Download Complete Idan Ba Ke Chapter 1&2 By NimcyLuv Hausa Novel PDF

Nimcyluv sarauta
Arewabooks@Nimcyluv

1.
Jimeta/Yola
Njoɓoli Rugar Rome

Gudu Saniyar take tana bin ta a baya itama, hannunta riƙe da sanda na korar Nagge, tamkar wanda suke wasan tsere haka Saniyar ke gudu a cikin jejin ita ma bata fasa bin ta ba, sauran Naggen suna gefe guda ko wacce na cin ciyayi wanda bisa kuskure tana can tana bin Saniya ɗaya tilo, sauran Naggen suka faɗa cikin gonar wani manomi, a yunwace suka rufarwa albarkatun gonar. Cikin siririyar muryarta mai nuni da Yarintar ta, da kuma nuna cewa ita ɗin zallar bafullatanar Yola ce ƴar Usul. “Waru! Waru! Waru” shi ne abin da yarinyar ke ta nanatawa cikin hausarta ta Fulani, yayinda Saniyar tuni tai mata nisa cikin gajiya wa da bin Saniyar ta tsaya a wajan wata gaɓar ruwa tana riƙe ƙugunta ta ce “Bone, lalashewa ta samu Nagge Aradu”

 

da sauri kuma ta ɗauki sandar tana ƙara yin kan Saniyar ganin ta tsaya da gudun da take, cikin sa’a ta cimmata tana zuwa ta kama ƙahonta tare da ƙifƙifta idanunta alamar zallar fitsarar dake tattare da ita “d’ume ngid’d’a?” Ma’ana “me kake so?” Kallon ta Saniyar ta yi sai kuma ta kaɗa jela tare da zubewa a wajan ta shiga shura ƙafafuwa kamar zata mutu, cikin tsoro haɗi da razani HALISA ta ce “Jomirawo ka taimakeni” ta faɗa tana kallon Saniyar wacce tai male-male a ƙasa ga wani ruwa mai kama da jini na fitowa ta ƙasanta, kuka Halisa ta sanya domin idan Saniyar ta mutu a nan wajan ta shiga uku, itama watan mutuwarta ya kama. Tsayar da kukan tai kafin ta fara duba cikin jeji babu kowa sai ita, ga wani kwantaccen baƙin hadari dake ƙasa wanda a koda yaushe zai iya tashi.

Juyawa tayi ta nufi wajan wata bishiya inda ta hangi ƙaramar igiya a jiki, tana zuwa jikin bishiyar ta zame hular Fulanin dake kanta, nan da nan sumar kanta ta sauka wacce take jajir babu alamar baƙi ko ɗaya, gashin ba wani cika ne dashi ba, kawai tsayin gashi gareta, domin har fatar tsakiyar kanta ana iya ganowa. cikin sayin jikinta ta fara jan igiyar tana ƙoƙarin kunce igiyar gaba ɗaya daga jikin reshen bishiyar, kamar daga sama taji saukar wani abu mai sanyin gaske zuwa kafaɗunta. Cak ta tsaya tana sauraren yadda abin ke tafiya sululuuuu a jikinta har ya gama sauka, hannunta ta miƙa da nufin kama abin da ya sakko mata domin bata da tsoro ko kaɗan,

 

rashin sa’a hannunta ya sauka saman ƙaton kan maciji wanda yake kwance a jikinta, wani santsi-santsi ta ji a jikin macijin ga wani sanyi sosai dake ratsa fatar jikinta, bata gama yadda da abin da zuciyarta ke ayyana mata ba, a hankali ta juya wani ihu ta kurma wanda ya yi daidai da ɗaukewar numfashinta, baya tayi zata faɗi kafin ta kai zuwa ƙasa macijin ya yi wata girgiza cikin sakanni ya juye zuwa wani saurayi wanda jikinsa ya ke sanye da wasu haɗaɗɗun kayan sarauta na farin saƙi, fari ne tas amma kamar Fatar mace haka fatar hannunsa da sauran jikinsa suke gaba ɗaya gashi ya kwanta luff. Zubewa ya yi a ƙasa ta faɗo jikinsa idanunsa a kan fuskarta, ya jima yana kallonta kafin cikin izza da nutsuwa ya ce “kin tsoratani, kin tsorata kanki Danejo, banyi niyyar zuwar maki ba yanzu” Danejo sunan da ƴan rugar Rome suke faɗawa Halisa ke nan. Sai da ya gama Kallon ta sosai, kallon da ya jima bai mata ba tun tana zanin goyo matsayin Jaririya. Ɗaukanta ya yi ya nufi inda Naggen suke yana zuwa ya tarar da wannan Saniyar dake Shure Shure ta haihu, ashe daman ciwon haihuwa ke damunta. Halisa ya kalla yana sakin Murmushi kafin ya zaro harshesa waje sai ga wani zobe ya bayyana, cikin sauri ya saka mata zoben mai ɗauke da tambarin wata masarauta, kafin ya yi Girgiza sai ga shi ya sauya kama, kamarsa a fuska na nan, amma kayan jikinsa sun sauya sun koma irin kayan Fulani sak komai da komai, goya Danejo ya yi a bayansa, ya ɗauki jaririn Saniyar cikin nutsuwa ya fara kaɗa Naggen zuwa Rugar Rome. Kamar ƙifatawar idanu haka ya ƙaraso Rugar..

Iskar dake kaɗawa na alamar tashin hadarin ya sanya matashin ɗaga kansa sama, yana kallon yadda gajimare ke haɗa kansa. A nutse kuma ya fara bin Rugar Rome da kallo ba wata babba bace, amma Ubangiji ya albarkaci rugar da dabbobi musamman Nagge, gasu manyan gwanin sha’awa yawancinsu jajaye ne kafin ka samu farar saniya zaka daɗe.

READ ALSO:  Download Complete Yar Aikin Karuwai Book 2 Page 111-115 Hausa Novel PDF

Wasu sun dawo daka kiwo wasu kuma na hanya sbd rashin yawaitar mutane da babu a rugar, daidai wajan wata bukka ya Ƙarasa yana gyara riƙon da ya yi wa Jaririyar Saniyar kafin ya ce “Sannunmu dai” ya faɗa a taushashe jin shiru ya sanya ya ƙara buɗe muryarsa mai sanyi ya ce “Afuwanku dai” daga cikin bukkar wata ƙaramar murya ta amsa da faɗin “Waye nan?” Ta faɗi hakan tana fitowa, lokacin da Idanunta ya sauka acikin ƙwayar matashin gabanta taji ya faɗi saboda yadda taga ƙwayar idanunsa, gane cewa kamar ta tsorata da yanayinsa ya sanya ya lumshe idanunsa kaɗan tare da buɗewa ya ce “

 

Ga ɗan uwanki na kawo shi, arado bashi da lafiya ne can na ganosa yashe a jeji ba rai, har naggenku ya samu zuri’a” yana faɗin hakan ya ajjiye Jaririyar Saniyar a ƙasa wacce take jajir da ita Kuma ƙatuwa. Shatu dai binsa take da Idanunta domin bata taɓa ganin mai kama dashi a rugar ba sai yau, kallon da yaga yai yawa ne yasa ya ce “Shai a mata magani” a hankali ya sauke Halisa Dajeno ya kwantar a ƙasa a nan gaban bukkar kamar zai juya ya tafi sai kuma ya ƙurawa zoben hannunta idanu wanda yake sheƙi sosai ga tambarin masarauta nan ya fito sosai a jikinsa, a ransa yake ji kamar bai dace daya mallaka mata wannan zoben ba, amma bashi da wani zaɓi dole ya bata ta haka ne kawai zai lalubota a duk sanda ta ɓace masa, tun tana ciki yake fama da rainonta lokacin haihuwarta ne kawai bai sani ba.

Ba tare da ya ƙara cewa komai ba ya juya da sauri ya fara tafiya tare da shankwana, yana barin wajan ya ƙara yin girgiza wata iska mai daɗi da guguwa ta mamaye gaba ɗaya cikin Rugar Rome. Nan take ya koma asalin macijinsa kamar yadda ya bayyana a farko, yana iya komawa duk suffar da yaga dama cikin ƙaramin lokaci amma zama maciji yafi masa daɗi sbd yawaitar macije dake cikin jejin daya zagaye Rugar Rome, a haka ya sulale tare da komawa cikin jejin.

Iskar dake kaɗawa ce tai sanadiyyar farkawar Dajeno daga barcin dolen da macijin ya sanyata a ruɗe ta miƙe tana dafe kanta dake mata ciwo sosai cikin sanyin murya ta ce. “Miyyati Allah” Shatu dake gefen Dajeno tana ɗaure Naggen a garken dake dab da bukkar ta ce “Nassu, ka shigo” Shiru Danejo tai kamar zata tuna wani abu sai kuma tai saurin ware manyan idanunta ta ce “Shai Shatu ina Dadana ya tashi daga barci hoo?” Shatu ta ce “E, yana ta kiranka baka dawo ba, ciwonsa ya tashi yana ta masa zafi” da sauri Danejo ta faɗa cikin bukkar Idanunta ya sauka akan Dada (her mother) tana kwance a rufeta da wani farin zani jikinta sai rawa yake, fara ce matar sosai amma yanayin jikinta kamar ta shekara 60 nan kuma ba tafi shekaru 50 ba idan ma ta cika.

 

“Shannu shannu Dadana” Idanu Dada ta buɗe da ƙyar ta ce “Zakiyi Albarka Halisa ki riƙe gaskiya da amana ki zama mai haƙuri ki daina saurin fushi da rashin kunya” Kallo juna sukai da Shatu da Halisa wacce akafi sani da Dajeno “Dada me yasa kake shaiwa haka?” Dada ta kalli Shatu kana ta juya ta kama Hannun Dajeno ta haɗa dana Shatu ta ce “Meyasa ba zance haka ba? Shatu kece ƙarama Halisa ita ce babba amma zafin zuciya ne da ita, rauninta akai na yake, kuma dole na tafi na barta” da sauri Shatu ta kalli Dada tana faɗin “Ina zaka Dada kuma?bayan Rugar Rome ina muke dashi” Dada ta numfasa ta ce “Babu da inda yafi wannan Rugar, zan tafi zuwa ga Mahaliccin daya samar da Rugar Romen, ciwon nan ba zai barni ba kuɗin amanata ce musamman ke Halisa”

 

Dajeno kasa cewa komai tai sai ƙurawa Dada fararen idanunta da tayi zuciyarta cike da fargaba. “Dadana ba zaki mutu ba, idan kin mutu wa muke dashi a nan rugar wazai dinga kulawa damu?” Dajeno ta ƙare maganar cikin sanyin murya gaba ɗaya jikinta yai sanyi sosai. Shiru kawai Dada tai can kuma ta ce “Hamma Yabi ya dawo?” “A’a birni da nisa Dadana yace gobe zai kai ki can asibitin birnin”. Jinjina kai Dada tai Dajeno ta miƙe bayan ta ce Shatu ta kula da Dada yanzu zata wajan Sarkin ruga ta amso magani.

READ ALSO:  Download All Top Sweet and Dark Romance Short Stories from Wattpad

Cikin sanyin jikin nan nata take tafiya kanta a ƙasa domin bata fiya kallon mutane ba, a yadda jikin Danejo yake da sanyi zaka ɗauka babu ruwan ta, musamman da fuskarta yai kala dana salihai amma zafi da zuciya gareta, ga kuma taurin kai da naci akan abu, idan tace zatai to tabbas zatai, amma idan tace A’a babu wanda ya isa juyata ko Dada sai dai ta zuba mata Idanu. Abin birgewa ga rayuwar Halisa Dajeno tana da saurin yafiya, da kuma tausayi da kuma kawaici. Cikin tafiyar nutsuwa ta Ƙarasa gaban wata bukka wacce tafi ko wacce bukka kyau da girma a cikin Rugar Rome. “Shai shai Mene haka kamar makauniya ina kwaɗa miki shandan nan Aradu” da sauri Danejo ta ɗaga idanunta ta kalli Gwaggo Niyabi wacce ke zaune tana kaɗa audiga, murguɗa baki tai ba tare data ce komai ba, jin tai shiru yasa Gwaggo faɗin “Ko njid’ud’a?”

 

“Magani za’a bawa Dadana” Gwaggo Niyabi ta ce “To baya nan” shiru tai kamar zatai Mgn sai kuma ta juya sai da tayi nisa kaɗan Gwaggo Niyabi ta ce “Yaka Dajeno waru” tsaye Dajeno tai domin ba shiri suke da Gwaggo ba, Murmushi Gwaggo tai sosai kafin ta numfasa ta ce “Idan kinje ki tambayi Dada waye mahaifinki, mene yasa daya rasu bata bar Rugar Rome ba, ta tafi danginta ko dangin mijinta” da mamaki Danejo ta ce

“To bayan Baffa ya rasu mene na tambayarsa, ki daina maganar Uwayena” Gwaggo ta miƙe tana kallon Danejo “To ana gab da kurarku a Rugar Rome, domin bama son mara gurbi” harara Danejo ta watsa mata ta ce “Miyidi saro’am” ma’ana ina son iyayena “Kalleki mai ƙaton baki da ƙwalaƙwalan idanu” tana faɗin hakan ta kwasa da gudu zuwa bukkarsu.

Da ƙyar suka samu zazzaɓi Dada ya sauka tasha paracetamol sai 12 na dare ta samu barci. Shatu ma barci take kusa da Dada a hankali Danejo ta miƙe daga kwancan da take har yanzu fararen kayan Fulani ne sanye a jikinta, hula ta ɗauka ta rufe kanta a nutse ta fita daga cikin bukkar kai tsaye garken shanun dake dab da bukkar ta nufa, wanda aka kunna musu wuta tana ci kaɗan kaɗan. Gobe da sassafe take son tafiya tallan kindirmon.

ƙwarya ta ɗauka ta tsuguna tare da kama nonon jikin wata Nagge ta fara tatsa gaba ɗaya hankalinta baya jikinta sai a lokacin maganar Gwaggo Niyabi ta faɗo mata, a haka ta gama tatsar nonon acikin ƙwayar ta ajjiye can gefe guda a bukkar tasu. Gari na waye ba tare da yin wanka ba ta shasshafa ruwa ƙafa duk lam’a ta dungura sallah.

Dada na gefe tana kallon yadda take sallah tana son tuna wani abu amma ta kasa har zuciyarta take jin kamar yadda Danejo ke sallah ba haka ake yi ba, amma ta kasa ganewa da kuma tuna yadda ake?. “Ina Hamma Yabi?” Danejo ta kalli Dada tace “Mi naddi mo (na kira shi)”. Jinjina kai Dada tai, Danejo sai kallon Dada take kamar zatai shiru sai kuma tace “Dada waye Baffa?” Da sauri Dada ta juya gabanta na faɗuwa sosai na rashin amsar tambayar Danejo tace “Kamarya Halisa? Baffa mahaifinku ne kuma ya rasu mene?”

 

“Na sani Dada, ina dangin Baffana suke me yasa muke zaune a Rugar Rome?” A hargitse Dada ta ɗaga hannunta tare da ɗauke Danejo da mari sai kuma ta fashe da kuka ta ce “Wacce masifa ce wannan kika koya Dajeno? Bance miki nice Dangin uwa dana uba a gareku ba? Ban gaya miki ba Halisa?

”Hawaye na sauka a fuskar Halisa ta ce “Kiyi haƙuri Dadana ba zan sake ba, ban san mene yasa nai miki wannan tambayar ba” kasa magana Dada tai saboda hakin daya fara cin ƙarfin ta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi Danejo na ƙwala ihu ta shiga kiran sunan Hamma Yabi wanda ke garken shanu, tattara Dada Hamma Yabi yai zuwa wani ƙaramin asibiti dake gefen Rugar, suna zuwa kusan sune na farko amma abin mmki sai kwasar wasu ake ana barinsu sbd cin hancin da suke bawa Nurse’s ɗin, har lokacin tashi yai ba’a samu damar duba Dada ba a haka suka dawo gida.

READ ALSO:  Download Rayuwar Duniya Jami’a Hausa Novel Complete PDF

Yola South
Abti America

Babbar makaranta ce Wacce ta kasance Private school tun daga primary school har zuwa University makarantar dake da ita, Abti America mallakin mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na yanzu Atiku Abubakar ce. Makarantar na cikin Yola South ko ace Yola town duk ɗaya. Makaranta ce wacce sai ɗan wane da wane suke zuwanta duk wanda ka gani a ciki to ka tabbatar ubansa ya mallaki arziƙi ba dukiya ba.
Adamawa/jimeta.

Yola shi ne babban birnin jihar Adamawa. Yola South ana kiranshi da Yola town acan fadar lamiɗon Adamawa yake ma’ana gidan sarauta (LAMIƊO’S PALACE).
Yola North, jimeta kenan. Acan fadar gwamnati yake, jimeta yafi kyau haɗuwa da tsari fiye da Yola South.

 

Manyan abubuwa gaba ɗaya acan Yola North wato jimeta suke. Babu wani nisa tsakanin Yola South da Yola North/jimeta hasali ma roundabout ne ya raba tsakaninsu, akwai wani roundabout mai ƙwayoyin ƙwaryar nono da ludayi a kai muna ana kiransa da Yola roundabout, akan hanyar express yake daga shi sai wata ƙofa, to wannan ƙofar shine da zarar ka shigeta ka shiga yola kenan, sunan ƙofar “JIPPAJAM” da kuma “JAƁƁAMA” Ma’anar Jippajam shi ne Ka sauka lafiya. Wannan idan kazo fita kenan ta cikin yola zaka ganshi, idan shiga garin zakayi kuma za ka ga an rubuta Jaɓɓama ma’ana Sannu da zuwa.

Njoɓoli wani ƙauye ne sosai dake cikin ƙauyukan dake zagaye da Yola south wato yola town,ƙauyen yawancinsu fulani ne makiyaya,amma akwai manoma ma, babu nisa da cikin gari, sannan suna da tashar mota mai tafiya ƙauyen a cikin yola. Wannan kenan.

Tana tafe hannunta riƙe da sanda tana kaɗawa, a hankali bakinta ke motsawa tana karanta 1,2,3-10 cikin fillatancin karatunta bai nisa ba, babu arabi ba boko kuma ba za’a kirata da jahila ba,ita dai gata nan ne dai, ba wanka sosai ma’ana ba tsafta.
Go’a 1 D’id’i 2 Tati 3 Nay 4 juy 5 Je go’o 6 haka ta dinga maimaitawa har ta ƙarasa can nesa da gate ɗin makarantar Abti America.

 

Ajjiye ƙwayar kanta tai tare da neman waje ta zauna tana jira a tashi duk da cewa ba’a talla amma sbd ƙarancin masu sai da kindirmo yasa ake siyan nono a wajanta sosai. Tana zaune wata mota baƙa ta taho da gudu gadan-gadan zata take Danejo cikin tsoro da firgita har tana ture ƙwayar nonon Danejo ta miƙe tsaye tare da fasa ihu tana ƙanƙame jikinta idanunta rufe sbd gaba ɗaya motar kanta tayo da alama giyar motarce ta ƙwace. Motar na gab da taka Dajeno ba zato taji an saka hannu tare da yin sama da ita…

😌🫣 let’s see yadda zaku amshi labarin HALISA DAJENO wanda ya faru a gaske bawai fiction story bane.

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Idan Ba Ke Book 3

The most reliable and easiest way to obtain the complete Idan Ba Ke Book 3 to purchase them from Jambandwaec.com (JAW)Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Idan Ba Ke Book 3 inPortable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete Idan Ba Ke Book 3 booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an emailcontaining the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

 

 

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.