Download Complete NIHAAD Chapter 17 By Khaleesat Haiydar Hausa Novel PDF

By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

Har daki Umma ta tadda Nihad tace “Toh Abbanki ya amince sai ki fara hada kayanki” Cike da farin ciki Nihad ta mike ta rungumeta tace “Nagode sosai Umma” Umma tace “Sai dai fa Abbanki yace driver xai dinga xuwa duk safiya yana daukarki ya kai ki makarantar sannan idan kun gama lectures ya maida ki gida” Nihad ta zaro ido tace “Toh Umma ya xan yi?” Umma tace “To na dai amsa ma Abbanki, amma ke yanxu sai ki samu Drivern kice masa ba sai ya je ba, xaki dinga tafiya da motar Kamila, should Incase Abbanki xai masa magana….”

Nihad tace “Toh shkkn Umma” Umma tace “Xaki makarantar yau?” Nihad tace “Ehh ina da lectures karfe sha biyu” Umma tace “Da sauran lokaci ai, sai ki fara harhada kayanki against tomorrow…” Daga haka Umma ta juya ta fita dakin, Murna a wajen Nihad ba a cewa komai, she is going to have enough freedom yanxu, wanka ta shiga bandaki tayi sannan ta fito ta shirya, bayan ta shirya ta fita xuwa bangaren Mumy, Mumy na gyaran bedroom dinta Nihad ta jingina da kofar dakin da damuwa tace “Mumy kin ji abinda Abba yace?”

Mumy ta kalleta tace “Na me kenan?” Nihad ta marairaice tace “Mumy ni ba son zaman gidan Aunty Kamila nake ba, it’s so boring there, ni kuma ban san ya xan yi ba” Mumy tace “Then u speak for ur self Nihad, ni me kike son ince a nan?” Nihad tace “I don’t Know what to tell Abba” Mumy tace “Ki nemi abinda xaki ce masa ai baxai maki tilas sai kin ji ba”

A hankali Nihad tace “Toh” Daga haka ta fita daga dakin ta koma dakinta, hada kayanta ta shiga yi a akwatunan ta cike da farin ciki, bayan ta gama ta sauka downstairs tayi breakfast, sae wajen karfe sha daya da rabi ta fita gidan zuwa makaranta ranta fari sol, yau ma dai adaidaita Sahu ta tafi ta hau bata bi ta kan Khalil ba, su Husnah da Naf har sun fi ta murna da ta sanar masu xata dawo hostel ta kuma gaya masu irin plan din da Umma tayi ma Abbanta, Husnah tayi shewa tace “Kai amma Allah ya shi ma wannan Umman albarka,

Allah tana sonki sosai, ta san kan komai…” Nihad tace “Ke dai bari, ba don ita ba i will keep on being miserable in that house ga Yaya Farooq ga Mumy, the house is already a living hell for me, yanxu gobe xan taho da kayana hostel, har na gama hadawa kafin in fito” Husnah tace “Kuma albishirin ki, kin san saurayina ya kama mana tsadadden hostel a off K, xuwa next week xa mu koma wllh…”

Nihad tace “Haba dai” Husnah tace “Wallahi, dama ina ta son xan gaya maki sai in manta, yanxu kinga Da ni, ke, Naf, Zully, da Ummi xa mu xauna dakin, ita Ummi part time xata dinga xama kinsan tafi zama wajen saurayinta sai in baya gari ne take xuwa hostel” Nihad tace “But bamu yi yawa ba Husnah? Kinsan fa bana wani son takura a rayuwata” Naf dake danna wayarta tace “Kin ji ki, 2 bedroom ne fa sannan har da parlor with two toilet, ai baki kai ni rashin son takura ba” Nihad tace “Ohk that’s enough….” Kamar shekaranjiya da jiya yau ma dai haka suka shiririce a Cafeteria babu wanda ya shiga lectures cikinsu, daga karshe ma suka fita xuwa cin pizza a cikin gari, suna wajen cin pizza Nihad tace

“Lah gashi har xan dawo hostel ba ku je gidan mu kun ga wawan yaron can ba” Husnah tace “Ai ko yau ya kamata kawai mu je” Nihad tace “Toh ae ke wannan gashin dake kanki ne matsalar kuma ya Farooq na gari wallahi” Husnah tace “A jakarki ba kina yawo da Hijab din sallah ba” Nihad tace “Eh” Husnah tace “To ara min kawai in sa don baxan iya wani komawa hostel ba” Nihad tace “Ohk” Zully tace “Kawai ku tashi mu tafi yanxu tunda biyu ya wuce” Naf tace “Amma yana gidan idan mun je yanxu?” Nihad tace “Nace maku 24/7 babu inda yake xuwa, da ma talla ya kasa a bakin gate din da ya dinga ciniki” duk suka kwashe da dariya, tashi suka yi gaba daya suka nufi motar Naf Husnah ta shige gaba, Nihad da Zully suka zauna baya, gaba dayansu tsadadden abaya suka saka, Nihad ce kadai ta sa atamfa da gyale. Karfe uku da yan mintuna Naf tayi parking dai dai gate din gidansu Nihad tace “Ashe dai xan iya gane gidan”

Husnah tace “Ka ji ta bayan na gama baki direction kenan” Nihad ta sauka daga motar praying and hoping that khalil na bakin gate, sauran yan matan ma duk suka sauka daga motar, ta shiga gaba suna biye da ita har suka shiga gate din gidan, Aminu ya mike yana masu barka da xuwa, Nihad na kallonsa daga sama har kasa tace “Ina Drivern?” Aminu yace “Ai ko minti biyar bai yi da barin nan ba, yaje can ciki ya watsa ruwa yace min” Nihad tace shit a xuciyarta, why today of all days xai bar bakin gate din, kallon su Husnah tayi sai kuma da turanci tace masu su shiga ciki kawai kafin su fito xai dawo bakin gate din, a haka duk suka bi ta har xuwa main parlor din gidan, Aminu ya bi su da kallo, direct parlon Umma ta tafi da su, Umma ta fito daga dakinta jin sallama tana kallonsu tace “Sannunku da xuwa”

Duk suka gaisheta suka xauna saman kujera, Nihad tace “Umma frnds dina ne da nake yawan baki labarinsu, Zully da Naf, Husnah kuma tana xuwa gidan nan ai kin ganeta ko?” Umma tace “Kwarai kuwa na gane Husnah, sauran ne dai sai yau na san su, Allah sarki, sannunku da zuwa yan mata, ya karatu?” Duk suka amsa da Alhamdulillah, Umma tace “Madallah, kun kwaso rana kuwa” Daga haka tace “Ina zuwa” fita tayi daga parlon, Naf tayi kasa da murya tana kallon Nihad tace “Is she ur step mom that u are talking about” Nihad tace “Yeah she is” Naf tace “Waow she is really nyc wllh, very nyc woman” Nihad tayi Murmushi tace “Sure she is” Ba a dau lkci ba sai ga Hafsah da tray din lemo da ruwa ta ajiye masu bayan ta gaishe su ta fita, sai gata ta dawo da warmer din abinci da plates da spoon,

READ ALSO:  Download Complete A Sanadin Makwabtaka Page 54 Romantic Hausa Novel PDF

ta ajiye ta fita, duk suka sauko suka yi serving kansu, Nihad ma ta dau plate ta debi abincin. Aminu na ganin shigarsu Nihad gida dama ya tafi da sauri ya kai ma Khalil tsegumin Nihad ta xo da kawayenta su biyar suna ta tambayarsa da harshen turanci, ko minti daya bai kara a chalet din ba ya koma bakin gate da sauri ya zauna, sai bayan la’asar su Naf suka shirya xa su bar gidan bayan sun ci sun yi nak, har da coslow Umma ta hada masu, Umma tace “Toh kin kai su sun gaida Maryam kuwa Nihad?” Nihad tace “Tana nan ko?” Umma tace “Aa tana ciki, su je su gaisheta” Ta fita da kawayen nata xuwa ɓangaren Mumy, duk basu xauna ba suka gaida Mumy da bata wani sake masu fuska ba, kai kana ganinsu kaga yara marasu tarbiya marasu kamun kai, Nails Naf tayi fixing a farcenta,

Zully kuwa kana iya hango tatoo dake bayan wuyanta duk da mayafin abaya dake jikinta, Husnah kuma boobs dinta da bayanta ba a cewa komai kuma farko da Mumy ta santa lkcn farawansu makaranta ba haka take ba, yar siririya ce ita ma, amma lkci daya ta dawo uwar mata, Duk gaba daya sun tsargu da kallon da Mumy ke masu, Nihad tace “Za su wuce ne Mumy shine suka shigo su gaisheki” Mumy tace “Toh maa sha Allah, Allah yayi albarka” suka amsa da Ameen suka fita daga parlon, Mumy ta kira Nihad ta dawo, Mumy na kallonta tace “Kar ki kuskura ki wuce bakin gate din gidan nan” A hankali Nihad tace “Toh” Daga haka ta juya ta fita tana turo baki. Downstairs ta tarda su, Zully tace “Ur mother is too serious oo”

Nihad ta kyabe baki ta fita suka bi bayanta, Naf tace “The real African Mothers they are talking about” Duk suka kwashe da dariya, tsaye Nihad tayi balcony ganin har sannan Khalil bai fito ba banda Aminu kawai da take hangowa a bakin gate, Naf tace “Toh ina ɗan iskan drivern ne?” Nihad tayi shiru, sai kuma tace “Ina xuwa, ku jira ni” Gun Aminu ta tafi tana kallonsa tace “Kai Aminu har yanxu bai fito bane, zai ɗan rage ma kawayena biyu hanya ne” Aminu yace “Ni ma kin ga shi nake ta jira a nan Hajiya”

Juyawa tayi ta koma balcony tace “Idan na tafi chalet da few minutes ku biyo ni can din” Tana fadin haka ta dau hanyar chalet din, bata ga takalmin kowa a bakin kofa ba, dama isiya da Saminu gantalallu ne wani lkcn idan suka gama duk abinda suke da safe sai su fita, su da dawowa kuma sai biyar xuwa shidda, a hankali ta bude kofar parlon duk da haka sai da yayi kara, ta shiga da takalminta tana yamutse fuska tana bin ko ina da kallo, ba laifi yau parlon bai yi kaca kaca ba, kuma babu wari, cikin sanda ta nufi corridor din dakuna, ta kai hannu handle din kofar dakin da Khalil yake ta murda a hankali ta tura kofar dakin, mikewa zaune yayi da sauri daga kwancen da yake saman gado, lkci daya ya hade rai kamar yanda ita ma ta hade rai, Tana masa wani kallo tace “Samun waje, kana bakin aikin ne xaka shanya baki da yamman nan kana bacci?”

Khalil ya dau pillow ya daura kan wayarsa dake gefensa sannan ya saukar da kafarsa daga saman gadon, kallon fararen ƙafafuwan nasa take wa enda kamar bai ta6a taka kasa ba har ya mike tsaye calmly yace “Don ina aiki gidanku ba shi ne ya baki daman ki fado min daki kanki tsaye kamar ba musulma ba Hajiya” Wani dariyar rainin hankali tayi tace “Toh ai naga ba da dakin ka zo gidan ba, ko da shi ka zo?? kuma ashe kasan aiki kake gidanmu amma kake min rashin kunya iri iri saboda kai fitsararre ne, banda rainin hankali ma yanxu lokacin shigowa daki a kwanta ne? Shi kansa mai gidan naga yana wajen aiki yanxu haka, to idan ka ga dama ka fito Mumy tana kiranka, sako ne dama aka bani in isar maka kuma na isar, idan kuma baka ga dama ba sai ka shanya bakin ka ci gaba da baccin…

” Jin motsi a parlor ta juya ta ga su Husnah bakin kofar duk sun shigo, alama tayi masu da su karaso, Khalil dake ta lura da ita ya karasa bakin kofar dakin bata ankara ba kawai gani tayi yayi banging kofar dakin almost on her face sannan ya sa makulli ya kulle, buda baki tayi da shock tana kallon kofar su Husnah suka karaso da sauri, tana zaro ido tace “Kun ga abinda yayi min yanxun nan” Naf ta kwankwasa kofar da karfi tace “Ashe dai kai karamin ɗan iska ne mahaukaci tunda har ka kulle kofar, da ka jira mu karaso kaga ikon Allah mana, wallahi da sai mun ji uban da ya tsaya maka yau kafin mu bar nan, kuma wallahi kaji kunya tunda har mata suka tsorata ka ka kulle kofa da sauri” Nan duk suka hau gaggayan bakaken maganganu marasu dadi a bakin kofar dakin, ita dai Nihad mamakin abinda

yayi mata ya sa ta kasa cewa komai sai kallon kofar take, suka kare masa zagi na cin mutunci tass sannan Husnah na huci tace “Mu je, ai akwai wani lokacin, ni ban san shegen matsoraci bane ba ma ai….” Duk Khalil na jin su, and he was calming himself and controlling his mood at the same time, duk da it’s too much and too heavy for him, lokaci daya launin idonsa ya canza, daga karshe ya daina juyo muryarsu gaba daya,

Mikewa yayi walking slowly ya tafi bakin window ya tsaya yana kallon waje ko kiftawa baya yi, tunda ya xo gidan sai ranan ya ji da gaske he truly hate the sight of Nihad, at first he was trying his best not to hate her sbda bai iya tsanar mutum, shi yasa yake kokarin ganin bai tsane mutum ba no matter what, but he now realized he hate everything about her, da ya san xai zo gidan nan har ya hadu da ita da ya hakura da zuwan nasa no matter what and he is going to loose nothing, juyawa yayi ya tafi

READ ALSO:  Download Complete Duk Karfin Izzata By Star Lady Romantic Hausa Novel PDF

jakarsa ya bincika har kasa ya fiddo wani abu me kamar diary da pen dinsa, ya bude plane page yayi rubutu da bai wuce layi uku ba ya ajiye pen din yana kallon takardan, rufewa yayi ya mayar karkashin jakar ya kulle sannan ya mike ya koma gun window din ya tsaya, he is so hurt, it’s been long he felt this way, but they can’t just come and insult him then go scot free, wayarsa dake vibrate saman gado ya karasa kamar bai son tafiyar ya daga pillown ya dau wayar, Nihal ce ke kiransa, ya ajiye wayar ya zauna gefen gado har ya katse, sake kira tayi hakan yasa ya dauka ya daga ya kai kunne cikin low voice yace “Barka da yamma Hajiya” Nihal ta gaishesa tace “Friend dita fatima tace min ka amsar min sakon

nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi” Gently yace “Ameen, ya karatu?” Tace “Alhamdulillah” Yace “Allah ya bada sa’a” Tace “Ameen nagode” Yace “Ki turo number Tailor din naki” Tace “Toh xan tura maka, nagode” Yace “Yauwa sai anjima” Daga haka ya katse wayar ya ajiye gefensa. Da daddare Nihad ta shiga bangaren Umma da sleeping dress dinta, zama tayi a bedroom dinta har ta fito daga bandaki tace “Ya aka yi Nihad?” Nihad tace “Umma dama wancan drivern xaki taya ni yi ma magana gobe da safe xai kai ni can gidan Aunty Kamila da kayana idan ya so daga can sai Naf ta zo da mota ta kwasar min kayan mu tafi hostel” Umma tace “Toh ke me yasa baxa kiyi masa maganar ba, tsoronsa kike ko me?”

Nihad ta wani zaro ido tace “Cabdi, inji tsoron wa? Ko Abbana bana tsoronsa sai wani mere Drivern gidanmu, kawai bana son ko wani magana ya sake hadani da shi har abada a gidan nan, don naga ba shi da manner sannan ya gama rainani, tunda Mumy ta mareni a gabansa shkkn ya daina respecting dina yana ganin dai dai muke, duk Mumy ce ta janyo min komai, to wannan yasa na yi vow har motar ma baxan dinga shiga tare da shi ba, wannan ma kawai dole ne ya sa don babu yanda xa ayi kayana ya dau adaidaita sahu”

Umma tace “Balle ma shiga adaidaita Sahu ba girmanki bane, ita kuma Maryam in taga disgaki gaban ma’aikatan gidan shine dai dai sai ta ci gaba, shi yasa a rayuwa kar ki kuskura ki raga ma talaka ina maki wannan hudubar, don da ya ga fuska shikenan raini sai wanda ya manta, barin yan kauyen nan shi yasa ko kallon arziki kar ki yarda ya hadaku ma” Nihad tace “Ai ni dama bana masu kallon arxiki Umma” Umma tace “Ya dai fi miki, ajin ki daban da nasu, shkkn ki je ki kwanta goben xan masa magana idan Allah ya kai mu” Nihad tace “Nagode Umma” Zata fita dakin Umma tace “Kuna dai waya da Aliyun ko?”

Nihad ta juyo tace “Ehh muna yi, yanxu ma da shi muka gama magana na fito” Umma tace “To madallah, yaushe xai kara zuwa?” Nihad tace “Umma kinsan akwai wani business din Abbansu a can kasar waje shi ne manager so he is not always in Nigeria, though sauran business din Abban nasu na nan kasar ma duk shi ke running dinsu, haka ne ma yasa bayan watanni kadan yake shigowa Nigeria, amma yace min in a month time xai shigo in sha Allah” Umma tayi shiru, Nihad tace “His father owns a big company shi da wani White Man, so Aliyu is managing it for him in there” Umma ta ɗan yi murmushi tace

“Ba shakka, Allah ya sanya Alkhairi, kice koman baban nasa a hannunsa yake” Nihad tace “Ehh, he is his dad favorite also” Umma tayi murmushi tace “Kamar ke kenan ko” dariya kawai Nihad tayi ta nufi kofa Umma ta bi ta da kallo har ta fita daga dakin sai kuma ta sauke ajiyar xuciya. Washegari Umma ta samu Khalil bayan ya dawo daga kai su Amina makaranta, da ladabi ya gaisheta fuskarta kamar bata ta6a dariya ba tace “Kai nan da karfe tara xaka kai Nihad gidan yayarta” Khalil da kansa ke kasa yace “Toh Hajiya” Juyawa tayi ta bar sa wajen a tsaye, ya daga kai ya bi ta da kallo. Kamar yanda Umma tace karfe tara saura Nihad ta fara fitowa daga akwatunan ta nan balcony ta ajiyesu ta tafi bakin gate tana kallon Khalil dake zaune, Ta ɗan tabe baki tace “Ga akwatunan da xa a sa a booth a can balcony”

Ko kallon direction din da take tsaye bai yi ba, sai ma kara hade rai da yayi, tace “Malam magana fa nake maka fa” Still khalil yaki kallon inda take balle ta sa ran yace wani abu, Aminu ya mike da sauri ya tafi balcony din Nihad ta bi sa da kallo, sai kuma ta kalli khalil cike da takaici amma ta kasa ce masa komai, har Aminu ya gama kwaso kayan ya ajiye a garage, ya taho gun khalil yace “Ɗan bude booth din a xuba su” Mikewa Khalil yayi ya tafi gun motar bayan ya bude booth ta makullin ya shiga driver seat, Nihad ta bi sa da wani shegen kallo, tana mamakin irin wannan feeling din da yake, sai kuma ta ji haushin kanta da bata sa Aminu ya kwaso akwatunan ba tayi ma wannan banzan magana ya kyaleta,

bayan ya tada motar ta tuna bata ma Mumy sallama ba, komawa cikin gidan tayi ta tafi bangaren Mumy, khalil ya fi minti sha biyar a kofar gida yana jiranta cikin mota, tana sane tayi xamanta cikin gida don yayi ta jiranta a mota, sai da taga ta 6ata minti ashirin sannan ta mike ta fita tana rike da handbag dinta, back seat ta zauna ta kulle motar tana kallonsa, ya ɗan kwantar da driver seat ya rufe idonsa kamar mai bacci, da har xata masa magana ta tuna sabon vow din da ta dauka na cewar ba maganar da xai sake hadata da shi, yau ne last. Har bayan minti biyar bata ga ya bude ido ba balle ya tada motar su bar wajen, ta wani hade rai tana kallonsa, wasa wasa har sai da aka yi minti goma suna nan a haka, tana ta control din kanta kar tayi masa magana, Aminu dai sai lekosu yake yana dariya kasa kasa, wato sai ya rama shanyasa da tayi cikin mota, tana ta xaune motar ta cika tayi fam amma taki cewa komai kuma bata sauka ba har sai da aka yi minti ashirin da biyar sannan ya bude ido ya gyara zamansa ya kunna motar suka bar wajen, da yake ya ta6a kai Nihal gidan yayarsu kamar yanda ta ce masa, saboda shi ma baya son wata magana ta hadasa da Nihad direct gidan ya nufa ba tare da ya damu can din ne ko ba can ba, the ride was so silent, ko wannensu fuska a tamke, lkci lkci take satan kallonsa sai kuma ta kyabe baki ko ta ja tsaki can kasa kasa, har yayi parking dai dai gate din gidan kamila ya kashe motar, Nihad ta bude ta sauka ta tafi ta kira mai gadin gidan tace

READ ALSO:  Download Complete Idan Ba Ke Chapter 1&2 By NimcyLuv Hausa Novel PDF

FAST DOWNLOAD

“Don Allah ka zo ka sauke min kayana a mota” Ya fito daga gate din ya bude booth don khalil ya riga ya bude, nan ya ciro mata akwatunan ya kai su bakin gate, kafin ya ciro na karshen tana kallonsa tace “Don Allah ka je kace ma wancan drivern nace ba sai ya wani zo yana kai ni makaranta ba don bana bukatarsa kwata kwata” Mai gadin ya tafi yana kallon Khalil bayan sun gaisa yace “Wai Hajiya tace ba sai ka zo kai ta makaranta ba” Khalil yace “Ok” Juyawa yayi ya tafi ya cire akwatin karshe ya kulle booth din, khalil ya ja motar yayi zoom off, Nihad ta bi sa da harara tace “Uwa motar ubansa, wllh ni ce sanadin aikinka a gidan nan mu dai je zuwa, sai kayi da ka sanin sanina a rayuwarka” Shi da mai gadin kallonta yake yana kokarin kai akwatunan cikin gidan, ko karamin bata dauka ba haka ta bar masa su dukka ta wuce ciki, Kamila dake parlor tace “Mutanen Maryam Abatcha American University”

Murmushi Nihad tayi tace “Aunty ina kwana?” kamila tace “Lafiya lau, amma fa ki kira warce xata xo ta dau kayan naki xuwa hostel don karfe sha biyu xan fita nima” Nihad tace “Ehh tace min karfe sha daya xata zo” Kamila tace “Toh ya dai fi, daxu ma Mumy ta kirani wai in sa maki ido nace toh” Nihad tayi dariya tace “Aunty kamila mumy sai tayi ta treating dina kamar wata er yarinya” Kamila tace “Gaskiya kam, ga ki ke ba yarinya ba, makarantar ki ma ba ta yara ba” Dariya kawai Nihad take, Kamila tace “Atoh dai”

Karfe sha daya Naf da Husnah suka iso kofar gidan Kamila na tsaye compound duk suka saka akwatunan a motar Naf, Bayan sun gama tace “Toh Allah ya tsare” Nihad tace “Ameen Aunty” su Naf suka mata sallama, tana kallonsu har suka bar compound din ta juya tayi komawarta ciki, murna a cikin Nihad ba a cewa komai, a haka ta koma rayuwarta a hostel babu me sa ta babu me hanata, duk sanda Mumy ta kirata sai ta shige bandaki ta kulle su yi waya don kar ma taji hayaniyar su Naf da Husnah, night party kuwa sai wanda suka mance ne baxa su ba, duk yanda suka so rinjayar Nihad ta dinga shan kwayoyin da suke sha bata ta6a sha ko da wasa ba, sau daya Husnah ta shammace ta ta xuba mata a lemo shi ma sai da ta kwana ta yini tana baccin wahala, hakan ya sa suka rabu da ita da batun drugs, sai kuma suka fara jan ra’ayinta zuwa kwanan hotels da suke da boyfriend dinsu, nan ma dai ta ki,

ko min daren da suka yi a waje ita dai sai ta dawo hostel, duk sanda suka yi waya da Umma sai ta ja mata kunne kan cewar kar fa ta dinga bin duk wani wuri da xata iya haduwa da Abbanta ko Farooq, ita kanta Nihad is so careful about that, a haka har suka fara exams, duk cikinsu Nihad ce ke maida hankalin karatu, sauran ko bude takarda, duk sanda Mumy ta bukaci Nihad ta zo gida sai tayi karyan karatun exams yayi mata yawa, bayan an gama exams din ma don kar Mumy tace Nihad ta zo gida Umma ta sa kamila ta kirata tace xa su garin mijinta, haka nan aka kare hutu Nihad na hostel abun ta suna baza life, su ne har Kaduna da hutun, sau biyu ta je gidan Kamila shi ma ɗon Aliyu ya shigo kasar ne xa su hadu sai taje gidan kamila shi ma ta ce masa mijinta ne yayi tafiya take taya ta zama……

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

FAST DOWNLOAD

How To Get Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 5

The most reliable and easiest way to obtain the completeMatar Damisa Book 1 Chapter 5 isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Matar Damisa Book 1 Chapter 5 in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the completeMatar Damisa Book 1 Chapter 5booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

 

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.