Download MATAR GWAMNA Hausa Novel Complete PDF

MATAR GWAMNA is a popular Hausa novel that tells the story of a young woman named Matar who falls in love with a man named Gwamna. However, their love is threatened by various obstacles, including family conflicts and societal expectations. In this blog post, we will provide information on how to download the complete PDF version of MATAR GWAMNA Hausa Novel.

 

Bismillahir Rahamanir Raheem*

Page

…..yana rungume da Teemah ya fito ya saita bindigarsa sai yaga su innah talatu duk sun fito su maheeda suna karkarwa kursiya sai. kuka take hanuwa akai fuskarta tayi shabe shabe da majina gunsu ya kawo teemah ya direta “Noor kushiga ciki har muga abinda Allah yayi kuka ta saka masa ta rikeshi”Wlh Haidar saide muje tare akashemu Allah bazan barkaba kallonsu innah yayi”mama kushiga d’aki ku zauna inada yakinin babu abinda zai samu kowa, da gudu suka koma ciki duk da, yana halin damuwa saida yaji dariya tazo masa ya kama hannun teemah suka sabko k’asa kofar da take had’e mai kaika har babban parlon Bintu ya bude yana rike
da hannunta suka shigo ya maida ya rufe har suka shigo tsakiyar parlon baiga Bintu ba yasan mugun baccinta ba lalai bane taji Harbin bedroom d’inta ya nufa ya murda aiku ta baje tana kirtar bacci kai ya girgiza ya kalli teemah Noor zauna nan bari na na dubo yaranki bakin gadon ya zaunar da ita ta kwakwab’e fuska tana binsa da kallo”My Haidar please kar fita amaka wani Abu bai saurareta ba ya fice ya nufi d’akin yaransa suna tsaitsaye jikinsu sai tsuma yake suna kuka da sauri ya isa gunsu ya kamosu ya rungume ya janyosu suka foto d’akinsu Rauda ya shiga muneerat ta tashi sai kuka take tsoro ya hanata fita Raudat ko bacci takeyi daukar muneerat yayi cak”Munnee yi shiru kalli
kanwarki na bacci karki tasheta kinsan rigima zatayi muje gun momynku babu abinda zai samu ko karan gidanan fitowa sukayi yana rike da yaransa ya kaisu d’akin Bintu suna shigowa daide lokacin akayi harbi na hudu Wanda shine sukayi nasara Harbin mutanan kuma shine ya tashi Bintu daga bacci saida ta wuntsulo daga saman gado agigice tana cewa”wayyo Allah nashiga uku sun kashemun my Man Dina da yarana Teemah
ko Ana Harbin ta Mike da gudu ta fada jikin Aliyun ta rungumeshi ya hada da yaransa ya rungumesu Bintu Sam idanunta sun rufe amugun tsorace take bata gansuba ta Mike tana kuka jikinta na kerrrma tana kiran my man Aliyu ganin Bintu bata haiyacinta ya janye Teemah jikinsa da yaran ya zaunar dasu kenan yaga Binta tayi kofar aguje tana kiransa da Raudat da Sauri ya bita ya sha gabanta ya kamota ya rungume” my Bintuna ki nutsu gamu yaranki suna lafiya dani babu abinda ya samemu rungumeshi tayi tana kuka”my man naji tsorone karsu tabamun kai Alhmdllh Kara matseta yayi yana buga bayanta “to kibar kukan my bintu zo ki zauna kalli yaranki suna kallonmu
da kanwarki Teemah da tacika tayi fam yada Aliyun yake rungume da Bintu yana lallabata kamar wata jaririya hawayen da suka soma zubo mata ta goge ta kauda kanta Aliyu ko saida Bintu ta dawo haiyacinta ya saketa ya kamo hannunta suka zo bakin gadon sai lokacin ta kalli Teemah wacce ko kallonsu batayi ba Bintu tayi kicin kicin da fuska tana ma teemah mugun kallo afakaice Aliyu ya zaunar da ita kusan Teemah “yauwa ku zauna bari na fita naga wani me kokarin ne ya kawoma Familyn
Abdallah Muhammad Damba hari Muneerat ya dauko ya rungumama Bintun dan har yanzu atsorace take ya nufi hanyar fita cikin kissa da kisi sina cikin sanyin murya Teemah tace”My chocolatyna Allah ya tsareka mijin Fatima Da Fatima Abban Fatima juyowa yayi ya kalleta yaji wani mugun dadi gira ta d’aga masa yace”Ameen my zahara ya juya ya fice daga bedroom d’in Bintu baki ta Saki tana kallon Teemah cike da mamaki ranta amugun b’ace Teemah ta kalli Bintu suka hada idanu Bintu na
hararata murmushi Teemah ta sakar mata”Aunty Bintu sannu Ashe tsorata kikayi bari na dauko Zaharata naji guminta ta Mike ta dauko zahara na bacci ta rungumeta ta kalli Asif “yarona kuzo kusan momynku kunji kubar damuwa Allah na tare damu kusanta suka dawo duk ta hadasu ta rungume Bintu abun ya girmame mata tarasa meke mata dadi da idanu kawai take bin Teemah da kallo tana tunanin anya ba karuwa bace my man dinta ya auro duba da yar rigar da take jikinta ta bacci Teemah kuwa itama haushin bintu takeji yada taga Aliyu ya wani makaleta dannewa kawai tayi Dan taba Bintu haushi Bintu ko
iya tashin hankali ta shiga yada taga Halitar teemah ace itace kishiyarta taji ta Kara tsanar Teemah mik’ewa tayi rungume da muneerat kamar wata yar yarinya ta kalli yaran “mucoter ku tashi muje ku kwanta basuyi musuba suka Mike daga jikin teemah ta tusasu gaba suka fito Dan so take tama teemah tijara tamata shegen duka bedroom d’insu Asif suka nufa bangaran Aliyu kuwa yana fita ya shiga bedroom d’insa ya sako jallabiya
ya fito harabar gidan ya isko wasu manya manyan kartine guda biyu duk an harbesu akafarsu da hannuwa Ana dauresu ya iso gurin jini sai kwarara yake daga jikinsu amma suma sun harbi Soja guda ahannu abinda ya fusata boos kenan Dan shine yayi nasara harbinsu kai tsaye Dan mutanan suna da hadari sosai wlh badan boos shegen mutum bane yasan kan iya saiti Dan idan yayi harbi baya kaucewa to fah tabbas makiyan gwamna da sunyi nasara akansa yana isowa gurin
Jami’an tsaro suka kewayesa
Boos yace” Oga koma ciki kayi kwanciyarka da yarda mai sama babu abinda zai sameka daga kai har iyalinka murmushin gefen baki Gwamna yayi ya kalli mutanan yada suka harbu an dadauresu ya kalli boos”da sauran sojojin yace” ina fatan ko karan gidana basuyi nasara akansaba? Boos yace”Oga sun harbi khalifa ahannu an tafi hospital dashi” Allah ya bashi lafiya Boos banason ayi bincike akansu ku kwashesu ku kaisu bakin titi ku zubar dasu kuma karku kuskura ku baza labarin wlh su da kansune zasu baza kansu insha Allah asirinsu zai Tonu kubarsu da jinyar suma ni Allah na kama mutum bai isa yaga baya naba Boos yace” amma Oga taya zamu bar Wanda sukazo da niyar ganin bayanka yanzu haka nakusa da kaine?
” Boos kuyi abunda nace daga can ku dubomun lafiyar khalifa ya fada yana zagaya gidan sojoji na biye dashi har bakin get saida Aliyu yaje tukun ya juyo wasu manyan karnukane suke shawagi Aliyu ya nufi gun wani jibgegen kare sai zaro harshe yake yazo gaban Aliyu ya tsaya murmushi Aliyu yayi” Dife ya ka tsorata ganin bakin dare karan sai sunsuna Aliyu yakeyi kansa Aliyun ya shafa ya juya ya nufi cikin lokacin da
Aliyu ya shigo parlo Bintu ta fito daga d’akin yaranta ta Teresa” my man su waye” rikota yayi” makiyane kawai amma ta Allah ba tasuba ina yarana” duk sun kwanta hannunta ya kama suka koma dakin yaran yaga duk sun kwanta dukansu saida ya sake musu Addu’a suka fito bedroom dinta suka shiga teemah na zaune da zahara ta kallesu suna shigowa Bintu ta wani ririkeshi Dan taba teemah haushi zahara ta kwantar ta Mike da sassarfa tayi kan Aliyun ta fashe da kukan kissa ta fada kirjinshi ta rungumeshi tana tatabashi”wayyo my chocolatyna sunnu ba abunda ya sameka ko
ta fadi tana shashekar kuka tana Kara shiga jikinsa duk ta rudashi yanayin yada take magana daukarta yayi cak “my Noor yi shiru babu abinda ya sameni bari kuka kinji yar babyna fuskarsa ta kamo tana shashekar kuka tace“my chocolatyna ya zan bar kuka kasan halin da nashiga kuwa wannan yan mintinan da na dauka ban gangaba muje kasani bacci my gwamnana ta fada tana lasar lips d’insa tana shafar fuskarsa duk ta susutashi cikin shagwaba yace my yar babyna kibari kukan sangarta ta saka masa ta makalkaleshi”Allah my chocolatyna bazan bariba Bintu da tacika ta batse ranta yayi mugun baci ko ganin kirki batayi tace”
kutumar ubancan kai Aliyu ba yar baby ba dai yar buro uba take narantse muku da girman Allah duk sai namuku buro uba da Baku taba sanin Ana irintaba aduniya ta fada tana nufar kan dressing mirror ta warto kwalaban turare har biyu ta fasa gudar turaren ya zube kansu ta nufo gadan gadan Teemah ta juyo ta kalleta tace “lah Aunty kiyi hakuri ni wlh na manta inda Muke har naji kunya my haidar saukeni karta fashemun kanka gwara ni naje ta fasamun nawa kan ta fadi tana kokowar Aliyu ya sabketa sabkota yayi yanabin Bintu da kallo Dan yaga da gaske take kai zata fashe musu dagashi har teemah da Sauri ya riko teemah da take kokarin zuwa gun bintu bedroom din guda yasaka teemah ya rufo kofar itama sai ihu take ta buga kofar Bintu na
kokarin buga masa kwallabar ya damko ta” wai meye zai sameki my bintu waye ya koya miki zagi da dabanci kokowa suka fara ya murdeta ya amshe kwallabar sai kuka take tana gaya masa magana cak ya dauketa ya nufi saman gado ya kwantar da ita ya haya Samanta babu shawara ya fara murzata da kissing dinta ihu take tana yagonsa bai denaba saida yaga tayi lakwas tana maida numfashi tana lumshe idanu tana hamma jikinsa ya shigar da ita yana mata tausa sai bacci ta makaleshi kansa ya dafe ya janyeta ya lulubeta ya matso da zahara kusanta ya safko daga saman gadon
“ko waye ya koya mata irin wannan zagin Sam ba halinta bane ya fada yana bude teemah wacce fadin bacin ranta bata lokacine amma ta danne daukarta yayi cak ya rungumeta suka fito ya bude kofar ya fito ya rufema bintu kofarta teemah ta shafi fuskarsa” my haidar Aunty tayi baccine? ta fada tana danne kukanta kiss ya sakar mata” eh tayi bacci kofar mai zuwa part din teemah ya bude ya shige ya janyo ya murza key kanta ta Dora kirjinshi tayi shiru matatakalar bene ya fara hawa ya haye saman bene adaide kofar dakinta tace” my chocolaty bari naga maheeda ko sunyi bacci sabkota yayi” babyna kiyi Sauri da gudu ta isa kofar ta bude ta juyo tana shashekar kuka tace” wlh na haramtawa kaina ganinka har tsawon sati guda Dama kasan baka sona ka auroni cikin hamzari ya nufota ta banko kofar da karfi ta murza key baki ya ciza a fili ya furta” zaku gane bakuda wayo naki wasane daga ke har bintun zanyi maganunku wlh sai kun jigata zan waiwayeku kishi ai ba hauka bane Dan kunga ina riritakune ya fada yana shiga bedroom d’insa toilet ya shiga ya dauro Alwalla ya fito ya hau kan darduma ya
fara sallah saida ya kwashe awa biyu cur Addu’a yai Allah ya shiga tsakaninsa da makiyansa duk inda suke Allah ya ragewa matansa kishi ya hada masa kansu ya Mike ya cire jallabiyar ya kashe wutar dakin ya haura saman gado yayi kwanciyarsa yana karanto Addu’a bacci teemah na zuwa gado ta haye su maheeda suna kwance tsoro ya hanasu bacci jin zauwar teemah suke tambayarta amma tayi banza dasu maheeda baki ta tab’e Dan tasan iskacin tane ya motsa saida ta gaji da kukanta taja bargo ta rufa sai juyi takeyi tanajin bazata iya ko kwana biyu ba bataga haidar ba ahaka har bacci ya dauketa Asubah ta gari
**********************************
*Bayan kwana hudu*
Yau teemah kwanata hudu gidan Aliyunta horo yake basu mai tsanani daga ita har bintu Dan babu wacce ya sake nema acikinsu bakinsa yaje yaga yaransa amma kallon arziki bintu bata samu agunsa hankalinta duk ya tashi amma saboda tsabar kishi da haushinsa da takeji ta danne bangaran teemah hakane kullum zaizo ya gaishe da bakinta amma baya ko kallonta teemah tun bata damuba har ta damu ganin har tsawon kwana hudu gashi tana bukatar mijinta kullum malika sai tazo tana Kara sa yar uwarta hanya kuma kullum sai ta kaita part din bintu ta gaisheta duk bata sakar musu fuska ajiyane da su innah talatu zadu tafi teemah taci kuka kamar tayi hauka Dan sunce dama bakin kwana uku zasuyi suka Kara kaita gun bintu suka musu nasiya bintum ta sauraresu amma aranta Sam bata kaunar Teemah Aliyu yayi musu shatara ta arziki wlh abun baacewa komai malika mata tayi musu abun kirki to fah gun shiga motane teemah ta rike Kursiya suna kuka saida Aliyun yazo ya dauketa cak ya kaita part dinta yana zuwa ya ajiyeta ta fara kiransa “my haidar nayi missing dinka zo ka lallasheni tausayi ta bashi mutika shi kansa dauriya yakeyi da rashinta yanaso ya gyara musu zamane yace”no kubari har ku gama haukan kishin tunda ni dayane Namijin da na taba auran mata biyu ya fice taci kukanta har yau mutanen da suka kawoma gwamna hari ba’asan ko suwayeba suka turosu saboda gwamna ya hana abinciki yace da yarda Allah asirinsu zai Tonu yau tun safe teemah ta daura damara shiri da gwamna ta had’e cikin kananun kaya mini skirt ne da wata ficiciyar Riga ko cibinta bata rufe ba ta saki kitson kanta ya zubo har kafadarta tayi makeup tayi mugun kyau tamkar yar tsana ta fito ta nufi dakinsa ta murda taji gam arufe ta sabko k’asa taga yan aiki sun gama komai anjera kayan breakfast saman dining taje taja kujera ta zauna ta cika cikinta
dam tazo ta zauna saman kujerun parlon lumtsuma lumtsuma tana jiran fitowarsa Dan ta gaji da fushinsa gasu kursu sun tafi dama sune suke debe mata kewa Abu kamar wasa har rana ba labarin Aliyu kuka ta fara ta haye sama tayi ta buga kofarsa shiru jikinta ya bata bayanan ta shiga dakinta ta zabo wata hadadiyar Abaya dukanta pink colour ce taji duwatsu ta saka ta yane kanta da mayafin rigar ta gyara fuskarta ta dauki wayarta tana kiransa amma baya dauka fitowa tayi ta sabko k’asa yan aikinta har biyu suna gaisheta ta amsa ta fito, bangaran, Bintun itama hankalinta atashe yake ayau bataga ko wulgin Aliyu ba ta gaji da rashin ganinsa kullum sai dare ko yamma take ganinsa da yaransa ko kiransa tayi baya dauka kuma takira Boos awaya ko Yallabai yana kusa yace mata ai yau hutawa yake ba inda yaje Jama’a suna ta zauwa yace ace baya gari yace yana bukatar hutawa kwana biyu baya wuni garin idanu bintun tazaro tamasa godiya ta kashe wayar to shinefa take suntiri tsakiyar parlon ta kasa zaune ta kasa tsaye duk yar aikin da tsautsayi ya hau kanta ta dura mata zagi Dan haushin kowa takeyi Sam yau idan bataga Aliyu batada nutsuwa gashi batadon zuwa part d’in Amarya ta qara laifi Dan yau tayi niyar bashi hakuri kafin bakin kwananta yazo su shirya bazata yardaba arabata da. Mijinta ba Teemah tana bude kofar parlonta direct part d’in Bintu ta nufa tana matse kwalla……….. ✍🏻
💃🏻Real Ladingo Yar gidan Janafty😘
✍🏻…Rahma ce Ummu Fareesa
READ ALSO:  Download Complete Nurul Kalb By Matar Manya Hausa Novel PDF
NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.