Download Complete SHAHAAB by Amnah El Yaqoub Romantic Hausa Novel PDF

SHAHAAB🌸

(Romance)

Writing By Amnah El Yaqoub

Dedicated to Aisha’s Name

9&10

Yauda sassafe yafita aiki, ko break bai tsaya yiba, wajan mama nede bai Isa yafita batare daya shiga yaga halin datake ciki ba, saida tasa masa Albarka sannan yafice a gurguje sakamakon wani zazzafan case dasuke dashi akan kama wani tsohon gwamna da sukayi, Ana tuhumarsa da cinye wasu kudade daya kamata ace anyi aiki dasu acikin jihar tasa beyi ba, banda Dan Karen bashi daya biyo baya Wanda akebin jihar, gaba daya dukkan kadarorinsa sun kama sun riqe, yana zuwa Yan jarida sukayi Kansa da tambayoyi, kasancewar labarin ya watsu acikin qasar, kowa da irin abunda yake fada, wasu na ganin laifin hukumar, wasu Kuma na ganin laifin gwamnan
Sai Bayan yagama tattaunawa da yan jarida sannan yawuce office dinsa, masu take masa baya Kuma suka dakata, ganin Ramadan na jiransa yasa yasaki murmushin dabai shirya ba, suka qarasa cikin office din
“mutanan Italy”
Cewar Shahaab
Ramadan yace “na’am Angon munirat ya ayyuka, jiya baka shigo office ba”
Kafadarsa buyu yadaga yace “wanne ango Kuma Ramadan, jiya mama ce taqi dadi, tace sotake na zauna taita kallo na”
Dariya Ramadan yayi “Hajiya Mama kenan, tana son wannan dannata qwaya daya”
“har mamaki takebani wani lokacin Ramadan, nikaina nasan idan babu ni Tofa babu mama” ya qarasa maganar yana murmushi dinmple dinsa yafuto
Ramadan yace “no, karka ga laifin ta, idan kaine a matsayin datake, nasan saika fita son Yara, saboda ita bata dauki lokaci Mai tsawo ba ta sameka, kaikuma ka dauki wasu shekaru kana jiran haihuwar baka samu ba, kaga kuwa Kai zaka fita son Yara,Kanada lafiya, aure kawai zaka qara, kafara zubo mana Yara, kaima kasan da hakan”
Cikin sanyin jiki yace “Allah yasa mudace”
Cikin rashin mamaki Ramadan ya Kalle shi, wato da gaske de bayason maganar aure, kamar Wanda munirat ta riqe masa zuciya ita kadai, akan suyi maganar auren shine ya kawar da zancen nasu Wai Allah yasa mudace, ajiyar zuciya yasauke yace “Amin, ga wannan file din, nagama aikinsu jiya Dana shigo office, binciken da’aka turani komai yayi daidai, idan kaduba zaka Gani, Bari in barka kayi aiki”
Batare da yace komai ba yaja file din gabansa, shikuma Ramadan yafice daga d’akin office din
******
Aisha data futo sassafe, tafara tattare kayan gidan ta share shi tas,radio ta kunna, Bayan tagama jin labaran safiya tana shirin kashe radio taji hukumar efcc ta damqe wani tsohon gwamna, girgiza kanta tayi ta kashe radion,al’amarin Mahmud Wakili Kuma yanzu yadena bata mamaki, tsoro yake bata,tadebi ruwan wanka a bokiti takai banda ki, Sannna Takoma Dakin Hajja tad’auki Dan qaramin brush dinta da makilin, saida ta kalli Hajja dake kan gado taga bacci takeyi sosai, sannan tasaki labulen Dakin tazare hijabin jikinta ahankali ta ajiye,sannan tacire yar yaluluwar doguwar rigar jikinta ta bacci wacce Taji jiki,
Nan da Nan farar fatar jikinta ta bayyana, abinda take 6oyewa cikin hijabi Shima yafuto muraran, gaban tsohon madubin Dakin taje ta tsaya tana qarewa qirjinta kallo,itade tunda tafara wannan abu takejin zafi, bata Isa tabigi wajanba Sai taji kamar Tai ihu,ga tauri bata Isa ko cikin bacci ta kwanta akansu ba, Kuma Sai qaruwa suke kamar tana saka musu wani abu, a tsaye suke qyam a qirjinta Yan madedeta da basufi madedecin lemon zaqi ba, ko yaushe zasu daina ciwon? Ta tambayi kanta
Jin kamar Hajja zata motsa yasa tayi sauri ta daura zanin wanka, sannan ta ajiye kayan data cire
Hajja data dade da bude ido ta kalleta tace “Mesunan qawa, idan kingama kallon kanki amadubin dage min labulen Nan zafi ya isheni, munafuka…. Idan Zaki kalli kanka saiki tasheni daga bacci kice Hajja A’i fice zanyi amfani da Dakin” (🙆🏻‍♀️😂🙈🙊)
Jitayi kamar ta nutse acikin qasa Dan Kunya, Dan qaramin bakinta ta turo gaba, sannan tafice daga d’akin tana bubbuga qafa cikin shagwa6a, ko labulen bata dauke ba (😃)
******
Da daddare suna zaune a dinning, Mai aikin mama takawo musu abinci tana jerawa, mama tace “Shahaab nifa nafara gajiya da Zaman dinning dinnan, takura nake yi, nafison na zauna aqasa”
Cikin ladabi yace “mama to mukoma Qasan mana, saina baki abincin dakaina”
“a a, yaushe zan saka wahala Shahaab, yakamata de ka nemo min wata yarinyar, wannan din aiki zaiyi mata wahala, ga girki gakuma kula Dani, ita Kuma munirat babu abinda ta’iya Sai danna waya”
Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi, yasan idan yaja maganar to ba’a Kansa zata huceba saide akan munirat din.
Mai aikin ce takawo musu lemon data Dauko a kitchen, zata zuba wa mama Nata, Sai munirat ta dakatar da’ita, tace “jeki, Bari in zuba mata”
Mai aiki tafice daga falon, mama ta kalli munirat tace “duk inda kissa take ni banason ta, nida ba namiji ba tayaya za’a min kissa nakasa ganewa? Dacan baki ta6a zuba min abincinba, Sai yanzu? Babu uwar da kike tsinana min a gidan Nan munirat, shiyasa Nima nafi ganin mutunci da qimar wadda take kula Dani akan ki, koba komai ita zata Dauko abinci na takawo min tunda tasan banason Zaman dinning, zata zauna ta dinga matsamin qafafu na saboda kumburi, zata zauna Dani tayi fira Dani ta debemin kewa idan d’ana baya Nan, duk abinda zakumin yanzu daga ke har mijin naki ai duk a banza, tunda Shima gashinan a zaune yakasa nemo min Qawata, Amma da neman 6arayin Gwamnati ne jikinsa yana rawa zaije yakamo su, anan yafi qarfi, saikace Gwamnatin ce ta haifeshi baniba”(🤭🙆🏻‍♀️)
‘Dago Kansa yayi zai bata haquri ta dakatar dashi ta hanyar d’aga masa hannu, “dakata Shahaab, banason jin komai…idan kuma zayyanomin abinda kata6a yimin zakayi danka wanke kanka saboda rashin nemo min qawata dakayi to Shima Bana buqatar ji, to mema kata6a yimin? Fadamin abinda kata6a yimin abaya, saina biyaka, barema nikam mekata6a yimin a duniyar Nan ne Shahaab?”(😂)
Girgiza Kansa yayi da sauri yace”A a, banta6a yimiki komai ba mama, kiyi hakuri”
Bata sake magana ba daga Nan, abincin da yar aikin tazuba mata ta d’auka tafara ci, munirat kuwa cikin ranta mamakin masifar mama take, akan wannan shegiyar qawar Tata da babu Wanda ya Santa, dannata ma datake mutuqar so bataqi ta6ata masa rai ba
******
Washe gari maqocin su Hajja Alhaji Audu yasake aiko musu da kayan Azumi sadaka, buhun shinkafa three brothers Dan madaidaici, da madara qaramin gongoni da siga kusan kwano biyu, Abba yafita da Kansa zaije har gida yayi masa godia, dama ya kammala sabon gidan mansa daya Gina akano, Mekai ashirin, Amma ba’a kaiga bude shi ba, duk saiya hada yayi masa Allah yasanya alkhairi tunda yazo Garin, dama Ana tunanin gobe za’a tashi da Azumi, gashi babu abinda suka siya a gidan, Sai Hajja ce take cewa zata siyo musu shinkafa awajan qawarta jummai ko kwano goma ce, Amma gashi sama taka sun samu wannan kyauta, sukam Dame zasu sakawa wannan bawan Allah?
Ummah tace “Hajja Dama wallahi babu komai a gidan Nan, Bari adiba Sai adafa”
Hajja tace “sosai kuwa, Mesunan qawa tashi kinemi wuqa kibudeta ki dauka kidafa mana, saide mu qaro macaroni da yar taliya ko guda biyar biyar ne Kuma”
Aisha tatashi ta kama buhun ta bude, Nan da Nan kuwa tadafa musu, aka zubawa kowa da Mai da yaji, suna cin abincin Hajja tace “Mesunan qawa wannan shinkafar Taki tadahu kuwa, three brothers cefa, Amma kinyi mata tahuwar three sisters”
Aisha datake hada gumi tace “tadahu mana Hajja, kede kinfi son kiji shinkafa tayi luguf, kodan ke tsohuwa ce, haqorin duk ya mutu”
Kafin Hajja tayi magana Ummah ta kalli Aisha tace “Dan Allah kicire hijabin nan, kewai bakya jin zafi ajikinki ne? Sai hada uwar zuffa kike Amma bazaki cire hijabin ba?”
Hajja ta kwashe da dariya tace “Wanne dare ne jemage bai Gani ba?”
Aisha tayi shiru, duk yanda takai da Bawa Hajja martani yau kasa mayar mata tayi, taga alama idan tayi magana to tsaf Hajja zata tona mata asiri akan abinda taga tana kallo yauda safe, haka ta kama hijabin tacire,lokaci daya taji iska me dadi tana shigarta, tsefaffan kanta me tsawo da qyalli Sai kad’awa yake saboda iskar datake shigarsa
******
Da daddare yayi shirin tafiya masallaci sallar magrib, Sanye yake da jallabiya ruwan toka, Sai carbi ahannunsa, baisaka hula ba, Amma jallabiyar tasa tayi mutuqar yimasa kyau,fatarsa tayi wani irin fresh, yana ganin musulman sojojin gidan suma suna alwala, da aqafa yake tafiya Amma yau mota yahau, kasancewar akwai kwalayen alqur’ani dazai raba, ko Allah zaisa yasamu Lada saboda gobe za’a kama azumi, Ana idarda sallar magrib din yatashi yafara Rabon alqur’ani, mutanensa suna tayashi.
Limamin masallacin ne yayi masa addu’ah, Sannna yafara yin wa’azi kafin lokacin sallar ishsha’i, wasu mutane ne guda biyu dasuke zaune asahun bayansa, yaji suna zance qasa-qasa, da alama ba’a Garin sukeba, zuwa sukayi, gaba daya Sai hankalin sa yabar kan wa’azin da akeyi, yakoma kansu, dayan yaceda dayan “yanzu Mansur kaduba kagani yanda masu kudi suke jin dadi a wannan Garin? Amma kwata kwata basa taimaka wa talakawan dasuke wasu qauyukan, kaduba kaga haduwar wannan masallacin fa, ni idan nasamu Nan ma ai naji dadi, wannan shi ake kira aljannar duniya”
Wanda aka kira shi da Mansur yace “wallahi hakane zakarai, kaga fa har kyautar alqur’ani ake bayarwa, mukam Bana zamuyi azumi a dadi, tunda ba yanzu zamu koma arewa ba, gashi babu zafi, ga ruwan sama, can Kuma Sai zafi”
Zakarai yasake yin qasa da murya yace “wallahi saida nazo Garin Nan nasan cewa bazan mutu acikin wahala ba, gaskiya kudi yayi, saboda yanzu rashin kudi yayi yawa, marasa qarfi suna buqatar taimako, inda ace masu kudi zasu dinga taimaka musu Aida sun samu Lada, wani ma baisan irin addu’ar da za’ayi masa ba, qarshan ta wani yana masa addu’ah kaga Allah ya amsa masa, saboda kowa da irin baiwar da Allah yabashi, wancen azumin fa, gidan wani maqoci na, kullum gero sukeci, safe rana dare, shine abincin, idan aka Sha ruwa kuwa farau-farau suke hadawa, dayake Ina Dan taba sana’ar qanqara to shine Nima nake Dan taimaka musu, Amma wallahi kafin akama azumi geron ne, haka cikin azumin ma de shine abincin “
Jikin Shahaab yayi Sanyi kalau, yanzu acikin wannan qasar ne za’a samu masu cin gero da azumi? Kuma Ahaka suke rayuwa?
Har aka idarda sallar Isha’i, yana wannan tunanin a ransa, daya koma gida ma suna yin dinner mama taga kamar hankalin sa baya kan abincin, kawai de yana cine
Shikuma tunani yakeyi a ransa, mutum yaci gero da Azumi?
Mama kuwa Kallan sa take,tun daga fuskarsa har zuwa faffadan qirjinsa, tambayar kanta take Anya kuwa Mahmud lafiya kalau yake? Kokuma bashida lafiya? Kwata kwata Bahaka mahaifinsa yakeba,saboda idan de bata manta ba, lokacin da sukai aure idan babansa yafara abu daya saita gudu(🙈)
Kuma idan de Shima ubansa yabiyo, to jarabar sama kadai zatasa matarsa tasamu ciki duk dade haihuwa tsari ne na Allah, to Amma shi shiru kakeji da alama de ba qalau din yakeba, duba da yanda yatsani ayi masa maganar qarin aure.
Ruwa yadauka yasha, Sannna yad’auki tissue ya goge bakinsa, zuwa yanzu yagama yanke shawarar rabawa talakawan wasu garuruwan kayan abinci, ko Allah zaisa Shima wani yayi Masa addu’ah Allah yabashi magaji, Kallan munirat yayi, ya qifta mata ido alamun yana jiranta, Sannna yayiwa mama sallama yatafi part dinsa
Bayan sunyi shirin bacci yaja munirat jikinsa ya rungume ta,ganin kamar baida damuwa yasa ta bijiro masa da maganar ten million din Dayayi mata alqawari zai bata.
Kallan ta yayi, “idan kina buqatane yanzu, to nayi Miki izni kibude loka ki dauka, ten million din Kuma tunda nayi Miki alqawarin baki to zan baki, but ba yanzu ba, akwai abubuwan dasuke gabana yanzu”
Rantane yayi baqiqqirin, Amma dayake yar duniya ce, bata nuna masa ba, saima kissing din wuyansa data hauyi, alamun furucin nasa yayi mata dad’i, dayaga tana neman janyo masa ruwa, saiya rungume ta yayi mata rad’a a kunne, yasan cewa idan tatada masa Hankali ma wahala kawai zaisha, saboda kwana biyun Nan gaba daya tasauya masa, jinta yake tamkar abinci ce medadi Amma Kuma babu Maggi da gishiri acikinsa(😲)
daga Nan yayi bacci, munirat kuwa, kasa baccin tayi, baqin ciki ne fall ranta, Sai gab da lokacin sahur bacci me dadi ya dauketa, shi kuwa tun qarfe uku da rabi yatashi yafara nafilfili, yana roqon Allah yasadashi da alkhairin dayake cikin wannan wata Mai Rahma daya kama yau
Sai shine yatashe ta tahada musu abunda zasuyi sahur dashi, shikam kawai baqin tea yasha, Bayan ankira sallah yafice masallaci.
Dasafe yana tsaye gaban mirror din dakinsa, agogo yake daurawa ahannunsa,kamar kullum yana Sanye cikin suit wadda ta kar6i fatar jikinsa, ya maqala waya a kafadar sa yana magana cikin aji
“Ramadan kayi magana da MD na company yahada manaTrella ta macaroni da taliya guda goma “
“yanzu ake buqatar trella goman?”
“no, cikin satin nan nakeso agama hadawa, Sai kayi magana da Baba yahuza, zai hadaka da mutanan dazasu dauka, Sai araba duk garuruwan daya kamata”
“ok to shikkenan, jiya naje ganin sabon company, komai yayi kyau sosai Abokina, Sai aiki ake wuta-wuta,da alama kana buqatar sa yanzu ne cikin qanqanin lokaci”
Murmushi yayi, Bayan yagama daura agogon yace “A a, ni Bani zanyi amfani dashi ba, akwai wacce zan Bawa, zan Bawa wata wadda Takeda mutuqar muhimmanci awajena”
Munirat data qaraso cikin Dakin nasa hannunta d’aukeda brief case dinsa, tasaki wani murmushi Mai qayatar wa Sannna tashigo cikin Dakin, tasan cewa itace, ta Kuma San Bayan ita, babu wadda Shahaab zaiyi wa wannan kyautar, Nan da Nan taji duk wani 6acin rai datake ciki yakau, bacin ran Data kwana dashi Daren jiya taji yatafi.
Ganin munirat din tashigo dakinsa yasa yakashe wayar, bayaso ko kadan tasan shirin dayake akanta, yafi son saide taga yabata takardun companyn
******
Hajja ce zaune cikin inuwa tana wanke jarkokin kunun Aya, tunda ankama azumi yau, tofa tarufe yin kunun Aya Kuma, Aisha na gefenta tana tsefe kalbar da’akayi mata wadda duk jelar tagama warware wa, ta kalli Hajja tace “Dan Allah Hajja kimin kitso, kullum saide amin kalba, ni wallahi nagaji kitso nakeso”
Hajja tace “haba ‘yar Nan, kika Bari saida muka dauki azumi Sannan Zaki kama Kai ki tsefe saboda kina tutiya Hajja A’i ta’iya kitso, aikuwa saide kije maqota a miki”
Kafin Aisha tayi magana wani yaro yashigo gidan yace “Hajja A’i Wai inji jummai idan kinada yar ashana kibata zata hura wuta”
Hajja tace “wacce irin ashana Kuma da wannan safiyar ko bata dauki azumin ba ita?”
Yaron yace”bansani ba “
Tace” kace mata banida ashana, saide kwalin ashanar idan tana so saikazo ka kar6a mata, saita nemi ashanar awani gidan “
Aisha tace” Hajja Dan Allah nikiji Dani “
Tace” ke bazan miki kitso yanzu ba, kanki yayi santsi dayawa, tsautsayin dayasa kika tsefe shi zaisa ki kitse abinki da kanki “
Aisha bata qara mata magana ba, tagama tsefe kanta, Sannna tadaureshi da Dan kwali, Dan batada ribom ko daya
******
Zaune suke shida mama dakinta, yanda Dakin ya tsaru, saika rantse Dakin wata budurwa ne, Kansa yana kan cinyarta, so yake yafada mata yanaso idan yagama ginin companyn yabawa munirat to Amma yana tsoro, danhaka saiya sauya shawara yace “mama akwai kayan Azumi dazan raba, idan akwai Wanda kike so akaiwa saiki fadamin Inyi musu magana”
Mama tace “A a Shahaab, banason komai, abu daya nakeso awajanka kawai”
Cikin Sanyi jiki ya kalleta, yana tsoro karta ce masa yaqara aure, yace “mekikeso mama?”
Tace “nariga na fitar da rai da ganin Qawata Aysha,inajin Sai a darussalam zamu hadu,lokacin danaje gidansu neman ta, mutanan unguwar sun fadamin babanta yakoma jigawa da aiki,danhaka inaso kasamu lokaci, kaje jihar kaginamin gidan marayu acan, inajin Aysha tarasu, bansan Kuma tayaya zan taimaki wani Nata ba, qila tarasu tabar marayu, idan Allah yasa yayanta suna daga cikin Wanda za’a kawo su gidan marayun shikkenan kaga Nima na taimaka mata, qila haka Allah ya qaddara mana nida ita, Allah baiyi zamu cika alqawarin mu, muhada Yayanmu aure ba”
Shahaab ya Lumshe Idonsa, yabude, shifa wannan maganar hadin auren ne yasa bayason aga matar Nan, to Amma Yaya zaiyi? Ahankali yace “to, za’ayi”
Tace “yaushe?”
Kallan ta yayi yakasa magana, Nan da Nan ranta ya6aci tace “nifa Naga alama bakasan nemomin qawata Shahaab, Kuma muddin a kaga Aysha, saika auri yarta inde mace ta Haifa, saide in ta aurar da’ita ne, daga min cinyata tunda ban’isa insaka kayi ba”(😅)
Sake rungume mata cinyoyi yayi,tamkar zaiyi kuka cikin shagwa6a yace “Allah bazan tashi ba, to yanzu ni mama yakike so inyi, aiki yamin yawa, da wanne zanji? Ga company’s, ga office dinmu, ga gida”
Kallan sa tayi yana magana kamar zaiyi kuka, ahankali tace “Shahaab, koba Dan qawata Aysha ba, zaka samu Lada kaima idan kayi”
Cikin gajiya da maganar yace “zansa ayi”
Cikin damuwa tace “to yaushe zakaje? Zanbaka kudin ma, nide fatana kawai ayi”
Jikinsa ne yayi Sanyi lokaci daya, lalle mama da gaske take, sake rungume ta yayi yace “mama kibar kudinki, awanne gari kike so ayi a Jigawan? Wanne Gari qawar Taki take?”
Tace “bansan garinda takeba Shahaab, kawai kayi a inda kaga ya dace”
“to mama zan shirya naje cikin satin nan tunda zan raba kayan Azumi, zanyi magana da Ramadan acikin jerin garuruwan da za’a raba kayan azumin, su saka da Garin jigawa, ni sai naje Jigawan da kaina, in raba musu kayan azumin, inyi maganar gina gidan marayun da Gwamnatin Jihar “
Ahankali mama tasaki wata irin ajiyar zuciya tace”nagode MAHMUD, Allah yayi Maka Albarka”
Tamiqa hannunta Qasan fillo, tad’auki kudi bandir daya tabashi tace “ungo wannan nakane”
Murmushi yayi, dimples dinsa suka futo, yatashi daga kan cinyarta, yayi kissing kumatunta, sannan yace “nagode mama” yatashi yatafi part dinsa cikin murna yana jin dadi kamar tayi masa kyautar miliyoyin kudi.
Bayan Ansha ruwa yana zaune agaban mama, munirat na Gefe tana danna waya kamar kullum, wayar Ramadan yakira, cikin zolaya Ramadan yace”kaga Angon munirah ita kadai “
Murmushi yasaki yace” Ramadan, a cikin kayan daza’a raba na dinnan, atura mota biyu zuwa jigawa, a Kwai aikin da zanje inyi acan, Nima inaso inshiga cikin masu rabawar araba Dani, inason in Dan wara jinin jikina”
Hakanan munirat ta tsinci kanta da faduwar gaba, batasan dalili ba, har saida ta daina danna wayar datake tazuba masa ido tana kallon sa, menene Kuma zai kaishi wata jigawa? Waye nashi a jihar?
Ganin babu Mai bata amsa Sai shi, shiyasa tabar maganar har zuwa lokacin da zasuje kwanciya.
Cikin murmushi Ramadan yace “Tofa, yauda kanka Abokina? Amma dakayi zamanka, duk abinda kakeso umarni kawai zaka Bani, zanje inyi ma shi, meyasa zaka wahalar da kanka kana Rabon abincin sadaka?”
“inason yine Ramadan, may be wasu suyimin addu’ah Allah ya amsa”
Ramadan yace “hakane, Allah yasa mudace, idan Kuma Rabon wata ne zai kaika shikkenan”
“babu wannan maganar”
Abinda yace kenan.
Ramadan yace “to ai shikkenan saika koyi cire suite, tunda kace da kanka kakeso ka bayar, kaga bai kamata kayi aiki da suit ba ranar”
“okay” shine kawai abinda yace Sannan yakashe wayar
Washe gari yana gab da barin office aka kawo masa wani file akan case din gidan man fetir din wani bawan Allah da’aka kama akano,Me Kai ashirin,Bai tsaya ya duba file din yanda yakamata ba,ya turashi zuwa wani office din,suje suyi aikin komai
******
Hajja da Aisha suna tafe, rana Sai dukansu take, ga azumi, dawowarsu kenan daga gidan Alhaji Audu maqocin su, Wanda suka je masa jaje sakamakon qwace masa sabon gidan mansa da hukumar efcc tayi, daga Nan Kuma suka biya suka gaisa da jummai, Sannna suka taho gida, Hajja Sai mita take “Kai wannan bawan Allah, Allah kadubeshi su sakar masa gidan mansa, mutum Mai mutunci, me sunan qawa kiduba kiga yanda yake dawainiya da duka mutanan unguwar Nan, akawo mana wannan akawo mana wancen, Allah yasaka masa, Allah yakwato masa haqqin sa, Dan baka Isa fada da Gwamnati ba, saide ka hadata da Allah “
Aisha tayi shiru tana tunani a ranta, tasan cewa de idan ba wannan Mahmud wakilin ne yakama ba to tabbas Shima zai iya sakawa akamawa Alhaji Audu gidan mansa, tunda shi kowama kamawa yake, bashida wani motsi saina kama kayan mutane, to gaba-gaba ma tsaf zai iya kama babansa, tunda kowama tuhumar sa yake. (🙆🏻‍♀️)
Ranar haka ta wuni tana tunanin wannan mutumin, ko abincin shan ruwa bata iya dorawa ba, shi kuwa wannan wanne irin mutum ne?
******
Yau azumi anyi sati daya kenan, Sai yanzu ne Kuma abubuwa sukayi masa d’an sauqi, duk garuruwan daya ce aza6a araba kayan Azumi ko’ina anbasu banda jigawa, Shima Dan yace yanaso yaraba da Kansa ne, yanar gizo, gidan TV, dakuma gidajen redio Sai maganar sa ake, Ana Jinjina wa namijin qoqorin Dayayi,su Hajja Kam dasuka ji Ana fada a gidan redio cewa tayi
“mukam Rabon Naka baizo mana nanba mesunan mamuda”
Aisha kuwa haushi hajjan ma tabata, Wai mesunan mamuda, ko Yaya ma za’ayi ta had’a wannan mutumin da baban ta?(🤔).
Kamar kullum Sanye yake cikin suit Tayi masa kyau sosai, munirat dake fesa masa perfume, gabanta Sai qara tsananta faduwa yake, batasan meyasa ba haka kawai itade batason tafiyar Nan tashi, ta Kalle shi cikin kissa tace “my dear, nifa banson tafiyar Nan taka,I don’t know why”
Fuskarta yakama yariqe ta tafukan hannunsa biyu yace “bafa dadewa zanyi ba, kema kinsan banson yin nesa dakeda mama, Amma nayi Miki alqawarin duk inda nake, kina Nan acikin zuciya ta,”
Cikin shagwa6a tafara yimasa wani irin kuka, baisan Yaya zaiyi mata ba, rarrashin ma kamar 6ata lokaci ne, lokaci daya yahade bakinsa danata, wayarsa dake kan gado ce tasa yadaina abinda yake, sakamakon Kiran Ramadan daya shigo.
Cikin kunnan ta ya rad’a mata “ki gyara min abuna sosai kafin nadawo”
Cikin kunya tasake boye fuskarta a qirjinsa.
Shi yana nufin tasake gyara yanda ya kamata tadawo kamar da, ita Kuma kunyar dataji tayi tunanin yaji ta yanda yakeso ne,magungunan datake Sha sun kar6eta, shiyasa yake fadar hakan
hannunta yakama cikin murmushi suka futo falo, daga Nan yayi mata sallama yatafi
Saida yabiya wajan mama yamata sallama, tayi masa addu’ah Sannna yatafi.
A Airport suka hadu da Ramadan, duk Wanda yasan shi saiya yi masa gaisuwa kafin yawuce, yau baisaka I’d card dinsa agaban suit din tasaba, a tsaye suke ko wajan Zama basu nema ba, kafin jirgi yatashi wasu daga cikin ma’aikatan efcc dakuma folice suka ruqo wani mutum kana ganinsa kasan badan qasar bane, Sai magana yake musu da Harshan turanci Amma yanda suka maqala baqin glass a’idon su babu ma Wanda yake saurarensa,hayaniyar datake tashi ne yasa suka juya shida Ramadan, suma ma’aikatan ganin MAHMUD din yasa cikin ladabi suka nufeshi, kudaden dasuke cikin jakunkunan suka juyesu aqasa, sun kamashi ne da kudi zai fita dasu wata qasar kimanin million Dari biyu na Dalar amurka cikin jakunkuna, me Yan jarida zasuyi inba dauka ba, shikam Shahaab kasa magana yayi, saboda da alama wani 6arawon Gwamnatin ne yayi amfani da Yaron domin a turashi da kudin yakaishi wata qasar.
ya kalli Yan jaridar yaga sun taru anaso yayi magana Kai kace Dama awajan suke suna jiran akama mutumin
Haquri ya basu yanemi uzuri tafiya ta kamashi, yanada ganawar da zaiyi tareda gwamnan jigawa nanda awa uku, wannan Kuma wani Babban case ne, idan ya dawo zasu zauna suyi tsatsauran bincike akan case din
Yana fadar haka yayi gaba, yana jin yanda Yan jarida suke kira “yalla6ai tambaya daya, please tambaya daya yalla6ai kawai”
Suna cikin jirgi Ramadan yana gefensa yana duba jarida, shikuwa Shahaab Lumshe Idonsa yayi, Qalubalen dasuke gabansa akan wannan matsayin dayake ciki shi yake tunani, yasan cewa tabbas baza’a Rasa masu shirya masa gadar zare ba, duba da yanda yake kama duk wani Mai sa hannu akan cin hanci da rashawa.
Kamar yanda yafada hakance ta kasance, suna sauka Kai tsaye Tahir guest palace (Annex) suka sauka, Sai lokacin dazasu ga gwamnan Sannan suka tafi, basu dauki lokaci Mai tsawo ba ya tabbatar musu za’a samu Dajin daya dace agina gidan marayun, acan kusa da Garin Kiyawa, saida aka nuna musu komai a photo dakuma wasu garuruwan ma daban, suka Kuma tabbatar masa kamar yanda ya za6a din, ayi adajin kiyawa Amma wajan da zai kasance kusa da cikin Gari suke so.
sunji dadin yanda aka kar6esu,Kuma abun yazo musu da sauqi kasancewar filin na Gwamnatin Jihar ne,Bayan sungama akayi musu photo Sannna suka koma masauqinsu
Suna zuwa Shahaab ya daura towel yashiga wanka, Bai dade da futowa ba aka kira sallar magrib, shida Ramadan suka tafi masallaci Bayan sun dawo suka Sha Fruit da sauran abubuwan buda baki
Bayan sun dawo daga sallar tarawih sun dade suna kallon labarai shida Ramadan, saida matar Ramadan din ta kirashi awaya Sannna yayi masa sallama yatafi dakinsa, shi kuwa da mama kawai yayi waya, yafada mata yanda sukai, taji dadi sosai, munirat kuwa wayarta akashe, tunda yayi try bata shigaba saiya haqura ya kwanta.
Washe gari sukaje sukaga wajan, aka auna yanda abubuwan zasu kasance, suka tsara yanda aikin zai dinga gudana, dakuma mutanen da aka damqa aikin a hannun su
Awajan suka wuni Sai gab da shan ruwa suka koma hotel, washe gari aka fara tono, manyan motoci suna kawo bulo, wasu yashi, wasu siminti, saida yaga aikin yafara kankama Sannna suka tafi, da magrib suna shan ruwa Shahaab duk tunanin matarsa ya isheshi, duk rashin dadinta yana rage zafi da’ita a hakan, cikin kwana ukun Nan da sukayi shi yasan yanda yakeji, wata irin sha’awa yake ji kamar zaici babu, sauqin sa daya yataho da qananun wandunansa masu kamar pant, yana sakawa, Amma badan hakaba ya tabbatar wataran idan yafita Sai yaji kunya,saide yadinga tafiya yana bude qafa saboda tsaro(😎)
Saboda haka Gara suyi abinda yarage musu kawai yakoma gida, yajuya ya kalli Ramadan yace “yakamata mu raba kayan azumin Nan Ramadan, yau ankai azumi na goma kenan,sonake gobe mu wuce gida”
Ramadan yace “Dasafe zamu raba kayan ne?”
Girgiza Kai yayi “da nayi niyyar mu raba da safe da yamma saimu tafi gida, to nariga nasai mana tickets Dasafe jirgin mu zai tashi”
Cikin sauri Ramadan yatashi zaune yace “Wai kana nufin yanzu daga shan ruwa zamu fara daukar kwalin taliya da macaroni muda yakamata ace mun huta?”
Murmushi yayi yace “ba Lada muke nema ba? Yazakayi?”
Kamar zaiyi kuka yace “to yanzu Yaya zamuyi?”
“kira mun Wanda kayan yake hannunsu kagani” cewar Shahaab
Babu musu Ramadan yakira su, yasaka wayar a hands-free sannan ya ajiye ta a tsakanin su
Cikin aji Shahaab yace “yawwa kana Jina, muna sone muwuce gida gobe insha Allah, so kayan Nan za’a rabashi yanzu, Wanda basu qare ba saiku qarasa gobe, Ramadan zai kar6i account number ku, insha Allah Zakuga saqona”
Cikin ladabi Yaron yace “to yalla6ai, yanzu Yaya za’ayi Rabon kenan?”
Shahaab yace “akai trella daya yankin Hadejia da gumel, dayar Kuma abarta anan yankin dutse,ku dauki Rabin trella ku raba a wasu qauyukan saiku saka mana Rabin acikin mota, direban yazo Nan Tahir guest palace ya daukemu muje mufara rabawa”
Cikin biyaiya yace “to wanne qauyukan zamuje yalla6ai?”
Murmushi yayi yace “aika fini sanin yanayin garin, ku kukasan yanda zakuyi, but mude mungaji,kafadawa direban qauyukan dazai kaimu, Amma qauyukan dasuke kusa, Wanda muna gamawa zai dawo damu hotel”
Nan da Nan Yaron yace “yalla6ai akwai,
Dan masara, da Chai-Chai, Abaya, Baranda, dakuma Chamo, da…. “
Cikin sauri Shahaab yatareshi yace”kai Kai kai kaga ya’isa haka, kafada masa yakaimu chai-chai, idan mungama dasu saiya kaimu inane kace na qarshen?”
Cikin sauri yace “CHAMO yalla6ai”
Cikin yatsina fuska yace “to yakaimu chai-chai da chamo, nagode” daga haka yayi masa godia suka kashe wayar
Kallan sa Ramadan yayi yace “wanne irin Rabon kayan abinci ne wannan da daddare kamar munafukai?, yaushe zamu tafi mufara to?”
Murmushi yayi yace “sahabban manzon Allah (S.a.w.) haka suke yi, suna ajiyewa talakawan su kayan abincin aqofar gida, duk Wanda yafuto Dasafe anan zai Gani, idan muka idar da sallar tarawih Sai mutafi, kafin Nan direban yazo, idan mun samu mutum aqofar gidansa saimu bashi, idan baya Nan saimu ajiye masa aqofar gidansa”
Suna wannan maganar aka kira sallah, futowa sukai suka tafi masallaci, tun kafin su idar direban yazo yake jiran su, suna futowa daga masallaci suka wuce, Ramadan ya kalli Shahaab ya kwashe da dariya
Kallan sa yayi yace “lafiya?”
Ramdan yace “kawai shigarka ce tabani dariya, yau babu suit, Kaci wani jallabiya kamar balarabe”
Murmushi yayi suna shiga motar Shahaab yace “aini dadin hakan nakeji, Jina nake wani iri, babu masu tsaro, babu sojoji, babu Yan sanda, sainake ganina kamar kowa”
Ramdan yace “gaskiya hakane ai Naga alama jihar akwai Zaman lafiya kowa yana harkar sa babu wani tashin Hankali”
Suna tattaunawa har suka Isa chai-chai, Shahaab Kam kallon mutane yake kamar yaga sabun halitta, idan yaga wani gidan Sai yaji kamar yayi kuka, Ahaka harsu ka sauka, aka hadasu Dame unguwar Garin, ya gayya to musu wasu mutanan, Shahaab da qura tafara tashi saiya nemi face-maks dinsa yasaka, shida Kansa yace “duk mutum daya abashi taliya katan biyar, macaroni katan hudu”
Nan da Nan masu unguwa suka fara rabawa mutane abincin gida gida, Shima yad’auki wani Ana kaiwa dashi, Ramadan ma haka, basu suka bar Garin ba Sai daya saura, Ramadan ya kalli Shahaab yace “Abokina bakasan wani abu ba, nifa Garin Nan ya birgeni, gashi dare yayi Amma muna tafiya cikin kwanciyar Hankali babu kidnappers, babu masu fashi, babu 6arayi, Dan Allah kagani”
Kafin Shahaab yayi magana
Direban ya jiyo ya Kalle su yace “yalla6ai zamuje can chamo din?”
Agogon hannunsa ya kalla yace “muje”
Babu musu yaqara gudun motar suka dauki hanya, Sai qarfe daya da wani abu suka qarasa cikin Garin chamo, Garin yayi shiru babu motsin mutane, Shahaab ya kalli gidajen Garin yana qare musu kallo, baisan meyasa ba, Bai kuma San dalili ba haka Nan yaji gabansa yana wata irin faduwa, Bai kawo komai a ransa ba haka ya share, suka tsaya a tsakiyar Garin, duk suka futo daga cikin motar, motar datake binsu da Kayan itama ta faka
Samarin dasuka zo da motar kayan suka Kalle shi “yanzu yalla6ai ya za’ayi? Garin nanfa sun kwanta wallahi, zaku tafi gida ne mu saimu kwana Dasafe muraba musu kokuma akwai shawara?”
Agogonsa ya kalla yace “no, kawai muraba musu, kowa idan yatashi saiya Gani da asuba”
Nan da Nan suka fara rabawa, babu motsin kowa saina su, wasu suna saukewa daga cikin motar, wasu Kuma suna rabawa, Ramadan ya tsugunna yadauka yanufi wani gidan yana tunani a ransa gaskiya sahabai sunyi kokari, Kuma suna neman aljannarsu da gaske
Shahaab ma dauka yayi yanufi wani gidan can daban, ya ajiye a kofar gidan, sannan ya dawo yasake dauka yakai qofar gidan Jummai qawar Hajja, sannan yasake dawowa ya dauka yakai gidan Alhaji Audu Wanda hukumar efcc ta qwacewa gidan mansa, dawowa yayi yarungumi taliya guda hudu ya jibge a kofar gidansu Aisha, Sannna yakoma zai Dauko sauran
Cikin baccinta taji wani irin fitsari, cikin sauri ta tashi tad’auki buta da gudu tashige bandaki Dan kwalinta a hannu,ta tsugunna tana fitsari tana daura dankwali, mamaki take wanne irin fitsari ne wannan kodan ta dirki ruwa da yawa Bayan tadawo daga masallaci sallar tarawih dazu.
Jitayi kamar an ajiye wani abu aqofar gida, mamaki ya kamata, saida tayi tsarki Sannan tafuto daga bandakin, cikin sand’a ta nufi hanyar kofar gida tana so ta leqa taga qaran menene wannan, tana zuwa bakin kyauren nasu Sai taji takun mutum, gabanta ne yafadi to kode 6arayi ne?
Matsawa ta sake yi, ta sunkuya taleqa ta cikin wata yar qaramar 6ula inda kyauren yafara cire wa, mutum tagani ya tsaya a kofar gidan, Amma bataga fuskarsa ba, Adede lokacin shikuma Shahaab ya ajiye sauran macaronin daya Dauko, yana ajiyewa kwalin macaronin ya bugi kyauren, jikake garam Sai a fuskar Aisha (😂)
Cikin azaba tace “wayyo goshina”
Mamaki yakama Shahaab, mutum, Kuma muryar mace acikin wannan Daren? Fitilar wayarsa ya kunna, sannan yasaka Hannunsa yatura kyauren cikin mamaki yaganshi yabude alamun basuda Sakata a gidan, yana budewa Idonsa ya sauka akan dogon gashinta Wanda yarufe mata fuska, dankwalin Nata na hannunta, yayinda hannunta guda daya yake kan goshinta tana mulmula wajan data bige, gabansa ne yafadi, wannan kwa mutum ce? Wanne irin gashi ne wannan?
Hannunta tad’auke daga kan goshinta ta d’ago fuskarta ta Kalle shi tace “waye?”
Baisan metake fad’a ba,gaba d’aya hankalin sa, tunanin sa, dakuma Idonsa yanakan kyakykyawar fuskarta yana qare mata kallo, hannunta ya kalla yaganshi fari tas, yasake kallon hannun ko zaiga alamun shafe-shafe, Nan ma yaga babu, ya kalli Dan qaramin bakinta Mai launin pink, mamaki yasake kamashi, tayaya? wannan kyakykyawar yarinyar acikin wannan qauyen?
Ganin tana magana yayi shiru yasa ta meqa hannu dede fuskarsa ta had’a hannayenta suka bata sautin d’as d’as, cikin sauri ya dawo hayyacinsa ya kalleta, cikin masifa tace “waye ya aikoka da wannan kayan?”
Yayi mamaki yar qarama da’ita Amma ta’iya masifa da wani Dan qaramin bakinta kamar gidan tsuntsu, abun mamaki Wai shi ake tambaya waye? Lalle Allah daya gari bambam,dama akwai mutanan da zasuce wai basusan waye MAHMUD WAKILI ba?
Baisan meyasa ba, baisan Yaya akai ba, lokaci daya ya tsinci Kansa dabin shawarar mama da Ramadan, maimakon yafada mata waye shi, saiyace “sunana SHAHAAB”
Cikin 6acin rai tace “to koma de waye, Mahmud Wakili ne kaima yaturo ka Rabon kayan abinci kamar yanda yaraba a wasu jihohin ko?”
Mamaki ya kamashi, Yaya akai tasan sunansa Amma batasan waye Shiba? Bai iya bata amsa ba Sai kansa daya daga mata kawai
Hannu tasa ta gyara dogon gashinta yakoma baya, Cikin jin dadi tace “Alhamdulillah, dama na Dade inaso na ganshi, ka dauki tsiyarsa ka maida masa, Bama so, kafin yabamu abinci Dama can muna rayuwa, shine matsiyaci Mai Kama kudin talakawan Allah yana riqewa,Kuma dayake kama mutane yana qwace musu Kaya Shima ai abun atuhumeshi ne, tunda bamusan daga Ina yasamu kudin dayake facaka dashi ba, qila ma kudin talakawan ne, saboda haka bamaso, Kuma kakoma kafada masa muddin nahadu dashi to haduwar mu bazatai kyaub……”
kafin ta qarasa ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.(✋🏻)
Bai saba ganiba, Bai taba ganin Wanda ya tunkareshi fuska da fuska yafada masa baqar magana haka ba, asalima kowa girmamashi yake Ana ganin qimarsa, babu Wanda yake masa rashin kunya saide lallashi, inda ace yana candy yayi aure ya tabbatar da tuni ya haifi kamar wannan yarinyar, cikin 6acin rai da daure fuska ya matso da fuskarsa dab da Tata har sunajin hucin numfashin juna, yace”ke!!!, marar kunyar yarinya, yar qanqanuwa dake kin’iya masifa, idan naqaraji kin zagi ogana saina kakkarya qasusuwanki na zubar anan wajan, maza dauke wannan kayan kikai ciki “
Mutara zuwa gobe

FREE DOWNLOAD

READ ALSO:  Download Complete GIDAN KASHE AHU Romantic Hausa Novel PDF

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete SHAHAAB by Amnah El Yaqoub

The most reliable and easiest way to obtain the complete SHAHAAB by Amnah El Yaqoubisto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete SHAHAAB by Amnah El Yaqoub in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete SHAHAAB by Amnah El Yaqoub booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.