Download Maraici Ne Yajaa Mun Hausa Novel Complete PDF

MARAICI NE YAJAA MUN

(True love and torching heart Storie)

_(Under the pens of merhreeyaert lerwerl and doctor ferhyeez m usmern as in-identical twins)_

Story and written by

Merhreeyaert lerwerl

*BISMILLAHIRRAHMAANIRRAHEEM

 

Alhamdulillah bisa amincewa da huwacewa ta ubangiji gani d’auke da sabon labari mai suna *MARAICI NE YAJAA MUN* Ina fatan Allah subhanahu wata’ala yasa yadda zan fara shi lafiya, na gama lafiya. Yasa mu amfana da abinda ke k’unshe cikin labarin, kurakuran da zamuyi kuma Allah ya yafe mana.

 

*ALLAHUMMA SALLI WASALLIM WA BARIK ALAA NABIYYINA MUHAMMAD, WA AHLIHI WASAHBIHI, WASALLIMAN TASLEEMA

Godiya ta ba zata k’are ba ga dukkannin d’aukacin masu bibiyar littattafan in-identical twins, na dangwala muku kyauta.

 

Ranakun posting d’ina sune

Litinin

Talata

Alkhamees

& Jumu’ah.

 

_salon labarin ya futa daban kamar yadda shi kanshi littafin zaizo daban da sauran littatafaina insha Allah_

Part 1️⃣

Rahama! Rahama!! Ya dinga kwala mata kira da kakkaurar muryarshi.

Wata matashiyar mace ce ta futo a kitchen da sauri sauri tana amsa kiran shi, “na’am Abban Hanan gani nan zuwa”. Ta fad’a tana ajiye tukunyar hannunta gaban shi.

Da sauri ya matsar da k’afarshi don saura k’iris ta d’ora mishi tukunyar a kai, yayi squeezing fuskarshi yace, “Wai meye haka rahama kina kallo zaki zuba mun abinci mai zafin nan kan k’afa, sannan in don nine ma kike duk wannan saurin ba tsayawa yin break zanyi ba don already nayi late, abincin kine dama in nace sai naci kullum zan futa to watarana sai futar ma ta gagare ni”.

Shiru tayi tana kallon shi, sai taji kuma ya bata tausayi, yau kusan 5days yana futa office ba tare daya karya ba, duk yadda take son ganin ta mishi bajinta kafun aje da nisa take sarewa. Saita k’ak’alo murmushi a fuskarta tana kallon shi ta sake cewa, “please Abban Hanan ko ba da yawa ba ka tsaya kaci”.

“Kinga bani sak’on nan zan huce nagode da k’ok’ari”.

“Don Allah ko tea ka tsaya kasha please”. Ta sake fad’a tana rik’e da tukunya a hannu har lokacin, ganin ta takura sai yace, “okay amma ki had’a da sauri”. Cikin jin dad’i tace, “yauwa ko kaifa! Har naji sanyi a raina wallahi ko ba komai k’ok’arina bazai tashi a banza ba”.

“Saura k’iris dai ya tashin”. Ya fad’a yana zama kan stool da take k’ok’arin gyara curtains dasu areef suka wullo mata kafun hucewarsu school.

Tana had’a mishi tean wata matashiyar budurwa ta futo sanye da wata yaloluwar rigar bacci daba abinda ta b’oye har shatin pants d’inta ana gani🙈 tayi mik’a da kiran “Auntie! Auntie!! Auntienaa”. Kusan su duka a tare suka waiwaya suna kallon direction da yarinyar take, rahama ta girgiza kai tana ci gaba da aikinta tace, “ko sai zuwa yaushe Aysha zata san ta girma ta daina mun wannan kira kamar na yaran goye?”.

Mukhtar da yake k’ok’arin amsa waya, sake maida kallon shi yayi gare ta, sai ya lumshe idonshi ya bud’e yana jin sautin daddad’ar muryarta daya jima baiji ba yana kai mishi har can k’arshen zuciyarshi, kafun a hankali ya maida akalar duban shi gareta duba irin na tsaf da tsana ki, saida tsigar jikin shi ya zuba a lokacin da yaga yaloluwar rigar data futo da ita. Itama sai lokacin ta lura dashi a parlon, ganin mayen kallon da mukhtar ke mata yasa taja tsaki tare da komawa cikin d’akin barcinta da sauri had’e da banko k’ofa. Sautin tsakinta ya d’auki hankalin rahama har ya assasa mata d’ago kanta tana kallon sashen da take zaton yarinyar take, sai taga wayam babu ita a gurin, ta sake girgiza kai kurum ta nufi inda Abban Hanan yake zaune ta mik’a mishi tean. Mik’ewa yayi ya d’auki keys d’inshi ba tare daya kalleta ba yace, “bar shayin nan rahama kawai ki bani takardun nan zan huce”.

“Meyasa Abban Hanan? Yanzu fa kace zaka sha kuma bayan na gama had’awa kace ka fasa?”.

“Rahama! Bani takardun nan na tafi”. Ya sake fad’a ba wasa sam.

Itama sai bata sake ce dashi komai ba ta nufi d’akin gadon shi, yabi bayanta da kallo cikin zuciyarshi yana jin wani abu yana tab’a ranshi. Har ta dawo yana gurin ta mik’a mishi ya karb’a, suka k’arasa yin sallama ya tafi ita kuma ta fara k’ok’arin k’arasa had’a gidanta kafun azo karb’an abincin yaran can don yau basu tafi da lunch ba na break ma da biscuits ta had’a su cox kwata kwata bata jin dad’in jikinta cikin ranakun.

 

Around 11:30 ta sake futowa cikin shigar doguwar riga maroon data zauna jikinta sosai, kanta ba d’ankwali sai wani irin k’ananan kitso da akayi shi da attachment ya sauko har kafad’arta, ta futo tana k’ok’arin d’aure shi a k’eyarta. Yarinyar d’azu ce, naturally ba fara bace amma ta hanyar amfani da tsadaddun mayukan k’ara hasken fata yanzun ta koma fara sol kamar yayarta rahama, za’a iya kiranta kyakkyawa duba da bata da wata makusa a fuska, tana da k’aramin jiki, ga wanda ya mata kallon tsoro ma zai iya ce mata siririya. That’s Aysha y’ar gayu kuma ma’abociyar aji da son kwalliya kamar d’aweesu.

A lokacin rahama tana zaune tana kallon wani program da ake mai matuk’ar muhimmanci da Jan hankali ga mata, tare da *AUNTIE FAUZIYYAH D SULAIMAN*, k’amshin turaren ta shiya ankarar da rahama zuwanta, ta d’ago tana kallonta har ta k’araso kusa da ita ta zauna a shagwob’e tana gaisheta, “auntie rahama Ina kwana”.

Zuba mata ido tayi ba tare data amsa ba har ta sake maimaita gaisuwarta.

“Aysha! Wai me yasa kullum abubuwan ki k’ara yin gaba suke? Saboda kinga nasa miki ido ko? Toh wallahi kuwa kwanan nan zamu sa k’afar wando d’aya dake, bar ganin Ina zuba miki ido ehe”.

A marairaice wannan karon ma tace, “kiyi hak’uri auntie rahama insha Allah zan kiyaye”.

“Yafi miki dai”. Shiru duk sukayi kafun rahama ta kalleta tace, “ga breakfast d’inki can a dinning”.

Bata amsa taba, hakan yasa yayar ta d’an kira sunanta da k’arfi, “Aysha!”, sai tayi firgigit tana kallonta, “zaki fara wad’an nan tunane tunanen banzan naki saboda na miki fad’a yau ko?”.

READ ALSO:  Download Complete Furar Danko Chapter 4 By Billyn Abdul Hausa Novel PDF

“A’a auntie, kawai dai so nake idan ba zaki damu ba ki daina sa baki akan duk abinda zaki gani tsakanina da Yaya mukhtar…”.

Cikin rashin fahimtar inda maganganunta suka tafi rahaman tace, “owkay na zuba miki ido kina rashin mutumci da da’a ga mutumin daya miki komai a rayuwa? Yayi dawainiya dake tun baki san kanki ba, yake ci gaba dayi har a yanzu ma?”.

“Ba haka nake nufi ba auntie, tabbas Abban Hanan yayi mun abinda bazan tab’a iya mantawa dashi ba, ya d’auki nauyin cina, shana, sutturata da d’awainiyar karatuna gaba d’aya, sannan dai dai da rana d’aya bai tab’a gazawa dani ba, Ina sane da abinda yayi mun matsayina na wadda ta taso cikin maraici da talauci, sai dai hakan ba yana nufin shi d’in bashi da kuskure ta wani fannin ba, ko ni bazan misbehaving a wasu abubuwan ba, a wannan gab’ar sai dai ince kiyi hak’uri auntie rahama, amma ki d’auki duk abinda nake ma mijin ki matsayin ajizanci irin na d’an Adam….. Ina fatan kuma don Allah zamu rufe babin wannan maganar gaba d’aya”.

Tunda ta fara magana rahama ta tsura mata ido tana kallonta, wani lokacin in Aysha tayi wani abun takan rasa gane Inda tasa gaba, ta kasa fahimtar abinda ke faruwa tsakaninta da mukhtar sam,,,,, sai dai fa ita no matter what ba zata yarda mutumcin mijinta ya zube a fuskar k’aramar yarinya kamar taba.

 

Basu sake ce da juna komai ba Aysha ta d’auki remote ta sauya zuwa wata channel da ake haska Indian series masu kyau, taso missing kuwa don an fara nisa a haska maimaicin firm d’in, tun asali shine abinda ya futo da ita da zumud’in ta sai kuma auntie rahama ta nemi b’ata mata rai a banza da maganar mijinta da a duniya bata iya ganin laifin shi.

 

*****Mukhtar yana zaune a office amma abun duniya ya mishi zafi da yawa, ya kasa fahimtar kanshi gaba d’aya cikin shekara d’aya zuwa biyun da suka gabata, akan Aysha yakan rasa gaba d’aya control, ya riga ya saba da rayuwa tare da ita, yadda take kula dashi ada ko rahama bata iyawa, zai iya cewa rahama tana auren shine amma yadda Aysha tasan komai nashi rahama bata sani ba, gashi yanzu gaba d’aya ta sauya mishi a lokacin da alak’ar su ta fara d’aukar zafi, maybe ko saboda tana tuna matsayinta gare shi da kuma rahama matarshi ne? Allah masani.

 

*****Da yamma ta sake yin kwalliyarta cikin wata rigar ba irin ta d’azu ba, tayi rolling madaidaicin gyale saman kanta, fuskarta d’auke da light make-up ta futo tana fudda sirrin k’amshi. Kitchen tayi don can take jiyo tashin k’amshin daddad’an girkin da rahama takeyi, tana shiga ta fad’ad’a fara’ar fuskarta tace, “mie auntie sannu da aiki?”.

Rahama tana kallonta tace, “ke za’a yiwa sannu Aysha irin wannan bacci haka wuni guda, da gaske dai hutun makarantar akeyi shiyasa ko d’an girkin da ake tayani shiryawa mukhtar an daina”.

A zuciyarta tace, “aikuwa in dai don mijin ki yaci yaji dad’i ne na daina wahalar da kaina a kitchen ina shiryawa k’aton banza abinci yana ci yana sude hannu”. (Nikam nace toh fah🤔) a zahiri kam cewa tayi, “ki bari hutuna ya k’are na koma school sai aci gaba da fafatawa”. Rahama tace, “toh Allah yasa”.

“Yauwa auntie zan futa Yaya Fu’ad yana jirana a waje”.

Rahama tace, “ayyah toh sai kin dawo, amma don Allah kiyi k’ok’ari ki sallame shi kafun Abban Hanan ya dawo kinsan baya so”.

“Hum kada Allah ma yasa yaso shiya sani matsalar shice ni kam ba abinda ya shafe ni, haka kurum duk friends d’ina suna aure shi yana son dak’ile ni saboda wani dalili nashi daban na banza, da anyi magana yace karatu karatu, karatun da in naso a yau zan iya zab’ar aure na barshi”…… Duka wad’annan maganganu Aysha tana yinsu ne a cikin zuciyarta.

Ganin ta tafi tunani sai rahama ta tab’o ta, “Aysha are you okay?”.

Da sauri tace, “I will take care insha Allah, saina dawo”. Ta k’arasa fad’a tana futa da sauri ba tare da ta sake jiran abinda rahaman zata ce ba,

Ita kuwa da kallo ta bita harta futa sannan taci gaba da aikinta tana girgiza kai, inda ace Aysha zata bi tsarinta daba zata tab’a zuwa gaban wanda ba muharraminta ba da wannan yalolon gyalen, hijab ya kamata tasa irin wanda shari’a tayi umarni, toh amma yata iya, fad’an da yafi karfinta dole zata mai dashi waasa, don tana mata magana yanzu zata ce ba haka ba, ita ga y’ar zamani wayayyiya……

 

Fu’ad wani kwallin mutum ne da rahama ba zata tab’a mantawa dashi ba a rayuwar Aysha, cox ya mata duk wani abu da masoyin gaskiya kad’ai ne zai iya yinshi, bai kyamace taba a lokacin da take tsananin buk’atar taimako, yaso ta tun tana asalinta na Aysha ba yanzu data samu y’anci ta goge ta zama wata mutum ta daban ba. Shiyasa itama Ayshan take son shi take jurar shiga kowanne irin matsala a kanshi.

 

Suna zaune suna hirar su a wannan yammaci, hira irinta ma’abota soyayyah, Banda murmushi ba abinda ke kan fuskar kowannen su, tuni ta manta da kashedin wata rahama hirarta kawai take, bata ankara da lokaci ba sai Jin horn d’in motar mukhtar tayi a k’ofar gida.

Fu’ad ya dubeta a gigice yana tambayarta, “Aysha dama Yaya mukhtar yana gari kika ce mun yayi tafiya?”

Ta harari wajen get kamar shine a gurin, ta yamutsa fuskarta tace, “eh mana toh ai inba haka nace ba nasan ba zaka zoba, ni kuma gashi nayi kewarka, kaima kuma nasan kana kewata”.

Fu’ad ya tsare ta da kallo yana jinjina k’arfin hali irin nata da rashin tsoro, bai manta yadda suka kwasheta da guy nan ba last time, da kakkausar murya ya mishi kashedin karya sake ganin shi cikin gidan sa.

READ ALSO:  Download Complete Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 101-105 Hausa Novel PDF

“Fu’ad wai meye naga duk ka wani tsure sai kace ba namiji d’an uwanka ba”.

Fahad ya mik’e tsaye ya d’auki mukullin machine d’inshi yace, “ba zaki gane ba Aysha, matsalar shine gidan shi na shigo”. Dai dai lokacin su Hanan suka shigo da gudu rik’e da lunch box, shi kuma uban gayyar ya tsaya bud’e get da kanshi, bai gansu ba kwata kwata, ihun areef ne ya ankarar dashi inda yake tama Fu’ad oyoyo.

Saida yaji gaban shi ya fad’i, ya fasa bud’e mukullin ya juya yana kallon gurin da suke. Fu’ad nata d’aga areef don k’arfin hali yana mishi wasa. Ya sauke shi kenan zai bashi alawa mukhtar ya k’araso yana fad’in, “kada ka kuskura ka basu”. Sai ya dakata har ya k’araso ya janye yaran shi daga jikin su ya tura su gida, saida suka shige ya maida duban shi ga Fahad yana tambayarshi, “Kai wai bana hana ka zuwa gidan nan bane? Okay baka jin magana ko? Toh bari ka gani police zan kira yanzun nan sai kayi musu bayanin abinda ya shigo da kai gida na”. Ya k’are fad’a yana k’ok’arin ciro wayarshi a aljihu. Fu’ad cikin neman laluma ya durk’usa yana rok’on shi da bashi hak’uri. Shi kuwa ko sauraron shima baiyi ba kawai neman no dpo yake, abun daya sake hassala Aysha kenan ta matsa gaba ta kira sunan Fu’ad tace, “biyo ni muje”. Fu’ad ya tashi zaibi bayanta mukhtar ya rik’o rigarshi da sauri, “aiba inda zaka saika fad’a mun ubanda yasa ka shigo mun gida ba tare da neman izinina ba”. Gaban shi Aysha ta dawo ta fuzge rigar Fu’ad daya rik’e tace, “ka barshi ya tafi Yaya mukhtar”.

“Idan nak’i fa?”. Ya tambayeta yana kallon cikin kwayar idonta.

Aysha ba tsoro taci gaba da kallon shi muryarta k’asa k’asa tace, “Zan fasa kwai mai d’oyin da warin shi zai kusa hallaka kowa”.

Tana fad’in haka ta juya tana kallon Fu’ad tace, “baby muje ko?”.

Ba musu Fu’ad da yake neman hanyar sillewa yabi bayanta suka tafi yana waigen mukhtar daya zama robbot a gurin har suka fuce bai iya motsawa ba.

Ta jima a k’ofar gida suna sallama da Fu’ad kafun ya tafi ta dawo gidan, yana tsaye inda ta barshi, ta d’auke kanta gefe tamkar bata ganshi ba zata huce, yasha gabanta da sauri ya kamo hannunta ya fuzge wayarta ya tura a aljihu ya shige gidan, tabi bayan shi zuciyarta na suya. Koda ta shiga baya parlon ma sai su Hanan kawai da suka sauya uniform suke hada hadar su. Suna ganinta suka taso zasu bata labarin makaranta har rige rige suke, ba tayi niyyar zama parlon ba, amma saboda yaran saita zauna ta biye ta tasu suna ta hira, har assignment tayi musu.

Kiran sallar magrib yasa mukhtar ya futo rahama a bayanshi cikin sabuwar shiga ba wadda ya dawo da ita ba, ta kalle shi sau d’aya ta d’auke kanta gefe, shi kuwa zuba mata ido yayi yana kallonta tun daga inda yake har ya k’araso kusa, hannu ya mik’awa areef yace, “zo muje masjid”. Yaron ya mik’e ya taho gurin mahaifin nashi yace, “dady banyi alwala ba ai”.

“Muje sai kayi a famfon waje”. Sukayi waje ita kuma ta mik’e tana harhad’a musu kayan su tace, “oya time for magrib prayer”.

Daga nan sukayi ciki ita da hanan suka bar rahama ma tana harramar tada sallah.

Saida ta adanawa yarinyar kayanta rankatakaf sannan suka d’auro alwala tare suka gudanar da sallarsu. Basu futo ba har dare saida rahama ta aiko areef ya kirawo su, ta futo rik’e da hannun Hanan.

Gogan yana zaune rahama a gefen shi tana had’a mishi kayan abincin shi. Aysha tana k’arasa futowa rahama tace, “yauwa Aysha zoki k’arasa had’awa mukhtar abincin nan, nayi mantuwa a bedroom d’inshi”. Aysha tayi saroro tana kallon auntien har saida tace, “ba zakiyi ba kenan saboda ban Isa na saki kona hana ki abu akan mijina ba…”. Saita girgiza kai ta k’arasa inda take ta karb’i trayn ita kuma ta tashi, daga durk’ushen take k’arasa zuba mayounace cikin had’in cole slow da rahama zatayi, ta zabga mishi ita kuwa da yawa cox tasan baya son duk wani abu dake da mai da yawa.

Ta mik’a mishi abincin, areef nata mishi zance, wayarshi ya ajiye ya kalleta na wasu sakanni kafun ya nunawa areef Hanan, “ga can Hanan zata cinye abincin ku duka”. Aikuwa ya tafi da gudu yana fad’in, “ke Hanan abincin mune fa mu biyu”. Ko kallon shi Hanan batayi ba Cox ita bata wasa da cikinta.

Ganin hankalin yaron ya bar kansu sai ya karb’i trayn ya ajiye gefe, ita kuma ya jawota jikinshi ya rungume ta tsam kan cinyarshi.

“Me yasa ke kullum baki jin magana”. Ya fad’a yana kallon kwayar idonta.

Kiciniyar kwace jikinta take har idonta ya ciko da hawaye tace, “don Allah malam ka rabu dani bana son wannan salon iskancin da kake yimun”.

“Ai bazan rabu dake ba har sai kin fad’a mun abinda yaron nan Fu’ad yake dashi ko yake baki da yasa kullum kike nacewa da son lallai sai kin kula shi? Duk mazan da suke sonki ki rasa wanda zaki kula sai Fu’ad? Bakisan ajin ki nesa yake da nashi ba?”.

A lokacin hawayen idonta ya fara sauka, cikin raunananniyar murya take cewa, “fintinkau ma, Fu’ad ya fiye mun kai da ire irenka sau dubu wallahi, kuma ka daina gurb’ataccen tunani akanshi don shi ba d’an iska bane, sannan ka bani wayata daka kwace, ka kuma rabu dani tun kafun auntie rahama ta futo ta ganmu, ga yaran kama zasu iya ganin mu koda yake kai ba kunyarsu kake jiba”.

Sake mata hannu yayi ta mik’e tana share hawayen idonta tana kallon shi, “ka bani wayata tun kafun na shuka maka rashin mutumcin da zaman gidan nan zai gagare ni…”.

READ ALSO:  Dowload Zain Abeed Hausa Novel Complete PDF

Kamar yayi dariya jin furucinta, Sai ya jawo abincin shi ya fara ci ya rabu da ita, “magana nake maka ka bani wayata”. Ta sake fad’a cike da rashin kunya.

“Ki sameni office gobe ki karb’a”.

“Aiba a office ka karb’a ba a gida ka karb’a don haka ba inda zanje”. Ta k’arasa fad’a tana juyawa tabar gurin, dai dai lokacin da rahama kuma ta sauko, tana ganin yanayin su tasan halin akayi.

 

Ita ko Aysha kitchen ta shiga tasha kukanta son rai ta wanke fuskarta, a nan taci abincinta na dare ta shige d’akinta.

 

K’iri k’iri mukhtar ya hanata kallace kallacen series da takeyi duk dare, yana da parlon shi da kayan kallo amma saiya taho nan ya kasa ya tsare kawai saboda ita.

 

*********

 

Washe garin ranar ta shirya tunda wuri cikin doguwar rigar atamfa data haska ta, ta d’aure tulin gashin dokinta a k’eya, tayi d’auri a saman shi, ta shafa jan baki pitch colour ta d’ora k’aton sun glasses daya kusa rufe rabin fuskarta, ta yafa mayafin a gefen kafad’arta, haka jakar ma, uban hill shoe data kwama ya k’ara mata d’an tsawo kad’an. Tayi bala’in kyau duk Inda ta gifta k’amshi ke tashi.

Banbancinta da rahama na zahiri kenan, tafi rahama son kyale kyale, kwalliya da iya d’aukar wanka dai dai da wanda zai karb’i jikinta, duk da in ana maganar kyau da sura rahama ta fita komai bata Isa ma ta had’a kanta da ita ba, sai dai Kuma Allah yayita Sam bata damu da rayuwa ba, iya tsawon rayuwarta da mukhtar bata tab’a yin wani abu da yake soba irin na wayayyun mata, tun lokacin suna daga shi sai ita Allah baisa ta iya sake saken k’ananun kaya ba, bare yanzu data tara yara take kafa hujja dasu in yayi magana, yayinda Aysha take sab’anin ta, ita komai nata da tsari take yin shi, ko kwanciya bacci zatayi irin kayan da take sakawa rahama bata tab’a gwada su a jikinta ba tunda take, haka da safe, a gurinta ta koyi girki amma yanzu in tayi girki ya dame na rahama ya shanye a taste, shiyasa suke d’asawa da mukhtar cox ta kasance dai dai da ra’ayin shi.

 

 

Da farko shak’uwa ce kawai tsakanin su, amma daga baya saboda irin dressing d’inta da shegun turarruka da take amfani dasu na d’aukar hankali da kunna futuna, sai akalar alak’ar ta nemi sauyawa, don wannan ma yana daga abinda ke d’aukar hankalin mukhtar matuk’a gaya, gashi sam bai tsara gidan shi da nufin auren mace sama da d’aya ba Cox yaga yadda maman shi tasha wuya a zaman kishiyoyi, yana tsoron ya auro wata tazo ta dinga azabtar mishi da mata, bayan yana mugun son matarshi. Don a halaye rahama tafi Aysha kirki hak’uri son mutane, da juriya. _Wannan kenan_.

Kusan wannan kusanci zamu iya cewa rahama ce ta fara shi, don itace ta dinga tura Aysha cikin al’amuran mukhtar sosai, kamar gyaran d’akin baccinshi a lokacin da yake bacci, ko had’a mishi ruwan wanka, yi mishi girki da saving d’inshi, sauketa makaranta a motarshi da sauran su. Da wannan dama shed’an yayi amfani ya dinga k’awata mishi Aysha yana gina soyayyarta da sha’awarta mai k’arfi cikin zuciyarshi, hakan yasa ya fara bijiro mata da wasu halaye na son tab’a jikinta ko kusanci da ita,

 

da farko Aysha tana d’aukar hakan ba matsayin komai ba, amma daga baya saita fara ganin sauyi na gaske, koda ta ankara tasan abinda yake yi ba mai kyau bane, amma saboda d’awainiyar da yake da ita yasa ta shanye koda wasa bata tab’a yarda rahama tasan halin da suke ciki ba. Yayinda ta gefe guda mukhtar yake zuba love romance da ita wanda yasan haramun ne a matsayinta na k’anwar matarshi, amma bazai iya hana kanshi abinda gangar jiki da ruhin shi ke so ba, a duk lokacin da zasu samu wata damar keb’ewa daga shi sai ita zai jawota jikin shi ya kissing d’inta ya mata abubuwa, amma a idon rahama ya fuske kamar bashi yayi ba, yayinda a duk d’aukar rahama take ganin kamar shak’uwa ce kawai tsakanin su.

Babban abinda ya fara d’agawa Aysha hankali shine korar duk wasu masoyanta da mukhtar ya fara, Koda yake sauran bata damu ba saida abun yazo kan Fu’ad da suke soyayyah hadda mafarkin aure amma taga mukhtar ya tasamma lalata wannan alak’a, wannan yana daga abinda yasa ta janye jikinta baya dashi, ta daina yi mishi gyaran d’aki, girki da duk wani abu na kyautatawa da yake kuma basu damar keb’ewa kamar rage mata hanya a mota da sauran su, ta kuma fara mishi rashin kunya don ta dad’e da gama raina shi, abinda ya fara d’aga hankalin mukhtar musamman a yanzu da rahama take fama da laulayin ciki take ta kanta.

 

Wannan page sadaukarwa ne ga d’aukacin members na MARAICI NE YA JAA MUN.

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Maraici Ne Yajaa Mun Book

The most reliable and easiest way to obtain the complete Maraici Ne Yajaa Mun book to purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Maraici Ne Yajaa Mun inPortable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete Maraici Ne Yajaa Mun booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an emailcontaining the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

 

 

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.