Download Complete Furar Danko Chapter 5 By Billyn Abdul Hausa Novel PDF:
Free pages end
………Gidane irin ginin da amma kuma babbane sosai, sannan kuma ko’ina mulmule yake da suminti. BQ ɗin yaran gidan maza itace a farkon shiga, sai daga can ciki iyayensu mata, baya can ƙarshe sashen mahaifinsu Malam Mika’il Idris Mawashi. Sam baya buƙatar shiga cikin gidan balle ya tada hankalin mahaifiyarsa, dan haka ya shige nasu sashen na samari. Da ga can ciki ɗakinsa yake, kasancewarsa tuzurun da duk ya girma sauran ƙanensa da basuyi aure ba yasa shi kadai ke rayuwa a ɗakinsa. Dan a yanzu haka akwaima ƙanan nasa da sunyi auren wasu ma matansu har sun haihu, shiko bama ya
kula ƴar kowa balle a saka ran zaiyi. Mahaifinsa yayi faɗan har ya gaji, hakama mahaifiyarsa har ƙwallar ɓacin rai take akan zaman nasa haka babu aure, babu aiki, babu wata ƙwaƙwƙwarar sana’a. Shi ba wani iskanci yake ba, ba shaye-shaye ba, vcukar magana ba. Amma sun rasa mi yake taɗe rayuwarsa haka. Duk inda ɗa nutsatstse mai nagarta yake Aliyu Hydar yakai har ma ya zarta, gashi mutum mai tausayin iyayensa da son tallafar rayuwarsu. Ga tarin ilimin addini dana zamani ALLAH ya bashi, ga addini.
Barshi dai da shegen taurin kai ga saurin fusatar tsiya da shiru-shiru, dan ko’a cikin abokai idan ba yaso ba baya fira.
Ɗakine ɗan babba mai ɗauke da kafet maroon color mai laushi, sai ƙatuwar katifa irin wadda ba’a sakawa a gadon nan. Wadrobe mai biyu sai kanta a gefenta cike da litattafan addini dama na bokon, an ɗan yi teburin karatu da kujerarsa. Ɗakin babu wani tarkace sannan fes yake ga ƙamshi kamar ba ɗakin namiji ba. Uniform ɗin da aka sharɗanta masa sakawa matsayin driver ya cire, a kujerar 2sitter dake ɗakin ƙwara ɗaya ya jefasu ya haye katifarsa da ga shi sai boxer da singlet yay kwanciyarsa yana furzar da tagwayen huci masu zafi da ɗaci, dan abinda yarinyar tai masa sam yaƙi barin ransa. Sai kuma shigar jikinta da tafi komai ƙona masa zuciya. Haka yake shi ya tsani mace haka.
Kai koda atamfa ko lass yaga mace tama ɗinkin fidda surar jikinta baƙin ciki yake ji balle wannan da gaba ɗaya ta canja suffarta daga hausawan ta koma kamar wata jinin kafirai. Tsaki yaja mai ƙarfin gaske ya juya kwanciyarsa yana mai ingije tunanin a ransa. Sai dai duk yanda yaso hakan bai yiwu ba. Al’amurin ma yaƙi barinsa yin barcin da yake buƙatar yin ko zai samu sassaucin baƙin cikin dake sukar zuciyarsa.. Da ƙyar ya samu barcin ya ɗaukesa, baima yi na minti talatin ba akai kiran sallar la’asar. tashi yay da ƙyar yana faman yamutse fuska dan a barcin ma harda mafarkinta. siririn tsaki yaja ya miƙe ya shiga toilet ɗin ɗakin nasa, a gurguje yay wanka da alwala ya fito jin har za’a shiga salla. jallabiya kawai ya saka da turare ya fita kasancewar masallacin a kusan ƙofar gidansu yake, dan baifi gida huɗu ba ne tsakaninsu….
Ana idar da salla gidan ya dawo, sai dai maimakon ɗakinsa yanzu ciki ya shiga ɓangaren iyayensu. Gida ne da tun a farkon shigowarka zaka iya fahimtar na zaman mace huɗu ne. Yaran dake kai kawo a tsakar gidan a ƙalla zasu iya kaiwa goma koma fiye da haka, wasu sanye da uniform na islamiyya wasu nacin abinci wasu kuma na ɗan kai kawon aiki. Tsit kake ji duk wani ihu da hayaniyar da gidan ya ɗauka ya tsagaita, yaran suka shiga gaidashi. Sau ɗaya ya amsa musu ya nufi ɗakin mahaifiyarsa kai tsaye. Sun san ba wasa yake da su ba dan haka babu wanda ya damu da yanayin nashi, sai dai sauri-sauri da suka shiga yi na son kowa ya kammala abinda yake ya fice islamiyya kafin ya fito ya sake ganinsu..
Daga ɓangarensa kam da mamaki mahaifiyarsa ke kallonsa daga inda take zaune. A hankali ya kai zaune a ƙasan carpet ɗin da aka saka a gaba ɗaya falon kalar blue. Basu da kuɗi, amma mahaifiyarsa mace ce mai tsananin tsafta da cikar kamala, tanada haƙuri sosai, sai dai bata son raini ko kaɗan ita, dan kana shiga sabgarta zata tabbatar maka da ita ɗin jinin zazzagawa ce.
“Ammah barka da yamma”.
Ya faɗa cikin muryarsa mai sauƙin amo da rashin son hayaniya. Maimakon amsa masa gaisuwar tambaya ta jeho masa cikin nutsuwarta da cikar kamala. Dan da yawan halayensa ya samosu da ga gareta ne, duk da ya ɗakko wasu da yawa ga mahaifinsu ma.
“Baka da lafiya ne?”.
Gajeren murmushi yayi da ɗan girgiza kansa. “Lafiya lau nake Ammah, na ɗan yi barci ne”.
“Shima wannan aikin an samu matsala kenan? Ya rabba..”
Ta ƙarashe faɗa a hankali cikin damuwa. Gaba ɗaya jikinsa sai yay sanyi, murya a sarƙe ya ce, “Amma ba matsala aka samu ba karki saka damuwa a ranki. Na dawo da wuri ne dai”.
Shiru tai tana kallonsa, sai dai har cikin ranta bata gamsu da maganar tasa ba. Ta sanshi fiye da yunwar cikinta akan zurfin ciki, sannan kuma bai iya ƙarya ba, ko yaya ya kuskure takan saurin harbosa. Tunda ya fara aikin ko ƙarfe biyar na yamma baya dawowa balle yanzu da azhar, alamuma sun nuna tun ɗazun yake a gidan tunda gashi yace har barci ma yayi.
Fitowar ƙannensa biyu ƴammata Maryam da Asma’u masu kama da shi sosai kamar mahaifiyarsu ya katse shirun falon. Ƴammata ne ƙyawawa masu tarin nutsuwa da rashin son hayaniya suma. Suma dai ɗan turus sukai na ganin nasa. Sai kuma cikin damuwa duk suka kalli mahaifiyar tasu. Ɗauke kanta tai, dan gaba ɗaya rauninsu da tashin hankali ya bayyana akan fuskokinsu.
“Yayamu ina yini”
Suka haɗa baki wajen faɗa a sanyaye. Kansa ya jinjina da amsawa cike da kulawa, duk ba wani yana wasa dasu bane ko sakewa yana ƙaunar ƙanensa, sannan suna bashi tausayi da ya gagara tsayawa akan al’amuran su na yau da kullum a matsayinsa na babba namiji a ɗakinsu tunda mahaifinsu abubuwa sun masa yawa yanzu, ga shekaru ga rashin tausayinsa da ga ƴaƴan gidan da kowa ya samu ya tsallake da ga shi sai iyalansa sai uwarsa ne..
“Babu wata damuwa ko?”.
Kai suka jinjina masa alamar babu duk da sunada buƙatu, sai dai sun san koma sun faɗa tayar masa da hankali kawai zasuyi tunda bashi da shi. Abincin da akai gidan kason ɗakinsu da aka kawo suka zuba masa, tuwon shinkafa ne da miyar ganye dai-dai ƙarfin talaka mai rufin asiri. Ya jima yana kallon tuwon bayan fitar su Asma’u har sai da Ammah tai masa magana sannan ya fara ci dan yunwa yake ji sosai, yau baya jin ko karin kummalo ma yayi, sai ruwan shayi da ya zame masa jiki ko yaushe bai rabo da shi a flaks da ya sha………..✍️
*_Humm rikitata-rikitata kenan. Masu karatu ina faɗa muku Bama a fara komai na fa, dan ko shimfiɗar labarin bamu kammalaba balle shiga cikinsa. Littafin FURAR DANƘO…!! Labarine da yazo muku da nashi salon na musamman. Babban abinda ke addabar al’ummar mu a wannan lokaci a cikin gidajenmu da ma wajen gidajenmu da rayuwar ƴaƴanmu mata da maza dama na gidan aure duk ya taɓo fiye da inda kuke zato._*
*_Ga dai Uncle Smart a matsayin drivern Lulu ƙamshi, yarinyar ƴar ƙwalisa mai tsananin wayewar rayuwa. Ƴar gata kuma ƴar hamshaƙan masu kuɗi. Uncle Smart matashin saurayi ɗan talakawa dake cikin jarabawar rayuwa kala-kala. Ya taso cikin gida mai yawan zuri’a da kowa kansa ya sani. Shin ta ina muke tunanin labarin waɗan nan mutane biyu zai kamanceceniya da juna?_*
_Minene abinda Lulu ƙamshi ke ɓoyewa na rayuwarta?_
*Minene ke faruwa a rayuwar Aliyu Hydar (Uncle Smart) da ke taɗe rayuwarsa da ga cigabansa?*
_Baku ba, hatta da ni kaina ina son sani. Dan haka ku garzayo domin kasancewa da ZAFAFA BIYAR ɗin nan naku abin alfaharinku. Ƴan amanarku, akoda yaushe labaransu masu gamsarwane a gareku._
*_Ki daure a matsayinki na mace mai kima da daraja, musulma da ta san muhimmancin hakki da son cigaban nata kasuwancin ko aiki kizo ki saya domin karanta halak ɗinki, karki bari ki ɗorama kanki nauyin da zaki iya yin kaico da sakacin ɗaukar watarana saboda ruɗi da ɗaukar komai a ba komai ba ƴar uwata._*
_ALLAH ya ƙarama rayuwa albarka, duk wanda ya tsare domin ALLAH shima ALLAH ya tsare masa kasuwancinsa ko aikinsa. Alkairin ALLAH ya kai gareku a duk inda kuke a duniya masoya. Muna sonku irin trillions ɗin nan. Duk wanda ya somu domin ALLAH shima ALLAH ya soshi haka shi da zuri’arsa baki ɗaya. ALLAH ya gafartama iyayenmu da duk al’ummar musulmi baki ɗaya😭🙏😘😘❤️❤️❤️❤️😘_.
How To Get Complete Furar Danko Chapter 5 By Billyn Abdul
The most reliable and easiest way to obtain the completeFurar Danko Chapter 5 By Billyn Abdulisto purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.
You can get the complete Furar Danko Chapter 5 By Billyn Abdul in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.
JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.
To get your own copy of the complete Furar Danko Chapter 5 By Billyn Abdul booklet, follow these simple steps:
Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.
Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.
Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.
Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.