Download Mundo Mai Hakuri Hausa Novel Complete PDF

MUNƊO MAI HAKURI: Na Zee Yabour Da

Ayusher Muhd

01

RUGAR JIJJI

Hayaniya ke tashi ta ko’ina wanda ta karad’e rugar, mata da yawa ta k’aramin ginin katangar gidajen su suke lek’e, a duk sanda kaga hayaniya irin wannan to tabbas ba lafiya ba, sannan matsalar dai mutum ɗaya ke jawo ta. Yau ma hakan ce ta kasance, gungun maza ne sanye cikin falmaran da akai da yadi, daga yanda suke hargagi kaɗai zaka shaida sun shirya ma fitina haka ransu a matuk’ar b’ace yake,

Kowannen su ɗauke da makami yake wanda ke nuna alamar sun shirya lahanta wanda ya tab’o su. Daga masu fatanya, sai wasu d’auke da gora, wasu da adda. K’ananan mazan dake cikinsu sune masu d’auke da muciya, wani ma murfin tukunya ya kinkima. Shigar su da fuskarsu kaɗai zaka kalla kasan fulani ne (Hmm mutanen mu)

A Mafarkina Hausa Novel Complete

Uku daga ciki ne suka fad’a cikin gidan. Matan dake zaune tsakar gida sukayi saurin fad’awa bukar su, kowaccensu na neman wurin b’oyo dan ganin mazan nan cikin yanayin nan kadai zai tabbatar maka ba lafiya ba.

K’aramin gida mai ginin laka da bulo na kasa suka ja burki suka tsaya, suna zazzare ido suna aikawa junansu sakon yanda zasu farma abin, ba tare da b’ata lokaci ba suka soma kaiwa randunan kasar dake waje bugo ji kake tass, tana fashewa ruwa na zubowa, suka sake nade hannu suka fara sarar sandunan dake jikin ginin wanda ake shanye ko kuma a d’aure tunkiya in anada bukata, yi suke tamkar zasu ruguza ginin, gidan kewaye yake da bukkoki wanda yawancinsu iri daya ne, sak ginin ainihin fulanin ruga.

 

Gaban bukka d’aya suka nufa, Cikin hargagi suke kiran sunan “MUNƊO!!”

 

Cikin karaji da ihu suke ta ke kiran sunan kai kace zasu fito da makogaransu.

Yarinya ce yar’ kimanin shekaru 13 a duniya tana kwance, tayi firgigit ta tashi daga nauyayyen baccin da take wanda ya ɗauketa ba tare da ta shirya ba, tsabar gajiya, daga can cikin bacci taji kiran da farko ta d’auka mafarki ne sai dai yanda taji ana kiran ya sa ta zabura.

“MUNƊO!” Suka k’ara kira cikin d’aga sauti da murya. A rikice ta diro daga saman gadon k’arfen dake d’akin ta shige k’ark’ashi gadan jikinta na kyarma da tsuma. Sanyin kasa na sake ratsa jikinta kasancewar yanayi ne na hunturu, k’aramar riga mai kama da vest dake jikinta ya k’ara sa sanyi shiga jikin ta, duk da ba kasafai fulani suka fiya jin sanyi ba, amma yau har cikin jikinta takejin sanyin.

Wuri d’aya ta k’udundune, tasa hannu biyu ta toshe kunnuwanta tare da runtse idanunta. Ba yau ce rana ta farko ba da take gamowa da irin haka ba, sai dai na yau ya sha bambam da sauran ranaku, Bata tab’a jin hayaniya irin wannan ba. Sunan ta da suka k’ara kira cikin karaji, shine yasa hawaye soma zirya kan kumatun ta “Baffa kazo na maka gani na k’arshe na tabbata yau ba zasu barni ba.” Abinda take fad’a cikin kuka kenan, har lokacin idonta a runtse, tana cikin tsoro da firgici.

 

“Aradun Allah Munɗo in kika bari na shigo baki bude ba sara ɗaya zan miki na aika ki lahira, tsinanniya, haihuwar Allah wadarai, gara mu kashe ki kowa ya huta.” Wani daga cikin su ya fad’a. Can k’arshe gadon ta sake shigewa ta manne da bango jikinta na kyarma kai kace cikin kankara aka sakata.

Wata dattijuwa ce ta taho a guje ta karaso tana hade hannayenta “Laddo na rok’e ka da girman Allah kuyi hakuri, ku tsaya ai magana, yarinyar nan wallahi ba yadda kuke tunani take ba.” Tai maganar tana zubewa gaban wanda ta kira da Laddo. A fusace yayo kanta rike da fatanyarsa kamar zai sareta yace “Wallahi Danejo in kika sake magana zan mik’a ki barzaho daga ke har jikar taki, abu ɗaya zan muku shine ki ce bak’ar kadarar can tazo ta tsallaka yarinyata da aka haifa, dan wallahi in har ta mutu kuma kunyi bankwana da duniya.”

 

Danejo tamkar zata mishi sujada tace “Laddo yarinyar nan wallahi bata je bukar ku ba yau kwana arba’in kenan da kuka hana ta fita tunda matarka ta haihu…..”

 

Wani daga cikinsu yayo kanta d’auke da adda tuni ta zame ta fad’i k’asa tare da runtse ido ya kalleta yace “Rufe muna baki munafukar Allah, Kowa yasan jikar ki mayya ce, mutane nawa tana lashewa a rugar nan, maitar ta ai ba sai taje guri ba take kama mutum ko kin manta wata uku kenan da ta kama yarona, wallahi yau sai mun zubar da jininta.”

 

Suna kaiwa nan suka hankade Danejo suka sake nufar bukar suka fara sara fatanya. Ai tana ganin haka ta sake kudundunewa tana sake sa kuka tare da kiran sunan Baffa…

A fusace Laddo yace “Aradun Allah kika bari na fasa ginin nan baki fito ba sara d’aya zan miki na mikaki barzaho.” Samari da yaran dake gun sai dadi sukeji ai gwara a zubda jinin ta ma kowa ya huta.

READ ALSO:  Download Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 114 Hausa Novel PDF

Sake shigewa kasan gadan tai ta cusa kanta cikin cinyoyinta ta sake toshe kunnanta tana hawaye.

 

Da gudu wani magidanci wanda bai gaza shekara arba’in ba ya shigo yana haki ya had’a gumi tamkar ba lokacin sanyi ba, d’akin ya nufa kai tsaye wasu daga cikin mazan suka finciko shi da k’arfi sukai baya dashi, idanunshi yayi ja yana girgiza kai da alama ba k’aramin gudu yayi ba, cikin tashin hankali yace “Dan girman Allah Laddo kuyi hak’uri, wannan ba shine mafita ba asibiti ya kamata muje .”

 

“Yi mun shiru makiri ai duk kaine sila, bakin ku d’aya, kai ka kawo mana fitina cikin ruga, ka fito da tsinanniyar ƴarka muje ta tsallake min yarinyata, dan wallahi in y’ata ta mutu kaima sai ka rasa taka.”

 

Maccido gwiyoyinsa ya kai k’asa ya kama k’afafun Laddo yana rokar shi sai dai fir yaki yace a fito da Munɗo, dole Macciɗo ya nufi ɗakin cikin tsananin tashin hankali. ” Zuciyarsa yake ji kamar zata fashe shikam sai yaushe Mundo zata fita daga mummunan zargi na mutanen rugar nan, sai yaushe zata samu ‘yanci tayi rayuwa kamar sauran mutane, tun tana jaririya ko dabba ce ta rasu sai ace itace, ko ciwon kai mutum yake sai ace itace, kome ya samu wani a rugar itace, saboda wani dalili nasu wanda yafi alak’anta hakan da son zuciya irin na d’an adam.

 

A hankali ya nufi kofar da suka kusa balleta takaici ya sake kamashi, ya tura kofar yana sake danne zuciyarsa. Cikin sanyin jiki ya kutso kai k’aramar bukkar tasu, D’akin yabi da kallo bai ga alamar ta a ciki ba, Cikin raunannen murya yace “Munɗo kina ina?”

“Baffa” Ta fad’a da dasashhiyar murya mai kamar rad’a wacce ke nuna tasha kuka. Cikin rawar jiki ta fito k’ark’ashin gadon ta k’ank’ame shi. Bayanta ya shafa a hankali yana jin hawaye na tausayinta na taho mishi yayi k’ok’arin mayar dasu.

 

 

Ɗagota yayi a hankali yana kallon yadda har lokacin hawaye basu fasa zirya kan kumatun ta ba. A hankali ya share mata hawayen, Ya kama hannun ta zuwa waje, yana rike da ita tana tana sake raɓewa ta jikinsa. Tana ganinsu ta fara ja da baya, tana k’ok’arin b’oyewa bayan Maccido.

Suna ganinsu suka hau zage-zage shidai kawai rike yake da ita baice komai ba. Laddo yai kwafa ya nunata da yatsa yace “Shegiya bakar mujiya, wuce muje ki tsallaka mun ‘ya ta”Cewar Laddo cikin d’aga murya, Munɗo jikinta kawai ke kyarma, haka suka taso su gaba, Haka suka cigaba da tafiya suna hargagi da zage-zage.

 

Laddo takaici ya kamashi yanda yaga tana tafiya sumi-sumi, yace “Munafuka kamar mutuniyar kirki, dole kiji tsoro dan wannan karon kin tab’o abunda zai yi ajalin ki idan kina cin mutane ki kwana lafiya d’iyar Laddo ta wuce maitar ki, bakar kadara.” Har suka iso bukkar Laddo yana faman mita da hargagi, Kuka da ihun da suka fara jiyowa yasa Laddo sakin fatanyar sa ya k’arasa ciki da gudu. Kallon mutanen yai a birkice yace “Kukan me kuke?”

 

“Ta cinye ta Laddo” Cewar d’aya daga cikin matan tana kururuwa, Wata kururuwa Laddo yayi yace “Ta me?”

Tsohuwar da ta sanar dashi ta fashe da kuka ta zube a kasa.

“Aradun Allah yau sai na kashe Munɗo.” Ya zaburi fatanyarsa yai waje a guje…..

 

Macciɗo ya fakaici idon mutane da hankalinsu yayi kan abinda ke faruwa yaja hannun Munɗo suka dinga gudu sai da sukaje can bayan gari, Suka tsaya k’ark’ashin wata bishiya har lokacin jikinta bai saki ba tana cikin tsoro da firgici sai ajiyar zuciya da take faman saukewa. Hawaye yaji ya zubo ta matse-matsin idanunsa, wani irin bala’i ne wannan? Yarinya an hanata tayi rayuwar data dace? Tunda ta taso bata mu’amala da kowa,

hatta k’awa bata da ita a rugar, babu mai barin ɗan shi yazo kusa da ita, yara idan sun ganta guduwa suke dan iyayen su sun musu hud’ubar mayya ce zata cinye su, tun tana k’arama sai dai tayi wasan ta ita kaɗai, yanzu har fita ma an hanata, kullum tana ɗaki. Zancen saurayi kuwa babu shi duk da kyawun da Allah ya bata, ga uwa uba diri tun yanzu mazaunanta sun fara bayyana, ga k’irjinta da ya soma cika kamar ba ƴar shekara sha uku ba, sai dai duk da haka ta zama tamkar mujiya a cikin rugar babu mai sha’awarta balle wani ya furta mata kalmar so, Ko a cikin bukkar su daga mahaifinta sai kakarta Danejo take jin sanyi wurin su.

 

 

Kallonta yayi cike da tausayawa yana bin jelar gashinta da kallo wacce ta sauka har saman kafad’a, wanda kitson ne a kanta manya da Danejo ta samu ta mata, shima ranar k’in cin girkinta akayi saboda ta tab’a kan Munɗo a cewarsu sunaci mutuwa zasuyi.

 

A hankali ta ɗago idanunta cikin kuka tace “Baffa Dan Allah ka nisanta ni da rugar nan, ka kaini can wani garin na zauna ni ko ni kadaice aradun Allah zanyi zamana, na gaji da nan, ba mai sona anan, na zama abun gudu da k’i. Har dabobin rugar nan sun fini daraja da nutsuwa. Dan Allah ka kaini inda zan samu sassauci inda zan san nima mutum ce kamar kowa. Wani sa’in har tunani nakeyi ko ni din ba mutum bace……”

READ ALSO:  Download Complete Matar Hariji Page 1-10 Romantic Hausa Novel PDF

Kuka ne ya kwace mata wanda yasa ta kasa ci gaba da kalamanta.

#Team Munɗo

#Mai Hakuri

#One Love 💕

 

*TEAM ƳAN TAGWAYE NOVEL*✍️

Ayusher Muhd

Page 2

Zuciyarsa ce ta karaya cikin rauni ya kalleta yace “Kiyi hak’uri Munɗo In Shaa Allah watarana komai zaizo karshe.”

Hawaye suka sake zubowa tace “Baffa sai yaushe? .”

Tausayinta ya sake kamashi ya rasa me zai ce mata. Shiru tayi itama bata ce komai ba, ita dai zata so ya nisanta ta da k’auyen nan.

Ganin duhu ya fara kawo kai yasa yace “Munɗo tashi muje gida?” Kai ta gyad’a masa ta mik’e dan batasan yimai musu.

Tunda aka hango su kan hanya, wasu da gudu suka sanar da Laddo, cikin k’ank’anin lokaci suka biyo hanya wasu da itace wasu ashana suna fad’in “Yau sai sun k’ona tsinanniya kowa ya huta.”

 

Maccido tsayawa yayi a hanyar shiga gari bayan ya aiki wani yaro ya kira Mahaifinsu.

 

 

Munɗo ihu da karajin su da ta jiyo ne ya sake firgita ta, ta kama Maccido ta rik’e, “Ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai faru.” Ya fad’a yana k’ok’arin kwantar mata da hankali, sake kankameshi tayi jikin ta na kyarma.

 

Su Laddo tuni suka had’a itacen, cikin hargagi yace “Wallahi Maccido karka bari na irga biyar baka ajiye yarinyar nan ba, gashi can Sahi tace in har ban ɗau mataki ba yarinyata da aka kashe ba, sai ta tafi gidan su, da rashin jaririyata zanji ko matata? wannan annobar ai gwara mu kasheta kowa ya huta.”

 

Wani ya matso yasa takardu ya kunna ashana, tuni wuta ta kama balbal gashi dama lokacin hunturu da wuta ke saurin ci, Maccido shi kansa tsoro ya fara shigar sa, na fargabar ganin suna neman kashe masa ‘ya tamkar zasu kashe wata kaza.

 

Laddo cikin zafin nama ya nufo su yana neman fincikar Munɗo, cikin tsawa dashi kanshi bai san ya iya ba saboda tsabar hakurin sa yace “Wallahi Laddo in baka matsa daga gun yarinyar nan ba zakaga yanda ake k’unar bak’in wake, na gaji da takurar da kuke ma munɗo, shin da wane dalili ma zaku d’aura mata maita, aradun Allah yau ni da ku ne?”

 

Laddo cikin zafin rai yace “Wallahi sai na zubar da jinin ‘yar ka tunda na rasa tawa, kasha k’arya ta cinye mun yarinya ta zauna lafiya.” Ya karasa maganar yana neman kara kai hannu gun Munɗo, banda kuka itakam ba abinda take.

 

 

 

Gyaran muryar da suka jiyo ne yasa kowa juyawa, mahaifinsu ne wanda kowa ke shakka, Ardo suke ce mishi, shine Babba a rugar, duk yaran yayye da kanne ne a rugar ma’ana jini d’aya, anan suka girma suka haifi nasu yaran, har sukai yawa haka. Kakansu ya rasu shekara biyar da ta wuce shine aka nad’a mahaifinsu Maccido a matsayin Ardo wato shugaba.

 

Cikin girmamawa kowa ya gaisheshi, ya kalli saurayin dake hada wuta yace “Kashe ku biyoni dukanku.”

Suka d’unguna suka bi bayanshi suna kunkuni akan koma menene sai sun zubar da jinin Aljanar mayu.

 

 

Gaban bukkar sa suka isa inda yake zama nan kowa ya sauke gwiwowinsa a kasa, Munɗo na gefe Maccido ta takure wuri d’aya haryanzu jikinta kyarma yake.

 

 

Gyaran murya yai yace “Laddo na dauka na sanar da kai yarinyar ka bata yi kalar kamun mayu ba?”

 

“Wallahi Ardo yarinyata mayyar can ta kama ta?”

Maccido cikin zafin rai yace “Akan me zaka dage itace?”

Laddo ya mike yana neman yin dambe, gyaran murya Ardo yai hakan yasa ya koma ya zauna cikin ladabi.

Maccido ya kalleshi yace “Ardo na gaji da abinda ke faruwa, shi yasa na nemi ka shiga maganar nan, tunda kowa ya gaji da zaman mu a rigar nan, zan d’auki yarinyata mu bar garin nan.”

 

Nan danan guri yai tsit, sukai tsuru-tsuru kowa na kallan dan uwansa, shi kanshi Ardo sai da idanunsa suka firfito waje, dan duk abinda zai faru bazasu tab’a gangancin barin Munɗo da Maccido subar garin nan ba.

 

Maccido ya cigaba “Ardo ina neman izininka zan koma birni gun Gidado shi kad’ai garini na tabbatar zai zauna damu.”

 

Ai cikin sauri Ardo yace “Babu inda za ka je, ko so kake ka nuna mana iyakarmu? To ahir dinka, aradun Allah in na sake jin kalamai irin wannan ranka sai ya b’aci.”

 

Kasa yai da kansa dan shikam baiga amfanin zaman ta a garin ba dan haka dauketa zaiyi ya gaji da rayuwa cikin fargaba.

 

Ardo cikin ɓacin rai ya kalli su Laddo yace “Kai kuma kada na sake jin maganarnan ta wuce yarinya dai ta mutu sai a kaita a birni Allah zai baku wata.”

READ ALSO:  Download Complete ƘANWAR MAZA Romantic Hausa Novel PDF

Laddo ji yake kamar zuciyarsa zata fashe sai dai ba yanda zaiyi, da barinsu Munɗo da Maccido gwara yai hakuri.

 

Ardo yana kaiwa nan ya mike a fusace yai ciki, Maccido ya kalli su Laddo kafin ya kama hannunta su kabar gun zuwa tasu bokar.

 

Suna shiga ta share hawayemta tace “Baffa baza’a barmu ba.”

Yai kalleta tare da murmushi. Zama yai a gefen gado ta zauna a kasa zaiyi magana cikinta yai karar yunwa ji kake kululu…. Dariya yai itama dariyar tai kafin yace “Munɗo kinci abincin rana?”

 

Ta girgiza kai alamar a’a tace “Yau ba Danejo bace da girki.”

 

Zuciyarsa ta sake kuna wai in ba mamansa bace da girki bamai bata abinci sai dai shi a nashi ya deba mata ko suci tare? Yarinyar da ake amsawa tai surfe ta bakace ta maida gari amma in an girka bamai bata.

Mikewa yai zai fita da sauri ta mike tace “Baffa fita zakai?”

 

Yake yai yace “Yanzu zan dawo, abincina zan amso, kinji?”

 

A hankali ta daga kai sannan tace “To!”

 

Kallan ta yai bayasan a sake hantararta ne shiyasa bayasan zuwa da ita can.

 

Bangaren matarshi ya nufa wacce take yarinyar kanwar mahaifinsa da aka aura mishi ita.

 

Tana zaune tanacin tuwon dawa miyar kubewa ɗanya yasha manshanu, macece da batafi shekara ashirin ba, gefe kuma radio ne takeji ga madarar shanunta a kwarya, daurin kirji ne a jikinta, tayi kitso irin manyan nan, daga damanta kuma ɗanta ne dan shekara uku yana zaune yanacin nashi tuwon shima, gefe kuma wuta ce da suka hada saboda sanyin gari.

 

Tsayawa yai daga ɗan nesa dasu kaɗan yana kallan ikon Allah zuciyarsa na sake kuna. Yanzu duk abin nan dake faruwa ko lekawa batai ba balle ma ta taimaki yarinyar sa? Tunowa yai da yanda tace bazata bari ta zauna da yarinyar nan a bukar ta ba dole sai inda suke tara abinci aka kwashe yasa gado yarinyar ke kwana a can da tana karama, bayan takai shekara tara ya barta take kwana ita kadai.

 

Gyaran murya yai ta waigo ta kalleshi kafin ta mike cikin girmawa da kunya tana mai sannu da zuwa, Giɗaɗo wato ɗanshj ya kalla wanda ya taso da gudu ya faɗo kanshi.

 

Hannunsa ya rike kafin ya ɗaga shi sama yace “Malam Giɗaɗo b’ata ni ake sanyi ne da miya?”

 

Dariya yaran ya shiga yi ganin yanda Baban kemai wasa, a hankali ya saukeshi sannan ya kalleta yace “Kinba Munɗo abinci?”

 

Nan danan yanayinta ya canza tace “Nima nawa aka aikomin da naka, bansan komai akai ba.”

 

Yawun bakinsa ya hadiya yace”Yanzu shikenan ke sai kisa ɗanki a gaba ita ko taci ko kar taci babu abinda ya dameki? Ace babu mai tausayin bata abinci kaf rugar nan? In ɗanki ne akewa……”

Katseshi tai da cewa”Macciɗo kar ka sake haɗa min ɗana da mayyar ƴar ka, banasan cin mutunci, sannan tun kafin ai aure na faɗa maka bazan kula da ita ba dan haka yanzu kar kuzo min da abinda bazan iya ba.”

 

Ta sungumi ɗanta da kwanan abincinta ta shiga ciki, saman kansa ya rike kawai ya ɗau langar abincinsa ya fita.

 

Ɗakin da take ya nufa tana jin motsinsa ta ruga a guje ta kankameshi, saman kanta ya shafa yace “Muje muci abinci, yau kinsan me aka dafa?”

 

Kai ta girgiza tana kallan kwanan kafin tace “Me aka dafa Baaba?”

 

Ya kalleta yana karasawa ciki yace “Canka zakiyi in ba haka ba yau ba hirar dare.”

 

Dariya tasa tace “Baffa nifa na sirfa dawar nasan tuwon dawa ne miyar ce dai bansan wace akai ba.”

 

Yace”Tunda kin faɗi zo na baki hukunci.”

 

Dariya tasa ya mika mata kwanan, amsa tai ta jawo roba a kasan gado ta gutsiri kadan ta tura ragowar gabanshi.

Fuska ya tsuke yana kallanta, sake karawa tai kadan tana neman turawa gabanshi ya amsa ya zuba mata sama da rabi sannan ya tura gabanta, kamar zatai magana ta fasa dan batasan bacin ran Baffa.

 

Kan kace me sun cinye abinci yo dama abincin mutum daya ina zai isa mutum biyu.

Kallanta kawai yake cike da tausayi, yarinya ko wasa da kawaye batasan yanda ake ba, kowa ya tsangwameta duk inda taje sai kya ra.

Gyatsa yaji mai y’ar kara wacce ta dawo dashi daga tunaninsa, kallanta yai kawai suka sa dariya, ya kalli kwanan wanda ta lasheshi tas kai kace wanke wa akai.

 

Dariya ya sakeyi itama tai dariya……..

 

 

Zee Yabour

Da Ayusher Muhd

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.