Download Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 5 Hausa Novel PDF

NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

BOOK ONE
PAGE ➡️16

Fitowarta kenam daga toilet, tana d’aure da towel a kirjinta, gashin kanta a baje agadon bayanta ta wanke shi fess har wani shining yake ga ba’ki ga tsayi har ya kusan isowa ‘kugunta, dake gashin Fulani ne da ita!

Ayush farar mace ce ta asali, ga manya manyan idanuwa gashin ido kuwa zara-zara ba’a magana, azo kan gashin gira acike tam da gashi har girar ya kusan had’ewa 2, ga shaden ta luf-luf kwance da gashi, gashin gaban goshinta kuwa ya sau’ko sun had’e da girar ta.
Allah yayiwa Ayush baiwar suman gashi ga kyau ba’a magana, ga tsayin hanci kamar Wanda kullum ake dad’a tsayinsa, lips d’inta kuwa kamar bakin tsuntsu tsabar ‘karanta tana da ‘karamin baki, colour bakinta yaci maroon sosai kamar wacce ta shafa jan-baki, kuma haka bakinta yake tin tana jaririya,
Ayush ko kad’an bata makeup saboda kwalliyar fuskarta Wanda Allah ya tsara mata mah ya isheta,
Ko tayi makeup ko kartayi kullum Ayush a cikin kyau take, doguwar mace ce, siririya marar kauri, sai dai akwai kayan alatu kam
Ta waran ‘kirjinta ba’a magana a cike fam kamar meyin ciko sai dai bata saka rigar breziya, saboda gurin da ta zauna da mahaifiyarta basa samun kud’i balle suyi siyayyan kayan da zasu saka, sai riga kala d’aya da take using dashi kullum…..

Anzo gurin kuma wato waran Baanbom d’inta ga hips kuwa kamar ita tayiwa kanta, ta ko Ina a cike yake a jinkinta duk da batada jiki amma tana da kyakykyawar surar jiki….
Tsayawa tayi a gaban mirror ta kammala shafa cream mai shegen ‘kamshi ta feffesa turare a jikinta ta gama gyara gashin kanta ta d’aure da rivon, shikenam makeup d’inta kenam ko powder bata shafa ba amma fuskar yanda kasan an tsara kyakykyawan makeup ne.
Ta nufi yanda Doctor Fatima ta ajiye mata kayan da zata saka, wata dan’kararriyar doguwar riga ne na kanti mai bell a jiki black color.

 

Zura rigar tayi sannan ta d’aure kunkumin ta da bell d’in, kunkumi kamar na sauro sai tilin ‘kugu, ga breast d’in ya fito sosai Masha Allah kayan ba ‘karamin kyau sukayi mata ba.
Ba tare da ta rufe kanta ba ta bar room d’in tana taka matakala a hankali ta sau’ko falo, ta nemi d’aya daga cikin jerin kujerun falon ta zauna ta d’aura ‘kafanta d’aya akan d’aya tana fuskantar television Wanda a ciki ake showing India film.
( (Ashe Ayush er Hutu kenam, wato da ace a gidan masu kud’i Ayush ta fito waii da anyi ‘karyar rai))

READ ALSO:  Download IYAYE NA GARI Hausa Novel Complete PDF

“Mom please stop crying, banyi haka don na 6ata miki rai bane, just I can’t believe any body, ni ban yarda da wannan yarinyar ba, zaifi ta bar mana gida”
Junaid ne yayi maganar yana ri’ke da hannun mom d’insa.
Doctor Fatima d’agowa tayi da rinanan idanuwanta wad’anda sukayi jawur tsabar kuka, “Junaid ba wai na’ki batunka bane kana da gaskiya, bama bu’katar yarda da kowa domin yarda da Bara’atu ne yayi silar mutuwar mijina mahaifinka, wanda Inna tuno da hakan nakanyi kuka mai rad’ad’in gaske, amma abunda nakeso ka Sani shine wannan yarinyar da zata zauna damu Yarinya ce ‘karama like bazata wuce 20yrs ba
Bata da mummunan ‘kudiri a ranta face neman taimakon da takeyi, tana bu’katar kulawa,
Mace ce mai rauni inta bar gurin mu bamu San hannun wanda zata fad’a ba maybe mai cutarwa ne,

Kar muyi gaggawar rabuwa da ita domin idan ta shiga hannun mungu tabbas sai Allah ya tambaye mu tinda nasan mahaifiyar ta bata raye marainiyace bata san yanda mahaifinta yake ba shin yana raye ko ya mutu sai Allah,
Please my son”
Dogon Numfashi yaja sannan yace “OK mom na Amince ta zauna a tare da mu, but idan naga robish anything can happen”. Yakai karshen maganar yana kallon mom d’insa
Murmushi ita kuwa tasau na farin ciki tace “insha Allahu ba abunda zai faru, thank you my son”
Mi’kewa yayi akan lallausar gadon sa yana fad’in “OK call her for me, I want to see her”

Mi’kewa tsaye tayi tace “to Zan kuwa Kira ta yanzu tazo ta gaida Boss d’in gidan”. Tana shirin fita yace “mom please am hungry let me eat something” yana kai karshen maganar ya wani d’aure fuska kamar bai ta6a yin murmushi ba,
Mommy kuwa ganin hakan yasa ta kwashe da dariya tana fad’in “OK don’t worry, yaro ba wasa da eating” fita tayi ta bar d’akin, shi kuwa rufe idonsa yayi kamar maiyin bacci …

READ ALSO:  Download Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 3 Hausa Novel PDF

Shima fa Junaid asalin kyakykyawa ne, white chaculate ba ba’ki bane still bai kai asalin farin fata ba domin ko rabin farin Ayush bai d’auko ba, but mutumin akwai dogon hanci ga bigger eyes bakin shima ‘karami ne, dirarren namiji ne ga tsayi ga fad’i ga jiki ga-ga-ga-gaaaa abubuwan sunyi yawa yara kamar su suka halicci kansu , shima akwai tara suman Gashi akansa baya son aski sai dai akwai son gyara suman kullum Gashi a kwance lufff azo kan jikinsa duk gargasa ne ta ko Ina a jikinsa a kwance luf domin ba ‘karamin cream na gyaran jiki Junaid yake amfani da shi ba, Gashi tin daga kan sajensa har zuwa gemunsa a kwance yake…..

Fitowar Doc. Fatima falo ta tarar da Ayush zaune tana ta kallo hankali kwance,
Sauran kad’an Mommy ta juya da gudu ganin Ayush ta d’au Aljana ce
Ayush ce ta kalli gurin da mommy take ta sau murmushi “Aunty na fito ban ganki ba”
Ajiyar zuciya mom tayi sai a yanzu hankalinta ya dawo dai dai jin muryar Ayush d’in
“Wayyo Alhamdulillah Ashe Ayush d’in ce”. Ta ‘karaso yanda Ayush d’in take.
“Masha Allah Ayush kinga yanda kikayi kyau ne, danma bakiyi makeup ba da ba’a San irin kyau d’in da zakiyi ba, said dai a kulleki saboda sumar da samari zaki rin’ka yi a titi”

Kwashewa da dariya Ayush tayi
Tana kallon Doctor Fatima wacce ta ‘kura mata ido
Ita kuma Ayush sai zabga uban murmushi take dimple d’in nan gwanin burgewa.

“Gaskiya zanso Junaid yaga yarinyar nan ko zai ‘kyasa, inada burin ta zamo surkata na samu jikoki kyawawa” Doctor Fatima ce maiyin maganar zuci, daga bisani tayi gyaran murya sannan tace “Yawwa Ayush Oga yana son ganinki”
Cikin mamaki Ayush take kallon Momy tace “wayene Oga kuma Aunty? Kodai mai gidan kike fad’a?”

Duk lokaci guda tayi tambayar still Idonta akan Mom,
Short laugh Mom tayi sannan tace “eh kusan hakan ne, ‘karamin maigidan ne domin babban maigidan ya rigamu gidan gaskiya, ‘karamin maigidan kuma shine yaron gidan”
Sai a yanzu Ayush ta dawo nutsuwarta taja ajiyar zuciya
“Toh shikenam Aunty Zan jeni, Allah ubangiji ya ji’kan maigidan”
Amsawa Mom tayi da Amiin.
Mi’kewa Ayush tayi tana tambayar yanda yake zata je gaisuwa,
Nuna mata hanya Mom tayi yanda zai sadata da d’akin Junaid, ta fara tafiya kenam Mom ta tsayar ta tana fad’in “tsaya ki tafi masa da lunch d’insa domin ya sanar mun da cewa yana jin yunwa.
Tsayawa Ayush tayi tana jiran momy cikin en mintina saiga Mom da manya manyan kuloli har kashi hudu asaman glass tray ta d’aura a kayi hannunta ri’ke da flas da’kananun kofina a Jere saman glass tray d’in,
Yanda Mom ta d’auko haka Ayush ma ta d’auka
Tana hawan upstairs a hankali tabi yanda akayi mata kwatance sai gata a d’akin Junaid,
‘Daki wayam ba kowa, sai’karewa d’akin kallo take yayi matukar burgeta
Ta sau’ke kayan abincin a saman dinning d’insa,

READ ALSO:  Download Complete Duk Karfin Izzata By Star Lady Romantic Hausa Novel PDF

Taje gaban mirror tana duban kanta, kwatsam sai ta hangoshi ta cikin madubi yanata sharar bacci akan gadonsa, dake akwai labule ta tsakanin gadon hakan yasa bata ganshi da wuri ba.
Juyowa tayi da sauri tana le’kashi ta bud’e labulan a hankali tana so taga fuskar shi amma sai dai hannayensa suna kan fuskarsa ta kasa ganin fuskar………

FAST DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 5

The most reliable and easiest way to obtain the completeMatar Damisa Book 1 Chapter 5 isto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Matar Damisa Book 1 Chapter 5 in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the completeMatar Damisa Book 1 Chapter 5booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.