin Gwamna ba zai iya aiwatar da komai na cigaban al’umma ba idan Gwamna baya nan. Ya tabbata kenan shi hoto ne.

***

Lokacin da Asiya su ka koma office har anfara kiraye-kirayen sallar Maghriba. Tana shiga office ɗin su aka sanar da ita saƙon MD da ya ke nemanta. A gajiye ta wuce office ɗinsa, ta sani ƙorafi ne zai yi ba komai ba. Tunda a wajensa kullum ba ta iya aiki ba.

“Miye matsalar ki ne Asiya?. Today’s report was full of  crap, sati biyu Gwamna baya gari amma kina ta faɗin Mai girma Gwamna ya turo jami’ai, Mai girma Gwamna ya damu da talakawansa. Give credit to whom credit belongs. Kina ganin da Gwamna Saminu Bacci ne zai tura jami’an tsaro cikin ƙanƙanin lokaci haka? I’m dissappointed in you”

Ita kwata-kwata ta manta da cewa Gwamna baya ƙasar to ko yana nan ai Deputy Governor hoto ne. Ba abinda ta taɓa jin ance yayi sai shegen yin ado kaman mace. Indai SSK ne ko mace sai  albarka wajen iya ado.

Chief Editor na su da ke zaune a office ɗin ya kalli Asiya ya ce ” miya faru na ga rahoton ki na yau ba wani armashi, ba ki da lafiya ne?”

 “no Sir, Ummata ce ba lafiya” Asiya ta faɗa ranta a ɓace.

“Allah ya bata lafiya”

Ta amsa ma sa da Amin. Da hannu ya ma ta nuni da ta fita daga office ɗin. Bayan ta fita Chief Editor ya kalli MD ya ce ” mutumina ka mata a hankali. The girl is good ba wanda ya fi ƙarfin kuskure”

“Idan har bama nunawa jama’a goodness na Mataimakin Gwamna kullum kallon hoto za a dinga ma sa. Wallahi da shine Gwamna da jahar nan ta fi haka cigaba cikin shekaru ukun nan. S S Kachallah mutum ne da ya san darajan ɗan Adam, he’s a man of vision and mission”

“Ni zan gaya maka halin Prof Kachallah tunda ya koyar dani lokacin ina Masters …” daga nan su ka buge da hiran mataimakin Gwamnan.

Asiya na fita daga office ɗin MD ƙasa ta koma wajen office ɗin su ta ɗau jakarta ta fito.  Wani mahaukacin yunwa ke cinta ga gajiya a haka tafito daga farfajiyar gidan Talabijin ɗin. Da Ubayd na gari da shi za ta kira ya zo ya ɗauketa amma yanzu sai dai ta nemi abin hawa. Tana tsaye C Y ya fito da tsohuwar baƙar roba-roba ɗin sa.

“Ke kalar mota ce da na miki lift zuwa gida” ga faɗa yana dariya.

“Ƙaniyarka C Y, kana nufin tafiya za ka yi ka barni kenan”

Ɗan dawowa yai da baya ta hau mashin ɗin sannan ya ja suka tafi. Suna tafiyan suna taɗi saboda Clement Yohanna (C Y) akwai surutu shima kamar Asiyar shiyasa ma tasu ta zo ɗaya.

A ƙofar gidan su ya sauketa yana faɗin ta gaida ma sa da Umma.

Da sallama ta shiga gidan na su, Inna Yaha na faman jan ruwa a rijiya amma ba ta amsa sallamar ba. Ko ba ta leƙa kitchen ba ta san sai yanzu za’a ɗaura abincin dare ko kuma yanzu aka fara girkin.

Sannu da aiki ta mata duk da ta san ba amsawa za ta yi ba. Wucewa ta yi ɗakin Ummanta wadda shine ɗaki na biyu cikin ɗakuna uku da su ke jere waje guda. A kan sallaya ta samu Umman ta idar da sallah tana jan carbi, ta san ba za ta amsa gaisuwarta ba har sai ta gama azkar ɗinta shiyasa ma ta wuce wajen wardrobe ta buɗe ta fito da wata doguwar riga mai laushi, rigar guntun hannu gareta. Kayan jikinta ta cire ta saka doguwar rigan. Lokacin da ta zauna bakin gado tana naɗe wandon jeans ɗin da ta cire ne Umma ta fara mata magana da yaren Kurame inda ta ke tambayarta ya aiki, obviously ta ga rahoton da Asiyan ta kawo ɗazu a TV. Itama Asiyan ya jiki ta mata tareda tambayarta ko ta sha magani.

Ƙarfe bakwai da rabi da minti takwas bayan ta idar da sallan Isha Cornflakes ta haɗa da madara ta fara sha tanayi tana danna wayarta. Kiran Ubayd ne ya shigo wayarta amma har ta katse ba ta ɗauka ba saima tsaki da ta yi. Bayan ya jera kira biyu ba a ɗauka ba sai a na ukun ta ɗauka amma ba ta yi magana ba.

“My Aseeya” ya faɗa da murya mai sanyi.

Tasirin da sunan yai ma ta ne ya sa ta yin guntun murmushi.

“Tuba na ke ranki shi daɗe. Na san na yi laifi amma a bani dama na faɗi uzuri na”

Still shiru ba ta ce komai ba

“Mine kina ji na?”

“Mine”

Asiya ta ɗan jinginar da kanta jikin gadon Umma sannan ta ce “ni mi zan ce tunda Matan Lagos sun ɗauke mun kai. Yau tun da sassafe da muka yi waya ba ka sake waiwaya na ba sai yanzu. Na san ka kalli report ɗina na yau amma ko ka kira ka tambayi lafiyata, you dont even care ko na dawo lafiya ko ban dawo ba, kawai kai…” haka ta yi ta rantings har sai da ta gaji da kanta ta yi shiru, a lokacin ne kuma Ubayd ya samu damar lallaɓata dan ya san halin kayan sa indai tana kwarwa to ba a katseta har sai ta gama.

Bayan ta karɓi haƙurin sa ne suka bige da hiran masoya ba ta ma ji shigowar ƙaninta Aliyu ba sai kawai gani tayi ya ɗauke kofin cornflakes da ke gabanta ya fara sha. Tana ma sa magana da hannu amma inaa bai kulata ba sai ya ma koma gefe ya shanye cornflakes ɗin tas.

Bayan ya gama kuwa ya dangwarar mata da kofi a wajen yai gaba. Shigowan Umma ɗakin ne ya sa ta yi sallama da Ubayd akan za ta kirashi anjima.

Da hannu Umma ta gaya ma ta cewa ta je ta samu Abbansu a falo yana nemanta.

Sanda za ta wuce falon Abban ta kula da Inna Yaha da ke ta kwaran-kwaran a kitchen tana rabon abinci, babu wuta kuma torchlight da ta ke amfani da shi ya dafe ba haske sosai. Ba ta taɓa gajiya da mamakin halin Inna Yaha.

Asiya ta yi sallama bakin ƙofar falon Abba. Abba ya ce ta shigo.

Abba dattijone da kallo ɗaya zaka ma sa ka san ya doki shekaru sittin da biyu zuwa da biyar. Fari ne sosai a lokacin ƙuruciya amma yanzu ya fara dafewa, fiskarshi da kanshi yana yalwacce da gashi wanda kusan ya riga ya zama fari gaba ɗaya sai tsilli-tsillin baƙi da ba za a rasa ba.

Bayan ta gaisheshi ne ya ke tambayarta gameda ƙauyen da su ka je yau ɗauko rahoto. Bayan sun yi alhinin abinda ya faru tare ya sanar da ita musabbabin kiranta da yai. Magana ce akan admission da ƙaninta ya samu a Congo University wanda ya dage akan ba zai zauna a hostel ba sai dai ya dinga jeka ka dawo,  shawaran Asiya ya tambaya ko dai ya siya ma sa babur kaman yadda Habib ɗin ya buƙata ne?.

Abba ya jima da retire har yanzu kuɗin pension ɗin sa su ke lallaɓawa. Ba dan Allah yayi ita da Umma suna sana’a ba da abubuwan ba za su zo da sauƙi ba. Ubayd ma yana nasa ƙoƙari akan mahaifinsa sosai.

Bikinta da na Faty da za ayi Abba ke yiwa taru dan haka maganar siyan Babur bai taso ba. Za ta yiwa Habib magana, gigin samartaka ke ɗibanshi yana ji yanzu ya gama sakandare zai shiga Jami’a.

Bayan ta bar wajen Abba ɗakin su ta koma inda Umma ke faman tura tuwon da aka miƙo ma ta. Sau ɗaya ta kalli tuwon ta kauda kai. Ga abinci ba za ayi da wuri ba gashi ba zai taɓa yin daɗi yadda ya kamata ba.

Kafin ta kwanta sai da su ka sake yin waya da Ubayd sannan ta kira Queen Bee su ka yi maganar Salon ɗin su…

*Mi za ku ce gameda Asiya-Shahida?*

***

A chan wani ƙaton gida da ke GRA wasu manyan mutane ne guda huɗu ke zaune a wani katafaren falo daya amsa sunan falo saboda girma da kuma irin kayan alatu da aka zuba a ciki.

Ɗaya daga cikin su wanda kusan shi za a kira da babban su ya kalli  wani da ke sanye da farar shadda da farin hula ya ce “Kachallah kana ganin za mu samu abunda mu ke buƙata a wajen sa?”

Kachallah ya ce “inada yaƙinin haka Yallaɓai. Shi mutum ne mai biyayya”

Wani mai baƙin suit ya tari bakin Kachallah da cewa “inada shakka akan wannan”

“Mr Paul mi kake so ka ce, ba dai kana nufin za a rusa tsarin wannan gwamnatin ba…”

“Mr Paul, Alhaji Kachallah wannan ba abun ɗaga hankali ba ne. Har yanzu akwai sauran lokaci dan haka zamu cigaba da saka mishi ido kafin lokacin ya cika. Ko mi ka ce Yallaɓai?”

Yallaɓai ya kalli Mutumin da yai magana sannan ya maida dubansa ga Alhaji Kachallah da Mr Paul. A hankali ya fara shafa gemun sa yana yi yana murmushi. Murmushin Yallaɓai na da ma’anoni daban-daban  amma a wannan lokaci dukkan su sun yarda cewa yana nufin su kwantar da hankalin su ne, wato akwai nasara a dukkan tsare-tsaren su.

***

LADIES HALAAL SALON & SPA waje ne da ya amsa sunan sa, domin kuwa dukkan abubuwan da ake gudanarwa a wajen suna ƙoƙarin tafiya da tsarin da bai kaucewa tsarin musulunci ba. Waje ne da Asiya-Shahida, Queen Bee da Alhaja Oyiza su ka buɗe saboda samawa mata wajen kula da jikin su. Ma’aikatan wajen dukkan su mata ne.  Cikin ayyukan da su ke gudanarwa a wajen akwai wanke gashi, drying da kuma stretching, suna gyaran farce (menicure and pedicure). Ana kitso da kuma ƙunshi sannan watanni biyar da su ka wuce da su ka dawo sabon shagon su da ke anguwar  GRA suka fara gyaran jiki da spa treatment a wajen (wanda ya haɗa da body, hair and foot massage,  facial treatment da sauran su)

Shigowar Shahidah sashen da ake yin gyaran gashi da kitso ya sa wajen yai wani irin tsit. Precious da ke yiwa wata mata kitson wig ta tsaya da kitson tana kallon Shahida jikinta na ɓari.

Matar ta ɗan ɗago ta ce “ya ki ka tsaya?”

Tunda ba sa saida gashin wig kenan matar ce ta zo da abinta. Shahida ta faɗa a ranta.

Precious ba ta san ma Shahida na cikin shagon na su ba da ba za ta yi gigin fara yiwa matar nan kitson wig ba. Ta san dokar shagon su amma wannan matar Comissioner ce, duk da ta hannun Queen Bee ta zo ta tabbata za ta raɓi maiƙo a jikin matar, shiyasa da matar ta nuna kitson wig za a mata ba ta iya yi mata musu ba.

READ ALSO:  Download Complete MATAR DAMUSA by MALLAKIN ASMEETAH Romantic Hausa Novel PDF

Shahida ta ƙaraso gaban matar sannan ta kalli Precious ta ce ” ina bawa mutane dama ɗaya tak a rayuwa, na ƙarshe kenan da za ki sake taka mana dokan wannan shago. Ki maida mata kuɗinta ta bar mana waje”

“Malama ban gane mi ki ke cewa ba. Da alama ba ki san ko ni wacece ba ce”

“Duk wanda ya shigo wannan waje domin a masa wani abu a nan to sunan sa customer. A dalilin an ɓata miki lokaci za a maida miki kuɗin ki dan haka ki wuce wajen da su ke yin irin wannan kitso a ƙarasa miki a chan”

“What nonsense” matar ta faɗa a fusace tana miƙewa tsaye.

“Idan kin fita ki ɗan ɗaga idon ki sama za ki ga sunan wannan waje. Saka gashin wig baya cikin services na mu”

Daga haka Asiya-Shahida ta bar wajen. Tana jin matar tana ta zage-zage amma ko ajikinta. Ta yiwa  matar  farin sani. Habiba sunanta a  ƙasan layinsu ta taso. ta tsula bariki sosai kafin ta auri kwamishinan ilimi shekaru uku da suka wuce.

Dole ta yi magana da Queen Bee ta jawa Precious kunne tunda ita ta bata aiki. Idan irin haka ya cigaba da faruwa Salon ɗin su zai zama babu wani banbanci tsakaninsa da sauran gama gari…

**

Shahidah na zaune tana zanawa Amarya Layla lalle a hannu ta ji matan da ke wajen sun saka ihu.

Basma ta ce “Jennifer ƙara mana volume mu ji mi ya ke cewa”

Kafin ta gama maganar ma ta riga ta ƙara volume ɗin.

Muryan daya doki kunnen Asiya ne ya sa ta jan dogon tsaki ba shiri.

“Yanzu dan Allah saboda wannan wawan ku ke ta ihu”

Banza su ka yi da ita suka cigaba da yaba mutumin da ke magana a cikin TV.

“Ki ga idon sa dan Allah, ko idon kaɗai Allah ya bashi wallahi an zuba ma sa baiwa” wata daga cikin ƙawayen Amarya da ake wa Lalle ta faɗa.

“Allah ya shiryeku gaskiya. Mutum tsohai-tsohai da shi ku dinga wani drooling akan sa kaman wasu ƙwailaye”

“Ke dai ‘yar baƙin ciki ce Asiya. Allah ya isan ma SSK ɗin mu za ki kirashi tsoho”

Kafin ta yi magana kuwa Asabe ta ce “ni kin san Allah yanzu haka idan da za ace na zaɓi tsakanin SSK da kuma Ubayd ɗinki Asiya Wallahi Tallahi SSK zan zaɓa”

Asiya ta fusata ta kaiwa Asabe duka Asabe ta kauce tana yi ma ta dariya. Ranan har Asiya ta gama yiwa Amarya Lalle ba ta dena diri ba. Hayaƙi ne kawai bai fito daga bakin Asiya ba saboda yadda ta dinga faɗa akan an haɗa masoyinta Ubayd da SSK…

**

“Gashi nan ai ya ƙi biyan albashi ya bar mutane da yunwa. Idan ka yi magana kuma a fara ganin baƙin ka mtsww”

“Mine kina da abun dariya Allah. Tunda mu ka zauna a nan ba hiran da mu ka yi sai ta SSK. Ki rage ƙiyayyar ki gareshi please. Abun ya fara yawa”

“Amma Ya Ubayd…”

“Yanzu dai a ajiye maganar sa a gefe tukunna. Albishirin ki”

Asiya ta haɗe rai ta juyar da fiska gefe.

“My Aseeya haka zan tafi gida ba tareda kin min murmushinkin nan mai sanyaya min zuciya ba”

“Ka je SSK ya maka murmushin tunda ka damu da shi”

“Mi zan yi da murmushin ƙato bayan inada kyakykyawar  budurwa a kusa da ni”

“Dama ina so na miki maganar gida ne amma tunda kinyi fushi shikenan”

“Dan Allah an gama gyara kitchen ɗin?” Ta faɗa cike da excitement.

“Wagga Bafulatana ba ta da kunya samsam”

“Eh ɗin” ta faɗa tana murguɗa ma sa baki.

“Kinga ɗan bakin nan da Allah zai kaimu wata biyar da kwana shauku da na jima da maganin sa”

Asiya ta yi saurin sunkuyar da kai tana rufe bakinta da tafin hannu  tana murmushi cike da jin kunyarsa.

“Na rufe bakin ko?, gara ma ki sani a matse na ke wallahi. Abba dai ya cuceni daya saka bikin nan da nisa haka. Tunda Mustafan Faty bai gama shiryawa ba da anyi namu bikin idan ya so sai ayi na su daga baya”

“Ya Ubaydu wai ka je inji Abba”  muryan ƙaninsa Musa ya doki kunnen sa.

“Musa kana so in zaneka ko? Za ka faɗo kanmu ba sallama sai kace wani dabba”

Musa ya fece daga wajen da sauri tun kafin Ubayd ya damƙeshi dan ya san halin yayan na sa sarai.

“Barin je wajen Abba”

“Idan ka je ka kai ma sa ƙorafin ka ƙila ya chanja ra’ayi”

“Ahaf ashe ba ni ɗaya na matsu ba kenan”

Ba ta amsa ma sa ba ta wuce ɗaki da sauri.

Murmushi yai mai daɗi yana addu’ar Allah ya kai shi lokacin da Asiya Shahidah za ta zama mata a gareshi.

Asiya na shiga ɗaki ta faɗa kan gado. Murmushi ta ke yi tana jin tsananin shauƙin son Ubayd. Ba za ta ce a matse ta ke ba amma harga Allah ba ta so aka saka bikin su wata shida ba, ta ɗauka wata uku ko huɗu Abba zai sa. Koda yake duk dalilin Mustafah wanda zai auri Faty aka kai bikin da nisa saboda ya ce bai gama shiri ba. Suma ɗin cikin wata shida kam sun gama shirya komai.

Ƙaran shigowar notification ta ji a wayarta da ke gefen gado, da sauri ta jawo wayar dan ta san ba zai wuce saƙon favourite poet ɗin ta ba ne wato KaSaSa. Ai kuwa tana buɗewa taga  saƙon email ɗin daga KaSaSa ce. Tunda ta  subscribing a website ɗin ta koyaushe  ta ɗaura sabon poem za ta gani a email ɗinta.

Ta karanta poem ɗin ya fi sau biyar kafin ta miƙe ta je ta ɗauko littafinta da ta ke rubuta duk poetry na KaSaSa a ciki, ta rubuta sabon poem ɗin da aka turo. Idan Ubayd ya zo sallama dole ne ta karanta mishi poem ɗin dan ya taɓa zuciyarta sosai. A zuciyarta ta ce Allah ya zubawa KaSaSa baiwar kalamai.

***

Motoci guda biyar ne su ka shigo wani katafaren gida, irin gidajen nan ne da ƙusosin gwamnati da manyan ‘yan kasuwa kaɗai ke iya mallakan su a wannan ƙasa, shi ɗan talaka sai dai ya gani kawai ya buɗe baki ya cika zuciyar sa da buri sannan ya kaɗa kai yai gaba, amma gidan yafi ƙarfinsa.

Motocin sun tsaya ne a  farfajiyan gidan. Motar da ke tsakiya wacce ta fi kowanne  kyau wani bodyguard ya buɗe ya fito daga gaban motar da sauri sannan ya buɗe ƙofar baya.

Ƙafafuwansa da ke sanye da designer sneakers ruwan toka ƙirar Dior ne suka fara sauka ƙasa kafin sauran jikin ya biyo baya.  Dogo ne da tsayinsa zai kai kamu ɗaya da ɗigo takwas a ma’unin meter (1.8m) kusan a ido za ka ƙiyasta tsayinsa da ta shahararren ɗan film ɗin ƙasar India (Bollywood) wato Amitabh Bachchan.

Baƙi ne sosai irin baƙin da ya fi kama da na larabawan ƙasar Sudan. Sai dai na shi baƙin ya haɗu da hutu da jin daɗi sai ya zama har wani sheƙi ya ke yi yana ɗaukar ido. Idanunsa sun fi ko ina ɗaukar hankali a jikin sa. Fari fat da ɗigon baƙi wanda yai kamar an ɗiga baƙin tawada a cikin ruwan madara. Zara-zaran gashin ido da kuma gira da ke cike da baƙin gashi su suka haɗu suka ƙara ƙawata manyan idanunsa. Baƙin saje da ya haɗe da fiskarsa zuwa gemu da gashin baki suka bawa fiskar kyau da kamala.

A zahiri kallon yaro ake ma sa saboda kyaun jikinsa da ke ɓoye shekaru ,da kuma yadda akoda yaushe ya ke shiga irin ta Matasa. A ranakun Jummu’a da lokutan zuwa wajen taro na musamman kawai ya ke shiga irin ta Malam Bahaushe, amma fiye da rabin shigar sa shiga ce ta mutanen ƙasar waje. Ba abun mamaki ba ne ka ga SSK sanye da Tshirt da jeans a office tun ma kafin ya shiga siyasa har zuwa yanzu kuwa da su ke kan Gwamnati.

Kasancewar ya samu sa’ar karatu da wuri ya amshi Phd ɗin sa yana shekaru ashirin da bakwai ne yayinda ya kai matsayin Professor a shekarun sa talatin da biyar, kusan shekarun da ake ɗiba ma sa kenan idan an kalleshi wanda a zahiri an zaftare ma sa kusan shekaru goma kenan cikin shekarun sa.

Yanzu ma SSK na sanye ne da riga mai dogon hannu kalar sararin samaniya, irin yadda sama ke kasancewa  a ƙarshen yammaci kafin dare kamar wajajen ƙarfe biyar da rabi zuwa shida ɗin nan, musamman a lokacin sanyi. Wandon jikin sa ta jeans ce kalar light blue, yana sanye da agogo da kuma zoben azurfa a yatsarsa ta tsakiya da ke hannunsa na dama.

Tuni bodyguard ya amshi jakar hannunsa bayan ya sara ma sa yana ƙame jiki tareda faɗin “Excellency”

 Mataimakin Gwamna kenan *Professor Saifuddeen Sa’ad Kachallah* ingarman namiji mai cikar zati da haiba  wanda a yanzu ya ke riƙe da jahar saboda Gwamna baya gari.

Kai tsaye cikin gidan sa ya wuce wanda ya gina da halaliyarsa tun ma kafin ya shiga siyasa dan ya ƙi komawa gidan gwamnati. Daga falon farko ba kowa sai dai yana iya jiyo  hiran matarsa a ɗaya falon da wasu matan. Ya haura matattakala da zai kai shi sama inda ɗakunan gidan su ke. Ɗakin ƙaramin ɗan sa ya fara leƙawa. Yaron ɗan kimanin shekaru shida na zaune akan gado yana buga  game a laptop ɗin sa. Sa’ad Saifuddeen Sa’ad Kachallah kenan wanda kowa ke kiransa da Junior. Ya kissing goshin yaron yana tambayarsa ko yayi homework ɗin sa yaron ya amsa da eh. Ya shafa kan yaron sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin. Bai leƙa sauran ɗakunan yaran na shi ba saboda kwana uku da su ka wuce su ka tafi hutu. Babbar ‘yar sa Nana Khadija ta tafi gidan ƙanwar matarsa yayinda Aisha da su ke kira da Mahira ta tafi wajen Dadda wato kakar sa.

Wanka SSK yai sannan ya sanya farar jallabiya ya fito saboda kiran sallah da ya ke jiyowa daga masallacin kusa da gidan sa.

Hajiya Bilkisu na zaune a falonta tareda wasu mata guda uku. Ɗaya matar Comissioner ce, ɗaya kuma matar wani Senator ce, sai ɗayar kuma tsohuwar comissioner of Health ce wato Dr Madam Helen Audu.

“Yanzu dai ina so komai ya tafi dai-dai gobe, kar ya zama saboda first lady ba ta nan sai mu kasa gudanar da taron yadda ya kamata”

“Hajiya Bilkisu kar ki ji komai, ai abinda ki ke yi a wannan jaha ko firstlady albarka” inji matar senator

Bilkisu ta yi ƙasaitacciyar murmushi ta ce “indai akan cigabar jahar nan ne dole na yi ƙoƙari wajen ganin komai ya tafi dai-dai”

Madam Helen ta ce “Hajiya Bilki ni zan wuce”

“Nagode Mommy, sai mun haɗu goben” Hajiya Bilki ta faɗa da sigar girmamawa saboda Madam Helen ta girme ta sosai, idan ba ta yi sittin ba to za ta kusa kaiwa hakan.

Bayan tafiyar Madam Helen da kusan minti shabiyar sannan sauran matan su ka tafi sai a lokacin Hajiya Bilkisu ta samu damar sauke nannauyan ajiyar zuciya tana tararradin yadda gobe zai kasance. Wannan ne karo na farko da za ta gudanar da babban taro ita kaɗai. Taro ne na matan Gwamnonin Arewa wanda tun kafin tafiyar Firstlady aka tsara shi, ita ne ta kawo shawaran kuma Firstlady ta amince da shi sai dai rashin Firstlady a gari ya sa aka yi tunanin ɗaga taron  har sai ta dawo amma Hajiya Bilkisu ta nuna ba sai an ɗaga ba za ta wakilci Firstlady a wajen taron.

Bayan tafiyar matan nan ta lalubo wayar ta ta cigaba da bibiyar yadda za a sauki baƙin gobe ba tareda an samu matsala ba.

Lokacin da ta samu nitsuwa ta haura sama ɗakinta ta wuce ta yi wanka ta saka kaya sannan ta fara sallah, ta haɗa sallar La’asar, Maghriba da Isha wanda zirga-zirga bai sa ta samu yinsu akan lokaci ba.

Ƙarfe goma da kwata ta shiga ɗakin mijinta wanda ke kishingide akan gado yana danna waya yana murmushi.

READ ALSO:  Download Complete Bintu Diyar Bayi Book 3 Romantic Hausa Novel PDF

Zuciyar Bilkisu sai da ya kusa bulloƙowa  waje saboda tsallen da yai, kamar walƙiya ta zo ta ɗauke wayar hannunsa tana huci tana duba abinda ya sa shi irin wannan murmushi haka. Shafinsa ne da ya ke rubuta poems ya ke dubawa, ba mamaki yana dariya ne saboda yadda mabiya shafin ke alaƙanta shi da mace.

Saƙon wani fan ɗin sa ta gani da ya ke cewa shi a duniya ba macen da ya ke so kamar KaSaSa.

“Darling har yanzu ba za ka ce mu su kai namiji ba ne ba mace ba” sai kuma ta yi saurin gyara maganarta da cewa “gara su cigaba da yi maka ganin macen, kafin yanzu mata su dinga damunka da waya”

Mayar ma sa da wayar ta yi tana murmushi ” My Darling ka san ina kishin ka dayawa”

Bai ce ma ta komai ba ya cigaba da duba saƙonnin masoyan na sa.

“Ka ci abinci?” ta tambaya lokacin da ta kwanta gefen sa.

“Na leƙa ɗakin Junior ya riga yayi bacci, i guess tare ku ka ci dinner kenan”

Still bai amsa ma ta ba.

Ta sani idan SSK yana harkan rubuce-rubucen sa baya taɓa ba da hankali a wani abun daban, shiyasa ta haƙura da maganan ta manna  ma sa kiss a kumatu tareda faɗin goodnight ta ja bargo ta kwanta. Gobe babban rana ce a gareta shiyasa dole daren yau ta samu isasshen bacci.

A wajen SSK ba komai ya hanashi kula matar ta sa ba sai ganin cewa ɓata lokaci ne a gareshi ya faɗa ma ta kuskurenta. Shi ba ma’abocin yawar magana ba ne hakan ya sa tun farkon auren su ya ke ɗagawa Bilkisu ƙafa, sai dai maimakon abubuwan su ragu sai ya zama ƙaruwa kawai su ke yi.

 Irin rayuwar da yai buri idan yai aure ba ita ce rayuwar da ya ke yi yanzu ba.

 A wassu lokutan yakan yi tunanin idan da Misturah ya aurah abubuwa ba za su zo ma sa haka ba. Kafin ya faɗa soyayyar Misturah ta kasance abokiya a gareshi wacce ya ke iya  gayawa damuwar sa, wacce ya ke iya neman shawara a gurinta kuma ya samu shawara mai kyau.

Duk da sun taso gida ɗaya babu wannan kusancin tsakanin sa da Bilkisu. Har yau da su ka kusan cika shekaru shabakwai da aure ba zai ce ya gama sanin halin Bilkisu ba haka nan itama yanada yaƙinin ba ta san wanene Saifuddeen ba. Suna rayuwa ne tareda shamaki kamar labule a tsakanin su. Tun kafin ya zama Mataimakin Gwamna baya samun kulawar daya dace a wajen Bilkisu sannan daga shiga gwamnati abubuwa suka sake taɓarɓarewa.

 A lokutan dayake cikin ƙunci ya ke buƙatar nitsuwa daga matar sa. A lokutan da kansa ya ɗau zafi daga harkokin gwamnati ya ke buƙatar samun mafaka a wajen matar sa. A lokutan ne za ka ga Bilkisu ta shagalta da harkokin siyasa ko kasuwanci.

Tunda ta sako maganar taron matan Gwamnoni da za ayi baya tunanin ta sake saka shi a lissafinta. Idan har ta tuntuɓeshi to tana neman shawara ne bisa jadawalin da ta tsara na abubuwan da za a gabatar ranan.

SSK ya juya ya kalli Bilkisu da ta ke gwarti alamun baccinta yayi nisa kenan.

 Kafin ka yi aure duk irin waɗannan ƙananan abubuwa ba ka saninsu sai kun zauna tare na wani lokaci.

Akwai lokutan da idan zai kwanta sai ya saka auduga ko earbud a kunnensa saboda yadda Gwartin Bilkisu ke hana shi bacci, a hankali har jikinsa ya saba da hakan.

Aure sai da haƙuri, abunda ake gayawa sabbin ma’aurata kenan. Alokacin ba sa gane me ake nufi da haƙuri har sai sun kwana biyu da aure.

A farkon auren su yayi haƙuri da lokutan da zai shiga banɗaki yaga Bilkisu ta jefa pant mai haɗe da pad cike da jini a loundary basket ɗin su. Ko kuma a lokutan da ta ke fama da mura ka ga tissue papers da ta face majina da shi a kan gadon su. Ba zai taɓa mantawa da ranan da ya shiga banɗaki tsantsin majina da aka fyace a ƙasan tile ya ɗebeshi ya faɗi ƙasa ba. Yayi haƙuri da kasancewarta ba ta girki saboda a gidan su bata yi, duk da kuwa girki na cikin abubuwan da ke taɓa ma sa zuciya. Girkin Misturah na ɗaya daga cikin abubuwan da suka saka shi faɗawa soyayyarta tun bai shirya hakan ba.

“Saif wannan pepper soup ɗin yana narka zuciyar namiji yana saka mishi nitsuwa. Inada yaƙinin koma mi yake damunka idan ka ci wannan peppersoup ɗin za ka samu sanyi” abinda ta faɗa kenan lokacin da ta miƙa ma sa ɗan ƙaramin food basket da ta riƙo ma sa.

Misturah ta yi gaskiya domin ranan da ya sha wannan peppersoup ɗin ya samu nitsuwa.

SSk ya kai hannunsa ya shafa gashin wig da ya ɗan bulloƙo ta gefen hular baccin Bilkisu.

Yayi haƙuri da kasancewarta mai saka gashin wig duk da kuwa warin gashin na tada ma sa hankali.

Namiji na son mace da za ta fahimceshi, ta saurari maganar sa. Sai dai Bilkisu ba ta ɗaya daga cikin irin matan nan.

Sau dubu Bilkisu za ta yi iƙirarin tana tsananin son shi tana kuma kishin sa, hakanan kuma sau dubu ba za tayi abubuwan da zai cire shamakin da ke tsakanin su ba, har ta samu damar mallake zuciyarsa.

A lokutan kaɗaici he find solitude in poetry, shiyasa ya ke ɓoye kansa da sunan KaSaSa wanda acronym ne na sunansa.

SSK yai murmushi ganin Bilkisu ta maki kanta tareda sosa tsakiyar kan.

Duk wani mulki daya ke da shi ya tsaya a bakin ƙofar gidan sa ne, a cikin gida shi mijin Bilkisu ne, Abban Nana, Mahira da kuma Junior.

SSK ya muskuta ya jawo Bilkisu jikinsa yana sauke ajiyar zuciya, rabon daya samu nitsuwar miji da mata daga gareta kusan sati biyu kenan.

“Darling na gaji” ta faɗa cikin magagin bacci

“Kar ki damu ba abinda zan yi” ya furta a hankali wani abu na sukan ƙirjinsa…

***

“Kina jina? zan turo miki kuɗin idan na dawo daga office. Ya jikin Muttaƙa?

Tana saƙale da waya a kunnenta yayinda ta ke ƙokarin ɗaura agogo a hannunta.

“Sumayya ki tabbatar Ale bai san da kuɗin nan ba. Kuɗin maganin Muttaƙa kuma ki tabbatar an siyi duka magungunan shi”

Ajiye wayar ta yi ta fice daga ɗakin. Kai tsaye kitchen ta wuce inda Umma ke ƙoƙarin raba abun kari. Kunun gyaɗa ta yi da ƙosai da kuma soyayyen dankalin Hausa.

“Umma zan wuce” ta faɗa da yaren kurame

Umman ta amsa ma ta da cewa ta tsaya ta ci abinci.

“Zan makara Umma, amma ki haɗa min kunun da dankalin in tafi da shi office”

Murmushi Umman ta yi sannan ta fara neman inda za ta zubawa Asiya kunun.

Minti shida kacal ta ƙara aciki ta fito ɗauke da jakarta da kuma ledan da Umma ta ba ta. Motar Ubayd na jiranta a ƙofar gida dan haka tana shiga ya ja motar da gudu. Gaisawa su ka yi a tsanake ta cigaba da duba wayarta tana bitar report ɗin da ta haɗa jiya.

Tafiyar minti shabiyu ya kaisu ma’aikatar su ta yiwa Ubayd sallama ta shige ciki yayinda shima Ubayd ya wuce Asibiti.

Tana shiga office ɗin su ta printing report ta wuce da shi office ɗin Editor I.

“Weldone Shahida” ya faɗa lokacin da su ka gama duba report ɗin tare wanda kusan gyaran da ke ciki kaɗan ne.

Tana komawa office ta samu sauran colleages ɗinta suna hiran taron da za ayi yau a jihar ta su. Da SSK da matar sa Bilkisu duk babu wanda ke burge Asiya  a cikinsu.

“Shahida kin san wa za’a tura yau?”

Shahida ta girgiza kai tana cigaba da latsa laptop ɗinta.

Mike ya sake cewa ” Shahida ina tunanin Abigail za a tura fa gashi har yanzu ba ta iso ba”

“Mike kar ka dameni dan Allah. Idan ba ta zo ba MD zai iya bawa wani ai, ko kai ko Usman”

Ta sani magana ya ke son gaya mata akan kada ma ta sa ran MD zai bari ta je ta covering report ɗin wajen taron da za ayi na matan Gwamnoni. Ba ta san mi ta tsarewa Mike ba a wannan office ɗin. Tun tana bautar ƙasa kafin a ɗauketa aiki yake sa mata ido cikin lamurranta.

Ta cigaba da aiki tana yi tana shan kununta.

CY ya shigo office ɗinsu da sauri. “Aseey  ki je office ɗin MD yanzu-yanzu”

“Miya faru?” Ya ɗaga mata kafaɗa ya fita da sauri.

Ta yi saurin kurɓan sauran kunun daya rage sannan ta goge bakinta da tissue  ta fice daga office ɗin da sauri tana lura da yadda Mike ke binta da mugun kallo.

Ba ta da ikon yiwa MD musu lokacin daya sanar da ita cewa itace za ta kawo rahoton wajen taron da za ayi yau.

Lokacin da za ta tafi ya ce “Asiya bana son shirme”

“Ok Sir”

Ta sani Abigail yai niyyar tura wa saboda Abigail ta fita gogewa a wajen aiki. Tunda aka buɗe gidan talabijin ɗin ta ke aiki da su kusan shekaru shahuɗu da suka wuce kenan. Rashin Abigail Manji ne ya sa MD ya waiwayeta. A wajen CY ta ke jin labarin wai Abigail tayi tafiya, jiya da daddare mahaifinta ya mutu a chan ƙauyen su.

Ba su kaɗai ba ne ‘yan jarida da su ka zo ɗaukan rahoto kusan kowanne gidan jarida sun aiko da wakilan su. CY ya fito da kayan aiki ya shiga saita camera ɗin.

***

Chief of staff (COS) ne ya shigo ofishin mataimakin Gwamna da sauri hannunsa riƙe da ipad.

“Your Excellency za ka so ganin wannan”

SSK ya karɓi pad ɗin daga hannun COS ya danna kan video dake screen   ɗin.

Yar jarida ce a gaban hall ɗin da ake taron matan gwamnoni tana bada rahoto.

“Kaman yadda al’umma su ka shaida irin almabazzarancin da akayi a wajen wannan taro wanda ake iƙirarin anyi shine saboda talakawa. Ko ta ina talaka zai anfana da mawaƙan nan Wizkid da Patoranking da aka ɗauko daga Lagos domin matan Gwamnoni su shaƙata da waƙoƙin su?. Yayinda matar mataimakin Gwamna wato Hajiya Bilkisu S Kachallah take magana akan yadda za a gina gidan marayu, talakawa na nan suna alhinin rashin albashi, rashin ruwa ga uwa uba malaman makarantar firamare da ke yajin aiki tun sati uku da suka wuce har yanzu Gwamnati ba ta waiwayesu ba.

 Na zanta da wasu matasa inda su ka bayyana mini cewa taron da Hajiya Bilkisu ta yi wani farfaganda ce kawai da ke son ɗauke hankalin talakawa daga matsalolin da su ka sha mu su kai…”

Tsaida video ɗin yai ya miƙawa COS ipad ɗin

“Your excellency kana buƙatar mu tuntuɓi gidan talabijin na Hill TV ne?”

“A’a”

COS na fita daga office ɗin SSK ya ɗau waya ya kira commisioner of financ

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete The Governor’s Wife Book 3

The most reliable and easiest way to obtain the complete The Governor’s Wife Book 3 to purchase them from Jambandwaec.com (JAW)Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete The Governor’s Wife Book 3 inPortable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete The Governor’s Wife Book 3 booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an emailcontaining the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

 

 

 

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.