Dowload Abban Sojoji Hausa Novel: Complete Popular Book 1, 2 3 and Reviews

Abban Sojoji is a popular Hausa novel written by Hafsat Bature, also known as Boss Lady. The novel tells an intriguing love story between two young lovers who must overcome cultural differences, family expectations, and personal struggles to be together. The novel has gained a lot of popularity in the world of Hausa literature and has become one of the most sought-after Hausa novels.

The Abban Sojoji Hausa Novel has been widely appreciated for its captivating storyline, relatable characters, and vivid descriptions of the Hausa culture. The novel explores themes such as love, sacrifice, and the challenges of intercultural relationships. The author, Hafsat Bature, has been lauded for her ability to create a compelling narrative that keeps readers engaged from start to finish.

The novel has been widely read and has received positive reviews from readers who have praised its ability to capture the essence of Hausa culture and traditions. The popularity of the novel has led to its adaptation into a movie, further cementing its place in the world of Hausa literature. Overall, Abban Sojoji is a must-read for anyone interested in Hausa literature and a testament to the power of love and sacrifice.

 

*ABBAN SOJOJI* 💖

💖💖

💖💖💖

💖💖💖💖

“`The father Of Soldiers“`

 

 

Story

&

Written

by

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Dedicated to my beloved sisters. 😍

Special thanks to Fadeela Lamido & Sadeeq Abubakar. Wannan littafin sadaukarwa ne a gare ku, jinjina ta musamman.

Proud Of My First Novel💋

Warning banyarda wani yayi amfani da wani sashe na littafina ba, kada a ta6amin komai na littafina in kuma mutun yayi shi da Ubangiji 😇

Sa’an kada ki karanta Littafin nan in har yakasance lokacin Sallah ne !!! ko kuma lokacin da iyayenki suka saki aiki ko mijinki, in har kikayi hakan wlh ke zata shafa 👌

*Page  1-2*

Hannu tasa ta toshe kunnenta saboda ta gaji da jin masifar da Buzun maigadin yake ta surfa mata, “Ke wannan idan mayya ce kika kama mutun wallahi sai an yi da kyar za a samu magani.”

“Na she miki hajiya ba ta nan kullum sai kin zo, ba ki da zuciya ne kare ya lashe ko? Yarinya karama da ke sai taurin kan tsiya, da wasu kwala-kwalan idonki kamar na kwarton mazuru, kina kallon mutane da su ba kunya ko? Kai ga d’an iska!”

Dagowa ta yi a hankali tana kallon sa jin cin mutuncin da yake yi mata , idonta ne suka ciko taf da kwalla, kananun labbanta suka soma kyarma, tuni yanayin fuskarta ya canza.

Duk a tunaninsa yarinyar za ta mayar masa da martani saboda ya san yaran zamanin nan ba ka taba su su yi maka shiru, zuba mata ido ya yi kuri yana kallon ta. Gani ya yi tana ja da baya a tunaninsa tafiya za ta yi tabar wurin amma sai ta samu wuri a jikin bangon gidan ta tsugunna tare da kifa kanta a saman guiwowinta sannan ta soma rera kuka mai tsuma zuciya.

Tsayawa ya yi yana kallon ta, da alamun nadama a tattare da shi, har cikin zuciyarsa yake jin bai kyauta mata ba, yana Musulmi da shi ya gaza fahimtar yar karamar yarinyar da ke zarya kullum a bakin gate din gidan, bai taba tambayar kansa dalilin da yasa yarinyar take zuwa wurin ba. Ba irin korar karen da bai yi mata ba amma hakan bai sa gobe taki dawowa ba.

Jiki a sanyaye ya matsa inda take ya tsugunna a gabanta ya ce, “Kai kukan ya isa haka! Dago ka gaya mini mene ke damun ka me yasa kake zuwa kullum kana neman hajiya?”

Dagowa ta yi fuskar nan ta yi jaga-jaga da hawaye ga majina cikin shesshekar kuka ta ce, “Ina zuwa neman hajiya ne saboda na ji an ce tana taimakon ‘yammata ta sama masu aikatau ana biyan su kudi.”

Jim ya yi yana kallon ta kafin ya ce, “Kai ko mai yasa kake neman aiki karamin yaro da kai gidanku ba manya ne?”

Girgiza kai ta yi, “A’a babu kowa, ba mu da n ni da ‘yan uwana ne kuma ba su da lafiya an kwantar da su a asibiti, kuna likita ya ce aiki za a yi musu, ba ni da kudin aikin saboda suna dayawa, shi ne nake so na samu aikin da zan yi ina samun kudin da zan tara a ayi musu aiki kada su mutu su bar ni ni kadai!” Karasa maganar ta yi tare da mayar da kanta kasa tana kuka.

Yanzu ya gane dalilin da yasa yarinyar ta nace sai taga hajiyar, a cikin zuciyarsa ya ce, “Baiwar Allah tana shikin damuwa karama da ita. Oh amma yana da tunani mai kyau!”

Riko hannunta ya yi tare da cewa, “Share hawayen ya isa haka, zan taimaka maka ka ga Hajiya, taso mu je ka zauna saman benchi ka ji.”

Mike wa ta yi ta bisa, a tare suka zauna saman bencin, jim suka yi na d’an wani lokaci kafin ya ce, “Ka yi shiru kaji ka daina kuka Allah shi ne gatan bawanSa ko mutun bai da kowa indai ya yi imani da Allah shi ne zai zama gatansa, ka shi gaba da addu’a ‘yan uwanka za su samu sauki har ku yi wasa da su.”

Murmushi ta yi saboda ta ji dadin maganarsa, hannu ya kai ya dauko ruwan bunun da yake dafawa a saman ‘yar butarsa, dama akwai karamin kofi guda biyu da yake amfani da su wurin zuba shayin.

Lekensa ta dinga yi tana kallon ‘yar butar karfen da yake dafa shayin da ita, ta burge ta musamman abin da ke cikinta. Kofin ya dauko ya tsiyaya mata  a ciki, mika mata ya yi. Hannu biyu ta sa ta karba don rabon ta da ta ci wani abu a cikin ta tun jiya. Sannan shi ma ya zuba wa kansa a d’ayan kofin yana kurba yana ba ta labarin gizo da koki.

Sam ba ta gane me yake cewa, d’an ruwan bunun da ya ba ta ya dauke mata hankali saboda dadinsa musamman daya sanya sugar a ciki, a hankali take kurbarsa, kusan so uku tana shanyewa yana kara mata, a karshe ya ce “Aradun Allah shegen ci ne da kai ga shi harka shanye mini ruwan bununa, idan hajiya ta samo maka aiki ka fara yi sai ka biya kudin shayina.”

Murmushi ta saki tana sauraron shi tana mamakin yadda yake suffanta ta da namiji, ga shi shi dai ba makaho ba sarai ya gan ta da kayan mata a jikinta,

har marece ya yi hajiya ba ta dawo ba, da lokacin sallar Azahar ya yi da kansa ya bude musu kofar dake a jikin gate din suka shiga. Ruwa ya debo musu a buta, suka yi alwala tare sannan ya shimfida musu tabarma, shi ya ja su sallar yana gaba tana daga bayansa.

Bayan sun gama , suka ci gaba da zama a saman sallayar yana jan cazbi a hannunsa ita kuma ta shiga tunanin duniya, a haka har La’asar ta yi suka sake kabbara sallar, tun kafin su sallame yake jin karar motar hajiya alamar ta iso.

 

Dadi har cikin ranta yau dai Allah ya yi za ta gana da hajiyar nan, yana sallame sallar da sauri ya tashi ya bude mata kofa, ta shigo da dankareriyar motarta, wucewa ta yi da motar zuwa wajen ajiya. Zuge kofar ya yi sannan ya bi motar hajiyar a baya yana mata kirari kamar yadda ya saba.

Farinciki ya sa ta kasa rufe bakinta sai faman murmushi take yi, ba ta tashi daga samman sallayar ba, zama ta yi tana jiran maigadin ya yi wa hajiyar maganarta. Bude mata motar ya yi ta fito, ma sha Allah irin matan nan ne masu jiki ‘yar dumurmur da ita, ta ji hutu fara ce tas amma da alama tana karawa da man bleaching, jikinta na sanye da tsadadden leshi shudi wanda aka yiwa ado da stones, ba karamin kyau ya yi mata ba. Ta kashe daurin kallabinta, hannunta na sanye da diamond rings, haka sarkar wuyanta ta diamond ce, kwalliya ce sama-sama a fuskarta tana da dara-daran idanu ga hanci dogo, tubarkalla, sai jan-baki da ta shafa ja ne.

Cikin girmamawa ya ce, “Barka da isowa hajjaju makkatu!”

Ya mutsa fuska ta yi da alamun gajiya a tare da ita ta ce, “Yawwa Aku sarkin dumi akwai wanda ya zo ba na nan?” Ta yi maganar ne a yayin da take bude kofar motar ta baya, saboda ba ita kadai ta zo ba akwai ‘yammatan da ta zo da su daga kyauye.

Maigadin ya amsa mata da cewa “E mutane sun zo sosai amma duk ban rike shunansu ba na dai ce musu ba ki nan kin yi tafiya, sai dai akwai yaro d’aya da ya zo neman ki kullum shai ya zo yau dai na ce mashi ya jira ki dawo.”

D’aga idonta ta yi tana hangen ‘yar yarinyar da ke sanye da hijab saman sallaya, mayar da idonta ta yi kan ‘yammatan da ke zaune cikin motar, ganin ta bude musu motar amma sun ki fitowa, tsaki ta ja tare da cewa, “Kwana za ku yi ne a cikin motar?”

Washe baki su ka yi wata mai surutu a cikinsu ta ce, “Hajiya wallahi dadi motar nan ga wani sanyi da ke ratsa zuciyata kamar kada na fito.”

Girgiza kai hajiyar ta yi tare da sakin guntun murmushi ta ce, “Ai irin wannan sanyin da kuke sha na A.C ne kuma in mun shiga ciki ma akwai A.C ko ina.”

Cike da jin dadi suka fito daga motar su biyar ne, kai ka ce wadanda aka kwato ne daga bakin kura kayansu sun yi uban squeezing, ga shi riga daban zane daban dankwali daban, takalman kafafuwansu wari da wari ne, ga wata irin kwalliya da suka dambara a fuskarsu, janbaki ya sauka daga saman labbansu har kumatunsu, kamar wasu mayu. Ga black point din da suka diddiga a hancinsu har izuwa goshinsu, sai faman soshe-soshen kai suke.

A haka take dauko su daga kauyen kayau ta gyara su ta sama masu gidanje aiki, a nan take samun kasonta ita ma.

Kallon buzun ta yi ta ce “Ka shigo mini da yarinyar.”

Sannan ta kalli ‘yammatan ta ce “Mu shiga ciki amma kusa ni duk wacce ta yi mini hauka kauyensu zan mayar da ita ta je can ta ci gaba da tallar fura a bakin kasuwa.”

Cikin falo ta shiga da su a daidai lokacin ita ma yarinyar ta biyo su, nan fa suka fara kalle-kalle ganin yadda wurin ya hadu, har kokawa suke yi wurin yunkurin hawa saman lumbutsa-lumtsan kujerun da ke a ciki, dakatar da su ta yi ta hanyar yi musu tsawa, “Kul! Kada wacce ta hau mini saman kujeruna, ga carpet nan shimfide ku zauna, haba ku rinka abu irin na mata mana.”

Nutsuwa suka yi kowacce ta samu wuri ta zauna, ita da ma ba iri su ba ce da wayewarta wuri ta samu ta zauna ita kadai, yayin da su kuma suka cunkushe wuri daya kamar kifin gwangwani. Shiga ciki hajiyar ta yi tana kwalama mai aikin ta kira, “Larai, larai! Ina kika shiga haka gida sai ka ce ba kowa?” Karasowa ta yi tana hamma alamun daga barci ta tashi.

“Sannu da dawowa hajiya, wallahi barci ne ya yi awon gaba da ni da ma na sha maganin mura saboda ta takura mini.”

Tabe baki ta yi ta ce, “Ni fa ban yarda da ke kullum shan maganin mura anya ba shaye-shaye kika fara ba?” Cikin zolaya ta yi maganar tana kallon ta,

Dariya Larai ta yi ta ce, “Haba hajiya Allah ya tsare ni dayin shaye-shaye tsofai-tsofai da ni.”

Murmushi hajajju ta yi “Ya yi kyau! Yanzu dai akwai abinci gidan na zo da yara ne daga kauye.”

Girgiza kai larai ta yi, “A’a hajiya sam ban yi tunanin yau za ki dawo ba ai, da na girka muku abinci.”

A jiyar zuciya ta saki kafin ta ce, “Koma mene dai laifina ne da ban sanar da ke cewa yau zan dawo ba. Yanzu dai na san muna da bread, ko shayi ne ki hada musu da indomie.”

Amsawa ta yi da, “To hajiya!” sannan ta juya ta nufi hanyar kicin din.

 

Hajiya ta nufi dakinta saboda tana bukatar ta d’an watsa ruwa ta canza kayan jikinta.

Rokon Allah yarinyar take yi a cikin zuciyarta, Allah Ya sa ta samu wannan aikin ko ta samu ta taimaki ‘yan uwanta wadanda suke cikin wani mawuciyan hali, muryar d’aya daga cikin ‘yammatan nan ta jiyo tana mata magana, “Ke kin iya kunna kallo ki kunna mana mu kalla.”

Girgiza kai tayi alamar a’a, ba wai don ba ta iya ba sai don tsoron kada hajajju ta yi mata fada har ma ta kore ta ta hana ta samun aikin. Tana jin su suna cewa, “Karyar banza babu wani ta iya kawai ba ta kunna mana ne ‘yar bakin ciki.”

Dagowa ta yi ta kalle su harara ta watsa musu ta ce, “E na iya ba zan kunna ba ne ba ku da hannuwa ne ku?” Tsit suka yi ganin yadda ta daure musu fuska sun yi tunanin ‘yar shiru-shiru ce, ashe ita ma ta iya fada. Fitowa hajjaju ta yi jikinta sanye da kayan barci, riga da wando ruwan madara, ta daure gashin kanta da ribbom, hannunta rike da waya kirar Infinix Hot 10, suna ganin ta suka gyara zamansu cikin natsuwa.

Wuri ta samu ta zauna a saman 3 seater, yadda za ta ji dadin yi musu magana, yarinyar na jingine jikin 2 seater wadda ke bangaren dama su kuma suna duban ta ta sashen hagu.

A nutse ta soma magana, “Ku na riga da na yi muku bayanin komai ko?” Da’ga kai suka yi alamar e.

Ta ci gaba da cewa, “Yanzu abin da ya rage mini shi ne na koyo muku yadda za ku gudanar da aikin naku don ba zai yi yu ku je gidan mutane a matsayin ‘yan aiki ba, a haka kaca-kaca da ku ba tsafta ba. Dole ne kusan yadda za ku tsaftace kanku, da tsaftar muhalli da kuma yadda za ku tsaftace abincin da za ku girka. Kuna bukatar sanin abubuwa sosai daga wajena, kuma insha Allah zan nusar da ku.”

Ta mayar da idonta kan yarinyar ta ce “Yammata kin yi shiru ga shi ni ban san ki ba amma yanzu ina son na san me yasa kike nema na ne?”

Bude baki ta yi za ta fara magana amma ganin yadda ‘yammatan kauyen nan suka zuba mata ido kamar zomaye, hakan ya sa ta kakare ta kama in ina.

Muryar hajjaju ce ta sa su janye idonsu akanta, “Ku fa matsalarku ke nan sai shegen kallo salon gulma ko?” Sunkuyar da kansu kasa suka yi amma kunnuwansu na bude don su ji me za ta ce?

Cikin sanyin murya ta soma magana, “Da ma na ji an ce kina taimakawa ki sama wa yara aikatau shi ne na zo ni ma ki taimaka ki samo mini don Allah!”

Dafe kai hajju ta yi da hannunta na hagu ta ce “Kash! Da na san wannan ya kawo ki da tun dazu na ce ki koma gida saboda yanzu babu wadanda suka yi mini magana akan na samo musu ‘yar aiki, wad’annan ‘yammatan da kika gani su ne kawai suka rage na mika su ga wadanda na yiwa alkawarin zan sama musu ‘yan aiki amma yanzu babu wani da ya yi mini magana. Ki yi hakuri ‘yata!”

Tamkar an d’aga guduma an buga mata a kai haka ta ji, jikinta ya yi mugun sanyi tuni kwalla ta ciko mata a idonta, saboda ba karamin wahala tasha ba, kusan kullum tana fama zaryar zuwa gidan matar neman aiki, tunanowa da ta yi da halin da ‘yan uwanta ke ciki ne ya sa ta ji ba za ta iya hakura ba komai zai faru sai dai ya faru, amma ba inda za ta je sai ta samu aikin da za ta samu kudi, saboda ta san ba wanda zai taimake ta ya ba ta kudi haka nan don Allah face ya nemi wani abin daga gare ta.

Tamkar za ta fashe da kuka ta ce, “Don Allah ki taimaki wallahi ko wane irin aiki ne zan iya yin sa. Ki taimaka mini ‘yan uwata na kwance asibiti  ba ta da lafiya kuma aiki za a yi mata, kudin da doctor ya fada ba mu da su kuma ba mu da wanda zai taimaka mana ni ce kawai nake fafutuka akan yadda zan samu na biya.”

 

Ganin yadda yarinyar ta bi tana rokon ta cikin lallami ya sa ta ji tausayin ta ya shiga ranta, “Ya isa haka, share hawayenki. Nawa likitan ya ce kudin aikin nata?”

“Dubu dari takwas ne.” Ta ba ta amsa tana kokarin goge hawayenta. Jinjina kai hajjaju ta yi jin kudin, “Da a ce ina da su da na taimaka da wani abu  amma halin da muke ciki yanzu komai tsada hakan yasa kudi ba sa jimawa a wurina. Amma yanzu abin da nake so na sani ina ne gidanku saboda dare ya yi sosai, na mayar dake gid, idan kuma za ki tsaya nan is shike nan in yaso gobe sai ki koma ko?”

Cikin sauri ta ce “Zan tsaya a nan, ba kowa gidan suna asibiti kuma na yi sallama dabsu babzan sake komawa ba har saibna fara biyan kudin aikin, babzan iya jure ganin su cikin mawuyacin hali ba!”

Hajajju ta ce “To shike nan amma gobe zan bincika kuma za mu je asibitin tare saboda ba na daukar yaro ba tare da iyayensa ko wani nasa ya sani ba!”

Yarinyar ta amsa da, “To!”

Larai ce ta shigo dauke da faranti, ta jera sinkin bread guda 3, sai jug mai dauke da tea da kananan kofuna, a jiye masu tayi sannan ta koma ta dauke sauran abin da ta hada musu a kicin.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

💖💖💖💖

💖💖💖

💖💖

💖 *ABBAN SOJOJI* 💖

💖💖

💖💖💖

💖💖💖💖

“`The father Of Soldiers“`

 

Story

&

Written

by

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Dedicated to my beloved sisters. 😍

Page 3-4

Tun da y’ammatan nan suka ga bread suka gaza samun natsuw, sai kokarin zura hannu suke su dauka, ganin haka yasa ta taso da kanta ta rarraba musu ta bawa kowa nasa, dawowa larai tayi dauke da  karamin tray wanda ta baza musu taliyan a ciki ta ajiye masu,  zama sukayi suna ta aikin ci, ita dai a hankali take ci tana kallonsu hannu baka hannu kurya suke cunkusa wa a bakin, bakomai yazo mata a ranta ba face y’an uwanta, in ta tuna irin wannan yanayin sai taji komai ya fita ranta.

Bayan sun kammala ci , hajjaju ta kai isu zuwa bedroom din da ta ware domin irinsu in ta dauko su anan suke kwana sannan ta yi masu sallama ta fice, tana fita y’an matan kauyen nan suka haye saman bed din dake ciki kuma shi kadai ne, bin su da kallo tayi ganin yadda suka wawware kafafunsu saboda kar tasamu wuri tace zata hau.

Murmushi tasaki, “Allah sarki rayuwa ni ina ne bazan iya kwana ba, bed is ur problem, Sisters dina sune damuwata,

Cire  hijab din dake jikinta tayi, wardrobe din dake manne a bango, ta bude babu wasu kayan kirki a ciki, zannuwan atamfa ne kawai, saka hijab din tayi ciki ta rufe,

toilet din dake ciki ta shiga, komai na ciki a tsaftace yake, fari kal! Gaban mirror ta karasa tana kallon fine face dinta, fanfo ta kunna ta tarba hannuwanta tana wanke fuskanta, bayan ta gama tasa hannu ta cire head din dake kanta, ta yi holding dinsa a hannunta tana kallon doguwar kitson kalabar da akayi mata guda biyu ta zubo tun daga head dinta har zuwa west dinta, tana da Yalwatacciyar sumar kai dark brown colour very smooth ga kwantaccen saken gefen fuska.

Fitowa ta yi daga toilet din, samunsu tayi sai minshari suke ja tamkar raguna, wardrobe din ta sake bude wa daya daga cikin zannuwan da ta gani ciki ta dauko, ta shimfida a kasa, ta kwanta

Washe gari tunda sassafe suka fita, hajajju ce ke driving yayin da yarinyar take a gefenta , sai kalle kallen hanya take ta glass din motor, hajajju ta ce “Har yanzu baki fadamun sunanki ba ! da age dinki yakamata nasani ko”? tayi maganar ne a lokacin da take kokarin juya sitiyarin motar wurin canza hanya tabi titin da zai kai ka har izuwa asibitin.

Murmushi yarinyar tasaki tare da cewa “Sunana SEHRISH amma Oumman mu tana ce mun RISHI , shekarata 17 cif ,” jinjina kai hajajju tayi tace “Wow nice name and it really deserves , ” cike da jin dadi Sehrish tace “thanks”  har suka isa asibitin basu kara magana ,

Sehrish tayi ma hajjaju jagora har izuwa ICU intensive care unit , inda aka kwantar da sisters din nata, lokacin da suka shiga ciki, da gugu wata kyakkyawar yar matashiya ta taso ta rungume sehrish, tsananin mamaki yasa hajajju sakin baki, sai ta dinga ganin tamkar mafarki take yi, tun da Allah ya halicce ta bata taba ganin yara masu shegen kama irin wadannan ba basu da wani banbanci ko miskala zarratin komai nasu iri daya sak , lokaci guda ta rikice takasa gane wacece ma suka zo da ita, wacece sehrish din don ta saje da dayar, hajjaju bata gama mamaki ba sai da taga dayar wadda take kwance saman gadon marasa lafiya ansa mata Oxygen dakyar take jan numfashi gwanin ban tausayi , nan takara rikicewa saboda itama wacce take kwancen Sak kamaninsu ba banbanci hakan na nufi su y’an uku ne kenan.

Kankame ta tayi tana kuka , itama sehrish din kukan takeyi hannunta tasa tana d’an bubbuga bayanta tace “Jahad ki daina kuka hankalina yana kara tashi komai zai tafi dai dai insha Allah, janye jikinta tayi daga nata tace “ina kuka ne ba don kai na ba sai don Husanna dr yace in ba mu fara biyan kudi an mata aiki ba , mutuwa zatayi kuma ynx haka kudin gado ya kare sallamar mu zasuyi ko kudin magani babu ,”  hankalin Sehrish ba karamin tashi yayi ba,

Hajajju dake tsaye tana kallonsu, jikinta yayi mugun sanyi saboda tsananin tausayi, ita kanta wadda sehrish takira da Jahad akwai wound a goshinta, anyi mata dressing da bandage duk jini a jikin sa , hannunta ma akwai kanula alamun anyi mata karin wani abu jini ko ruwa , a kagare hajajju take da taji labarin wadannan y’an ukun lallai bakaramar wahalar rayuwa suka sha ba.

Muryar Sehrish ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga “Jahad ga hajajju ku gaisa kuma kiyi mata godiya sbd  itace zata sama mun aikin da zan fara yi nasamu kudi nabiya ayi maku aiki,” matsawa tayi gaban hajjaju tana share hawayenta cikin girmamawa tace” ina kwana hajiya ,” murmushi hajajju tasaki tare da dafa kadarta tace “lafiya lou ya jikin naku “? Jahad tace “Alhamdllh ni da sauki husanna ce abun sai kara gaba yake yi don dr yace koda an mata aikin ba lallai ta dawo yadda ake so ba….”

Kuka ne yaci karfinta har takasa karasa maganar , rungumo ta hajjaju tayi a jikinta tana lallashinta ” am sorry my daughter stop crying insha Allah everything will be ok , cikin kuka ta amsa da “zandaina mungde ssai ,” karasawa Sehrish tayi wurin husanna dake kwance rai hannun Allah , gefen gadon ta zauna tana kallonta idonta cike tab da kwalla tace “Allah ya baki lafiya yar uwata ina jin duk wani irin radadi da kike ji a zuciyarki wanda yayi sanadiyar shigarmu cikin wannan halin bazai taba gamawa da duniya lafiya ba Allah ya isa tsakanin mu dashi mugu azzalumi macuci …” a karshe ta fashe da kuka ta kwantar da kanta a saman jikinta , har cikin ranta take kukan.

Tsohuwar dake kula dasu ce ta shigo cikin sauri hannunta rike da magunguna da takarbo masu , a nan tasamu hajjaju tsaye ita da jahad tana lallashin ta , jin alamar shigowarta yasa suka jiyo suna kallon , cikin sakin fuska tace “Sannun da zuwa hajjaju ke ce da kanki ,” murmushi hajjaju tasaki dama sun son juna da alama , ” kwarai kuwa nice gwaggo dama ke ce ke rike da yarannan amma ni ban taba ganinsu ba gsky ,” murmushi gwaggo tayi tace “bakya leko mune shiyasa amma sun jima wuri na ni nake kula dasu ,”  jinjina kai hajjaju tayi tace “hakane amma gwaggo jikokinki ne su”? Goggo ta girgiza kai tare da cewa “a’a Allah ne ya hadani dasu nima labari ne mai tsawo , amma ynx bani da kwanciyar hankalin da zan zauna na baki shi , ki bari saina samu natsu,” tana gama fadan hakan ta mika ma Jahad magungunan “karbi nan naki ne dakyar nasamu kudi na siyo su,” godiya tayi mata ta karba , a tare suka taka izuwa inda sehrish ke kwance jikin Husanna , cike da nuna tsantsar tausayi hajjaju tace “Allah ya bata lafiya Allah sarki mutum baya sanin halin da duniya take ciki wani sa’in sai ziyarci asibiti nan zai ga marasa lafiya iri iri gwanin bantausayi hakika na tausayawa wannan yarinyar tana cikin hali Allah ya kawo musu sauki da duk marasa lafiyan dake fama da ciwo ,” amsawa sukayi da amin , har time din sehrish bata dago da kanta ba , ita kadai tasan yadda take ji aranta.

Hajjaju ta mayar da idonta kan Gwaggo tace “idan ba damuwa muje ki raka ni wurin likitan zanyi magana dashi ,”

fita sukayi a tare , wuri Jahad tasamu ta zauna a chair din dake facing din gadon mara lafiyar, kallonsu takeyi su biyun tana kara jin kaunar y’an uwan nata , taji dadin zuwan rishi har cikin ranta , jajircewarta akan ganin sun samu rayuwar mai kyau yana kara mata ninkin son yar uwarta ta, tazama tamkar uwa agare su , alhalin ita age dinsu daya duk da tare suka zo duniya amma sun tsere wa rishi da mintina a wurin haihuwa ,  tunani iri iri ke zo mata a ranta runtse idonta tayi hawaye na kwaranyo wa daga idonta

Gabad’ayansu sun shiga cikin yanayi , duk sunyi zurfin tunani , numfashinta suka soma ji da karfi da karfi wani irin sauti mai matukar razanarwa , a firgice sehrish ta dago da kanta cikin rudu ta furta “Subhanallah! jahad husanna ta cire oxygen da aka samata,” a rude jahad ta matso kusa da su hannu tasa ta tana kokarin mayar mata roban oxygen din , buge mata hannu tayi tana wani irin gurnani ga zufa sai ke to mata take yi ga wani irin tari da take yi cikin kuka take ambaton “Seh..seh..sehrish ,”

Dakyar sound din ke fita , hakan ya tambatar masu da cewa so take tayi ma Sehrish magana amma takasa , matsawa sehrish tayi kusa da ita tare da sa hannu tana shafa mata gefen fuskarta cikin kuka tace “pls husanna kiyi hkr kinji Allah zai baki lafiya , nasan mai kike ji a zuciyarki, zanyi kokari koda zan rasa raina ne wurin ganin kin samu lfy , wlh sai inda karfina ya kare , ina sonki sosai my sister,” gaba dayansu kuka sukeyi , mayar mata da roban oxygen din Husanna tayi , bin ta su kayi da kallo ganin tana kokari kakaro murmushi a fuskarta , wani sabon kukan suka sake fashe wa dashi.

“Yar’uwata kada ki tafi kibarni ni nafiso na mutu a gabanku dan Allah kada ki tafi ,” lokacin da sehrish ta tuna da wannan kalami na Husanna sai jikinta ya kara mutuwa lukus , kamar ba kasusuwa a jikinta, zamewa tayi ta zauna kasan tiles din tare da jingina kanta gefen gadon , wasu abubuwa ta dinga tunawa arayuwarsu wanda in har taci gaba da tuna su to tabbas zuciyata zata buga ne!  komai ya dawo masu sabo fal , komawa Jahad tayi ta zauna tana shesshekar kuka hada majina a hancinta ,

Hannun husanna taji cikin nata , dayake ta aza hannun nata a saman bed din, ta rike shi gam cikin nata , dagowa sehrish tayi da fuskanta wadda tayi jawur , ga idonta sun kada , fuskarta tayi kwaba kwaba cikin kasalalliyar murya tace “Husanna ki daina zubar da hwayenki nasani abun da ciwo , zafinsa yakai kunar wuta amma ki daure pls , ba irin whalar da bansha ba wurin ganin nasamu kudi an miki aikin nan ke da jahad especially ke , kai karshe ma an kokarin bada kaina nayi amma dana tuna abunda mama ta fada saina gaza , duk da haka ban hkr ba na soma kokarin samun wanda zai siye ni yabani kudi kawai na kawo muku ni natafi amma saina tuna cewa in na tafi wazai kula daku ? duk da nasan akwai Allah shine gatan kowane bawansa …’ muryarta ce tashaqe ta gaza idasa maganartata saboda kululun bakin ciki daya tokare mata makoshinta .

Jahad da ke sauraron maganar yar uwarta su sai taji wani sabon kukan ya balle mata,  domin duk wannan gwagwarmayar da Sehrish tayi sam basu sani ba a boye tayi kayanta.

Sun sha kuka kamar ba gobe nima na tayasu kukan duk da bansan takaimaiman tarihin rayuwarsu ba da kuma dalilin kukan nasu.

A haka goggo da hajjaju suka same su gwanin ban tausayi , wayar hajjaju dake cikin yar purse dinta sai ringing take yi don haka tace ma serish ta taso su tafi , cikin kuka ta tashi a hankali take tafiya tana waiwayansu , goggo tace ” kada ki damu rishi hajjaju ta biya mana kudin gadon kuma tace zata samu koda bashi ne a fara biyan kudin aikin inyaso daga baya kin fara aikin kin samu sai ki biya,”

Ba karamin dadi sehrish taji ba , haka jahad ma godiya suka shiga yi mata , a karshe tayi masu sallama suka tafi ,

Har a cikin motan kuka takeyi dakyar hajjaju ta lallashe ta tayi shiru….

Time din da suka dawo , larai  na kitchen ita da y’an matan kauyen nan tana koya masu wasu abubuwan daya kamata su sani.

A falon suka zauna gaba daya jikinsu a sanyaye, sehrish na zaune kasan carpet jingine da 2 seater , tana sauraron abunda hajjaju zata ce ,

magana ta soma mata “Sehrish ni yanzu bansan ya zanyi dake ba, game da aikin nan m, gashi ni already ina da y’ar aiki kuma gsky ko da ace ban da ita, ba zan iya daukarki sbd kina bukatar kudi masu yawa ni kuma iya salary din da nake biyan larai 10k ne.”

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️

───────────────────────

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 5-6

Jin wannan bayanin daga bakin hajajju yasa jikin Sehrish yin sanyi , bata ce mata komai ba sai ma ta ci gaba da wasa da yatsun hannunta. Ci gaba da magana hajajju tayi “abunda za’ae tunda dai naga sisters din naki kuma munyi magana da gwaggo da take kula daku , ynx ki koma ki ci gaba da kula dasu saboda suna bukatarki kafin Allah yasa asamu aikin ,”

Kamar an dasa ta haka tazauna idonta suka ciko da kwalla, kiris take jira ta fashe da kuka , dama bata jima da gama wancan kukan ba

Wayar dake hannun hajajju ce ta soma ringing , picking tayi tare da karawa a kunnan ta tana fadin ” Manyan manyan gari ! Abban sojoji ashe kana nan ba’a neman mu , koda yake dama ku hamshakan masu kudinnan ganin ku sai an cike file.”

Natsuwa sehrish tayi tana sauraranta , ta lura da yadda hajjaju ke washe baki da alama koma wanene take wayan dashi Babban mutum ne ,

tuna damuwar da take ciki yasa ta daina sauraron wayar tasu ta shiga tunani kala kala a cikin zuciyarta , har hajjajun ta kammala wayar bata sani ba sai da taji tace “Ga samu ga rashi !!” dagowa tayi da idonta tayi tana kallon , hannu hajjaju tasa ta dafe kanta alamar takaici.

Sehrish tace “Hajiya meya faru?” Hajajju tace “Aiki ya samu mai tsoka , jin hka yasa sehrish ta soma murmushi “amma sai dai kash Namiji suke so mai aiki ba mace ce ba !” lokacin da hajajju ta idasa maganar tuni sehrish ta gumtse fuska hankalinta ya tashi.

Hajjaju ta ci gaba da cewa “ina tayaki bakin ciki gsky, sbd kinga mutumin nan daya kira ni ba karamin mai arziki bane , cos they can pay u 50k as your salary after that zasu dauki dukkan responsibilities din ! Ci  da shan ki wurin kwana lafiyayye sannan har school zasu iya saka ki ga sutura ya kike gani “?

Takaici ya hana tace komai ga samu ga rashi , ji take kamar ta cire takalmanta ta watsa da gudu saman titi kota rage radadin da take ji a zuciyanta  ,

“Sehrish kinyi shiru baki ce komai ba “? ta jima ba tare da ta ce wani abu ba sai da tayi zurfin tunani kafin tace “ZanJe ! Zan yi aikin a matsayin NAMIJIN akan y’an uwana babu abunda bazan iya yi ba don nayi basaja a matsayin namiji wannan abune mai sauki a wurina ,”

In serious matter take mgnan ba tare da jin wani dar a zciyarta ba dagaske take dai , murmushi hajjaju tasaki don ba karamin burgeta tayi ba saboda tana da confidence akan komai da take so , ” hmmm sehrish kenan how can u change ur creator frm a girl to a boy i dont think u can act like a male zasu gane ki ne , ”

Matsawa tayi kusa da hajiyar tare da rike kafarta tace “Don Allah hajiya ki taimake ni wlh zan iya , indai za’a samu makeup artist din da zai tsara ni ya mayar dani kamar namiji this is a simple thing , kawai amincewarki nake bukata,”

hannu hajjaju tasa ta cirewa Sehrish hannunta data rike mata leg dinta dashi sannan tace “Babbar magana ! tun da nake bantaba yin wannan kasadar ba , natura house maid mace a matsayin namiji , sannan wannan mutumin da kika ji ina magana akan sa wato Abban Sojoji , y’ay’ansa maza goma sha takwas kuma dukkansu sojoji ne masu rike da manyan mukamai , dalilin dayasa yace namiji suke so a matsayin d’an aiki saboda ba yadda za’ai mace ta iya , bai ma dace ba , balle ma yaransa da kwata kwata basa da sauki , zafin rai ga ji da isa , ”

Kamar zata yi kuka ji take in har hajajju bata amince mata ba zata iya rasa ranta , cikin kasalalliyar murya tace “Hajiya ki amince mun kawai ae ni nace zan iya wlh idan baki amince ba shinkafar bera zanci kawai na mutu kowa ya huta don bazansu naga mutuwar y’an uwana ba , ”  zaro ido hajajju tayi jin ta anbaci zata je taci shinkafr bera , kuma dagaske take ba alamar wasa a mgnrta ,

ruko hannunta tayi saboda harta mike zumbur zata figi hanya , “Meya yi zafi haka dawo ki zauna kinji , ni bazanso nayi sanadiyar mutuwar wannan innocent face din ba ,” komawa tayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya ,

Shiru suka yi na wani lokaci daga ita har hajajju , jin shirun yayi yawa yasa tace “Hajiya baki ce komai ba am so eargerly to hear frm u ,”  ta karasa maganan tana kallon ta ,

Wan nan shirun da hajajju tayi sake sake takeyi a cikin zuciyarta “taya zan kai yarinyar nan gidan soldiers a matsayin namiji ! duk ranar da asiri mun  ya tonu daga ni har ita kashin mu ya bushe ,  maganar da sehrish tayi ce ta dawo da ita ,  ” Sehrish i dont know what to do am just comfused ina tsoron hakan fa ,”

“Nima ina goyon bayan yarinyar nan” larai ce tayi maganar shigowarta kenan taji suna tattauna wa , bin ta su kayi da kallo , wuri ta samu ta zauna kafin taci gaba da magana “Wurin samun biyan bukata rai ba abakin komai ya ke ba , tun da har tace zata iya kawai ki amince mata ! saboda ni na taba kallon wani korean film irin haka actress din ciki ta yi shigar namiji ba tare da wani ya gane ta ba kuma tacimma nasara ,”  jinjina kai hajajju tayi tare da watsa hannayen ta tace “Shikenan Finally i agree tunda har larai ta Jefa miki kuri’a kun rinjaye ni ,” dariya sukayi su duka ba karamin dadi sehrish taji ba , ynx hajajju ta yarje mata sauran shirin yarda abun zai kasance ,

Mayar da idon ta kan larai tayi tace “To ynx ta ina zamu fara “? Larai tace “ae magana ta kare kawai mu da muke da Professional makeup artist a hannu ko kin manta da Mariiiya ? murmushi hajajju tasaki tare da cewa ” ae Mareeya karshe ce ! Indai wurin canzawa mutun kamanni ne insha Allah gobe zan yi inviting din ta kuma a gobe za’a kammala komai don ya ce mun Jibi suke son mai aikin ta je ,”

Har larai ta bude baki zatayi magana ta jiyo muryar yaran nan dake cikin Kitchen wadanda take koyama aiki , suna kokoyi muryar d’aya daga cikinsu taji tana cewa “Aunty larai gatanan xata wanke gas cooker da ruwa ,” da sauri ta mike ta nufi hanyar kitchen din tana cewa “Allah ya wadaran naka ya lalace har waning nayi muku kada ku taba komai amma saboda kan kifi gare ku baku gane komai salon kujama mutane ko !?

Hajajju tace “ke ma da laifinki akan me zaki baro min su a kitchen salon suyi mun barna ,”  mayar da idon ta tayi kan Sehrish “ki je ki huta time din sallah ma yayi nima bari na tashi ,”

Ta shi tayi ta shiga ciki , wanka tayi ta dauro alwala , ta fito ta shimfida prayer mat tayi sallah , kamar yarda ta sama kullum sai ta daga hannayenta tayi sama da 30mins tana rokon Allah cikin harshen larabci take jero addu’oin ta da bukatanta da damuwarta tana neman Allah ya yaye mata su ,

Bayan tagama ta tube hijabin ta ajiye , sannan ta hau saman bed ta kwanta dama jiya bata samu isasshen bacci ba , don haka lokaci guda bacci ya kwashe ta , tana cikin bacci y’an matan nan suka shigo , sai faman fadin wash Allah suke , koda sukayi arba da ita kwance ta baje gashi ta cire hijabin kan ba head tie, nan fa suka fara santin gashin kanta , ita dae bata son meke wakana ba tadai ji sama sama ana ja mata gashin kai ,

Zama sukayi kamar sun sami television sukai ta kallonta , ba karamin lalata sukayi ma kanta ba duk sun cukuikuye mata gashi yar kalaban nan sun warware mata ita , sun mai da karamar mahaukaciya ,

Nauyin bacci ne ya hana ta farka amma tabbas taji ana shafa mata kai kasa kasa ,

Sai da ana kiran sallan isha sannan ta farka , mika tayi tare da yin hamma , time din sun fita daga cikin bedroom zuciya sauko da legs dinta tayi kasan tiles din tana sauke ajiyar zuciya , kafin ta mike ta shiga toilet , tana cikin yin alwala tayi shafuwan kai ta shafo gashin kan ta mamaki ne ya kamata jin ba kitson dake kanta da sauri ta idasa alwalar ta je gaban mirror ita kanta sai da ta firgita da ganin yadda suka susuce mata gashinta , amma ba wannan bace damuwarta , zullumin kada husanna ta mutu da kuma aikin da zata fara ,

Zama taci gaba da yi a bedroom din , tana tunene tunane , ga yunwa tana ji amma takasa fita ta nema ,

Turo kofan sukayi suka shigo hannunsu dauke da tray abincin aka zuba musu shinkafa da miya ne sun cinye sun rage mata d’an kadan, ajiye mata sukayi suna dariya suka fice , abunda basu sani ba ita kallon Shashashu take masu ,

Bin a bincin tayi da kallon ba don tana jin yunwa ba da bazata ci Ba don sun jagula shi, haka ta zauna ta dinga turawa a baki kamar zatayi kuka , har dare yayi tana zullum abu daya kuma dashi ta kwana,

…………………………………ABBAN SOJOJI

…………………..Story by MrsBature

………………Part 1

In the morning

Around 10:30am makeup artist dinan ta iso gidan a time din duk sun hallara a falon hajjaju , bayan sun gama gaisawa , ma’reea ta bukaci ganin Sehrish , kwala mata kira hajajju tayi fitow tayi da sauri ta iso inda suke , bin ta da kallo mareeya tayi frm head to toe , sannan tace “Wannan ae mai sauki ne , naga tana da tsayi jiki ne dai babu sosai , abunda za’ae kayan maza za’a samo riga da wando oversize saboda su kara mata girma , sannan wadannan abubuwan , tayi magana tana nuna kirjinta da hannunta ” dole a matse su don naga suna da girma ssae tubarkalla , ” cikin jin kunya rishi ta dukar da kanta kasa ,  murmushi larai da hajajju sukayi , su kuwa y’an matan nan dake baje a kasan carpet dama  basu da burki washe baki suka shiga yi wato anzo dai dai inda suke so ,

Hajajju tace “ynx me za’a sa a yi tighting dinsu “? Ma’reeya tace “mai sauki ne akwai wani abu da muke amfani dashi na matse tumbi shima zai iya yi ,”  hankalin rishi ba karamin tashi yayi ba har bata son lokacin da tayi subul da baka ba tace “in suka bace fa ya zanyi ,”? gaba dayansu suka kwashe da dariya mareeya tace “wato kada su bace a rasa nayiwa miji gayu ko ,” cikin jin kunya ta dukar da kai ,  larai tace ” dagaskiyar ta fa nono ae yana daya dagacin abunda ke kayatarda maza in suka bace ae ba magana ,”   ta karasa magana tana dariya , duk kunya ta gama kamata,

Ma’reeya ta ci gaba da magana “Sannan naga kamar tana da tsayin gashi ko,”? hajajju tace “Sehrish cire hijabin mana tagani , hannu tasa ta cire hijabin ta rungume a kirjinta ,

Hada baki sukayi wurin cewa “Tubarkalla masha Allah ,” ma’reeya tace ” yarinyar kamar balarabiya wurin tsawan gashi, gsky ni kishi nake da wannan gashin naki don haka dama dole indai zakiyi acting a matsayin namiji sai an datse miki shi ya koma guntu kamar nawa dai”,  nan fa hankalin ta ya tashi saboda tana bala’en son gashin nan nata , kamar zatayi kuka tace “don Allah hajajju karki bari ayimun aski ni inason gashi na ,” takarasa maganar tana kallon hajjaju ,

Murmushi hajajju tayi tace ” Sehrish ba Aski zata miki ba rage miki shi za’ae , ke da zaki neman kudi wake ta wani gashi , ”

Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta , larai tace “Gsky yarinyar nan da ace a matsayin mace zata je aikin nan tsaf zata auren mai gidan,”  hannu hajiya tasa abaki tace “ke ! tab y’ay’an sa kuwa da sun yi farfesu da namanta sojoji fa akace hmmm !! ”  dariya sukayi su duka , mareeya ta cigaba da bada bayani “Sannan dole a canza mata suna daga SEHRISH  zuwa TUKUR ,” a tare suka hada baki wirin cewa “Tukur kuma !”? murmushi ma’reeya tayi tare da jaddada masu maganarta ta  ” kawai kuwa ! sannan zan sa mata gashin baki irin na maza wanda ake fixing dinsa tare da eyebrows na kanti.

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 7-8

Hajajju ta ce “Gashin baki dai. wannan dana nasani ? amma me amfanin hakan “? ma’reeya tace “Wannan wani salo ne kuma ina tabbatar miki da zaiyi aiki , duk da sehrish yarinya ce har a fuskarta amma indai nasa mata gashin baki dana jagira , zata kara suffanta da namiji zata koma kamar d’an daudu kuma dama in kin lura yanayin jikin y’an daudu basa da kiba sai tsayi ,”

Gaba daya sun amince da maganar ma’reeya , shiri na musamman akayi ma Sehrish a washe garin ranar cikin riga ta maza milk colour mai maballai a gaban rigar , sai wani burgujejan wando falazu da aka sama ta kamar kafar agwagwa haka yake pink colour , sun matse mata kirjinta , shafe ta koma kamar babu su , an datse dogon gashin kanta an barmata guntu irin nawa sai suka samu kallabi irin launin  trouser din suka nannade mata shi akai kamar rawani , kallabin nada tsayi sai da yar jela ta zubo ta gefe , sai ta koma kamar d’an chali chali , ga gashin bakin da suka sanya mata , ya hau radau ya zauna , haka jagirar da suka samata , ta zauna cuf  , duk wani abu na ado na jikin y’a mace babu shi a tattare da ita yanzu ,

Shin koya wannan wasan kwaikwayon zai kasance ? mezai faru ranar da suka gane cewa sehrish macace ba namiji ba ? Kowa yasan ya sojoji suke  👊.

Tunda a sussuba suka kama hanyar zuwa abuja , ita da hajjaju , zuciyarta sai dar dar take yi mata , a natse hajjaju ke driving dinsu , yayin da sehrish ke gefenta , idonta nakan glass din motar , tana kallon yadda suke wuce wurare daban daban , zahiri tana kallon bishiyoyin da suke giftawa na cikin dajijjikan da ke a side road  kamar suna gudu da kafafuwansune , a hankali zuciyarta ta sauya mata akalar tunaninta izuwa rayuwarsu ta baya , nan take taji wasu zafafan hawaye na sintiri a idonta , zuciyarta ce ta soma yi mata magana “Sehrish kowane d’an adam yana da irin tasa kaddarar, Allah yana jarabtar bayinsa ne domin ya gwada imaninsu , kiyi kokari ki cinye wannan jarabawar , ki rungumi kaddara a duk yadda tazo miki dama can rutacce ne daga Allah dukkan tsanani yana tare da sauki ! Allah yana sane daku kuma shine gatanku ,”

Hannu tasa tana clearing face dinta saboda bata so hajjaju tagani , tunanin y’an uwanta shine yafi komai tayar mata da hankali , bata san wani gidan mahaukata bane zasu juri daukar nauyin haukan ta ba idan akace yau husanna tarasa ranta , haka abubuwa suka dinga zuwa mata aranta har suka isa garin abuja,  wuraren karfe 2:30 na rana  ,

Wannan ne karo na farko da ta fara yin tafiya mai nisa irin wannan ,

tunda suka shiga take kallon manya manyen gine gine , har suka iso gidan da zasu wato gidan Abban sojoji , sehrish ta razana da ganin katafaren ginin mai matukar girman gaske da daukar hankali , irin gidan da ta saba gani a cikin  mafarki,

Lokaci da idonta suka sauka kan Narka narkan sojojin  dake tsare da babban gate din gidan sai da taji gabanta ya fadi rass , bakake ne wulik dasu sanye cikin uniform dinsu , ga bindigu rike a hannunsu , ga wasu guns din soke a west dinsu ,

Wani irin miyau ta hadiye ganin an tsaida motarsu , nan take taji zufa na gangaro mata ta cikin sumar kanta ,  guda biyu ne suka karaso inda motar tasu take , d’aya ne yasa hannu yayi knocking  , hajjaju ta zuge glass din , ita kanta a tsorace take cikin en ena tace “barka dai sannu ku da aiki ,”  amsa yayi da “yawwa muna bukatar sanin daga ina kke kuma wurin wa kka zo “?

Da sauri hajjau ta dauko wayarta cikin yar purse dinta ta shiga neman number abban,  yatsun hannunta sai kakarwa suke , kira d’aya tayi masa ya daga , bayan sun gaisa ta sanar masa da abunda ke faruwa, ya umarce ta da ta basu wayar , mika musu tayi daya daga cikinsu yasa hannu  ya karba tare da karawa a kunnansa ,   juyawa hajjaju tayi tana kallon sehrish wadda tuni ta ta gama tsuma , ta nannade wuri d’aya ta matse jikinta , idon nan sunyi furi furi kamar wadda tayima sarki karya ,  muryar sojan taji yana cewa “take your phone , u got permission to go in , but firstly we must check the car ,”  kallon sehrish tayi tare da cewa ” mu fita zasu bincika motar ,” bude mota sehrish tayi ta fita , itama hajjajun ta fito , suka tsaya suna jiran su gama binciken nasu ,

Matsawa Sehrish tayi kusa da hajiyar tayi kasa kasa da murya tace “hajiya amma nan barrack din sojoji ne ko “? cikin rashin natsuwa hajjaju tace ”  A’a gida ne na sojoji dae not a barrack ni bana cikin kwanciyar hankalin wadannan sojojin sun firgitani , sai kace wasu masu safarar miyagun kwayoyi za’a tsare mu ! that’s why ban cika son zuwa gidannan ba ! ,” takarasa maganar tana yatsina fuska ,

Jikin sehrish ya gama yin sanyi , bin jikinta tayi da kallo tasha kayan maza , ga uban burgujejan wandon da tasa kamar zata tashi sama, kara kankame jakar dake hannunta tayi wacce ke kumshe da y’an kayan  da hajjaju ta bata kyauta ,

Hatta purse din hajjaju sai da suka bincika , zuciyar sehrish sai bugawa takeyi tunanin ta masu gadi sun kasance haka da ban tsoro ina ga y’ay’an gidan da taji ance they’re all soldiers 😒

Muryar sojancce ta ratsa kunnanta “lemme see your bag “! cikin sauri ta mika mar jakan , zazzago kayan ciki yayi kasa yana duddubawa , trousers ne da riguna na maza , da hijabai da ta kudundunesu saboda sallah  ,  bayan ya gama checking dinsu ya dago ya zuba mata ido yana kallonta , nan take taji fitsari ya cika mata mararta , sunnar da kanta tayi kasa , jikinta na rawa , Ji tayi yasa hannunsa ya dankwashi kanta yana cewa “mara kunya kana namiji baka iyasa Cap akan ka , kai ga d’an daudu ko ? sai dai kasa abu na mata ka nannade kai kamar wani limamin masallaci “,

Karasa maganar yyi tare da wurga mata jakar , sannan ya juya ya tafi , hannu tasa ta dafe wurin don taji zafin rankwashinta da yayi mata wannan gabjejan hannun nasa , dole ita ta zukunna ta kwashe kayanta daya zubar a kasa ,

A karshe dai Sun sami shiga ciki , a jiyar zuciya Sehrish tasaki , time dinda motar tasu ta wuce babban gate din ta shantalelen titin da zai kai ka can cikin gidan ,

A hankali take bin ko ina da kallo ta cikin glass din motan , tana kara jaddada haduwar ginin , taga wurare daban daban  masu ban sha’awa , sai ta dinga tunanin cewa kodai tabar nigeria ne domin daga inda kasa kafarka cikin gidan kamar ka fita daga 9ja ne 😔

ihu da sowar da taji ne  yasa takai idonta wurin , y’an matasan samari ne kyawawan gaske suke wasan football , acikin playing field n gdn , gwanin burgewa tabisu da kallo har sai da suka wuce su ,

A wurin da aka ware na parking space , hajjaju ta tsaida motarsu , wurin cike yake da motocinsu Na gayu ga kuma jibjibgan motocin irin na sojojin man

Waigawa hajjau tayi ta kalle ta tace  “sehrish ki natsu dan Allah in mun shiga kada ki jamun , kuma kada ki manta sunan ki tukur daga ynx ,” cike da gamsuwa ta masa mata da “Toh”

Fitowa sukayi daga motan suka miki hanyar data zata sada ka da babban falon gidan , tuni sehrish ta raina kanta , tamkar karta taka kasan tiles din take ji saboda wani irin design ne mai daukar ido , duk yadda ka taka saiya bada sauti kwas kwas ,

Komai na cikin living room din mai tsadar gske ne , kana gani kasan bana nan bane , an kawata shi da expensive furnitures , wasu hamshan royal sofa ne aciki  , set shida ne a jere , ko da ido ka kallesu kasan zasuyi laushi da dadin zama  , duk yawansu basu cike falon ba saboda girmansa ya isa a gina madai madaici gida acikinsa,

Komai da ake bukata acikin falo akwaisa sai da ba tarkacen nan na hauka komai a natse ,

Bin ceiling din tayi da kallo ba irin rufin da tasaba gani bane , wannan na glass ,  acikinsa akwai light bulbs masu haske wurin ,

Hankalin hajjaju ba karamin kwanciya yayi ba ganin falon tsit ba kowai sai sanyin a.c dake ratsa sassan jikin mutun, dama zullumin ta ace wadannan sojojin na nan ,

Ruko hannun sehrish tayi wadda hankalinta ke kan twin stairs din da tagani wato tagwayen bene guda biyu wadanda zasu kai ka upstairs, tsantsararrun gaske  ,

Sehrish tace “hajiya naji tsit ko ba kowa ne ? hajjaju tace “ina ga duk suna wurin aiki , mu samu wuri mu zauna mu jira wata’kil mai aikinsu na nan ,”

Suna kokarin zama suka ji takon takalmi daga left dinsu , karfaffar maca ce irin giantess dinnan , tana da hasken fata , jikinta na sanye da doguwar riga ta atampa har kasa ta kashe daurin d’an kwalinta , tana ganin hajjaju ce ta saki fara’a tana fadin “me nake gani kamar hajjaju makkatin “?  murmushi hajjaju  tasaki tare da cewa “kwarai kuwa nice AZUMI ashe kina ciki , nayi tunanin ba kowa ciki ne ,”

Karaso wa tayi inda hajjaju take tayi hugging dinta tana cewa ” I really missed u alot hajjaju  kin boye mana nayi expecting din bakya kasar ne ,” sakin juna sukayi hajjaju tana dariya tace “Ina nan mana ina zani an gaya miki ynx barin kasar nan sauki ne yadda komai ke kara farashi , yar dubai dinnan danake zuwa kamar hauka ynx nadaina saboda rashin kudi ,”

Murmushi azmi tasaki , tare da nuna masu wurin zama tace “bismillah ku zauna bari na shiga na kawo muku abin sha , firar zata fi dadi idan kuka jika makoshinku ,

tana gama fadan hakan tajuya ta nufi hanyar da zata kai ka kitchen dinsu , zama sukayi a tare saman 3 seater , har lokacin sehrish na makale da yar jakarta a kirjinta , sai karewa falon kallo takeyi tana jinjina kyansa , wai itace zata rayu a cikin katafaren gidannan , wayyo dadi boye farin cikinta kawai take yi , ta wani bangaren kuwa hankalinta a tashe yake , saboda batasan ya rayuwarta zata kasance ba a matsayinta na yar basaja , matsayin namiji a gidan sojoji ,

Dawowa azumi tayi hannunta dauke da tray , plate ne mai dauke da snacks , sai 2 cups da jug , a jiye su tayi a sman table sannan ta janyo shi izuwa gabansu ta ajiye ,

Koma tayi tazauna tana murmushi , Sehrish kuwa sai kallon matar take yi har taji ta burgeta saboda tana son mutum mai fara’a ,

Lemu ne a cikin jug din zuba musu hajjaju tayi ta mika ma sehrish , cikin sauri ta karba dama kishi take ji , kurbarsa tayi wani irin sanyi ya ratsa ta ga dadin gaske ,

Azumi ta bi ta da kallo cikin mamaki tace “in ce ko wannan ne d’an aikin da akace za’a kawo mana”? hajjaju ta danyi guntun murmushi tace “eh shine sunan shi tukur kwararre ne wurin iya sarrafa abinci ,” saboda jin karyar da hajjaju ta shirgo akanta yasa ta kusa fetsar da lemun da takurba a bakinta , abunda ya kusa sata ta shake shine da ta ce kwararrene wurin iya sarrafa abincin shin yaushe ta son da wannan ?

Sauraron hajjaju ta ci gaba dayi jin  tana introducing dinta a wurin azumi ” yaro ne mai matukar basira ga wayau , zakiji dadin yin aiki dashi ,” takarsa maganar tare da ajiye cup din dake a hannunta saman table din gabanta , sannan ta kalli sehrish tace “tukur wannan itace azumi , itama y’ar aiki ce a gidannan amma taji ssae tana kula da yaran gidan hakan yasa ta zama tamkar uwa agaresu , ina fata zakuji dadin yin aiki da juna ,”

Dakyar sehrish ta kakaro murmushin dole tace “Insha Allah hajiya ,”

Ita kadai tasan halin da ta shiga , wannan zaman da tayi  ji ta , kamar ta dosa na ass dinta  a saman wuta , saboda tsabagen tsoro , A ranta sai maimaita kalmar ‘yaya goma sha takwas kuma duk sojoji  take yi ,

Azumi ta janye idonta daga kan sehrish (tukur) ta mayar da idonta kan hajjaju tare da cewa “am inaso na tambaye ki tundazu maganar ke shigemin meyasa kika daina leko mu bayan ina da tabbacin cewa kina zuwa abuja zuwane kawae ke baki yi ,”

Murmushi hajjaju tayi tare da yin yar dariya tace “ai dole zuwa gidannan ko jaraba ! oh kin manta Abunda ya faru last time dana zo ko ? Ina wannan BABBAN YAYAN nan nasu wani mai shegen kyau tubarkalla kamar d’an sarkin aljanu mai kirar zakunan nan ,” dariya azumi tayi tare da cewa “wai wa kike nufi cikinsu , kinsan suna dayawa , akwai major , akwai Captain ga janar , akwai Marshall ga kuma Canal da sauransu , kowa da sunan da ake kiransa  ” takarasa maganar tana kallonta

Sarai tasan wa take nufi amma tafiso taci gaba da zuzutashi don hajjaju ta iya bada labari ,

taci gaba da cewa “oho nidai nasan shi kadai suke ce ma babban yaya , ina gaya miki last dana zo , lokacin nazo dubiyar wannan younger bro dinnasu mai asthma wanda  aka fidda kasar waje akayi masa aikin a kirjinsa , ” azmi tace “oh nagane junaid kike nufi ae suna waje suna buga ball ynx yaji sauki Alhmdllh ,”

Hajjajun ta ci gaba da cewa “ina fadamiki daga zuwa abun arziki , wlh ina shigowa falon nan ni bansan meya faru ba , nasame shi da y’an uwannan nasa sae faman rirrike shi sukeyi sai huci yake yi just like a hungry lion from the bush gaba daya yayi watsi dasu  kasa , ya daga dining table yayi wurgi dashi , gabana ya fadi  rass banyi aune ba naji yace “don ubanki kama hanya ki fice, ashe ya ganni ”

Wallahi a tsorace  a fujajen nabar gidan don tsabagen rudi , da kafa nakama hanyar fita babban gate din saida wani soja cikin security din gidan nan yace mun hajiya kin manta motarki , sannan fa natuna jiki na rawa nakoma nadauko,”

Tun kafin ta idasa labarin azumi da sehrish suke ta faman tikar dariya , kamar cikinsu zai kulle , ita kanta hajjajun dariyar take yi ,

dakyar azumi ta tsaida dariyarta tace

“Hmmm sai ynx nagane wa kike nufi , ai da kinsani ba ki daina kawo mana ziyara ba domin shi ba sojan nigeria bane , US ARMY ne ba a kasar nan yake ba yna dai zuwa sometimes in yasamu hutun aiki ,”

Hajjaju tace “bazaki gane ba ne , yadda na tsorata , ai ko ba don shi ba , wadannan tantiran na gidannan marasa jin magana…” Azumi ta katse mata maganarta ta da cewa “twins kike nufi , tom & jerry suna nan haryanzu basu canza ba sai ma abunda yayi gaba “,

Hajjaju tace “ehen su nake nufi”,

Ci gaba da fira sukayi , yayin da hankalin sehrish ke atashe , tunda taji sun ambaci babban yaya sai taji tsoransa har ya shiga ranta , sam ta nemi natsuwarta ta rasa ,

Sun jima suna fira har time din ba wanda yashigo daga cikin soldiers din ,  har hajjaju tayi shirin tafiya , bayan ta yiwa azumi bayanin akan nemawa tukur wato sehrish alfarmar in tayi one month da fara aiki ta taimaka a ansar mata kudin wata uku a dunkule ,

A tare suka fita har bakin motar ta , sannan suka tsaya suna idasa takarkare zancen

“meyasa bazaki jira abban ba yazo? koya yi miki sallamarki ne “? hajjaju tace “ae indai abba ne bani da matsala dashi nasan zanji alert kinsan hannunsa a bude yake , kuma Abunda yasa nake sauri zan shiga gwarinpa ne gidan wata goggo na ”

Murmushi azumi tayi tana kallonta,

Ita ma murmushin tayi mata , harta bude mota zata shiga tasake juyo wa ta kalli azmi tace “pls game da tukur na baki amanarsa , ki kula da duk wani motsi nasa pls ,”

Azmi tace “in dai nice u don’t ave to worry about it I will look after him insha Allah ,” sallama sukayi hajjaju ta shige cikin motarta ta ja ta ,

Bayan fitarsu sehrish ta zabga uban tagumi tana jin kewar kasancewarta ita kadai a wannan hamshakin gidan da batasan kowa a cikinsa ba , gashi tazo a matsayin namiji , duk in ta tuna wannan hankalinta tashi yake , abu dayane ke kara mata karfin guiwa , y’an uwanta in ta tuna su sai taji ba irin kasadar da bazata iya shiga ba ,

Dawowa ciki azumi tayi fuskarta a sake tace da sehrish ” tashi mu shiga ciki na nuna mka bedroom din ka , in ka huta zuwa anjima  before magrib zamu shiga kitchen”,

Sehrish ta amsa da toh tare da mike wa tabi bayan azmi , suka shiga ciki tayi mamakin bedroom din da azmi ta nuna mata a matsayin nata na yar aiki , wannan koda amayarce tasamu wannan falillahil hamdu , ba tarkace a ciki , single bed ne , ga beside drawer mai dauke da bedside lamp a samanta  ga wardrobe madai-daiciya ta manne jikin bango ,  ga wadatattun curtains a kowane window , komai na cikin bedroom din brown color be banda labulayen da suka kasance milk colour , da zanen gadon ,

Ba abunda ya kara burgeta sai dressing mirriow din da tagani , duk da ba cosmetics a samansa , madubin yayi mata da yar chair din dake gabansa ,

Murmushi azumi tayi ganin yadda yaron yake ta farin ciki don haka tace “komai yayi ko “? da sauri ta amsa da “eh hajiya harma yayi yawa ”

Dariya azumi tayi jin yace harma yayi yawa ,

“Ynx dai ni zan shiga ciki , ka zauna ka huta , sannan akwai bedsheets a cikin wardrobe din nan , in zaka canza saika dauka ,” tana gama fadan hakan ta fice ,

Kamar jira takeyi azumi ta fita tahau ihu tana tsalle , kafin ta tsagaita da haukan nata ta shiga bathroom din dake ciki ,

Nan fa ta soma wani sabon kallon , ko a mafarki bata taba tunanin zata mallaki irin wannan tsantsararren bathroom dinba mai kama da bedroom saboda haduwarsa ,

Dakyar ta samu natsuwa , ta dauro alwala tafito , a cikin wardrobe din ta samu prayer mat (sallaya) ta dauko ta shimfida , ta kabbara sallah , duka ta hada tayi zuhr da isha saboda batasamu damar yi ba a kan hanya , gashi ynx ankira isha’e shiyasa ta hadesu duka tayi ,

Bayan ta idasa sallar , ta daga hannayenta sama tana addu’ei at the end ta fashe da kuka , Sbd tuna wa da halin da y’an uwanta ke ciki , magana ta soma yi cikin kuka ” har ynx na gaza yarda cewa nice zan yi rayuwa a cikin wannan daular ba tare da y’an uwana ba , taya zanji ddin rayuwata batare dasu ba , ni ina nan sukuma suna asibiti cikin wani hali , Allah sarki rayuwa ! bazan taba yafe ma wanda yayi silar shigarmu cikin wannan tashin hankalin ba , Ya Allah ka hana sa jin dadin duniyar nan gaba daya , Ya Allah ka kaskantar da rayuwarsa kamar yarda yayima ta mu…..” kuka ne yaci karfinta har ta kifa kanta saman sallayar tana cewa “I will never forgive u in my life and I will neva forgt u ! i must take revenge koda ace nikadai ce na rageda zan yafe maka ka shiga aljanna to tabbas bazaka taba shigar ta ba.

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 9-10

Bata tashi daga saman sallayar ba har aka kira Magriba tana tunanin abu daya, sai da ta kammala sallar sannan ta nad’e carpet din ta turasa cikin wardrobe , tare da hijab din duka.

tsayawa tayi gaban dressing mirror tana kallon kanta a cikinsa , sak namiji ba wanda zai gane mace ce sai yanayinta ya koma kamar d’an daudu , hannu tasa tare da shafa gashin bakin da ma’reeya ta sanya mata , murmushi ta d’an saki a ranta ta ce “Sehrish ke nan dramatic girl.”

Kara kimtsa kanta tayi saboda azmi tace mata akwai aiki a kitchen da zasuyi, sai da ta fara rufe kofar dakin gudun kada Azumi ta same ta tana canza kaya , ta gane cewa maca ce ita ,

Cire kayan jikinta ta yi , ta maida su cikin bag dinta , sannan ta dauko wasu riga da wandon , ta rige a hands sinta gaban mirror din ta koma ta tsaya tana kallon jikinta , ziririn pant ne a ajikinta , takai hannu tasha fa flat tommy dinta , wanda yake a dam’e kaman bata cin abinci saboda shafewarsa ,

Mayar da hannun tayi saman boobs dinta wadanda ta matse su gam , da abun matse belly , har cikin ranta ba taso hakan ba tana son abunta ssae , amma ba yadda zatayi duk cikin aiki ne ,

ga hairs dinta da aka maida mata shi guntu , amma hakan bai dame ta saboda a iya sanin ta in aka aske mata gashi irin hakan cikin one month zai koma yadda ya ke tsayinsa ma harya karu ,

Jin alamar tafiyar mutun kamar bedroom ta ake nufowa shine ysa ta yin saurin , zura dogon wandon tare da rigar sa , tayi gaggawa gyara daurin da m’reeya ta yi mata , mai kamar rawani ,

Kwan ! kwan !kwan taji an knocking , cikin sauri ta karasa ta bude kopan azmi ce tsaye fuskanta da murmushi tace “tukur ina fata ka shirya sbd ynx zamuje na nuna maka yarda abun aikin yake  ,”

Cikin girmamawa sehrish tace “toh hajiya ,”

Azmi tayi mata wani irin kallo har gaban sehrish ya tashi a tunaninta ta gano lagwanta , amma sai taji tace “stop calling me hajiya , my name is azmi call me by my name , cos we re d same , am a house maid just like u ,”

taka rasa mgnr tare da fice wa tana cewa “follow me” rishi ta bi bayanta tana d’an murmushi ,

Kitchen suka shiga amma sehrish ta gaza gane a ina suke , haduwar wurin ce ta rikitar da ita , an kawata komai na kitchen din da dukkannin abubuwan da akeso,

Sam ta manta aiki ya kawosu sai faman kalle-kalle take yi , sai da taji muryar azmi a kunnanta sannan ta dawo dai dai

“tukur ynx bamu da enough time , we’ll make a dinner now in yaso zuwa tomorrow i will explain everything  to u ,  Especially zama da samarin gidan nan darasi ne me zaman kansa duk zan koya maka ,”

sehrish sai take ganin maganar azmi kamar shiriri tace , ynx har akwai mutumin da za ace sai  an koyi darasin zama dashi ?

haka suka fara aiki , azmi ce ke yin girkin , yayin da tabarma sehrish ferar dankalin turawa , ga yankan albasa , acewarta tafara da karamin aiki ,

Suna cikin aiki sehrish tafara jiyo karar shigowar motoci , rass taji gabanta ya fadi , da jiniya motocin ke shigowa ,

“Hmmmm wannan alama ce mai nuna cewa masu gidan sun dawo ” a cewar azmi ,

Zuciyar sehrish sai harbawa take yi saboda tsananin firgicin da wa zata fara cin karo ,

“Ka’ida ne daga sun shigo babban falo zasu fara kwalamin kIra ka saurara kaji  ,” azumi ta fada tana murmushi ,

Hannun sehrish sai  kakarwa suke yi ,

ita dai baza ta iya tantance muryar mutun nawa bace amma taji sauti iri iri

“Azumi ! Azmi !! Azam zam !!!” da karfi suke kwala mata kiran without any respect ,  cikin sauri azmi ta fice tana ce ma sehrish “pls ka kula da girkin am coming back now ,”

Sehrish ta amsa da toh , daga inda take tana iya hangosu saboda kitchen din irin model design dinnan ne wanda ba kopar shiga gare sa a bude yake bata iya identifying faces dinsu ,

Hankali a tashe azmi takarasa wurunsu tana fadin “welcome back Sirs ,”  ko arziki amsa bata samu ba sai complaining da suka soma yi mata, “Ina fata angyara min bedroom dina don bansan kazan ta ! in ma kinsan baki gyara ba let me know ,” daya daga cikinsu ne yayi wannan maganar ,

matsawa tayi kusa dana gefensa don taji shi mai zaice  , hannu ysa yana shafa ciknsa yace “Ni matsala ta abunda zansa ma cikina pls kafin na shiga ciki nayi bath na tarar da abinci jere saman dining table if not kinsan sauran ,”

matsawa azmi ta sake yi kusa dana gefensa dayake duk suna a jere kusansu takwas,

” Na fadamiki Injin wanki  na ya samu matsala dazu da safe ga shi na tara kayan dauda , gajerun wanduna na ma duk sunyi dirty dafatan kin wanke mun su ,”

Haka ta dinga sauraransu ba wanda baiyi magana ba acikinsu , bayan ta gama sauraransu one by one tace ” Komai da kuka lissafamin na kammala sa , abinci ne kawai shima ynx zan idasa ,”

Kama hanya suka yi kowa ya wuce bedroom dinsa , wasu na upstairs wasu na a downstairs,

Babu abunda ya burge sehrish sai kakin sojojin dake jikinsu , abunka ga handsome guys ga tsawo ga hadaddiyar sura sai abun ya bada citta 😘

tunanin ta soma yi a ranta “oh ni ko wanene babban yaya acikinsu , koda yake naji azmi tace ba sojan nigeria bane U.S ARMY ne , zanso nagansa daga ji ya hadu yadda hajjaju ke zuzu tashi ,”

takarasa tunanin tana murmushi ita kadai abunta , shigowa azumi tayi tana fadin “maza tukur a shirya abinci a dining before su fito, ai ina ji girkin ya isa ya kammalu ,”

Wasu hadaddun kuloli ta dauko daga kitchen cabinet kamar ranar aka budesu daga kwalinsu tsantsar kyansu kamar ba abinci za’a zuba ciki ba , saboda yadda murfinsu ke glowing har face dinka zaka iya gani aciki just like mirror ,

A wani faffadan tray ta shirya komai ciki , ta mika wa sehrish azuwan taje ta fara shiryasu a dining ,

Gaban ta na faduwa ta karba tsoranta da wa zata fara cin karo a cikinsu ,  time din da ta isa dining room din , mutun d’aya ta samu zaune shi ya rigasu fitowa jikinsa na sanye da white tshirt da black  short  , bai lura da ita sai da yaji cool voice dinta ta sauka a kunnan sa ” sannu da hutawa ” a natse ya dago yana kallonta ,

lokacin da suka hada ido kara ware idonta tayi ganin irin kyawunsa , dan matashi ne ba zai wuce 18years ba , a tunaninsa zai ga mace amma sai ya ga namiji tabbas shi muryar mace ya ji mai dadin gaske a kunnan sa ,

Wani kayataccen murmushi ya sakar mata , wanda yasa ta shiga yanayi ,  cool voice dinsa ce ta ratsa ta “am nace ko sabon mai aikin da akace za’a kawo mana ne?daga masa kai tayi alamar eh ,

Jinjina kansa yayi tare da d’an tabe small lips dinsa  ,

Soma jera abincin tayi , bayan ta gama ta koma ta dauko sauran abubuwan da bata kawo ba ,

Allah Allah take ta kammala jera abincin kafin sauran su karaso , muryarsa ce ta kara katse ta ” chicken pepper soup din nan zaka zuba mun ka hadamin da irish cikin plate din ,” ta amsa toh kamar wata munafuka haka take sunnar dakai , Ji take kamr asirinta zai to nu ,

Plate ta zaro daga cikin set na filattan da takawo , bude daya daga dana cikin kulolin tayi , nan da nan kamshi ya gauraye wurin , saving spoon ta dauko ta soma zuba kazar a cikin plate din , sai faman hadiye miyau take yi , ga hannun ta dake kakarwa ga wani gumi dake sauka daga gefen sajenta ,

Kammala zuba kazar tayi sannan ta bude kular da ke dauke da irish ta zuba masa k’adan  muryarsa ta sake ji “yayi mun k’adan ka take mun plate din ”

cika masa plate din tayi dam sannan ta tura masa gabansa , cikin sauri ta kama hanya zata koma ciki  “spoon din fa ko so kake na dauka da kaina ne sannan a gidan ku haka ake ba mutun abinci ba tare da drinks ba ‘? har zuciyarta taji wannan maganar a tunanin zaiyi saukin kai ganin da farko yayi mata murmushi ,

lallai ta jinjina wa izzarsa , ga cokulan kusa da shi ga kuma drinks din da ta jera amma yafi karfin yasa hannu ya dauka sai da ita ta mika masa ,

guntun murmushi tasaki koma tayi ta mika masa cokalin sannan ta zuba masa lemu a cikin glass cup ta mika masa , yamutsa fuska yayi tare da sa hannu ya karba yana cewa ” gsky kana bukatar training don da ace babban yaya ko captain kayima haka da ka gane barno gabas take don sai kayi tsallan kwad’i ,”

Ya karasa maganar yana kurban lemun da ta mika masa , a wani irin yanayi sehrish ta juya wannan ne karo na biyu da taji an ambaci BABBAN YAYA , hakan nakara sa mata tsoransa a zuciyarsa ,

Komawa tayi kitchen ta samu azumi tana gyara wuraren da suka bata , jin shigowarta yasa ta dagowa tare da cewa “subhanallah meyasa ka dawo ka kammala saving dinsu ne “?

“A’a naga basu fito bane shiyasa na tafo ,” tayi maganar fuska a yamutse  sbd rashin natsuwa da take ciki , azumi tace “maza ka koma karka ja mun bala’i , bakasan halin mazan gidannan ba ,”

Ba haka sehrish taso ba , jiki a sanyaye ta kama hanyar komawa dining room din ,  hannu azumi tasa ta rike habarta alamun mamaki tace “lallai dole na mike tsaye akan yaron nan ! yana abu kamar mace anya wannan ba dan daudu bane ? ta tambayi kanta ,

Tunkan takarasa ta ke hangensu , a lokacin suke karasawa  saman dining din kowannen su yaja kujera yazauna , Kasancewar table din dogone mai mazaunin mutum goma sha 12,

Tana jin dayansu na cewa “wai uban wa ake so ya zuba mana abincin ne? cikin sauri sehrish ta karasa tana cewa “ni ce yallabai ,”

Gaba daya suka d’ago suna kallon ta sai ta tsorata tayi wuri wuri da ido.

👮🏻‍♂️ *ABBAN SOJOJI* 👮🏻‍♂️

“`The father Of Soldiers“`

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️

───────────────────────

“`{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa’idar Adabin Hausa.“`

“`Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}“` ✏️✏️✏️

____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•

Page 11-12

‘Yan kame-kame ta shiga yi hankali a tashe tana wurwurga ido, ” wannan d’an daudun daga ina kuma aka samo shi?” Daya daga cikinsu ya tambaya yana kallon ta , hantar cikinta ce ta ji ta kad’a , su duka sauraren ta suke yi su ji mai zata ce?

Motsi ta soma yi da lips dinta alamar tana so ta ce wani abu “Amm… Amm..” Duk ta bi ta dabarbarce. Jin muryar Azumi yasa Sehrish sauke ajiyar zuciya, karasowa ta yi tana fadin “Afuwan y’an samari ban yi maku bayani game da sabon d’an aikin da aka kawo domin ya rinka taya ni aiki ba.”

Kasa kunne suka yi suna sauraron ta , dafa kafadar Sehrish ta yi tare da cewa “Sunan shi tukur daga yau zai rinka taya ni aikace aikacen cikin gidannan ,’

Ta kare maganar tana kallon kowannan su tabe baki yyi  ba tare da sunce komai ba dama haka ta yi tsammani , don haka taci gaba da cewa “tukur bari na gabatarka maka da kowannan su saboda ka kiyayi zama dasu ,”ita dai ba ta ce komai ba saboda a rud’e take ,

Azumi ta soma gabatar mata da su daga na farko “Wadannan biyun da ka ke gani sune tagwaye  in ka lura komai nasu iri d’aya , suna da son zolaya musamman idan abun mugunta ne sun fi auki a nan na farkon sunansa Jahan shine babba sai twin brother dinsa Ayaan”

Tana gama wa dasu ta matsa na kusa dasu tace “wannan kuma sunan shi Kanal yusif sarkin tsafta , bai cika son surutu ba kuma baya son kallo , na gefensa kuma shine Khaleed bai da matsala shi indai za ayi masa abunda ya ke so ba tare da ya tambaya ba ,

Duk Sehrish na sauraron wannan bayanin na azmi , bayan ta kammala da na hannun damarta ta koma other side din taci gaba da cewa “wannan Junaid kenan sarkin murmushi, duk yadda za’a bata mai rai baya fushi sai in an kuresa , yana da son wasa faran faran da jama’a, burinsa a bashi kulawa  a bangaren ci kuwa ba’a magana ,” karasa maganar tayi tana y’ar dariya , shima dariyar yake yi haka zalika wasu daga cikinsu sun d’an murmusa ,

Sehrish tagane sa shine wanda ta fara zuba ma abinci mai kyakkyawan murmushin nan

“n6a kusa da shi kuma fawan kusan halinsu daya da Junaid ,  sai jabir da irfan basu da matsala in dai ba tsokanarsu akayi ba.”

Murmushi sehrish tayi taji dadin wannan gabatarwar , sai dai ranta na bata cewa wadannan kananun ne , akwai sauran mutun goma daga cikin sojojin da basa nan , su kuma koya zasu kasance !?

A tare da azmi suka yi saving dinsu abincin har suka kammala kowannnen su ya kama hanyar makwancinsa , tattara  plates din da kulolin sukayi a tare suka kakkauda komai izuwa ma’ajiyarsa ,

daga nan sehrish tayi ma azmi sallama ta koma bedroom dinta , tana mai jin dadin fara kasancewarta a wannan awesome family din Babbar damuwarta shine , da tazo a matsayin namiji a maimakon mace batasan ya abun zai kasance ba ranar da asirin ta ya tonu.

Tunda samu gadon nan ta haye ta soma minshari bata kara sanin meke wakana ba sai da tajiyo kwankwasar kopar da azumi take yi mata ,

A firgice ta farka tana neman mayafin da take nad’e kanta da shi , can ta hangosa kasa ashe anan tayi wurgi dashi, daukowa tayi ta hanzarta daure kanta dashi, sannan ta tashi ta nufi kofan ta bude mata, fara’a azmi ta sakar mata ” am sorry na Katse maka bacci ko naga ana kiran sallah ne raina ya bani baka yi ba nasan an sha gajiyar tafiya ga aikin da mukayi da dare ,”

Cikin y’ake sehrish tace “a’a wlh naji dadi da ki ka tashe ni saboda banyi sallah ba amma ynx zanje na yi,

Azumi tace “ok in ka  kammala karfe 7 ka fito akwai aikin breakfast na jiran mu”  reeshi ta amsa da “toh ” sa’annan tajuya ciki”

Cikin sauri ta shiga toilet, sai da tafara cire gashin bakin da aka sa mata ta tura sa cikin aljihun wandon ta, sannan taje bakin fanfo ta daura alwala , ta fito tana yarfa hannun ta, hijabi ta dauko ta zura sannan ta shimfid’a kafet, ta soma yin sallar,

Bayan ta kammala sallar wata irin hamma ta rinka ji, ga bacci bai ishe ta ba ga kuma yunwa don jiya da daddare bata nemi abincin ba gashi available

Agogon dake manne jikin bango ta kalla akwai sauran lokaci don haka sai ta baje saman sallayar taci gaba sharar bacci, ba ita ta tashi ba sai wurin karfe 9 na safe  hankali a tashi ta wartsake, ganin cewa wannan ce rana ta biyu da fara aikinta gashi zata fara bada matsala, cikin hanzari ta cire hijab dinta ta hada da kafet din sallan ta adana su a saman gadonta, sannan ta zaro gashin bakinta da take likawa ta manna sa a fuskarta, ta gyara nad’in mayafin kanta ta fi ce,

A kitchen ta Sami azmi ta kammala shirya komai na kalacin safen , duk sai taji ba dadi sukuku ta isa gare ta ta ce “barka da safiya nayi laifi dan Allah ayimun uziri,”

Babu alamun bacin rai a fuskar azmi ta ce ” karka damu tukur, ba wani abu nan gaba dae aguji yin hakan”

Sehrish ta amsa da toh insha Allah yanzu wani aiki zan yi ?

Ba wani aiki kawai abunda ya rage ynx  kabi bedrooms din kowannan su ka Sanar dasu su fito su yi breakfast ya kammalu,”  azmi ta karashe maganarta ta tana kallon ta,

Cikin zullumi sehrish ta fita ta tunkari jerin dakunan dake a downstairs , na farko ta fara kwankwasa wa shiru ba’a bude ba , kara knocking tayi da karfi , har sai da ya isarwa mai dakin , muryarsa tajiyo ashake yana cewa “who’s trying to disturb me? d’aga murya tayi tare da cewa “tukur ne sabon mai aiki,”

“Shigo ciki” ya ba ta izni , turo kofar tayi tare da kutsa kai ciki, har cikin ranta dakin ya yi mata kyau bedroom kamar na mace saboda kyau ga tsafta sabanin wasu mazan da idan ka shiga dakunansu kamar wurin safkar y’an gudun hijra saboda tsaban tarkace da har mutsi,

“Idan ka kammala kalle kallen naka sai ka sanar dani abunda ya kawo ka,” muryarsa ce ta dirar mata a kunne sai lokacin ta mayar da idonta akansa , kwance yake a baje  saman katafaren gadonsa rabin jikinsa yayi covering dinsa da lallausan blanket , Yusif kenan

Cikin en ina sehrish ta ce “am ..emm dama an kammala breakfast ne shine aunty azmi tace nazo na sanar daku.”

ta kammala maganarta ta tana wasa da yatsun hannunta , jin shirun bai ce komai ba ya sa ta dagowa ta saci kallonsa , samun shin tayi yana yamutsa fuska alamar an takura masa cikin lallausar muryarsa ya ce “Idan ina jin yunwa ai ba sai anzo an tayar dani ba ni zanzo da kaina ciki na ne ko cikin wani? ya tambaya yana kallon ta ,

Cikin sauri tace “cikin ka ne” ok fi ce ka ban wuri , ya fada tare da jan bargonsa ya idasa rufe face dinsa ,

Kamar wacce kwai ya fashe mawa a kai haka ta fita salalau salalau , a cikin ranta kuwa tana jinjina ma isa irin tasa ” tab aiki y ganni ni sehrish daga abun arziki, wannan shi ake kira da samun wuri tusar asuba, Allah sarki mukam ya’yan talakawa don uban mutun kar Allah yasa ya nemi abinci har rana ta fadi ya ga in za’a a damu dashi kasha iya barcinka yunwa ta taso ka, ka lallaba ka je neman kason ka wani sa’in ma an manta dakai, su kam wadandannan genius din bibiyarsu akeyi suzo suci suna make wa,”

Ta karasa tunanin nata a dai dai lokacin da tazo kofar dakin the next person , knocking tyi  bugu d’aya taji ance “Come in”

turo kofan tayi ta bude Samun shi tayi zaune saman sallaya jikinsa sanye da jallabiya ga kur’ani yana karantawa gwanin burge w, da alama wannan zaiyi saukin kai a cewarta

“Barka da safiya yallabai an tashi lafiya” sai da ya kai aya sannan ya juyo ya kalle ta ya ce “da ban tashi lpy ba zaka ganni ina karatun Qur’ani ne?  to fah ta ambata acikin zuciyarta , shin mai ya kawo ka ma tukunna ? ya tambaya yana kallon ta a matsayin namiji,

Muryarta na rawa tace “dama an kammala breakfast ne shine …..” Interrupting dinta yayi tare da cewa “shine me ? kai shashashan ina ne da zaka fadowa mutun haka kawai tunda sanyin safiya,kama hanya ka fi ce tunkan nayi football dakai”  (Jahan).

Jiki na rawa Sehrish ta fi ce zuciyarta na bugawa saboda tsananin tsoro, dafe kirjinta tayi domin ta samu natsuwar karasawa ga daki na gaba,zullumin ta kar asamu wanda zai kai mata duka don ta lura cewa fusatattu ne, ba mai sauki a cikinsu farawa da iyawa ta fara fuskantar haka nan gaba batasan mezai biyu baya ba.

Next room kwankwasa tayi tana jira taji an bata iznin shiga amma shiru , sake buga kofan tayi da d’an karfi da alama kowanane mamallakin dakin nan ya datse kofar ne,

Jin alamar ana tunkaro kofar yasa ta natsuwa, bude kofar yayi fuskar nan a daure kamar Alkubus “lafiya”? ya ambata rai a bace.

Har ta bud’e baki zata yi magana tajiyo muryar wani daga can cikin ɗakin yana cewa “Wai wane ne”?

“Wannan shashashan sabon mai aikin ne,” wanda ke tsaye a gabanta ne ya basa amsa, sai lokacin ta gane cewa dakin twins ne wato kamar yadda suke y’an biyu haka ma wurin kwanansu d’aya ,”

Tuni taji zufa ta ke to mata ganin wancan dake daga ciki ya taso , dukkan su sleeping dress ne riga da wando ajikinsu kala daya milk colour masu kyan gaske,

Jerawa suka yi tsaye a gabanta kowanne na kallonta alamar sun ma rasa wane hukunci zasu yi mata saboda ta katse masu baccinsu,

Gudun kar ta ja ma kanta bugu yasa ta ce “Am…Da ma breakfast ne an kammala shine aunty azmi tace a zo a sanar daku,”

Kallon juna su kayi tare da cizon labba atare, Ayaan ne yasa hannunsa ya kamo kunnanta ya idasa shigo wa da ita ciki , ba karamin zafi sehrish taji ba har sai da tad’an saki y’ar kara “ko da gigin wasa next time ka kara attempting zuwa tashe mu bacci na rantse saika yabawa aya zaki sususu kawai,”  ya karasa maganar tare da sakin kunnan nata cikin sauri sehrish ta fice tana sharar kwalla don ba karamin zafi taji ba,

Sai da ta samu wuri ta tsugunna ta gama matse yar kwallarta sannan ta tunkari sauran dakunan kowane daki taje da abunda zata tarar na wulakanci, yanzu dai gashi ta tunkari saman bene last room da ya rage ta shiga,

Sai da ta tabbatar ta share dukkan ruwan hawayen da ya zubo mata sannan ta kwankwasa , kusan 3 times tana knocking a na karshen ne taji wata sanyayyiyar murya tace” shigo ciki.”

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

Page 11-12

‘Yan kame-kame ta shiga yi hankali a tashe tana wurwurga ido, ” wannan d’an daudun daga ina kuma aka samo shi?” Daya daga cikinsu ya tambaya yana kallon ta , hantar cikinta ce ta ji ta kad’a , su duka sauraren ta suke yi su ji mai zata ce?

Motsi ta soma yi da lips dinta alamar tana so ta ce wani abu “Amm… Amm..” Duk ta bi ta dabarbarce. Jin muryar Azumi yasa Sehrish sauke ajiyar zuciya, karasowa ta yi tana fadin “Afuwan y’an samari ban yi maku bayani game da sabon d’an aikin da aka kawo domin ya rinka taya ni aiki ba.”

Kasa kunne suka yi suna sauraron ta , dafa kafadar Sehrish ta yi tare da cewa “Sunan shi tukur daga yau zai rinka taya ni aikace aikacen cikin gidannan ,’

Ta kare maganar tana kallon kowannan su tabe baki yyi  ba tare da sunce komai ba dama haka ta yi tsammani , don haka taci gaba da cewa “tukur bari na gabatarka maka da kowannan su saboda ka kiyayi zama dasu ,”ita dai ba ta ce komai ba saboda a rud’e take ,

Azumi ta soma gabatar mata da su daga na farko “Wadannan biyun da ka ke gani sune tagwaye  in ka lura komai nasu iri d’aya , suna da son zolaya musamman idan abun mugunta ne sun fi auki a nan na farkon sunansa Jahan shine babba sai twin brother dinsa Ayaan”

Tana gama wa dasu ta matsa na kusa dasu tace “wannan kuma sunan shi Kanal yusif sarkin tsafta , bai cika son surutu ba kuma baya son kallo , na gefensa kuma shine Khaleed bai da matsala shi indai za ayi masa abunda ya ke so ba tare da ya tambaya ba ,

Duk Sehrish na sauraron wannan bayanin na azmi , bayan ta kammala da na hannun damarta ta koma other side din taci gaba da cewa “wannan Junaid kenan sarkin murmushi, duk yadda za’a bata mai rai baya fushi sai in an kuresa , yana da son wasa faran faran da jama’a, burinsa a bashi kulawa  a bangaren ci kuwa ba’a magana ,” karasa maganar tayi tana y’ar dariya , shima dariyar yake yi haka zalika wasu daga cikinsu sun d’an murmusa ,

Sehrish tagane sa shine wanda ta fara zuba ma abinci mai kyakkyawan murmushin nan

“n6a kusa da shi kuma fawan kusan halinsu daya da Junaid ,  sai jabir da irfan basu da matsala in dai ba tsokanarsu akayi ba.”

Murmushi sehrish tayi taji dadin wannan gabatarwar , sai dai ranta na bata cewa wadannan kananun ne , akwai sauran mutun goma daga cikin sojojin da basa nan , su kuma koya zasu kasance !?

A tare da azmi suka yi saving dinsu abincin har suka kammala kowannnen su ya kama hanyar makwancinsa , tattara  plates din da kulolin sukayi a tare suka kakkauda komai izuwa ma’ajiyarsa ,

daga nan sehrish tayi ma azmi sallama ta koma bedroom dinta , tana mai jin dadin fara kasancewarta a wannan awesome family din Babbar damuwarta shine , da tazo a matsayin namiji a maimakon mace batasan ya abun zai kasance ba ranar da asirin ta ya tonu.

Tunda samu gadon nan ta haye ta soma minshari bata kara sanin meke wakana ba sai da tajiyo kwankwasar kopar da azumi take yi mata ,

A firgice ta farka tana neman mayafin da take nad’e kanta da shi , can ta hangosa kasa ashe anan tayi wurgi dashi, daukowa tayi ta hanzarta daure kanta dashi, sannan ta tashi ta nufi kofan ta bude mata, fara’a azmi ta sakar mata ” am sorry na Katse maka bacci ko naga ana kiran sallah ne raina ya bani baka yi ba nasan an sha gajiyar tafiya ga aikin da mukayi da dare ,”

Cikin y’ake sehrish tace “a’a wlh naji dadi da ki ka tashe ni saboda banyi sallah ba amma ynx zanje na yi,

Azumi tace “ok in ka  kammala karfe 7 ka fito akwai aikin breakfast na jiran mu”  reeshi ta amsa da “toh ” sa’annan tajuya ciki”

Cikin sauri ta shiga toilet, sai da tafara cire gashin bakin da aka sa mata ta tura sa cikin aljihun wandon ta, sannan taje bakin fanfo ta daura alwala , ta fito tana yarfa hannun ta, hijabi ta dauko ta zura sannan ta shimfid’a kafet, ta soma yin sallar,

Bayan ta kammala sallar wata irin hamma ta rinka ji, ga bacci bai ishe ta ba ga kuma yunwa don jiya da daddare bata nemi abincin ba gashi available

Agogon dake manne jikin bango ta kalla akwai sauran lokaci don haka sai ta baje saman sallayar taci gaba sharar bacci, ba ita ta tashi ba sai wurin karfe 9 na safe  hankali a tashi ta wartsake, ganin cewa wannan ce rana ta biyu da fara aikinta gashi zata fara bada matsala, cikin hanzari ta cire hijab dinta ta hada da kafet din sallan ta adana su a saman gadonta, sannan ta zaro gashin bakinta da take likawa ta manna sa a fuskarta, ta gyara nad’in mayafin kanta ta fi ce,

A kitchen ta Sami azmi ta kammala shirya komai na kalacin safen , duk sai taji ba dadi sukuku ta isa gare ta ta ce “barka da safiya nayi laifi dan Allah ayimun uziri,”

Babu alamun bacin rai a fuskar azmi ta ce ” karka damu tukur, ba wani abu nan gaba dae aguji yin hakan”

Sehrish ta amsa da toh insha Allah yanzu wani aiki zan yi ?

Ba wani aiki kawai abunda ya rage ynx  kabi bedrooms din kowannan su ka Sanar dasu su fito su yi breakfast ya kammalu,”  azmi ta karashe maganarta ta tana kallon ta,

Cikin zullumi sehrish ta fita ta tunkari jerin dakunan dake a downstairs , na farko ta fara kwankwasa wa shiru ba’a bude ba , kara knocking tayi da karfi , har sai da ya isarwa mai dakin , muryarsa tajiyo ashake yana cewa “who’s trying to disturb me? d’aga murya tayi tare da cewa “tukur ne sabon mai aiki,”

“Shigo ciki” ya ba ta izni , turo kofar tayi tare da kutsa kai ciki, har cikin ranta dakin ya yi mata kyau bedroom kamar na mace saboda kyau ga tsafta sabanin wasu mazan da idan ka shiga dakunansu kamar wurin safkar y’an gudun hijra saboda tsaban tarkace da har mutsi,

“Idan ka kammala kalle kallen naka sai ka sanar dani abunda ya kawo ka,” muryarsa ce ta dirar mata a kunne sai lokacin ta mayar da idonta akansa , kwance yake a baje  saman katafaren gadonsa rabin jikinsa yayi covering dinsa da lallausan blanket , Yusif kenan

Cikin en ina sehrish ta ce “am ..emm dama an kammala breakfast ne shine aunty azmi tace nazo na sanar daku.”

ta kammala maganarta ta tana wasa da yatsun hannunta , jin shirun bai ce komai ba ya sa ta dagowa ta saci kallonsa , samun shin tayi yana yamutsa fuska alamar an takura masa cikin lallausar muryarsa ya ce “Idan ina jin yunwa ai ba sai anzo an tayar dani ba ni zanzo da kaina ciki na ne ko cikin wani? ya tambaya yana kallon ta ,

Cikin sauri tace “cikin ka ne” ok fi ce ka ban wuri , ya fada tare da jan bargonsa ya idasa rufe face dinsa ,

Kamar wacce kwai ya fashe mawa a kai haka ta fita salalau salalau , a cikin ranta kuwa tana jinjina ma isa irin tasa ” tab aiki y ganni ni sehrish daga abun arziki, wannan shi ake kira da samun wuri tusar asuba, Allah sarki mukam ya’yan talakawa don uban mutun kar Allah yasa ya nemi abinci har rana ta fadi ya ga in za’a a damu dashi kasha iya barcinka yunwa ta taso ka, ka lallaba ka je neman kason ka wani sa’in ma an manta dakai, su kam wadandannan genius din bibiyarsu akeyi suzo suci suna make wa,”

Ta karasa tunanin nata a dai dai lokacin da tazo kofar dakin the next person , knocking tyi  bugu d’aya taji ance “Come in”

turo kofan tayi ta bude Samun shi tayi zaune saman sallaya jikinsa sanye da jallabiya ga kur’ani yana karantawa gwanin burge w, da alama wannan zaiyi saukin kai a cewarta

“Barka da safiya yallabai an tashi lafiya” sai da ya kai aya sannan ya juyo ya kalle ta ya ce “da ban tashi lpy ba zaka ganni ina karatun Qur’ani ne?  to fah ta ambata acikin zuciyarta , shin mai ya kawo ka ma tukunna ? ya tambaya yana kallon ta a matsayin namiji,

Muryarta na rawa tace “dama an kammala breakfast ne shine …..” Interrupting dinta yayi tare da cewa “shine me ? kai shashashan ina ne da zaka fadowa mutun haka kawai tunda sanyin safiya,kama hanya ka fi ce tunkan nayi football dakai”  (Jahan).

Jiki na rawa Sehrish ta fi ce zuciyarta na bugawa saboda tsananin tsoro, dafe kirjinta tayi domin ta samu natsuwar karasawa ga daki na gaba,zullumin ta kar asamu wanda zai kai mata duka don ta lura cewa fusatattu ne, ba mai sauki a cikinsu farawa da iyawa ta fara fuskantar haka nan gaba batasan mezai biyu baya ba.

Next room kwankwasa tayi tana jira taji an bata iznin shiga amma shiru , sake buga kofan tayi da d’an karfi da alama kowanane mamallakin dakin nan ya datse kofar ne,

Jin alamar ana tunkaro kofar yasa ta natsuwa, bude kofar yayi fuskar nan a daure kamar Alkubus “lafiya”? ya ambata rai a bace.

Har ta bud’e baki zata yi magana tajiyo muryar wani daga can cikin ɗakin yana cewa “Wai wane ne”?

“Wannan shashashan sabon mai aikin ne,” wanda ke tsaye a gabanta ne ya basa amsa, sai lokacin ta gane cewa dakin twins ne wato kamar yadda suke y’an biyu haka ma wurin kwanansu d’aya ,”

Tuni taji zufa ta ke to mata ganin wancan dake daga ciki ya taso , dukkan su sleeping dress ne riga da wando ajikinsu kala daya milk colour masu kyan gaske,

Jerawa suka yi tsaye a gabanta kowanne na kallonta alamar sun ma rasa wane hukunci zasu yi mata saboda ta katse masu baccinsu,

Gudun kar ta ja ma kanta bugu yasa ta ce “Am…Da ma breakfast ne an kammala shine aunty azmi tace a zo a sanar daku,”

Kallon juna su kayi tare da cizon labba atare, Ayaan ne yasa hannunsa ya kamo kunnanta ya idasa shigo wa da ita ciki , ba karamin zafi sehrish taji ba har sai da tad’an saki y’ar kara “ko da gigin wasa next time ka kara attempting zuwa tashe mu bacci na rantse saika yabawa aya zaki sususu kawai,”  ya karasa maganar tare da sakin kunnan nata cikin sauri sehrish ta fice tana sharar kwalla don ba karamin zafi taji ba,

Sai da ta samu wuri ta tsugunna ta gama matse yar kwallarta sannan ta tunkari sauran dakunan kowane daki taje da abunda zata tarar na wulakanci, yanzu dai gashi ta tunkari saman bene last room da ya rage ta shiga,

Sai da ta tabbatar ta share dukkan ruwan hawayen da ya zubo mata sannan ta kwankwasa , kusan 3 times tana knocking a na karshen ne taji wata sanyayyiyar murya tace” shigo ciki.”

Comment and share

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

💖💖💖💖

💖💖💖

💖💖

💖 *ABBAN SOJOJI* 💖

💖💖

💖💖💖

💖💖💖💖

“`The father Of Soldiers“`

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 13-14

Da sallama tashi ga wani irin daddadan kamshi ne ya ratsa hancin ta, har sai da tasa hannu ta d’an matse hancin saboda scent din ya kai mata karo,

Samun shi tayi a kwance tsakiyar gado wani irin sabon salon kwanciya da bata taba gani ba, up yake fuskanta ya rungume fillow a kirjinsa ga wani filon a tsakankanin laps dinsa ya makalkalesa, fuskar nan dauke da murmushi just like always, Junaid kenan sarkin smiling,

Karasawa tayi gaban bed din yadda zaiji ta dakyau ta ce “barka da safiya’  Zuciyarta na mata dar dar gudun karya yi mata abunda sauran su kayi mata,

A hankali ya bude idonunsa ya sauke su akanta “menene”? ya ambata cikin kasalalliyar murya,

“Breakfast ne ya kammala” ta fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa da jajayen lips dinsa,

Cikin shagwaba ya ce”wlh naji dadin zuwanka tukur dama tundazu nakeso na tashi kasala ta hanani pls taimaka min na mik’e” ya idasa maganar tare da mika mata hannunsa ,

Waro ido waje tayi domin wannan yafi sauran iyayi, fuskarta tamkar zata yi kuka gaba daya ta rasa me zata yi tun nan sehrish tagane kuskuren da ta tafka na zuwa amatsayin namiji bata da wani zabi fa ce tayi abunda ya ce if not her secrets will expose,

Mika masa hannunta tayi ya ruko cikin nasa, nan take taji wani irin yanayi a tattare da ita mara misaltuwa, lallausar fatan hannunsa ba karamin gigita ta tayi ba saboda softness dinta, a cikin ranta tace “wannan wani irin hannu ne mai laushin gaske da dadin tabawa, daga jin wannan hannun bai taba wanki ba,”

Gam ya ruke hannun nata a yunkurin ya taso ya janyo ta gaba d’aya ta rikito ta fada masa, dalili kuwa karfinsa ya rinjayi nata nesa ba kusa ba,

Wani irin bugu zuciyarta ta shiga harbawa duk tabi ta susuce ta rasa inda zata tsoma kanta, tashi ga yanayi mara misaltuwa, tsigar jikinta duk ta tashi tsaye hai kam, karo na farko da ta fada jikin namijin da ba muharramin ta ba, gashi ko riga babu jikinsa d’an short ne dai-dai guiwarsa,

Kamar anyi mutuwa haka sukayi tsit, junaid kam yarasa meyasa yaji tamkar maca ce ta fada masa a jikinsa shaukin daya ji ya basa mamaki, ita kam sehrish ji take kamar an manna mata magnet a jikinsa sam tagaza yunkurin tashi

Kasala ce ta rufe mata jiki sai da ta tattaro dukkan sauran karfin daya rage mata a jikinta ta yunkura ta mik’e cikin sauri ta zame jikinta daga nashi ta fi ce da gudun gaske kamar walkiya haja yake kallon lamarin,

Tunaninsa me yasa d’an aikin ya shiga feelings haka kodai d’an daudu ne mai bin maza ba shakka kuwa haka ne, ya fada aransa

A bangaren sehrish kuwa da ta fita a guje dakinta ta koma, tana tura kofar tashiga ta maidata ta datse sannan ta jingina da kofan tana shesshekar kuka,

ta riga da ta san ta yi kuskure tun farko cikin raunanninyar muryarta ta furta ” Omg! i ave made a mistake Ya Allah makes it easy for me,

A cikin 2 weeks sehrish ta gama fita hayyacin ta, a tunanin zata huta a wannan katafaren gidan amma ashe ba haka bane, aikinsu Junaid kamar zai kashe ta, ga wani karen tsana da twins dinnan Jahan da Ayaan suka sa mata, yini take tana aiki tun safe har dare basa so suga tana hutawa sunfi so suga tana aiki kamar ansa mata battery, kullum sai azmi ta turata taso su suzo suci kalacin su na safe, haka Zata bi dakin kowannansu daya bayan d’aya, kowa taje tadawa da irin wulakancin da zata kwasa saboda jan kunnanta da suke yi har fatar kunnan tayi jawur, ga gyaran dakunansu, wanke toilet dinsu, gugar kayansu duk ita ke yi, wani lokacin ma idan suka ga babu aiki tana hutu sai su tattaro kayansu dake cikin laundry basket su bata ta wankesu tas, in azmi tace musu ba da injin wanki suke amfani ba dak sai suce ae wankin hannu yafi fidda kaya suyi kyau,

Baiwar Allah lokaci guda ta zama wata zararriya wani sa’in ko bacci take yi sai ta dinga jin muryoyinsu nayi mata gizau a kunnanta suna cewa “tukur tukur tukur kur ”

Girki kad’ai azumi ke yi saboda sunce sauran aiyukan bana ta bane na d’an uwansu namiji ne wato tukur mai aikinsu,

Akwai lokacin da suka shigo atare suka same ta, ta kammala goge goge tayi aiki ta gaji, ta samu wuri saman 3 seater ta kwanta tana hutawa asalima batasan bacci ya dauke ta ba,

Kayan wanki suka shiga suka dauko kowa dana sa, bata yi aune ba sai  dai taji ana zazzage mata jibgin kaya a jikinta, haka take faman hakuri dasu,

Yau ba ta makara wurin shiga kitchen ba, azumi ta taras tana gyara naman kaji, ba qaramin mamaki azmi ke bata ba sam ba ta gajiya da aiki kamar engine, gashi ta kware a wurin iya sarrafa abinci ta iya girki

“Barka da safiya aunty azmi” ta fada tana kallon ta , da murmushi a fuskarta tace “yawwa mlm tukur ya gajiyar jiya? Sehrish ta ce “Alhamdllh”

“Yau ba a makara ba kenan” azmi ta tambaya,  sehrish  ta ce “eh”

Zame hannun tayi daga gyaran naman da take yi, can cikin kitchen din tashi ga kofar da store yake ta bude, wasu manyan doyoyi ne ta dauko guda 3 lafiyayyu, tazo ta ajiye a saman table din da suke yanke yanke a saman sa da sauransu, ” gasu nan a fere su da kyau in ka gama ka shiga store za ka ga crack din kwai ka debo 20 a cikin roba a farfasa su,”

Amsa wa kawai take da toh, wuka ta dauko ta fara daddatsa doyar , a natse take ferewa , junaid ne ya fado mata a ranta tunaninsa ta soma yi “har yanzu nagaza gane masa ni bansan meyasa ya ke da shagwaba ba kamar karamin yaro  gashi da shiga rai uwa uba ga kyau kai dukkansu ma kyawawa ne idan har akace mun na zabi daya cikinsu to tabbas zanyi ruwan ido, amma fa gaskiya junaid na daban ne inason namiji mai shagwaba mai kyakkyawan murmushi domin murmushi alama ce dake nuna cewa mutun nada saukin kai, matsala da shi son jikin tsiya shi a tunaninsa ni namiji ce baijin komai ya rika ruko mun hannu baisan yana sani cikin yanayi ba.

Muryar azmi ce ta katse mata tunanin nata “sai kayi sauri fa tukur naga alamar yau shiririta kake ji,”

Mayar da hankalin ta tayi ta ci gaba da ferar doyar, bayan tagama tayi mata shape, gaban tap taje ta zuba ruwa ta wanke ta tas, ta dawo kan eggs din da cokali ta farfasasu ta dauko Whisk abun ƙaɗawa ta k’ada shi ya haɗe jikinsa, kayan kamshi azmi ta miƙa mata ta karba ta zuzzuba a ciki, bayan tagama ta shiga soya wa da doyar.

A kalla suna yin abinci kusan kala 8 na breakfast hada kayan snacks irinsu bugger, donuts, pancake, soyayyiyar ayaba (plaintain) chips doya da kwai, chicken pper soup, pasta wit stew , coffee , slide bread, gasasshen kifi, fried meat tarkace iri iri ,

Mafi rinjayen aiki azmi ke yi hakan ba karamin taimakon sehrish ta yi ba saboda bakomai ta iya ba,

“Ka je ka fara tado su lokaci karya kure tunda mun kammala da wuri” A cewar azmi da take shisshirya kayan abincin wanda zata je ta jera a dining,

fita sehrish tayi da sauri gaban ta na ɗar ɗar gudun abunda zata taras wurinsu,

Dakin kanal yusif ta fara zuwa, bayan ya bata iznin tashigo, ganin shi daga shi sai short towel a west dinsa ya sa ta yin ƴan kame Kame da alama daga wanka ya fito duba da yadda ruwa ke ɗigɗiga daga jikinsa,

Sam ta gaza control ɗin kanta har sai da ya juyo ya kalle ta dayake a gaban dressing mirror yake, ganin yadda mai aikin ya zuba masa ido yasa shi jan dogon tsaki tare da cewa “Stupid ! Why are you Looking at me? Ina namiji kana namiji amma kake kallo na anya kai ba ɗan iska ba ne?

Sunkuyar da kanta ta yi tare da cewa, “An gama shirya…’ Bai bari takarasa ba ya ce “Na ji but this is the last warning da zan yi maka as from today bana bukatar sai an zo an sanar da ni in sauko in ci abinci,”

Cikin girmamawa ta amsa masa da ta toh insha Allah hakan bazai sake faruwa ba, fi ce wa tayi ta wuce dakin khaleed har cikin zuciyarta taji dadin abunda yusif ya ce mata saboda ita hutu ne a gare ta,

Shima khaleed kusan hakance ta faru ya ce baya bukatar ana zuwan masa ɗaki da safe haka indai ba shi ya bukata ba,

Wuce wa tayi dakin twins kwankwasa tayi taji shiru ba a bata izinin shiga ba amma kofar a bud’e take, a matsayin ta na me ragaggen hankali sai ta kutsa kai tashi ga kwata kwata babu su a saman gadonsu sai dai wani abu daya tayar mata da hankali, gurnani da wani irin nishi tadinga ji daga cikin toilet dinsu alamun akwai mutun ciki kona ce mutane ciki, tamkar ana sukuwa saman doki yanayin sautin.

Hakan ba karamin firgitar da ita yayi ba sai ranta ya riƙa bata cewa kodai wani ne bai lafiya a cikin toilet ɗin da bukatar tayi sauri taje ta sanarwa azmi abunda ke faruwa, juya wa tayi da sauri zata fita sai taji ana koƙarin buɗe kofan, tsayawa tayi tana kallon kofan toilet ɗin taga ikon Allah, a tare suka fito daga toilet din Ayaan ne ya fara fito wa sai jahan biye a bayansa dukkansu sanye da gajeran towel a ƙugunansu,

Gaba ɗaya tabi ta firgita sam basu lura da ita ba don haka ta lallaba ta fice cikin saurin,

Jikin ta a mace take tafiya abubuwa iri iri ne suke zo mata a ranta ” dama mutum biyu na shiga toilet a lokaci ɗaya, menene dalilinsu nayin hakan? Shin nishin da naji da gurnanin nan na menene ? Allah wa alamu ta tambayi kanta sam ba ta kawo wa ranta wani abu ba amma hakanan take jin tabbas da akwai matsala a tattare da twins din nan.

Bedroom din fawan ta wuce tun kan tashi ga take jin sa yana waya, tsayawa tayi bakin kofan tana saurarinsa  “baby nifa bana so a samu matsala bakisan halin yayyen mu ba muddin suka gane cewa ina mu’amala da mata to tabbas sai sun kusa kashe ni,”

Rass taji gabanta ya faɗi ” mu amala da mata kuma wata irin mu’amala kenan?

Ta jefa wa kanta tambaya zuciyar ce ta bata amsa “duk wata mu’amala da mutun ke gudun a san yanayin ta to tabbas ba mai kyau bace,”

Wani irin miyau ta haɗiye lokacin da ta samu amsar tambayarta , sai da ta samu natsuwa sannan ta kwaɗ’a sallama,  jin muryar mai aikin nasu yasa fawan saurin yin rejecting kiran ya yi throwing phone ɗin nasa saman gefensa, rai abace yace ” wai wanene ”

Ko izinin shiga ba ta samu ba, murya na rawa ta ce “tukur ne dama an kammala shirya breakfast ne”

Wani irin dogon tsoki ya ja tare da cewa” Naji sai me”?

Jiki a sanyaye sehrish tabar kofan ɗakin nasa ta wuce na irfan, ita kanta ta shaida cewa yau babu sa’a ynx fargabanta me zata taras ɗakin sauran.

💖💖💖💖

💖💖💖

💖💖

💖 *ABBAN SOJOJI* 💖

💖💖

💖💖💖

💖💖💖💖

“`The father Of Soldiers“`

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 15-16

Kwankwasa kofar ɗakin nasa tayi , da wata irin kakkausar murya taji ya amsa mata da cewa”Uban wanene” kai kanaji kasan yasha ya bugu har takai masa aka.

Saboda tsoro bata basa amsa ba ta yi gaba da sauri, tun a lokacin ta gane cewa tabbas akwai matsala kuma sam bai kamata tana bin kowannan su ɗaki don tayar dasu ba, ta gama yanke shawarar sanarwa azmi cewa baza ta ƙara zuwa ba, tun da cikinsu ne in suna jin yunwa dakansu zasu fito su nema.

Gaba ɗaya a firce take da lamarin kan ta ya gama ɗaure wa, ɗakin Jabeer ta wuce tana sa hannu ta kwankwasa kofa , tana jiyo har mutsinsa ta ciki sallar karya ya kabbara , shiga ciki tayi abun saiya daure mata kai,  Sallah karfe 9 na safe.

Har zata juya idon ta ya hango mata kwayoyi na shaye~shaye ga kwalabe kuma a gabansa.

Shi duk a tunaninsa yayansu ne kanal yusif amma jin shiru yasa shi katse sallar ya ɗago ya kalle mai aikin, wani mugun kallo ya wurga mata tare da nuna mata hanyar fita ya ce ” karka kuskura ka ƙara zuwan min ɗakina in ba haka ba saina canzama kamanni shashasha,”

Abun da bai sani ba ita sam ba ta san kwayoyin menene a gabansa ba, a tunaninta bai da lafiya ne shine ya ajiye magunguna zai sha.

Ficewa ta yi a ranta tana cewa” Allah ya ba ka hakuri,”

Saura ɗakin shagwababben sarkin murmushi, har tsoran zuwa ta ke yi saboda manne mata da yake yi,

Tunkan ta shiga take jin muryasa yana faɗin “Coffee i need coffee pls ” cikin magagin bacci ya ke wannan sambatun na neman coffee,

knocking tayi masa kusan sau uku kafin taji muryarsa yana cewa “wanene shigo ciki mana,”

Gyarawa tayi ta shiga ciki samun shi tayi kamar yadda ta saba samun shi irin kwanciyar nan tasa daya saba, kamar wani karamin yaro haka yake,

Karasawa tayi gabansa tare da cewa”barka da safiya junaid , tukur ne,” ta idasa maganar tana kallon cikin idonsa daya buɗe,

A duk lokacin da ta kalle sa wani irin natsuwa da kwanciyar hankali ne ke shigarta, murmushi taga yana sakar mata dimple din nan nasa masu lotsawa guda biyu suka bayyana,

“Ohh tukur ne am really happy to see u, dama yau inaso ka taimakamin tun jiya nakeson wanke sumar kaina na kasa amma yau kam tare zamu shiga toilet ka taimakamin,” a wani shagwab’e ya ke maganar.

Sehrish kuwa waro ido waje tayi jin abun da ya ce wannan da alama wata rana cewa zaya yi tayi masa wanka,

Cikin sanyin murya ta ce “ka yi hakuri dan Allah ba yadda za’ai na bi ka toilet sam a tsarin aiki na a gidan nan ba’a ba mai aiki izinin yin hakan ba,

Wani irin kallo ya wurga mata kafin ya ce” wa ye wanda ya tsara wannan dokar? bayan ni ne silar da aka kawo ka aiki a gidannan, tukunna ma kai ba jinsina bane? to kodai maca ce tayi shigar maza bansani ba,”

Jin wannan maganar tasa yasa sehrish jin faɗuwar gaba tuni ƴan hanjin cikin ta suka ƙaɗa har ta soma tunanin anya Junaid bai gane cewa ita MACACE ba NAMIJI ba !? duk tabi ta rikita kanta

Muryarsa ce ta sake katse ta “Am asking you ! answer me,” dakyar voice ɗinta ke fita “ba haka bane, kawai a ganina bai da ce ba ina matsayin mai aiki nayi hakan,”

“I command you to do that! ae mu ne masu gidan kuma umarnin mu ake bi,”

Cike da isa junaid yayi maganar,ba yadda sehrish ta iya a dolen ta, tabi umarninsa, haka ya tashi yana yauƙi yana cika yana batse wa kamar bashi bane mai murmushin kashe zuciyarnan ba,

Miƙewa ya yi daga saman bed din ya sauko daga shi sai shorts a jikinsa, bin jikin shi tayi da kallo fari sol ba tarin gashin jiki a skin dinsa , ga kirarsa dai dai wa dai dai, kusan hasken fatarsa dana twins jahan da Ayaan ɗaya ne akan na sauran don haskensu ba irin na nan bane zai iyiyuwa cikin iyayensu akwai farar fata, mahaifiyarsu ko mahaifinsu,

“Idan ka gama kallon zamu iya shiga ciki ko” ya ambata yana kallon ta, gaba yayi cikin toilet din tabi bayansa zuciyarta na ɗar ɗar tsoranta kar ya ce zai cire shorts ɗinsa a agaban idonta batasan ya zata yi ba,

Da farga jikin ta na rawa ta dauko ɗaya daga cikin jerin shampoo dinsa na wanke kai, juya tayi da nufin ta nuna masa in da wanda ta dauko yake amfani kar asamu matsala, samun shi tayi yana kokarin cire shorts ɗin jikinsa, aiko a firgice ta saki roban shampoo ɗin ƙasa, ta karasa da gudu ta cafke hannayensa dake a saman mararsa gam ta ruke su, kallon juna suka shiga yi na wani lokaci, shi mamakinsa wai namiji ne ke gudun ɗan uwansa namiji a ganinsa is not a bad thing don ka cire kayanka gaban jinsin ka, ita kuwa miyau kawai take haɗiya gabanta na faduwa sai faman huci take kamar wadda ta yi ƴar tseral, Tuni hancin ta ya soma tsattsafo da zufa, tsoranta wane hukunci zai yi mata a sakamakon abunda tayi, ita dai tayi hakan ne don da abunda zata gani na tsiraicinsa kwara koma meye yayi mata tasan ba laifinsa bane, laifin ta ne da tayi shigar namiji,

Zame hands ɗinta tayi daga rikon da tayi masa, hannayenta ta aza a saman kanta tare da faɗin “nashiga ukuna am so sorry sir am just out of sense,” duk a riki ce tayi maganar,

‘Stop calling me sir! Cos may be am just your age mate, call me wit my name Junaid,

Ya karsa maganar tare da ƙara gyara gyara shorts ɗinsa yace ” get out of my sign,”

Cikin sauri ta nufi hanyar fita har ta 6uɗe kofan tajiyo muryarsa yana cewa” Am watching you!” juya kanta tayi ta kallesa da yatsunsa yayi mata nuni da idonsa alamar zai sa ido akanta,

Cikin sauri ta fi ce tana faɗin ” Insha Allah junaid bazaka gano komai ɗangane dani ba zan ta addu’a ina rokon Allah yaci gaba da rufamin asiri har nasamu na hada kudin aikin Husanna nabar maku gidanku,

ta fada acikin zuciyarta (abunda sehrish ba ta sani ba wannan gidan is part of her destiney)

Azumi ta kammala shirya musu abincin sai da kowannansu ya mula yasha iska sannan suka firfito, one by one duk sun shirya cikin kakin sojojinsu, banda mutun ɗaya junaid wanda ke sanye da  jeans a jikinsa tare da farar tshirt mai dogon hannu ta ɗanyi tighting ɗinsa,

Kowannan su ya samu wuri ya zauna, sehrish ce ta fito frm the kitchen don ta fara saving ɗinsu, azmi kuma ta wuce bedroom ɗinta don dama already ta sanar da ita cewa zata shiga ciki tayi wanka don tasha aiki,

Hannu ta har kekkerwa yake yi saboda tsananin tsoran guyabarsu, junaid ta fara kallo tare da cewa”me zan zuba maka’? Kafin ya buɗe baki ya yi magana fawan ya kar6e da cewa”saboda shine babba acikin mu !”

Ayaan ya ce “thats what i was trying to say! Wannan house boy din ba karamin ɗan iska bane shi junaid ɗin special salary ya ware maka ne ɗayasa kke kokarin fara zuba masa abincin? ya tambaya fuska a ɗaure yana kallon ta,

nan fa hankalinta ya tashi ita batayi don wani abu ba ashe abun yana damunsu,

Muryar Jahan ce ta katse ta “Nima na lura da haka in banda iskanci ka rasa wanda zaka fifita sai karamin kanin mu wanda ko aiki baya zuwa sai dai yazauna kamar mace a gida,’ ya ƙarasa maganar yana wurga masa harara.

Ran Junaid ba ƙaramin baci yayi ba, abun duk saiya bashi haushi musamman da Jahan yace masa kamar mace, wani irin ƙululu bakin ciki ne ya tsaya masa a maƙogwaronsa,

duk wannan abun da suke kanal yusif na jinsu bai ce komai ba haka zalika sauran y’an uwan nasa su irfan, sauraronsu kawai suke yi dama basu cika shiga faɗansu ba.

“Nima abunda nagani kenan Jahan kullum zaman kashe wando ya iya bai da wurin zuwa daga buga ball sai atake masa abinci a plate yaci yayi haikam ƙarshen wata nayi Babban yaya ya turo masa da dollars a account shiyasa gayanan duk yafi mu kyan gani,’ fawan ne yayi maganar yana kallonsa daya ke suna facing ɗin juna a table ɗin,

ganin yadda suke ta faman yada masa magana a gaban ɗan aikinsu tukur yasa shi cewa “Ya Isa haka ! Ku ce koma me zaku ce! in da na gode ma Allah ma ba da son raina nima nake zaune gidan ba! Ciwo ne kuma zai iya samun kowa acikin ku!,’ ya karasa maganar idonsa sun cicciko da kwalla,

Ran sehrish dake tsaye ba ƙaramin baci yayi ba ganin yadda manyan suka kasa dakatar dasu daga gaya masa magana musamman kanal yusif da yake babbansu a yanzu,

Dariya fawan yayi tare da cewa ” aikin kenan! daga magana ƙaɗan sai ka nemi zubarwa mutane da hayawa kamar kafi kowa ruwan hawaye a …’ bai idasa maganar ba yaji saukar ruwan tea mai zafi a fuskarsa Allah yaso ba tafasasshe bane, ihu ya saki tare da faɗin “innalallahi junaid baka da hankali ne! ni ka watsa wa ruwan tea! wlh bazan yarda ba saina rama,

Hannunsa ya zura ya dauki kular da farfesu ƴan ciki mai zafin gaske ke aciki ya yunkura zai watsa wa junaid, da gudu junaid ya tashi , shima fawan ɗin yabisa kamar tom& jerry haka suka rinƙa zagaye wurin,

Hankalin sehrish ba karamin tashi yayi ba bata ta6a sanin haka suke ba wannan ai sai suyi kisan kai.

Ga haushin ƴan uwan nasa da take ji hankalinsu kwance sai ma umarni da suka bata ta zuba masu abincin nasu su ci, saving ɗinsu take yi amma hankalin ta nakansu Junaid da fawan dake ta faman ƴan guje guje , tsoran ta kada fawan ya zuba masa farfesun nan a farar fatar nan tasa mai laushin gaske don tasan tuni zaiyi mummunar ƙuna.

Har ta kammala saving ɗinsu ta koma ɗaki cikin rashin kwanciyar hankali, a bangaren su fawan kuwa dake faman faɗa tunda junaid ya samu ya shige room ɗinsa ya datse kofar, a dole fawan ya haƙura a zuwan Zasu haɗu ne ae ba kwana zaiyi a rufe ba,

Gaba ɗayansu sun fita tana jin tashin motocinsu, cikin sauri ta fita domin da ma ta ƙagara su fita taje ta sanarwa junaid ko ya samu yazo ya ci kalacinsa,

A falo ta gamu da azmi tana goge goge, cikin girmamawa tace”sannu da aiki aunty azmi me zai hana ki bani na idasa aikin tun da dama ni nake yi kinyi aiki sosai nasan kin gaji,”

fuskarta a sake ta ce” kada ka damu tukur ai an jima na nan, yanzu dai abinda zaka yi kabi bedrooms ɗinsu ka gyaggyara tsaf don Allah,’

Sehrish ta amsa mata da toh wuce wa upstair tayi ɗakin junaid babbuga kofan tayi, muryarsa taji yana cewa”wanene”?

Gyara muryarta ta yi tare da cewa”tukur ne mai aiki dama naga baka ci breakfast ɗinka bane,’

Ɗan guntun tsoki yaja tare da cewa”Naji a kawomin a ɗaki na zanci,’

Amsa sehrish tayi da toh sannan ta juya time ɗin da ta sauko azmi har ta kamma gyara falon yayi fes gwanin burge wa sai ƙamshi dake tashi, kai matar taji daɗi ga iya girki ga iya gyaran wuri ya koma kamar sabo uwa uba ga kyan hali, sehrish ta faɗa a ranta tana dan murmushi,

Kitchen ta wuce nan ma ta samu azmi ta gyarasa komai tsaf, shirya masa abincin tayi a tray, ta koma ɗakinsa nasa sai da ta jira ya 6uɗe mata sannan ta shiga.

💖💖💖💖

💖💖💖

💖💖

💖 *ABBAN SOJOJI* 💖

💖💖

💖💖💖

💖💖💖💖

“`The father Of Soldiers“`

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 17-18

A wani madaidaicin table dake a bedroom ɗin nasa ta aza tray ɗin ta matsar dashi gabansa, yana zaune a gefen gadon yana daddana wayarsa,

satar kallon wayarsa tayi ba kowa ya faɗo mata a rai ba fa ce husanna da jahad tabbas tana bukatar tayi waya da su, amma babu hali cos bata da waya, kuma ba yadda za’ai ta ce zata ari wayar sa, hauka ma take yi ashe?

Muryarsa taji a kunnanta “Thank you zuwa nan da 30 mins ka dawo ka dauki tray ɗin,”

Ta amsa masa sannan ta fi ce, acikin ranta tana faɗin’ tabbas ya kamata nakira naji wani hali husanna da jahad suke ciki wayyo Allah na gashi na lura kamar aunty azmi bata da waya a hannunta,

A ɗakinsu twins ta tsaya domin gyarawa masu shi, a hargitse ta samu ɗakin sun tarwatsa komai, haka ta kama aikin gyara masu shi, bed ɗin ta soma gyarawa bed sheet din takai hannu zata cire, tsayawa tayi tana kallon wani abu a jikinsa, wani irin ruwa ne mai kitib kitib kamar kokko mai yawan gaske a jikin zanin gadon, tunani ta soma yi’ shin wannan menene ajikin zanin gadon a iya sani na gidan nan basa shan kokko to kodai madara ce ta zube a wurin gsky i na tunanin haka,

kasancewar zanin gadon maroon colour ne hakan yasa abun ya fito sosai raɗau, cike da jin kyankyami ta tattare bedsheet ɗin ta zuba a laundry basket ɗinsu,

Kammala gyaran gadon tayi sannan tayi mopping ɗin dakin tsaf ta gyara komai, gaban dressing mirror ɗinsu taje, mayuka tagani tsadaddun gaske iri iri, karaf idonta suka sauka akan wani kwalban magani, hoton dake a jikin kwalbar kawai take kwallo namiji da namiji ne zir babu kaya a jikinsu ɗaya yayi holding penis ɗin ɗayan,

Gabanta ne taji yayi mugun bugawa duk da batasan ma’anar hakan ba sai ranta ya bata cewa kawai magani ne na wani ciwon nasu na maza,

Kammala gyarawa tayi afterwards ta koma bathroom ɗinsu, anan ne fa kwalwarta ta ƙara rikice wa ganin wannan farin abun da tagani a bedsheets ɗinsu, gashi nan a har jikin bathtube ɗin ko’ina sun hargitsa shi, haka ta daure ta wawwanke ko’ina tass,

Bayan ta fito sai da ta sake duba kwalbar maganin nan a jiki taga an rubuta (Homosexual) shi kaɗai ta iya ganewa amma ita kanta bata san ma’anar kalmar ba don ba komai ta sani ba.

Sam ta manta da sakon junaid na ta koma after 30mins ta kwashi tray din abincin sa takai masa.

Sai da ta kammala gyarawa ɗakunan kowannansu ba ƙaramin gajiya ta kwasa ba, sauƙin ma ɗakunan sauran ba hargitsi ba kamar nasu Jahan da Ayaan ba,

Har yanzu sehrish ta gaza mantawa da wannan abun da tagani ɗakin su twins, akwai wani abu da ya tsaya mata a rai wanda take tuna shi da jima wa daya faru dasu tana kokwanton cewa kodai wannan abun ne, bakomai bane fa ce Sperm !!!

Tafiya take yi jikin ta a kasalance wata irin kasala ce ta dabaibaye ta, labari mara daɗin ji, abunda take kokarin yi musu shine (Kyakkyawan Zato)

Dakyar take taka matattalar benen, idonta a cike taf da hawaye ‘Ya Allah kada kasa abunda nake zargi ya tabbata Ya Allah kasa nayi aiki na ba tare da na fuskanci wata matsala ba cikin salama na tafi nabar masu gidansu, ni kuɗi kawai nazo nema domin na taimaki ƴan uwana dake kwance asibiti bayan wannna bana bukatar wani abu,

Tura kofan room ɗin junaid ta yi, samun shi tayi ya gama cin breakfast bacci ya kwashe sa, sai sharar baccinsa yake cikin kwanciyar hankali da natsuwa,

ɗan murmushi ta saki tare da cewa” Ya Allah ka tsare wannan bawan naka bansan halinsa ba amma ina yi masa kyakkyawan zato”

Hannu takai zata ɗauki tray din karaf idonta suka sauka akan wayarsa dake ajiye saman nightstand, ba komai ya fado mata a rai ba fa ce ta saci wayarsa ta kira goggonsu taji ya lafiyarsu Jahad, murmushi tasaki a hankali ta soma tafiya cikin sanɗa, saɗaf saɗaf ta tafi,

Sai da tasha wahalar daukar wayar tasa sannan taga ashe thumbpring gare ta, dole sai da yatsansa sannan za ta 6uɗe, ɗafe kanta tayi tare da faɗin “wayyo Allah na” dama sarar ta ce,

Juyawa tayi tana kallonsa yadda ya ke kwance yana baccinsa a natse, sama ya ke fuskanta ya wawware hannayensa, murmushi tasaki tare da fadin ‘abun zai zo mun da sauƙi,’

Hawa saman bed ɗin ta yi a hankali cikin sanɗa kamar mage, rarrafe a hankali tayi ta isa inda hannun damansa yake, yatsun hannunsa a buɗe suke gasu nan tsirara masu kyan gaske, bayan wayar ta juya inda thumbprint din ya ke, kwafa wa tayi a yatsansa na tsakiya, yasa mata wrong, matsar da wayar tayi ana gabansa cikin sa’a wayar ta bude, tsananin farin ciki ne ya bayyana a fuskarta, cikin sauri ta sauka ta lalla6a tafita ta tsaya a bakin kofan room din nasa, jikinta har kerma yake yi karta ya farka, tuni zufa ta soma tsastsafo mata a hancinta,

Time ɗin da ta aza idonta akan wayar, Hoton da tagani a wellpepper ɗinsa ne yasa jin zuciyarta wani irin bugu,

Zuba ma hoton ido tayi wato ainihin wani haɗaɗɗen matashin saurayi ne, ko a mafarki bata ta6a ganin mutun mai irin kyansa ba, kwayar idonsa ce tafi ɗaukar hankalinta, blue eyes ne da shi, wannan wani irin zazzafan kyau ne! irin wannan kyan shine mutane ke neman tsari da shi, jikinsa na sanye da kakin sojoji ba ƙaramin daukarsa su kayi ba, yayi hoton ne kamar a shirin film a saman mota yayi irin wannan zukunnawar da suke yi in zasu yi harbi da bindiga,  hannunsa riƙe da bindigar yayi hoton, doguwar sumar kansa wanda ya ɗaure ta tsayin ta har bayan wuyansa baka wulik,

Kyawawan lips ɗinsa tabi da kallo dark pink kamar ya shafa janbaki, ga wani dogon hanci tubarkalla masha Allah,

Tayi nisa cikin ƙurewa hoton kallon, sam ta manta da abunda take kokarin yi sai da wayar hannunta tayi ƙarar shigowar sako sannan ta dawo hayyacin ta,

Da sauri ta shiga wurin contacts, numbar goggo ta rubuta ta danna mata ƙira, ba tayi tunanin ko akwai recharge card a phone din nasa ba, amma ranta ya bata cewa ba zama a rasa ba, su da kullum cikin kuɗi suke,

A jiyar zuciya ta saki jin numbern ya fara ringing, sai Allah Allah take suyi sauri su ɗaga before he get up,

Jin muryar goggo yasa sehrish sakin murmushin jin dadi

“Assalamu alaikum goggo sehrish ce! Ina jahad don Allah inason magana da ita cikin sauri,” ta karasa maganar tana waige waige kar wani ya ganta,

On the other hand goggo ta miƙa wa jahaad wayar, cikin dauƙi ta ƙarba tare da fadin”yar uwa ! dagaske ke ce ! Wayyo Allah na farin ciki,”

Dariya sehrish tasaki jin abunda jahadar ta ce, kamar zatayi kuka itama ta ce”I really missed you my sisters, so much, dana ji voice ɗinki i just felt like to cry,” ta karasa maganar idonta cike taf da hawaye,

“sister dama akwai abunda nake na fada miki amma narasa taya zanyi magana dake,”

Sehrish ta ce “yanzu ina jinki pls kiyi sauri ba wayata ba ce ta yaron gidan ce baisan ma na dauka ba,”

Cikin fargaba take sauraron jahaad ɗin”sister doctor ya ce ƙarshen month ɗin nan indai ba ayiwa husanna aiki ba, to ciwon nata zai habbaka sai dai a fidda ita ƙasar waje in ba haka ba mutuwa zata yi, sun sa mana ranar aiki 5 ga watan da zamu shiga….” kuka ne ya ci ƙarfin ta, itama sehrish ɗin kukan take yi haka suka dinga kuka ta wayar, babu mai lallashin wani,

“Idan kin gama wayar ina jira!!!

A firgice ta juya idanuwanta azare jin muryar junaid, rufe idonta tayi tare da buɗe su ashe kunnanta ne suka jiyo mata hakan sam bashi bane ,

Ganin ya fara yi mata gizau yasa ta ce da jahad ta ajiye waya, zasuyi magana next time in ta samu chance irin wannan,

Cikin sauri ta goge numbar goggo da ta sanya, a wayarsa da duk wata shaida da zata tona cewa tayi amfani da wayarsa,

Cikin sanɗa ta lalla6a ta mayar masa da wayar, har time din bacci yake yi,

Haka ta koma ɗakin ta tana sharar kwalla,  safa da marwa ta shiga yi tana zagaye ɗakin, tunanin ta yadda zatayi ta samun kuɗin nan,

“Yanzu yaya zanyi! kada husanna ta rasa rayuwarta! sam bata cancanci haka ba, tazo duniya a wahalce kuma ta koma! Ya ilahi i dont ave any other choice fa ce kai Ya Allah, nayi imani dakai, kai kaɗai ne gatan mu, Ya Allah ka kawo mana mafita Albarkacin manzon Allah (SAW) ❤

Dakyar ta samu ta shiga toilet don wanke jikinta, ganin cewa basu da wani aiki a kitchen saboda guys ɗin gidan in suka fita sai da marece suke dawo wa, hakan yasa basa making lunch da wuri,

Don haka tana kammala wankan ta, da alwalarta tafito domin time ɗin azhar ya yi, har ta kammala sallah bata tuna cewa tabar gashin bakinta a cikin toilet ba,

A saman sallayar ta kwanta tun tana shesshekar kuka tana rokon Allah har bacci ya ɗauke ta,

Sehrish ta manta bata rufe kofan ɗakinta ba kamar yadda ta saba, shin na tuna mata ko kuma na kyale ta? tuna wa da cewa ba’a so a tashi mutun in yana bacci indai ba abu mai mahimmanci bane kamar sallah yasa na ƙyale ta, me zai biyo ba?

“Babu amfanin zama da mutun fasiƙi irin ka ! Ka saida mun ƴaƴa ! Saboda son abun duniya da son siyasa kai mutunne ko dabba! hakan baiyi maka ba sai da kabi ƴaƴana ka lalata musu rayuwa wannan wace irin masifab ce?

“Wayyo Allah abba kadaina dukan oumman mu, jini ke zuba a jikinta, oumma ki daina kada ya kashe ki ! Oumma! Oummahhhh!

Da ƙarfi ta ambaci sunan a firgice lokaci ɗaya ta farka, kukan da take a mafarkin har a fili sharkaf haka tayi da zufa, zaune ta tashi a fujajen tana kuka bil haƙƙi,

Dafe kanta tayi saboda wani matsanancin ciwo da yake yi mata, cikin shesshekar kuka take ambaton “umman mu,’ fuskarta duk ta jagule dama dama da hawaye, da alama wani mummunan abune daya taba faruwa a rayuwarta ta tuna,

Haka ta dinga maimaita “Innalallahi wa inna ilaihirraji’un,

Cike da jimami ta tashi daga saman sallayar, agogon dake manne jikin bango ta kalla ƙarfe 4:00 dai dai time ɗin la’asar yayi har yana kan wuce wa,

dole ne ta canza sabuwar alwala saboda tayi bacci mai nauyi,

Cire hijab ɗin dake jikinta tayi ta aza asaman gadon, ta jiƙe sharkaf da zufa, shiga toilet ɗin tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, hannun na dafe da chest ɗinta, cire kayan jikinta tayi , ta sakarwa kanta shower , yadda sassanyar ruwan ke sauka a jikinta haka zuciyarta ma ke sauka daga hawan da tayi, (ruwa rahama Ne!) duk yadda kake cikin kunar rai indai zaka shiga ka watsa ruwa a jikinka to tabbas zaka samu natsuwa,

Bayan ta kammala bath ɗin ta karasa gaban mirror ɗin dake cikin toilet ɗin, tana bin jikinta da kallo, tana da tsayi ba laifi , sam bata da ƙiba amma ƙirjinta cike suke da boobs, sannan daga kasa akwai hips sosai faffadan gaske, launin fatarta choculate colour ce, expensive skin colour, tana da sexy eyes masu lumshe wa sometimes kamar na mai jin bacci wani lokacin kuma sai kayi tunanin tana shaye shaye ne, kwayar idonta fara ce tass mai launi brown colour, hancin ta ba dogo bane ƙarami ba ƙaramin kyau yayi mata ba, a bangaren lips kuwa tamakar shape ɗin love ❤ red colour masu tafshin gaske (macen novel ke nan komai nata is 100% 😂

Hannu tasa tare da shafa gefen wuyanta inda ke akwai wani rubutu a jikin fatar wurin da bakin rubutu kamar na tattoo aka rubuta (Sb) murmushi ta ɗan saki tuna wanda yayi mata rubutun, mayar da hannunta tayi akan sumar kanta wadda tayi tsayi yanzu ta sauko mata har kafaɗar ta , asalin gashin kanta har ƙugunta ya dira, amma silar hajjaju da ma’reeya suka datse mata shi saboda gudanar da aikin ta a matsayin namiji,

Tunawa da sallah yasa tayi gaggawar mayar da kayanta, ta dauki gashin bakinta da ta bari a gaban mirror, ta fita

Cikin sauri tayi sallar , bayan ta gama ta nufi kitchen wurin azmi taga in akwai aiki, samun ta tayi tana a ciki tana shirye shiryen fara aiki,

“Barka da aiki aunty azmi ” sehrish ta faɗi hakan tana kallonta, ɗagowa tayi da fara a fuskarta tace “ke ke da sannu saboda naganki kina ta sharar bacci,”

Ras! Sehrish taji gabanta ya faɗi hankali a tashe take kallon azumi, itama kallon ta take tana sakin wani bazawarin murmushi, lokaci guda sehrish tabi ta susuce murya na rawa tace “dagaske kin ganni ina bacci !” dariya azmi tasaki tare da cewa “kwarai malam tukur ɗan basaja naganka kona ce naganki, ”

Kallon kallo suka shiga yiwa junansu sehrish na tunanin tabbas ƙaryarta ta ƙare saboda azmi ta kira ta da ke amaimakon kai sannan taganta tana bacci da hijabi kuma ba gashin bakin nan nata da take sawa ya ilahi,

Yayin da azmi ke mamakin wayau irin na wannan yarinyar, har tasan tayi shigar namiji tazo gidan sojoji aikatau ko tsoro bata ji, gskya ba ƙaramar ƙuruwa ba ce,

 

Sai faman wurga ido sehrish take yi,hannu tashiga tafawa tana faɗin “nashiga uku shikenan komai ya ƙare”

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

💖💖💖💖

💖💖💖

💖💖

💖 *ABBAN SOJOJI* 💖

💖💖

💖💖💖

💖💖💖💖

“`The father Of Soldiers“`

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 19-20

sai faman wurga ido sehrish take yi,hannu tashiga tafawa tana faɗin “nashiga uku shikenan komai ya ƙare”

Kana kallonta ka ga tsananin tsoro a fuskarta, lokaci guda tabi ta rikice ganin bata da wani mafita fa ce ta roƙi azmi ta rufa mata asiri, don haka jiki na rawa takarasa gaban azmi ta zube saman kneel ɗinta tana roƙonta “nasan nayi laifi amma bani da wata mafita ne don Allah ki rufamin asiri aunty azmi kamar yarda Allah ya rufa miki,”

Hmmm ja da baya azmi ayi tare da cewa”am sorry to say bazan iya rufa miki asiri ba ! laifin zai shafe mu mu biyu, wannan babbar qarya ce a girma na bai kamata na goyi bayan hakan ba, sannan bugu da ƙari sojojin gidan nan suka gane cewa ke maca ce ba namiji ba to tabbas ƙasusuwanki za’a fidda daga cikin gidan nan! kinsan matsalarki ? Cikin sauri ta ce “a’a ”

“matsalarki shine kin aikata laifi biyu, na farko namiji suke so a matsayin ɗan aiki ba mace ba, ke kuma kinyi shigar mace kinzo, duk sunyi tsammanin ke namiji ce hakan yasa suka amince da ke rinka shiga har ɗakunansu kina gyara musu da sauransu, nabiyu laifin ƙarya! sun tsani maƙaryaci, kinyi karya baiwar Allah idan har suka son da wannan zancen ko ! Ba ma ke ba ni kaina ta shafa! don haka cikin salama ki tattara kayanki ki bar gidannan kafin su ankara”

Azmi na kaiwa nan ta juya mata baya ta ci gaba da abunda take yi,

Jiki a mace sehrish ta miƙe, hawaye na gangarowa daga idonta kamar an kunna fanfo, cikin sanyin murya ta ce “shikenan…bakomai naji daɗin hakan zan tafi insha Allah,”

Fi ce wa tayi a guje tana shessheƙar kuka, fadawa tayi ɗakinta ta datse kofar ta faɗa saman gadon ( kamar a indian film 😂)

Tasha kuka kamar ba gobe lokaci guda fuskarta ta kumbura tayi suntum, idonta suka yi jawur suka ƙankance kamar na ƴan chaina,

Haka ta taso daga saman bed ɗin tana bin bedroom ɗin da kallo “ko a mafarki ban taba tunanin haka zata kasance dani ba, yanzu zan tafi nabar wannan daular, ni bama wannan bane damuwata ba ya rayuwar su husanna zata kasance su da suke cikin wani hali a asibiti, gashi bansamu kuɗin ba, wayyo Allah na, bansan wane irin zunubi muka aikata ba da rayuwarmu bata tafiya adai dai ba, tun kafin mu mallaki hankalinmu mu ke fuskantar ƙaddara iri iri meyasa !?

Zube wa kasan tiles ɗin tayi tana kuka jikinta har jijjiga yake yi,

Sam bata ji shigowar azmi ba sai dai mutyarta taji ta dirar mata a kunne” Ya sunanki ? ta jefa mata tambaya ,

yunkurawa tayi ta tashi tsaye tana matse hanci ta ce “SEHRISH”

Jinjina kai azmi tayi tare da ƙarasawa inda take, tafin hannunta ta sa tana share mata hawaye, sam sehrish bata yi tunanin hakan ba,

sannan cikin natsuwa ta ce” nayi takaici dana sa wannan kyakkyawar fuskar zubda hawaye am so sad,” cike da mamaki sehrish ke kallonta, azmi ta ci gaba da cewa “kiyi hakuri ko kusa bazanso na raba ki da aikin ba! duk da ina tsoran abunda zai biyo baya, amma zan iya jurewa don ganin na taimaka miki,” jin wannan bayani yasa sehrish sauke nannauyiyar ajiyar zuciya,

mayar da hannunta tayi a saman shoulders ɗinta taci gaba da cewa” da farko ina so ki fadamun dalilin dayasa ki kayi basaja a matsayin namiji”?

Muryar na rawa ta soma magana cikin sheashekar kuka” ƴan uwana ne basu da lafiya rai hannun Allah an kwantar dasu asibiti, kuma doctor ya ce aiki za’a yi musu, shine nake kokari naga nasamu ƙudi na biya musu, ɗayar ma dr yace in har ya wuce 5 ga watan da zamu shiga sai dai a fidda ita Qasar waje ko tarasa ranta…..’ kukan ne yaci ƙarfin ta,

Cikin lallashi azmi ta ce “daina kuka ya isa haka, na fuskanci matsalarki, duk da ina buƙatar bayani amma bani da enough time, riƙe wannan zamuyi magana an jima yanzu dai taimakon da zan miki shine, zaki ci gaba da aiki a matsayin Namiji kamar yadda kike yi, ko da gigin wasa karki bari su gane cewa ke maca ce ! sannan maganar kuɗi kuma nawa ne ake bukata ?

Azmi ta tambaya tana kallon ta, sehrish ta ce “dubu ɗari tara ne” a tunanin ta azmi zatayi shock in taji kuɗin amma sai taji tace”zan iya ansar miki albashinki na wata na shekara ɗaya da rabi ! a baki a ɗunkule amma inaso ki sani ! duk runtsi duk wuya duk kuma duk irin wahalar da zaki fuskarta da wulaƙanci a wurin masu gidan nan, dole kiyi haƙuri ki jure! kiyi musu biyayya sau da ƙafa, ba maganar barin aiki , in kuma har kika ce zaki bari toh sai fa kin biya sauran kuɗin da kika ƙarba kin amince!!? 😰

taji ma tana nazari kafin tace”Eh na amince !!! zuciyarta na wani irin bugawa ba kowa ya faɗo mata a rai ba face Ayaan da jahaan , ynx ana nufin ta ɗaura aure da kaddararta na zama cikin gidan nan! ya ilahi,

“Yanzu account number zaki bani na wanda za’a turawa kuɗin aikin nasu,” azmi ta faɗa tana kallon cikin idonta, tsananin farin ciki ta gani a fuskar sehrish 😇

cikin jin daɗi tace “babu a wuri na amma zuwa anjima ko gobe zan samu na kawo miki,” azmi ta amsa da toh sannan ta kama hanyar fita har takai bakin kofa xata buɗe ta juya ta kalli sehrish dake ta faman sakin murmushi tace “kada ki manta ynx kina ƙarƙashin Iko na! komai zakiyi saida umarnina, idan har kika saba hakan, hmmmm,

bata ida ba ta fi ce,

sam sehrish bata damu da hakan ba, ita dai indai akan sisters ɗinta ne toh ko fiye da hakan ma zata iya jurewa,

Jiki na rawa baiwar Allah ta shige toilet ta dauro alwala taci gaba da zabga nafilfilin miƙa godiya wa ubangijin mu Allah subhanahu wata’ala,

Matsalar su husanna tazo ƙarshe, sauran damuwa ta kau, shin yaya kke tunanin rayuwar sehrish zata kasance a gidan ABBAN SOJOJI ? 😢

yinin ranar da fara’a a fuskarta hakoranta a washe kamar mai tallar maclean, cikin jin daɗi suka gudanar da aiki a kitchen tare da azmi don shirya dinner,

tunanin yadda zata sake ɗaukar wayar junaid takira husanna ta ce su turo mata account number, har zuciyarta take jin ƙaunar azmi saboda tayi mata rana ! Har abada kuwa ji take bazata taba sa6a mata ba! tayiwa kanta alkwarin zatayi mata biyayya bazata taba bijire mata ba ko taci amanarta ba,

A 6angaren junaid kuwa, bayan ya tashi daga bacci da jimawa ya wuce masallaci daya dawo ya tsaya a filin da suke buga ball na gidan tare da wasu daga cikin sojojin dake tsaron gidan,

yunwa ce tasa shi shigo wa ciki after magrin prayer, muryasa suka dinga ji yana kiran “tukur ! ,

Wani irin farin ciki ne ya lullu6e sehrish, cikin ɗauki ta ajiye wanke wanken da take yi agaban fanfo, na kayan da suka yi amfani dasu,

Karasawa tayi wurinsa yana zaune saman 3 seater, yana daddana wayarsa, cikin girmamawa tace”gani ya ya junaid”  ta kirasa da hakanne saboda ya hana ta ce masa yalla6ai, girman jiki ne kawai dashi da kuma tsawo fuskarsa ce kawai zata nuna maka cewa yaro ne sharkaf,

ta6e baki yayi tare da ɗan jefa mata kallo ya ce” ƴunwa nake ji, ” ya faɗa a shagwa6e, yana kallon ta

cikin zumuɗi ta ce ” a shirya ma abinci a dining ko nan zan kawo maka,?

ta tambaya tana kallon wayar hannunsa kamar ta fisge ta saboda ita take bukata,

ɗan yatsina fuska yayi kafin ya ce” No a tsarin gidan nan bama iya cin abinci in ba tare da junan mu ba, duk yunwar da mutun ke ji dole sai an tattara an haɗu a table aci a tare, don haka kawo min coffee kawai, zan jira brothers ɗina su dawo sai mu ci dinner a tare,”

Wannan haɗin kan nasu ya burge sehrish sosai, suna son junansu, juya wa tayi, taje da tadawo hannunta dauke da cup din saman ɗan plate ɗin da ake aza sa, miƙa masa tayi tana kallon fine face ɗinta,

Ƙarba yayi tare da faɗin”thanks”

komawa dining room ɗin tayi, tana goggoge chairs ɗin dake kewaye dashi, daga inda take tana satar kallonsa shi da yake zaune a falo,

Bayan ta kammala ta koma kitchen ɗin, azmi ta samu tana a ciki tana ganin ta ta ce “yawwa mlm tukur ayi maza a fara jera abincin a dining ko,” sunnar da kai ƙasa sehrish tayi cikin jin kunya, azmi tace “gsky hajjaju yar daru ce! da ita duk aka shirya wannan ƙaryar,” murmushi kawai sehrish take yi tana wasa da yatsun ta,

Ba tare da bata lokaci ba, suka soma shirya abincin, tana kaiwa tana jera masu,

Ƙiris ya rage a fara kiran sallar magrib, bayan sun girma shiryawa azmi ta wuce ɗakin ta , sehrish kuwa falo ta wuce, anan ta samu Junaid yana sharar bacci, ya mimmiƙe kafafuwansa a saman doguwar kujerar,  Alhamdulillah thanks to Allah ta fadi hakan, ƙyalle ido tayi ta ga inda ya ajiye wayarsa saman chest ɗinsa,

Cikin sanɗa ta soma tafiya a hankali a hankali take takawa, har ta idasa isa gabansa, leƙa fuskansa tayi kyakkyawa mai annuri, dimples ɗin nan nasa a lotse, kamar ba bacci yake yi ba,

Hannu takai a hankali ta ɗauki wayar tasa cikin rashin sa’a ta zame daga hannunta ta faɗi kasa ta daki haɗaɗɗen tiles ɗin dake kasa, har cikin zuciyarta taji faɗuwarnan, tsadaddiyar waya irin wannan, dafe ƙirjin ta tayi tana kallon wayon, ƙarar faɗuwar wayar tasa junaid yunkurin buɗe idonsa daga baccin da yake, cikin sauri ta boye bayan hannun kujerar tana sauke ajiyar zuciya, gyara kwanciyarsa yayi ya ci gaba da bacci, jin sakin ajiyar zuciyarsa yasa ta gane ce ya koma baccin nasa, hannu ta zura ta janyo wayar tana kallon screen ɗinta, Alhamdulillah ta fada ganin ba abunda ya same shi,

Yunƙurawa tayi ta tashi tsaye, tana kallon sa, ya aza hannunsa ɗaya a saman stomach ɗinsa, ɗayan kuma a saman kansa, abun yazo mata da sauƙi, don haka cikin sauri ta jona wayar a yatsarsa, nan take wayar ta buɗe,

murmushin jin daɗi ta saki, wannan hoton ta sake gani a wallpaper ɗinsa na wannan haɗaɗɗen matashin saurayin, har ranta so take tasan wanene wannan sarkin kyawun nan,

Ja da baya tayi a hankali tayi nesa dashi, izuwa gefen stair ta tsaya, contacts dinsa ta shiga ta rubutu numbar goggo, bugu ɗaya wayar ta shiga kuma aka ɗaga, cikin sa’a muryar jahaad taji tana kwaɗa sallama, da farin ciki ta ce”Jahaad ni ce Sehrish! banda isasshen lokaci pls listen to me,” a can 6angaren jahad ta natsu tana sauraron abunda sehrish zata ce mata”Nasamu kuɗin aikin account number zaki turomin cikin gaggawa saboda na fadamiki wayar ta yaron gidan ce nake dauka shi kansa baisani ba,”

tsananin farin ciki ne yasa jahad yin ihu da fadin Alhamdulillah a cikin wayar tasu, ta ce “narasa inda zansa kaina don farin ciki ƴar uwa kice mun kusa barin asibitin nan dama wlh nagaji da zamansa….” sehrish ce ta katse ta ganin zata ja masu lokaci ga tsoran kar junaid ya farka “ke ba surutu zakiyi mun ba ki anso acct number ɗin likitan yanzu yanzun nan ki turamin kada fa ki 6ata lokaci asiri na zai tonu,”

Tana gama faɗan hakan ta yi rejecting kiran, ta tsaya nan tana jiran shigowar saƙon jahaad, jikinta har rawa yake gudun kar junaid ya farka, har leƙen sa take yi taga ko yana motsi,

Safa da marwa tashiga yi kamar mai ɗawafi, Allah Allah take jahaad ta turo saƙon tayi sauri ta kwafa ta mayar masa wayarsa,

tana nan tana jira, tajiyo ƙarar shigowar motarsu Ayaan,da wata irin jiniya motocin nasu ke shigowa, aiko nan take junaid ya soma motsi , saboda tsabagen ruɗu 😳, maimakon taje ta ajiye masa wayar ta ruga , sai ta haɗa da wayar duka ta watsa aguje sai bedroom ɗinta.

Ana dara ga dare yayi ?😳

tashi zaune yayi tare da yin miƙe, da hamma lokaci guda hannu yasa ya rufe bakin nasa, wayarsa ya soma lalube yaga bata nan bai kawo komai aransa ba sai yayi tunanin ko ya barta a room dinsa ne,

Shigowarsu brothers ɗin nasa ne yasa shi, sakin fara’a , a jere suka shigo su 7, ƙarasa wa kanal yusif yayi ya russuna tare da rungumesa yace”barka da hutawa my bro ina fata kana cikin koshin lafiya,” da fara’a ya amsa masa da cewa “am fine bro kun dawo lpy,” kanal ya masa masa da eh, kafin ya wuce, shima khaleed karasawa yayi inda junaid ɗin ke zaune ya rungume sa tare da cewa”My sweet bro ya enjoyment,” bai basa amsa ba sai murmushin da yayi masa, haka irfan da jabeer duk suka rungumesa kafin suka wuce ɗakunansu,

Ya rage saura twins da fawan, harara fawan ya sakar masa tare da wuce wa ta gabansa yana rera waka cikin zolaya yake cewa”Lalatacce lalatacce ne ko a gidansu wannan haka yake,” ɗaure fuska junaid yayi don ya tsani tsokanarsa da fawan ya ke yi,

A tare Ayaan da Jahan (Masoya 😂) suka ƙarasa kowanne ya manna masa kiss a cheeks ɗinsa kafin suma suka wuce ciki,

Shima junaid ɗin tashi yayi ya shiga ciki domin ɗauro Alwala saboda liman na ta kwaɗa kiran sallah,

A bangaren sehrish kuwa, tana nan maƙale da wayar junaid a hannunta, zuciyarta na harbawa, sai zagaye ɗakin take tana faɗin, nashiga ukuna ynx ya zanyi in junaid ya nemi wayarsa ya rasa, in kuma ya ganta a hannuna nasan dukan tsiya zan sha, kuma su kore ki daga aiki ace mun 6arauniya, yanzu ya zanyi ni nasamu na mayar masa da wayarsa wayyo Allah na,

Ƙarar shigowar message ne taji ƙirrrr! da sauri ta duba, account number ne jahad ta turo mata, cikin sauri ta laluba cikin drawer chest, inda ta ajiye diary din da take rubutu acikinsa Wanda tazo dashi , biron da ta saka a tsakiyar littafin ta dauko ta bude page tayi copying numbers ɗin, tana gama wa , ta mayar ciki ta ajiye,

Sannan ta yi hanzarin deleting sakon daga wayar tasa, fitowa tayi daga ɗakin tana leken ko akwai mutun, duk basu kai da fito wa,

har tasa hannu zata koma ciki taji alamun mutun, junaid ɗin ne ya fito yana naɗe hannun rigarsa, da alama masallaci zai wuce,

Ba karamin dadi taji ba, yana fi ce wa, ta lallabawa cikin sauri ta shiga ɗakinsa ta ajye masa wayar a saman nightstand,

Fito wa tayi tana sauke ajiyar zuciya, yanzu abunda ya rage mata takai ma azmi acct number ɗin,

ɗaki ta koma, ta ɗauki diary ɗin ta yago papern data rubuta numbar, ta fito ta tunkari ɗakin azmi, dayake ba nisa yana kusa da nata, wannan ne karo na farko da ta fara shiga ɗakin ta,

Sallama tayi, azmi dake zaune saman sallaya ta amsa da “wa’alaikum salam shigo ciki,”

Cikin natsuwa sehrish ta shiga ciki, wuri ta samu ta zauna kusa da ita ta lankwashe kafarta tayi zaman cin tuwo,

Cazbaha take ja, a hannunta ɗan murmushi tayi tace”wai malam tukur ne yau a ɗakin namu kodai mafarki nake ne? Cikin jin kunyarta sehrish ta ɗukadda kai tana murmushi,

“tabbas kuwa shine to mara ba lale marhaban daga ganin wannan gashin bakin naka akwai magana,” dariya ce ta kubce ma sehrish, ta shiga 6a66aka ta,

daga bisa ni ta tsagaita tare da cewa “aunty azmi dama acct number ɗin ne na kawo miki,” ta karasa maganar tana miƙa mata paper ɗin, karba azmi tayi tare da fadin”kin tabbata ta likitance? Sehrish ta ɗaga kai tare da cewa “Eh tashi ce,”

“Toh shikenan kije kawai insha Allah zuwa gobe za’a tura masu kudin,”

Azmi ta fada tana adana takardar a saman carpet din.

~ABBAN SOJOJI~

Written by

~HAFSAT BATURE~

~Boss Lady~

Page 20 to 21

sai faman wurga ido sehrish take yi,hannu tashiga tafawa tana faɗin “nashiga uku shikenan komai ya ƙare”

Kana kallonta ka ga tsananin tsoro a fuskarta, lokaci guda tabi ta rikice ganin bata da wani mafita fa ce ta roƙi azmi ta rufa mata asiri, don haka jiki na rawa takarasa gaban azmi ta zube saman kneel ɗinta tana roƙonta “nasan nayi laifi amma bani da wata mafita ne don Allah ki rufamin asiri aunty azmi kamar yarda Allah ya rufa miki,”

Hmmm ja da baya azmi ayi tare da cewa”am sorry to say bazan iya rufa miki asiri ba ! laifin zai shafe mu mu biyu, wannan babbar qarya ce a girma na bai kamata na goyi bayan hakan ba, sannan bugu da ƙari sojojin gidan nan suka gane cewa ke maca ce ba namiji ba to tabbas ƙasusuwanki za’a fidda daga cikin gidan nan! kinsan matsalarki ? Cikin sauri ta ce “a’a ”

“matsalarki shine kin aikata laifi biyu, na farko namiji suke so a matsayin ɗan aiki ba mace ba, ke kuma kinyi shigar mace kinzo, duk sunyi tsammanin ke namiji ce hakan yasa suka amince da ke rinka shiga har ɗakunansu kina gyara musu da sauransu, nabiyu laifin ƙarya! sun tsani maƙaryaci, kinyi karya baiwar Allah idan har suka son da wannan zancen ko ! Ba ma ke ba ni kaina ta shafa! don haka cikin salama ki tattara kayanki ki bar gidannan kafin su ankara”

Azmi na kaiwa nan ta juya mata baya ta ci gaba da abunda take yi,

Jiki a mace sehrish ta miƙe, hawaye na gangarowa daga idonta kamar an kunna fanfo, cikin sanyin murya ta ce “shikenan…bakomai naji daɗin hakan zan tafi insha Allah,”

Fi ce wa tayi a guje tana shessheƙar kuka, fadawa tayi ɗakinta ta datse kofar ta faɗa saman gadon ( kamar a indian film 😂)

Tasha kuka kamar ba gobe lokaci guda fuskarta ta kumbura tayi suntum, idonta suka yi jawur suka ƙankance kamar na ƴan chaina,

Haka ta taso daga saman bed ɗin tana bin bedroom ɗin da kallo “ko a mafarki ban taba tunanin haka zata kasance dani ba, yanzu zan tafi nabar wannan daular, ni bama wannan bane damuwata ba ya rayuwar su husanna zata kasance su da suke cikin wani hali a asibiti, gashi bansamu kuɗin ba, wayyo Allah na, bansan wane irin zunubi muka aikata ba da rayuwarmu bata tafiya adai dai ba, tun kafin mu mallaki hankalinmu mu ke fuskantar ƙaddara iri iri meyasa !?

Zube wa kasan tiles ɗin tayi tana kuka jikinta har jijjiga yake yi,

Sam bata ji shigowar azmi ba sai dai mutyarta taji ta dirar mata a kunne” Ya sunanki ? ta jefa mata tambaya ,

yunkurawa tayi ta tashi tsaye tana matse hanci ta ce “SEHRISH”

Jinjina kai azmi tayi tare da ƙarasawa inda take, tafin hannunta ta sa tana share mata hawaye, sam sehrish bata yi tunanin hakan ba,

sannan cikin natsuwa ta ce” nayi takaici dana sa wannan kyakkyawar fuskar zubda hawaye am so sad,” cike da mamaki sehrish ke kallonta, azmi ta ci gaba da cewa “kiyi hakuri ko kusa bazanso na raba ki da aikin ba! duk da ina tsoran abunda zai biyo baya, amma zan iya jurewa don ganin na taimaka miki,” jin wannan bayani yasa sehrish sauke nannauyiyar ajiyar zuciya,

mayar da hannunta tayi a saman shoulders ɗinta taci gaba da cewa” da farko ina so ki fadamun dalilin dayasa ki kayi basaja a matsayin namiji”?

Muryar na rawa ta soma magana cikin sheashekar kuka” ƴan uwana ne basu da lafiya rai hannun Allah an kwantar dasu asibiti, kuma doctor ya ce aiki za’a yi musu, shine nake kokari naga nasamu ƙudi na biya musu, ɗayar ma dr yace in har ya wuce 5 ga watan da zamu shiga sai dai a fidda ita Qasar waje ko tarasa ranta…..’ kukan ne yaci ƙarfin ta,

Cikin lallashi azmi ta ce “daina kuka ya isa haka, na fuskanci matsalarki, duk da ina buƙatar bayani amma bani da enough time, riƙe wannan zamuyi magana an jima yanzu dai taimakon da zan miki shine, zaki ci gaba da aiki a matsayin Namiji kamar yadda kike yi, ko da gigin wasa karki bari su gane cewa ke maca ce ! sannan maganar kuɗi kuma nawa ne ake bukata ?

Azmi ta tambaya tana kallon ta, sehrish ta ce “dubu ɗari tara ne” a tunanin ta azmi zatayi shock in taji kuɗin amma sai taji tace”zan iya ansar miki albashinki na wata na shekara ɗaya da rabi ! a baki a ɗunkule amma inaso ki sani ! duk runtsi duk wuya duk kuma duk irin wahalar da zaki fuskarta da wulaƙanci a wurin masu gidan nan, dole kiyi haƙuri ki jure! kiyi musu biyayya sau da ƙafa, ba maganar barin aiki , in kuma har kika ce zaki bari toh sai fa kin biya sauran kuɗin da kika ƙarba kin amince!!? 😰

taji ma tana nazari kafin tace”Eh na amince !!! zuciyarta na wani irin bugawa ba kowa ya faɗo mata a rai ba face Ayaan da jahaan , ynx ana nufin ta ɗaura aure da kaddararta na zama cikin gidan nan! ya ilahi,

“Yanzu account number zaki bani na wanda za’a turawa kuɗin aikin nasu,” azmi ta faɗa tana kallon cikin idonta, tsananin farin ciki ta gani a fuskar sehrish 😇

cikin jin daɗi tace “babu a wuri na amma zuwa anjima ko gobe zan samu na kawo miki,” azmi ta amsa da toh sannan ta kama hanyar fita har takai bakin kofa xata buɗe ta juya ta kalli sehrish dake ta faman sakin murmushi tace “kada ki manta ynx kina ƙarƙashin Iko na! komai zakiyi saida umarnina, idan har kika saba hakan, hmmmm,

bata ida ba ta fi ce,

sam sehrish bata damu da hakan ba, ita dai indai akan sisters ɗinta ne toh ko fiye da hakan ma zata iya jurewa,

Jiki na rawa baiwar Allah ta shige toilet ta dauro alwala taci gaba da zabga nafilfilin miƙa godiya wa ubangijin mu Allah subhanahu wata’ala,

Matsalar su husanna tazo ƙarshe, sauran damuwa ta kau, shin yaya kke tunanin rayuwar sehrish zata kasance a gidan ABBAN SOJOJI ? 😢

yinin ranar da fara’a a fuskarta hakoranta a washe kamar mai tallar maclean, cikin jin daɗi suka gudanar da aiki a kitchen tare da azmi don shirya dinner,

tunanin yadda zata sake ɗaukar wayar junaid takira husanna ta ce su turo mata account number, har zuciyarta take jin ƙaunar azmi saboda tayi mata rana ! Har abada kuwa ji take bazata taba sa6a mata ba! tayiwa kanta alkwarin zatayi mata biyayya bazata taba bijire mata ba ko taci amanarta ba,

A 6angaren junaid kuwa, bayan ya tashi daga bacci da jimawa ya wuce masallaci daya dawo ya tsaya a filin da suke buga ball na gidan tare da wasu daga cikin sojojin dake tsaron gidan,

yunwa ce tasa shi shigo wa ciki after magrin prayer, muryasa suka dinga ji yana kiran “tukur ! ,

Wani irin farin ciki ne ya lullu6e sehrish, cikin ɗauki ta ajiye wanke wanken da take yi agaban fanfo, na kayan da suka yi amfani dasu,

Karasawa tayi wurinsa yana zaune saman 3 seater, yana daddana wayarsa, cikin girmamawa tace”gani ya ya junaid”  ta kirasa da hakanne saboda ya hana ta ce masa yalla6ai, girman jiki ne kawai dashi da kuma tsawo fuskarsa ce kawai zata nuna maka cewa yaro ne sharkaf,

ta6e baki yayi tare da ɗan jefa mata kallo ya ce” ƴunwa nake ji, ” ya faɗa a shagwa6e, yana kallon ta

cikin zumuɗi ta ce ” a shirya ma abinci a dining ko nan zan kawo maka,?

ta tambaya tana kallon wayar hannunsa kamar ta fisge ta saboda ita take bukata,

ɗan yatsina fuska yayi kafin ya ce” No a tsarin gidan nan bama iya cin abinci in ba tare da junan mu ba, duk yunwar da mutun ke ji dole sai an tattara an haɗu a table aci a tare, don haka kawo min coffee kawai, zan jira brothers ɗina su dawo sai mu ci dinner a tare,”

Wannan haɗin kan nasu ya burge sehrish sosai, suna son junansu, juya wa tayi, taje da tadawo hannunta dauke da cup din saman ɗan plate ɗin da ake aza sa, miƙa masa tayi tana kallon fine face ɗinta,

Ƙarba yayi tare da faɗin”thanks”

komawa dining room ɗin tayi, tana goggoge chairs ɗin dake kewaye dashi, daga inda take tana satar kallonsa shi da yake zaune a falo,

Bayan ta kammala ta koma kitchen ɗin, azmi ta samu tana a ciki tana ganin ta ta ce “yawwa mlm tukur ayi maza a fara jera abincin a dining ko,” sunnar da kai ƙasa sehrish tayi cikin jin kunya, azmi tace “gsky hajjaju yar daru ce! da ita duk aka shirya wannan ƙaryar,” murmushi kawai sehrish take yi tana wasa da yatsun ta,

Ba tare da bata lokaci ba, suka soma shirya abincin, tana kaiwa tana jera masu,

Ƙiris ya rage a fara kiran sallar magrib, bayan sun girma shiryawa azmi ta wuce ɗakin ta , sehrish kuwa falo ta wuce, anan ta samu Junaid yana sharar bacci, ya mimmiƙe kafafuwansa a saman doguwar kujerar,  Alhamdulillah thanks to Allah ta fadi hakan, ƙyalle ido tayi ta ga inda ya ajiye wayarsa saman chest ɗinsa,

Cikin sanɗa ta soma tafiya a hankali a hankali take takawa, har ta idasa isa gabansa, leƙa fuskansa tayi kyakkyawa mai annuri, dimples ɗin nan nasa a lotse, kamar ba bacci yake yi ba,

Hannu takai a hankali ta ɗauki wayar tasa cikin rashin sa’a ta zame daga hannunta ta faɗi kasa ta daki haɗaɗɗen tiles ɗin dake kasa, har cikin zuciyarta taji faɗuwarnan, tsadaddiyar waya irin wannan, dafe ƙirjin ta tayi tana kallon wayon, ƙarar faɗuwar wayar tasa junaid yunkurin buɗe idonsa daga baccin da yake, cikin sauri ta boye bayan hannun kujerar tana sauke ajiyar zuciya, gyara kwanciyarsa yayi ya ci gaba da bacci, jin sakin ajiyar zuciyarsa yasa ta gane ce ya koma baccin nasa, hannu ta zura ta janyo wayar tana kallon screen ɗinta, Alhamdulillah ta fada ganin ba abunda ya same shi,

Yunƙurawa tayi ta tashi tsaye, tana kallon sa, ya aza hannunsa ɗaya a saman stomach ɗinsa, ɗayan kuma a saman kansa, abun yazo mata da sauƙi, don haka cikin sauri ta jona wayar a yatsarsa, nan take wayar ta buɗe,

murmushin jin daɗi ta saki, wannan hoton ta sake gani a wallpaper ɗinsa na wannan haɗaɗɗen matashin saurayin, har ranta so take tasan wanene wannan sarkin kyawun nan,

Ja da baya tayi a hankali tayi nesa dashi, izuwa gefen stair ta tsaya, contacts dinsa ta shiga ta rubutu numbar goggo, bugu ɗaya wayar ta shiga kuma aka ɗaga, cikin sa’a muryar jahaad taji tana kwaɗa sallama, da farin ciki ta ce”Jahaad ni ce Sehrish! banda isasshen lokaci pls listen to me,” a can 6angaren jahad ta natsu tana sauraron abunda sehrish zata ce mata”Nasamu kuɗin aikin account number zaki turomin cikin gaggawa saboda na fadamiki wayar ta yaron gidan ce nake dauka shi kansa baisani ba,”

tsananin farin ciki ne yasa jahad yin ihu da fadin Alhamdulillah a cikin wayar tasu, ta ce “narasa inda zansa kaina don farin ciki ƴar uwa kice mun kusa barin asibitin nan dama wlh nagaji da zamansa….” sehrish ce ta katse ta ganin zata ja masu lokaci ga tsoran kar junaid ya farka “ke ba surutu zakiyi mun ba ki anso acct number ɗin likitan yanzu yanzun nan ki turamin kada fa ki 6ata lokaci asiri na zai tonu,”

Tana gama faɗan hakan ta yi rejecting kiran, ta tsaya nan tana jiran shigowar saƙon jahaad, jikinta har rawa yake gudun kar junaid ya farka, har leƙen sa take yi taga ko yana motsi,

Safa da marwa tashiga yi kamar mai ɗawafi, Allah Allah take jahaad ta turo saƙon tayi sauri ta kwafa ta mayar masa wayarsa,

tana nan tana jira, tajiyo ƙarar shigowar motarsu Ayaan,da wata irin jiniya motocin nasu ke shigowa, aiko nan take junaid ya soma motsi , saboda tsabagen ruɗu 😳, maimakon taje ta ajiye masa wayar ta ruga , sai ta haɗa da wayar duka ta watsa aguje sai bedroom ɗinta.

Ana dara ga dare yayi 🐽򜰊tashi zaune yayi tare da yin miƙe, da hamma lokaci guda hannu yasa ya rufe bakin nasa, wayarsa ya soma lalube yaga bata nan bai kawo komai aransa ba sai yayi tunanin ko ya barta a room dinsa ne,

Shigowarsu brothers ɗin nasa ne yasa shi, sakin fara’a , a jere suka shigo su 7, ƙarasa wa kanal yusif yayi ya russuna tare da rungumesa yace”barka da hutawa my bro ina fata kana cikin koshin lafiya,” da fara’a ya amsa masa da cewa “am fine bro kun dawo lpy,” kanal ya masa masa da eh, kafin ya wuce, shima khaleed karasawa yayi inda junaid ɗin ke zaune ya rungume sa tare da cewa”My sweet bro ya enjoyment,” bai basa amsa ba sai murmushin da yayi masa, haka irfan da jabeer duk suka rungumesa kafin suka wuce ɗakunansu,

Ya rage saura twins da fawan, harara fawan ya sakar masa tare da wuce wa ta gabansa yana rera waka cikin zolaya yake cewa”Lalatacce lalatacce ne ko a gidansu wannan haka yake,” ɗaure fuska junaid yayi don ya tsani tsokanarsa da fawan ya ke yi,

A tare Ayaan da Jahan (Masoya 😂) suka ƙarasa kowanne ya manna masa kiss a cheeks ɗinsa kafin suma suka wuce ciki,

Shima junaid ɗin tashi yayi ya shiga ciki domin ɗauro Alwala saboda liman na ta kwaɗa kiran sallah,

A bangaren sehrish kuwa, tana nan maƙale da wayar junaid a hannunta, zuciyarta na harbawa, sai zagaye ɗakin take tana faɗin, nashiga ukuna ynx ya zanyi in junaid ya nemi wayarsa ya rasa, in kuma ya ganta a hannuna nasan dukan tsiya zan sha, kuma su kore ki daga aiki ace mun 6arauniya, yanzu ya zanyi ni nasamu na mayar masa da wayarsa wayyo Allah na,

Ƙarar shigowar message ne taji ƙirrrr! da sauri ta duba, account number ne jahad ta turo mata, cikin sauri ta laluba cikin drawer chest, inda ta ajiye diary din da take rubutu acikinsa Wanda tazo dashi , biron da ta saka a tsakiyar littafin ta dauko ta bude page tayi copying numbers ɗin, tana gama wa , ta mayar ciki ta ajiye,

Sannan ta yi hanzarin deleting sakon daga wayar tasa, fitowa tayi daga ɗakin tana leken ko akwai mutun, duk basu kai da fito wa,

har tasa hannu zata koma ciki taji alamun mutun, junaid ɗin ne ya fito yana naɗe hannun rigarsa, da alama masallaci zai wuce,

Ba karamin dadi taji ba, yana fi ce wa, ta lallabawa cikin sauri ta shiga ɗakinsa ta ajye masa wayar a saman nightstand,

Fito wa tayi tana sauke ajiyar zuciya, yanzu abunda ya rage mata takai ma azmi acct number ɗin,

ɗaki ta koma, ta ɗauki diary ɗin ta yago papern data rubuta numbar, ta fito ta tunkari ɗakin azmi, dayake ba nisa yana kusa da nata, wannan ne karo na farko da ta fara shiga ɗakin ta,

Sallama tayi, azmi dake zaune saman sallaya ta amsa da “wa’alaikum salam shigo ciki,”

Cikin natsuwa sehrish ta shiga ciki, wuri ta samu ta zauna kusa da ita ta lankwashe kafarta tayi zaman cin tuwo,

Cazbaha take ja, a hannunta ɗan murmushi tayi tace”wai malam tukur ne yau a ɗakin namu kodai mafarki nake ne? Cikin jin kunyarta sehrish ta ɗukadda kai tana murmushi,

“tabbas kuwa shine to mara ba lale marhaban daga ganin wannan gashin bakin naka akwai magana,” dariya ce ta kubce ma sehrish, ta shiga 6a66aka ta,

daga bisa ni ta tsagaita tare da cewa “aunty azmi dama acct number ɗin ne na kawo miki,” ta karasa maganar tana miƙa mata paper ɗin, karba azmi tayi tare da fadin”kin tabbata ta likitance? Sehrish ta ɗaga kai tare da cewa “Eh tashi ce,”

“Toh shikenan kije kawai insha Allah zuwa gobe za’a tura masu kudin,”

Azmi ta fada tana adana takardar a saman carpet din,

Godiya sehrish tashiga yi mata har da matse ƴar kwalla, murmushi azmi tayi tace “Ki gode wa Allah, domin shine abin godiya, kuma shine silar shigowarki gidan nan! ,”

jinjina kai sehrish tayi alamar gamsuwa da bayanan azmi, daga bisa ni ta tashi ta fice,

A bangaren su twins kuwa lokacin da suka shiga ɗakinsu suka tarar angyara ko ina tsaf, jahan ya kalli ayaan tare da cewa “yaushe zaka daina wannan gangancin ne !,” ya faɗi hakan rai abace, cikin rashin sanin laifin daya aikata yace “what do you mean?

tsoki jahan ya saki tare da ƙarasawa gaban dressing mirror, yakai hannu ya ɗauko kwalbar maganin nan ya ce”wannan nake nufi !”

ɗafe kai Ayaan ya yi tare da faɗin “Omg!! am sorry for that, ni kaina na manta ban mayar ba,”

harararsa jahan yayi ya ce “we’re sorry for our self dai ! kai ka sani duk ranar da aka gane cewa muna aikata homo sai kashin mu ya bushe a hannun babban yaya, don haka i warn u this is last time dont repeat it again stupid !,”

ya ƙarasa maganar yana mayar da kwalbar cikin drawer chest ya janyo ya zura ta ya mayar,

Zama ayaaan yayi abed side ransa a bace jin sweet heart ɗin nasa ya kira sa da stupid akan ƙaramin laifi,

Satar kallonsa jahan yayi ganin yadda idonsa suka ciko da kwalla, sam baisan 6acin ransa don haka, ya dawo ya zauna tare da riko hannayensa yace cikin sanyin murya “am sorry my honey nayi laifi ko? ya faɗi hakan yana kallonsa,

Cikin fushi ayaan ya fisge hannunsa daga na jahan, ya kwantar da kansa jikin fillow, binsa jahan yayi ya hau saman jikinsa ya kai bakinsa saitin kunnan sa ya ce “I love u so much i dont wanna see u in angry fushi ba ya yi maka kyau honey,”

A hankali ayaan ya fara washe fuskarsa daga daure war da yayi mata, kiss jahan ya soma manna masa a side face ɗinsa har izuwa wuyansa tamkar zai cinye sa, dawo wa yayi ya sa harshen sa a kunnan ayaan yana ɗan taunarsa, hakan yasa ya fara jin sha’awarsa na tashi, (to fah)

Sehrish

Cike da jin daɗi ta koma bedroom ɗinta, don murna hada ƴar rawa ta taka, yanzu abu ɗaya ne ya rage mata shine jiran sakamakon aikin jahaad musamman husanna ita da tafi shiga hatsari, taci alwashin hana kanta bacci domin yi musu addu’a ta roƙa masu sauki a wurin Allah, (Ya Allah kabarmu da beloved sisters ɗinmu masu son mu, ka ƙara zumunci a tsakanin mu tare da ƙara hada kawunanmu much love 😇)

💖💖💖💖

💖💖💖

💖💖

💖 *ABBAN SOJOJI* 💖

💖💖

💖💖💖

💖💖💖💖

“`The father Of Soldiers“`

_HafsatBature_

_Boss Lady_

Page 22

After isha prayer, kowannan su ya hallara domin gudanar da dinner ɗinsu, amma banda mutun biyu, Ayaan da Jahaan wato twins,

duk sunyi dressing cikin pyjamas ɗinsu gwanin kyau, abunka ga mazajen novel ga haske ga tsari ga kwantacciyar suma 😉. (Allahumma arzukni 😂)

Kowannansu yaja kujera ya zauna suna fuskantar junansu, a tsaye dogon dining table ɗin ya ke, mai 12 seats ne

“Abinci ya riga masu cin shi hallara ikon Allah,” acewar jabeer, fawan ya ce “gasu aci ci mala’ikun tauna suma sun hallara ” ya ƙare maganar cikin zolaya yana kallon junaid fuskarsa da murmushi, tsoki junaid ya ja baice masa komai ba don bayasan hayaniya wani lokacin,

Khaleed ya ce “zaku fara disturbing ɗin mutane ko”? ya ambaci hakan yana kallonsu, kanal yusif ya ce “barsu su fara mai rabon shan duka baya jin bari sai ya sha sa,”

dariya irfan yayi tare da cewa”Zanso naga ana dukan junaid wai waya ga shagwa6a haka zai dinga ihu yana buga ƙafa a ƙasa kamar ƙaramin yaro yana cewa mommy daddy babban yaya ,”

jin wannan maganar ta irfan yasa sauran tuntsirewa da dariya, hakan ba ƙaramin ƙulesa yayi ba,

“Ae naga yaron ya girma ! Jin ya ke we’re equal wit him, wuyansa ya isa yanka, bansan dalili ba, ” acewar jabeer

Fawan ya ƙarbe da cewa “ah ba dole ba tunda Ak47 ɗinsa ta yi girman tamu,”

gaba ɗayansu suka tuntsire da dariya, adai~dai lokacin sehrish ta karaso domin yin serving dinsu abincin taji suna wannan maganar ba abunda ya dira a kunnanta sai kalmar (Ak47),  sam batasan mai hakan yake nufi ba,

iya ƙuluwa junaid ya yi shiru kawai ya yi bai tanka musu ba, ya rasa maiyasa suke masa haka,

Shi kansa kanal yusif saida ya murmusa amma bai bari sun gani ba, gudun kar raini ya fara shiga tsakaninsa da younger brothers ɗinsa,

Jin jina kai fawan ya yi ya ce “haba no wonder ! no wonder! thats y naga y’an mata sun fara bin layi, kai ka ga followers ɗinsa a insta da tiktok, ka ce ashe Ak47 ce ke ruɗarsu …..”

dariya ce ta ci ƙarfinsa ya kasa idasa maganar, haka sauran ma dariya suke yi, ran junaid ba karamin 6aci yayi ba, kiris yake jira ya fara kuka,

duk wannan firar da suke a kunnan sehrish wadda ke zuzzuba musu abinci a plates da abin sha, sam batasan inda suka dosa ba,

Kanal yusif ne ya yi gyaran murya tare da cewa “Is enough ! Stop teasing him, kuna bata wa bro ɗina rai, ” dakatawa yayi da maganar yana kallon junaid wanda ya ci ka ya batse, tuni ruwan hawaye sun kwanta a idonsa, cikin sauri kanal yusif yace “karka kuskura ka bari wannan expensive tears ɗin naka su zuba, kai in banda abunka ae yabonka su kayi, AK47 abun so ce ynx mata sun fi son namiji mai wannan size ɗin, kuma wannan alama ce da ke nuna cewa ƙanin namu ya ƙosa aure yake so,”

wata irin dariya ce ta 6alle wa sehrish ita kanta batasan ta sake ta ba, gaba ɗaya suka dago suna kallon ɗan aikin nasu a matsayin shashasha, cikin jin kunya sehrish tasa hannu ta toshe bakin ta tana sunnar da kai kasa,

Harara khaleed ya wurga mata tare da cewa “ƙaramin ɗan iska nifa nasan wannan mai aikin namu kwarto ne, ƙurun ɗan duniya ne, rikakken ɗan tasha, in ba haka ba menene abun dariya a nan? ya tamabaya yana hararar ta, ita dai shiru tayi bata ce komai ba, a tare sauran suka ja tsoki,

Har sun soma cin abincin kanal yusif ya lura cewa babu twins a wurin don haka ya ɗago ya kalli tukur tare da cewa “jira kake sai an baka umarnin ka kira twins?wai kai wane irin sullu6iyo ne am just doubting abt u,”

Jiki na rawa sehrish ta ce “am sorry sir,”  sannan ta kama hanayr bedroom din nasu,

“wai ku baku lura da wani abu ba”? jabeer ya tambaya yana kallonsu, fawan ya ce “me kenan,” jabeer ya ce gaba da cewa “wlh wannan ɗan aikin namu tukur sam ni banga abunsa ba babu alamarsa,” bin shi sukayi da kallo a yayin da suke ƙoƙarin fahimtar me yake so yace musu,

Junaida ya ce “which thing are u talking abt”? yayi maganar ne a lokacin da yake ƙoƙarin tura dambun nama a bakinsa, jabeer ya ce “hmm kada ku ce naci ka sa ido amma Allah ku lura da gaban wandonsa sam babu alamar abun namiji a wurin,”  sakin baki su kayi suna kallonsa , kafin fawan ya ce “maganarka gsky wlh, nima najima ina tunanin hakan, cos duk yadda namiji yasa trouser sai ka alamun abun nan amma shi shafe ko dai ba mutun bane”?

Ya tambaya cikin mamaki, dariya junaid ya yi tare da cewa “may be it is small like atom,” gaba daya suka dara

Kafin kanal yusif ya dakatar dasu da cewa “shame on u guys, kuna maza , mazan ma sojoji kuna gulma, u have to stop it bana so mai aikin nan ya ji wannan maganar a barta anan, kowa ya mayar da hankalinsa ya ci abincin sa,”

A bangaren sehrish kuwa time ɗin da ta isa dakin su twins, gabanta faduwa kawai yake yi gudun abunda zata taras,

tana sa hannu a ƙofar ta 6uɗe, sun mata da kofar a buɗe, sallama ta kwaɗa musu jin ba amsa ya sa ta tura kai,

Gabanta ne yayi mugun faɗuwa rass !! tuni zuciyarta ta hau bugawa da ƙarfi, ta gaza believing da abunda idonta ke nuna mata, kwance suke zir haihuwar uwarsu babu kaya ajikinsu, sun harɗe da junansu suna shan jikin junansu , wannan wane irin tashin hankali ne !

dukkan ilahirin jikinta rawa ya ke yi, a tsora ce taja da baya ta juya ta fi ce cikin sauri, wannan fitar da tayi ne ƙarar kofar da ta daka yasa su, dawo wa hayyacinsu suka ɗago a tare suna kallon kofar da ta mayar da kanta ta rufe, alamar wani ya shigo, cikin sauri Jahan ya zame jikinsa daga na Ayaan,

shima ayaan ɗin ya tashi zaune cikin wata irin kasala ya ce “meya faru sweetheart wani ya gan mu ko? ya tambaya yana lumshe idanunsa da alama bai gamsu ba, cikin damuwa jahan ya ce “i think so ! mun shiga uku duk laifin ka ne ayaan why u didnt close the door bfr we start doing it,”

hararar sa ayaan din yayi ” komai sai ka ce its my faults you’re also a guilty, cos you too why u didnt close it !,”

ya tamabaya yana kallon cikin idonsa cike da sha’awarsa,

hannu yasa tare da dakatar dashi ya ce” its ok ynx ka tashi mu shiga ciki, mu wanke jikin mu ya 6aci sosai,

ruko hannunsa yayi kamar mata da miji suka shiga cikin toilet a tare,

duk wannan maganar da suka yi akan kunnan sehrish wanda ke zukunne a kopan ɗakin nasu tana kuka ƙasa ƙasa, abunda yasa bata tafi ba saboda tsoran abunda kanal yusif xaice mata, ya zama wajibi ta sanar dasu su fito su halarci teburin cin abincin,

cikin kuka take faɗin “ya Allah ka shiryi waɗannan bayin naka ! su gane gaskiya su daina aikata wannan mummunan zunubin da suke yi, ina jin su har cikin raina, ina ji musu tsoran su mutu suna aikata wannan babban zunubin, wa’iyazu billah !

Alamun motsi taji wanda ke nuni da cewa suna kan hanyar fito wa ne, a guje ta tashi ta samu wuri ta 6oye,

ruƙe da hannun junansu suka fito, sunyi fess da su, kai ka ce bazasu iya aikata wannan zunubin ba,

Lokacin da suka ƙarasa dining ɗin suka ga ƴan uwan nasu duk suna a wurin sai hankalinsu ya kwanta, hakan na nufin ba wanda ya gansu,

wata irin soyayya ce mai ƙarfi tsakanin Ayaan da jahaan, ga tsananin sha’awar junansu da suke kamar hauka, kullum cikin saduwa da junansu suke basa gajiya, abun har ya wuce na hankali, su yi a bedroom wani sa’in suyi a toilet,

Allah yana rufa musu asiri domin babu wanda yasan suna aikata hakan, sai sehrish ! wata irin rayuwa suke yi a gidan, yasu yasu ba mai shigar ma wani ɗaki, sai fa in wani kwakkwaran dalili ne,

Lalacewarsu har ta kai ga sun ɗaurawa junansu aure, da kansu ba tare da wani ya sani ba,

Shi kuma Fawan jarabar bin mata gare sa, duk da matan ne ke binsa, shi kuma yana basu haɗin kai, yayin da irfan da jabeer suke gogaggun ƴan shaye shaye, duk wani abun shaye shaye da kasani to suna dashi, mugayen kwayoyi suke sha ba tare da sanin kowa ba, ga wata ɗabi’ar fita ƙarfe shabiyun dare da suke yi , sai ƙirfan2 suke dawo wa in suka tafi night club ukun nan, fawan jabeer da irfan,

tun da azmi ta sanar da ita cewa ta tura masu ƙudin, nan fa hankalinta yaƙi kwanciya, burin ta taji ya ake ciki can asibitin, kullum ita ce kamar kusu wurin satar wa junaid waya ko tsoro ba taji,

Kamar kullum haka yau ma ta saci hanya ta lalla6a taje daukar wayarsa, yana bacci, wyar na ajiye a saman ƙirjinsa, jikin sa na sanye da nightwear,

hawa saman gadon tayi cikin sanɗa kamar munafuka, ɗaukar wayar tayi cikin sa’a, sai da tagama duk wannan wahalar ashe ya canza password ɗinsa, yanzu dole sai da fuskar shi sannan wayar zata bude wato face security ya sanya, haka ta zaune dirshen tana saman gadon tana kallonsa, tunani take yi meyasa ya canza security ɗin wayarsa to kodai ya gane ana ɗaukar masa wayarsa ne, a’a bana tunanin haka kawai ra’ayi ya yi ya canza, tae wannan maganar a zuciyarta,

Lalla6awa tayi ta matsa dai dai face 6insa, ɗaga wayar tayi wadda ke riƙe a right hand ɗinta, ta saita fuskar screen ɗin wayar a fuskarsa, amma taƙi buɗe sai ya rubuta mata not recognized,

ran ta ne ya ba ta cewa tabbas sai idonsa na 6uɗe sannan security ɗin wayar zata 6uɗe, cike da takaici takai hannu zata ajiye masa wayar a ƙirjinsa kamar yadda ya ajiye ta, tana ƙoƙarin lalla6a ta sauka, bata yi wani aune ba taji yayi wani irin ƙwaƙƙwaran juyi ya haɗa da ita duka ya rungume ajikinsa kuma ruƙo bana wasa ba, 😳

Allah kaɗai yasan tashin hankalin da sehrish ta shiga, zuru zuru tayi da ido, hancin ta na shaƙar ƙamshin turarensa, lokaci guda ta shiga cikin yanayi, ganin bata da wata hanyar tashi yasa ido ya raina fata, bin wuyansa tayi da kallo gwanin kyau, ji take kamar ta gartsa masa cizo a wannan lallausar fatar tasa ko ta samu ta tsere,

tashin hankalin da ba’a sa masa rana, ga azmi na jiran ta a kitchen saboda safiya ce akwai aikin haɗa breakfast, da sauran aikace aikace, ga junaid ya maƙale ta a jikinsa ta rasa yadda za’ae ta fita,

tana cikin wannan tunanin na yadda za’ae ta raba jikinsa da nata, ya ƙarayin wani kwakkwaran juyi, atare suka mirgina ƙiris ya rage su faɗo ƙasa, saboda tsabagen ƙiɗima tuni taji fitsari ya zo mata, komai ya tsaya mata cak, bugun zuciyarsa kawai take saurara,

Sun ɗau 30 mins a haka, ta ƙura masa ido yayin da shi baisan meke wakana ba,

Wayarsa ce ta soma ringing da ƙarar gaske, wannan sautin ne ya dirar masa a tsakiyar kunnansa, nan ya soma nuƙu nuƙu buɗe ido,

tsananin tsoro ne suka bayya na a fuskar sehrish, yana ƙoƙarin buɗe idonsa, cikin sauri ta janye hannayensa daga jikin ta, ita kanta batasan ta iya wannan ƙarfin halin ba sai yau, juyi tayi da ƙarfi ta sulale a ƙasan bed ɗin ta  durkushe a ƙasan, hankali a tashe

kamar mafarki haka junaid ke kallon lamarin, tabbas ya ga gifcin mutun daga jikinsa, amma sai ransa ya basa cewa duk cikin bacci ne abunda ya gani,

hannunsa ya kai tare da ɗaukar wayar tasa dake ta faman buga ringing, tare da karawa a kunnan sa cikin shagwa6a ya ce “Assalamu alaikum babban yaya na, am angry wit u cos i ave been waiting for your call since yesterday night, ” ya yi maganar tamkar yana a gabansa,

Sehrish da ke zuƙunne kasa cikin tashin hankali, tabaza kunne tana sauraron wayar da junaid ya ke yi, jin ya ambaci sunan babban yaya yasa ƴan cikin ta ƙadawa, sam tarasa dalilin daya sa in aka ambaci sunan nan take jin faɗuwar gaba,

ganin yayi nisa a wayar tasa ne yasa tayi tunanin ta rarrrafe ta fi ce daga ɗakin, don haka ta soma tafiya a ɗurkeshe a ɗurkushe, cikin sanɗa take rarrafa wa,

Ko waiwayen bayanta bata yi burin ta ta fice daga ɗakin before ya ankara, junaid kuwa dake maƙale da waya yana zabga wa yayan nasa shagwaba sam bai lura sai da yayi wani kwakkwarn juyi yana faɗin “just come back home i wanna see you serious…” bai ida maganar ba karaf idonsa suka sauka akan ɗan aikin nasu wanda ke tafiya cikin sanɗa yana rarrafawa zai fi ce,

Ƙura ido 👀 junaid yayi yana kallon ikon Allah, acikin ransa yana cewa” lallaima wannan ɗan rainin hankalin wato raini ya fara shiga tsakanin mu, bari in tsara in ga ƙarshen game ɗin,

sam batasan ya ganta ba,lokacin da ta isa ƙofan ɗakin ta saki wata irin ajiyar zuciya, maimakon ta fice ba tare da ta waiwaya ta kallesa ba, amma ina ranta ne ya bata ɗan juya mana ta kalle sa tun da ta tsira, juyawa tayi a hankali tana sauke ajiyar zuciya, karaf idonsu ya shiga na juna, ganin dagaske ita yake kallo ido cikin ido ya ganta asiri ya tonu, hannu ta shiga tafawa da yake ta kware wurin iya fauzewa sai kawai ta 6a66ake da dariya hhhhhhhh kamar mahaukaciya,

Tsananin mamaki ne yasa junaid yin kasaƙai yana kallon ikon Allah,

bata dakata da dariyarba cikin salon wayau da dabara ta fice tana tikar dariya, hada janyo masa kopa da rufe wa,

tana ganin ta fito ta tsagaita da dariyar tare da aza hannunta a saitin zuciyarta tace”wai Allah na tsira” da gudu ta sauka kasa ta wuce kitchen,

har ynx junaid bai dawo daga duniyar mamakin da ya tafi ba, tunda ya ke a rayuwarsa ba’a ta6a raina masa wayau irin na yau ba, ya ma rasa mai zaiyiwa ɗan aikin nan nasu, wane hukunci zaiyi masa,

“Zamu haɗu” ya fada a fili, kafin ya tashi ya shiga cikin toilet,

gaban wash basin ya tsaya, yakai hannu ya ɗauko toothbrush ɗinsa, ya matsa maclean a jikinsa, ya shiga goge hakoransa,a hankali yake komai saboda tunanin mai aikin nan nasu daya tsaya masa aransa,

Bayan ya kammala ya kunna mixer tap ɗin ruwa ya soma zubo wa wanke mouth ɗinsa yayi sannan shima brush ɗin ya wanke sa ya mayar dashi cikin holder dinsa,

wanka yayi shaf shaf ya dauro towel a west ɗinsa, ya fito yana matse sauran ruwan dake ɗiɗɗiga a sumar kansa da hand towel,

a gabn mirror ya tsaya yana kallon zunzurutun kyansa, a nan ne idonsa yakai saman fatar wuyansa, wani dogon gashi ya gani siriri mai tsayin gaske, tsananin mamaki ne ya kamasa, a cikin ransa ya ke faɗin “ynx duk wankan danayi amma wannan gashin bai bar jikina ba kodai har yanzu ban iya wanka bane haba junaid be a big man mana kana abu sai ka ce na ƴara,”

hannunsa yasa a hankali ya tsafko gashin, ya ɗago sa izuwa saitin eyes ɗinsa yana kallo, sai lokacin ya lura cewa tabbas wannan gashin mai tsayi bana sa bane to na wanene !!!! 😱

Sannu da zuwa mlm tukr, acewar azmi wadda ke magana tana kallon sehrish dake shigowa cikin kitchen, ɗan murmushi tayi tare da cewa ……………………

💖💖💖💖

💖💖💖

💖💖

💖 *ABBAN SOJOJI* 💖

💖💖

💖💖💖

💖💖💖💖

“`The father Of Soldiers“`

_HafsatBature_

_Boss Lady_

https://facebook.com/groups/1215415832595836/

Page 23-24

Kin riga da kin gane cewa ni maca ce,” ta faɗi hakan da ƴar shagwaba

Azmi ta ce “Oh kin shirya asirinki ya tonu ko? muddin nakira ki da sunanki na ƴan gayunnan to zasu gane cewa mai aikinsa fa maca ce ba namiji ba, daganan zasu ɗauke shi izuwa barrack ɗinsu na sojoji a acanza masa halitta,”

azmi tayi maganar ne da zolaya, yayin da tsoro ya bayyana a fuskar sehrish hannu tasa tare da rufe baki alamar ta shiga uku,

dariya azmi tayi tare da cewa” idasa shigowa mana, ina so zaki yanka mun wasu fruits nan zan hada fruit salad ne, ki duba cikin fridge ki dauko kayan marmarin kizo ki fara,”

karasa wa tayi inda refrigerator ɗin ya ke sai da ta fara daukar bowl ɗin da zata zuba su ciki sannan ta buɗe sa, kaya ne iri iri shaƙe acikinsa, dangin kayan marmari dasu vegitables, ga ɗanyen nama iri iri na dabbobi daban daban,

Zubo su tayi da yawa ta fara wanko su sannan ta dawo ta aza saman table, ta dauko knife ta shiga gyarasu, yayin da azmi ke ta faman ƴan soye soye,

Jin shirun yayi yawa yasa sehrish cewa” aunty azmi wai inaso in san wanene wannan babban yayan dasu junaid suke yawan faɗansa, wai shine babba a gidan nan ne,”?

da ta ambaci sunan shi sai da azmi ta ɗan girgiza, tajima bata yi mata magana ba, sai da tasamu natsuwa ta kana  face ” idan na fara baki labarinsa to tabbas zamu kwana muna yi, bashi bane babba ba amma shakkarsa da suke ji yasa yazama babba, wani irin mutun ne mai zazzzafan zuciya, bai da sauki in dai akan aikinsa ne, baya ragawa kowa, baya sauraron kowa, yana da matukar karfi tun daga kan surar jikinsa zai tabbatar maki da cewa mugun karfi gare sa, idan yaga Mara gaskiya kuwa idonsa makancewa yake yi, in fara hukuntasa har sai ya ɗanɗani kuɗarsa, ko ni agabana kwanakin baya daya zo sai da ya kashe mutun 4 acikin gidan nan, ko kai ɗan ubanwaye kayi laifi, haka zaisa a kawo masa kai har cikin gidan nan ya yanke ma hukunci kuma ba uban da ya isa ya tanka, to wama ya isa? Jikan soja,ɗan shugaban sojoji mahaifiyarsa soja, yayyensa sojoji ƙannensa sojoji, shima kuma soja a bangaren kyau kuwa sai dai mu ce Tabarakallahu ahsanul khaliqin, wlh tunda nake a duniya ban taba ganin mutun mai zazzafan kyau irin nasa ba! irin kyan da sai Allah kawai ke tsare mutun saboda bakin mutane da masu kawo masa hari, wani irin miskilin mutun ne ke zan iya ce miki akwai lokacin daya jera kwana uku baiwa kowa magana ba hatta abbansu sai dai kawai yayi nuni da hannunsa ayi masa abu kaza, Isarsa da jin kansa ga izza dayake takama da abun sai addu’a,

Jinjin kai sehrish tayi kafin ta ce “amma meyasa shi bazai dawo gida bane ya zauna cikin ƴan uwansa,”

Azmi tace “ya za’ae ya dawo nan bayan a can us ya taso tun yana yaro  a can kuma yake aikinsa a matsayin surgeon general,” maimata sunan sehrish tayi “Surgeon general meke nan,” murmushi azmi tayi saboda ta lura sehrish so take su ƙare firar tasu akan babban yaya ,

“Matsayinsa ne na aiki na faɗa miki bari nayi miki a ware yadda zaki fahimta, he’s a professional surgeon doctor kuma general ne na sojoji,”

Sakin baki sehrish tayi don mamaki wannan matsayi har haka ! surgeon general, tabɗijan can ta ambata tana jinjinawa lamarin ashe mutun inya karanci military surgery zai iya kuma zama general ɗin sojoji lallai iko sai ubangiji matsayi biyu,

murmushi tasaki Cikin zumuɗi ta ce “zanso naganshi ga kyau ga class ga matsayi biyu gsky ba ƙaramin jarumi bane,” a tunanin ta acikin zuciya tayi maganar sai ji tayi azmi tace”Insha Allah muna sa ran zuwansa nan kusa, amma kafin yazo ina tunanin Abbansu zai riga sa dawo wa domin shi ma yayi tafiya zuwa Qasar chaina, wani muhimmin taro ne yakaisu nasu na sojoji,”

wani irin daɗi ne ya rufe sehrish, saboda ta ƙosa tagansa, acikin zuciyarta tace “naso naga ranar da zanyi tozali dashi nagadai wanene wannan babban yayan wayyo daɗi….

Muryar azmi ce ta tsaida ta daga tunanin “meyasa baki tambaye ni sauran matansa da baki taba ganinsu ba sai babban yaya,”? tayi tambayar tare da juyowa tana kallonta,

Sukuyar da kai sehrish tayi tace “saboda tun ranar da hajjaju ta kawo ni gidan nan da sunan sa na fara cin karo,shiyasa na kosa nasan wanene shi,”

Hmmmm azmi tace ” akwai sauran zafafan ma irin su Captain duk wani matsayi da kika sani na soja agidan nan akwaishi, mutum goma ne sauran matasan da baki sani ba, ynx bamu da lokaci amma duk lokacin dana samu natsuwa sosai, zamu shiga garden ko muje swimming pool area akwai kujeru na shan iska awurin saina zauna na baki labarin gidan Abban sojoji,”

Cikin jin daɗi sehrish ta ce “zanji daɗin hakan sosai kinga saina san ta yadda zan zauna da kowa,”

Shiru su ka ɗanyi na wani lokaci kowa naci gaba da aikinsa, can da jimawa sehrish ta sake cewa “last question about babban yaya aunty azmi,” dariya azmi tayi tace “ina sauraron ki,” sehrish ta ce “wai bayan babban yaya menene sunansa ne na gaskiya,”?

“Zan faɗa maki amma da sharaɗi daga wannan tambayar mun rufe babin babban yaya,” acewar azmi a yayin da take sauke kasko daga saman gas,

“Na yarda toh,” sehrish ta ce tana ƴar dariya, azmi tace “Sunan shi……” shiru tayi ba ta ida ba,

Sehrish data ƙosa ta ƙagara taji sunan cikin zumuɗi tace “pls aunty azmi ki ƙarasa mana,”

murmushi azmi tayi dama ita take jira don ta ga yadda take son taji sunan,

gyaran murya azmi tayi sannan tace “Sunan shi RAFAYET!,” 💋

kamar yadda sunan ya diro mata a kunnanta haka zuciyarta ma ta bata wani sauti na musamman, cikin sanyi murya ta maimaita sunan “RAFAYET suna mai daɗin gaske,”

daga nan firar tasu nasamata aya.

suka shiga shirya breakfast ɗin sehrish ce ke kaiwa kamar kullum tana jerawa a dining, har lokacin maimaita sunan take acikin zuciyarta “rafayet,rafayet, tarasa dalilin hakan (dama in mutun ya kasance ƙaddarar ka hakan ce take faruwa) 😉

Sun kammala shirya komai tsaf, one by one suka soma fitowa, duk sun shirya tsaf cikin kakinsu, banda junaid wanda jallabiya ce milk colour a jikinsa, abun ba’a magana,

Ynx sehrish ta daina bin ɗakinsu, tana tashe su, saboda sunce basa buƙatan hakan, taji dadin wannan saukin da ta samu, mutun ɗaya ne wani sa’in dole sai taje, wato junaid don nauyin bacci gare sa, bai cika tashi dakansa ba sai an tashe shi, gyaran ɗakunan su kawai ke kaita, sai kuma wani abun inya taso,

Kowa yasamu wuri ya zauna ana jefa wa juna kallo, kafin su soma gaishe da junansu cikin so da ƙauna,

Kowanne sai ya faɗi abunda yake so ya ci sannan saita zaro plate ta zuba masa, haka abun ke tafiya,

cikin natsuwa suke cin abincin nasu, fawan ne yayi gyaran murya tare da cewa “Uhm AK47 yau ba magana,”?

tuntsire wa suka yi da dariya su duka hatta shi kansa sai da ya yi murmushi, Ayaan yace “she’s eating food thats why,” nan ma wata dariyar ta tashi, ɗagowa jahan yayi ya saci kallon Ayaan tare da kashe mishi ido, dama suna facing ɗin juna, murmushi ayaan ya yi,

Jabeer daya lura da su ya ce “toh ƴan iska kashe kashen idon me naga ana yi ne,” dariya su kayi su biyun, khaleed yace “there’s something behind they’re trying to hide it,”

ganin za’ayi babu shi yasa shi tsoma baki “abun sirri ne atsakaninsu,” acewar Irfan wanda ke ƙoƙarin ajiye spoon ɗin dake hannunsa saman plate ɗin gabansa,

junaid ya ce “what ever it is, idan kero na yawo zabo na yawo wataran za’a haɗu,” cikin sauri Ayaan yace “ubanka mai bakin ja6a insha Allah baza’a taba haɗuwa ba,”

wannan maganar tasa su fashewa da dariya, ita kanta sehrish dake tsaye akansu daurewa kawai take yi amma bakinta na ƙumshe da dariya ,

kanal yusif dai baice komai ba yau baya jin ƴ’an maganar sai dai in sunyi shiriritar tasu ya ɗan murmusa 😊

kallonsa khaleed yayi ganin yau yaƙi cewa komai don haka ya ɗanyi gyaran murya cikin zolaya ya ce “su yaya yusif ciki yana ta ɗauka ko magana babu,”

ɗagowa yayi tare da ɗan jefamar harara cikin sanyayyiyar muryarnan tasa yace”bana son shashanci fa, kar na sake jin wani yayi magana acikin ku”

Shiru su kayi tsit kowa ya natsu yana zubawa cikinsa,

Karar faɗuwar cokalin junaid ne yasa su dagowa suka kallesa, cikin sauri sehrish ta duka domin ta ɗauko masa,

Zuƙunna wa tayi kasan table ɗin takai hannu zata ɗauko cokalin kenan !

Idonunta suka hango mata abunda su Twins ke yi, dayake suna facing ɗin juna shida jahaan, ƙafafunsu na maƙale dana juna sun harɗe su ,

girgiza kai tayi aranta tace”jaraba” ɗagowa tayi ta miƙa masa cokalin hararar ta yayi tare da cewa”change another spoon for me i can’t use this one,”

mamaki ne ya kamata ganin inda cokalin ya faɗa a tsaftace yake, don ita ji take ko abinci za’a zuba mata a ƙasan wurin to tabbas zata sa harshe taci don ta shaida tsaftar wurin,

giɗa kai kawai tayi, ta ɗauko wani a inda suke jere ta miƙa masa, yasa hannu ya karba,

Sam ta gaza tsaida idanunta a kan wanda zata kalla cikinsu, kowa ta kalla kyau, shi dai kanal yusif wani irin sanyin kyau ne dashi ba fari bane tass wankan tarwaɗa ne, shi kuma khaleed tamkar ɗan kasar Ethiopia, launin fatarsa yayi irin choculate ɗin nan, da jabeer da irfan duk kalar fatarsu daya da yusif,

Amma in akazo wurin junaid, Ayaan da jahan da fawan farare ne tass kamar ka ta6a jini ya fito, natural white ne a tattare da junaid su twins kuma sunyi jawur, fawan kuma bai kaisu haske ba nasa mai yellow ne, dukkansu masha Allah suna da dogon hanci, ga kyawawan idanu ga kuma launin lips ɗinsu ga dimples ga kwantacciyar suma, duka dai 😇

Idonta yafi tsayawa akan junaid kallonsa take amma zahiri tunanin wayarsa take yi, har ranta bata ji daɗi daya canza security code ɗinsa ba, yanzu yaya zatayi ta kira su tsohuwa ?

ɗaya bayan ɗaya suka fara tashi kowa ya fi ce, wato wata irin motace jibgegiya ta sojoji idan suka hau ta, kowa sai yasan cewa ƴan gidan Abban sojoji ne suka fito Saboda da wata irin jiniya suke janta,

Sehrish

gyara wurin ta shiga yi, ta tattara komai da sukayi amfani dashi ta wuce dasu kitchen, sai da ta wawwanke komai tsaf ta mayar dasu cikin kitchen shelves,

Sannan ta koma tana gyaggara dining table area ɗin, ta tsaftace wurin sosai,

komawa tayi tana gyara babban falourn, ƴan goge-goge ƴan kakkabe kakkabe, da sauransu nan take wurin yayi tsaf, bakomai yake ƙara burgeta ba face komai nasu zaka ga launin sojoji ne (army colour) hatta teburin cin abincin da chairs ɗin dake zagaye dashi duk kafafunsu launin army ne, daga saman teble ɗin ne kawai glass,

Hatta 2 sets na royal sofa ɗin dake a katafaren palourn suma army colour ne, haka sofa tables ɗin duk launi ɗaya, da sauran abubuwan, lallai wannan yaci ka gidan Abban sojoji.

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

💖💖💖💖

💖💖💖

💖💖

💖 *ABBAN SOJOJI* 💖

💖💖

💖💖💖

💖💖💖💖

“`The father Of Soldiers“`

_HafsatBature_

_Boss Lady_

https://facebook.com/groups/1215415832595836/

Page 25-26

Ita kaɗai take ta faman wannan aika ce aikacen saboda azmi bata jin daɗi headache ke damunta dama ta sanar da ita, zata sha magani ta ɗan kwanta,

tunanin ta ynx yadda za ta goge waɗannan long stairs ɗin kullum wahalar su take ji, bin wurin tayi da kallo, wasu irin tagwayen bene ne masu double starcase ɗin nan, a zagaye suke, left & right , in kabi na hannun haggun zaka iya zagayo wa ka sauko ta hannun daman ka, a tsakanin su akwai space, a space ɗin nan zaka iya shiga ta tsakankanin benayen ka miƙi hanya anan zai kai ka bedrooms ɗin su Ayaan waɗan da ke a down kenan,

In kuma ka hau saman ɗaya daga cikin stairs ɗin zai kai ka , upstair in da ke akwai hanyoyin da zasu sada ka da jerin ɗakunansu junaid, a kalla bedrooms ɗin dake a gidan totally da wanda ke akwai mutane da wanda babu zasu kai 30,

Falo kuwa akwai manyan manya sunkai 9, kuma kowanne an ƙawata shi da attractive & expensive furnitures,

Amma babban cikinsu shine wanda kana shigowa ciki zaka fara cin karo dashi, main palour ɗinsu kenan

Ni nasan duk yadda zan kwatanta haɗuwar gidan nan ba kowa bane zai gane ba saini dana shirya kuma na gabatar

don hka just imagine it like the one u used to see in your dream, 🙅

tasha wahala sosai wurin gyara gyatan ɗakunansu don ma ba ɗauda kawai iya bedsheet ne zaka samu an yamutsa, sai kaya in an cire kaga anyi wurgi dasu ƙasa, wani ma don iyayi kayan nasa a saman mirror ta same su,

Bayan ta kammala dukan aiyukan, gajiya ta saukar mata bagatatan, ɗaki ta koma cike da jin ƙyanƙyamin jikinta,

Maballin rigar ta ciccire ta zame ta duka ta ajiye ƙasa, cire wandon tayi shima, sannan tasa hannu ta cire naɗin mayafin kanta, kafin tasa hannu ta 6an6are abunda take matse ƙirjinta dashi, tana ciresa taji wata irin iska na shigarta, gaba ɗaya boobs ɗinta a mugun taƙure suke, ba abunda ya same su, amma ƙan nipples ɗinta ba ƙaramin hurting ɗinta ya ke ba,

Ita kanta tausayin kanta taje ji, yadda ƙiri~ƙiri ta canza kanta daga mace zuwa namiji, duk tabi ta takure halittarta, hannu tasa ta cire ɗan gashin bakin da take mannawa, ɗago dashi tayi tana kallonsa tana matuƙar son ainihin halittarta ta mace,

gaban dressing mirror taje ta ajiye shi, toilet ta shiga tasakarwa ƙanta shower, ta haɗa hada hairs ɗinta ta wanke saboda ya fara tashi, gashi tana buƙatar tayi shaving, batasan ya zata yi, sauƙin bata da gashin armpit amma can under ɗinta kuwa akwai sosai,

ta gama yanke shawarar zata ɗebo shaving cream ɗin junaid taga hada set na shaver gare sa, dama shine marainin wayan ta,

ganin cewa babu kowa gidan daga ita sai azmi wadda ke can kwance tana sharar bacci, hakan yasa ta yanke shawarar cewa yau zata sakata ta wala, don haka ta shirya tsaf cikin riga t-shirt white colour da black trouser, sai da ta tabbatar ta matse ƙirjinta kamar yadda ta saba, sannan ta aza gashin bakin da take sawa, lalubawa tayi cikin jakar kayanta dayake ba duka kayan ta zuba cikin wardrobe ɗinba, anan tasamu hular da hajjaju ta siya mata, irin wannan hular da ake kira da tashi da kwakwa,

sai da ta tabbatar ta naɗe gashinta cikin ta cunkushe ta matse shi sannan ta kifa hular a saman kanta, sai gashi ta fito fes kamar ɗan saurayi,

Ita kanta ba ƙaramin daɗin jikinta taji ba, fitowa tayi ƙafarta sanye da takalmi roba na maza,

Kama hanyar ɗakin junaid tayi, cikin sauri take tattaka matattakalar stair ɗin, a gajiye ta iso ɗakin tura sa tayi ta buɗe ta shige,

Komai tsaf a tsanake dama ita ce tayi gyaransa, cikin jin daɗi ta wuce cikin toilet ɗinsa, agaban bathroom cabinet ta tsaya, anan taga jerin tsaddun mayukansa, duk wani abu na gyaran jiki akwashi kai kace na macene ba na namiji ba,

Tsawa tayi tana tunanin me yakamata ta ɗauka, tunani ta shiga yi ” kodai kawai na tsaya anan nayi shaving ɗin inyaso in na gama in tsaftace masa wurin yadda bazai gane ba sai in samu in lalla6a in fi ce, saboda in na ɗaukar masa zai iya gane wa, ƙarshe ya kamani a matsayin 6arauniya, ya zanyi ni,” ta fada tana ƙarewa wurin kallo

hannu tasa ta ɗauko roban shaving cream ɗin ganin yana da kusan guda uku yasa ta yanke shawarar ta ɗauki ɗaya bazai gane ba, sai ta haɗa da shaver guda biyu, tun da taga yana dasu dayawa a cikin ledarsu,

ruƙo su tayi a hannun ta saboda haɗama irin tamu ta bil’adama zuciyarta ta raya mata cewa mai zai hana ki haɗa da shampoo saboda wanke kai ga kuma sabulai masu ƙamshi sannan kina buƙatar turare na fesawa a jiki,

Murmushi tasaki jin wannan zancen na zuciyarta,

A fili tace “abun sai na samo wurin da zan zuba su baxan iya ɗauka ba a hannu na,

Fitowa daga bathroom ɗin tayi ta shiga neman wurin da zata sa kayan, a nan tasamu wata shopping bag, ƴar jakar nan ta siyayya, komai cikin sauƙi take ganin sa,

Komawa cikin toilet ɗin tayi ta shiga jidar kaya tana zurawa aciki, Sam bata tunanin cewa sata take yi ita ina gani take kamar ta zama ƴar gida in ta ɗauka halal ne.

A gajiye ya shigo cikin gidan jikinsa sanye da kayan kwallo riga da gajeran wando, yellow colour ba ƙaramin kyau sukayi masa ba, hannunsa riƙe da kwallo yana ɗan bugata a hannunsa, kafin ya rungumo ta a ƙirjinsa, cikin sauri ya haye upstair yana isa kofan ɗakinsa, yasa ƙafarsa ya harba door ɗin ta buɗe,

Saboda tsananin firgice sai da tasaki kayan dake rungume a ƙirjinta, zo kaga tashin hankali, daga cikin toilet ɗin take jin shigowarsa, tuni ido ido ya raina fata musamman da taji tabbas shine ɗin dai ya shigo, ana dara ga dare yayi 🙉

“Nashiga ukuna junaid ya dawo tafaru ta ƙare ” ta faɗa ido luhu-luhu, tuni jikinta ya fara rawa, matsawa tayi jikin kofan tana leƙansa,

samun shi tayi yana cire takalmansa, ganin he’s trying to takeoff his clothes,

Hakan yasa ta fargaba, koma wa tayi ciki tasa tafin hannunta tana bugun goshin ta, tuni ƴan matan hawaye sun bayyana, sintiri hawayen suka soma yi suna sauka a kumatunta, tashin hankalinta kada junaid ya ce zai cire kayansa saboda shi baisan da human being aciki ba,

Kuma tana da tabbacin cewa yadda ya dawo a gajiyen nan, wanka zai buƙaci ya fara yi, cikin tsananin tsoro ta furta “ae shikenan waman ƙadarallahu hakka ƙadrihi,”

wayyo Allah na there’s no way out, ya Allah ka kawo min mafita, ni nasan alhakin satar dana zo yi masa ne Allah ya kamani, hannu ta ɗaga sama tana addu’a tana cewa Ya Allah bazan ƙara ba ya Allah kafi kowa sanin cewa ni ba 6arauniya bace wlh sharrin shaɗain ne da kuma zuciya 😥

Ashhhh ! a wani irin yanayi yayi wannan sautin yayin da yake cire rigarsa da alama something is hurting him may be he gets wound,

Wurgi yayi da rigar saman bedmatress ɗinsa, hannu yasa yana shafa gefen cikinsa wurin yayi jawur abunka da kalar madara, ciwo ne wurin amma is not much,

A gefen gadon ya zauna yana sauke ajiyar zuciya,

Leƙo shi sehrish ta ƙarayi ganin sa zaune yasa taji sanyi aranta, zuba mishi na mazurin ta tayi tana kallonsa

A wani irin yanayi yake lumshe kyawawan idanuwnsa, teeth ɗinsa ya ɗansa yayi biting red lips ɗinsa, kai ka ce wanda ke cikin shauƙi ne,

hakan ba ƙaramin feelings ya sa sehrish ba, ita da ke leƙensa ta cikin toilet,

Mayar da kanta ciki tayi tana tunanin dabarar da zata yi masa ta samu ta fice, ranta ne ya bata cewa kawai ta fauze tayi kamar wanke toilet ɗin take yi tunda ita house maid ce tana da damar shiga ko’ina,

Murmushi tasaki tuna wannan dabarar, acikin zuciyarta ta ce ashe hakanan nake wahalar da kaina gaskiya kan kifi ne dani, bana gane komai cikin sauƙi

wurga idonta rayi kan kayan da ta zubar, ji tayi bazata iya barin shaving cream ɗin nan ba, koda zata mayar masa da sauran, matsawa tayi wurinsu da ta zubar da kayan, ta zuƙunna ta kwashi robar shaving cream ɗin da shaver guda ɗaya,

Cikin aljihunan wandon jikinta ta sanya su, amma robar tayi ɗan zumbuɗi tayi tayi amma taƙi idasa shiga haka tabarta,

Sauran ta tattara su ta mayar masa a cikin bathroom cabinet ɗin,

cikin sanɗa ta tura kofan ta fara zuwa kai tana leƙansa, ganin idonsa rufe ya tabbatar mata da cewa junaid fa bacci yayi awon gaba dashi don haka ta soma tafiya cikin sanɗa maimakon ta wuce ta fice cikin salama,

Amma hango jerin turarurrukansa da tayi agaban mirror yasa ta tsayawa, koma wa tayi a hankali ta cafko kwalbar turare ɗaya, ƙiris ya rage kwalbar ta faɗi kasa saboda ta kusa ta zame daga hannunta,

Wani irin bugun zuciya taji amma ganin ta same ta raɗau a hannunta ysa ta sauke ajiyar zuciya,

“na tsira” ta faɗa alokacin da ta samu ta fice cikin sa’a ,

Sam sehrish batayi tunanin cewa yaya Qarfin ƙamshin turaren yake ajikin mutun ba ! Kunsan turaren maza da ƙamshi,

cikin jin daɗi ta wuce bedroom ɗinta, jera su tayi agaban mirror ɗinsa, ran ta fal da farin ciki ganin itama yau ta fara jera abu a gaban mirror,

junaid

Bacci yayi na ɗan wani lokacin sai wuraren asr prayer ya farka, ƙarar shigowar message a wayarsa ne ya tayar da shi, a ɗan firgice ya tashi hannu yasa tare da shafa face ɗinsa yana sauke ajiyr zuciya,

Idonsa yakai kan well clock ɗin dake manne, hadaddiyar gaske ƙarfe 3:59 dai dai time haryaso ya goce masa,

Cikin kasala ya tashi kamar wanda ke shirin yin kuka, faɗawa cikin toilet yayi ya jagwalgwala wanka ya fito,

Closet ɗinsa ya bude riga da wando ya dauko, t-shirt ɗin ja wandon black colour,

Hannu ya kai ya dauki wayarsa dake gefen fillow ɗinsa, buɗe wayar ya yi tare da karawa a fuskarsa nan take security ɗin wayar ya buɗe,

buɗewa yayi ya fito daga room nasa, a natse yake tafiya yana daddana wayarsa message ɗin ya buɗe ya soma karantawa kamar haka

“Sister kwana biyu naji baki kira kin tambayi ya ya jikin mu ba, anyi mana aiki cikin nasara, naji sauƙi sosai husanna ma taji sauƙi sai dai hanyarzu akwai sauran mentel illness akanta, sunanki kawai take kira sehrish sehrish dan Allah ki kira mu muji voice ɗinki,”

tsayawa ya yi cike da tsananin mamakin ganin wannan saƙon a wayarsa a fili yace wacece kuma sehrish da husanna ! A wayata kuma !! me hakan yake nufi, wani namin amfani da wayata ne shin wai ma wanene wannan sehrish ɗin !!!

Kansa ya gama ɗaure wa, a hankalin ya idasa saukowa daga saman stair ɗin, ransa ne ya basa cewa kawai wasu ne sukayi kuskuren hada numbarsa, don haka ya share lamarin da cewa in ya samu lokaci zai kira number ɗin ya sanar dasu cewa its a wrong number, tunda yaji maganar rashin lafiya ce tana da mahimmanci kwara su son cewa basu sa number dai dai ba. 😳

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 27-28

Fitowa ta yi tana leƙensa, lalla6awa tayi ta ƙaraso gabansa kamar wata munafuka tace “barka da fitowa yaya Junaid,” ɗagowa yayi tare da kallonta ya ce “zan fita masallaci before na dawo pls a shirya min abinci bazan iya jurewa ba cos am starving,” dariya ce ta kusa kubce mata hannu tasa a bakinta, harara ya jefa mata “dariyar uban me ka ke?

hannun ta cire daga bakinta tare da cewa “dama….ran nan ka ce min baka iya cin abinci saboda tare da brothers ɗinka kke ce kun sa6a dole sai kun haɗu sannan kke ci atare shine….” tsayawa ta ɗan yi tana kallonsa

sakin baki yayi yana kallon wannan ɗan rainin hankalin ɗan aikin nasu, rai abace ya ce “kai !! NI tsaran wasanka ne ? raini ya fara shiga tsakanin mu ko !” ya ƙarasa maganar yana kallon ta,

Hankalin ta ba ƙaramin tashi tayi ba, bakin ta ya ja mata,

Saboda bacin rai muryarsa har rawa yake yi wurin kwalawa azmi kira,

Nan fa ta aza kai a saman ka tana faɗin “wayyo Allah na Sorry sir,”

duk a tunanin ta korarta zai sa ayi, jiki na rawa azmi ta fito baiwar Allah kana ganin ta kaga wadda bacci bai isheta ba,

Ƙaraso wa tayi tana faɗin “meya faru junaid kke kwalamin kira,”

Mayar da idonsa ya yi akanta ya ce “wannan mai aikin so nake nabasa punishment, cos he distains me ,

Ya ƙarasa maganar tare da kallon sehrish ya ce ” kasan yadda ake tsallen kwaɗi ko,” cikin tsoro ta girgiza masa kai alamar bata sani ba,

Jinjina kansa yayi tare da cewa “amma kasan yadda ake up and down,”

Zuru tayi da ido don batasan me ake nufi da up and down ba, juya wa tayi ta kalli azmi,

da ido azmi tayi mata alamar tace masa batasani ba,

Amma rashin fahimtar hakan yasa ta ce masa “eh na iya,”

cike da bada umarni ya ce “azmi inaso ki samun ido akansa, har nadawo daga masallaci nasame sa yana yi if not kowa zai gane kuransa,”

Yana gama faɗar hakan yasa kai ya fice,

Kallonta azmi tayi tana murmushi tace “oya start ae ke kika ce masa kin iya, ke kinsan menene up and down kuwa? mugun punishment ne mai wahalar gaske,”

murya na rawa tace” i don’t know how to do it ,”

Dariya azmi tayi , tare da gyara tsayuwarta, ta some yin ƙasa da sama tana nuna mata yadda zata yi,

“Toh kin ga yadda zaki yi, maza ki fara kafin ya dawo sbd kowani lokaci zai iya faɗowa, ni zan koma ciki saboda haryanzu kaina ciwo ya ke min,”

tana gama faɗan haka ta shige ciki, zugudum sehrish tayi ganin ba kowa yasa ta lalla6a tasamu wuri saman 2 seater tazauna, daga taji motsi sai ta ɗan firgita in taga bakowa sai ta natsu,

zaman zuru tayi ga fargabar karya zo yasame ta zaune batayi abinda yace ba, bacci ne ya ziyarce da kuma dama kowa yasan bacci 6arawo ne, nan ta soma gyangyaɗi a hankaki yayi Wuuuf da ita,

Tsayawa yayi cike da mamaki yana kallon ikon Allah, mutumin da aka ba punishment ya shi baiyi ba, kuma yasamu wuri dirshen kamar ɗan masu gidan ya kwanta,

Jinjina kai junaid yayi wanda shigowarsa kenan, zuwa yayi inda tanƙamemiyar freezer ɗinsu take yasa hannu ya buɗe, robar ruwa ya dauko mai sanyin gaske har ya fara kankara,

Yana zuwa inda sehrish take, ta saki baki baiwar Allah sai sharar bacci take yi ga gashin bakin nan da take manna wa yamayar da ita wata yar cartoon guda,

Buɗe murfin robar yayin, kai tsare ya zazzage mata shi ajikinta,

Wani irin firgit tayi ta farka lokaci guda ta tashi zaune jin yadda ruwa mai sanyin gaske yayi mata dirar mikiya,

dogon numfashi taja tana sa hannayenta tana yarfo da ruwan dake zuba a fuskanta, idonta jawur ta ɗago ta kallesa,

faɗa yasamo yi mata” saboda raini in saka ka aiki kazo kasami wuri ka zauna kana bacci ko kai ga riƙeƙƙen ɗan bariki ko,”?

Saboda tsananin baƙin ciki fashe mashi tayi da kuka kamar jinjira, tama rasa me zata yi, me zatace masa

Ganin yadda tukur ɗin ke shesshekar kuka yasa yaji kamar baiyi adalci ba, kasancewar junaid nada matukar tausayi wani sa’in,

juyawa yayi ya mayar da robar ruwa, sannan ya dawo ya zauna kusa da ita, har lokacin kuka take kamar ranta ze fita,

Muryarsa ce ta ratsa sa” Am sorry” ɗagowa tayi cikin mamaki tana kallansa bata ta6a tunanin zai iya bata hakuri ba,

Ci gaba da magana ya yi ” ka gane am very simple man kaine ka cika sa ido,komai kaji sai kaja bakin ka kayi shiru karka sake mun haka !,”

Tsagaitawa tayi da kukan tace” kayi hkr bazan ƙaraba bazan ƙara ba insha Allah,”

yanayin yadda tayi maganar sai ya ji kamar muryar mace amma aduk lokacin da yaji hakan sai kawai yasa wa ransa cewa namiji ne saboda akwai waɗan da halittarsu ce hakan,

“Its ok now i need something to it, go get it for me, am waiting ,”!

ya faɗi hakan cikin nuna buƙata, ta shi tayi ta nufi kitchen tana mai tunanin me zata sama masa ya ci, babban tashin hankalin ta azmi bata jin daɗi hakan na nufin cewa yau ita ce zata haɗa masu dinner kenan, gashi bata iya irin girkinsu ba na ƴan gayu,

da wannan tunanin ta shiga kitchen ɗin, babu wani dafafen abinci sun cinye komai da safen nan, dole sai dai tayi preparing wani, cikin gaggawa cos he needs it immediately,

cikin sauri ta za masa taliya saboda ita ce abu mai saurin dafuwa, kayan miya ta ɗebo ta gyara su ta markaɗesu , ta haɗa da kayan kamshi duka, ta jagwal gwala masa sai gashi ta fara ƙamshi, murmushi tasaki “Allah sarki har miyau na ya gwada bari in zuba masa sai in rage saura nima inci,”

a cikin plate ta zuba masa ta haɗa masa da spork a ciki, lokacin da ta isa samun shi tayi yana daddana wayarsa,

Cikin girmamawa tace “na kammala gashi,”

ajiye phone ɗin yayi side ɗinsa sannan yasa hannu ya karba, a hankaki ya furta “shukran laka,”

maimakon ta tafi sai ta tsaya tana kallon yadda yake sargafo taliyar a cokali mai yatsun yana turawa bakinsa, da alama tayi masa daɗi,

Sai wani ɗan murmushi take saki, ita dae a rayuwarta tana so tayi abu aci, hakan yana mata daɗi axuciyarta expecially da ya kasance junaid ne ke ci 😘

. Bata gajiya da kallonsa batasan meyasa ba amma tana da tabbacin cewa ba so bane na soyayya kawai burge ta yake yi,

ganin mai aikin tsaye akansa yasa shi tsagaita wa da tura abincin abakinsa ya ce “lafiya ka tsare ni da ido”?

da sauri ta girgiza kai tare da juyawa ta koma kitchen, zuba taliyar tayi itama ta samu wuri a ɗaya daga cikin chairs ɗin dake zagaye da dining table wanda ke a kitchen, ta soma ci farat ɗaya zuciyarta ta tunano mata da wani abu nan take ta fashe da kuka mai cin rai , tura abincin kawai take yi amma ita kaɗai tasan me take ji acikin ranta,

Aduk lokacin da takai abu mai daɗi zata sa abakin ta, sai ta tuna cewa wani hali ƴan uwanta suke ciki, me suka ci ? Shin suna samun abunda zasuwa cikinsu

😥

Babban tashin hankalin ta, shin ya aikin da akayi masu asibiti ke tafiya, husanna taji sauƙi ? shin ta rayu ko ta mutu saboda doctor yace ba tabbas ta rayu,

Cire hannunta tayi daga plate ɗin abincin ta turasa gefe, tashiga matse kwalla,

Bata jinkirta ba har saida taji alamar shigowar mutun, cikin sauri ta shiga goge hawayenta don batasan wani ya gani balle ya tambayi dalilin zubarsu,

“Sehrish me kike yi a zaune, i think zanzo na same ki kin fara aikace aikacen fara girki,”

tashi tsaye tayi cikin sanyayyiyar muryarta tace ” ae mun afwa aunty azmi,”

Hmmm azmi ta tace , kafin ta wuce ciki domin fiddo kayan da zasu fara aiki da su,

Lafiyayyen abinci aka girka masu, fatan doya da wake, sakwara da miyar egusi taji kayan ƙamshi ga naman ganda a ciki, farfesun iri biyu na kifi dana naman shanu,

Saboda rashin lafiyar azmi yasa suka girka abinci kaɗan, saboda a kalla abincin dare suna yin kusan kala 6,

Sehrish ce tayi aikin daka doyar tasha bakar wahala, azmi na kallonta sai dai tayi murmushi ganin yadda take faman zubda gumi,

sai da ana kiran sallar magrib sannan suka idasa aikin, har time ɗin ba wanda ya dawo daga cikinsu, junaid ne kawai wanda ke zaune yana a falo yana kallo a cikin laptop ɗinsa,

bayan sun gama gyaggyara kitchen ɗin, ta wuce domin yin sallah ga kuma buƙatar watsa tuwa,

wani korean drama yake kallo (true beauty) series ɗin yayi masa daɗi daga kwance saman doguwar kujerar ya ke kallo, ya kishingiɗa laptop ɗin kuma na asaman cikinsa,

Twins ne suka fara shigowa hannunsu riƙe dana juna, bai lura da su ba sai da yaji muryar Ayaan yana cewa “Lazy army we’re back,’

da murmushi a face ɗinsa ya miƙe zaune yana kallonsu ya ce” welcome back my brothers am glad to see you, nd i missed u,’

ƙarasawa sukayi atare suka manna masa kiss kowa agefen face ɗinsa,

sannan Jahan ya ce “what are you watching my bro,’

Junaid ya ce “its a korean series i really like it,’

“Ohh thats good enjoy your self,’ jahan ya faɗi hakan tare da sa kai suka wuce bedroom ɗinsu,

Cike da zumuɗi suka shiga ciki saboda a ƙagare suke da su soma,

“gsky mai aikin nan tukur yana ƙoƙari kalli fa yadda ya gyara komai fes,’ acewar jahan da yake ƙoƙarin cire kayansa,

Ayaan yace nima ina jinjina masa gaskiya kalli fa yadda muke hargitsa ɗakin amma ya gyare sa tsaf,

matsawa ayaan yayi kusa da jahan haɗe wa sukayi da junansu, a lokacin duk sun cire rigunansu da takalmansu, saura trouser ɗin jikinsu shiga cikin juna sukayi sosai, haɗa ido su kayi cikin na juna tare da sakarwa kansu murmushi, zura harshensa ayaan yayi a cikin na jahan nan take suka soma nishi alamar kai ya fara ɗaukan chargy,

A hakan da suke a tsaye manne da juna, jahan yasa hannunsa agaban wandon ayaan ya zame masa belt ɗin jikinsa, shima ayaan ya cire masa nasa kamar wasu mayu haka suka koma, ba sallah ba salati ba neman na ɗan caka

“Tell me how did you feel it ‘? Jahan ya faɗa cikin wani irin salo a lokacin da yake bin jikin ayaan yana licking ɗinsa kamar yasamu Sweet

Zamewa ƙasa yayi agaban ayaan yayi kneel down cikin wani irin salo, yasa hannu ya idasa zame masa trouser ɗinsa,

Tuni ayaan ya gigita tajin abunda jahan ke masa nan fa suka fita hayyacinsu,

Sai bayan sallar isha’e sannan sauran suka dawao kowa agajiye ya wuce bedroom ɗinsa,

A time ɗin Junaid ya koma bakin swimming pool saman ɗaya daga cikin chairs guda biyu dake kewaye da ɗan table,

wayarsa na ajiye a saman table ɗin, bakomai ya ke tunani ba fa ce babban yayansu rafayet yayi kewarsa sosai, gashi ba kullum ake samun sa a waya ba sai in shi ya kira mutun,

idonsa yakai yana kallon tsaftaccen ruwan dake malale a cikin faffaɗan pool ɗin launin sa yayi blue sky gwanin burgewa ga wata irin sanyayyiyar iska wacce kai tsaye take ratsa sassan jikin mutun, natsuwa da kwanciyar hankali ne suka zo masa loka ci guda har ya soma tunanin ya ɗauki wayarsa ya bibiyi numbar nan da aka turo masa message da ita ɗazu,

ɗaukar wayar yayi ya shiga laluban number cikin contact ɗinsa, dakyar ya gano ta , danna wa numbar kira yayi ta soma shiga ba’a ɗaga ba.

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 29-30

*Katsina State*

Kwana 3 kenan da sallamo su daga asibiti, an basu magungu nan da zasu rinƙa sha na tsawon wasu kwanan ki, sun dawo gidan tsohuwa dama wurinta suke zaune a wani tsohon gida wanda ya jima da fita hayyacinsa saboda tsaban talauci , babban matsalar da suke fuskanta rashin abinci gashi doctor yace suna buƙatar su samu abinci mai gina jiki sosai ,duk sun rame bayin Allah ita kanta tsohuwar ta rasa yaya zatayi da su ita ke fafutukar yadda zata samu abunda zata ciyar dasu, dama ƙosai da kokko take yi da safe shine sana’arta toh sakamakon rashin lafiyar su komai ya ƙare mata jarinta ma ya karye komai ya ƙare musu ƙarƙaf,

A wani ƙuƙuƙun ɗaki suke kwana gidan ɗaki biyu ne tabasu ɗaya suke kwana ita kuma a ɗayan,

Sam babu komai a ɗakin kamar kango haka yake, yar jakar kayansu ce sai wata guiguyayyaiyar katifa wadda ko kyauta akan ban ita banaso sai dai na kwana a ƙasa,

Husanna na kwance a samanta idonta a rufe, ga busassun hayawe a fuskarta, kana ganin ta kasan taji jiki har ynx akwai wasu raunukan a jikinta,

Shigowa jahad tayi da lemar ruwa ajikinta alamar alwala tayo, cikin jakar kayansu ta ɗauko wata tsohuwar hijabi ta sanya ta shimfiɗa wankakken ɗankwalinta a ƙasa kasancewar basu da abun sallah, kabbara sallah tayi ta shiga karanta fatiha sbd sallar isha’e ce karatu a bayyane ake yinsa,

takai raka’a ta biyu kenan taji muryar Husanna tana faɗin “sehrish sehrish ina so naje wurinta ina so naganta, nidai akaini wurinta bazan zauna a nan ba,

Sallah take amma hankalinta atashe yake saboda sanin cewa husanna nada ciwon hauka in ta fara ba wanda ya isa ya dakatarta da ita,

a firgice ta farka tana kiran sunanta tashi tayi a fujajen ta nufi hanyar fita ɗakin cikin sauri jahad ta katse sallar saboda gidan da suke ciki bai da kofa buhu ne akayi kofar dashi in kuma husanna tafita hanya zata miƙa,

ruƙo ta tayi da ƙarfi ta janyo ta nan fa suka kacame da faɗa dama haka ake fama da ita, ga wani irin ƙarfi dake gare ta saboda ba ita kaɗai bace, cikin kuka jahad ke cewa “dan Allah kidaina ya kike so nayi da kaina ne! nima jiran kiranta nake yi kiyi hakuri kizauna,’

muryarta har rawa take yi wurin faɗin “ni ita nake son gani, ki kaini wurinta ko ki ce mata tazo yanzun nan husanna nason ganin ta,’

ganin dagaske husanna fita zatayi yasa ta ƙara ƙanƙame ta, aiko batayi wani aune ba taji tayi wurgi da ita sai gata baje a ƙasa, nan take kuma goshin ta da hancinta suka fashe jini ya soma fito wa,

a guje husanna ta fita jikinta daga ita sai ɗaurin gaba kanta ba ɗankwali, sai tarin uban gashin dake gare ta mai yawan gaske ga tsari irin mai buzu-buzun nan mai kanan naɗar indomie , ya zubo mata har side by side ɗin fuskanta,

tana gab da zata fita tsohuwa tashigo cikin gidan hannunta ɗauke da kwano ta samo musu abincin da zasu ci,

Aikuwa karaf suka ci karo da husanna tuni kwanon hannun tsohuwa yayi sama ya faɗo kasa wainar dake ciki ta zube cikin ƙasa,

saboda tsabagen takaici yasa tsohuwa tafashe da kuka cikin kuka tace” kinsan wahalar nada sha kafin nasamo muku wannan wainar, sai da akayimun wulaƙanci da girma na da shekaruna kafin akaban ita bashi, amma kalki yadda kika zubar da ita kasa….’ kasa idasa maganar tayi cikin kunar rai ,

tsayawa husanna tayi jikinta yayi mugun sanyi saboda ita ba a cikin hayyacinta tayi ba, hasalima ta manta meya faru ita dai kawai taga tsohuwa na kuka agabanta, nan ta shiga tambayarta meya faru meyasa take kuka,

fitowa jahad tayi itama tana shesshekar kukan, juyawa husanna tayi tana kallonta cikin mamaki tace “wai meya faru meyasa kuke kuka pls tell me ?

Ƙarasa wa jahad tayi gaban tsohuwa cikin lallami tace” kiyi haƙuri dan Allah, kin sha wahala sosai akanmu duk da baki da wata alaƙa damu, akanmu ba irin wulaƙancin da ba’ayi miki ba amma ki kara jure insha Allah wahalarki baxata tafi abanza ba, Allah zai kawo mana mafita,

tana gama faɗan hakan takarasa inda kwanon wainar ya ƙife cikin ƙasa, zukunnawa tayi ta kwaso ta saman guda uku ce ƙasar bata shiga sosai ba, kwaso wa tayi ta zuba cikin kwanon ta miƙe da nufin taje ta wanko ta,

cikin sauri tsohuwa ta ruƙo hannunta tare da cewa” kin manta lalurar da ta same ki, idan har kikaci wannan wainar ciwonki zai iya dawo wa, ki aje kawai zanje na sake samo wani bashi tunda bazan barku da yunwa ba,’

gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi tsananin tausayin kansu ne ya kamasu, juya wa tsohuwa tayi zata fita jahad tace “dan Allah ki aramana wayarki mu kira sehrish dama saboda ita ne haukan Husanna ya tashi,”

Tsohuwa tasa hannu a ha6ar zaninta ta zaro yar nokia ɗinta wadda ake kira da rakani toilet ta miƙa wa jahad tare da cewa “na manta in faɗa miki naga kiran wannan numbar da sehrish ke kira da ita ban ɗauka ba ynx sai ku kira ta,’

Wani irin farin ciki ne ya baibaye su, jin cewa sehrish takira su kara su , karbar wayar jahad Tayi tare da riƙe hannun husanna tace mu shiga ciki mukira ta, sam husanna takasa rufe bakinta burinta taji muryar ƴar uwarta akwai abubuwa dayawa da take so ta faɗa mata waɗanda ke damunta,

Abuja city……..

message ɗin Fawan ne ya shigo wayrsa karantawa yayi “kai kana ina gayanan zamu fara ɗa’amin kashigo ciki,”

Murmushi ya saki tare da miƙewa ya shiga ciki samunsu yayi kowa ya hallara a dining table ɗin, zama yayi shima binsu yayi da kallo kowa ya shirya tsaf, twins nasanye da kimono robe ajikinsu, irfan da jabir nasanye da jallabiya fara, kanal yusif ya kimtsa cikin pyjamas ɗinsa haka khaleed da jabeer ma,

Cikin girmamawa ya shiga gaishe su amsa wa suka shiga yi, kafin kowa ya soma jiran isowar tukur mai aiki don yayi serving ɗinsu,

ɗagowa khaleed yayi ya kalli su twins ya ce “Oh shegentaka iri iri ynx ku wannan har abun sawa ce ƙirji a waje ,guiwowi a waje ,’ yaƙarasa maganar yana jiran amsa

” kai kuma ubansa ido naga cewa duk maza muke kaima in kaso u can wear ur shots nobody will disturbs u,’ jabeer ne yayi maganar yana harararsa,

shima khaleed ɗin harararsa yayi ya ce “am i talking to u stupid mind your own business if not u will see the rest,’

dariya irfan yayi “kai kun cika faɗa kamar kaji,”

fawan yace ” kaji fa kace ? Just like a women ina laifin kace kamar zakaru,”

dariya sukayi su duka sai lokacin kanal yusif ya tsoma baki “twins kunburge ni da baku sa baki ba, halin girma kenan,’

ta6e baki fawan yayi “a ina girman ya ke a tanan, kalle su fa kamar mata Ayaan ya tara uban gashin kai gayanan ya sauka har kafaɗarsa kamar wata mace,’

tsoki Jahan yaja jin an ta6a masa rabin ransa don haka ya ce”tubarkallah masha Allah aniyarka tabi ka, kuma yaje ya tara sumar kansa ne ko naka’

cike da jin dariya fawan yace “nasa ne, amma kasani duk ranar da Babban yaya ya dawo wlh duk sai kun aske kawunanku,’

ambatan sunansa yasa duk sauran jin bugun zuciya, murmushi junaid yayi tare da cewa ” u ave to get ready cos he informs me about his coming very soon,’

Shiru su kayi gaba ɗayansu kamar malam yaci shirwa ayaan ya ce “Are you serious about what are u saying !” cikin tashin hankali yayi maganar,

Junaid ya ce “of course”

Kallon juna suka yi shi da Jahan cikin rashin natsuwa,

Adai dai nan sehrish ta ƙaraso dama bacci ne ya kwashe ta, bayan tagama sallar isha’e

sai faman ƴan kame kame take, tayi tunanin zasuyi mata faɗa amma saita same su tsit kowa shiru tunda aka ambaci sunan babban yaya jikinsu yayi la’asar,

gaishe su ta fara yi sannan ta jinkirta tana jira taji me zasu je,

Yusif ne ya ce “ka zubamin farfesun naman nan asa mun romo sosai sai a haɗamin da slide bread a sama,’ ta amsa da to tafara zuba masa ta miƙa masa,

twins suka bada umarnin asa musu sakwara da miyar egusi wadda taji naman ganda 6aro 6aro, haka ta zuzzuba musu, sai ƙamshi ke faman tashi haka tabi sauran ta sassa musu wasu fatan doya da wake , shidai junaid farfesun kifi yace asamasa har fawan na jansa faɗa “karasa abunci sai farfesun kifi salon kaje kaita ƙarni,’

murguɗa masa baki yayi tare da cewa”ina ruwanka,’

bai ƙara cewa wani abu ba, binsu tayi ɗaya bayan ɗaya tana ajiye musu cup mai ɗauke da abunsha,

Sun natsu suna turawa cikinsu abinci wayar junaid ta shiga ringing , tissue ya yago ya goge hannunsa sannan ya dauko wayar daga cikin aljihunsa, ganin numbar ɗazu yasa shi ɗaga wa saboda dama jiran kiran yake yi,

“Amma kasan dai an hanamu picking calls while we’re eating food so u break the rule now,’? Fawan ne yayi maganar yana kallonsa, harararsa junaid yayi baice komai ba saboda ya sanya waya a kunnansa,

ji yayi kiran ya datse hakan na nufin flashing ne aka yo masa, bin kiran yayi tana fara ringing aka ɗaga, sa wayar yayi a handsfree yadda kowa zaiji me ake cewa, sallama yayi sannan ya saurara yana jiran mai wayar yayi maganar

“Aslm yar uwa jahad ce muna ta jiran kiran ki tun kwanaki baki kiramu ba,meyasa ?’

Saboda tsabagen ruɗin jin muryar jahad yasa sehrish sakin cup ɗin dake hannunta wanda ta zubawa Ayaan coffe cikinsa, nan take ruwan coffee ɗin ya 6arar masa a hannunsa har ƙirjinsa yayi tsalle ya ɗiga, tsananin zafi yasa shi fidda wani sound me ƙarfi,

Hakan yasa junaid katse wayar da yake yi saboda ganin halin da Ayaan ya shiga , gaba ɗayansu sun raxa na musamman jahan wanda rai , a6ace ya yunkura ya mike ya sharara mata mari har sau uku at the same time,

Cikin kunar rai yake cewa “wannan wane irin rashin hankali ne twin bro ɗin nawa kake so ka halakar, mutumin da ko sauro bai ta6a cizon fatarsa ba sai kai zaka illatar dashi,

👮🏻‍♂️ *ABBAN SOJOJI* 👮🏻‍♂️

“`The father Of Soldiers“`

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 31-32

Ba ƙaramin zafin marin nan sehrish taji ba, don kuwa har hancinta sai da ya fashe cikin kuka take basu hakuri ” kuyi hakuri bada sani na hakan ya faru ba bazan ƙara ba,

tsawa fawan ya daka mata “hakuri fa ? A wannan babban laifin da ka aikata zamuyi maka hakuri dole ka ɗanɗani kuɗarka kasancewa agidan Abban sojoji kake aiki,!”

duk sai junaid yaji jikinsa yayi sanyi ganin yadda mai aikin yake ta zubar da hawaye amma ba yadda zaiyi kuskurensa ne!

cikin tsananin 6acin rai Jahan ya ruko hannun Ayaan suka shiga ciki saboda ya shafa masa magani don wurin har yayi jawur ya tattare,

dukar da kai sehrish tayi tana jiran sauran hukuncin da zai biyo baya,

Fawan ne yaso ma magana ” ka fara tsallen kwaɗi daga nan har zuwa saman stair ka zakayo ta ɗayan stair ɗin ka kewaye falon gaba ɗaya haka zaga dinga yi har mu kammala cin dinner ɗin mu, bayan nan akwai wankin motoci kusan goma da sukayi ƙura sun jima a ajiye, a wanke su tsaf duk a cikin daran nan nakeson hakan, sannan ba shikenan ba gobe akwai wani horon,’

ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba jin irin wannan muguntar da fawan ya tsara mata, ta razana sosai saboda girman wurin babban tashin hankalin shine tsallen kwaɗi a saman matattakalar bene har biyu ya abun zai kasance?

muryarsa ce ta katse ta “Oya start frm now, we’re watching you banda tsayawa if u do so you will see the trouble,’

Zukunnawa tayi ta fara tsallen kwaɗin ta miki hanya ta tafi , idonta cike taf da hawaye damuwa iri iri, tasha wahala fiye da tunanin mutun tun tana yi cikin daɗin rai har kafafunta suka soma rirriƙewa ga wani irin raɗaɗi da suke yi mata, numfashin ta ne ya soma fita agalabaice amma haka ta jure ta daure taci gaba da yi , lokaci guda ta hada jini da majina a fuskarta hancin ta yasoma bleeding dama tana yi in taji wuya, babban tashin hankalin ma nan take period ta balle mata jini ya soma zuba ta ƙasan ta Subhanallahi ,

tana jin ɗiɗɗigar wani abu ta cikin pant ɗinta yana gangarowa amma batasan menene ba, Allah yaso wandon jikinta baƙi ne bazaiyi saurin bayyana ba, shi dama jinin al’ada sometime bakar wahala na kawo sa a time ɗin da bakayi tsammani ba,

Sam junaid ya gaza samun natsuwa yarasa dalilin dayasa yake jin tausayin tukur ɗin nan mai aikinsu, ganin bazai iya jure ganin wannan zaluncin na fawan ba yasa shi tashi cikin sauri yabar table ɗin duk da bai koshi da abincin ba ya miƙi hanyar zuwa ɗakinsa yana hawa saman stair ɗin suka ci karo da ita alokacin take saukowa , dakyar take numfashi kamar kwaɗo haka ta koma , bin kafafunsa tayi da kallo a hankali ta ɗago da idonta wadanda suka kaɗa su kayi jawur ta kallesa shima a lokacin  idonsa nakanta da take zuƙunne hannunta ruƙe da kunnuwanta,

Ido cikin Ido suke kallon juna tazama gwanin ban tausayi baiwar Allah, shi kuma amatsayin namiji yake kallonta tsananin tausayi ne ya kamasa a hankali ya furta “Am sorry” cikin wannan sanyayyiyar muryar tasa, yana faɗin hakan yabi ta gefenta ya haye sama,

Sai da kowa yabar dining table ɗin amma fawan mugu yana nan zaune yana jira mai aikin nasu tukur yagama punishment ɗin daya basa, sannan suje ya nuna masa motocin da zai wawwaken duk acikin daren nan kusan ƙarfe 9,_

JUNAID

tun da ya shiga room ɗinsa ya gaza samun natsuwa tunaninsa yaron nan mai aikinsu tukur bai kamata abarsa yayi wankin motoci cikin daren nan ba saboda shima mutun ne kamar kowa, in akai masa hakan ba’ayi masa adalci ba!

Tunano wa yayi da maganar babban yayansu (talaka da mai kuɗi duk ɗaya suke a wurin Allah babu wani banbanci don haka kada ku kuskura don Allah yabaku wani matsayi aduniya kuce zaku wulaƙanta wanda ke ƙasa da ku domin bakusan Wace rana zai yi muku ba, kuma Allah zai iya kar6e wannan matsayin da kuke taƙama dashi yaba shi wannan wanda kuka ƙasƙantar aranar ya zakuyi ? kowa zai iya kuskure a rayuwarsa amma aduk lokacin da wani yayi maka badai dai ba kazamzo mai hakuri da yafiya domin Allah ma yana gafarta mana in mukayi ba dai dai ba sai mu ƴan adam zamu gaza yin haka bazamuyi koyi da manzon Allah (SAW) ba ?

tuna wannan maganar yasa shi fita cikin sauri ya , cikin gaggawa yake saukowa down stair a lokacin har sehrish ta sume a ƙasan last step ɗin benen, shi kasan fawan baisan hakan ya faru ba saboda wayarsa yake ta faman daddanawa ,

Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yadda me aikin nasu yake sume a kwance ba numfashi ,

tsallake sa yayi ya wuce inda fawan ke saune sai faman murmushi yake yana daddana waya ,

Kamar daga sama yaji an fizge wayar daga hannunsa, cikin sauri ya ɗago yana kallonsa yace “Junaid wannan wane irin abune zaka sa hannu ka fisge waya daga hannuna kamar wani tsaranka,’

harara junaid ya wurga masa tare da cewa “bansani ba! saboda tsabagen mugunta irin taka kasa wancen mai aikin wahala wadda tasa shi sume wa amma sam baka damu ba ,”

tsoki fawan yasaki tare da sa hannu ya ƙarbe wayarsa ya wuce tagabansa yana faɗin “Matsalarsa ce,”

Binsa da kallo yayi har ya shige bedroom ɗinsa,

Ba yadda junaid ya iya dole ya koma inda tukur ke sume yasa hannu ya ɗaukesa, sam baima san ina ne inda ɗakin kwannansa yake  ba ,

Amma yasan cewa bazai wuce kwanar da ɗakin azmi take ba, kama hanyar yayi , ko nauyi baya ji haka ya dauke ta kamar yar baby ,

cikin sa’a ya samu ɗakin,da kafarsa ya turo kopar ɗakin ya shiga da ita , a saman bed ya kwantar da ita

Ransa ne ya basa ya dauko ruwa a freezer yazo ya yayyafa masa , yana sa hannu zai buɗe kofar idonsa yakai a jini dake hannunsa, har sai da gabansa ya faɗi rass ! ya soma tunanin jinin menene wannan !!! 😳

Bin jinin da kallo yayi tunani yayi kodai kansa ne ya bugu ayayin da ya sume a gefen stair,

Don haka cikin sauri ya koma yahau saman gadon inda ya kwantar da shi, a hankali yasa hannunsa yana tattare hular dake kanta a ƙoƙarinsa na ya cire hular yaga ta inda jini ke zuba,

Can kuma ya fasa saboda ganin yadda fuskar tukur ɗin ta dame da jini da majina, handkchief ya zaro daga front pocket ɗin rigarsa, ya shiga goge mata fuskarta,

Kwatsam gashin bakin da take manna wa a fuskarta ya ya goce saboda ya jigata gashi dama gam gare sa ruwa ya taba sa sosai ,

Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba ganin ya cirewa tukur gashin bakinsa duk sai yaji ba daɗi yakai hannu domin ya gyara sai yaga ya ballo gaba ɗaya, da ya ƙura ido yana kallon ƙasan hancin sai ya gane cewa dama babu gashin bakin fixing ɗinsa akayi,

Saboda babu hudojin gashi a wurin sai kansa ya ɗaure ya gaza gane menene dalilin liƙa gashin baki,

tabe bakinsa yayi alamar i don’t care, ci gaba da gogewa yayi ana haka sai ya ga gashin girar ta da aka liƙa masa shima ya zame gefe guda, tashin hankali a fili ya ce meke faruwa ne wai

Hannunsa ya sa ya ciro gashin girar duka guda biyun nan take asalin jagirarta mai kyau ga tsari ta bayyana,

Natsuwa yayi ya ƙurawa face ɗinta ido sai yaga fuskar ta koma ta mace sak ! Kansa ya gama ɗaure wa sanya gashin girar dana bakin yayi cikin handkchief ɗinsa ya naɗe su ciki ya ajiye gefen bedside drawer ɗinta,

Ya jima yana kallon wannan kyakkyawar fuskar har lokacin bai kawo wa ransa cewa maca ba ce ba sai da yasa hannu ya tumbuƙe hular dake kanta, nan take gashin kanta ya tarwatse ya warwaro har saman shoulder ɗinta mai kyau ga laushin gaske,

Nan fa junaid yayi zuru yana ganin wannan ikon Allah ( wonders shall neva ends)

ganin ta soma motsi zata farka, yasa shi yin wuff ya dira daga saman bed ɗin ya boye abayan curtins ɗin dakin,

buɗe idonta tayi waɗanda suka cika tab da kwalla, sunyi jawur sun ƙanƙance, wani irin raɗaɗi taji a marar ta, gashi sam ba ƙwarin jiki atattare da ita, wata irin kasala ce ta dabaibaye ta a galabaice ta miƙe tana zubar da hawaye, yunƙurawa tayi tare ɗan matsawa gefe nan taga jini malale a saman bedsheets ɗinta ya baci sosai ,

Wani irin mugun bugu xuciyarta tayi mata saboda ita sam batasan jinin menene ba, saboda bata ta6a yinsa ba wannan ne karo na farko a wannan shekarun nata 17years,

lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka ganin jini 6aro 6aro na fitowa daga jikinta, cikin kuka take faɗin “innalallahi wa’inna ilaihirraji’un shikenan na mutu wayyo Allah wannan wane irin ciwo ne naji haka, nasan mutuwa zanyi

tashi tayi a firgice tasa hannu ta cire zanin gadon ta nannaɗe sa ta ajiye sa anan,

gaba ɗaya ta fita hayyacinta ta zabure kamar wata mahaukaciya  tama rasa me zatayi , cikin toilet tashi ge tana kukan baƙin ciki ,

A jiyar zuciya junaid yasaki, har yanzu ya gaza gasgata abunda idonsa ke ganin masa, shin wanene wannan tukur mai aikin mu ko kowa ? kamar mace nake gani fa, oh my God mafarki nake ko gaske, kodai idanuna ne ke nuba min hakan taya tukur mai aikinmu zai kasance mace !! Ya jefa kansa wannan tambayar

Hannu yasa tare da murxa eyes ɗinsa don yayi comfirming abinda ke faruwa cewa gaskiya ne its not a dream,

yana nan tsaye la6e a bayan labulen yana jiran fitowarta, saboda ya gane wa kansa zahiran abunda ke faruwa ,

Sehrish kuwa tamkar ranta zai fita, saboda tsoran jinin da ta gani ga kuma ƙyanƙyami daya kamata,

cire wandon jikinta tayi sannan ta cire rigar ma, hannu tasa ta balle abunda take matse ƙirjinta dashi tayi wurgi dashi,

ta firgita da ganin yadda jinin yake gangarowa a tsakankanin cinyoyinta  kai kace fanfo aka buɗe,

Cikin tsananin tsoro ta ƙarasa gaban fanfo tashiga dambe da jinin nan ita ala dole sai ta dakatar dashi daga fitowa 😟

Tana wanke wa yana sake kwaranyo wa kamar ana ingiza shi,

ganin yaƙi tsayawa yasa ta dakata, ta zuƙunna a wurin tana kuka tayi mai isarta, sannan ta yanke shawarar ta koma cikin bedroom ɗin ta samu wani abu ta cusa, sam ta manta cewa pant ɗinta ɗaya ne kuma ya bace shima, koda me zata sa ?

A haukace ta fito cikin sauri junaid ya rufe idonsa tare da jan labulen ya rufe face ɗinsa, bai jin daɗin tsayawa ba saboda yaga abunda yake haramin agare sa sam babu kaya ajikinta,

Jikinsa ne yasoma kerma nan take yadinga jin zuciyarshi na tashi ynx ya tabbatarwa kansa cewa tukur mai aikinsu zankaɗeɗiyar budurwa ce ba namiji ba, shigar maza kawai take yi saboda wani dalili nata,

buɗe wardrobe ɗin tayi saboda rashin natsuwa duk ta watso da kayan dake ci tashi ga laluben ɗan kyallen da zata sa, wani mayafi ta ɗauko sai da ta riƙe sa gam a hannunta sannan ta tuna cewa bata da pant ɗin da zatasa,

zuƙunne wa ƙasa tayi ta shiga rera wani sabon kukan, gwanin ban tausayi jin har yanzu wannan blood ɗin yana mata flooding a under ɗinta yasa ta koma cikin toilet tana kuka,

Shiga tayi taja kofar ta rufe …

Ganin ta shige yasa junaid saurin fita daga ɗakin, tafiya yake amma tunanin yadda zai taimaka mata yake yi saboda ya gane cewa akwai abubuwan da take buƙata, amma tayaya? bayaso ta gane cewa ya ganta a matsayin mace, baisan wani hali zata shiga ba,

Maganar abbansu ya tuna a inda ya ke cewa

_aduk lokacin da kuka ga wani na buƙatar taimako, to kutaimaka masa indai kuna da halin yin hakan, a sanadiyar hakan kuma Allah zai agaza muku a lokacin da kuka shiga wani hali na rayuwa,”

Cikin sauri ya hanzarta nufar bedroom ɗinsa , key ɗin motarsa ya dauko tare da kuɗi , sannan cikin gaggawa ya kama hanya ya fita daga main palour ɗin ,

Babu kowa tsit kake ji amma ko’ina akwai haske kamar rana, saboda an ƙawata gidan gaba ɗaya da wasu irin electric bulbs,

Moto park ɗinsu ya nufa buɗe inda tarin motocinsu ke nan, motarsa yayi ya shiga nan take yayi mata key yaja ta,

Sam junaid ya manta cewa security guards ɗin gidan soldiers ne kuma bana wasa ba, kuma ba’a basu iznin subar wani ya fita a wannan lokacin ba kosu fawan dake satar hanya su fita night club su suka san ta boyayyiyar hanyar da suke fita,

Santal ya miƙi titin da zai sada ka da babban gate ɗin gidan, yana isa wasu gabza gabzan sojoji guda 4 suka tunkare sa kamar zakuna,

a dolensa ya dakata da tuƙin ya tsaida motar, jikinsa sai rawa yake yi ba don komai ba sai don uzirin dake gare sa, zuge glass ɗin motar yayi yana kallonsu a yatsine, .

“Where are you going in this darkness night,”? ɗaya daga cikinsu ya tambaya yana kallonsa, banza yayi baice musu komai ba don yasan koya ce ɗin ba barinsa zasu yi ya fita, rigima ce zata tashi ƙarshe suce zasu sanar da Abbansu a tada hargitsin duniya,

jin yayi shiru yasa ɗaya daga cikinsu daka masa tsawa tare da cewa “maza ja mota ka koma gida ƙaramin yaro dakai sai taurin kai,’

Ɗaya daga cikinsu ne ya kwatsa ma wanda yayi masa tsawa magana” stop shouting at him ! he’s a young lallashinsa ya kamata kayi ya koma ”

xukunno wa yayi cikin lallami ya ce masa “pls go back ba’a bamu izni mubar wanin ku ya fita ba daga gida a wannan time ɗin,’

girgiza kai junaid yayi tare da cewa “am sorry to say i won’t go back just allow me to go, duk rigimar da za’ayi sai dai ayi amma ba inda zani i will stay here till u give me the permission to go,’

Ya ƙarasa maganar tare da jingina kansa jikin kujerar motar yana kallonsu fuska adaure”

*_Hafsat Bature_*

~(Boss Lady)~

Page 33-34

Kallon juna suka shiga yi, ganin cewa ya toge yasa ɗaya da cikinsu sake yi masa magana cikin lallami ” tell me why do u want to go out ? if u need something i can go and buy it for you ,”

Jin hakan yasa junaid jin sauƙi aransa, hannu yasa ya zaro kuɗi kusan dubu goma ya miƙa masa sannan ya cije ya daure ya ce “pads nake so na mata kwali guda sannan panties dozen ɗaya bansan size ɗin ba amma karya wuce na ƴar 17 years ”

tsananin mamaki ne ya kamasu jin yace pad da panties, amma basu ce komai ba saboda baya a tsarin aikinsu fira ko tambaye tambaye da ɗan masu gida,

“Sojan yace shikenan, ka koma ciki nan da 15 minutes sakonka zai iso,

Amsa yayi da cewa “thank you i will be waiting,”

Sannan yaja motar a hankali yayi baya da ita ya karya kwana ya koma ciki,

A bangaren sehrish kuwa tagama galabaita, ta jigata sosai tarasa uwar ubanta , sai faman zarya take tsakanin toilet da bedroom , daga taji ya zubo sai taje ta wanke ta dawo ciki yana ƙara zubowa sai ta koma da gudu tana kuka 😖

Junaid sai faman zagaye zagaye yake yi acikin babban falon yana jiran dawowar sojan da ya aika, sai faman zullumi yake yi gudun kada yarinyar ta halakar da kanta da damuwa saboda ya lura ta tsorata sosai,

Knocking yaji da sauri ya ƙarasa bakin kofan shiga falon , sojan ne ya dawo hannunsa ɗauke da kwalin pads tare dozen na pant kamar yadda ya umarta , hannu junaid yasa ya karba yana zabga masa godiya,

Sergiant ɗin yace “ga sauran chanjin ” ko dubu biyar bai kashe ba a siyayyar junaid yace ” bana buƙata”

Yana faɗin hakan ya kama hanyar da ɗakin sehrish yake,

murmushi sojan yayi tare da cewa a cikin zuciyarsa “lallaine yaro! iyayenka sun tara ma kana daga zaune kana shan iskar A.C,’

yana faɗan hakan ya juya ya fi ce,

Cikin sanɗa yake tafiya time ɗin da ya isa kofan ɗakin tsawa yayi jikin door ɗin yana sauraren kukanta tana cewa ” Ya Allah kadauki raina na huta, narasa me zanyi bansan menene ke faruwa da ni ba, jini ko ina ya ilahi

lumshe idonsa yayi tare da buɗe su lokaci guda, hannunsa na rungume da kwalin pads ɗin ga panties ɗin dake cikin leda asaman kwalin ya haɗa ya rungume a ƙirjinsa,

“Junaid ynx taya za’ae ka kai mata wannan ? Shin zata ji daɗi kuwa idan ta gane cewa ka gane cewa ita maca ce ba namiji ba? mezai faru idan tagane cewa ka ganta acikin wannan yanayin zata ji daɗi kuwa !?

Natsuwa yayi yana sauraran abunda zuciyarsa ke sanar dashi , rufe idonsa yayi tare da cizon red lips ɗinsa yana mai jin takaici gaza shiga yakai mata taimakon gaggawa, ga kukanta da yake ji ba ƙaramin hurting ɗinsa yake yi ba, tausayinta yake ji saboda bata da kowa anan da zai taimaka mata in bashi ba dayasan halin da yake ciki, Allah sarki daɗin uwa kenan da ƴan uwa da ace tana da ɗaya daga cikinsu a kusa da ita da abun yazo mata da sauƙi,

Jin alamar ta shiga cikin toilet yasa shi yin saurin kutsa kai a hankali ya shiga, ya ajiye mata kwalin pads ɗin a saman gadonta abunda bai sani ba sehrish bata da masaniya akan wannan abun daya ajiye mata,

Jin alamar tana ƙoƙarin fitowa yasa shi yin wuff ya fice, a kofar ɗakin ya tsaya yana sauke ajiyar zuciya natsuwa yayi yana sauraran ta taciki,

Sai faman wiping tears take yi, tayi jaga jaga tafita out of sense ɗinsa, har wata ƴar rama tayi ga azabar menstruation ga tashin hankalin blood din dake bleeding a in between legs ɗinta,

dakyar tasamu ta ɗaura wannan mayafin fari mai sharara ajikinta, tsayawa tayi agaban mirror tana lalube lalaube ita kanta batasan me take nema ba kawai burinta tasamu abunda zata cusa a vagina ɗinta ko tasamu yadaina zuba tana cikin laluben nan ,

Karaf idonta ya hango mata kwalin nan da junaid ya ajiye mata a saman bed, ta cikin madubi ta hangosu,

A firgice ta juya tana kallonsu, cikin tsananin tsoro take takawa a hankali tana tunkararsa har ta isa gabansu,

Tsayawa tayi cak tana kallonsu , ledar sama tabi da kallo dayake ta kana iya hangen set na panties ɗin da ke ciki, tabbas tagane cewa pant ne amma tarasa gane wannan madai-daicin kwalin na menene 😥

Karanta jikinsa tayi tare da furta “Dry love” sunan pads ɗin da tagani ajikinsa kwalin kenan,

tunani take wanene ya ajiye mata wannan? anya ba al’janu bane ba? waiwaye ta shiga yi tana kallon gefe da gefenta taga ba kowa sai ita,

Kamar wata sullu6uyo haka ta koma, hannu takai cikin tsoro ta ɗauki ledar panties ɗin ta zaro su tana kallo,

Ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, amma bata jin zata iya anfani dasu saboda batasan waya ajiye mata ba,

Ajiyesu tayi sannan takai hannu tasha fa saman kwalin pads ɗin kafin ta janye hannun cikin wani irin yanayi furta ” Ya allah ka tsare ni daga sharrin aljanu, ni dama nasan wannan blood ɗin da nake gani bana lafiya bane, ashe sune suka shafe ni,”

Nan tashiga jera wani kukan, duk a kunnan junaid ganin cewa zasu kwana ido a buɗe ga dare yayi sosai kusan ƙarfe 1:00 ynx ,

Cikin kuka ya sake jiyo ta tana cewa “Dan Allah koma wane aljani ne yake hukunta ni akan ƙaryar da nayi na shigar mace a matsayin namiji don Allah ayi haƙuri a haife mun wlh nima ba da son raina nayi ba..” kuka ne yaci ƙarfinta

Jin cewa yarinyar tayi amanna da cewa aljanune suka kawo mata kayan nan kuma sune suke horar da ita yasa junaid gyara muryarsa cikin wata irin amsa kuwa yace “Ke ! Yarinya ! mune nan ke hukunta ki bisa zunubin da kika aikata ! ,” .

Zaro ido sehrish tayi jin wannan  muryar mai ban tsoro tabbas wannan muryar aljanin ce ta faɗa a ranta, nan take zufa ta soma sintiri a fuskarta dukkan ilahirin jikinta kuma ya soma makekketa, ta ƙanƙame jikinta a tsorace tace “dan Allah kuyi hakuri bazan ƙara ba i promised u kuskure ne ku yafe mun wayyo Allah na nashiga ukuna,”

murmushi junaid ya saki dama yayi tunanin hakan yadda take a firgice tsaf muryarsa zata koma mata ta aljanu,

don haka ya ƙara gyara muryarsa ya ɗaga ta sosai ya ce “Munjiiiiiii ! Zamu iya yafe miki amma bisa wasu sharruɗɗa in kuma kika kuskure zamu raba sassan jikinki mu kaisu bayan duniya hhhhhhhhh,”

ya ƙare da wata irin dariya mai razanarwa, nan take fitsari ya kubce mata ta tsorata matuka kuma ta ƙara tabbatarwa kanta da cewa aljanun ne ke maganar saboda ita dai bata ga kowa ba acikin ɗakin,

cikin kuka tace “Na amince komai kuke so zanyi,” .

lumshe ido junaid yayi shi kaɗai yasan yadda yake jin daɗin wannan yanayin,

Hannu yasa tare da gyara makoshinsa yace “Sharuɗi na farko ! Zaki runtse idanunki kada ki buɗe har sai munce ki buɗe in ba haka ba hhhhhhhhhhhhhhh zamu tsoma ki jikin rijiya gaba dubu,”

la66anta har rawa suke yi wurin faɗin “Na amince na amince zann ..zann nama rufe yanzu haka wlh banzan buɗe ba don Allah kada ku sani acikin rijiyar nan banso zan bi umarninku,” ta ƙarasa maganar tare da runtse idanunta cikin tsananin tsoro,

“Kin rufe !!! taji aljanin ya ambata cikin sauri tace “eh na rufe, .

dariya cike fal a bakinsa dakyar yake gumtse ta, a hankali ya tura kofan ɗakin yasa kai ya shiga,

Bin ta da kallo yayi bil’hakki ta damtse idonta garam, kawar da kansa yayi daga kallonta saboda hakan na isa yasa shi cikin yanayi saboda mayafin da ta ɗaura shara shara yake,

Cikin sanɗa ya ƙarasa gaban kwalin pads ɗin yasa hannu ya buɗe sa, zaro dami ɗaya yayi ya ajiye saman gadon, 6an6are sa yayi cikin gaggawa wa ya curo guda ɗaya, sannan ya ɗauko pant guda ɗaya ya shimfiɗa a saman katifar gadon, ya buɗe sa sannan ya ɗauko pads ɗin ya cire ledar jikinsa mai gam, ya manna a tsakiyar pant ɗin ya sanya mata shi da kyau sannan ya ajiye, ɗagowa yayi ya sake kallon fuskarta ba ƙaramin tausayi ta bashi ba ganin yadda eye lid ɗinta ta kumbura, hancinta yayi jawur saboda yasha matsa ga lips ɗinta sun kumbura sosai,

Sai da yasanya mata pads ɗin ajikin panties kusan guda biyar, duk ya jera mata su, sannan ya lallla6a ya fice ya tsaya jikin kofar, yana sauke ajiyar zuciya kafin yayi gyaran murya ya ce “muna baki umarni da ki buɗe idonki yanzu,”

A hankali ta buɗe idonta basu sauka akan ko’ina ba sai kan abunda ya haɗa mata, binsu tayi da kallo gasu nan ajere gwanin kyau, muryar aljanun ce ta sake katse ta ” Sharaɗi na biyu kina sauraron mu da kyau ,”?.

Cikin natsuwa tace Eh ina sauraronku,

Murmushi jubaud yayi tare da ɗaga muryarsa da ƙarfi yaci gaba da cewa ” muna baki umarni da ki ɗauki ɗaya daga cikin panties ɗin nan ki sanya shi in kika kuskure zamu ɗauki gangarar jikinki mu kaita ƙasa ta bakwai,”

Jiki na rawa tasanya hannu ta ɗauki pant ɗaya ta zura a jikinta, nan take taji wani sanyi a ranta, cike da biyayya tace “Aljani na sanya,”

gaza jure dariyar dake cinsa yayi don haka ya kwashe da dariya cikin wani irin salo kamar Aljanun ne ke dariya yace “Hhhhhhhhhh yarinya kinyi kyan kai, don haka ! daga ynx in kina so ki tsira daga faɗawa daga tarkon bakin aljani dole ki rinƙa sanya wannan abun da muka aje maki in ba haka ba zaki fuskanci matsala …..hhhhhhhh,’

Cikin sauri tace ” zan….zanyi komai kuka ce,”

sannan ya ce”Sharaɗi na ƙarshe ! Hhhhhhh yanzu ki hau saman gado ki kwanta da safe zamu kawo miki saƙo hhhhhhh,”

Cikin gaggawa ta haye saman gadon, har ta kai hannu zata ɗauki bedsheet ɗinta ta tuna cewa ya 6ace don haka dole ta hakura, ta ƙudundune kanta, tayi lamo tana jiran bacci yazo ya ɗauke ta,

Ajiyar zuciya junaid ya saki don shima ya gaji ga bacci dake damunsa shida ya saba bacci da wuri,

Jin shirunta ko shesshekar nan ta kuka ta daina yi hakan ya tabbatar masa cewa she’s sleeping , don haka ya lallaba ya tura ƙofar ya zuwa hannu jikin bangon ya kashe mata hasken ɗakin sannan ya tafi,

Tabbas taji ƙarar kashe mata ƙwan ɗaki da akayi amma bata kawo komai aranta ba, don haka tace acikin zuciyarta “daga gani waɗannan aljanun masu imani ne basu cutar dani ba, sun taimake ni, Ya Allah na gode maka

Da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da ita,

A bangaren junaid kuwa hmmm ina sam bacci ya ƙauracewa idonsa daga ya runtse ido fuskar Yarinyar yake gani, sam ya gaza sukuni sai fama juyi yake yana rungume fillow a ƙirjinsa ya gaza mantawa da wannan beautiful face ɗin mai cike da annuri ga sanyin kyau launin fatarta ba ƙaramin burgesa tayi ba ya jima baiga mace me qualities irin na yarinyar ba,

(to dama ai macen novel ce 😂)

Asubar fari kowannensu ya farka domin shirin tafiya gabatar da sallar asba banda wasu daga cikinsu,

Kamar junaid wanda bai samu bacci ba Daren jiy, ya ƙudundune cikin lallausan blanket ɗinsa kamar wani jinjiri ga fillow ya yi hugging ɗinsa tightly a chest ɗinsa,

Fawan ne ya shiga bubbuga kopan ɗakin nasa ƙwan! Ƙwan !! shiru ba alamar zai zo ya buɗe, ƙara knocking yayi bai taso ya buɗe kofan ba,

Tsayawa bakin kofan yayi yana kiransa “Junaid ! Junaiiiid !!! Wake up bro its time to pray oh shirt ! am tired pls open the door,” ya ƙasa maganar cike da ƙagara,

jabeer, irfan ,khaleed da kanal yusif suna ata down stairs suna jiran su, saboda atare suke tafiya sai sun harhaɗu duka sannan,

tsoki yusif ya saki tare da cewa “ni fa bana son wasting time, nauyin baccin nan nasu junaid da twins abun yayi yawa don haka daga ynx ƙarfe 9 kowa zai rinƙa bacci wannan umarni na ne,’

Amsa wa sukayi da “toh insha Allah zamu kiyaye hakan,

Khaleed ya ce “bari naje na tada su twins , yana faɗan hakan ya kama hanyar ɗakinsu, time ɗin daya isa ya tsaya a bakin kofan yana knocking da ƙarfin gaske,

Suna cikin manne da juna kamar chew gum, sautin bugun ƙopan da khaleed ke yi musu ne yasa jahan farka wa, fuska a kumbure alamar anyi disturbing ɗinsa cikin ƙuƙuni yace” who is that pls,”

Khaleed dake waje ya ce “ubanka ne in hakan bai ishe ka ba ka fito ka gane wa Idonka stupid,’

turo baki yayi kamar yana gabansa, hannu yasa yasha fa sumar Ayaan tare da kai bakinsa saitin kunnan sa ya ce “wake up honey its time to pray !

Shiru bai motsa ba zubawa fuskansa ido jahan yayi yarasa dalilin dayasa a duk time ɗin daya kalli ayaan sai yaji ya koma mesa mace sak, kodan yana da kyau sosai ne oho,

hannu yasa tare da jan dogon hancinsa cikin zolaya ya ce”ko dai kafarka ko kuma in sa ma cool water a face ɗinka,”

Murmushi ayaan ya saki dama yana jinsa shiru kawai yayi, cikin muryar shagwa6a ya ce” i know u can do that cos u love me so much u dont wanna hurts me,”

murmushi jahan yayi “now its ok ga yaya khaleed can yana buga ƙopa, time ɗin sallah yayi ka tashi muje toilet mu tsarkake jjikinsu saboda jiya mun 6ata shi da sperm,’

ƙasa ƙasa su ke magana saboda sun son khaleed na tsaye a kofan door ɗin yana jiransu,

“Ni bazan iya tashi ba sweetheart kasala nake ji, jiya duk ka kashe mun jikina… Cikin shagwa6a ayaan ya faɗi hakan,

Ba ƙaramin yanayi yasa jahan ba ganin yadda ya ke magana cikin kwarkwasa,

Sauka daga gadon jahan yayi ya zuƙunna at d egde of the bed ɗin ya juya masa bayansa ya ce ” ina fatan hakan yayi maka,’

yar dariya Ayaan yayi tare da janye bargon jikinsa ya sauko ya haye bayan jahan tare da ƙanƙame sa, a haka suka shiga cikin toilet ɗin

Shaf shaf suka sakarwa kansu shower suka ɗauro Alwala, suka fito cikin sauri kowa ya cire kimono robe ɗin dake jikinsa suka sanye jallabiya don tsabagen yaudara hada riƙe cazbaha a hannunsu kamar wasu larabawa haka suka fito hmmmm

Fawan kuwa har ya gaji da buga kofan junaid ƙarshe yasa ƙafarsa da ƙarfi ya harba kopan ta buɗe, sakin baki yayi ganin sa ya faɗo daga saman bed ɗin bargon lulluban yayi gefe ga fillow daya ƙanƙame a ƙirjinsa,

to fah fawan ya faɗa tare da ƙarasa wa inda yake baje , samun fuskarnan tasa yayi ɗauke da wani irin matashin murmushi dimples ɗinsa sunyi matuƙar lotsa wa kai kace ba bacci yake ba,

russinawa yayi tare da kai hannunsa ya cafki fillow dake ƙirjinsa yana ƙoƙarin ciresa, nan fa junaid ya damƙe fillow gam cikin magagin bacci yake faɗin “kyakkyawa ce ! ita ta musamman ce meyasa bazata bayyana min komai ba ,

Tsananin mamaki ne ya kama fawan , ganin zai bata masu lokaci yasa Shi sa ƙarfi wurin cire filon aikuwa junaid ya haɗa dashi duka ya rungumo a jikinsa ya ƙanƙame yana faɗin “naji daɗin kasance wa tare da ke a daren jiya zanso na sake ganin wannan kyakkyawar surar,’

Tsananin haushi ne yasa fawan ya gartsa masa cizo a kunnansa,

A firgice ya farka tare da sakin fawan da filon ya tashi zaune idonsa sunyi ja alamar bai samu enough sleep ba,  cike da ƙululu yake kallon fawan “dama nasan kaine bakin mugu laifin me na maka ka cizar mun Kunne na saboda rashin tsoron Allah,’

Ya faɗa yana kallon fawan wanda ke zabga masa harara “dan Allah malam tashi kaje ka ɗauro Alwala kai kaɗai muke jira,’

rai abace junaid ya tashi yana faɗin “dole sai munje tare ne, kuyi gaba sai na biyo ku abaya,’

 

Ya idasa faɗan hakan yana turo kopan toilet ya shige yana ci gaba da ƙuƙuni,

Sun kammala harhaɗuwa don haka suka kama hanya  domin zuwa gabatar da sallah.

Comment and share.*🔥ABBAN SOJOJI🔥*

_WRITER_ *HAFSAT BATURE*

~BOSS LADY~

page  35~36

SEHRISH ❤

baiwar Allah tana ƙudundune gwanin ban tausayi ta farka da wani irin matsanancin ciwon kai, ga zazza6i ga ciwon ciki duk ita kaɗai ga fuska a kum6ure saboda kukan da tasha,

Ko kakkwaran motsi ta gaza yi tarasa yaya zatayi da rayuwarta, jikinta sai kerma yake hatta haƙoranta game wa suke da juna suna bada wani sauti kaf kaf, tayi matuƙar galabaita tana so taje ta sanarwa azmi amma tagaza ko tashi sai faman nuƙurƙusa take yi,

……hmmmm ina matuƙar tausayawa waɗanda basu da uwa atare dasu basu da wani nasu a kusa da zai kasance tare dasu aduk lokacin suga shiga hali irin wannan Allah sarki much love to our mothers & sisters and so on ,

Addu’o’e kawai take jero wa daga bakinta tana neman sauƙi a wurin Allah, raɗaɗi iri iri ga matsananciyar damuwar dake damuwanta, wa zata kaiwa kukan ta in ba Allah ba ?

A wannan halin wani baccin ya qara ɗaukanta,

tun da suka dawo daga masallaci kowa ya koma bedroom ɗinsa wasu suka koma bacci wasu kuma suka kama karatun ƙur’ani kowa da kiwon daya kar6e sa,

gaza samun natsuwa yayi tunda ya dawo tunaninsa wane hali yarinyar take ciki? ga kuma promise ɗin da yayi mata nacewa da safe zata ga sako a matsayinsa na bakin aljani,

Cikin sauri ya buɗe closet ɗinsa jerin kaya ne iri iri masu tsadar gaske, gidan ƙasa ya duba jerin sababbin barguna ne da zanin gado, hannu yasa ya zaro blanket ɗaya da bedsheet ɗaya sababbi fal masu kyau da tsada, ajiye su yayi a saman bed ɗinsa,

gaban dressing mirror ɗinsa ya koma a cikin drawer ɗin dake haɗe da madubin ya janyo gida na farko,

Katan katan ne na kwalin sabulu masu kyamshin gaske, dozen ɗaya ya ɗauko tare da wani haɗadden soson wanka acikin ledarsa,

a saman blanket ɗin ya ajiye su,

Zuba musu ido yayi yana kallo yama rasa me zai yi gani yake kamar sunyi mata kaɗan, sam bayaso ta gane cewa shi ba aljani bane ,

fita yayi ya wuce ɗakin da suke ajiyar magunguna iri iri da allurar da sauransu tamkar patient room haka yake , saboda suna da military doctor & nurse hakan yasa suka buɗe ɗakin don ko mutun bai lafiya za’aya iya duba sa acikin gidan,

yasan cewa dole ta tashi da ciwon kai saboda kukan da tayi kuma dole ta tashi da ciwon ciki, don haka ya ɗauko mata magungunan da yasan zata samu relief, ya zura cikin aljuhun rigarsa,

Duk hakan bai ishe shi ba, yana ji aransa cewa dole ta buƙaci abinci akwai yunwa a tattare da ita,

Komawa ɗakinsa yayi cikin sauri ya rungumo kayan da ya ajiye a saman gadonsa ya fito dasu,

Ya ci sa’a ba kowa har yanzu gari bai idasa washewa ba suna can suna sharar bacci,

Lalla6awa yayi a hankali ya wuce bedroom ɗinta tsayawa yayi a kopan ɗakin saboda baiso ace idonta biyu, kasa kunnansa yayi yaji shiru ba motsin komai ɗan tura kopan yayi ya leƙa yana kallonta,

Kwance take idonta rufe alamun bacci take amma jikinta sai rawar sanyi yake a haka ta kwana tun jiya dama da bedsheets ɗinta take lullu6a kuma ta 6ata sa, ga tsoron baƙin aljanin daya ziyarce ta daren jiya duk shi ya firgita ta tarasa kwakkwaran motsi balle ta ɗauko wani abu tayi covering jikinta da shi,

Ajiyar zuciya ya saki, cikin sanɗa ya kutsa kai ya shiga yana takawa a hankali a gefenta ya ajiye mata kayan, sannan ya zaro lallausan blanket ɗin ya rufa mata a jiki a hankali, har cikin ranta taji shi gaba ɗaya har kanta ya haɗa ya lullu6e mata, sai gata tsulum acikin bargon kamar wata new born baby,

smilling yayi alokacin da yaga ya kammala sa mata batare da ansamu matsala ba,

Yana fita ya wuce ɗakin azmi tsayawa yayi bakin kofa yayi mata knocking,

“Shigo ciki”

Ta faɗa daga ciki kutsa kai yayi ya shiga, zaune ya same ta saman sallaya da ƙur’ani a hannunta alamar karatunsa take yi,

murmushi tasaki ganinsa tare da cewa “junaid yau kaine a ɗakina i forgt when last ka shigo min,’

bai bata amsa ba sai da ya Samu wuri ya zauna agabanta ya lankwashe kafa sannan yace “barka da safiya dafatan kun tashi lafiya,’

“Lafiya lou Alhamdulillah ince ko lafiya,’ ? ta tambaya tana kallonsa don tasan dalili kawai ke kawo su wurinta,

Cikin natsuwa ya ce “meya faru jiya baki fito ba wurin dinner ɗin mu,’

“Bani da lafiya ne dama na faɗawa tukur meyasa ka tambaya,?

ta faɗa tana kallonsa, murmushi junaid yayi yana kallon azmi ya ce “nasan komai fa ynx!”

Ji tayi gabanta ya faɗi duk da batasan me yake nufi ba cikin nuna rashin fahimta tace” me kake nufi da kasan komai junaid?

“Ina nufin na gane cewa tukur ba namiji bane maca ce kuma nasan kinsan da haka azmi,”

shiru azmi tayi tare da yin jigum tana kallonsa ƙarya ta ƙare amma sanin cewa junaid ne yasa bata tashi hankalinta ba saboda sauƙin kansa,

“taya akai ka gane hakan”? ta jefa masa tambaya,

“Jiya bayan fawan ya bata punishment sakamakon kuskuren 6arawa Ayaan ruwan zafi a hannunsa,’

Nan junaid ya kwashe duk abunda ya faru daren jiya ya sanarwa azmi, hankalin azmi ba ƙaramin tashi yayi saboda ita batasan duk wannan budurin da akayi ba da ace tana kusa da bazata bari fawan ya hukunta sehrish ba, a wani 6angaren kuwa taci dariya sosai jin shiriritar da tayi daren jiya don junaid bai 6oye mata komai ba,

dakyar ta tsagaita dariyar da take tace masa “ynx me ka yanke akan yarinyar zaka sanarwa yan uwanka cewa maca ce ita ?.

girgiza kai junaid yayi tare da cewa “a’a korarta zasu yi nasani koda zasu sani ba yanxu ba sai sun saba da ita sosai, ni ma kuma bazan bari tasan na sani ba insha Allah,’

azmi taji daɗin hakan dama tasan hakance zata faru domin junaid yaron kirki ne duk cikin yan uwansa tafi sonsa ji take kamar ita ta haifesa saboda yadda yake respecting ɗinta,

“Ya sunanta’?

Ya tambaya yana kallonta azmi tace” sunanta SEHRISH”

short smile ya ɗan saki kafin yace” ynx azmi pls ki taimake ita, nayi mamaki jiya alamu sun nuna cewa bama tasan menene menstruation ba, tasha wahala sosai akwai kayan da nakai mata pls kice ke ce kika kaimata, sannan ga magani nan ki bata ta sha amma kafin nan ki sama mata abunda zata ji saboda akwai yunwa atattare da ita,” ya ƙarasa maganar yana sa hannu cikin front pocket ɗinsa ya zaro maganin ya miƙa mata, ajiye kur’anin tayi akan sallayar kafin tasa hannu ta kar6a tana cewa “kada ka damu insha Allah komai zai tafi dai dai nima ina ji araina tabbas akwai damuwa a tattare da yarinyar, a yanayin da kafaɗa min abunda ya faru jiya ya tabbatarmun da cewa tarasa wani 6angare na ilmi arayuwarta sakamakon wani dalilin,’

Har cikin ransa ya ƙara ganin girman azmi a idonsa, itama taga farin ciki a fuskan junaid wannan ya tabbatar mata da cewa akwai wata a ƙasa, Murmushi tasaki kawai

Yunƙurawa yayi ya mike ya kama hanyar fita har yakai bakin kopa ya sake jiyowa ya kalli azmi yace”pls & pls take care of her,’

Dariya azmi tayi ganin yadda ya susuce aranta tace tun ynx daga daren jiya kawai,

Shima fice wa yayi yana murmushi yanzu ya samu natsuwa don haka ya koma bedroom ɗinsa ya kwanta yana jiran safiya ta idasa yi koya samu yaga wannan kyakkyawar yarinyar,

Sehrish

Motsin mutun da taji a kusa da ita ne yasa ta farkawa tayi mamakin ganinta cikin bargo sai tayi tunanin cewa ko mutuwa tayi ne aka rufe ta don ita tasan ba komai ta kwanta,

Hannu azmi tasa ta zame mata bargon ta yane shi gefe ɗaya,

Ta tsorata da ganin yadda sehrish ta koma fuska tayi sumtun ido jawur ko magana bata iya yi,

“Subhanallahi meyasa sameki haka sehrish”? Azmi ta faɗi hakan cikin yanayin tashin hankali a matsayin batasan meke faruwa ba,

wani sabon kuka ne yazo ma sehrish cikin kukan take cewa “jiya baki nan fawan yasani tsallen kwaɗi saboda na 6arawa ayaan ruwan coffee mai zafi bansani ba, nasha wahala sosai aunty azmi har ciwo naji sosai tun jiya nake faman bleeding bansan me ya kawo hakan ba,”

ta ƙarasa maganan tare da sa ƙarfi cikin rashin jin kwarin jiki ta mike zaune,

Cike da damuwa azmi tace ” am sorry for that, I was not feeling well I ave told u about my headache it really pained me yesterday night tunda bacci ya dauke ni I no longer knew where my head was, now am listening to you tell me what happen to u ?

nan sehrish ta shiga jero mata abunda ya faru hada labarin aljanin daren nan da kuma maganar jini da taga yana bleeding daga under ɗinta,

bayan ta kammala bayanin ta shiga Nuna mata kayan da aljanin ya kawo mata sannan tace “Aunty azmi dama akwai aljani me mutunci irin haka ?

nan sehrish ta shiga jero mata abunda ya faru hada labarin aljanin daren nan da kuma maganar jini da taga yana bleeding daga under ɗinta,

bayan ta kammala bayanin ta shiga Nuna mata kayan da aljanin ya kawo mata sannan tace “Aunty azmi dama akwai aljani me mutunci irin haka ?

data shoulder dinta azmo tayi tare da cewa ” dukkan abun da kika gani jiya ba gaskiya bane ! you’re just dreaming cos you were scared but am the one that brought all these stuffs to u, kuma ni ce na kawo ki dakin ki, bansan dai mai ya faru ba amma nafito around 10 na ganki while u were fainted on the floor

sai nayi deciding na dauko ki na kawo ki bedroom dinki shine naga blood na zuba a jikin ki, dama already Ina da pad da panties shine na kawo miki wannan shine gaskiyan abunda ya faru,’

Azmi ta karasa maganar tana kallon sehrish wadda tasaki baki galala don mamaki gashi azmi ta rikita ta ta canza mata tunanin ta,

Azmi ta lura da yanayin da sehrish ta shiga sai taji tsoran karfa yarinyar ta rikice don haka ta kara da cewa “Nima na taba yin irin wannan mafarki just like u did, ba wani Abu bane, then maganar menstruation wato blood din da kika gani ba na cuta bane ko ciwo sakamakon punishing dinki da fawan yayi , wannan Jini ne na al’ada Wanda ko wace mace take yi shin baki taba sani ba kuma dama baki taba yi ba am just doubt abt it,

Ta ƙare maganan tana kallon ,

ɗan shiru tayi tana nazari ita dai tasan kamar ta ta6a ji game dashi sai ynx take ɗan tuna wani abin husanna da jahad sun riga ta farawa tasan game dashi rashin kwanciyar hankali da rashin natsuwa yasa ta gaza fahimtar cewa na al’ada ne tabbas tsohuwa ta ta6a koya musu wannan ,

” nasani mantawa nayi amma aunty azmi wai dagske ba wani aljanin da yazo min ? kina nufi is not true amma fa har abu aka samin a pant na sanya kuma ni banga kowa nd i didnt see u a time ɗin ,’

ganin ta fara ƙoƙarin gane ƙarya take mata ne yasa ta ce “pls forget about the past ! we’ll talk about It later ,

Daganan azmi ta ƙara wayar mata da kai game da yadda zata tsarkake jikinta da sauran muhimman abubuwan,

Duk ranar batayi aiki ba azmi ce tayi komai kuma har room ɗinta takai mata breakfast lafiyaye hada kayan marmari , sannan ta tunatar da ita akan tasha maganin da ta bata,

Junaid yayi kewar ganin ta, ya kasa fita ko ball ya buga saboda tunanin ta , sai faman sintiri yake yi yaga ko zata fito amma shiru babu ita ji yake kamar yaje bedroom ɗin nata yayi mata magana,

Gaza jurewa yayi cikin sauri ya sauko down jikinsa sanye da jeans da tshirt

A kopar ɗakin ya tsaya tare da yin knocking ,

lokacin har tayi wanka ta shirya tsaf shigar da ta saba yi ta maza, ta canza kuma pad ɗin data sa,

har ynx batayi tunanin wasu abubuwan ba  kamar hankicif da taga an naɗe mata gashin bakinta da na jagirar ta duk ba tayi tunanin wani abu ba, sai ta sawa aranta cewa duk azmi ce tayi wannan,

ta gyara komai daƙar tayi fixing ɗin gashin bakin saboda gam ɗinsa ya ɗan saki saboda jikinsa yayi wetting sakamakon kukan da tasha,

Jin knockinga yasa ta yin gaggawar idasa kifa hular akanta, sannan ta ƙarasa gaban kofan ta buɗe,

Lokacin da ya yi arba da kyakkyawar fuskar nan tata sai yaji natsuwa da kwanciyar hankali sun zo masa

“am tukur dama nazo naji meke faruwa ne yau banganka ba,’;

ɗan murmushi tayi jin yadda ya damu da ita tace” Zazza6i nayi amma ynx da sauƙi Alhmdllh,’

ta ƙarasa maganar tana sunnar da kai, aransa ya ce “mai ƙarya ɗan wuta, amma a zahiri sai ya ce “Allah ƙaro sauƙi,

“Ameen ngde” ta faɗa tana ƙara gyara tsayuwanta,

Shiru su kayi na ɗan wani lokaci wani irin kallo yake binta dashi confidence ɗinta na bashi mamaki 🤔*🔥ABBAN SOJOJI🔥*

_Writer Hafsat Bature_

~Boss Lady~

Page 37 to 38

Shiru su kayi na ɗan wani lokaci wani irin kallo yake binta dashi confidence ɗinta na basa mamaki ita ala dole namiji ce,

“Can u make a choculate cake for me,’?

Ya tambaya yana kallonta

ɗan zaro ido tayi hakan ba ƙaramin kyau tayi masa ba,

Cikin en ina tace” choculate cake kuma ranka shi daɗe banda lafiya,’ ta faɗi hakan tana ɗan dafe waist ɗinta alamar akwai ciwo wurin,.

yar dariya yayi kafin ya ce “naso ace zaka iya haɗamin da nayi ko browsing ne a wayata sai na baka ka ga yarda akeyi saboda ina buƙatar cin…..’

tun kan ya idasa ta katsesa “zan iya tsaf in ka ban wayr zan ga yadda ake yi sai nayi….

abun yaso yasa shi darawa dama dagangan yayi mata haka saboda ya gane cewa ita ce ke satar masa waya tana kiran yan uwanta, yayi hakan ne don ya haɗa ta da ƴan uwanta dake nemanta,

tayi tunanin ita ce tayi masa wayau batasan cewa shine yayi mata wayau ba domin yasa recording da za’rar ta fara wayar recording ɗin zai soma yana so ya ji meke damun ƴan uwan nata,

Bayan ya bata wayar ya fi ce daga gidan, jikinta har rawa yake yi ta samu nama,6oyewa tayi a wani corner ta danna wa su husanna kira,

A lokacin jahad bata kusa sun fita amsar wani tallafi da ake rarrabawa a gidan wani ɗan majalissa ita da tsohuwa sun bar wayr a gida,

wayau su kayi ma husanna don ta zauna suka bata wayar tayi game sannan suka datse ta a ɗaki da key gudun kar ta fita kar kuma wani ya shigo ya cutar da ita tun da ba kofa a gidan buhu ne kamar labule,

da tagama buga game ɗin taji shiru gidan ba kowa ta kwakkwala masu kira kawai sai ta kama rera kuka tayi mai isarta ta koma ta kama bacci,

Ringing ɗin wayar ne ya tayar da ita har sai da ta tsorata saboda ta ajiye wayar a saitin kunnan ta,

Cikin sauri  tasa hannu ta ɗaga wayar tana sauraran jin muryar wanene,

Sehrish ta gyara murya tare da cewa”assalamu alaikum yar uwa ni ce pls kiyi mgna da sauri ya jikin naku ya husanna taji sauƙi ko har ynx da haukan nan akanta ?

ta tambaya tana jiran amsa

Sautin kuka taji tunda taji hakan ya tabbatar mata da cewa husanna ce ta ɗauki wayr saboda ta tsani ace mata tana hauka ita bata yarda ba har yau !

“Subhanallahi kash ! husanna ke ce..? ta tambaya kamar tana a gabanta,

Cikin muryar kuka tace “ni ce! shine kika tafi ki ka barmu ko ? cikin wahala da bakin talauci kullum ba abinci sai mu jera kwana 5 muna cin ɗumamen tuwa….’

Jin wannan maganar yasa kwalla ta taru a idon sehrish ci gaba da sauraronta tayi

“ni nagaji dan Allah ki dawo ko kizo ki dauke ni wlh bana jin daɗi, ko isasshen bacci bana samu ga sauro ga yunwa ko kayan sawa babu kullum wasu tsummo karai tsohuwa take bamu muna sawa ni nagaji gsky,’

Sehrish batasan lokacin da kuka ya 6arke mata ba, sam tagaza magana tuni jikinta ya soma jijjiga kamar wadda sanyi ya buga

“Kinyi shiru baki ce komai ba ? kin manta oumman mu tace duk runtsi duk wuya karmu rabu da juna amma kika tafi ko ? baki sona ko ? So kike na mutu ko, to shikenan zan je na kashe kai….’

tsawa sehrish ta daka mata wanda hakan ya dakatar da ita daga magana ” ya isa ! Ya isa! ya kike so nayi? saboda ku nake zaune a nan husanna, bashi ne na dubu ɗari tara akaina how can i pay it ? i dont ave anything dole na tsaya nayi musu aiki na tsawon shekara ɗaya da rabi,saboda ku !

daker ta ƙarasa maganar tana share kwalla,

Jin yadda sehrish ke faman shesshekar kuka yasa jikin husanna yin sanyi ta ce “kiyi hakuri in na 6ata miki rai bansan ran ki zai 6ace ba,’

dakyar sehrish ta tsaida hawayen ta gyara wayar a kunnanta tace” rai na be baci ba ina kuka ne saboda ku halin da kuke ciki, amma karki damu kinji ƙanwa ta in na samu kuɗi zan tura muku insha Allah ki tayani da addu’a,’

cikin sanyin murya husanna tace” ina miki addu’a kullum bana mantawa,’

Murmushi sehrish tasaki kamar suna kusa da juna tace”I love u so much shashasha,’

tana jiyo muryar husanna ta cikin wayar tana tiƙar dariyar saboda ta tuna mata da wani abu,

daga nan sehrish tace “zan ajiye waya send my regards to jahad & tsohuwa,’

husanna tace”insha Allah zasu ji”

daga nan ta katse wayar ranta fal saboda taji muryar husanna, cikin koshin lafiya,

nan fa ta soma tunanin yadda zata haɗa masa chocolate cake ita hasalima a suna kawai tasan cake ɗin,

Wuri ta samu saman ta zuƙunna ta shiga lalubar masa waya instead taje tayi aikin daya sata,

Gallery ɗinsa ta shiga madaddalar hotuna, na fa ta fara ganin haɗaɗɗunan pictures ɗin samarin familƴ ɗinsu hada waɗanda su kayi a ƙasashen waje,

A nan ne taga hotonan wannan haɗaɗɗen matashin saurayin mai shegen kyan nan, shi da junaid su kayi hoton a cikin jirgi da alama privet jet ne mallakinsu saboda su biyu ne acikinsa, sunyi hugging ɗin junansu fuskarsu ɗauke da murmushi,

wuce wa gaba tayi next picture nan fa ta ƙara ganin hotonsa cikin dandazon sojoji suna sara masa,

Ƙasa tayi ta shiga videos nan fa ta gane wa kanta zahiri,

Videos ɗinsa tagani kamar hauka da alama junaid na yinsa sosai,

ran ta yana bata cewa wannan ba kowa bane face BABBAN YAYA wato surgeon general RAFAYET,

ta jinjina wa matsayinsa ganin kowane video zakaga dubban sojoji ne turawa kewaye da shi suna taka masa baya, ko suna sara masa ,

tana cikin wannan laluban wayar ta soma ringing bin hoton da ya bayyana a calling ɗin tayi ,

zaro ido waje tayi tare da buɗe baki alamar mamaki, mutumin da take bibiya ynx haka shine ke kiransa a waya,

tunani ta soma yi ta yi ɗaga ko kar ta ɗaga ? katse wa kiran yayi wani kuma ya sake antayo wa wayr ta ci gaba da ringing,

Cikin tsananin tsoro da jin fargaba ta ɗaga tare da karawa a kunnanta bata ce komai ba, tayi shiru tana sauraronsa

abun da ya ɗaure mata kai shima bai ce komai ba ! hasalima alamu sun nuna cewa ya manta daya danna kiran saboda tajiyo hayaniya mutane ta cikin wayar alamar tattauna wa ake,

katsewa kiran yayi, janye wayar tayi daga kunnan ta ta zuba ma number ido da sunan da aka a jiki “My everything”

ta jima wurin zugudun tana kallo kamar daga sama taji muryar junaid

“An kammala haɗa min cake ɗin”

A firgice ta tashi zaune tana kallonsa tayi wuri wuri da ido tana mazurai,

Murmushi ya saki tare da miƙa mata hannu ya ce “Gimme my phone,”

cikin rawar murya tace”am..umm..dama ynx nake am..:

hannu yasa yayi mata alamar tayi shiru kafin yace its ok ba damu zan sa a kawo min ne kawai,’

ya faɗi hakan tare karban wayar ya shige ciki binsa da kallo tabi shi har ya 6ace wa ganin ta,

A cikin waɗannan kwanakin wata irin shakuwace ta shiga tsakaninta da junaid tarasa dalilin dayasa yake kyautatamata sannan abunda ke ɗaure mata kai ynx baya bari ta shigo ɗakinsa musamman inda ga shi sai shorts (gajeran wando) a jikinsa, abunda bata sani ba shine ya gane cewa ita macece da cen abunda yasa yake sakin jiki bai kunyar yin komai a gabanta saboda a tunaninsa namiji ce, ga shi kullum sai ya bata aron wayarsa ya ce ta buga game, waɗannan abubuwan na matuƙar ɗaure mata head,

Ba ƙaramin daɗin hakan taji ba, kullum sai sunyi waya dasu jahad da husanna, kullum sai tayi mata complain akan ta turo musu kuɗi sun gaji da talauci, tai ta faman basu hakauri akan su bata lokaci,

bata samun matsala da kowa ynx, tana taka tsantsan akan duk wani abu da zai sa a kore ta daga gidan, Mutunci tsakanin ta da azmi sai ƙara habbaka yake abun ba’a magana ta maida ta kamar auntyn ta ita ma haka azmi ta maida ta kamar yar cikinta ko nace ƙanwarta komai na tafiya dai dai,

A 6angaren su husanna kuwa dake cikin mawuyacin halin kamar kansu farau talauci, suna buƙatar agajin gaggawa domin maganungunan da doctor ya ba ta sun ƙare dole sai an samu ƙuɗi an siya mata wani,

don haka jahad ta yanke shawarar turama sehrish saƙo, a lokacin da message ɗin ya shiga wayar na hannun junaid,

Karantawa yayi kamar haka” sister maganin husanna fa sun ƙare akwai matsala tazama wata zararriya ta hana mu sakat pls ki taimaka mana,”

Koda junaid ya karanta message ɗin sai ya tura masu da “Send me your account number,’

ganin wannan saƙon cikin zumuɗi jahad ta zari hijabi don tashiga gidan makwabtansu saboda yarinyar gidan nada account number su nan basu dashi,

kafin ta dawo husanna tafarka daga bacci saboda cikinta daya katsa, ta soma laluben waya saboda toilet ɗin akwai duhu irin na gargajiyar nan ne ginin ƙasa, nan ta samu yar nokia ɗin da jahad ta ajiye a saman jakar kayansu taɗauka  ta shiga da ita toilet ɗin, to ka’ida in ta kunna fitilar wayar ta zukunna sai ta fara buga game tana sukuni,

Tana cikin zuƙunno nan wani ƙaton kyankyaso mai fiffike yayi tsalle sai saman kanta, cikin firgici ta tashi a razane nan take wayar dake hannunta ta sulale daga hannunta ta faɗa cikin ramin masan Subhannallah,

Can ance a turo account number nan kuma wayar da suke da ita kwalli kwal ta faɗa cikin masai,

Zaro ido tayi tare da buɗe baki saboda tsoro, taji haushin kyankyasan nan har taji cewa bazata kyalesa ba dole ya mutu,

Nan suka shiga sintiri ita dashi shidai wings ke gare sa, ita kuma da ƙafa take binsa sai faman tashi sama yake yake yi tana binsa da gudu, hada ɗauko takalmi tana kokarin kwaɗesa,

Baki a washe jahad ta shigo ta samo account number ɗin yarinyar ta rubuta mata a farar paper,

ɗakinsu ta shiga tana neman waya, sama ko ƙasa babu ita ta shiga lalube ko’ina babu, tashiga mamakin ina aka kai wayar bayan babu,

tunawa tayi da cewa tabar husanna a kwance tana bacci tabbas tana wurinta , fita tayi cikin saurin tsakar gidan

Adai dai lokacin Husanna tafito tana sauke ajiyar zuciya tace”wash Allah da ace ban kashe shi ba dana binne kaina,’

“Husanna ina wayar nan take”?

jahad ta jefa mata tambaya ita bama ta lura da ita ba sai da tayi magana, nan fa tashiga wurga ido na mara gaskiya shiru tayi tana kallon ƙasa,

hakan ba ƙaramin tayarwa jahad da hankali yayi ba, saboda akwai abunda ko ba’a faɗa maka ba zaka fahimta ne ta yanayin mutun,😿*🔥ABBAN SOJOJI🔥*

*writer* *HAFSAT BATURE*

 

~Boss Lady~

*page* *39 to 40* 😁

jiki na rawa ta ƙarasa gabanta cike da tsoro tace” husanna ina waya ?

Shiru tayi tana mazurai, hannu jahad tasa ta shaƙo wuyan rigar dake jikinta cikin matsanancin tashin hankali ta sake cewa “tell me where did you kept it ?

muryar na rawa husanna tace” wani kyankyaso ne ya hau mun saman kaine shineee…sai wayr ta faɗa cikin….’

“Cikin Uban me !? jahad ta tambaya cikin daka mata tsawa,

duk tabi ta gama firgita tata cikin takura tace “cikin ramin”

Aikuwa rai a tsananin bace jahad ta shiga kai mata bugu ta ko’ina, nan suka shiga dambe, faɗa ya katse me a tsakaninsu kai kace basu son junansu,

A ƙarshe jahad tasake ta cikin tsananin ƙunar rai tace”shikenan kinyi farin ciki ko? kada kiyi tunanin ina bakin ciki ne don kin jefa waya, ina bakin ciki ne saboda kinyi mana babbar asara, taimakon da zamu samu na kuɗi a siya miki magani mun rasa, sannan ƴar uwarmu ma mun rasa ta ! saboda daga ni har ke ba wanda ya riƙe numbar da take kira, sannan ita inta kira zata ji waya a kashe kinga shikenan tamu ta ƙare…..’

Zuƙunnawa tayi tare da fashe wa da matsanancin kuka, itama husannar koma tayi ta tsaya jikin bango tana shesshekar kuka jin jahad tace sun rasa ƴar uwarsu SEHRISH

A cikin wannan yanayin mara daɗi tsohuwa ta same su, shigowa tayi hannunta ɗauke da bakar leda wadda fura ce aciki ta samo musu don su sha tun safe rabonsu da abinci har izuwa yanzu da ake ta faman kiran sallar isha’e

hankali a tashe ta ƙarasa inda jahad take tana faɗin”lafiya meya faru ƴa’ƴan ne me kke wa kuka? Nasan yunwa ce ku kwantar da hankalinku gashi nan na samo mana ƴar fura musha,’

Jin wannan maganartata yasa jahad ƙara sautin kukan nata, tana kuka tana magana “ba wannan zararriyar bace nasamu sehrish tace mu tura mata acct number, nashiga gidan makwabtan mu wurin mamee nace taban nata acct number ɗin, sai da na anso ina shigo wa nasamu husanna wai ta jefa wayar cikin masai,”

Jin wannan maganar yasa tsohuwa sakin ledar furar dake hannunta, tashiga tafa hannu tana faɗin “Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un shikenan ae kun gama dani shekara 10 kenan wayarnan da ita nake lallabawa ashe kune ajalinta, kun kyauta,’

tana faɗin hakanan ta shige cikin ƙuƙuƙun ɗakin nata ta rufo kopa, tunda suka ga hakan yatabbatar masu da cewa ran tsohuwa ya bace, saboda bata taba yi musu haka ba,

Gashi ɗaki ɗayane a gidan ɗayan ɗakin ya rushe sakamakon ruwan sama da akayi,

ga wani irin sanyi a wajen nan da nan jikin husanna ya soma kakarwa, hankali a tashe jahad ta tashi daga zukunnawar da tayi ta tunkare ta,

“zo muje mu lallashe ta tabuɗe mana ɗakin mu kwanta waje sanyi,”

Haka suka je bakin kopan ɗakin sukai ta kwankwasa wa amma tsohuwa tayi shiru babu alamar zata buɗe,

A ƙarshe sai dai suka rungume junansu suka ƙanƙame juna saboda sanyin dake akwai, wannan abun ya tuna musu da wani lokaci daya shuɗe a rayuwarsu mara daɗin ji 😭

Rashin gata baiyi ba a duniya

Story by (Hafsat Bature)

Rashin kwanciyar hankali yasa ko kwakkwaran bacci bata samu ba a daren jiya, tunaninta meyasa samu wayar tsohuwa ba’a samu tayi tarying amma swich off, hakan na matuƙar tayar mata da hankali tsoronta kar ace wani abu ya same su su duka,

Jiki a sanyaye ta kammala shiryawa ta wuce kitchen wurin azmi,

“Good morning aunty azmi”

ta faɗa tana kallonta, azmi dake faman gyare gyare a kitchen ɗin tace “morning baturiya hope u slept well”

yar dariya sehrish tayi ta shiga daga ciki tana faɗin “dame zamu fara ne?

Azmi tace “yau fa akwai manyan baki da zasu zo,”

dafe ƙirji sehrish tayi kamar wadda taji mugun abu tace”suwa!”?

dariya axmi tayi ganin yadda ta ɗan raxana,

“suna da yawa wasu yau zasu zo wasu sai gobe, daga ciki akwai chief of army staff wato Abban su junaid wanda zai dawo daga ƙasar chaina, amma shi gobe ne zai zo yau dai wasu daga cikin manyan ƴa’ƴansa dake other states ɗin zasu zo domin tarbarsa,

Da buɗan bakin sehrish sai cewa tayi “Babban yaya fa shi bazai zo ba,”?

girgiza kai azmi tayi tace”oh shirt! ni wannan babban yayan da kike ta faman zumuɗin gani bansan dalili ba,’

“Aunty azmi it’s just a question ba wani abu ba, naji kince manyan ƴa’ƴansa shiyasa na tambaya,’ ta ƙara maganar tana wasa da yatsun hannunta,

Kafin azmi tace wani abu junaid ya shigo da sallama, nan fa sehrish ta hau satar kallonsa yayi fes abunsa yayi dressing cikin suit black colour

A cikin zuciyarta tace “wai madarar kyau”

“Morning azmi how was everthing” ya faɗa shima yana ɗan satar kallon sehrish,

Azmi tace “barka dai komai lafiya kana buƙatar wani abu ne”_?

sam baiji me tace ba domin idonsa nakan sehrish wadda ita ma shi take kallo,

Sai da ta maimaita da cewa”junaid ina magana”?

a ɗan firgice ya mayar da kwayar idonsa kan azmi da ɗan murmushi yace” am dama nazo na sanar miki da cewa sai gobe jirginsu abba zai sauka, sannan jibi babban yaya tare da marshall Omar da Captain suma zasu taso, ”

Saboda tsananin zumuɗi sehrish tasa hannu a baki irin mamakin nan ga wani farin ciki daya baibayeta kai kace tasan shi ne,

Junaid ya ci gaba da cewa “kada kusha wahalar yin aiki, akwai ma’aikata da zasu zo daga company zasu tsara komai ku hutu kawai,’

yagama faɗan hakan tare da juyawa ya fice,

Ita kanta azmi murmushi kawai take yi ba don komai ba sai don ta ƙosa sehrish taga wanene wannan babban yayan da take ta zumuɗi a kansa, tayi tunanin ganinsa abune mai sauƙi , mutumin da saboda tsabagen zafin rai ko magana bayayi saboda abu kaɗan ke 6ata masa rai,

“Yanzu hankalin ki zai kwanta tunda kinji cewa babban yaya zai dawo ko “?

murmushi sehrish tayi ita kanta tana mamakin wannan zumuɗin nasan ganinsa

tunda aka sanar da su cewa Babban yayansu zai dawo next tomorrow saboda kiɗima ranar ko breakfast basu ci ba, ba inda suka je kowa zullumi yake yi ba don komai ba sai don tsoransa,

a bangaren su twins kuwa suna a bedroom ɗinsu sai faman safa da marya suke yi yau ba harka, duk hankalisu ya tashi su sunsan mezai faru a zuwan Babban yayansu,

cike da damuwa Ayaan yace”gsky jahan am gonna cut my hairs today if not babban yaya will accuse something about us am afraid of him seriously,”

Ya faɗi hakan tare da zama a side bed ɗin yana kallon Jahan wanda ke faman zarya frm well to well yana haɗe hands ɗinsa yana naushin su atare,

“just feels like to cry wlh, Ayaan i dont wanna see him, am really scared of his eyes, mutumin da ko haɗa ido kukayi dashi sai gaban ka ya faɗi, we must find the solution,

cikin damuwa ayaan yace “what is the solution now ? do u ave any plan?

wuri jahan ya samu ya zauna gefensa tare da cewa “yanke gashi da kace zaka yi is not the solution, sbd shima yana tara doguwar suma ,ayaan kasan bama iya rayuwa even one hour without having sex , and if he finds out about it we are already doomed,”

Zugum su kayi kowa na tunanin yadda zasu 6ullowa lamarin,

Can Jahan yace “me zai hana mu kama room a hotel ? when ever we are horny we can go there hakan yayi ?

Jinjina kai Ayaan yayi ganin jahan ya kawo shawara ruƙo hannunsa yayi tare da cewa “thats why i love u so much cos you’re very smart hakan yayi,’

murmushi jahan yayi yana kallon cikin idonsa ya ce “since i found the solution ynx sai muje mu ci abinci ko? ko ba kajin yunwa?

Ayaan ya ce “Am starving too let’s go nd ave something to eat”

A tare suka fito

Tabbas jin zuwan baban yayan nasu ba ƙaramin kashe musu jiki yayi ba domin duk wanda yasan yana aikata ba dai dai ba neman takansa yake yi,

cleaners ɗin da aka ɗauko daga company sun hallara kuma sun fara gudanar da aikinsu, wasu parts aka buɗe wanda ita kanta sehrish batasan da zaman su a katafaren gidan gidan ba ,

ta dai san akwai wuraren dake a rufe bata taba ganinsa a buɗe ba, kamar other parlours ɗin dake a gidan amma yau ko’ina buɗe sa ake yi muraren saboda gyara,

Bayan sun kammala aiki ta shiga neman junaid saboda ta damu da rashin su husanna tana damuwa sosai,

ganin sai faman zarya take yi daga upstair zuwa down ga ma’aikata sai fama aikace aikace suke,

“Zonan sehrish” azmi ta kira ta alokacin itama ta shigo babban parlourn ita kuma sehrish tana saukowa down ƙarasawa tayi gaban ta tana faɗin “gani aunty azmi”

Azmi tace”lafiya kike ta faman yawa ce yawace baki ganin ma’aikata na aiki ne”? ta tambaya tana kallonta,

“Junaid nake nema ne” ta bata amsa, azmi tace i don’t think yana kusa ki koma ɗakin ki idan ya dawo i will inform you,’

Amsawa tayi da toh sannan ta wuce izuwa room ɗinta, kasa zama tayi sai faman safa da marwa take burinta taji wani hali su husanna suke ta damu da son jin hakan,

tana cikin wannan zagayen ta dinga jin jiniyar shigowar motoci kamar hauka, har sai da gabanta ya faɗi rass, cikin sauri ta ƙarasa gaban window ɗinta ta janye curtain ɗin jiki ta zuge glass ɗin tana leƙen abunda ke wakana a waje,

motoci ne na sojoji ke ta faman antayowa ciki, sanye cikin uniform ɗinsu, kowanne hannunsa sanƙame da jibga jibgan bindigu, wani irin miyau ta shiga haɗiye wa saboda tsananin tsoro, kamar mara gasky kamar ita suka zo kamawa,

Sakin labulen tayi ta koma ciki ta ci gaba da zagayen tana zare ido, abubuwa dayawa suna zuwa mata aranta damuwarta shine yaya zatayi idan suka gane cewa ita mace ce? tana tsoran waɗanda zasu zo musamman abbansu chief of army staffs da kuma surgeon general rafayet ga marshall Omer tare da Captain Adams da zasu zo daga outside country , gashi taji hada sauran ƴa’ƴansa waɗan da batasani ba, wasu ma anan garin suke wasu kuma na other states,

Yinin ranar cikin fargaba tayi shi, ga tunanin wani hali su husanna ke ciki ga kuma tunanin zuwansu Abban sojoji,

A bangaren junaid kuwa ya jira yaga ko zasu turo masa account number yaji shiru ba text message a time ɗin yayi niyar ya tura masu 300k duk da baisan ko su wanene ba, amma yana ji aransa cewa siblings ɗin Sehrish ne,

Jahad & Husanna

Abunda ya faru daren jiya A waje suka kwana, cikin dare jikin husanna yayi tsanani sosai saboda weather din akwai sanyi and she’s athmatic, haka ta rinƙa tari jikinta har jijjiga ya ke yi, hankalin Jahad ba ƙaramin tashi yayi ba, tana rungume a jikinta, wani irin ajiyar zuciya taji husanna na saki wanda bata ta6a jin irin hakan ba, a hankali ta kira sunanta “Husanna!”_.

Cikin wata irin galabaitacciyar murya tace”mutuwa zanyi baki ji yadda ni ke ji ba, dan Allah idan kin haɗu da sehrish ki ce mata ta yafe min ke ma ki yafe min nasan najima ina 6ata maku rai…….’

tana gama faɗin hakan rai yayi halinsa 😖

*🔥ABBAN SOJOJI🔥*

_the father of soldiers_

_Story by_ _Hafsat Bature_💓

*Boss Lady*

*page*  *41 to 42*

Theres some typing errors like spelling mistakes🥱its not edited just manage 🤨

_     Sulalewa tayi daga jikin jahad ta yi ƙasa luuuuuu….wani irin ihu jahad ta saki cikin tsananin tashin hankali tabi ta ƙasan inda take kwance a baje rai hannun Allah,

“Kada kiyi mun haka ƴar’wa pls stay alive me kike so na faɗa ma sehrish? In ki ka tafi ni kuma ya kke so nayi da rayuwata? narasa sehrish ynx ke ma zan rasaki…’ cikin ƙunar rai tayi maganar tana kallon face ɗin Husanna wadda ke fidda numfashi sama~sama idonta na ƙoƙarin rufe wa gaba ɗaya,

Fashewa tayi da kuka saboda tsoran karta rasa husanna, hannu husanna ta miƙa tare da riƙo nata dakyar ta iya buɗe baki tace “Idan kika rasa ni ba akwai Allah ba,’

Wannan maganar tasa jahad bin husanna da kallo bakomai ne ya faɗo mata arai ba face mahaifiyarsu haka kullum ta kece musu aduk lokacin da suke tunanin zasu rasa ta sai tace,

“Idan kuka rasani ba akwai Allah ba, shine gatan kowane bawansa, shi zai tsare ku ya kare mun ku ba wanda ya isa ya taba ku batare da izninsa ba, yana sane daku,

tuna wannan yasa jahad jin komai ya dawo mata sabo fal azuciyarta

Jiki a mace ta kwanta itama  a ƙasan cikin ƙasa a side ɗin husanna ta ɗan ruƙo hannunta a haka suka kwana, ga sauro ga sanyi ga tsoro saboda gidan ba ƙopa,

tun da safe da jahad ta farka cike da tsoran kar ace husanna ta mutu, amma tana buɗe ido taga akasin hakan , samun ta tayi zaune hannunta ɗauke da kofi ta dama furar da tsohuwa ta kawo masu jiya wnda ta yarda a ƙasa, sai sha take yi hankalin ta kwance,

Cike da tsananin farin ciki tace “shashasha ashe kina nan ! I thought u ave already gone, ”

murmushi husanna tasaki tare da cewa “Ba kin ce kar na tafi na barki ba that’s why i stayed alive,’

yar dariya jahad tayi kafin tace”nima yunwa nake ji dan Allah ki rage mun furan wai yaushe ma har ki ka tashi ki ka dama ta? bayan jiya ki ka ce mun mutuwa zaki yi?

“Lokaci na ne baiyi ba in yayi zan tafi,’ husanna ta bata hamsa tana idasa sipping porridge ɗin da takai a bakinta,

dakyar jahad tasamu ta rage mata furar, itama ta sha sai da cikinsu ya ɗanyi nauyi sannan suka tuna basu yi sallar asuba ba, ga tsohuwa har time ɗin she didn’t open the door,

Haka suka tashi su kaje su ka dauro alwala suka tsaya a kofan ɗakin da tsohuwa take suna cewa “dan Allah ki buɗe mana ko sallaya mu ɗauka muyi sallah, kuma tun jiya muke baki haƙuri amma kin ƙi buɗe mana kopan,

Jin shiru bata alamun motsi balle tayi masu magana yasa suka wuce gidan makwabtansu don su gudanar da sallar acen,

haka suka ruƙe hannu cikin na juna suka fice gidansu mamee, bayan sun kammala gudanar da sallarsu, mamansu mamee ta kawo musu kosai da kunu a plate saboda ta lura da yunwa a cikinsu, nan suka samu wuri suka zauna saman ledar ɗakinsu suka hau ci, ita mameen ba bata gidan ta tafi school,

After each 30 mins sai sun leƙa sun ga ko tsohuwa ta buɗe masu ƙofa but still a datse ta ke,

Abun ya wuce na hankali har ƙarfe 2 na rana tayi time ɗin mamee ta dawo daga school nan ta same su jugun, sai da tayi wanka taci abinci sannan ta zauna kusa dasu saman tabarma wadda mamansu ta shimfiɗa musu saboda ciki akwai zafi,

kallonsu tayi tace”meya faru ne ? laifi ku ka mata ko har tayi fushi haka? Jahad ta nuna husanna da hannunta tare da cewa “gata nan ita ce ta jefa mata waya a cikin toilet tun daga lkcn ta shike ɗaki ta datse tun daren jiya zuwa ynx”

murguɗa baki husanna tayi tace”ae ni ma ba laifina bane kyankyaso ne mai fiffike ya hau mun kaina shine na firgita har wayar ta sulale cikin masan,” ta ƙare maganan tana hura hanci,

Jinjina kai mamee tayi kafin tace”gsky bana tunanin cewa tsohuwa zata iya yin wannan fushin saboda ƙaramar waya nokia harta rufe ɗaki tun yesterday night up to now bata buɗe ba, tabbas there’s something behind we’ve to find it but firstly ya kamata mu fara trying na buɗe kopan,

tana cikin wannan bayanin mamansu ta fito daga kitchen tana cewa “nima ina tsammanin hakan, saboda baiwar Allan nan duk yadda zaka 6ata mata rai bata nunawa, maca ce mai haƙuri gsky tsohuwa fa akwai na annabawa sai dai wani abun na daban,’

Jikinsu ne yayi sanyi sosai jin wannan maganar daga bakin mamansu mamee, hankalin jahad ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin sauri ta miƙe tana cewa”dan Allah ku tashi mu je musa ƙarfi mu buɗe kopan, nidai Allah yasa lafiya…’ ta ƙare maganar tana zura silifa ɗin ta a ƙafarta,

Suma suka tashi kowa ya zura takalmansu suka fice mamansu mamee kawai suka bari a gidan tana idasa sanwar rana da ta aza,

Shiga cikin gidan su kayi cikin hanzari, jahad da mamee suka shiga kaiwa kopar bugu da hannunsu da ƙafafunsu, amma gam bata buɗe ba,

ganin zata basu wahala yasa jahad dakatawa ta shiga kitchen ɗinsu ta ɗauko tabarya,

“Matsa mamee kar na buge ki” ta faɗi hakan tana ƙoƙarin kaiwa kofan naushi, cikin sauri mamee taja da baya ta koma gefen husanna ta tsaya,

Da iya ƙarfinta na ƙarshe ta shiga kaiwa kopan bugu da tabaryar nan, amma gam taƙi buɗuwa ko motsi, a wahalarce ta miƙa wa mamee tabarwar “ke ma ki gwada” hannu tasa ta karba ta shiga bugun kopan amma garam taƙi ko motsi,

Sai da husanna ta bari suka sha wahala sun haɗa uban gumi sai nishi suke sannan tace” ku matsa na jaraba nima”

ja da baya su kayi suka bata hanya, baya husanna tayi dama shegen ƙarfi gare ta, da gudun gaske ta tunkari kopan naushi ɗaya tayi mata kofar ta balle gaba ɗaya,

gaba ɗayansu suka sauke ajiyar zuciya suna murmushin jin daɗi sai dai me !?

husanna ce ta fara kutsa kai cikin ɗakin kafin jahad da mamee suka shiga su ma, gabansu ne yayi mugun faɗuwa cikin tsananin firgici jahad ta dafe ƙirji tare da cewa “Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un! Mun shiga uku!!!!

Tana faɗin hakan ta yanke jiki ta faɗi sumammiya, fashewa da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali husanna tayi tana faɗin “shikenan komai yazo ƙarshe” zube wa tayi saman guiwowinta tana kuka cikin ƙunar rai,

Mamee kuwa fita tayi da gudun gaske sai gida ta sanarwa mamansu da abinda ke faruwa, ko hijabi bata tsaya dauka ba, zani ta lullu6a a kanta ta biyo ta suka shigo gidan,

Hankalin ta ya tashi ganin tsohuwa baje a ƙasa bakin ta na fidda ruwan kumfa, tama ji ma da mutuwa bakomai bane yafi tayar ma mamansu mamee da hankali ba face ruwan kumfar dake malale a bakinta wannan alama ce dake nuni da cewa poison ne!!! hakan na nufin cewa bata akai tasha, meke shirin faruwa ne? menene ke faruwa? Meye zai biyo baya !?

Wannan koke koken da suke yi ne yasa sauran makwabta ji, nan fa mutane suka yo buya guda sai cikin gidan, lokaci guda gidan ya cika da mutane kai hada cincirundon samarin unguwar wasu harta saman katangar gidan suna leƙe,

Babban tashin hankalin ma wata mata nan da suke kira da maman baffa tayi tsalle ta dire da cewa “Dama ni banyarda da waɗannan yaran ba! Mayu ne sune suka bata guba taci! dama bamu san asalin su ba haka rana tsaka muka gansu a gidan munafukan Allah asirin ku ya tonu,” wata da ga cikinsu ma ta ƙara da cewa”maganarki gaskiya ce maman baffa yara sai shegen kyau ga rashin son shiga mutane ashe su suka son me suke ƙullawa, dama ance tsintacciyar mage bata mage wlh dole mu ɗaukar mata fansa tunda ku bakusan halacci ba, ta janyo ku inuwa kun kaita rana har kunyi silar mutuwarta,’

Nan fa wuri ya ɗau cece kuce hayani ta cika wurin, mamansu mamee na ƙoƙarin ta kare su amma abun yaci tura,

Ga matasan dake waje jira suke kawai a basu dama su halakar da yaran dama haushinsu suke ji saboda rashin basu haɗin kai, basa kula kowa yau ga dama ta samu,

Hankalin husanna ba ƙaramin tashi yayi ba ita dake zaune ido biyu tana jin abunda mutane ke cewa ita kuwa jahad har yanzu bata farfaɗo daga suman da tayi ba,

Mamee ce ta taimaka ta ɗebo ruwa a cup suka yayyafa mata, da wani irin matsanancin ciwon kai ta tashi idonta sunyi jawur, bala’i biyu ga raɗaɗin da take ji a zuciyarta ga kuma abunda tafarka taji mutane na cewa,

ganin cewa dagaske hukunta yaran zasuyi su kashe su suma, yasa mamee gudu izuwa gidansu cikin hanzari ta laluba school bag ɗinta, wayarta ta ɗauko ta dannawa ƴan sanda kira, taci sa’a an ɗaga nan tayi reporting akan abunda ke faru tare da basu address na anguwar,

Abunda yasa tayi hakan kwara hukuncin da ƴan sanda zasu ɗauka akan wanda ƴan unguwa zasu ɗauka, kisan wulaƙanci zasu yi masu ba bincike,

Lokacin da ta koma gidan dakyar ta samu hanyar shiga mutane sun cunkushe ko’ina,

Ta raza na da ganin wasu matasa guda biyu hannunsu ɗauke da galons na fetur ga ashana a hannunsu kira suke abasu hanya su ƙone mayun, saboda rashin imani matan dake cikin gidan suka shiga basu hanya, haka aka janyo su waje daga cikin ɗakin sai kuka suke yi gwanin bantausayi,

Zazzaga musu fetur ɗin suka soma yi ajikinsu nan take numfashin husanna ya soma hau hawa, jahad kuwa ta ƙanƙameta tarungume ta ajikinta sun rungume juna suna jiran ta Allah ta kasance,

A dai-dai wannan lokacin jiniyar motar ƴan sanda ta karaɗe ko’ina, mota guda suka yo sai a kopan gidan dandazon mutanene da suka gani ne ya tabbatar masu da cewa nan ne address ɗin da yarinyar ta basu,

Tabbas a ranar sunga bakar rana, dakyar ƴan sanda suka kwace su, suka sanya su a bayan kanta suka tafi dasu,

Mamee da mamansu sun sha kuka saboda tausayin ya rayuwar yaran zata kasance ?

Case ya koma hannun police sai yadda hali ya bada, a police station suka kwana ana investigation akan mutuwar tsohuwar, ga baƙar yunwa ga tashin hankali, duk yaran su firgita matuka ga kwanan cell sai uban sauro dake cizonsu,_ 😭•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•

*ABBAN SOJOJI*

_mallakin_

*HAFSAT BATURE*

_wannan ƙirƙirarran labari ne wasu abubuwa ma daga cikinsa ƙirƙirarsu akayi domin ilmantarwa faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa_

_gargaɗi ko da gigin wasa ban yarda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan ba batare da iznina ba, wahala tace ban shiga harkar kowa ba kuma nima bana so a shiga tawa kowa ya tsaya iya matsayinsa_

*page* *43* to *44*

_The Father Of soldiers

Kamar yadda su husanna suka kwana a cell ba bacci itama haka ta kwana ido buɗe, banbancin shine su suna cikin matsanancin hali, ga sauro ga yunwa ga ba wanka komai ya hargitse musu bayin Allah,

Zuciyarta ce ke matsanancin buga mata wanda hakan ya tabbatar mata da cewa, ƴan uwanta na cikin mawuyacin hali, saboda aduk lokacin da wani abu mummuna ya faru dasu sai taji a jikinta,

zuciyarta ce ke matsanancin buga mata, zufa ce ke ta faman sintiri a jikinta, kai kace akwai zafi ne Alhalin yanayin garin sanyi ne,

dukkan ilahirin jikinta sai makekketa yake yi, sam zama saman gadon ya gagare ta, tadawo ƙasa jikinsa ta jingina bayanta, tausayin rayuwarsu ce ta kamasu,

tun suna cikin ciki ƙaddarar su ta soma, sun sha baƙar wahalar rayuwa, ba irin tashin hankalin da basu gani ba, wani lokacin har tambayar kansu suke wai Allah baya sonsu ne? astagfirullah 😥

Amma hakan baisa sehrish tadaina nafilfilin da take yi ba, yau ma rashin tsarkin da bata dashi ne ya hanata yin sallolin, addu’o i kawai take faman maimaitawa duk wacce ta zo mata a bakinta,

Amma fa a daren nan tasha kuka, kamar ba gobe, dole mane sehrish tayi kuka domin kuwa halin rayuwar da suke ciki duk juriyar mutun yaji sai ya matse kwalla,

fargabarta wane hali su husanna ke ciki tana tsoran ta rasa jininta, na biyu wane hali mahaifiyarsu take ciki shin tana raye ko ta mutu? na uku wanda shine take jinsa sosai a ranta wato zuwan SGR, BABBAN YAYA,

tarasa me yasa ya tsaya mata a zuciyarta meyasa take jinsa, meyasa take fargabar ganinsa,

Zuciyarta tana azalzalarta akan son ganinsa, idanunta na kwaɗayin sa shi a idonta, Amma a ƙarshe tayi addu’ar Allah yasa ya zama alkhairi agare ta !!!

sai da asuba bayan ta shiga toilet ta canza pad ɗin cikinta, sanna fa bacci yayi awon gaba da ita,

A can ciki kuwa suna shiryawa zuwan Abban nasu, farin ciki a gun junaid ba’a magana, saboda ya gama tsara shagwa6ar da zaiyi masa in yazo, sannan akwai abunda yake burin ya sanar dashi ,

Har garin Allah ya waye sehrish batasan meke wakana ba, aunty azmi ta shigo ta same ta tana sharar bacci, ganin yadda jikinta ke kerma ya tabbatar mata da cewa sehrish ba lafia ba, har jikinta ta ta6a temperature ɗin jikinta yayi zafi,

Don haka bata attempting tayar da ita ba, kawai sai dai ta gyara mata blanket ɗin jikinta, sannan ta fice,

ganin cewa aiki zai yi mata yawa time zai iya ƙure mata, saboda baƙin da zasu zo yau, da buƙatar su kammala girke girken da zasuyi da wuri,

Kanal yusif ta nema ta sanar dashi halin da ake ciki na rashin lafiyar mai aikinsu tukur, taji daɗi da yasanar da ita cewa, akwai chefs da zasu zo kada ta samu damuwa,

tun 7 suka ƙaraso, kwararru ne a fannin sarrafa abinci kala-kala, su biyu ne, chef ummu da abokiyar aikinta momina, azmi taji daɗin zuwansu, nan fa kowa ya naɗe hannun riga aka soma gudanar da aiki,

Tuni ƙamshi ya soma gauraye ko’ina harta cikin hancina, irin ƙamshin da ke tada mutun daga bacci,

Wurin 9 na safe, jirginsu hajiya azeema yayi landing daga legos, ƙanwar Abbansu ce, hamshakiyar attajirar mai kuɗi ce, tatara har sunyi mata yawa, a tare da ita akwai Captain najeeb da Talal ƙannensu kanal yusif ne da take ruƙo a wurinta, saboda bata ta6a haihuwa ba, lalura ce ta same ta na rashin aihuwa, gashi Allah ya jarabce ta da sonsu kamar hauka,

Hakan yasa Abbansu ya mallaka mata su, a wurinta suka taso har suka girma,

Kanal yusif ne ya ɗauko su daga airport, izuwa gidan murna agunsa har ba’a magana, saboda ganin captain najeeb da Talal, an jima ba’a haɗuba duk da suna ƙoƙarin sada zumunci, aiki ne ya ke hanasu wani time ɗin, saboda aikin soja ba aiki bane na zama wuri ɗaya ba,

Bayansu sai general Ishaq wanda ya kasance shina first born a wurin abbansu wato yayansu gaba ɗaya, wanda ke zaune a kaduna state, tare da matarsa yazo shuwa’arab ce suna kiranta da Aunty Babba, saboda tana auren babban yayansu gaba ɗaya,  sun zo ne tare da Hafsat yarsu ɗaya tilo, wadda take karantar military nurse, ynx haka ta kammala karbar training ɗinta aiki take yi, ta gaji abbanta kenan

daga su kuma sai mai bi ma ishaq wato na biyu a wurin abbansu, Abbas mai riƙe da muƙamin Colonel general, tare da matarsa yazo (AMANI) itama balarabiya ce ƙanwar Aunty babba ce yake aure, kuma dama ita ta haɗasu,

A nan cikin abuja suke da zama su ma, babu ƴa’ƴa a tsakaninsu soyayya suke sha,

daga shi kuma sai na ukunsu matashin saurayi bai ta6a aure ba,

Bakowa bane face brigadier general Abuhaisam, shi kaɗai yazo daga jos sai security ɗinsa,

Waɗannan sune suka samu damar halarta zuwa tarbar abban nasu sauran kuma suna kan hanya,

Ina fata dai kun riƙe sunan kowanne daga cikinsu saboda in labari ya tashi basai munsha Wahala ba, 😒

A babban main palour kowannansu ya hallara, domin dama nan yafi dacewa saboda girmansa da faɗinsa gashi set na royal sofas ɗin dake ciki guda biyu ne a jere,

Hajiya azeema ta hakimce a kujera mai mazaunin mutun biyu, jikinta na sanye da french less haɗaɗɗen gaske ash colour an mata riga bubu dashi, ta kashe ɗaurin ɗankwalin nan irin ture gaka tsiya, amma fa ita ba tsiya bace domin tana da gashi sosai shukune a kanta ta ɗaure da ribbom ya zubo har bayanta, hannayenta na sanye da diamond rings uku uku a kowane fingers na left & right hands ɗinta, price ɗin kowane ring ɗaya yayi 1.5million,

Haka ziririyar chain ɗin dake a wuyanta da earrings ɗinta, sun kai kimanin 200m, agogon diamond ɗin dake hannunta ƙirar graff diamonds ce, farashinta ko ba’a magana, billions ne ke magana  😯

Bata jin wuyar kashe wa kanta kuɗi, kai kace ruwan samansu ake tana kwasa, ko kuma daga saman bishiya take tsinkarsu 😂

takalman ƙafafuwanta kuwa kuɗinsu sun ishi wani talakan jari daga ciki hada ni,

aunty Babba kuwa tana cikin wata jigunanniyar riga haɗaɗiyar gaske,

Ta larabawa mai round neck yellow colour abunka ga fara sai ta fito ɗau kamar hurul aini, kafafunta na sanye da high heels tsadaddun gaske, launin rigarta, tayi rolling mayafi a wuyanta, ya sauka har kafaɗarta, amma hakan bai boye dogon gashinta ba,

tana zaune saman kujera mai mazaunin mutun uku (3 seater) mijinta ishaq shine a gefenta yayi shigarsa cikin manyan kaya namu na hausawa,

Hafsa na a zaune A saman 1 seater, kimono dress ne ajikinta, riga doguwa mara nauyi brown colour, ta ɗaure igiyar rigar a under chest ɗinta, babu head a kanta sai kitson manyan kalaba da akayi mata, ya zubo har gadon bayanta, fuskarta na sanye da light make up, tun da suka shigo kowa na tsoma baki ana fira dashi amma banda ita, cos she’s very arrogant, ji dakai ne da ita, bata da mutunci ko kaɗan guyababbiya ce, fitinanniya, ga rashin kunya kamar 6eran gida,

hannunta na riƙe da waya kirar i phone 13pro, sai faman ƴan danne danne take yi,

 

Amani na zaune tare da mijinta a mazauni ɗaya,

Sai Abuhaisam na zaune jere tare dasu kanal yusif da Captain najeeb a saman 3 seater, sai talal a next chair din dake jikinta su , firar yaushe rabo suke yi, ana ta faman gaishe gaishe gida ya gama katsame wa,

wasu na dannar waya  yayin da wasu ke tsoma baki ana fira dasu,

Su khaleed ne suka fito kowannansu na sanye cikin shiga ta alfarma wankan shadda gezna suka ɗauka launi ɗaya blue sky riga da wando, ba ƙaramin kyau tayi musu ba duba da launin fatarsu chocolate,

Nan fa aka shiga yan rungume rungume kowa cikin fara da nuna farin ciki, kowa ya fito amma banda mutun ɗaya wato junaid gashi kowa ya ƙosa ya ganshi,

Duk magana ɗaya biyu sai an ambaci sunan shi, ina junaid? Wai junaid baya nan ne,

azmi ce ta shigo tare da chef ummu hannunsu ɗauke da abunsha, jere acikin tray a cikin wasu fancy cups,

ɗaya bayan ɗaya suka bisu suna miƙa musu, kowa na ɗauka yana sha,

Hajiya azeema tace “ina fata dai an tanadarmana abunda zamu zubawa cikin mu domin ni ko breakfast ban tsaya ci ba na kamo hanya,’ tayi maganar ne a lokacin da take ɗaukar cup daga saman tray ɗin da azmi ta miƙa mata,

da fara’a a fuska azmi tace “ae mun tanadarmaku abinci kala kala sai wanda kuka za6a,’

general Abbas ya kalli matarsa dake gefensa yace “me na faɗa miki? ai tun a gida nace ni bazanci komai ba, sai na zonan don na kwashi girkin azmi don ban mantawa da wannan farfesun nata mai zautar da mutun,’

dariya sukayi gaba ɗaya musamman azmi da ake yabon girkinta,

Aunty babba tace “ai ko munyi dabara domin ni kaina zumuɗin girkin azmi nake yi kamar kamar me,”

Cikin sanyin murya Amani tace “aunty azmi zanzo ki koyamin pls wannan dambun shinkafar sbd, baby na yana son shi ssae,’

Yadda tayi maganar cikin kwarkwasa ya basu dariya, aunty azeema tace”amma dai Amani ba ta ido, gashi nan kinsa mijin naki jin kunya, gaban ƙannensa kike ce masa baby da girmansa ,’

dukaddar da kai tayi tana murmushi, shima Abbas ɗin  kansa na ƙasa Ya aza idonsa kan screen ɗinwayarsa, su kanal yusif sai murmushi suke yi,

Su azmi da chef ummu sun gama miƙawa koya abunsha don haka suka koma kitchen domin shirya abincin izuwa dining,

_wai dagaske ne su Babban yaya Zasu dawo gobe? Captain najeeb ne yayi tambayar_

_jin an ambaci sunansa yasa hafsat shaƙewa daga Kurbar lemun da take yi, tari ta shiga yi Ba don komai ba sai don jin sunansa domin ta ta6a shan Zazzafan marinsa_😂

Page *45 to 46*

_wlh am so eager so see Babban yaya too😢_

_Subhanah, Walhamdulillah,allahu Akhbar_

“Yeah but we are not sure, ba tabbacin cewa gobe zasu dawo, muna zuba ido dai,’ kanal yusif ne ya bashi amsa,

Jinjina kai captain najeeb yayi tare da cewa “aiko bazan kwana ba, yau zan koma lagos, ba dani ba

dariya su kayi hajiya azeema tace “ashe muna da manyan baƙi, lion da tiger zasu dawo kenan, wannan karan bansan da wata rigima zai zo ba, Allah kaɗai yasan jinin da za’a zubar,’

Hankalisu twins ba ƙaramin tashi yayi ba dama suna zaune matse da juna, sunyi zuru zuru, zuciyoyi na bugawa,

Basu kaɗai ba hada fawan da su jabeer da irfan da sauran atakure suke jin kansu, a wurinsu zuwan Babban yayansu ba alheri bane, bawai don basu son shi ba, sai don tsoran abunda zai faru zuwansa,

“ae na jima ina bama ishaq shawara akan ya tunzura Abba, ya aurar dasu, wlh indai su kaji mace atare dasu zasu samu weakness ajikinsu su daina jin kansu tamkar dodonni,’ sakin baki su kayi jin abunda aunty babba tace,

Azeema tace “da alama bakisan wanene RAFAYET ba, ai rafayet zuciyarsa tamkar dutse take ! ban ta6a ganin mutumin da mace sam bata gabansa ba irinsa, sam bai da shauqi akan mata, ke shi fa hasalima yadda yake kallon jinsin sa namiji haka yake kallon mace,’ 😧

ta ƙarasa maganar tana kurbar lemun hannunta, general ishaq yace “kwara ki faɗa mata da kanki may be she will understand it now, i had been explaining to her about rafayet but taƙi fahimta,’ ya ƙare maganar yana kallonta,

Murmshi azeema tayi tare da gyara zama tace “Anzo inda nafi auki, anzo dai dai wurin ba mai sauka, rafayet da kike gani ba mutun bane ……..

dariya ce ta kubce mata su kansu dariyar suke ba don komai ba sai don maganarta takarshe da tace rafayet ba mutun bane,

dakyar ta saita dariyar ta ci gaba da cewa, ” Ai dashi da mahaifiyarsa halinsu kusan ɗaya ne, kaifi ɗaya ne wasu irin bauɗaɗɗun mutanene, koda yake in mukayi la’akayi da cewa mahaifiyarsa baturiya ce, sannan kuma ba musulma ba, yanayin rayuwarmu da tasu ba ɗaya bace, amma gasky munsha Wahalar fatima fiye da tunanin mai tunani, ta azabtar damu saboda muna kwakwar ƴa’ƴanta, har yau fa ita bata yarda cewa Allah ɗaya bane, taƙi karbar musulunci, kuma bata yarda cewa ƴa’ƴanta sun musulunta ba, in har zasu taka suje wurinta to fa basu ba yin sallah ko karatun qur’ani sai dai in ba dasaninta ba, dakyar fa aka samu rafayet ya musulunta har yakai shekara 20 aduniya ba shi ba musulmi bane,

ta tsagaita da maganar tana sauke ajiyar zuciya, gaba ɗaya sauraronta sukeyi, musamman Aunty babba da Amani su da basu son komai ba game da su rafayrt ba,

Su twins kuwa da fawan jikinsu yayi sanyi domin ana magana ne akan mahaifiyarsu,

Aunty babba tace “nikam inaso nason wacece fatiman nan, ya akai abba ya aure ta ba tare data karbi addinin musulunci ba, Kuma har akayi gangancin barin ya’yanta suyi koyi da addininta ina nufin rafayet da ki kace yakai 20 yrs batare da yakarbi addinin musulunci ba, sannan ina fatiman take a yanzu, don ni ban ta6a ganin ta ba,’

Anzo dai dai wurin, ina fata kowa zai kasa kunnansa ya saurara muda akayi agaban mu, acewar aunty azeema

 

…….  ………….Bismillah……… ………….

Asalin family ɗinmu Hausa fulani ne, mahaifin.mu bahaushe ne haifaffen garin zariya, mahaifiyarmu kuwa bafullata ce yar jihar damaturu, Haɗuwarsu tafarko a barikin sojoji na kaduna state Allah ya haɗa jininsu har takai su gayin aure ❤

Mu uku ne a wurin iyayenmu banban cikinmu Shine hussain wato (Abban sojoji) tagwaye ne su Allah yayiwa hassan ɗin rasuwa tun kafin su mallaki hankalinsu, Akwai tazarar shekaru a tsakanin mu sosai dashi, shi ne nafarko sai kuma ni azeema daga ni kuma sai ƙanin mu gaba ɗaya, wanda shine autanmu mun girme shi sosai, wato ABUSUFYAN wanda ynx yake zaune a Ƙasar turkey,’

tun yana 20years a duniya, wan mahaifiyarmu ya bashi auren ƴarsa maryam, yarinyace mai ilmin addini sosai ga hankali da natsuwa, maca ce mai saukin kai, bata ɗauki duniya da zafi ba,

Itace matarsa ta farko, sun sha sosai kamar laila da majnun, domin mu kanmu shaida ne akan hakan, duk in yana gari tashiga tarairayarsa kenan, idan aka turasa aiki kuwa nesa ba ƙaramain shiga damuwa take yi ba, duk tabi ta susu ce,

Abban mutunne mai son ƴa’ƴa koda yake bashi kaɗai ba, mu dukkan mu haka muke da son ƴa’ƴa zumuncin family ɗinmu yana da ƙarfi sosai, bama wasa da sada zumunci,

Cikin ikon Allah maryam ta samu ciki, kowa ya hau murna musamman ammin mu grandma ɗinmu, dayake maryam mutuniyarta ce tana sonta sosai kasancewarta yar yayanta modibbo,

Haihuwa tafarko maryam ta haifo kyakkyawan ɗanta, santalelen yaro yaci sunansa Ishaq (wato general ishaq) daga shi kuma sai Abbas wanda ynx yake rike da mukamin colonel general, daga Abbas sai brigadier general Abuhaisam gashi nan zaune kuna ganinsa,  daga shi kuma  sai major genaral Osman dukansu tazarar 2 years ne a tsakaninsu su duka, daga shine maryam ta ɗan huta,

Bayan nan ne tafiya ta kama su Abba izuwa ƙasar america, an tura su zuwa halartar wani special training na sojoji da za’a gudanar, da courses na dabarun aiki,

Hankalin maryam ba ƙaramin tashi yayi ba, jin za’a tura mijinta ƙasar turai, tsoranta kada wata tagansa ta liƙe masa Acan, saboda yana da farin jini sosai, 😇

Aiko hakance ta faru domin kuwa da zuwan su Abba u.s wata zankaɗeɗiyar budurwa kyakkyawar gaske ta ƙella ido tagansa taji cewa duk duniya bawan da take so sai shi,

baturiyar ƙasar amurika sunanta Alexandra ita ƴa’ce ga commender in chief na armed forces, 😯

Mace mai tsananin ji da kanta, ita a tsarin rayuwarta, Namiji baya gabanta, idan akayi mata maganar aure sai tace, ita jin kanta take yi tamkar namiji don haka ba abunda zaisa ta yin aure don tafi ƙarfin ta zauna a ƙarƙashin wani, idan akayi mata maganar ɗa kuwa, sai tace ita karenta tony ya ishe ta, wani jibgegen kare ne Wanda ta raine shi tun yana jinjiri har ya fara tsufa,

Abba shine namiji na Farko daya karya wannan kudurin nata, At first sight taji duk duniya ba wanda yai mata sai shi~

Kuma gadan gadan taji tana son aurenshi, Iyayenta sun so su dakatar da ita, amma dayake su in yaro ya wuce 18yrs yana da ƴanci ba wanda ya isa ya takamasa burki, har shari’a zai iya yi da iyayensa insun takura masa,

Hakan yasa suka ƙyale Alexandra ta auri Abba, ba tare da sanin family ɗinsa ba, shi kuma soyayya ta rufe masa ido baya ganin kowa in ba ita ba, dama fa su akwai iya tarairaya ga ɗaukar wanka da jan hankali,

A nan los angels california  suke da zama a katafaren gidanta, nata na kanta dayake itama ta tara kuma ta fito daga babban gida, kuma ita ma soja ce tana riƙe da muƙamin major genaral,

Sunsha soyayya kamar romeo da juliet, acan kuwa 9ja sunyi mamakin jimawar abba, ganin sauran da aka tura Us tare dashi duk sun dawo sai shi kaɗai,

Ga maryam da ƙaramin ciki, kullum cikin zullumi take akan mijin nata,

time ɗin daya shirya dawowa 9ja yasha wahala kafin Alexandra ta amince cewa zata biyo shi na wucen gadi,

Aiko lokacin sun ga tashin hankali, ganin abba ya dawo da mata jinsin turawa, ran mahaifiyarmu baƙaramin 6aci yayi ba, saboda ta tsani jinsin turawa, sbd tasancewa basu da kunya fitsararru ne, an tada tarzoma a lokacin, gaba ɗaya danginmu sukayi masa caaa akan alexandra,

Amma abun mamaki mahaifinmu Salahudeen ya amince masa, kuma ya tsawatar da kowa akanta, ya hana kowa ya sa baki akan alexandra, haka yayan mahaifiyarmu modibbo ya tsawatar mata akan taja bakinta tayi shiru, haka kowa ya zubama sarautar Allah ido 👀

A katafaren gidansa dake abuja suke zaune ya ware mata part ɗinta daban, na maryam ma da ya’yanta daban, kowa baya shiga harkar kowa,

Sam maryam bata kishi da alexandra, tafison su samu zaman lafia a tsakaninsu,amma ita alexandra kishin maryam take ji, bakomai yaja hakan ba face sanin cewa su ba’ayi musu kishiya, basa zama da kishiya,

Cikin rashin sani sai ga ciki a jikin alexandra wanda ya tayar mata da hankali saboda tana shan maganin hana ɗaukar ciki don ita bata buƙatar ƴa’ƴa arayuwarta,

taita faman kiciniyar cire cikin hankalin abba ya tashi, faɗa sosai sukayi a lkcn, yasha wahalarta sbd sai da takai ga har zuƙunna mata yake akan guiwarsa yana roƙonta akan karta cire masa ciki yana so,

dakyar ta amince bisa sharaɗin inta haihu, ba ita zata shayar da yaron ba, kuma ba a nigeria zata haifesa ba, tafi so taje can ƙasarsu saboda tafi yarda da likitocinsu, kada a kashe  ta tsoran mutuwa gare ta, 😂

haka ta maida Abba kamar ɗan aikinta da matsayinsa da komai haka zai zauna, yana mata aiki komai takeso shi zatayi, ita dai maryam bata cewa komai binsu kawai take da ido 👀

Hankalinta kwance saboda haryanzu Abba yana tsananin sonta bai wulaƙanta taba, bai kuma canza mata ba, sa6anin wasu mazan da zaka gani daga inda suka yi sabuwar amarya tofa ita waccen tazama expire product, 😥

wata rana yana zaune ɗakinsa saiga alexandra ta shigo da ƙaton cikinta, hannunta ɗauke da farar takarda da wani rubutu ajiki wanda aka rubuta da harshen spanish, ta miƙa masa takardar da biro tace yasa hannu,

_Gudun rigima yasa bai tambaye ta takardar mecece ba kawai ya raftaka signature ɗinsa, ajiki tare da miƙa mata , tayi murmushi ta kar6a, 😂_*💋ABBAN SOJOJi💋*

_mallakin_

_Hafsat Bature_ *Boss Lady*

_subhanallah_Walhamdulillah_Allahu akhbar_🙏

*page* *47* to *48*

_Dont worry your self guys, sergeon general is on the way soon insha Allah_😘

Ya Allah kaji ƙan waɗanda suka rasu, ka gafarta musu, muma in tamu tazo kasa mu cika da kyau da imani, 😔 Mutuwa ake kamar hauka, yakamata muji tsoran Allah muyiwa kanmu tanadin kyakkyawan ƙarshe tunkan tazo kanmu, mu kasance a cikin shiri domin akowane lokaci mutuwa zata iya zuwa😭 Ya Allah kasa mu cika da kyau da imani, Ya Allah ka haife mana zunubbanmu, Ya Allah ka kare mu daga aikata aikin dana sani😢 mu rage dogon buri a rayuwa, mu rage kwaɗayin abun duniya wanda daɗinsa ƙalilan ne, wannan rayuwar bata da tabbas wlh, amma wasu sun mai da ta wurin zama, suna aikata abunda suka ga dama, zalunci iri iri basa tunanin menene makomarsu 😭 Allah kasa mu dace 🙏 wlh sai mun gyara indai muna so muga dai-dai arayuwarmu 😔

Bismillah

a na nan lokacin haihuwarta yayi, abba dakansa yakai ta Airport kamar yadda yayi mata alƙawari,

kuma ya cika,

Cikin sa’a Alexandra ta haifi santalelan yaronta na farko, wanda ya gigita kowa, kyakkyawan gaske mai matuƙar ɗaukar ido, komai nasa na mahaifiyarsa ne ya ɗauko, hatta launin idonta blue eyes,

Ta jima a us kafin ta zo nigeria, domin ta gwada musu babynta, aikuwa nan fa dangi suka susuce akansa, amma ta hana kowa ya ta6a mata yaronta, iya kallo daga nesa, jinsa take tamkar gold koda yake darajarsa tafi darajar zinari,

Abba yayi mamakin ganinta tana shayar da yaron, bayan ita da kanta tace anemi mai raino don baxata shayar dashi nono ba inyazo duniya, da alama soyayyar yaronce ta kamata,

A lokacin itama maryam ta haifi nata yaron kyakkyawan gaske wanda duk cikin ya’yanta bamai kyansa, farinciki a wurin abba ba’a magana a lokacin yama rasa ina zai tsoma kansa, saboda ƙaunar yaran nasa da aka haifa masa,

Babban tashin hankalin shine, Alexandra ta tada 6alli akan cewa yaronta addininta zai biyo kuma tasanya masa suna Alex, nan fa hankalinmu ya tashi, kowa ya harzuƙa akan lamarin,

Ran abba ya 6aci sosai kamar yayi ihu, a ƙarshe daya takura mata akan cewa shifa yaronsa addininsa zai biyo, sai ta ɗauko masa wannan takardar daya sa hannu ajiki wadda akayi rubutu ajikinta da harshen spanish ta nuna masa,

Cikin rashin sanin ma’anar hakan yace “me wannan ke nufi”?

Dariya tayi masa tare da cewa ” wannan takarda dace, ta yarjejeniya dake nuna cewa ka amince ƴa’ƴana su bi addini na! in har ka matsamin zamu shiga court ne ayi shari’a, kuma kada kayi tunanin zaka iya ɗauke takardarnan domin akwai copy ɗinta awurina ba ɗaya ba, signature ɗinka ne ajiki, 🙆

Hankalin abba fa ya tashi, bai ta6a dana sanin auren Alexandra ba sai alokacin domin takaisa ƙarshe, Ashe wayau tayi masa, tasan hakan zai faru shiyasa tayi rubutun da harshen spanish, shi kuma gudun rigima ya sa bai tambayi menene fassarar abunda aka rubuta ajiki ba kawai yasa hannu, 😥

yaso ya tada 6alli akan koma mai zai faru sai dai ya faru , amma maryam ta dakatar dashi takwantar mashi da hankali ta nuna masa cewa, inya bi komai asannu wata rana ita da kanta zata canza, canjin da har yau muke jira amma Alhamdllh an samu ci gaba,

Bakowa bane wannan yaron  da ake tada jijiyoyin wuya akansa ba face Surgeon general Rafayet wato BABBAN YAYA,

tun yana jariri bai ta6a kuka da hawaye ba, kuma likitoci sun tabbatar da cewa lafiyarsa garas, amma momynsa har ƙasar waje ta fiddasa aka ƙara dubasa aka tabbatar mata da lafiyarsa, sannan ta yarda,

A lokacin da yana yaro yayi tashen ƙiwuya, ya tsani bakar fata indai launin fatarka ba fara bace irinta mahaifiyarsa tofa kun raba jaha,

Duk bala’inka baka ɗaukarsa, hatta mahaifinsa dake mutuwar son shi, bai yarda da shi duk da hasken fatar abban nasa, tsakaninsu sai dai kallo daga nesa , sai kuma in yana bacci uban ya lalla6a yaje ya zuba mishi ido yana kallonsa,

Shi kuma yaron da maryam ta haifa, ba kowa bane fa ce Marshal omer tazarar satittika ne a tsakaninsa da Rafayet,

Tun suna yara omar ke son wasa da rafayet, amma bai yarda dashi ba duk da kasancewar omar fari ne sosai  kamar balarabe, yabiyo mahaifiyarsa Maryam bafullatana,

Gashi shima rafayet ɗin yana son Omar amma tsakaninsu sai dai daga nesa a rinka jefawa juna murmushi 😊

daya ƙara wayau hankali ya fara shigarsa, wata irin shaquwa ce ta shiga tsakaninsa da omar, duk da momyn shi bataso yana hulɗa dasu,

kai har takaiga idan dare yayi sai ya saci hanya daga bedroom ɗinsa izuwa nasu, ya haye saman gadonsu wurin omar ya kwanta kusa da shi,

Shima omar ɗin harya gane idan dare yayi, yazauna yaƙi bacci yayi ta zaman jiran rafayet, har sai yazo sannan su kwanta tare suyi bacci,

Maryam kaɗai ce ta lura da hakan, ita dai ba ruwanta, tana son rafayet tanajinsa kamar ɗan cikinta, haka zata je tayi musu addu’a tashafa musu kawunansu,

Ranar da alexandra ta gane hakan akan idonta, taga rafayet ya shiga ɗakinsu omar tsakar dare , aiko washe garin ranar tarinƙa zabga masifa har sai da kowa ya gaji,

Bayan wannan lokacin maryam taci gaba da haihuwa a inda ta sake haihuwar namiji again wanda yaci sunan shi najeeb, gaya nan kuna kallonsa, wato captain najeeb,

daga shi kuma sai Kanal yusif shima gashi nan zaune, daga yusif kuwa sai commender haroon, daga haroon sai Captain adams,

daga adams sai khaleed daga shi kuma sai jabeer da irfan, haka ta haifesu, daga nan ne ta dakata,

A bangaren Alexandra kuwa shiru sbd tace ta kammala nata, abba najin baƙin cikin musamman inyaga Ya’yansa zasu masallaci sun haɗu su duka amma babu rafayet acikinsu,

Ya so ya sake tada 6alli akan yaron, saboda yana da hanyar da zai kwaci kayansa daga faɗawa daga halaka, amma mahaifiyarsa tayi masa tatass akan cewa lokacin da ya aurota dawa yayi shawara, taja masa kunne akan cewa kada ya kuskura ya ƙara tankawa akan alexandra,

A dolensa yaja bakinsa yayi shiru bisa umarnin mahaifiyarsa,

A karshe ya koma yana nuna mata soyayya don yaja hankalinta, y rinƙa binta sau da ƙafa,

dalilin komawar Rafayet us da zama ba kowa bane face wan mahaifiyarsa mr donald, mugun son rafayet yake kamar hauka, duk weekends sai yazo nigeria don kawai ya gansa, kai daga baya ma sai ya kai sau 3 yake zuwa a week sam baya gajiya da zarya daga us zuwa 9ja, ran abba yayi matuƙar 6aci, har dai wata rana ya tambayi donald yace masa wai shi bai da ƴa’ƴa ne? da buɗen bakinsa sai cewa yayi, shiya riga da yayi plan ƴa’ƴa biyu yake so arayuwarsa, yanzu ya samu ya’yan kuma dukkansu mata ne, guda biyun ,

abba tamkar ya shaƙe shi haka yaji, wato tunda yasamu biyun duk mata, shiyasa ya dakata  bayan yasan cewa yana son ɗa namiji,

Ba yadda abba ya iya haka ya zuba ma sarautar Allah ido 👀 haka donald zaizo yaita kashe ma rafayet kuɗi shida omar, kamar hauka bai gajiya,

bayan wannan kuma abba yaji yana son ya sake samun ƙaruwa da Alexadra, yaje cikin lalama yayi mata magana, sai yaga tana dariya abun ya ɗaure masa kai ,

gyara murya tayi tare da cewa ” na amince zan sake haifa maka ƴa’ƴa har 3 amma bisa sharaɗin cewa zaka amince Alex ya koma wurin ɗan uwana Donald da zama gaba ɗaya, don na fi yarda da ya zauna can sbd zai fi samun tarbiya, zai wataya ya samu rayuwar ƴanci,

.(wai tarbiya a us 😂)

Kai tsaye Abba yace ya amince dalili kuwa shine ya gaji daganin rafayet ba sallah ba salati ba karatun ƙur’ani, kwara ma yayi nesa dashi zaifi samun salama,

Amma shima yace yana da sharaɗi guda ɗaya, tace tana sauraronshi,

Abba yace “yaran da zata haifa mashi dole su bi addininsa wannan karan,’

Batayi masa gardama ba tace ta amince, a wannan lkcn ALexandra ta ajiye aikinta gaba ɗaya, sbd ta mallaki komai takeso a ynx, tayi mai isarta ynx lokacin hutun rayuwarta ne acewarta,

A nan ne kuma cikin ikon Allah ta samu ciki, a inda ta haifi twins tagwaye wato Ayaan da jahan, kyawawan gaske Allah ya zuba musu kyau, abba yayi farin ciki sosai, da aka tashi sa masu suna akexandra tace Za6i na wurinta, sbd a yarjejeniyarsu bai ce zaisa ma yara suna ba, don haka tasanwa Ayaan (John) Jahan kuma (James) kowa ya zuba mata ido 👀

daga su kuma ta ƙara samun ciki inda ta haifi fawan shima tamkar sauran wurin kyau, kyakkyawan gaske Fari sol, a inda tasanya mishi suna (Michael) nan Ma kowa ya zuba mata ido 👀

Bayan shine ta dakata da haihuwar gaba ɗaya, nan fa abba yasa rigimar cewa haihuwa uku tace zata yi masa, ita kuma tace ae inya lissafa da twins da fawan ƴa’ƴa uku kenan, ba dole sai ta yi ciki uku ba, Allah ya kawo mata cikin sauƙi,

Rigima ta 6alle a tsakaninsu daga ƙarshe da Abba yaga ba riba sai ya koma yana lallashinta akan ta taimaka masa ta haifa masa last born, uhmmmmm

A lokacin maryam tana ɗauke da cikin autanta na ƙarshe wanda a wurin haihuwarsa ne ta rasa rayuwarta, bakowa bane fa ce Talal,

Aunty azeema ta faɗi tana nuna sa, jikinsa yayi mugun sanyi, tuni hawaye sun zubo masa, haka sauran ma duk jikinsu ya mutu,

Ita kuwa alexandra dakyar abba ya samu ta haifa masa last born ɗinsa,

Wanda ya tafi da zuciyar kowa, da irin kyawunsa, shi na musamman ne, kowa rububinsa yake tun yana yaro yake fama da athma, ko ban faɗa ba kunsan ko wanene, mahaifiyarsa tasa mashi suna ROMEO, a inda mukuma muke kiransa Junaid,

Ansha wahala sosai kafin alexandra ta kar6i musulunci, a inda sunanta ya canza daga Alexandra zuwa FATIMA, kowa yayi tunanin cewa tayi imani da Allah ne, ashe ita bada son rantaba takar6i addinin,

Takurawar abbace,

dalilin barin alexandra nigeria tsakaninta da mahaifiyarmu ne basu shiri, hajiyarmu ta tsane ta ba don komai ba sai don yadda take wahalar mata da ɗanta,

Duk in tazo abuja gidan abba sai sunyi cece ku ce, tun daga ranar da hajiyarmu ta buɗe baki tace ma Alexandra musuluncin ta ba kar6a66e bane, ta musulunta a banza domin kota mutu wuta zata shiga,

Ran Fatima ya 6aci sosai jin wannan maganar hakan yasa, ta koma addininta kai tsaye,

shiyasa ba a so in mutun ya shiryu arinƙa ƙyamatarsa ko kuma ana goranta masa, sbd gudun irin hakan ynx gashi ta koma yar gidan jiya, a ƙarshe da hajiyarmu ta Tsananta mata da baƙaƙen maganganu, ranta ya 6aci sosai

Wannan shine silar da fatima ta koma ƙasar Australlia  da zama wurin danganin mahaifiyarta can sydney, babban tashin hankalin ma tabar masa jinjirin yaro batare da idasa shayar dashi ba,

Junaid yaga rayuwa, naso na ɗauke shi,amma azmee ta nuna cewa tana so ta shayar dashi, shiyasa nabarmata sbd nima ina shayar da talal da mahaifiyarsa ta bari,

Rafayet ya musulunta ne a sanadin omar, saboda duk ƙarshen wata donald yana kawosa su gaisa da mahaifinsa, a haka ahaka har suka ja ra’ayinsa duk da ansha wuya kafin asamu ya kar6a, abba yaji daɗi sosai a lokacin, shima kuma donald yayiwa abba alƙawarin cewa bazai ta6a takurawa rafayet akan addininsa ba, zai bashi ƙwarin guiwa duk da kasancewar shi mabiyin addinin catholic,

A lokacin abba ya haɗa rafayet da omar tare ya damƙawa donald ba don komai ba, sai don kukan da yake yi mashi akan yana son ya zauna kusa da ɗan uwansa, sun shaƙu sosai, duk in zasu rabu sai sunyi zazza6in rashin junansu,

Sannan kuma haɗa omar da rafayet ba ƙaramin ci gaba muka gani ba , domin shike juya rafayet, ya ja ra’ayinsa sosai akan musulunci yana ƙara nutsar dashi, yana tunasar dashi akan ibadarsa da kuma addininsa, da haka aka samu rafayet har ya sauke al’qur’ani mai girma, A shekarar daya musulunta kowa yayi mamakin hakan, duk da munsan  cewa shi na musamman ne lu’u lu’u  ne , mr donald yayi bajinta domin har yau muna ƙara jinjina masa kuma muna yi masa addu’ar Allah yasa ya musulunta dashi da yar uwarsa fatima,

Domin shi yayi ɗawainiyar su rafayet da marshal omar har suka kai wannan matsayin da suke a yanzu wanda duniya tasan dasu ,

Kuma shi da kansa yasama musu malamin addini wanda ke koyar dasu littattafan addini tun suna yaransu,

Tun wannan lokacin fatima bata ƙara taka nigeria ba, sai dai duk mai son ganinta yaje inda take,

Wannan shine takaitaccen labarin gidan Abban sojoji, Allah yasa an fahimta,

Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa “Allah ya jiƙan surukata, ya haskaka ƙabarinta,yasa Aljanna ce makomarta, da dukkan waɗanda su ka rasu Allah ya gafarta musu, Alfarmar annabi muhammad (SAW) ❤

gaba ɗayansu suka amsa da amin ,sannan ta ƙara da cewa “sannan muna yi ma fatima addu’ar Allah ya shirye ta, yasa ta gane gaskiya ɗaya ce, ya bata ikon musulunta, da ita da ɗan uwa Donald,’

Jikinsu twins da fawan yayi mugun sanyi, ta shi su kayi cikin wani irin yana yi zasu shige ciki…………………😔*💋ABBAN SOJOJI💋*

_mallakin_  *HAFSAT BATURE*💓

*BossLady*🫶

_Subhanallah_ _Walhamdulillah_ _Allahu akhbar_ ☝️

*page* *49* to *50* 🤗

_💋Extraordinary Love💋_

general ishaq yace “kai ina zuwa? Maza ku dawo ku zauna, ku ka yana magani ne? ynx tsakanin ku da mahaifiyarku addu’ace kawai, that’s the only solution, in Allah yasa fatima zata musulunta ae ba wanda ya isa ya hana hakan,’

Cikin shesshekar kuka fawan yace”idan ta mutu fa ba tare da ta karbi addinin musulunci ba, azabar Allah zata tabbata akanta ne, kuma wuta zata shiga, aduk lokacin dana tuna wannan ina jin ƙunci araina…’

Ayaan ma yace “abba bai kyauta mana ba, kullum cikin zullumin makomar mahaifiyarmu muke,’

Jahan yace “kuma bata son mu, ta kama hanya tayi tafiyarta, ko waiwayan mu bata yi, ita wata irin uwace? cikin rashin tausayi ta tafi ta6ar ƙaninmu shi da bai mallaki hankalinsa ba, da tun farko Abba ya za6a mana uwa tagari munyi rayuwarmu cikin salama, da ynx labarin ba haka zai kasance ba,

“Kada na sake jin wani daga cikinku yayi magana, ku koma ku zauna, koba komai ae kuna da mu, wani irin gatane bamu nuna muku ba, mu fa jini ɗaya ne, babu wani banbanci a tsakanin mu ! ku kun kasance jinin dake yawo ajikinmu, kasancewarku farar fata ba hakan yana nufin kun fita daban acikin mu ba, kuma don mahaifiyarku ta tafi ta barku ba hakan yana nufin kun rasa wani sashe na jin daɗin rayuwarku ba,

Da ran mu da lafiyarmu bazamu ta6a bari hawayen ɗaya daga cikin ku ya zuba ba, Allah ya riga ya haɗa kuma ba wanda ya isa ya raba, nasan cewa abunda Ammy take yi muku bakwa jin daɗinsa, shine abunda yasa ku ke jin kan ku daban, to inaso kusancewa zumunci a tsakaninmu yanzu ya SOMA,

Wannan maganar ta yayansu Ishaq yasa su jin wani sanyi a ransu, har suka samu ƙwarin guiwar koma wa suka samu wuri suka zauna,

Suna cikin wannan zaman motoci suka soma antayowa cikin gidan da gudun gaske da wata irin jiniya, wannan alamu ne dake nuna cewa Salahuddeen hussein ya dawo wato chief of army staffs,

Farin ciki a wurinsu ba’a magana, Abbansu jigon rayuwarsu, backbone ɗinsu ya dawo cikin ƙoshin lafia,

Lokaci guda hayaniya ta kacame agidan manyan mutanen da suka zo tar6arsa ba adadi, sai faman marhaban lale ake yi, gidan ya cika fam da manyan mutane ko’ina ya ɗauka, su azmee da chef ummu da momina sai faman kai komo suke wurin rarraba musu abunsha,

Abban nasu ba ƙaramin daɗi yaji ba lokacin da yaga warriors soldiers ɗinsa cikin ƙoshin lafiya, murna a gunsa ba’a magana, sai dai har yanzu baiga Sanyin idaniyarsa ba, gashi ya matsu daya gansa, duk da ɗumbin mutanen dake kansa hakan bai hanasa ambaton sunan JUNAID ba, ❤

dakyar fa mutune suka lafa har abban yasamu damar shiga haɗaɗɗen bedroom ɗinsa, wanka ya shiga bayan ya fito ya kimtsa cikin jallabiya fara, kallon kansa yayi a cikin dressing mirror murmushi ya sakarwa kansa tare da cewa “ABBAN SOJOJI” a fili ya yi maganar,

Abba mutunne mai matuƙar daraja da cikar kamala, mutunne da kowa yake kwaɗayin haɗa iri dashi ba don komai ba sai don sanin kyawawan ɗabi’unsu, mutun ne dayasan darajar ɗan adam, yana da sauƙin kai sosai, hakan yasa naƙasa dashi ke prouding dashi a matsayinsu na shugabansu ❤

Mutunne mai matukar tausayi, hannunsa a buɗe suke indai wurin taimako ne baya gajiya, irin waɗanɗan mutanen na musamman ne su, domin suna da kishin ƙasarsu, shiyasa suke sadaukarwa kansu ga ƙasarsu, kowa zaiyi burin ya mallaki uba irinsa 💕

Kwanciya yayi a saman katafaren king size bed ɗinsa, domin ya samu relief kafin ya wartsake ya gana da ƴa’ƴansa,

A can ciki kuwa kowa ya hallara a saman dining table domin gudanar da ɗa’amin, su azmee sun kammala jera komai, saving ɗinsu kawai suke kowa na faɗin abunda yake son ci, su kuma suna zuba masa,:

Cikin natsuwa kowa ke zubawa cikinsa, suna cikin cin abincin aunty azeema tace “wai ina baby junaid nifa na ƙosa na gansa, i really missed him so much,’ ta idasa maganar tana tura dambun naman da ta dumbuzo a hannunta, sam bata wasa da abinci,

Fawan yace “hmmm indai junaid ne ynx zaku gansa, yunwa ta koro sa, nasan yana cen rungume da pillow kamar jinjiri yana sharar bacci,’

gyaran murya Abbas yayi “idan ana cin abinci ba’a magana,’ ya faɗi cikin zolaya,

Amani tace “amma agida fa muna yi,” dariya su kayi gaba ɗayansu jin abunda tace,

….,……….SEHRISH…………………….

A 6angaren sehrish kuwa, baiwar Allah jiki fa yayi rau, ido a kumbure ta farka daga bacci, duk ta tsorata da mafarkin da tayi akansu Husanna, tayi wani mummunan mafarki akansu, cikin mawuyacin hali, jikinta ya gama mutuwa, hawaye ne kawai ke rolling down on her cheeks, tana jin zuciyarta babu dɗi, tana kewar siblings ɗin nata, tana jin cewa bata kyauta ba, da tayi nesa da su amma ya zata yi? the hard way is the only way 👌

Cikin sauri ta shiga toilet, wanka tayi sannan ta fito, jikinta na ta faman rawa, kayan nan da tafara zuwa aiki dasu gidan at her first day, su ta ɗauko, wato burgujejan wandon nan Falazu,

Wanda ƙafar mutun 5 sai ta shiga ciki ba tare da ya matse su ba, pink colour sai riga ta maza launin ruwan madara (milk) mai ma6allai dayawa ajikinsu da aljihuna, ta gyara gashin bakinta ya zauna raɗau, sannan ta nannaɗe sumar kanta kamar yadda ta saba,

ta aza hukar nan, yar tashi da kwakwa sannan ta aza kuma mayafinta launin wandon daga saman hular ta naɗe shi,

sai da tatabbatar da komai ya zauna raɗau,

Sannan ta fito gabanta na faɗuwa saboda taji alamun bakin nan fa sun iso, suna cikin gidan batasan ya zasu kalleta ba, ko’ina na jikint rawa yake yi saboda zazza6in da take ji,

tun daga inda take ta hango su a zungureran table din, binsu da kallo tayi, musamman aunty babba da Amani da tagansu ƴan larabawa, ga kuma su ishaq da abbas da abuhaisam da sauran duk batasan su ba, amma kamanninsu ya tabbatar mata da cewa yayyansu Kanal yusif ne,

“To fa wanene wannan kuma, baƙon saurayi ku ka yi ne:? .

Sai da sehrish ta firgita jin maganar aunty azeema, lokaci guda kowa ya ɗago yana kallonta 👀

Cikin sauri azmi dake tsaye akansu suna saving ɗinsu dasu chef ummu tace “he’s our new house boy, tukur yana taimaka mun wurin aiki sosai,”

Jinjina kai azeema tayi tare da cewa “that’s gud”

ƙarasawa azmi tayi ta ruƙo hannun sehrish tare da janta izuwa kitchen suka tsaya, sannan ta kalle ta tace “meke damunki ƙanwata na shiga na Same ki jikinki zafi baki lafia ne,”

Hawaye ne suka soma zubo ma Sehrish cikin nuna tsananin damuwa tace “aunty azmi dan Allah ki taimake ni, ke kaɗai ce zaki iya taimako na a halin yanzu, ina cikin tashin hankali…’

“tell me whats happening wit u? Azmi ta tambaya,

“Aunty azmee ina ji araina cewa ƴan uwana suna cikin mawuyacin hali, inaso naje nagansu, dan Allah ki taimakamin naje katsina na duba su koda kwana ɗayane ina tsoran na rasa su bani da kowa sai su….. …..’

kuka ne yaci ƙarfinta ta gaza ƙarasa maganar, azmi ta janyota jikinta tare da hugginta ɗinta tightly a jikinta tace….

“I feel your pain sehrish,ina mai takaicin sanar dake cewa bazai yiyu ba hakan!

ɗagowa sehrish tayi daga jikinta tana kallonta ido jawur, cikin muryar kuka tace “meyasa aunty azmi”?

“Banso na sanar dake ba amma ynx dole ne kiji, sehrish kuɗin da na baki na aikin ƴan uwanki, bana salary ɗinki bane kawai, hada kuɗaɗen dana jima ina tarawa domin na yi amfani dasu, na haɗa miki duka sbd na tausayawa halin da ki ke ciki sosai, salary ɗinki bazasu isa ba dole saina cika miki, a yanzu haka da nake miki magana nikaina banda kosisi domin duka na tattara miki su….”

Shiru ta ɗanyi tana wani tunani idonta akan sehrish, ita kuwa jikinta yayi sanyi ba don komai ba sai don jin cewa Azmee hada kuɗinta ta haɗa mata don ta biya kuɗin aikinsu husna, sai taji ta ƙara ƙaunar azmi sosai, tana da matuƙar tausayi, ga kyan hali

“ki daina kuka sehrish, duk kan tsanani yana tare da sauƙi, ki daina sa damuwa aranki, insha Allah ba abunda zai sami ƴan uwanki, Allah yana tare dasu, maganar zuwanki wurinsu zanyi ƙoƙari akan hakan amma ba yanzu ba,’

cike da rashin kuzari sehrish tace “shikenan aunty azmee, nagode sosai bansan da wasu irin kalmomi zan gode miki ba, narasa mahaifiyata amma gashi Allah ya bani ke alokacin da nake cike da jimamin rashin wani nawa akusa dani mai sharemun hawaye na,

Murmushi azmee tayi kafin tace “samu wuri kizauna, me kike so na kawo miki ki ci? tun da safe baki ci komai ba,’ tayi mgnr cikin nuna damuwarta,

“Aunty azmee i cant eat anything now, zuciya ta tashi take yi bani da kwanciyar hankali,’

dafa shoulder ɗinta tayi tace “Calm down your mind reeshi na, just ave a seat, bari na haɗa miki abu mai daɗi mana ki ci, zaki ji daɗi,’

Ajiyar zuciya sehrish ta saki, wuri ta samu a saman dinner table ɗin dake a kitchen ɗin ta zauna, tana jiran azmi,

a tray ta shirya mata abun tattaunawa, ta ƙaraso da murmushi ta ajiye mata tana faɗin”Ina mai tabbatar maki cewa indai ki kasa wannan Cheese burger ɗin abakin ki sai kin manta da duk wata damuwa da ki ke ciki, musamman in ki ka haɗa da  Cornflakes ɗin Zan haɗa miki ynx da madara haɗi na musamman ,’

Wani irin sanyi ne ya ratsa reeshi haƙi ka azmi ta musamman ce acikin na musamman, cikin sanyi murya ta furta “thank u aunty azmee kina ji dani sosai, only God can rewards you,’

“Don’t worry your self reeshi i just wanna see you always in happy mood, bana so naganki cikin yanayi na damuwa,’ ta faɗi hakan a yayin da take ƙoƙarin juyawa,

Murmushi sehrish tayi ta zuba wa tray ɗin ido, Cheese burger ce aciki tare da hot dog ga sandwhich, lumshe idanunta tayi aranta tana tunanin me ƴan uwanta suka ci su 😥

ruwa azmi ta ɗebo a Dispenser mai zafi cikin tea cup, ta haɗa wa sehrish cornflakes yaji madara da sugar, tasan cewa sehrish akwai son zaƙi shiyasa ta zuƙa mata shi,

Ƙaraso wa tayi ta jiye mata shi a gefen tray ɗin, sannan tace “ko kina buƙatar wani abu ne?akwai sauran abubuwa da muka haɗa masu daɗin gaske,

yar dariya sehrish tayi ganin yadda azmi ke treating ɗinta sai kace ƴar masu gida,

“oh dariya na baki?dama dariyarki nakeson gani kuma gashi naki har dimple ɗin nan naki ya lotsa,’

azmi tayi maganar tana kallonta, cikin jin daɗi sehrish tace “daga ynx zan rinƙa yin dariya aunty azmee tunda kina so insha Allah,’

hannu azmee tasa tare da jan kumatunta tace “yawwa haka nake so my daughter, bari na shiga ciki, keep enjoying ur meal banda loma,’ .

ta faɗi hakan cikin zolaya kafin ta fice daga kitchen ɗin,

tana fita sehrish ta fashe da wani irin matsanancin kuka ba don komai ba sai don, tunawa da ƴan uwanta, kuka take bil haƙƙi da gaske hawaye na sintiri a face ɗinta, Allah sarki baiwar Allah, aduk lokacin da taga abu mai daɗi agabanta zata ci sai ta tuna da ƴan uwanta, wane hali suke ciki? shin sun samu abunda zasu ci kuwa, in ta tuna hakan sai taji ɗaci aranta, maganar oummansu ta tuna a inda take cewa

_sehrish ke ce mai wayau acikin ku, dan Allah duk runtsi duk wuya kada ku rabu ko bayan raina, ku haɗa kanku ina son ku sosai ƴa’ƴana rabin raina_ 😭

Hafsat Bature

*page 51 to 52*

Abban Sojoji

*💋romantic love story btwn Sehrish & Surgeon General Rafayet💋*

_Heart touching story abt a Triplet_😢

mamaki ya ke ganin taƙi ɗauke eyes ɗinta akansa, kuma bata da niyar daina kallonsa, hannunta har rawa yake yi wurin ajiye spoon ɗin da ta ɗauko,

Lumshe idanunsa yayi a hankali yana ƙare mata kallo acikin zuciyarsa yana cewa “Ya Allah ka mallakamin wannan baiwar ta ka,’

A yayin da sehrish ke cewa”

_tsarki ya tabbata ga ubangijin daya halicci wannan kyakkyawar surar Junaid duniya ne_💋

_shigowar azmee ne ya dawo dasu daga wannan tunanin na ƙurawa juna ido kowa ya waske_

cikin fara’a azmee tace” junaid me ka ke bukata ne na kawo maka? naga baka ci komai ba,

A cikin zuciyarsa yace”kallon ta danake koshi nake Aunty azmee”

A fili kuma yace” nima cornflakes ɗin zan sha, a haɗo mun da fresh fruits’

“Junaid ba ka son cin abinci ko? Kafi son ƴan lashe lashe kamar Tukur”?

Wani irin murmushi ya saki jin abunda azmee tace har time ɗin idonsa nakan sehrish wadda ta mayar da idonta kan cheese burger ɗin dake gabanta so take ta ɗauka taci amma zuwan junaid yasa duk ta dabarbarce sai ƴan kame-kame take

“Aunty azmee ae we are the same ni da shi,’

Azmee tace “gsky saina haɗa maka da farfesu mai zafi zaka ji daɗinsa,’

Junaid yace “its ok am waiting,

zuciyarta sai faman ɗar ɗar take yi mata, kamar mara gsky koda yake ba gaskiyar ae,

Shi kam ya zuba mata ido yana kallonta, yarinyar ta kwanta masa a heart ɗinsa, just he is affected 💘

Azmee ce ta ƙaraso hannunta ɗauke da plate wanda ta zuba masa farfesun ganda aciki, ajiye wa tayi a gabansa, sannan ta koma ta Kawo masa fresh fruits ɗin daya bukata acikin wani haɗaɗɗen round tray,

sannan ta koma ta kammala haɗa masa corn flakes ta kawo masa,

A hankali ya furta “shukran aunty azmee’

azmee ta juya ta fice tana ɗan murmushi bata ta6a sanin cewa junaid Romeo bane na gaske sai da ya gane cewa reeshi maca ce ba namiji ba, ❣️

Ƙamshin farfesun gaban junaid ne ke ta faman kai mata hari, ɗagowa tayi tana satar kallonsa,

A hankali yake sa hannu yana ɗaukar gandar ta dahu tayi tubus taji kayan haɗi na kamshi, irin wadda daga kasa a baki zata dagargaje😋

A hankali yake turawa abakinsa yana tauna, ganin bai kara ɗagowa ba yasa tayi saurin wawurar burger ɗin tana turawa a baki,

Muryarsa ce ta katse ta “Ki ci a hankali,” ya furta yana ɗan smiling ashe ya ɗago bata sani ba

kaɗan ta gutsara ta maida ta ta ajiye, hot dog ɗin ta dauka tana ci,

a yayin da shi kuma ya ɗauki spoon yana shan cornflakes ɗin da azmee ta kawo masa,

Wani tunani ne ya faɗo masa aransa a lokacin da yake kallon sehrish wadda take ta faman ƴan kame kame,

Bin ta da kallo yayi aransa yace ” Wani abu na ban mamaki nikam, ko ya aikai take matse boobs ɗinta, suyi flat tamkar babu, dama Allah yasa su 6ace muga yarda zata yi……..

Shi kansa baisan dariya ta kubuce masa ba, har ya fetsar da cornflakes ɗin dake bakinsa, zuba mishi ido sehrish tayi gaban ta na faɗuwa tsoranta kada ace wani abu junaid ya ganu wanda zaisa ya gane cewa ita maca ce,😳

Sai faman tiƙar dariya ya ke yi ba kakkautawa, sam ya gaza stopping kansa,

Tamkar tv haka ta ƙura wa junaid ido yana dariya, fararen hakoransa jere rass take kallo ga ƴar wushiryarsa siriri ya,

ganin ya kasa controlling kansa ya sa ya miƙe ya kama hanyar fita yana ci gaba da dariyar,

Abun ya bata mamaki, ganin ya tashi yana ta dariya gashi baici abun kirki ba, anya junaid yana da lafia kuwa? Ko dai yana da psycriatric disorder ne?

daga bisa ni ta ta6e bakinta alamar i dont care taci gaba da shan abunta,

Bedroom ɗin abbansu ya wuce directly, a hankali ya tura kopan ya shiga, samun shi yayi a tsakiyar gadon ya baje abunsa, ya warware,

Murmushi ya saki ganin abban nasa, har cikin ransa yaji daɗi ganinsa ya dawo cikin ƙoshin lafia,…

“Lallai abba abu yayi kyau, shine an dawo ko a neme ni, aiko yanzu baccin nan naka zai ƙare,’

Ja da baya yayi sannan ya watsa a guje ya faɗa saman gadon sai ajikin abban nasu a firgice cikin magagin bacci abban ya rinƙa faɗin “a miko bindiga 6aro ya shigo ‘

fashe wa da dariya junaid ya yi, yana kallon abban nasu wanda idonsa ke a rufe yana ta faman sambatu,’

tabbas yaji nauyin mutun akansa, amma sam ya gaza buɗe eyes ɗinsa sbd a gajiye ya ke,

Cikin rashin imani junaid yasa hannunsa yana gwale masa idanu, sunyi ɗan ja, biji-biji yake ganin junaid sai faman zabga murmushi yake,

Cikin nishaɗi ya ce “Abba its me your heart beat, i came here to disturb u,  🤣

a hankali abban ya idasa buɗe idanunsa, a firgice ya yunkura ya janye junaid gefe ɗaya, ba ƙaramin tsorata yayi ba, saboda idonsa wani farin aljani nuna masa sai da ga baya gane cewa she junaid ne,

“Yanzu ka kyauta ? dama ina ji an hau saman jikina nasan cewa kaine, duk duniya babu maiyi mun haja sai kai,’

“Cikin shagwa6a junaid yace “ka dawo baka neme ni ba abba,’ ya ƙare maganar yana zumbura masa baki,

yatsina fuska abban yayi yana kallonsa aransa yana cewa ” ynx fa sai yace zaiyi mun kuka shi ala dole gabu auta, bari na jaraba shi nagani ya canza ko hanyarzu yana nan yadda na barsa,

ɗaure fuska yayi tare da nuna ma junaid hanyar fit yace “kai tashi ka fice mun bana son takura jarababbe,’

cikin yanayin mamaki junaid ya ce” abba Ni kake ce ma jarababbe? Kadawo baka neme ni ba kuma shine kake korata ?

Abba yace “ka ga tashi ga fice mun tunkan nawaje suji mu,’ ya faɗi yana kara tamke fuska,

.ganin cewa dagske abban nasu yake yasa ahi tashi jiki a sanyaye ya sauka daga saman bed ɗin ya isa bakin kopa, bai bude kofan ba tsayawa yayi yana jiran abban ya bashi hakuri,

ɗan juyawa  yayi da kansa ya saci kallin abban nasu wanda ke zaune tsakiyar gadon, haɗa ido sukayi lokaci guda 👀

narai narai da ido junaid yayi alamar zai yi kuka, shi kam Abban abun ɗaure masa kai ya ke yi, har wani sa in tunani ya ke anya Junaid namiji ne ba mace ba? Ace har yau mutun jin kansa ya ke kamar jinjiri, ko don ba nonon fatima yasha ba ? Don tabbas yasan cewa da ace fatima ta shayar dashi da guyababbe zai zama ba susu ba, amma duk da hakan ƙara son yaron nasa ya ke fiye da sauran, zuba mishi ido ya ci gaba da yi,

Junaid dake tsaye yana sum6ura baki, biji biji ya soma gani a idanunsa, lokaci guda ya soma sakin tari, hannu yasa tare da dafe saitin zuciyarsa, yana ambaton kalmatussha hada,

Hankalin abban nasu a tashe a wani irin firgice, shi kansa baisan lkcn da ya wuntsilo daga saman gadon ba, sai wurin junaid wanda kafin isowar abban nasu ya zube ƙasa 😨

Cikin wani irin tashin hankali, abban ya dire guiwarsa a gaban junaid inda ya ke kwance ba numfashi,

Muryarsa har rawa rawa take yi wurin furta “Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un junaid !! Junaid!!! meke faru wane ! Ka tashi dan Allah nifa wasa nake ma,

hannunsa yasa yana bubbuga ƙirjinsa, tuni idon abban nasu ya cicciko da kwalla “kai ka tashi bana son wasa ! ya kake so nayi da rayuwata in na rasa ka,

Junaid bai buɗe ido ba sai da yaji dirar hawayen abban nasu a fuskarsa sannan ya buɗe su yana dariya,

Aikuwa abban ya rufesa da duka, ta ko’ina, tashi ya yi ya watsa a guje suka shiga zagaye ɗakin suna yar guje guje

“wlh junaid baka da mutunci, ko tausayina baka ji, ka rasa irin wasan da zakamin sai wannan, kasa shugan sojoji zubda hawaye, ‘

Yana biye dashi  yana magana, haye wa saman gadon junaid yayi abban ya bisa,

A tare suka kwanta sama suna facing ceilling, junaida yace “abba na gaji wlh”

“nima na gaji junaid, dan Allah kada ka sake min irin wannan joke ɗin bana so, baka ji yadda hankali na ya tashi ba,’ abba yayi maganar yana haɗiye yawu,

Junaid ya ce “dama haka kake so na abba, tab dole na tsula tsiyata son raina, wlh abba ka ban mamaki hada yar hawaye,’ 🤣

dariya abban yayi tare da cewa “ba dole ba, hmmm baka son yarda nake jin ka bane shiyasa, ynx dai tell me da bana nan waya ta6amin kai ? muɗaura ɗamarar yaƙi, ? 🤨

tashi zaune junaid yyi saman bedmattress ɗin yace “zan faɗa maka daddy but firstly tell me ka yi mun tsarabar da nace ?

Abba yace “ya za’ae na manta babyna, ba traditional dress ka ce kana so ba ,na ƴan china? Ae na siyomaka abubuwa da dama ma, suna nan,’

Wani irin murmushin jin daɗi junaid ya saki tare da cewa “abba kayima kanka ƙiyamul laili da ace baka siyamun ba ko, hmmm da kaga rigima,

dariya abban yayi yana kallonsa har time ɗin yana daga kwance, junaid yaci gaba da cewa “amma abba baka haɗu da wata zazzafar ƴar budurwa haka ba acen? Nasan ka da farin jini  ,

Cikin zolaya junaid yayi maganar, ɗan zaro ido abban nasu yayi tare da cewa “tab ! ae na gama wlh, Wa ? ni hussein la la la laa, waɗannan fararen basu da guarantee, yadda momynku ta gasa mun aya a hannu, wannan gasuwar ta ishe ni haka, na ɗauki darasi,

Ae ko zan ƙara aure iya nan ne, bazan wuce hausa fulani ba, mata masu kunya, ga riƙo da al’ada ga girmama muji Allah sarki maryam 😢

dariyar junaid yayi tare da cewa “su Abba anji jiki, dama ance jiki magayi ne, ynx kaji jiki ko? sai yanzu ka gane cewa matan mu suna girmama muji ko amma ka  tashi ka auro mana  ….’

bai bari ya idasa maganar ba ya yunkura ya janyosa jikinsa yana yi masa dundu a baya, yana cewa “junaid wai tsaran wasanka ka maida ni ko ? na ta6a cire kaya agabanka ne ? Shiyasa ka raini ko,?

dariya junaid ke ta faman 6a66akawa, shima abban dariyar ya yake yi, haka suke in suka haɗu suyi ta shiririta kai kace ba uba da ɗa bane, 💓

………….Sehrish…………………

ta koma cikin ɗaki kasancewar babu wani aiki da zatayi, su aunty azmee da chef ummu da momina duk suke gyara komai,

zarya take ta faman yi a room ɗin nata, zuciyarta husanna da jahad kawai take Calling, aranta tana cewa “meyasa duk cikin abunda bature ya ƙirƙira baiyo wings ba ? fika fiki, a shiriritar ta , da ace tana da fiffike da tuni tayi sama ba tare da sanin kowa ba ta ware sai wurinsu husanna 😢

ita ce har wurin sallar magriba tana tunanin abu ɗaya,

Acan ciki kuwa abba , yasamu ya fito shida baby junaid, bayan sun gudanar da sallah kowa ya hallara a main palour ɗin mazan kawai suka zauna, suna kara gaisawa da abban su,*💫💫HAFSAT BATURE💫💫*

~BossLady~

*Novel writer of*

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*page 53-54* 😍

general ishaq na zaune a 3 seater shi da Captain najeeb da talal,

Abuhaisam na tare da Abbas da kanal yusif atare suma a mazauni ɗaya,

Fawan da khaleed da jabeer da irfan suma duk suna a tare,

Yayin da abba ke zaune tare da junaid a side ɗinsa sai twins,

gyran murya abban nasu yayi sannan yace ” ina kara godiya ga Allah dayasa na dawo na same ku cikin ƙoshin lafiya, naji daɗin hakan sosai, naga wasu sunyi ƙiba, wasu sunyi haske wasu kuma fara ajiye tumbi 🤣

gaba daya suka fashe dariya, dama indai zolaya ce abban nasu ya saba,

general ishaq yace “wannan dai dani ake, maganar masu ajiye tumbi, kuma na gode,

murmushi abba yayi tare da cewa ” Sorry first born ni na isa na sa dakai, kai fa na fara gani kafin sauran,’

Abbas yace “ƙwarai mu aka fara gani kafin sauran, ƴan shisshigi da kutsu, ‘ yayi maganar yana kallon junaid wanda ya kwantar dakansa ajikin abbansu,

“Ya fi kowa iyayi abba, kamar shi kaɗaine auta nima fa autan ne,’ acewar talal,

fawan yace ” ae wani aikin ma sai in BABBAN YAYA ya dawo nan zaku ga shagwa6a da narkewa da yake mutuminsa ne,

Abba yace “oh wai harynx kuna yiwa junaid irin wannan taron dangin, narasa me ya tsole maku, to bari kuji nan gani nan bari dukiyar uban wani ehe, ya faɗi yana kara janyosa ajikinsa,

dariya su kayi abuhaisam yace “Abba kana sane kuwa da zuwan Lion da tiger?

ɗan zaro ido abba yayi tare da cewa “kai haba ? Badai wannan uban ƴan ji dakan ba, ɗan wurin Alexandra kke cewa ba? Ka ce na tattara kayana na gudu ,”

Yayi mgnr ne cikin zolaya sai kace ba akan ɗansa ake magana ba,

“Abba kana kiran sunan momynmu kai tsaye ko sakayawa baka yi, ina laifin kace ɗan wurin fatima a musulunce dai,”

Ayaan ne yayi maganar yana hura hanci,

dakuwa Abbas yayi masa tare da maimaita sunan ance “alexandara ba sunan ta bane ? ita da kanta tace ko ƴa’ƴanta bataso su kira ta da mommy tafison sunanta Alexandra ko ƙarya nayi?

Kanal yusif yace “aɗan sakaya dai yayanmu, saboda ƙannenmu,”

Abba yace “ynx don rashin kunya, abbas agaban idona kake faɗin sunan masoyiyata kai tsaye? gaban kuma shalelena ?

Junaid ya ƙara rakwabe fuska, dariya su kayi  cikin nishaɗi suke firar kowa na ɗan tsoma bakinsa,

Azmi ce ta kawo musu abunsha kowa ya kar6a, dama ka’ida ne duk bayan ƴan minti na sai ansha tea ko coffee 😌

tura kopan ɗakin tayi ta shiga tana faɗin “Amani baki ga text ɗina bane nace ki same ni a ɗaki”?

aunty babba ce ta shigo ɗakin da amani ta sauka tana mata magana,

Amani dake kwance saman bed hannunta rike da waya tana daddanawa, jin muryar auntyn tata yasa ta tashi zaune, bakar jallabiya ce a jikinta, kanta ba ɗan kwali sai doguwar sumar kanta data zuba a shoulder ɗinta,

“Sorry aunty na ban ankara ba, na dai ji shigowar message ban duba ba,’

Ƙarasa wa tayi kusa da ita ta zauna a side bed din suna facing juna tace “hmmm amani kenan, wato tunda nayi miki hanyar arziƙi, ki kayi kyau kika ƙara haske, kwanciyar hankali ya samu ki ka daina tako wa kizo inda nake ko? Ko phone calls babu ? A whatsapp ma ina ganin ki online ba magana,  wato naira ta zauna ko?

Yar dariya amani tayi “haba aunty na, pls stop saying that, ke fa ce silar shigata wannan daular taya zan share ki ? Ae kullum ƙara gode miki nake, sbd ynx ko a mate ɗin mu ba wadda takama kafa ta wurin arziƙi, ynx fa takai ga ko taro za’a yi na class mate ɗinmu indai ban halacci taron ba to fasa shi akeyi, kowa burinsa na zo ba don komai ba sai don aga wanka leshin da zan ɗauka da zinaran da zan sanya,’

jinjina kai Aunty babba tayi tana ƴar dariya “haka nake son ji my sister, nafi so naga kuna wuta ana binku da fetur, ku zama on top kai kuzama ma topic ɗin gaba ɗaya, inji kawai ana zancen ku a ko’ina,

ta ƙarashe maganar da cewa “ina fata dai baki raga masa ko? Kina tatsarsa sosai kina matso sa sbd kinsan fa abunda ya kawo mu family ɗin nan dukiya muka zo mallaka domin mu raya namu family ɗin,’

Zuru Amani ta ɗanyi tana kallon auntyn tata, cikin sanyin murya tace “Mallakar dukiya kuma aunty? banda kuɗaɗen da muke samu a hannun mazajen mu har wata dukiya zamu mallaka ?

dariya aunty babba tayi tare da dafa kafaɗar Amani tace “ke fa matsala ta dake wani lokacin baki da lissafi, bakya gane wa, ae ynx kowa ta kansa ya ke yi, kuɗi kawai dole mu nemi kuɗi kamar hauka, saboda ynx mun shigo wani zamani da in baka dasu ba’ayi dakai, ka zama tamkar non living thing, masu kudi sune living thing, masu rai kenan,’

Ta ƙare mgnr tana kallon Amani wadda ta ɗan dabarbarce sbd auntyn tata ta fara bata tsoro,

Aunty babba taci gaba da cewa “Oh wai ke da soyayya kika zo kisha wurin ABBAS? Ae ni ban haɗa auranki da abbas ba don soyayya kawai, face don ki rinƙa tatsar mana shi, sannan naga haryanzu babu ciki a jikin ki, uban me kika tsaya jira !?

Hankalin Amani fa ya tashi ganin yadda lokaci guda auntynta ta, ta bayyana mata mummunan ƙudirinta akan family ɗin Abban Sojoji,

Ajiyar zuciya tasaki kafin tace “aunty ra’ayinmu ne yazo ɗaya, shima bayason haihuwa da wuri munyi planing sai nan da 5yrs, ynx soyayya kawai muke sha……. ”

Katse ta auntyn tayi da cewa “ko ba soyayya ba? Nabi soyayyar da gudu, ashe head fish gare ki sam bakya gane wa, to bari kiji in faɗa miki, ki aje wannan planing ɗin, ki ɗauki ciki kawai ! mun samu mai cin gado, nima nan da kike gani na, ba don lalurar da ta same ni ba,  da tuni na jima da sauke wani,

Jinjina kai Amani tayi tana kallonta cikin mamaki,

ƙasa ƙasa da murya tayi kafin tace “ke nifa wani target gare ni akan wasu cikin family ɗin nan, kuma ina mai tabbatar miki da cewa it will work,’

Amani tace “me ke nan aunty”?

wani shu’umin Murmushi aunty babba ta saki kafin tace “BABBAN YAYAN su ! da MARSHAL OMER, ”

zaro ido amani tayi tare da dafe kirji tace ” aunty me kike nufi dan Allah, fahimtar dani, kaina ya ɗaure,’

ƴar dariya Aunty babba tayi sannan tace “So nake na sama ma, ƙannan mu gurbi acikin gidan nan ! Kuma waɗannan shahararrun su nake hari ! ta ƙarfi ta tsiya 😳

cikin tsananin tashin hankali Amani tace ” Aunty anya ba giya kika sha ba ? kinsan suwa ki ke magana akai kuwa ? Babban yaya fa da marshal omer ?

Cikin jaddadawa Aunty babba tace “ƙwarai kuwa ! Su nake nufi kuma a shirye nake da nayi koma mai zanyi don na asirce su naja ra’ayinsu akan Hayaam da Abrah,”

Zuba wa juna ido su kayi suna kallon kallon, har ynx Amani ji take tamkar mafarki take yi ba gske ba, ƙarfin hali irin na auntynsu ya bata mamaki tarasa wa zata ce sai Rafayet da Omar ? Anya kuwa aunty bata sha wani abu ba?

Katse mata tunanin ta tayi da cewa “na lura har ynx bakisan me nake hari ba, bari nayi miki dalla dalla,

Rafayet da ki ke gani duk family ɗin Abban sojoji ba wanda yakama  ƙafarsa wurin tarin dukiya, gashi matashi ga kyau, a binciken da nayi Rafayet ya mallaki  billions of dollars nasa na kansa, bayan tarin gidajen dake gare sa a us da sauran countries ɗin da yake yawan zuwa, sannan kuma ya mallaki privet jet nasa nakansa, ga tsadaddun motoci dake gare sa ƙirar bugatti, ƙirar mercedes benz, ƙirar pagani da ferrari da sauransu, ke duk wani abu da kike sani mai tsada rafayet ya mallake sa, shi kanshi tsadar gare sa, ke nifa farko dana fara ganin shi wlh, sai da nayi danasanin auren ishaq, hmmm ke fa bakisan shi ba ko, ae zai zo ne,

Amani ta gama rikice wa da jin irin dukiyar Babban yaya, cike da mamaki tace “wai dagaske kike auntyna ?

Murmushi Aunty babba tayi “ƙwarai ma kuwa, Rafayet he’s among the most richest men in the world, youngest billionaire ne, Kuma yana ɗaya daga cikin most handsome men  saboda kyansa da structure ɗin jikinsa,

Jin jina kai kawai Amani take yi ta jin jinawa lamarin,

Murmushi aunty babba tayi kafin taci gaba da cewa “Bayan Babban yaya kuwa a wurin arziƙi cikin family ɗin nan sai Hajiya azeema, wannan matar da ki ke ganinta ƙuruwa ce wurin arziki,business ɗin golds take yi da diamonds, ina wannan agogon ta hannunta ? Kin ganta ae ko ?

ta faɗi cikin son fahimtar da Amani,

“Eh aunty na ganta mai kyau kamar na sace wlh,’

“Hmmmm to wannan da ki ke gani ƙirar graff diamonds ce, $40 millions a us dollars, a naira kuwa sun kai 24 billions,’

dafe ƙirji Amani tayi gaba ɗaya tabi ta susuce, jin abun take tamkar a mafarki, sakin baki kawai tayi galala jin wannan daular,

Aunty babba taci gaba da cewa “daga ita kuwa sai marshal Omer wurin arziƙi, shima billionare ne duk wani abu da Babban yayansu ya mallaka shima ya mallaka, don dai ya wuce shi da wasu abubuwan, sune kawai nayi bincike akansu, sauran kuwa kowa attajirin kansa ne, ya ki ke  gani idan Hayaam ta samu shiga Wurin Rafayet ita kuma Abrah muka kutsa ta wurin Omar ?

Washe baki Amani tayi tare da cewa “ae shikenan kawai ba sauran magana, mun gama kwaɗaice wa,”

dariya su kayi gaba ɗayansu a dai dai lokacin Azmee tayi knocking kopan ɗakin, cikin sauri suka gyara natsuwarsu,

Amani tace “Shigo ciki” tura kopan azmee tayi ta shigo da fara’a a fuskanta tace “dama an kammala dinner ne, naji shiru baku fito ba shine nace bari nazo na sanar daku,”

*Me zaku ce game da Aunty babba da Amani dake shirin mallake dukiyar da ba ubansu ya tara ba ?*😡*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

_written story by_ *HAFSAT BATURE*

~BossLady~

*Page 55 to 56*

Yinin ranar jin jikinta take yi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa, shi dai gayanan wata ni’ima ni’ima , ga wata irin kasala da ta mamaye ta, sai wani lalaci da take ji, saukin ma aunty Azmee ta sanar da ita cewa bata da aiki ta zauna ta huta kawai, yau ranar hutun ta ce , yini tayi tana safa da marwa frm wall to wall, zullumi iri iri agame da su HUSANNA da JAHAD, ga kuma wani irin bugu da zuciyarta take yi mata, ita dai tunkan ta sa wannan Babban yayan nasu a ido take jin feelings agame dashi  (kina ruwa 😂)

Har cikin bedroom dinta azmee ta shigo mata da dinner dinta, ba karamin dadi taji ba, kaunar azmi na kara shiga cikin zuciyarta, sbd tana kula da ita kamar yar cikinta, ta damu da ita sosai, Allah sarki,

Zuba wa meatballs din dake shake cikin plate din dake ajiye saman bedside drawer dinta tayi, ga fresh milk acikin glash cup, shiru tayi tana kallonsu, jikinta a mace yake, ga kamshinsa ya cika ta, amma a kullum ji take kamar batayi wa yan uwanta adalci ba, tana cin irin wannan dadin yayin da suke ciki mawuyacin hali,

Zugudum tayi a yayin da take zaune a saman gadon daga baki baki, ta lankwashe kafanta a sama,

Azmi ce ta sake turo kopan ta shigo hannunta dauke da fresh fruit acikin dan plate,

“Ya akai har yanzu baki fara ci ba? me kike jira ?

ajiyar zuciya sehrish tasaki tare da cewa “Aunty azmee zuciyata bata mun dadi in na tuna da yan uwana, sai naji bana son cin komai,

Cikin nuna damuwa azmi takarasa ta ajiye mata plate din a hannunta, sannan ta zauna gefenta cikin natsuwa tace ” kin yi imani da Allah!?

daga kai sehrish tayi tare da cewa”Eh”

“Ina so aduk lokacin da zakiyi addu’a ki kasance mai cike da imani, kiyi imanin cewa addu’ar nan da kika yi Allah ya karbeta, don’t doubt about it sbd karancin imanin kesa muna rasa wani abun,  amma muddun ki kayi masu addu’a kina me cike da imanin cewa Allah ya karbeta, ba tare da kinsawa ranki kokwanton cewa Anya Allah ya karbi addu’ a ta kuwa? Ko kuma kinji shiru har ynx ba ki ga sakamako ba, duk ba’a son wannan, kawai kisa ma ranki cewa duk in kikayi addu’ a Allah ya amsa kuma tom insha Allah zaki ga sakamako mai kyau, kuma zakiji natsuwa acikin zuciyarki,”

Jinjina kai sehrsh tayi tare da cewa “ngde aunty azmee kuma insha Allah zanyi kamar yadda ki kace”

Murmushi azmee tayi tare da cewa “yawwa rishi na, ko kefe yanzu dai ayimun wannan murmushin kashe zuciyar nagani” ta fadi cikin zolaya tana kallonta,

Sunnar da kai sehrish tayi tana murmushi, itama azmeen murmushi take yi, hannu azmee tasa ta dauki yankakkiyar abarbar dake cikin plate din dake ajiye a saman hannun sehrish,

A baki takai mata tare da cewa “Ha bakin nasa miki’

Bude baki sehrish tayi tana yar dariya, zura mata abarbar tayi, sehrish ta taune, nan take zakin abarbar ya cika mata baki, takama lasar labba,

Azmee tace “yawwa ko ke fa ynx naji magana, bari na baki meatballs din abaki,”

Cikin sauri sehrish tace “a’a aunty azmee zanci ynx, kunsha aiki kun gaji, gashi ban tayaku ba,’

“Kada ki damu sehrish, ae ni nace ki zauna tun da gasu Chef ummu aiki na tafiya yadda ya dace, ina fata dai bakiyi tunanin BABBAN YAYA ba yau ?”

Ta karasa maganar tana kallonta, cikin zolaya,

Sunnar dakai tayi tana murmushi jin an ambaci sunan da ke mata kaikayi a cikin zuciyarta,

“Bani da amsa kenan, tam ni zan tafi ynx kada ki manta, a daren yau kiyi sallolin nafila, kiyi addu’o’i wa yan uwanku da kuma sauran al’ummar musulmai,”

“Insha Allah aunty Azmee ngde sosai”

Tashi Azmee tayi ta fice 👋

Hakika sehrish ta samu natsuwa a ranta, azmee ta iya kalami masu dadi masu sanyi da ratsa zuciya,

zama tayi ta dinga cusa fruits din dake agabanta cikin bakinta, cikin dadi take shan su,

bayan ta gama dasu ta ajiye plate din ta dauko na meatballs din ta shiga dauka tana jefawa a baki, kunnanta har motsi yake, yayi dadi sosai, yaji kayan kamshi,  lokaci zuwa lokaci ta kan hada da cool milk din dake acikin cup, tana kurba 😋

Kwance suke rungume da juna, daga su sai dan towel a waist dinsu, da alama daga bathroom suka fito duba da ruwan dake a jikinsu,

“Ayaan ba karamin dadi naji ba wlh’

“game da me kenan ? Jahan ya tambaya yana kara shafa sumar kan ayaaan,

“game da zuwan babban yaya, i felt so happy da junaid ya sanar damu cewa ba date ba time na zuwansu,’

murmushin takaici Jahan ya saki tare da cewa “hmmm da alama bakasan wannan mutumin ba, ni nayi imanin cewa daker babban yaya zai wuce gobe baizo nigeria ba !!!! Ina ji araina !

dan dagowa Ayaan yayi daga jikin jahan yakasance yana kallon face dinsa, cikin kwarkwasa yace “pls stop thinking about that, kawai musa wa ran mu cewa ba nan kusa zai dawo ba, hakan zai bamu courage din ci gaba da jin dadin junan mu,,”

murmushi Jahan ya saki yana kallon cikin kwayar idon Ayaan wadda takasance ash colour ce, mai ruwan toka, mai kyan gaske , shima kallonsa yake yi cikin tsananin sha’awar junansu, zuciyoyinsu na kara azalzalansu akan su kara second round, hannu jahan yasa ya janyo ayaan bakinsu ya hade dana juna ya zura harshensa acikin nasa, nan suka shiga misayar saliva a tsakaninsu,

………………….AUNTY BABBA…………………

zaune take agefen amani sbd dama basu tafi ba, suna jiran zuwansu babban yaya, duk da ita amani acikin garin take , amma abbas ya bata iznin ta zauna ta kwana tunda auntyn ta na nan itama , Inyaso zuwa gobe sai ta dawo gida,

Dukansu suna sanye cikin sleeping dress, riga da wando, masu kyan gaske, kowa ta zubo gashin kanta dayake Allah yabasu,

“Ina sauraronki aunty na” amani tayi mgnr tana kallon auntyn tata dake gefenta saman gado,

“Shiri na musamman ya kamata muyi wa lamarin domin cin nasara akan wadannan zafafan guda biyu, shawo kansu ba abu mai wuya bane, dole sai an hada da shahararrun bokaye, kamar wannan bokon na kurmin dajin nan dake a enugu, ”

Xaro ido Amani tayi tare dacewa “Aunty enugu fa kikace ? gsky da kamar wuya wlh,’

Dariya aunty babba tayi tare da cewa “a wurinki ba, ae ni akan na cimma buri na wlh ba abunda bazan iya yi ba, hmmm ke dai kawai abar kaza cikin gashin ta har ynx bakisan wacece yayarki Laila ba, ‘

zugun Amani tayi tana kallonta hankali a tashe, lamarin ya fara bata tsoro “yanzu aunty yaushe zaki enugun?

Cike da kwarin guiwa aunty babba tace “Ni bana aiki cikin gaggawa,  a sannu zamu cimma nasara, amma kafin nan muna Bukatar kudade dayawa, don tunkarar wannan bokan ba abu bane mai sauki, dole mu hada karfi da karfe ki tatsar mana wurin abbas nima na tatso wurin Ishaq, daga bisa ni mayi mgnr zuwa can,’

shiru amani tayi ita dai haryanzu akwai karaya atare da ita, cike da kasala tace ” aunty nifa ina tsoro wlh,”

Mtswww aunty babba taja tsoki “ke dallah wane tsoro, aje wannan ma gefe, ke bakisan abunda nake hango mana ba, muddin muka ci nasara akan Babban yayansu da marshal omar to ina mai tabbatar maki da cewa gabadaya zamu rinka juya kowa na family dinnan, sai yadda muka so za’ayi”

ta idasa magabar tana kallon Amani, wadda tayi tsuru tsuru,

ajiyar zuciyata tasaki har zatayi magana wayarta dake saman saman pillow ta soma ringing, da sauri takai hannu ta duba sunan “Babyna” ya bayyana

Aunty babba tace “halan Abbas ne ? Amani tace “eh shine,’

“Yawwa maza ki daga, ki rinka kashe masa murya kina masa ladabi ko mun ci nasara akan kudin da muke bukata,’

amani ta amsa da to, tare da picking call din ta kara a kunne tare fadin ” baby na y kke? nayi kewarka sosae,”

Saurara wa tayi tana sauraran muryar abbas dake cewa “nagaza bacci ne, na fito daga wanka ne, naji ba abunda nake son ji face muryarki,”

Murmushi Amani tasaki tana kallon aunty babba data kura mata ido, cikin sanyin murya tace “nima haka babyna, ynx haka maganarka nake ma,’

“Are u serious ? Zamu yi video call ne inaso naganki cikin sleeping dress din nan naki, ‘

Kallon aunty babba tayi taji me zatace saboda wayar a handsfree take, da ido tayi mata alamar tace masa eh,

“Eh babyna a shirye nake , nima a kagare nake dana ganga, ”

Murmushi aunty babba, tayi tare da mike wa ta fita daga dakin tana ji  aranta cewa burinta zai cika,

Dare yayi sosai Junaid na dakin abbansu , ya addabe shi ya hana shi sakat, shi ala dole ga auta, suna kwance atare saman king size bed dinsa, junaid ya aza masa kafarsa a saman jikin abbannasu, zallar rigima yake ji,

“Junaid dan Allah ka barni na huta, ka tafi bedroom dinka ka kwanta mana, ko kaje Wurin yayyen ka kwana mana,” abban nasu ne yayi maganar cikin jin bacci,’

cikin shagawaba yace “nafi jin dadin kwanciya ajikin ka abba,  In kuma kana so nadaina zuwa kwana nan, tam ka je ka dawo da mommyn mu, ”

rai a dan bace abban nasu yace ” kada na sake ji ka kira min sunanta Allah,”

Cikin zolaya junaid yace “kaifa kace kana so Abba, ba wanda yayi maka dole, saboda dadin soyayya ko su Ammi basu sani ba kaje har us ka aurota, wato kaga kyakkyawa, doguwa fara mai dogon gashi ko ?

Yunkura wa abban yayi tare da fadin “bismillah” ya janyo pillow, ya shiga bugun junaid dashi, dama sun saba ya maida shi tamkar tsaransa, kuma Abban ba karamin dadin hakan yake ji ba, cikin kukan wasa junaid kecewa ” Abba dan Allah kadaina ae gsky na fada, wlh momyn mu akwai kyau, shi ya rudaka ma,

Cikin mamaki abban yace “wai junaid ko dan muna kwana shimfida dayane yasa ka raina ni?

dariya suke gaba dayansu, duk yadda yaso junaid ya rufe bakinsa ya daina masa maganar Alexandra (Alekzandra)  amma yakiya, dakyar bacci ya kwashe su, su duka,

Insha Allah za’a samu Lunch ko dinner, in Allah ya yarda amma ✨

*💋💋SURGEON GENERAL RAFAYET & MARSHAL OMAR💋💋*

*Welcome to Nigeria* 😍

*finally our Stars Sun bayyana* 😂

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*ku kaddara cewa page 1 ne wannan domin kuwa yanzu labarin ya soma*

Page *57*

Writer *HAFSAT BATURE*  ~BossLady~

Bayan ta kammala cin abunda azmee ta kawo mata kitchen ta mayar da kayan, sannan ta dawo ta shiga toilet ta daura Alwala, ta zura hija bi ta shiga jera salloli, bayan ta kammala ta rufe da zafafan addu’o’i tana nema ma rayuwarsu sauki, tasha kuka ayayin da ta daga hannunta sama tana rokon ubangiji, hawaye na gangarowa a idonta,

Ba ita ta kwanta ba sai cikin dare ya taba, sannan ta kwanta, tare da rungumo pillow a chest dinta kamar yadda ta saba, tabbas ranta na bata cewa Babban yaya bazai wuce gobe ba bai dawo ba, saboda taji wani sanyi aranta, amma bata da tabbacin hakan , sai in Allah ya kaimu da rai da lafiya sai kuma in hafsat bature ta so hakan, dayake wuka da nama suna hannunta, 😜😜😜

****************************************

Mutum biyu ne suka san da zuwan su Abba da junaid sbd sunyi receiving call dinsu in d midnight, a time din mu na nigeria jirginsu  zaiyi landing around 9:00am,

A Wani irin haɗaɗɗen katafaren privet jet ne ya ɗauko su, wanda ya kasance mallakin Surgeon general RAFAYET, ya haɗu fiye da tunanin mai tunani, cikinsa bai da banbanci da hamshaqin parlour wanda yaji tsadaddun furnitures, saboda an ƙawata shi da jigunannun furnitures,

Wato Aljannar duniya ce, acikinsa ya ƙawatu, 👌

Wasu hamshaƙan leather seats ne acikinsa jigunannun gaske, wanda ko a ido ka kallesu kasan zasu yi tafshi da daɗin zama, masu numfashi irin waɗanda kana zama zasu lumbutse dakai ciki,

A jere suke biyu suna facing ɗin biyu zungura zungura, a tsakankaninsu wani ƙayataccen table ne haɗaɗɗen gaske, mai ɗauke da travel cups wanda abunsha ne acikinsu, tukunna ma shin su wanene acikin jirgin ? 😒

tunkan na fara zayyana su zan fara da faɗin tabarakallahu ahsanul khaliqin 😇

Haɗaɗɗiyar sura, dogaye ne masu cikakkiyar ƙira irin ta zakuna, irin ta mazan gaske sadaukai kuma jarumai, ƙerarrun gaske, duk inda namiji yakai to su sun zarce nan, komai nasu na kece raini ne ba wasa a tattare dasu babbar harka ne, duk iya haɗamar mace bazata wuce waɗannan handsome stylish guys ɗin ba, buri kowace ƴa mace nesu, a fage na kyau kuwa ba’a magana, ƙarshe ne su, a bangaren wadatar arziki kuwa basai an faɗa maka ba, kana ganin su  kasan cewa sun wanku da pawns da dollars, fatar jikinsu kaɗai abun kallo ce, su huɗu ne zaune kowa ya hakimce, jirginsu kawai suke jira yayi landing,

3 daga cikinsu suna sanye cikin expensive dress na suits, biyu launin nasu blue ne ɗayan kuma black ne,

Mutun ɗaya ne baya sanye cikin suits ɗin nan,  shin wanene shi? Jikinsa na sanye cikin V-neck shirt , tayi tighting ɗinsa, white colour yayin da yake sanye da army trouser,

Yana da wata irin sura mai matukar rikiɗarwa mai razanarwa mai matukar jan hankali da ƙayatarwa, saboda a halitta dogo ne, mai wani irin faffaɗan ƙirji a  buɗe yake, ga wannan six pack din nasa baro baro, ya cika vest ɗin kana ganin zanen ƙirjinsa ga breast ɗinsa sunyi 6ul-6ul ata ciki kana hangensu, daga gani yana gym (motsa jiki) sosai, in ka kalli damtsen hannunsa sai ka tsorata, kana gani kasan cewa yana da matuƙar ƙarfi kamar ɗan wrestling (dambe) haka surarsa take, mutun ne mai ji da ƙarfi,

Idan muka je wurin tommy dinsa kuwa a shafe yake ba alamar tumbi ko kaɗan, yayi flat, tamkar baya zuba abinci acikinsa saboda ɗamewarsa,

Launin fatarsa fari ne sol irin hasken fatar ƴan korea, natural white kasancewarsa half cast (ruwa biyu) mahaifinsa hausa fulani, mahaifiyarsa baturiya, ya kuke ganin abun zai kasance?

A wurin kyau kuwa sai dai muce tubarkallah, domin Allah yayi sa da wani irin ƙayataccen kyau mai matuƙar razanarwa, ko namiji jinsin sa ya kallesa sai ya ƙyasa balle mace, yadda kasan shi ya zana kansa, don duk mun haɗamar bil’ama aka basa damar ya tsara yadda kyansa zai kasance, bazai wuce nasa ba sai dai ma ƙasa da nasa 😯

Komai na halittar jikinsa dogo ne, kakkarfa domin Allah ya wadatasa da duk wani abu da mace zata buƙata ajikin ɗa Namiji!

Idan muka koma kan haɗaɗɗiyar suman kansa kuwa mai tsayin gaske wadda ta sauko masa har saman kafadarsa , tasha gyara na musamman ya ɗaure ta, dark brown ce Allah kaɗai yasan nawa ake kashe ma wannan suman wurin gyara,

Hatta gaban forehead ɗinsa sumarce a kwance, ga wani kwantaccen saje mai shegen kyau, eye brows ɗinsa kuwa tamkar an zana ta, tayi wani irin shape ga gashi cike da ita, kiris ya rage jagirarsa su haɗe da juna saboda yawaitar suma a wurin, idan muka koma kan idonsa kuwa yana eyelid (kwarin ido) wadatacce wanda ke lullu6e da eyeballs ɗinsa, yana da dogayen eye lashes masu cukowa da tsari, ga kyan gaske

Allah yabasa kyawawan idanuwa ga girma ga su so sexy, farare tass tass masu ɗauke da kwayar ido, blue colour masu shining masu ɗaukar ido,

daga ƙasa kuwa dogon hancinsa ne, ba wai irin ziƙau ɗinnan ba, a’a mai tsari dai dai wa daida, daga nan kuwa sai pink lips ɗinsa tamkar ya shafa jan baki, ga skin din la66ansa irin mai squeeze ɗinnan ce,

Cikin natsuwa yake daddana laptop ɗin dake gabansa saman table, ƙirar Luvaglio wadda price ɗinta yakai $1 million ne (dala miliyan ɗaya)  a naira kuwa yakai 600millions, miliyan ɗari shidda, cikin natsuwa yake daddana ta da zira ziran yatsunsa, hannunsa na sanye da wrist watch kirar piaget emperador temple ce, farashin ta yayi $3.5 million a naira kuwa ba’a magana billions ne ke magana,

Zan iya cewa duk macen da zata so shi ba don Allah bane, zai yi wuya asamu macen da zata so shi hakanan kawai ba don wani abu nasa ba, kamar kyansa, tarin dukiyarda shi kansa baisan adadinta ba, surar jikinsa ga kuma ilimin addini dana zamani, komai ya haɗa komai nasa is Extraordinary,

Basu kadai bane acikin jirgin akwai wasu gabza gabzan soldiers wadanda suke a matsayin security guards nasu, mostly dinsu black americans ne, ba wasa a tare dasu, basa ji basa gani umarni kawai suke jira su aiwatar 😳

Bakowa bane wannan face SURGEON GENERAL RAFAYET 😘 wanda kowa ke zumuɗin ganinsa, wanda hafsat bature da sehrish suke kwakwar ganinsa, tare da mamee da kuma readers😂

BABBAN YAYA wanda kowa ke shakkarsa ko sunansa aka ambata sai an girgiza, baya wasa da aikinsa, kaifi ɗaya ne,babu mai iya tankwara shi, sam mace bata gabansa a tsarin rayuwarsa baya da burin yin aure gaba ɗaya, cos bashi da interest akansu, mata bibiyarsa suke kamar hauka, ƴa’ƴan manya yayan shuwagabanni ya’yan sarakuna,  amma ko kallo basu ishe shi ba, 😂

yadda yake kallon namiji haka yaje kallon mace ba banbanci, sam bai da shauƙin soyayya a tare dashi,

Tun saura 30 mins jet dinsu yayi landing , manyan motoci suka isa airport din jibga jibga na sojoji, baka jin komai sai tashin jiniya kamar ana yaki, a cikin motocin akwai na gayu tsadaddun gaske kirar mercedes benz da aka zo daukarsu da ita,

Time din da jirgin yayi landing, cikin isa kowannansu ya fito, yana saukowa daga matattakalar benen, a jere suka sauko gaba daya ido na akan Babban yaya tare da marshal omer, cika ido suke kamar kamar me, a bubbude suke tafiya irin tafiyar nigogin nan, wadanda suka ji karfi, shi marshal omar sam bai kai rafayet tsayi ba amma fa akwai kira ta mazajan gaske,

Masha Allah,

🫶🫶🫶🫶🫶🫶🫶

Su wa ke farin ciki da zuwan *BABBAN YAYA*😍

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•

*page 57 to 58*

Ci gaban page 57 cikin nan

 

**********************  ⬇ **************************

**********    Ai Hausa Novels  ****************

*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

 

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

**********************  ⬇ **************************

***************   Ai Hausa Novels   ****************

**********************  ⬆ **************************

Not edited like always 👀

…………..SEHRISH…………………………………..

Bacci take ta faman sha, hankalinta kwance batasan meke wakana ba, time din da azmi ta shigo ta same ta, tana ta sharar bacci bata yi yunkurin tashe ta ba, saboda tasan halin da yarinyar take ci, akwai damuwa atare da ita sosai, tana bukatar hutu brain dinta ma ta huta ko ta samu natsuwa, hakan yasa ta juya ta koma kitchen domin gudanar da aiki  ita kadai, sbd dama an sallami su chef ummu ynx aiki ya rage daga ita sai sehrish,

Azmi bata gajiya da aiki, maca ce mara kyashi, in dai tana girki tana tazbihi a cikin zuciyarta shaf shaf take kammala komai, Ita a tsarinta ma bataso Sehrish na aiki, tafi so ta zama kamar yar masu gida saboda son da take yi ma yarinyar, tana jinta kamar yar cikinta, ❤

bayan ta kammala, da kanta tabi ta jera a dining, a hankali su ka fara fito wa, wadanda yunwa ta koro, lokaci guda duk suka hallara kowa ya zauna,

Abba na kusa da junaid dama suna atare, kanal yusif, da irfan da jabeer da khaleed duk suna a right hand yayin da suke facing din, Aunty azeema, Amani da aunty babba,  sai bg Abuhaisam na kusa da Fawan, kowa sai zuba wa cikinsa yake a natse, mutun biyu ne ke basu hallara ba a dining din ba,

sai faman wurga ido junaid yake yaga ko zai ga fitowar sehrish amma babu alamarta, hakan yasa shi jin wani yanayi tsoransa kar ace bata da lpy, dago wa yayi ya saci kallon aunty Azmee dake saving dinsu daga tsaya, a hankali yake motsa lips dinsa yana tambayarta ina Sehrish ba tare da sauti ya fita ba,

Murmushi azmee ta saki tana dan kallonsa, da hannu tayi masa alamar cewa bacci take yi, lumshe idonsa yayi alamar jin dadi aransa, maida idonsa yayi akan Chips din dake gabansa cikin plate,

gyaran murya Aunty azeema tayi tare da cewa “uhm ana ta kulu wash rabu, su yusif ba baka sai kunne,”

murmushi kowannansu yayi, dan dagowa yusif yayi ya kalle ta cikin sanyayyiyar muryarsa yace “Aunty azmee bakyau ana da’amin ana magana,” .

murmushi aunty azeema tayi tare da cewa”dadi na da yusif akwai hankali ga natsuwa komai nasa na bin ka’idar addini ne masha Allah,”

Abba yace “ae ina ji duk cikinsu shine ya biyo halin ummansu komai nata, hatta kyan fuskarsa in ka cire Marshal omar,”

“gsky abba ka tara kyawawan samari masu ilmin addini dana zamani ya kamata ace kowannan su iyanzu ya fidda matar aure tun da aun mallaki komai,”

Aunty babba ce tayi mgnr, wani irin kallo yusif yabi ta dashi sbd baison yaji ana masa maganar aure bama shi kadai ba hada bg Abuhaisam,

“Aunty babba matan ne basu da tabbas, mutun na bukatar tsawon lkc kafin ya fidda wadda ta dace da rayuwarsa, aure baya bukatar gaggawa kuma shi  lokaci ne”

Bg abuhaisam ne ya bata amsa, jinjina kai tayi, yayin da yusif yace “you’re right yaya haisam, we’re waitin for the time, in yayi zamu yi ne,”

dan murmushi aunty babba tayi ita burinta tafara tunzura abba akan Babban yaya da marshal omar saboda abun yazo mata da sauki,

“mgnar ku gasky ne, amma abun da nake so ku sani, shi lokaci baya jira ! lokaci tafiya yake yi, this is the right time daya dace ace kunyi deciding akan sama ma kanku abokiyar rayuwa, its very hard to find a righteous partner in this situation of life, rufe ido kawai mutun zai yi ya canka,”

tayi mgnr tana kallon yusif dake facing dinta, kafin yusif ya bata amsa abba ya katse masa hanzarinsa da cewa “kwara ki fada musu, ynz ni ba abun kwatance bane a wurinku ? ina da 20yrs akayimun aure dayake na mallaki komai na rayuwa, in Allah ya baka dama ka damata alokacin daya dace, gashi ynz Allah ya albarkace ni da ya’ya da karfi na ban tsufa tukuf ba, naji dadin hakan sosai, ada ina jin haushin anyimun aure wuri, amma at the end naga amfanin abun,’

Jinjina kai su kayi kanal yusif yace “pls muna barar addu’arku aunty azeema aunty babba and aunty Amani atayamu da addu’a Allah ya bamu mata salihan mata na gari masu koyi da matan Annabi muhammad (S.A.W) Ba shaidanin  zamani ba,”

Gaba dayansu suka amsa da (S.A.W.) kafin suka bi da ameen, suna dariya jin maganarsa ta karshe da yace shaidanin zamani,”

Junaid ya kalli abbansu tare da yin kasa kasa da murya yace “Nima abba atayani da addu’a mace tagari,”

Dariya su kayi gaba dayansu don sun ji shi, fawan yace kama cire batun aure a ranka, domin kai da yin aure sai nan da 20yrs lkcn ka kara hankali,”

Harara junaid ya watsa masa tare da cewa “Yanzun ma da hankali na, abunda dan shekara 30 zaiyi in an masa aure nima zan iya fiye da haka   …….”

Bai ida maganar ba bg abuhaisam yayi masa dakuwa da hannu tare da cewa “gidanku ! Ja’iri ina maka kallon ustaz ashe kaima dan duniya ne,”

Abbansu ko murmushi kawai yake yi sbd yasan cewa sarai junaid yayi maganar ne batare da yasan me zasu fahimta ba su,

Aunty azeema tace “yaro ya girma abun sai addu’a’

Dariya su kayi gaba dayansu ,

Ba zato ba tsammani suna cikin wannan nishadin, kwatsam su kaji dirar motoci a tsiyace, ba kakkautawa da gudun gaske suke shigowa cikin gidan, lokaci guda jiniya ta karade ko’ina, hankalinsu ba karamin tashi yyi ba Abun kamar a filin Yaji,

Antayo wa suke ciki ajere suke kurdadowa,

Sehrish sai faman toshe kunnata take da pillow saboda jin tamkar za’a fasa mata kanta, ga nauyin bacci tana ji sam ta kasa kakkauran motsi ta tashi, jiniyar motocin dake shigowa har tsakiyar kwalwarta, sai faman matse ido take ta ciccije lebe,

Kamar daga sama taji sautin harbin bindiga mai karfin gaske kamar fashewar bomb haka taji, a wani irin firgice ta wuntsilo daga saman gadon izuwa kasa gefensa, daga ita har pillow kowa ya ware gefen, bargon ne kawai kankame a hannunta, gaba daya dukkan ilahirin jikinta rawa yake yi, sai faman zazzare ido take yi, tuni zufa ta soma wanke mata fuska, da karfi take breathing in har mutun sai natsuwa tsaf zaiji bugun zuciyarta,

Wani harbin da aka sake yi nan take ta fashe da kuka, sbd dama a tsorace take da mafarkin da tayi,

Acan ciki kuwa, lokacin da jiniyar motocin nan ta karade ko’ina nan take fawan ya saki cokalin dake hannunsa, idonsa akan junaid sbd yasan cewa sarai junaid yasan da zuwan bazatan da Babban yayan nasu yayi bai sanar dashi ba, su kam sauran musamman aunty azeema da Abban nasu su bg abuhaisam da su kanal yusif farin ciki a wurinsu ba’a magana, juyawa aunty babba tayi ta kalli Amani wadda itama kallonta take wani shu’umin murmushi suka sakarwa junansu jin wadanda suke hari sun karaso,

Su irfan da jabeer kuwa da khaleed kallon kallon suka shiga yiwa juna kowa na sauraran jiniyar motoci yayin da zuciyoyi ke beating

Duk ba wannan ba ina maganar su twins wadanda ke kwance kankame da juna suna cikin shan soyayya suka jiyo sautin nan, zuba wa juna ido su kayi ba tare da kiftawa ba, hankali a tashe Ayaan yace “Maganarka ta tabba jahan wlh shine ya dawo,” shiru jahan yayi sam ya gaza cewa komai, gaba daya jikinsu ya gama mutuwa ,

Cikin sauri wasu gabza gabzan sojoji sanye da kaki ga manyan bindigu a hannunsu suka diro daga saman motarsu,

Cikin hanzari suka karasa tare da bude masu mota, fitowa marshal omar yayi yayin da babban yaya ya fito ta other side din,  abun gwanin burgewa, haka suka bude wa major general tare da Captain adams motarsu wadda ke bayansu ta Omar, suma suka fito

With respect sojojin nan gaba dayan su suka buga kafa tare da sara musu abun sai wanda ya gani, mu da akayi a gabanmu 😍😂

Sehrish dake a tsorace jiki na rawa ta lallaba ta taso, daga ita sai yar shirt wadda takai mata dai dai guiwa, ba dogon wando jikinta, sai santala santalan kafafuwanta,

Jikin window ta karasa tasa hands dinta dake ta faman kerma ta janye labulen tare da zuge glass din windown, zuba ido tayi tana hangen Zugar sojojin dake a cikin gidan kai kace yaki ne ya taso,

A hankali take lumshe idonta tare da budesu tana kare wa mutanen dake wurin kallo, sam sojojin da sukayi masu kawanya basu bari tagansu ba,

Sai da soldiers din suka dare biyu tare da bude masu hanya sannan sehrish ta samu damar hangensu, Marshal omar ne a gaba sai Mg osman a bayansa sai Captain adams ne, a hankali take kallonsu a ranta tana fadin “wanene babban yaya acikinsu, inaji araina cewa tabbas shine ya dawo,”

Bata idasa tunaninta ba eye balls dinta suka sauka akanshi, kasancewar duk yafi su tsayi nesa ba kusa ba, Allah yayi mishi tsayi, sumar kansa ce tafara hangowa wadda ke kwance luf a bayansa da gefen forehead dinsa, zuciyarta ta dinga ji tana mata wani irin mugun bugu, bata da tabbacin cewa shine, amma ba karamin razana tayi ba da irin kyansa, duk da bata samu damar ganinsa da kyau ba, amma irinsu ko daga nesa ana shaida kyansu, kamar tauraro haka yazama acikin taurari 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

duk yadda sehrish taso ta kare ma wannan da ta hango daga nesa kallo hakan baiyu ba, bakomai take tunawa ba sai wannan hoton na cikin wayar junaid datake yawan gani, tabbas wannan shine na cikin wayar wato BABBAN YAYA,”

zuge glass din tayi tare da janyo curtains din ta rufe, murmushi kawai take sakarwa kanta tare da ajiyar zuciya at same time,

Tarasa ina zata sa kanta don farin ciki, sai faman sakin fara’a take kamar wacce aka ma Albishir da gidan Aljanna 😂

Tarasa tsaye tarasa zaune tarasa ina zata tsoma ranta, tsilli tsilli haka take yawo da yan kafafuwanta cikin room din nata,

A can ciki kuwa lokacin da suka shigo, hankalin Amani ba karamin tashi yayi ba ✨✨✨✨•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·

_Warning ❗❗❗ko da gigin wasa banyarda wani ya ta6amin littafine ba kamar canza wani sashe na labarin nan ba , ko haɗa document ko makamancinsu, in hakan ta faru kuma wlh mutun bazai ji da daɗi ba, duk inda yake a faɗin duniyar za’a samomin shi koda aljani ne ba mutun ba_😡

*page 59 to 60*

A can ciki kuwa lokacin da suka shigo, hankalin Amani ba karamin tashi yayi ba data fara cin karo da marshal omar, duk tabi ta zuzuce, a hankali tace ma aunty babba wadda ke kusa da ita a tsaye tace “Shine “? girgiza kai aunty babba tayi tare da cewa “wannan Shine marshal omar, ki zuba ido kawai bama saina fada maki gashi ba kina ganinsa zaki gane sa da kanki,”

tun kan Amani tace wani abu Babban yaya ya shigo cike da wannan tafiyar tashi ta Qasaita, wani irin bugu taji zuciyarta tayi juyawa tasake yi ta kalli aunty babba wadda idonta ke akansa ko kyaftawa basuyi,

Cikin tsantsar farin ciki kanal yusif yayi sauri zai hugging din omar, dakatar tashi omar yayi da cewa “bari na fara kwasar Albarka wurin Abbana tukunna,” murmushi su kayi gaba dayansu especially Abban nasu, karasawa yayi tare da rungume abban nasu, so tightly hannu abban yasa yana bubbuga bayansa yace “I really really missed u my guys” omar yace “i missed u too my daddy,’

Mg osman kam wurin su Bg abuhaisam ya karasa suka shiga rungume juna ana ta faman gaishe gaishe, bayan omar ya gama da abbansu ya koma yana rungume sauran,

gaba daya idon abbansu ya koma kan Rafayet wadda ko kallo bai ishe su ba, kawai bedroom dinsa yake kokarin tunkara,

Cikin sauri bg abuhaisam yace “kai ina zuwa……..? dakatar dashi abban yayi daga yi masa magana, kowa binsa da ido yayi,

Cikin sauri junaid ya shiga gabansa don ya riga sa isa sbd key din na hannunsa, can upstairs katafaren bedroom dinsa yake mai hade da palour, Aljannar duniya ce aka shimfida,

tunkan ya karaso Junaid ya bude masa, ya shige ciki, an kawata shi sosai sehrish ce zata fada mana ya haduwarsa yake, 😝

“Amma abba anya Rafayet bai fara shaye-shaye ba? Kalli yadda yabi ta gabanmu ko kallo babu, atlease ko kai ae ya kamata ya tsaya ya gaisar ko,”? abuhaisam ne yayi maganar ransa ya baci sosai,

Aunty azeema tace “kada ku damu indai rafayet ne dakansa zai fito,”

Zama su kayi a saman royal sofas din suna kara gaggaisawa da juna, hankalin Omar bai kwanta ba da yanayin abban nasu, kuma yasan duk akan babban yayan ne, ya kwalfa rai akansa yasaran daya shigo shi zai fara runguma amma sai yaga akasin hakan,

Aunty azmee ce ta shigo musu da abunsha itama da fara’a a fuskarta, tabi su tana musu sannu da zuwa, tare da mika musu abun sha,

Cikin rashi  kwarin jiki abban nasu yace “am really glad to see you, ina godiya ga Allah daya dawo mun daku lpy, amma nayi mamakin jin cewa tare da su Omar zaku zo ina ABUSUFYAN din?

Captain adams ne ya bashi amsa da cewa “daga can wurinshi muka wuce us sbd mu tafo atare,” jinjina kai abban nasu yayi tare da cewa “hakan yayi kyau,’

“Nima naji dadin ganin ku sosai, dalilin dayasa na tsaya nace dole saina ga ya’yana,’ murmushi su kayi jin abun da aunty azeema tace,

“Muna tayaku murnar dawowa cikin koshin lpy ni da yar uwata Amani,’ aunty babba ce tayi maganar, mg Osman yace “munji dadin ganin ku gaba daya, Allah yabar zumunci,” suka amsa da ameen,

Idon aunty azeema nakan abba wanda jikinsa ke kerma zuciyar ta motsa, jiki ba kwari ya mike tsaye tare da cewa “yakamata ku shiga ciki ku huta, zuwa anjima, nima bari naje ciki,’

Cikin sauri ya wuce room dinsa, da hanzari aunty azeema tabisa,

Yana shiga ciki gaban mirror ya tsaya, idonsa sunyi jawur ransa yayi mugun baci,

Shigowa tayi tana fadin “haba yaya Hussein meyasa ?, duk don sbd da abun da Rafayet yayi yasa ka shiga wannan halin,”

Juyowa yayi muryarsa na rawa tamkar zai yi kuka yace “meyasa zaimun haka ? gaba daya na kwallafa rai akansa, yaushe rabon dana sa shi a ido na? Amma  yadawo shine ko kallona baiyi ba? meyasa yake son azabtar dani ne da soyayyarsa kamar yadda mahaifiyarsa tayi mun !? yayi mgnr ne tamkar zaiyi kuka,

(Dama ko acikin gida dan banza yafi shiga rai 😂)

Cikin sanyin murya Aunty azeema tace “Am sorry yaya na, kamar yadda kke son ganinsa shima haka yakeson ganin ka, ni na tabbata akwai dalilin hakan, u shouldn’t worry ur seft abt him, ”

dagawo su kayi jin tura kopa, marshal omar ne ya shigo, yabiyo abbansu ne sbd shima ya lura da halin daya shiga,

Karasawa yayi inda suke yana cewa “daddy duk akan rafayet ne wannan ? Amma kasancewa sarai ba haka yake maka ba, rafayet bfr mu shiga jirgi yayi ma kansa allura, sbd aikin dayasha kasan yadda yake kamar enjine baya gajiya da aiki, allurar ce bata sake shi ba, just calm dowm ur mind dakansa zai zo ya same ka,in ya samu natsuwa”

ajiyar zuciya abban yasaki jin abunda omar ya sanar dashi, har yaji sanyi aransa,

Murmushi aunty azeema tasaki tare da cewa “ynx hankali ya kwanta ko, zamu iya komawa ciki ko ? Murmushi shima yasaki atare suka fito,

Yinin ranar gidan ya cika fam saboda zuwan SGR Da Marshal omar, mutane kamar kyankyasai sai bullowa suke yi abokanan arziki da kuma yan uwa, da sauransu hada su karare irinsu Hafsat bature yan shisshigi gayya soɗi, 😥

Duk wannan budurin da ake yi Babban yayan na can ciki a hakimce, yana sharar bacci cikin natsuwa, gashi kowa tambayarsa yake yi ina Babban yaya, Ina Sgr, ina rafayet amma shiru, ba wanda yayi attempting zuwa ya tashe shi saboda ba wanda ya isa ya tashe shi yana bacci, mutun yaji naushi alkur’an 😂

Dole fa sehrish ta fito aiki yayiwa azmee yawa, don haka tunkan ma azmeen ta buɗe ta, tayi gaggawar zura dogon wandonta, ta gyaggyara kanta da gashin bakinta,

kamar barauniya haka ta fito, tana tafiya cikin sanɗa ta tsorata da yawan mutanen da tagani, gasu nan bakake da farare kowa dai masha Allah,

Bama wanda ya lura da ita, direct kitchen ta wuce, abun ya bata mamaki ganin junaid tsaye aciki aunty azmee ta jera masa abunsha a tray cikin cups , alamar cewa hada shi ke taimaka mata wurin share ɗinsa wa bakin,  saukin kan junaid na bata mamaki he’a so Special 😍

Jikinsa na sanye da t shirt red colour sai trouser black colour, abun ba’a magana,

Sallama tayi ta shiga da murmushi a face dinsa ya dago yana kallonta, itama kawai saita tsinci kanta da sakar masa murmushi,

“Sannunku da aiki aunty azmee, am so sorry ban samu fitowa da wuri ba, because of sleepless night shiyasan ya,’ ta faɗi tana wasa da yatsun hannunta,

“Babu komai ae, ga Junaid nan yana tayani, tun da ynx kin fito sai mu fara shirin lunch, tunkan time ya kure mana,”

karasawa tayi gaban junaid tare da kai hannu ta rike tray din dake a hannunsa tace “Bari naje na kai musu,”

“A’a ki barshi kawai, zan kai” ya bata amsa cikin sanyin murya,

“A’a bai dace ace ɗan masu gida yana aikin daya dace ace ƴan aiki ke yi ba,”

ta faɗi tana kokarin janye tray din daga hannunsa,

“Ae ni nace zan iya just leave me to do it ba wani aiki bane mai wahala kawai kaiwa zanyi,”

“A’a ni dai kabarshi pls zan yi tunda nazo”

Zuba musu ido Aunty azmee tayi  baƙaramin burgeta su kayi ba,

“Kun ga ya isa haka, junaid ka bashi yakai musu kaje ciki nasan anata neman ka,”

kallon ta yayi suka haɗa ido, ya ɗan murguɗa mata baki kafin yabi ta side dinta ya wuce, ajiyar zuciya ta saki,

Idasa jera mata drinks din azmi tayi sannan ta juya tashiga ciki zuciyarta na bugawa tsoranta kada ta ci karo da Babban yayan nasu, duk da har ynz bata shaida shi ba,

Haka Sehrish ta shiga zarya cikin manyan bakin nan tana miƙa wa kowannansu abunsha, tun tana yi cikin daɗin rai har tafara fidda gumin gajiya, bayan ta kammala suka shiga aikace aikace a kitchen na preparing Lunch,

Lokaci guda kamshi ya gauraye ko’ina, girki na musamman suka shiga yi, abinci iri iri, namu dana kasashen waje, musamman sbd Babban yaya bakowane kalar abinci yake ci ba, sai an tabbatar da tsaftar maiyinsa da kuma amfaninsa a lafiyar jikin mutun,”

Dama azmee ce ke masu girkin sun saba da delicious dinta, sbd sun shaida kwarewarta, da kuma tsaftarta da lafiyar abincin ta,

tana lura da duk wani motsin sehrish wani murmushi data ga tana saki kamar gonar auduga, cikin nishaɗi take aikinta, zumudin son ganinsa take,

mutane sun rage sosai ya raga saura mu na cikin gida kawai, su marshal omar sun samu damar shiga cikin rooms dinsu domin hutawa,

Aunty babba da Amani sun shige cikin daki baki cike da gulma, tsaitsaye su kayi,

“Wai dama haka Babban yayan yake ? Ya ilahi aunty ya hada komai da nake bukata ajikin ɗa namiji meyasa tun farko baki haɗa ni dashi ba sai Abbas”?

Murmushi aunty babba tasaki kafin tace “idan kura na maganin zawo tafara yiwa kanta mana ! Kinsan irin haukan da nayi at the first day dana fara sashi a eyes ɗina, Allah sai da nayi regretting auran Ishaq, Rafayet shine irin namijin da nake kwaɗayin samu ! Amma kaddara ta riga fata,”

Jinjina kai Amani tayi tana kallon auntyn tata, acikin zuciyarta tana tunanin meyasa bata haɗa ta da babban yayan ba ko marshal omar, Amma take yi wa Hayaam tanadinsa, kodan ta kasance ita shakikiyarta ce?

*Annoucement ba posting a weekends sbd nasamu damar typing friday ma sai ina hutu amma ko za’a samu ba da wuri ba,”*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ

ﺭﺍﻓﻴﺖ

Story by *HAFSAT BATURE* 🌹♥️

~BossLady~

*page 61 to 62*

“Yanzu buri na shine, mu fara haɗa kudin zuwa wurin bokan nan, Baba Iblis domin gudanar da target ɗinmu,’ aunty babba ce ta katse ta da maganar,” .

Jiki a sanyaye Amani tace “yanzu me ake buƙata? Aunty babba tace “kuɗi nake so daga wurinki, nima kuma zan haɗa nawa don ziyartar wurinsa,

Murmushin takaici Amani tayi tare da cewa “Ita hayaam ɗin baza ta bada komai bane?

Ƴar dariya aunty babba tayi tare da cewa “amma dai kinsan hayaam da shegen maƙon tsiya, bazata bada ko sisi ba, kuɗin ta a gantali suke karewa, mu dai taimaka mata mu yayyenta, mu yi mata inyaso in tasamu shiga wurinsa ni nasa zata ru6anya mana abunda muka kashe,’

Baki a sake Amani take kallonta, oh ashe tasan ma cewa Hayaam ɗin nada kuɗi, ita bazata bada ba sai dai ita gantalalliya, waye zai amfana acikinsu,

“Yanzu nawa kke so kafin zuwa can ɗin”? Amani ta tambaya tana kallonta, cikin salon wayau Aunty babba tace “miliyan ɗaya da rabi nake so a wurinki da farko kafin abun ya nutsa,”

Wani irin kallo Amani take binta dashi, cikin rashin fahimta tace “aunty  million ɗaya da rabi fa? daga wuri na kuma , gold ɗina kke so na siyar ne?

girgiza kai Aunty babba tayi tare da cewa “to menene aciki ? Abbas ɗinnnan fa ya mutu akan ki, daga kin kashe masa murya buƙata zata biya,”

Ajiyar zuciya Amani tasaki kafi  tace “I will think about it,” murmushi aunty babba tasaki acikin zuciyarta tace “ki gama yi mun aikina, ke ma nakaiki ƙasa, ƴar kishiyar da ta azabtar da mahaifiyata, tasanya mahaifina tsanata, bazata ta6a zaba ƴar uwa awurina ba face maƙiyi ya !!!”

A fili kuma tace “yawwa my sister shiyasa nake sonki, duk cikin ƙanne na cos you’re so special,” murmushi Amani tasaki tana kallonta,

Wannan bokan da suke magana akansa Baba iblis, wani hatsabibin boka ne fasiƙin gaske, wanda ya sharaha, Asiri kala biyu yake yi, akwai Namijin asiri wanda ƙa’ida inzaiyi sa sai ya kwanta da namiji na tsawon kwana uku yana biyan buƙata, na biyu kuma Macen asiri, idan zaiyi wannan asirin dole sai an kawo masa matar Aure wadda bata ta6a haihuwa ba ya biya buƙatarsa na 3 days, shu’umi ne nagaske, muddin yayi asiri to fa sai yaci mutun, ko yayanene, in ba wani ikon na ubangiji ba,

Kuma a haka zakaga mata na rubibun zuwa wurinsa saboda neman abin duniya, wa’iyazubillah 😥wanda kowa zai mutu yabarshi !!!!

Around two ya farka, fito wa yayi yana saukowa down, duk sun hallara a palor ɗin suna fira, jin takon tafiyarsa yasa su ɗagowa suna kallonsa, bai bi takansu ba direct bedroom ɗin Abbansu ya shiga, saboda baigansa a cikinsu ba,

Abun da ya faru Abban nacen ɗakinsa yana zarya, shi dai burinsa Babban yaya ya kawo kansa har bedroom ɗinsa ya miƙa masa gaisuwa, if not he will not be calm,

safa da marwa yake ta faman yi, jin tura kopa yasa shi dakatawa ya juyo yana kallonsa, tsaye yake jikinsa sanye da jallabiya fara ƙafarsa cikin slippers, ya riƙe waist ɗinsa yana kallon Abban nasu,

Ƙinyi masa magana yayi yana jira yaga iya gudun ruwansa, shi kam kewar abban nasa yayi sosai, yama rasa wani irin tarba zaiyi masa,

Zuba mishi ido abba yayi ganin yana naɗe hannun jallabiyar dake jikinsa kamar wanda ke shirin yaƙi, yana ganin hakan ya gane mai zaiyi masa,

Cikin sauri yace “wlh kada kace zaka ɗauke ni Rafayet, kar ka kuskura Allah, ka matso saina nannaushe ka….” bai ƙarasa maganar ba, rafayet ɗin ya ƙarasa caraf ya ɗaga abban nasu a hannunsa kamar wani yaro,

dariya abban ya dinga yi yana faɗin “Ka sauke ni rafayet, kada ka balla ni fa, ynx in wani ya shigo ya ganni haka fa, ‘

“bazan bari hakan ta faru ba abbana” cikin wata irin sanyayyiyar murya mai daɗin gaske yayi maganar,

Ko nauyi baiji sai da ya tabbatar da cewa yaci ka abban nasu da farin ciki sannan ya sauke shi, sai faman ajiyar zuciya abban ke saki yana kallonsa, ƴar harara abban  ya watsa masa tare da cewa “duk ranar daka ƙara daukata haka, nima saina rama, kadaina ganinka da tsayi kamar fal waya , hakan bazai mun wuya ba,

Matsawa babban yaya yayi gaf da abbansu yace”bismillah” yadda yayi masa tamkar zai rufe sa da duka, hannu abban yasa ya janyo chair ɗin dake gaban dressing mirrior , ya daddage ya hau samanta ya miƙe tsaye, yadda tsayinsa zai fi na Rafayet ɗin sosai, sbd yafi so in zaiyi masa magana yadinga ganin tsakiyar kansa, 😂

“Hmmm kayi kewata kuwa? Ni bana gane wa kullum fuska atamke ba fara’a,’ abbansu ne yayi maganar yana kallonsa daga saman chair ɗin dayake tsaye,

“Abba i really missed you just feels like to swallow you,’ yayi maganar yana kallonsa,

Shi kam abban sai murna yake yi, ba don komai ba sai don ganinsa, “amma dai zaka jima anan ko ? Bana so kana jimawa bakazo naganka ba,”

Lumshe idonsa yyi tare da buɗesu a hankali yace”duk yadda kke so haka za’ayi abba,” murmushi abban yasaki, abun da ke ɗaure masa kai har ynx babu fara’a a fuskarsa ba alamar murmushi ko dariya, amma sanin cewa haka mood ɗinsa yake ne yasa baiji komai ba,

“Yakamata mu fita, ku gaisa da aunty azeema da sauran ƴan uwa, kuma nasan kana buƙatar abunda zaka sawa cikin ka ko? Ya tambaya yana kallonsa,

“No am not starve dad, and i will stay here in your bedroom, duk mai son gani na yazo nan ya same ni,”

yana gama faɗan hakan ya wuce saman bed ɗin abban nasu ya kwanta a hakimce,

Saukowa abban yayi yana murmushi aransa yace “wannan shine ainihin jinin Alexendra (alekzendira)”

Fita abban nasu yayi fuska asake duk sun hallara a main palour ɗin ana ta fira,

“Abba ina Babban yayan yake, nagansa ya wuce part ɗinka, nayi tunanin zan ganku atare ne,” aunty azeema ce tayi masa wannan maganar,

“You knew him well, yace duk mai son ganinsa ya same shi acan room ɗina,”  jinjina kai su kayi, aunty azeema tace “to bari muje mai son ɗan tsuntsu ae shi ke binshi da jifa,” dariya su kayi gaba ɗayansu, tashi tayi bg abuhaisam ma yabi ta tare da kanal yusif, da sauran banda su fawan,

Sun gaisa dashi sosai, anyi kewar juna asake yayi magana da kowa, amma fa face ɗin nan tashi kamar an ɗinke ta saboda rashin fara’a,

Bayan sun fito ne abba ya kora su fawan da twins wadanda suka samu damar fito wa, munafukan hada sa jallabiya brown colour hannunsa riƙe da cazbaha,

gaba ɗaya suka tafi fawan, Ayaan da jahan dama sune basu je ba, tsayawa su kayi abakin door ɗin suka kasa shiga sbd shakkarsa,

“Enter first pls fawan,’ jahaan ne yace ma fawan, harararsa fawan yayi tare da cewa “kai ka fara shiga mana, ayaan yace “dan Allah fawan kafara shiga we’ll follow ur back pls, kowa ya gaza shiga sai faman jayayya suke yi abakin kopan ɗakin,

Duk wannan surutun da suke yi kaf a kunnan babban yayan nasu yana jinsu, sarai yasan cewa shaggun ne, ƙannensa ba,

“Yawwa Alhamdulillah ga junaid nan shikenan ma, zo ka fara shiga,’ ayaan ne  yyi mgna with smile on his face,

Binsu da kallo junaid yyi wanda ya ƙaraso shima zuwansa kenan don ya miƙa masa gaisuwa don ɗazu yaga mood ɗinsa basu samu damar mgn ba bayan ya bude masa ƙopa, shima abban ne yasanar dashi cewa yaje ya same shi a room ɗinsa,

“Baku da gaskiya Allah, yanzu big bro ɗin namu ne kke tsoran zuwa wurinsa, maimakon kuyi kewarsa sosai, sai faman la6e la6e ku ke…..’

Buge masa baki fawan yayi tare da cewa “parrot meye naka aciki, mu dallah zo ka fara shiga,”

Shigewa gaba Junaid yayi suka bi bayansu, sai faman ƴan kame kame suke yi, sai kace ba jininsu bane shi,

Cikin natsuwa suka ƙarasa har sun naɗe riga zasu zauna a 3 seater ɗin dake facing bed ɗin abban nasu, ya buɗe idonsa tare da yi musu wani kallo jiki na rawa suka dawo ƙasa kowa ya lankwashe ƙafa yayi zaman cin tuwo,

Haɗa baki su kayi wurin cewa “Sannu da zuwa babban yayanmu ya gajiyar tafiya,”?

Suka tambaya suna kallonsa, shiru yayi baice komai ba, zuba musu ido yayi yana kallonsu, nan fa suka soma ƴan sunne-sunnen kai,

“Is that how your mom taught u how to greet each other,!? (Haka mahaifiyarku ta koya muku yadda zaku gaisar da juna?

Ya tambaya ayayin da yake tashi zaune daga kwanciyar da yayi,

Cikin sauri suka miƙe zumbur, junaid ne ya fara ƙarasa inda yake zaune a side bed ɗin, hugging ɗinsa yayi tare da manna masa kiss a side face ɗinsa, lumshe idonsa yayi tare da jinjina kai,

fawan ma ya karasa yayi masa kamar yadda junaid yayi, haka su ayaan da jahaan ma duk suka je suka rungumesa tare da manna masa kiss,

Sannan suka koma daf dashi daga ƙasa saman carpet suna naɗe ƙafa suna jiran jin me zaice,’

Shi dai junaid sai faman murmushi yake don murna, ba don komai ba sai don ya gama lissafin kuɗaɗen da zai samu a wurinsa, don yaci alwashin in ya amshi kuɗi wurin big bro ɗin nasu, sai ya yi wa Sehrish ɗinsa Siyayya saboda yasan tana buƙatar abubuwa da dama, 😥

“Listening to me !! Bana so ɗaya daga cikin ku yajamin abun magana a family ɗin mu har na koma US , just i don’t wanna hear anyone saying this word again ƴa’ƴan fatima basu da kunya, if that happen you will see the trouble,’

Jinjina kai su kayi tare da cewa “insha Allah babban yayanmu hakan bazai faru ba, zamu kiyaye,’

“You can leave,’ ya basu umarni tashi su kayi jiki ba ƙwari suka fice, banda junaid wanda ya zauna yana ta faman kallonsa,”

“What do you want from me junaid”?.

Ya tambaya yana kallonsa, murmushi junaid yasaki cikin  shagwabar nan tasa yace “akwai magana babban yaya, amma in ka huta zuwa gobe,”

wani irin kallo babban yayan yake masa, yana son yaron sosai, duk duniya in dai har za’a samu lagwansa toh ata6a junaid nan zakaga jijiyoyin wuya, yana ji dashi more than u think,

“Ya jikin ka? kana shan maganinka akai akai,”? ya tambaya yana kallonsa,

Junaid yace “yeah am getting well, kawai nayi missing ɗinka sosai,”

“Wow kayi missing ɗina kodai kuɗi na kayi missing, which one i have to know?

Dariya junaid yayi sosai, wato ya karto sa, tsagaita dariyar yayi kafin yace “a’a kafi mun komai mahimmanci arayuwata, kai nayi missing sosai,”

“I miss u too junaid, sbd kai na ɗau hutu sbd inaso nabaka kulawa ta musamman game da athma ɗinka,”

Cikin jin daɗi suke firar tasu, abun gwanin ban sha’awa, sai naji kamar na tsoma baki, amma nasan naushi zansha, 😂

duk yinin ranar sehrish batasa ɗan tahalikin nan a idonta ba, saboda bai fito ba balle tagansa, in ma ya fito ɗin bata cin sa’a duk zumuɗin nan nata,

A ranar wuraren ƙarfe 4 Aunty babba ta koma kaduna gidanta, bisa umarnin mijinta, yayin da Amani ma ta koma gidanta cike da zullumin abunda auntyn tata ta kitsa mata zasu aitawar,

tsawon kwana 3 kennan Allah bai haɗa ta da Babban yayan ba, sai dai marshal omar da take gani da sauran da suka dawo, a yau aunty azeema ta koma lagos shima bg abuhaisam ya koma Jos inda yake da zama,

Tara su abban nasu yayi a main palour ɗin, su 3 banda babban yayan saboda yasan maganar bata shafeshi ba, maganar zumunci ne da family ɗinsa, sam basa ga maciji da Ammi, jarababbiyar tsohuwar bata son farar fata, jinsi indai ya wuce hausa fulani ! tom sun raba jaha, har yau bata shiri da ƴa’ƴan fatima, daga abu ya faru sai tace “halan ƴa’ƴan fatima ne, ae ƴa’ƴan fatima basu da kunya, jinsin fitsararru masu jan kunne,” wannan kalmar babban yayansu ya tsane ta, bai mata da wasa in suka haɗu, gashi shegen tsoransa take ji , saboda kwayar idonsa da take blue, muddin SGR na gari to bata zuwa Abuja,’

duka suna zaune saman 3 seater wadda ke facing abbansu dake zaune yana kallonsu, gyaran murya yayi tare da cewa “Alhamdulillah nayi murnar dawowarku cikin koshin lpy , kun jima bakwa ƙasar, tun da Allah yasa kun dawo, sai ku shirya ku shiga dangi, asada zumunci !

Mg Osman ne ya fara magana “haka ya dace abba, ni inaji zan fara zuwa damaturu ne wurin modibbo da sauran relatives ɗinmu, kafin na dawo na ziyarci sauran,”

Abban yace “hakan yayi kyau kai fa Captain ? gyara zama yayi tare da cewa “ni zan wuce kaduna ne wurin yaya ishaq daga nan zan wuce zariya ne, wurin dangi,

“Hakan yayi kyau, naji daɗi sosai amma fa yakamata asamu wanda zai je katsina wurin goggonku saboda kullum mu kayi waya sai ta tambaye ni ina, ƴa’ƴanta musamman kai Omar tafi tambayarka,”

ɗan kayataccen murmushi Omar yasaki kafin yace *I will think about it abba*, ”

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ

ﺭﺍﻓﻴﺖ💫🔥

*Mallakin*

🌹 *HAFSAT BATURE MOHD

~BossLady~🔥

*63 to 64*

Cikin jin daɗi suka ci gaba da firarsu, sai da suka washe gajiyarsu na tsawon one week sannan kowa ya shirya tafiya, marshal omar tare da Captain suka je kaduna, daga nan zasu wuce zari’a a tare, daga nan Omar ya shirya ziyartar ƙanwar amminsu da suke kira da Goggon katsina 🌹

Yau da sassafe suna kitchen suna making breakfast, azmee na tsaye agaban gas tana making suya, yayin da sehrish ke wanke kayan lambu agaban kitchen sink, ta kunna tap sai ruwa ke zuba tana wanke wa, a kasalance take yin komai, gaba ɗaya hankalinta, nakan yadda zata haɗuwa da *BABBAN YAYA* she’s so earger to see him, cos zuciyarta azalzalarta take akansa, gashi har yau batagansa ba, gashi acikin gidan amma Har yau Allah bai bata damar ganinsa ba, a ranar da suka dawo saboda ɗauki ko bacci ba tayi ba, da tunanin yadda zasu hadu ta kwana,

Junaid ne ya shiga da kitchen ɗin da sallama, jikinsa na sanye da sleeping dress ne masu kyan gaske pink colour abun ba’a magana,

Sai xabga murmushi yake saboda sehrish daya hango, ita kam hankalin ta baya atare da ita, ta kura wa cabbage ɗin dake hannunta ido sai shafa shi take yi da sunan wanke wa,

Azmee ce tagansa ya kura wa sehrish ido, murmushi tasaki aranta tace ”

*ROMEO kenan shugaban ƴan soyayya* (Romiyo)

Kafin tayi gyaran murya tace “junaid lpy kuwa ? Do u need something?

firgit ya dawo da idonsa kan azmee wit smile on his face, yace “am…dama…..Big bro ne ke buƙatar Fresh fruits akai masa a part ɗinsa immediatly right now,’

Sunan sa ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, sai lokacin ta ɗago tama lura da junaid daya shigo, duk maganar da suke yi bata tsinci komai ba, sai da akai mentioning sunan Babban yaya,’

“Shikenan ynx zan sa sehrish ta kai masa,” sai da junaid ya sake kallon sehrish itama a lkcn idonta na akansa sannan yace “Okey” ya juya ya fice, yaji sanyi aransa daya sata a idonsa,

Zuru tayi tana kallon azmee, murmushi azmee tayi tare da cewa “Finally sehrish wants meet Babban yaya today insha Allah,”

Tsananin farin ciki ne ya bayyana a fine face ɗinta, murya na rawa tace “aunty azmee pls, ni zan kai masa, ni wlh tsoron haɗuwa nake da shi,”

ta faɗi tana sunnar da kai, ƴar dariya azmee tayi tana faɗin “whether u like it or not, u don’t Ave choice, aje akaiwa big bro fruit, salon kiyi hauka, kisha mari,”

Shirya mata tayi acikin wani ƙayataccen tray tare da knife ta yankawa ta hada mata,

Hannunta har kerma yake yi wurin amsa, sai faman mazurai take yi, har takusa fita tajuyo jiki a mace tace “Aunty azmee i don’t know  Where to find his bedroom,’ dariya azmee tayi don ta lura cewa sehrish fa a tsorace take da babban yaya, ga zumuɗin son ganinsa ga tsoransa kuwa,

” a uptairs ne, part ɗinsa ya ke in ki ka miƙa gaba da room din junaid ba nisa,”

jin jina kai sehrish tayi, tana tafiya zuciyarta na bugu, Just feeling nervous ta riga ta tsorata dashi, ta sama kanta tsoransa since bfr she saws him,

a hankali take taka steps din benen, hannunta riƙe da tray din, time din da ta isa neman part dinsa ta shiga yi, sai da ta wuce room din junaid daga gaba can, ta hango wata haɗaɗɗiyar kofa, tana gani ranta ya bata cewa tabbas nan ne,

a hankali ta yi tura door din ta shiga ciki tana wurwurga ido, lokaci guda ta rikice da ganin haɗuwarsa, wato aljannar duniya ce aka zuba aciki, parlor ne hamshaƙin gaske yaji hadaɗɗun furnitures komai na cikinsa Golden color ne ,

ko’ina sehrish ta wurga ido kyalli kawai take gani saboda haɗuwarsa, ga wasu windows na glass masu ɗaukar ido, wasu haɗaɗɗun royal sofa ne aciki  L shape, ga jerin pillows asaman su,

bin ceilling ɗin tayi da kallo wani kwan fitila ne na zamani (chandelier) mai girman gaske sai kyalli yake kamar zai faɗo mata akai haka take ji, mutun zai iya 6ata 15 mins yana kallonsa Don kyau , daga ƙasa kuwa wasu kayattun floor lamps ne acikin glass suke masu bama wurin haske,

mayar da idonta tayi, a saman ƙayataccen table ɗin dake a middle ɗin kujerun Container ce mai ɗauke da furanni kyawawan gaske masu tsayi sai ɗaujar ido suke,

Shiru tayi jugun sanyin a.c ne ke ta faman karaɗe ko’ina, tambayar kanta take yi ko nawa aka kashe wurin ƙawata wurin nan?

Wuce wa tayi ciki a hankali mamaki bai ƙare mata ba sai da ta hango wata ƙofar acikin palourn, shiga ciki tayi to fa, zamu tsaya bata baki ne, Bedroom ne ƙayataccen gaske, baki sake sehrish ke bin komai da kallo kamar a mafarki take ganin lamarin, ƙamshin ne kawai ke shiga hancin ta, ganin ba alamun mutun ne yasa ta juya wa domin ta fice,

jin alamar an buɗe kopan bathroom yasa ta juyawa taga wanene ne ?  Karaf idonta suka sauka a kansa sbd tsabar firgita tasaki tray ɗin hannunta mai ɗauke da kayan marmarin suka watse a ƙasa, zaro ido tayi waje saboda tsabagen tsoro a ruɗe take,

jikinsa na sanye da bathrobe (rigar wanka) fara mai laushin gaske, wadda ta tsaya masa dai dai guiwarsa, ya ɗaure igiyoyinta guda biyu a tsakiyar stomach ɗinsa, daga sama kana ganin wide chest ɗinsa,

Hannunsa na ruƙe da hand towel yana matse doguwar suman kansa a natse, sam bai juyo ya kalle ta ba, amma tabbas ransa ya basa cewa wani ya shigo kuma anyi masa 6arin fruits a room ɗinsa tunda ga Apples nan guda uku ƙasan ƙafafunsa sun gangaro, ya jima yana mamakin wani isasshen ne wannan mai walkin sa, 😡

Ita kam sehrish da ke tsaye kamar gunki tarasa makama, tsantsar tsoro ne a fuskanta, dukkan ilahirin jikinta rawa yake yi sbd tsoran hukuncin da zata fuskanta, tabbas ranta ya gama yadda da cewa wannan shine Big Bro (Babban yaya)

lips ɗintaa sai rawa suke yi hakika ta tsorata da ganin ƙirar ƙarfinsa, wannan yayiwa mutun naushi ɗaya sai dai uwarsa ta haifi wani,

So take ta duka ta kwashe fruits ɗin da ta zubar masa a ƙasa, amma babban tashin hankalinta yadda zata ɗauko 3 apples ɗinnan da suka gangara wurin ƙafarsa 😳😳😳😳

In ka ga fuskarta sai ka tausaya mata, miyau kawai take haɗiya kut kut, yayinda zuciyarta ke buga wa da sauti mai ƙarfi,

Har time ɗin babban yayan bai juyo ba, yana tsaye yana matse sumarsa da towel ɗin hannunsa,

gaban dressing mirrow ya ƙarasa ya tsaya cak, ɗagowa yayi da sexy blue eyes ɗinsa ta cikin mirror yana kallon yaron dake tsaye jiki na kerma,

Allah yaso bata ɗago ta kalli cikin mirror ɗin ba, da tabbas sai tayi fitsari a wando, in tayi arba da kwayar idonsa me rikitarwa,

gaba ɗaya komai ya tsaya cak, jiki ba ƙwari sehrish ta duƙa a hankali tana tattare abunda ta zubar, cikin gaggawa take tsince bananar da ta zubar da tufan da lemun 6awo sai tsintarsu take tana jerawa a tray ɗin, zufa na ɗiga a face ɗinta sunan Allah kawai take ambato,

Abunda bata sani ba, jira yake kawai ta ƙaraso zata ɗauki  apples ɗin dake wurin ƙafarsa yayi mata Kyakkyawan riƙo, itama ba hauka take ba a hankali take bin tufan dake wurin ƙafarsa da kallo so take takai hannu ta ɗauka, amma zuciyarta nace mata “Karki kuskura”

hawaye har sun soma wanko mata a fuska, cije wa tayi ta daure zata ɗauka har takai hannu, Junaid ya turo door ɗin yana faɗin “Am back babban yayanmu,”

Jinsa yasa tasaki ajiyar zuciya, shima ganin sehrish ga kuma halin da take ciki yasa shi ƙarasawa da sauri yana faɗin “Let me help”

.shiya sa hannu ya tattaro mata apples ɗin, yasa mata a tray ɗin yana kallonta duk ta firgice,

Cikin rawar murya tace “Nasa ne aunty azmee tace na kawo masa,”

Ƙarba junaid ya yi tare da cewa “ok ki je kawai,”

tana miƙa masa ko waiwaye batayi ba, ta fice jiki na rawa wato tagama rikice wa, wai a hakan ma bata ga fuskarsa da kyau ba,

Kamar wata zararriya haka ta koma kitchen din, duk tabi ta ruɗe she was amazed by his beauty,

Kallo guda azmee tayi mata tagane cewa ba lafiya, cikin mamaki tace “Sehrish lafiyarki kuwa”? da budar bakinta sai cewa tayi “Babban yaya aunty azmee,’  wuce wa tayi gaban kitchen sink ɗin in da tabar vegetables din da take wanke wa,

Bin ta da kallo azmee tayi tana sakin murmushi aranta tace “kaɗan kenan,”

“Sehrish ni zan je nafara jere breakfast din a dining pls ki kular mun da farfesun dana ɗaura,sannan na manta bansanya salt ba ki zuba mun,”

A cikin wasu haɗaɗɗun food warmers ta shirya su, ta jerasu a saman faffaɗan tray ta fice don tafara jerawa,

sehrish sam bata farimtar komai still she’s out of sense , ita dai taji kamar tace ta zuba gishiri,

Cikin rashin sani tasanya Hannu ta ɗauki Ledar detergent, bil’haƙki da gaske taje  ta bude murfin sauce pot (tukunyar miya)  dake a saman gas, ta zazzage sa duka kaf Aciki , ta kuma ɗauki turner tana motsawa, gaba ɗaya hankalinta nakan surar babban yaya da ta gani, ta mutukar jan hankalinta,

bakomai idonta ke hasko mata ba fa ce wannan doguwar sumar kan tasa mai dan bala’in kyau, 😳😳😳

Shigowa azmee tayi tana fadin “kinsa mun gishirin aciki “? jin muryar azmee yasa ta dawo daga tunanin da take yi, sai lkcn ta ankara da ledar detergent ɗin da ta zazzage acikin farfesun wadda ke a ƙasa,  a razane ta dafa ƙirji tana fadin “Nashiga ukuna, wayyo Allah wlh omo na zuba maimakon gishirin !!!?

Sakin baki azmee tayi tana kallonta, jinjina kai kawai take yi, tana jinjina wa lamarin, sehrish kuwa ido yayi luhu luhu duk ta kame kanta,

“Sannu kin ji ? Azmee ta fadi tana kallonta, sunnar da kai ƙasa tayi tana fadin “am so sorry aunty azmee sharrin shaidan ne ba yin kaina bane,’

Azmee tace “sharrin shaiɗan kuma ko dai sharrin babban yaya wanne ciki? cije le6enta kawai take yi itama tarasa meke damunta,

“U did a good job sehrish, u need to ave some rest, aikin ki ya ƙare, sai da anjima in kin dawo hayyacin ki,’ cikin sanyin murya tace “dan Allah aunty azmee kiyi hkr, nasan fushi ki kayi dani, I made a big mistake am so sorry, bazan kara ba”

Murmushi azmee tayi tace “sam ni baki 6atamin rai naba, hasalima tausayin ki nake ji, Je ki huta,’

Kama hanya sehrish tayi ta fice daga kitchen ɗin tana mamakin haukanta na yau  akan big bro, (nace ba saura na anjima ko na gobe) 😂

Sehrish bata dawo cikin hayyacinta ba sai da tayo wanka, tasamu natsuwa sosai, a gefen gadonta tazauna tana ta faman zabga murmushi, farat ɗaya taji wani irin yanayi atare da ita, har takai ga ko runtse ido tayi shi take gani sanye cikin bathrobe, a tunaninta jinsa yafi ganinsa ashe ganinsa yafi jinsa nesa ba kusa ba, hannu tasanya ta janyo fillow ta kwantar da jikinta a saman gadon, idonta na kallon ceilling,

*tabbas shiɗin burin kowace ƴa mace ne 💋

_Alƙalamin_  *HAFSAT BATURE MOHD*

~BossLasy~ 🔥💋

*Page 65*

*Baki washe an samu dinner 😂*

………………..*………………………

~Husanna & Jahad~

Ƙanƙame suke da junansu A cikin Cell ɗin, cikin mawuyacin hali, sun rame sunyi baƙi, haƙiƙa sun ga rayuwa, yanzu an kammala shirya komai na shigar dasu kotu domin gudanar da shari’a A next week,

ƙarar bude cell ɗin suka ji, da sauri suka ɗago, wata jami’a ce sanye cikin kakin ƴan sanda, mai riƙe da muƙamin inspector,

su biyu ne ita da wani jami’i amma ita kaɗai ta shigo ciki, zuƙunnawa tayi gabansu tana binsu da kallo fukarta cike da tausayinsu,

a tsorace suke kallonta, baka ce babu annuri a fuskarta sai manyan tsaguna a fuskarta na rumawa,

“Idan zaku bani haɗin kai zan taimake ku, ku fita daga haɗarin da kuke ciki,” ta faɗi tana kallonsu

Cikin sanyin murya Jahad tace “komai kike so zamuyi dan Allah ki taimake mu mubar wurin nan, mun gaji, bamu ji daɗin zama anan, kuma bamu so akwai mu kotu a yanke mana hukuncin kisa,” ta kare maganar idonta cike tab da kwallo,

Murmushi inspector eesha tayi kafin tace “tabbas zaku fita, amma bisa sharaɗin in muje kotu zaku amsa cewa kune ku kayi kisan batare da jayayya ba !!!?

Zaro ido jahad tayi tana fadin “sabod me ? taya zamu ansa hakan bayan bamu ne muka kashe ta ba “?

shiru inspector ɗin tayi tana kallonta, da alama yarinyar zatayi taurin kai,

Husanna dake kanƙame gefen jahad tace “Ni na amince zan ce ni nasanya mata shinkafar 6era taci ta mutu, indai zaki fidda mu dan Allah,”

“Husanna !!! kada ki kuskura ki amince wlh ni banyarda ba wlh,”

Jahad ce tayi maganar tana kallon fuskar jami’ar, wadda tabisu da ido,

“Wlh ni na amince dan Allah aunty ki fidda mu, zance ni nayi kisan indai zaki cika alƙawari,

hannu jahad tasa ta rufe mata baki daƙarfi tana cewa “amma sai yau na tabbatar baki da hankali husanna wlh bazan bari hakan ta faru ba sbd we’re not guilty, ‘

ganin sun soma ƙoƙarin ɗaga murya yasa ta dakatar dasu da cewa “You have to trust me, ni turo ni akayi na taimake ku kuma dole sai ta wannan hanyar,

Cikin mamaki Jahad tace “wa”?

Murmushi tayi kafin tace “daga wurin ƴar uwarku SEHRISH,”

Jin ta ambaci sunan sehrish yasa su gyara zama suna masu tsananin mamaki,  wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskarsu,

“Dan Allah dagaske ne sehrish zata taimake mu ? dama tasan halin da muke ciki ne, Allah ne ya amshi addu’ar mu zamu fita daga wannan uƙubar,”

Jahad ce tayi maganar da tsantsar farin ciki aranta, husanna kam sam tagaza rufe bakinta murya na rawa tace “Dama nasani Sehrish bazata bari a cutar damu ba, nasan tana son mu sosai, dan Allah a fiddamu daga nan akaimu wurin ƴar uwarmu,”

Kallansu kawai inspector ɗin take yi, wani irin kallo na shu’umanci ganin sun miƙa wuya yasa tace “kun amince zaku amsa cewa kune ku kayi kisan!!”?

Atare suka haɗa baki wurin cewa ehh mun amince,’

ƴar dariya tayi kafin ta fita daga cell ɗin, a  harabar police station ɗin ta tsaya jikin motarta, hannu tasa a aljihun wandonta ta ɗauko wayarta ƴar nokia, daddanawa tayi kafin ta kara a kunnanta tare da cewa  “Yaran fa sun amince, zasu amsa cewa sune su kayi kisan, yaushe zanji alert na cikon kuɗi na ?

Natsuwa tayi tana sauraron mutumin da ta kira a waya, wanda ba’a bamu damar jin me yake cewa ba,

Dariya inspector ɗin tayi kafin tace “nima fa shu’uma ce kamar kai, muddin banji alert ba na cikon kuɗi na, ina mai tabbatar maka da cewa, zansa su fasa amsa laifin,’

Ta jima tana wayar kafin ta kashe wayar tana tikar dariya (to fa)

A can cikin cell ɗin kuwa, wani tunani ne yazo ma Jahad ita mai hankalin taya akai ƴar sandar nan tasan sunan sehrish !!!!? Kuma taya akai Sehrsh tasan halin da suke ciki ? Tabbas akwai makirci acikin lamarin,

Miƙewa tsaye tayi tana zagaye, can dai tace “husanna so ake mu amsa laifin kisan nan don akashe mu, ba don ataimake mu ba !!

jiki a mace husanna tace “jahad ni nagaji da rayuwarnan, so nake na mutu kuma yanzun nan,!!

hankali atashe jahad tayi hanzarin komawa kusa da ita tazauna tare da dafa shoulder ɗinta tace “Husanna bakya jin daɗi ne,”

“Eh mutuwa zanyi yanzun nan,”

ta bata amsa, bin ta da kallo jahad tayi a tsorace ganin , jini ya soma biyowa ta hancinta, daga magana sai abu ya tabbata, kafin ta ankare husanna ta zube ƙasa, ba numfashi,

Wata irin razananniyar ƙara Jahad tasaki tare da faɗin “Innalallahi wa’inna ilaihirraji’una !!! Nashiga uku !!Wayyo Allah na Husanna ta mutu………..

da gudu police ɗin dake waje suka shigo ciki, sun gigita da ganin halin da yarinyar take ciki tamkar ba numfashi, kuma sun son tabbas ta mutu a hannunsu sai anji dalili,

hakan yasa aka kira women police  guda biyu suka ɗauki husanna, hada jahad aka tafi da su cikin mota domin kaita asibiti,

Sai faman kuka Jahad take kamar ranta zai fita saboda tana ji aranta cewa Husanna fa wannan karon dakyar zata rayu,

Ganinsu da ƴan sanda yasa, reception nurses saurin karbarsu, aka shiga da husanna ciki a (A&E) accident and emergency ward aka kwantar da ita,

nan da nan likitoci suka shiga duba ta, Jahad na zaune a saman waiting seats dake daga waje Ward din, tasha kuka ido sunyi jawur,

Ga ƴan sanda zagaye da su,kamar wasu 6arayi, addu’o’i kawai take karantowa abakinta , tana roƙon Allah yasa Husanna karta rasa ranta, tsananin ƙunci ne a ranta, kuma tasawa ranta cewa muddun *Husanna* ta mutu itama sai ta kashe kanta ❗‼⁉, 😭😭😭

……………….SEHRISH…………………………

Oya drop your comment after u finished reading i wll be waiting for u 😎

*🌹HAFSAT BATURE MOHD BOSS LADY🌹*

*page 65 to 67*

_Sannan daga numbers na pages ɗin littafin nan sun kai 80 zasu canza zuwa Episode one1_

………Sehrish………………

gaba ɗayansu sun hallara, kowannan su ya sami gurbi a dining chairs ɗin, azmee ce ke ta faman ɗawainiya yin saving ɗinsu, saboda sehrish na can cikin yanayi

_kowannan su ya hallara a saman dining chairs ɗin, kwansu da kwarkwatarsu,

Yau suna gida ba fita aiki, a bisa umarnin Babban yayansu,

_Duk sunyi dress cikin Jallabiya, dama yana ɗaya daga cikin favourite dress ɗin su, basu cika son kaya masu nauyi ba_

_azmee ce ke saving ɗinsu, kowa tana zuba masa abunda yake so_

_duk sun natsu suna ci, hannu ayan yasa acikin aljihun jallabiyarsa ya zaro wayarsa dialing ɗinta ya shiga yi Jahan ya tura wa saƙo kamar haka_

_”ya maganar hotel room ɗin? Kayi mana booking?_

Jin ƙara shigowar message a wayarsa dake ajiye gefen plate ɗin abincinsa yasa shi duba ya karanta, ɗan murmushi yayi kafin ya bashi amsa da cewa  _”Eh yaushe zamu fara zuwa don a matse nake wlh_

duba wa Ayaan yayi ya basa reply shima,

_”ko yau ka ce am ready to do it, am so horny dear kamar nayi hauka_😖

duba wa jahan yayi wit smile on his face ya tura masa reply shima, _” u must be horny dear, 2 days ba testing ɗin *Ak47* dole Mu shiga yana yi_

Before Ayaan ya bashi amsa muryar fawan ta katse su da cewa

*Ga Babban yaya nan kowa ya shiga taitayinsa*

Cikin sauri kowannan su ya mayar da wayarsa cikin aljihunsa, don ya hana ana cin abinci ana danna waya,

Atare da junaid suke saukowa ɗga stairs ɗin, farar shirt ce ajkinsa ta ɗame sa, mai dogon hannu , daga ƙasa kuwa shorts ne launin ash, gaba ɗya surar jikinsa a bayyane take sboda duk yadda Sgr zai sa sutura sai halittun jikinsa sun fito muraran,ba abunda ke 6oyewa nadaga kyakkyawar surarsu, hakan ba ƙaramin tayar musu da hankali yake ba especially abbansu yayi fama dashi saboda bakin mutane tun da dai abu tubarkalla, Bai jin kunyar shiga ko wata iri ce da zata nuna tsiricinsa, bai sa suturar kirki sai in takama yafi son yasa sexy underwears sune best dres nasa, hada ƙarin hakan yasa ake kai masa farmaki,

tun da azmee ta ɗago so ɗaya batasake ɗagowa ta kalle sa, sbd tshn hankali, wannan kallonsa ma a wurin mace zai iya zama haramun,

Kujera ya ja ya zauna yana facing kowannansu, shima junaid ya zauna yana ta faman zabga murmushi,

cikin sauri azmee takai hannu zata zari plate ta zuba masa abun sawa abaki , amma abun mamaki sai fawan ya riga ta kai hannu ya ɗau plate ɗin jiki na rawa, ya buɗe warmer ɗin dake ɗauke da farfesun naman shanu, yasa saving spoon ya shake masa plate ya ajiye masa a gabansa, sanna ya haɗa masa da kakkauran tea a gefe,

Ƙiris ya rage azmee ta fashe da dariya, wannan fadancin na fawan ya bata mamaki,

Bin su ya ke da kallo ɗaya bayan ɗaya, bayan sun gaishe shi, kowannansu ya shiga taitayinsa, don sun sani sarai bayason hayani ko kɗan, hakan yasa suka rage ƙarar spoon ɗin da hannunsa daga wannan sautin kwas kwas da ya ke yi,

Hannun sa ya miƙa acinkin wani empty bowl, azmee tasanya masa ruwa ya wanke, kafin ya tsoma hanun acikin naman, tsoka ya ɗauke ya jefa a bakinsa, a hankali yake taunarta, yana ci yana binsu da kallo One by one,

Ƙasa ƙsa da murya irfan yayi shi dake kusa da jabir yce “wannan kallon da babban yaya yake yi, bana lpy bane, duk ƴan ciki na sun kaɗa , jabir ya ɗauki cup of tea ɗin dake front ɗinsa ya kare fuskarsa dashi kamr zaisha, sannan yace “kai kenan ma, wlh jiki na kamar na mai zazza6i don fargabansa,’

Khadeel dake sauraronsu ya ce”jikin wasu na ƙaiƙayi da alama,’

Sun gane me ya kenufi cikin sauri suka ja baki su kayi shiru,

Kowa tsit kamar mutuwa ta gifta, sautin ƙarar cokulan da hannunsu twins yake yi ne (kwas kwas) ya cika masa kunne, ɗagowa yyi ya aza eye balls ɗinsa akansu, zo ka ga tashin hankali, bakomai ya haddasa hakan ba, face kermar da jikinsu ke yi,

mirya na rawa ayaan ya ce “mun shiga uku, idon babban yaya akan mu jahan,’

“menene” ya tambaya a ɗan firgice suka ɗago suna  Kallansa, ya sake cewa “are u not feeling well ? ganin yadda jikinsu ya ke rawa,

Ido luhu luhu Jahan yace” Ba mu jin daɗi ne, ni da ayaan, ”

ɗgowa yusif yyi yana kallansu, jin zasu ja masa bala’e, tun Kan big bro yace wani abu, yusif yayi hnzarin cewa “but why u didnt tel me about ur sick ? ya tambya yana kallansu,

cikin sauri ayan yace “dama tun jiya da dare ne,

“Atlease u should inform me abt ursick, ko ƙarfe nawa ne zan duba ku ae,? shiru su kayi shi dae Rafayet binsu da kallo kawai ya ke yi kafin ya dakatarsu da cewa “its ok, after we finish the breakfast, yusif makes sure that u check them well,’

“.Insha Allah babban ya ya” zuru su kayi jin za’a duba su, Bayan sun san cewa lfyarsu lou,

Mayar da idonsa yayi kan Junaid wanda ke ta faman murmushi, kamar zautacce, ada sun yi tuanin cewa yaron ta6in hankali gare sa, amma da aka bincika sa sai aka tabbatar da cewa haka Allah ya haliccesa wit smiling face,

ɗagowa junaid yayi suka haɗa ido da babban yayan, cikin sauri ya sunnar dakai yana ci gaba da murmushi, Shifa kallon dollar $ ya ke ma yayan nasu, shiyasa murnarsa ta ƙaru in ya kallesa $ kawai ya ke gani a fuskarsa, ya riga da ya kammala lissafin nawa zai amsa da nawa zai kashe wa sehrish ɗinsa 😥

……………..SEHRISH……………………

A 6angaren sehrish kuwa, zarce wa tayi da bacci, na ɗan mintina ta farka tana sauke ajiyar zuciya, sunan shi ne kawai zuciyarta ke ta faman ambato, idonta takai kan agogon bangon dake manne, ƙarfe 12:30am, ynx sun isa kammala breakfast ɗin,

tashi tayi ta kimtsa, ta fita taga me ke wakana, basa nan ciki duk sun fita, wayam kuma azmee ta gyara ko’ina yayi fess, a kitchen ta same ta, tana wanke dishes ɗin da su kayi amdani dashi,

“Aunty azmee sannu da aiki,” da fara’a a face ɗinta tace “Yawwa Sehrish ina fata kin washe yanzu,”

Murmushi sehrish tayi tare da cewa “eh Alhamdulillah da wani aiki da zanyi yanzu?. ta tambaya tana kallonta,

Azmee tace “a’a yau fa hutu ki ke hajiya sehrish, na ma kammala komai sai zuwa anjima zamu shirya dinner atare amma pls karki maimaita shiriritar ɗazun,”

Ƴar dariya sehrish tayi kafin tace”Insha Allah” ta ɗan yi shiru tana so ta zuba abinci, taci amma ƙunya take ji saboda 6arnar da tayi na zubawa farfesu abun wanki,”

“Ke bakya jin yunwa ne wai? kullum sai na ce ki zuba abinci ki ci, ko saina fara sa miki bulala ne?

Azmee ce tayi maganar cikin zolaya, dariya sehrish tayi da cewa “dama ynx nake so na zuba ne,”

ƙara sawa tayi ta ɗauko tray,

Bin ta da kallo azmee tayi ganin ta jera pancakes, ga sandwich ta kuma haɗa da scrambled eggs, duk a ciki a haka bai ishe ta ba sai da ta hada da fried chicken, taje ta ajiye  ta kuma dawo ta haɗa cornflakes a cup ta zazzaga uwar madara, ta tsula sugar,

Zama tayi asaman dining chairs ɗin na kitchen tana kallonsu, tunani take da me zata fara, muryar azmee ce ta katse ta da cewa “Sunyi miki haka? Ko zaki ƙara da wani abu ne? 😒

sunnar da kai sehrish tayi cikin jin kunya tace “sun isa haka,” Wato su sehrish banza ta samu, dama talaka bai iya samun wuri ba, ni bama wannan ba, Soyayyar babban yaya tasa ta manta da halin da su Hosana ke ciki, ada in zata sa abu mai daɗi a bakinta sai ta tuna dasu  tayi kuka  sosai, amma ynx ba wannan mgnr, *BABBAN YAYA* kawai 😥

Sandwich ɗin tafara ɗauka tana ci, tunanin ta nakan *RAFAYET* azmee na lura da ita duk wani motsi da sehrish zatayi murmushi take yi, hankalin azmee bai kwanta da irin wannan zauce war da Sehrish tayi ba akan Babban yaya, tabbas soyayyace mai ƙarfin gaske take masa, tunkan tasa shi ma a idonta, da jin sunansa kawai ta faɗa tarko, balle ynx da tasa shi a ido? hakika jikin azmee yayi mugun sanyi tunawa da Junaid, bawan Allah wanda kullum burinsa ya ga yarinyar cikin farin ciki,

Babu wanda yasan da zaryar da junaid ya ke yi izuwa ɗakin azmee, kullum roƙonta ya keyi akan dan Allah taba sehrish kulawa ta musamman, komai sehrish take buƙata, tagaya masa zaiyi mata,

Junaid ba ƙaramin so ya ke mata ba,  😿

(Tabbas akwai tashin hankali, ni babban damuwa ta, waɗannan zuciyoyin guda biyu ❗‼⁉

Wane hali zuciyar sehrish zata shiga ita da ta kwallafa rai akan mutun da ya kasance misoganist ! ya ƙi jinin mata, baya sha’awarsu basa gabansa, balle ma maganar aure, shin wane hali zuciyar junaid zata shiga ❓shi da bashi da ƙoshin lafiya, ga soyayyar wadda bashi ke gabanta ba, yayansa take so ❗  wane hali hosanna da Jahad zasu shiga in suka amince da bukatar Inspector Eesha!? shin za’a yanke musu hukuncin kisa ne, ko zasuyi zaman gidan yari ne ⁉  😭😭😭

Me zai faru idan su Aunty Babba Suka ziyarci Bokan nan na dajin enugu wato baba Iblis wanda muddin yayi asiri sai ya ci mutun jazamun, in ba wani iko na ubangiji ba 😿 dole fa ku gyara zama domin yanzu cakwakiyar ta soma 🔥🔥🔥

“Idan kin kammala cin abinci, inaso mu zagaye gidan nan tare dake ki ƙara ganin haduwarsa sosai,” murmushi sehrish tayi wadda tuni cikinta ya fara birkice mata dakyar ta iya cewa “tom aunty azmee, amma sai na fara shiga toilet shaf shaf,’

Azmew tace “dama nasan wannan jazamin ne ae, zuba miki ido kawai nayi Allah, ni zan shiga ciki, in kin kammala ki same ni a bedroom ɗina, kyau ma mu fara sallar azhar naga time yayi,”

Sehrish ta amsa da toh, cikin sauri ta kammala, sbd dama a ƙagare take ta zagaye gidan, ta gaji da zama wuri ɗaya, daga bedroom sai kitchen, shaf shaf ta wanke kayan da ta 6ata, sannan ta wuce ɗakinta toilet ta shiga, bayan ta fito da alwalarta tayi sallah, sai wurin addu’a ta tuno da su hosana, tayi musu addu’a sosai, kafin ta cire hijab ɗin ta tura a wardrobe, dama already dress ɗinta na maza ne ajikinta, gashin baki kawai ta aza, tagyara sumar kanta, ta naɗe ta cikin hularnan tashi da kwakwa, daga sama ta bi da mayafi ta yi kamar turban, ta saki jelar mayafin gefe,

A tare da azmee su ka zagaya, sehrish tasha mamaki, ganin haɗuwar katafaren gidan, ko’ina take bi da kallo kamar wuyanta zai 6alle, muryar azmee ce ta katshe ta da cewa “kin ga nan, wurin motsa jiki ne wato gym, bi da kallo sehrish tayi an kawata abun wurin da komai na motsa jiki, kamar ta shiga ta jaraba itama haka taji, amma taci alwashin watarana sai ta shiga ciki tayi gym itama,

gaba su kayi suka sake zuwa wani room ɗin, “nan kuma ɗakin bincike kenan ,” jinjina kai sehrish tayi ganin wasu matsiyatan Computers gava ɗaya na’urori ne a ɗakin ke sarrafa komai, wurare daban daban ta nuna mata Hada weapon’s room ( ɗakin ajiye makamai) , hada haɗaɗɗen parlor wanda suka ware domin yin kallo acikinsa, an ƙawata shi da faskekiyar plasma tv, ga speakers na sauti, ga ƙawatattun kujeru aciki da sauransu,

daga nan suka fita can harabar wajen, sehrish tasha kallo sai taga kamar tabar 9ja ne, saboda cikin gidan duniya ne, bakomai ya ƙara burgeta ba face swimming pool ɗin da tagani, mai faɗin gaske ruwan ciki yayi blue sky, daga gefe a hada kujerun shakatawa da table, bata ga komai ba sai da su ka shiga garden Aljannar duniya, juyawa tayi ta kalli azmee tare da cewa “har yanzu muna cikin nigeria”? dariya azmee tasaki tare da cewa “of course,” jin jina kai tayi wasu komai na cikinsa kore ne 🌲, sai aka ƙawata shi da Red & yellow flowers 🌹🌻, ga wani tsaftataccen ruwa dake guda na (waterfalls) yana gangarowa daga jikin dutsi zuwa ƙasa ya taru acikin pool yyi kamar lakes, Bakomai ya burge sehrish ba face agwagin dake ciki suna yawa farare,

“Aunty azmee gaskiya gidannan ina kokwanto anya ba hotel bane, girmansa da haɗuwarsa yayi yawa,”  tayi maganar tana kara bin ko’ina da kallo, azmee tace “haryanzu fa akwai sauran wuraren da baki gani ba, ynx dai na gaji mu zauna mana,

Wuri suka samu asamn  garden chairs ɗin suka zauna auna facing juna, bin ta da kallo azmee tayi ganin tana ta faman murmushi, wato bakomai sehrish ke tunani ba fa ce ranar da zasu fara magana da baban yaya harsu shaku ssae su rinka zuwa garden ɗinnan atare suna kewaya wa, lumshe idonta tayi sbd wata iska da ta ratsa ta, aranta tana cewa “Ya Allah ka nunamin wannan ranar da raina da lafiya ta, ni da shi atare muna strolling Cikin farin ciki,” 😥

“Me ki ke tunani ne”? Firgit sehrish ta yi jin maganar azmee a dodon kunnanta , cikin sauri tace “bakomai kawai ina mamakin haɗuwar gidan nan kamar a mafarki,”

Murmushi azmee tayi sbd sarai ranta ya bata cewa, tunanin ta na babban yaya ne,’

“Estate za’a mai dashi” cikin mamaki sehrish ta ce “dagaske aunty azmee? Amma zai fi kyau wlh girman yayi yawa,”

Azmee ta ce “eh naji da jima wa abbansu ya faɗi cewa za’a ƙara wasu part ɗin, yana so zai ware ma kowannansu nasa saboda baison in sunyi aure suyi nesa dashi, yace duk wanda yayi aure zai dawo ciki da matarsa, duk da sun mallaki gidajensu nakansu, amma shi yafi son hakan,”

Wani daɗi ne ya rufe sehrish, kamar anyi mata albishirin cewa itama zata kasance ɗaya daga cikin surukansa da zasu zauna agidan, 😒

Bayan sun ɗanyi shiru na wani lokaci azmee tace “i have something to discuss wit u,’

“Menene aunty azmee” sehrish ta tambaya da ɗan mamaki a fuskarta,

“Ko kinsan cewa a cikin sojojin gidan nan akwai wanda yasan cewa ke maca ce ba namiji ba !!”

A firgice sehrish ta mike hannu dafe da kirji tace “Who”? fuskarta da tsananin tsoro,

Dariya azmee tayi kafin tace ” zan faɗa miki but firstly ina so ki mun alƙawarin cewa u will calm urself,”

Jiki a sanyaye ta koma ta zauna zuciyarta na bugu, tsoranta kar ace cikin jarababbun ne wato Fawan ko Twins,

“Aunty azmee wanene dan Allah.. ..” tayi maganar tana haɗiye yawu,

Murmushi azmee tayi kafin tace “king of smile”

“Wanene haka azmee”? Ta tamvaya da mamaki,

“Oh baki gane ba tom nabaki satar amsa kije ki gano waya dace da sunan,’

duk iya tunanin sehrish bata gano wa azmee take nufi da *King of smile* ba, takasa samun natsuwa ta gano sa, sun jima suna fira bfr su koma ciki donyin sallar La’asar,

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

~🔥the father of soldierd🔥~?

💋💋💋💋💋💋💋💋

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ

ﺭﺍﻓﻴﺖ💞💞💞💞💞

ﻗﺼﺔ ﻛﺘﺒﻬﺎ ﺣﻔﺼﺔ ﺑﺎﺗﻮﺭ🌹🌹

_Story & written by_

*Hafsat Bature Moh’d*

~BossLady~ 💋

*page 68*

……….SEHRISH………………………

bayan ta kammala sallar la’asar, kimtsawa tayi kafin ta fito ta wuce kitchen tayi mamakin jin shiru alamun duk sun fita ne, tunanin ta ko’ina Babban yaya ya ke, ta lura baya fita sai dai azo a same shi in da ya ke, tun kafin azmee ta iso, sehrish ta fara ɗauko abubuwan da zasu yi amfani dashi, doya ta fara ferewa tasan suna yawan amfani da ita, tana aiki tana ɗan murmushi, sa6anin da tana aiki cikin damuwa saboda tunanin halin dasu Hosana da Jahad su ke ciki, zuwan big bro ya canzawa sehrish rayuwa gaba ɗaya,

Sam bata ji shigowar azmee ba, sai dae muryarta taji “Sannu da ƙoƙari rishi hakan ya burgeni,”

murmushi sehrish tasaki tare da cewa “Yawwa aunty azmee ina wurina,”

“Lafiya lou ta faɗi tare da shige wa ciki domin fara gudanar da aiki, cikin lokaci ƙankani kitchen ɗin ya fara kamshin abinci,

“Wani kalar abinci ki ka fi so”? Azmee ce ta jefa mata wannan tambayar yayin da ta ke zuba kayan ƙamshi acikin sauce ɗin da ɗaura, sehrish tace “farar shinkafa da jar miya ina son abincin nan sosai aduk lokacin da akayi mana shi a gida zumuɗi muke yi kamar hauka saboda muna jimawa bamu ci ba, shine abinci mafi daɗi a wurin mu,”  ta karasa maganar muryarta a sanyaye ba don komai ba sai don tuna wa da hosana, a lokacin da su ke tare da mahaifiyarsu duk in akayi musu tuwo tafi kowa mita ta rinƙa sababi tana cewa “oumma wai mu kullum tuwo kullum tuwo, da rana ayi tuwo, da daddare ma tuwo, in safe tayi ma ɗumamen tuwo, ni wlh nagaji zanje gidan makwabciya in ciyo shinkafa da jar miya hada ma wasilla zata samun, ”

Hawaye ne suka soma koƙarin zubowa a fuskar sehrish tunawa da rayuwarsu ta baya,

“Ni kuma nafison Tuwo arayuwata miyar ku6ewa da busasshen kifi wayyo daɗi in inaji kunne na har motsi ya keyi, musamman in ya kasance ɗumame ne,”

Azmee sai zuba ta keyi sam bata lura da sehrish ba wadda, take matsalar kwalla, jin shesshekar kukanta yasa azmee saurin ƙarasowa inda take tana faɗin “subhanallahi sehrish meke faruwa ne ? Cikin sauri sehrish ta dai dai ta natsuwarta,

Murya na rawa tace “ba komai aunty azmee, zafin albasar da nake yankawa ne, ya shiga ido na,’

“Eyyah sannu barshi na ƙarasa kawai,”

“A’a aunty azmee aikin zaiyi miki yawa, zan idasa,’

“Sehrish akwai ayyuka dayawa ba dole sai wannan ba, kibarmun yankar albasar ki kula da miyar dana ɗaura,”

“Shikenan aunty azmee amma kafin nan, ayimun uziri zan shiga toilet,”

“Shikenan ba damuwa kije kawai,”

Cikin sauri sehrish ta fice, saboda tana so tasamu space ta matse hawayen dake son zubo mata, tana shiga bedroom ɗinta, ta fashe da matsanancin kuka, a gefen gado tazauna tana matse hawaye,

Cikin murya kuka tace “Ya’ Allah ka karemun ƴan uwana, aduk inda su ke, ka sauƙaƙawa rayuwarsa, Hosana da jahad kowane yanayi zan shiga na rayuwa duk mun  daɗinsa I will neva forget about you, i will keep praying for u till d rest of my life 😭

haka ta dinga addu’o’i akansu, sai daga baya ta tuna da azmee wadda ta baro a kitchen tana aiki, cikin sauri ta shiga toilet, agaban wash basin ta tsaya, ta kunna fanfo ta wanke face ɗinta sannan ta fito,

ƙarar shigowar motoci taji, a lkcn da take ƙoƙarin barin ɗakin, nata cikin sauri tadawo ta tsaya agaban window ɗin da tasaba leƙe, janyen labulen tayi ta zuge glass ɗin tana kallonsu,

Motocinsu ne a jere, bayan sunyi parking wani Soja black american gabjejan gaske, ya fito ta gaba tare da buɗe mashi mota, a hankali ya zuro kafarsa dake sanye cikin slippers ɗin *Gucci* sun hau ƙafarsa raɗau ba ƙaramin kyau su kayi masa ba, idasa fitowa ya yi zuba mishi ido sehrish tayi sam batasan time ɗin daya fita ba, ashe baya gidan,

Sanye ya ke da V-neck shirt light green color, sai dogon wando Army trouser, surar nan fa tafito raɗau bai matuƙar jan hankali, sumar kansa mai tsayin nan tasha gyara na musamman ta zubo masa abaynsa ya ɗaureta,

Ba shi kaɗai bane tare da abbansu su ke, da Kanal yusif,

gaba ɗaya jikin Sehrish ya gama mutuwa, zuciyarta ta gama narkewa, tafiyarsa ma kawai abun kallo ce, ta majiya ƙarfi *Rafayet* tamkar Zaki ya ke, wanda ke mulkar namun dawa a ƙarƙashinsa,

Zuge glass ɗin window tayi, tare da cije le6enta, sam bata gajiya da kallonsa, cikin sauri ta fito ta wuce kitchen saboda tasamu damar ƙare masa kallo in sun shigo,’

“Sannu da dawowa ya idon nake”? Azmee ce tayi mata wannan tambayar,

“Alhamdulillah ae sun dawo dai dai aunty azmee,” sai faman murmushi take tana ƴan kame-kame,

Shigowa su kayi atare suna ɗan ta6a fira, anan main palor ɗin suka samu wuri suka zauna, abbansu na facing ɗinsu yayin da shi da Kanal yusif suke zaune a 3 seater,

Murmushi abbansu ya ke ta faman saki ba don komai ba sai don jin daɗin zuwan Babban yayan, musamman yau da suka yawata atare, duk da kin sakin fuskarsa da kuma ƙarancin maganarsa, _muryarsa tsada gare ta, saboda daɗinta shiyasa wata’kil ya ke rowarta_ (nace ba, da zai faɗi farashinta dana ƙulkula nasiya😂)

Hannunsa na riƙe da wayarsa, yana daddanawa, bazan faɗi ƙirar wani company bace, sbd wata irin haɗaɗɗiyar waya ce, very expensive wadda takasance mallakinsa, kuma sunan sane ajikinta wato (SGR) ba mai iya controlling ɗinta sai shi duk bala’in mutun, saboda sometimes da Voice ɗinsa take amfani, daga ya faɗi abu zata nuno masa, 😔

gyaran murya abbansu ya yi tare da cewa “Ina magana,” a hankali ya ɗago da sexy blue eyes ɗinsa ya aza akan abban nasu tare da cewa “Am all ears,”

Abba yace “Ina so kayi mun promise ɗin cewa har ka bar nigeria, bazaka ta6a kowa ba kayi shiru da bakin ka salin alin ka tafi cikin salama dan Allah,’

wani irin kallo babban yayan ya ke wa abban nasu jin abunda yace, hannu ya kai tare da ajiye phone ɗinsa saman table ɗin da ke front ɗinsa, ya jingina bayansa jikin royal sofa ɗin, tare da aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya, duk abban nasu na kallonsa burin sa ya ji amsar da zai basa,

murmushi kawai kanal yusif ya ke yi wanda ke ta faman danna wayarsa, amma kunnansa nakan maganar da suke yi,

ɗan ta6e small lips ɗinsa ya yi kafin yace “*IMPOSSIBLE*” atakaice,

Sauke ajiyar zuciya abban yayi dama yasan amsar kenan,

Cikin takaici yace “Oh sai kayi kenan”?

“Eh” ya bashi amsa ba wasa,

Jinjina kansa yayi tare da cewa “ni narasa gane tsakanin kai da Momynka Alexandra waya fi wani taurin kai, kafiya da ji da izza,’

da buɗen bakin babban yaya sai cewa ya yi “Ita,”

Fashewa da dariya yusif yayi, tare da sa wayarsa a saitin mouth ɗinsa yana karewa, saboda gudun kar babban yayan yakai masa naushi,

“Yi mai Isarka,” Babban yayan ya faɗi yana shafa damtsen hannunsa da right hand ɗinsa alamar zaiyi bugu,

yusif yace “Ai ni na wuce bugu ko Abba,” ya faɗi yana kallon abban nasu wanda shima dariyar ya keyi,

Da ƙarfin gaske babban yaya ya yunƙura zai kaiwa Yusif punch a face ɗinsa, jiki na rawa abbansu ya taso yayi saurin rikosa, duk da yasan wasa ya ke ba bugun nasa zaiyi na, yusif ihu yayi yana faɗin “Abba dont let him punch me,”

Dole yusif ya tsorata, shifa Babban yaya a ƙa’ida ya naushi mutun a cheeks ɗinsa, sai haƙori ya fita 😳

In kuwa yakai ma zazzafan naushi a saitin zuciyarka, sai dae uwar mutun ta haifi wani, bugu ɗaya sai lahira 😳😳😳

Murmushi kawai sehrish ke saki domin komai ke faruwa a idonta, duk da akwai tazara sosai amma tana hangensu ta cikin kitchen ɗin, bakomai ya burgeta ba, fa ce yanayin yadda Sgr ya ƴunƙura ya dunkule hannu zai kaiwa yusif naushi, sumar kansa da ta yarfo ta gefen forehead ɗinsa ba kamin tafiya yayi da ita ba,

“Bari na shirya miki abunsha ki kai musu,” muryar azmee ce ta katse ta daga kallon nasu,

ɗan zaro ido tayi jin ance zata kai masu abunsha, ga tsoran tunkararsa ga kwaɗayin son ganinsa da take yi,

A tray ta shirya mata cups masu ɗauke da coffee, ta miƙa mata jiki na kerma, sehrish tasa hannu ta kar6a, a hankali take tafiya zuciyarta cike da fargabarsa,

Da sallama ta isa inda su ke, duk suka amsa, miƙa wa abbansu tafara yi, da fara’a fuskarsa yasa hannu ya ɗauki cup ɗin tare da cewa “Yawwa madallah sannu da ƙoƙari,” murmushi ɗanyi tare da juyawa wurinsu heart ɗinta na beating, tsoro yasa tafara miƙa wa yusif cikin sauri yusif yayi mata alama da hannunsa tafara miƙawa babban yayan, Saboda ba’ayi masa haka sam, wato afara mika wa nakasa dashi abu kafin a bashi, hakan laifi ne a wurinsa,

Ita kanta batasan tana da irin wannan natsuwar ba, sai da taje gabansa, ji ka ke tsit hatta zuciyarta sai da ta lafa da bugawa cikin sauri,  daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya gauraye hancinta, zuba mishi ido tayi tana kallonsa,

Idonsa nakan screen ɗin wayarsa, jin alamar mutun ƙiƙam akansa yasa shi ɗan dagowa, tray ɗin hannunta yaci karo dashi,

cire hannu yayi yasa a hankali ya ɗauki cup ɗin, bin hannusa tayi da kallo, wasu irin zira-ziran yatsun hannu, dogaye farare ƙal, ga fatar nan sai ɗaukar idon tsiya, mutun kamar ya lashe, agogon hannunsa tabi da kallo tazauna masa raɗau sai kyalli take,

Mayar da idonta tayi akan sumar kansa mai ɗan bala,in kyau sam sehrish tagaza matsawa daga tsayen da take akansa, batasan bayason Kallo ba, a hankali yake kur6arsa a mouth ɗinsa,

Abun ya daurewa abbansu da kanal yusif kai, ganin yadda mai aikin nasu Ya tsayawa Babban yayan akai kamar sai lashe sa, duk da sun cewa shi abun kallo ne, dole akallesa,

“Miƙo mun mana,’ kanal yusif ne yayi maganar don yayi saurin dakatar da mai aikin nasu daga kallon ƙurullan dayake wa Babban yayan nasu, kafin ya fusata,

Lokacin da mgnr kanal yusif ta dira a ears ɗinta, jiki na rawa tadawo hayyacin ta, tare da matsawa ta miƙa masa shima ya ɗauka sannan jiki a matse ta koma kitchen, har ta shiga cikin ƙamshin turarensa ne ke ɗawainiya da ita,

Sam tarasa sukuni, sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke, kamar wadda tasha gudu,

Muryar azmee ce ta katseta da cewa “tun da mun kammala, mu bari sai after magrib ayi arranging ɗinsu a dining,”

Sehrish ta amsa da “Toh aunty azmee,”

tana ganin lokacin da suka kammala firar tasu, su ka kuma fita atare,

……..*Junaid*…………………….

Da tunanin sehrish ya yini, kasancewar ya fita gidan wani friend ɗinsa daya jima shima bai lpy, yaje duba sa, a can ya yini yana ta jansa da fira, hakan yasa ya jima, bashi ya dawo gida ba sai wuraren magrib ya shigo da motarsa, zuciyarsa cike da son ganin sehrish ɗinsa, da murmushi ya shiga ciki, bakowa duk sun je sallah da alama,

Bedroom ɗinsa ya wuce, cikin sauri ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito,  shirt yasanya tare da dogon wando, kullum ya kalli kansa a mirror sai ya furta wannan kalmar wato “Mallakin sehrish,”

(Sai naji dama ni yakewa tanadin kansa da ban bari yasha wahala ba, dama ƙopa a buɗe take musamman ga irinsu Junaid masu kyawun hali) 😅

Jin takon takalminsa yasa sehrish ɗagowa, wadda ke tsaye tana ta faman jera abincin a dining, ita ta riga azmee fitowa bayan sun gudanar da sallar la’asar, zuba mishi ido tayi atlease tayi kewarsa sosai don tun safe rabon da tasa shi a idonta,

Shima farin ciki ne ya dabaibayesa ganin muradin ransa, ƙarasawa yayi yaja kujera ya zauna yana kallonta,

Cikin sauri tace “me zan zuba maka,”

“duk abunda yayi miki,” kai tsaya ya faɗa,

Jim sehrish tayi shiru ta tsaya da jeran da take yi, maimaita maganar da yayi yanzu acikin zuciyarta tayi wato daya ce “duk abunda yayi miki amaimakon yace duk abunda yayi maka tunda amatsayin namiji take,”

ɗan ɗagowa tayi ta saci kallansa, har ynx idonsa na akanta fuskarnan ɗauke da murmushi,

Jiki a sanyaye ta zaro plate haɗaɗɗiyar jallop din taliya ta zuba masa, tare da haɗa masa da Cokali aciki ta miƙa masa,

“Thanks” ya furta tare da soma cin abincin, ganin yana ɗiba da zafinta yasa tace “ka bi a hankali kana ka ƙone,”

ɗagowa yayi ya kalle ta da buɗen bakinsa sai cewa yayi “kada ki damu zan kula”

daram taji gabanta ya ƙara faɗuwa, yau junaid yasaki layi sai kiranta ya ke da sunan macen ta,

Jin ƙarar dirar motoci ya tabbatar mata da cewa sun dawo, nan da nan taji zuciyarta ta bada wani sound, saboda tasan hada mutumin ta aciki,

Shigowa su kayi atare suna ta faman fira, kamar ba’a tare suke ba,

fawan da khaleed ne suka fara shigo wa tare da su Irfan da jabeer banda su twins,

tayi tunanin shima zai shigo ne amma babu shi, haka abbansu ma, da kanal yusif,

kai tsaye suma suka wuce izuwa dining ɗin suka ja kujera kowa ya zauna,

“Sannun ku da dawowa” acewar junaid,

Su ka amsa su duka, cikin sauri sehrish ta shiga yin saving ɗinsu,

“Ina yaya Ayaan da Jahan su ke, banganku atare ba? Su basu dawo ba ne?

Junaid ne yayi wannan tambayar,

Fawan ne ya basu amsa da cewa “taya muma zamu sani? mun jima da rabuwa dasu, su sukansan inda suka je”

Jabeer yace “ko tsoro basa ji, babban yaya ya neme su, su basusan su kame kansu ba, kamar yadda mukayi,”

“Ka rabu da shaggun jiki magayi,” acewar irfan,

 

 

~Hafsat bature~  ✍️

Keep sharing 😘*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

~🔥the father of soldiers🔥~

 

_💞Romantic Love story between Hosana& Marshal Omar💞_

*💋HAFSAT BATURE BOSS LADY💋*

*page 69&70* 💋

“Ka rabu da shaggun jiki magayi,” acewar irfan,

haka su kayi ta fira suna zuba abinci acikinsu,

Bayan sun kammala sehrish ta kakkwashe dishes ɗin da sauransu duka tayi kitchen dasu, har time ɗin azmee bata fito ba har sai da ta kammala wanke komai da su kayi amfani  dashi sannan tashigo agajiye tana faɗin”kin ji shiru ko wlh bacci ne yayi awon gaba dani shiyasa ban fito ba,

“Babu komai aunty azmee kwarama da kika huta sbd kina aikatuwa ssae,”

 

Azmee tace” hmmmm nasaba ne, bana gajiya da aiki,

shiru su ka ɗayin kafin rishi ta kuma cewa “Su babban yaya basu shigo ba, shi a part ɗinsa za’a kai masa abincinsa ko anan down ?

murmushi azmee tayi tace ” a can ake kai masa amma in yakasance dinner ne, wani time ɗin kuwa anan su ke haɗuwa suci gaba ɗaya, ke zaki kaimasa ?

“Eh zan kai masa,’ cikin zumuɗi sehrish ta bata amsa,

“Shikenan amma akwai wani abu da zan faɗa miki u ave to know it,”

Sehrish ta ɗan yi jim kafin tace “menene shi”?.

“Babban yaya fa, baya son kallo sai fa kin kiyaye, because in ana kallonsa yana ji ajikinsa, sannan in ya tambayi abu ko menene kawai ki ce akwai, karki kuskura ya ce yana buƙatar wani abu akawo masa ki ce bamu dashi, ya tsani wannan ki kiyaye ! Sannan baisan kwaratsi ko kaɗan, sannan shi mutun ne mai tsaftar gaske, ko da gigin wasa kada ki kuskura ki bar abun ƙazanta a part ɗinsa ko min ƙanƙantarsa ko da ajikin ki ne, ke ma ki ƙara tsaftarki abisa wadda ki ke yi don daga yanzu ke ce zaki rinƙa kula da part ɗinsa,”

Wani irin daɗi ne ya rufe sehrish, jin cewa itace zata rinƙa kula da part ɗinsa, koba komai zasu samu kusanci da juna, 😇

Azmee ta ci gaba cewa “and then he doesnt repeat words in yayi magana, dole yayi magana aji farat ɗaya, sannan in yana bacci ba’a tashin shi, don naushi ya ke kaiwa bana wasa ba……’

Katse ta sehrish tayi da cewa “In time ɗin sallah ne fa? Shima ba’a tashin sa? ta tambaya tana kallon azmeen wadda ke daga tsaye,

Azmee tace “Abun ajinin sa ya ke ! muddin lokacin sallah yayi dakansa ya ke farkawa, sometimes kuma alarm ke tashinsa,

Jinjina kai sehrish tayi aranta tace”akwai matsala, Anya kuwa zan iya ? ta tambayi kanta,

Muryar azmee ce ta dawo da ita “zaki iya mana, matukar ki kasa natsuwa,”

Wata tambayar sehrish ta ƙara jefa mata,

“Aunty azmee wai babban yaya ɗan wrestling ne?

“Meyasa ki ka tambaya”?

sehrish tace “naga yanayin kirar jikinsa ne, wlh irin ta tasu ce,”

Hmmm azmee tace “shi da ya ke soja, sojan ma bana wasa ba, wanda ya amsa sunansa ae fiye da wresting ma yana yi,”

Murmushi sehrish tasaki Aranta tace “a shirye nake dana zama tamkar baiwarsa wurin yi masa biyayya sau da ƙafa, zan yi komai zan yi iya ƙware wata don naga yasan da zamana acikin gidan nan,

tayi maganar atime ɗin da take jera dishes din da takammala wanke wa, a cikin shelves ,

Atare da azmee suka idasa gyara kitchen ɗin su kai mopping da komai,” daga bisa azmee ta wuce ɗakinta bayan ta sanarwa sehrish cewa idan sun dawo ta tabbatar da ta kai musu dinner ɗinsu,

Kasa bacci tayi burin ta, taji shigowar Babban yaya, domin takai masa dinner ɗinsa,

Murmushi kawai ya ke saki ynx ya yanke shawarar zai sanar wa sehrish da cewa yasan ita mace ce ba namiji, rungume ya ke da pillow a ƙirjinsa, night dress ne ajikinsa riga ce ta wuce guiwa, ya baje a saman gadon abban nasu yana jiran dawowarsa,

Ƴunkurawa yayi ya ɗan tashi zaune, yana tunanin taya zai sanar mata batare da ta tsorata ba, gyara murya yayi kamar yana agabanta ya ce “Sehrish na riga da nagane cewa ke maca ce, don haka ki kwantar da hankalinki, ni mai sauƙin kai ne bazan bari kowa yasani ba, i promise u, ni burina ki ɗauke ni tamkar ɗan uwanki na jininki, nima zan ɗauke ki amatsayin sister ɗita……..’

dariya ya saki bayan yagama tsara wannan maganar, ajiyar zuciya ya saki tare da cewa haka yafi dacewa na tunkare ta, na sanar mata, Allah yasa kada ta razana, ko taƙi accepting ɗinsa as her brother,

Koma yayi tare da kwantawa idonsa na facing ceiling, fuskarnan da murmushi, har cikin ransa yarinyar ta kwanta masa luf~~~~~~~

Har bacci ya soma ɗaukarta, taji dirar motocinsi, cikin hanzari ta buɗe idonta, murmushin farin ciki tasaki, tashi tayi zaune tana jira su kammala shigowa kafin takai masu dinner ɗinsu, zuru tayi tana jiran shigowarsu, tana jiyo muryar abbansu da kanal yusif suna magana, amma bata jiyo tasa ba, tamasan baza taji tashi ba, saboda wata irin Voice ce dashi bata da sauti sosae, wata’ƙil sai ransa ya 6aci sannan Za’aji tsiwarsa,

Sai da ba da kusan 30 mins, sannan ta tashi cikin sauri ta gyara kanta, kafin ta wuce kitchen, sai da tafara kaiwa kanal yusif nashi a room ɗinsa, sannan ta wuce kaiwa Abbansu nashi shima,

Da sallama tashiga,atare da junaid suka amsa mata, cikin natsuwa ta shiga da tray ɗin mai ɗauke da food warmer tare da plates da spoon, sai jug da cup,

Kwance suke atare shigowarta yasa su tasowa zaune, cikin girmamawa tagaishe da abbansu, da sakin fuska ya amsa mata,

umarni ya bata da ta ajiye mashi anan ƙasa, ajiyewa tayi a hankali kafin ta tashi, suka haɗa ido da junaid ya kashe mata ido,

gabanta ne taji ya faɗi, sai ta ga abun kamar a dream, tafiya take zata bar room ɗin nasu, tasake juyawa tare da kallonsa, again ya sake kashe mata idon,

Cikin sauri ta fice tana mamakin wannan abun, amma tariga tasawa ranta cewa “Junaid yana da ta6in hankali,” wasu ɗabi’un nasa yayi mata kama da na masu psychiatric disorder 😂

A ɗan kayataccen tray ta shirya mashi nasa, gabanta na faɗuwa ta tunkari upstairs apartment ɗinsa,

A buɗe tasamu kopan parlor ɗinsa, haske everywhere, bata gajiya da kallon hadaɗɗen parlor dinsa, sallama tayi taji shiru idasa shiga ciki tayi, asaman table ta ajiye masa shi, tsayawa tayi tana tunanin ya za’ae yasan ta an Kawo masa dinner ɗinsa, ran ta ne ya bata cewa ta shiga cikin bedroom ɗin nasa tayi informing nasa,

zuciyarta na ɗar ɗar ta tunkari cikin bedroom ɗin nasa, a hankali ta ɗanyi knocking door ɗinta, gabanta na faɗuwa,

shiru tayi tana jira abata umarning shiga, sexy Voice ɗinsa ce ta ratsa kunnanta da cewa “Come In”

Ajiyar zuciya sehrish tayi, tare da lumshe idonta, wani irin sanyi ne ni’imataccen gaske tare da ƙamshi su ka ziyarci hancin ta, a hankali ta idasa shiga ciki tana wurwur ga eyes ɗinsa can ta hangosa, daram taji wani irin bugu azuciyarta,

daga shi sai ɗan pant na maza ajikinta, yana tsaye at the front of the mirror Allah yaso ya juya mata baya, ba ita ya ke fuskanta ba, da taga tashin hankali,

Zuba wa surar jikin shi ido tayi cikin tsananin tsoro, dogo ne bana wasa ba, ga wannan ƙirar karfin tasa, idonta ta saukar akan zanen tattoo ɗinsa mai tsananin kyan gaske A farar fatarsa, bata ta6a lura dashi ba sai yau,

sam tarasa buɗe baki ta faɗi abunda ya kawota sbd kallon Kyakkyawar surar Babban yayanmu, 💞

hannayensa na cikin sumar kansa, yana shasshafa mata mai, sai salƙi take kafin ya ɗaure ta yasa ke ta izuwa bayansa, mayar da hannunsa yayi acikin jerin tsadaddun turarukansa dake agaban mirror  ya ɗauko kwalbar turaren (Imperial Majesty) haɗaɗɗen turare mai wani irin fragrance mai ratsa sassan jiki, sai wane da wane ke mallakar irinsa,

Feshe jikinsa ya yi dashi ta ko’ina kafin ya mayar ya ajiye,

Ya jima yana mamakin wanene ya shigo masa bedroom ɗinsa haka, ya ba da permission ɗin a shigo amma shiru ba aƙara magana ba,

gyaran murya yayi alamar son jin bayani daga wurin wanda ya shigo masa ɗaki,

gyaran muryar da yayi ne ya dawo da ita cikin hayyacin ta, cikin sauri murya na rawa tace “am…dama…dinner….ne ….na kawo……yana a parlor,

“Its okay, wait 4 me there, am coming now,” ya faɗi yana kai hannunsa saman bedmatress ɗinsa inda ya ajiye sleeping dress ɗinsa da zai sanya,

Jiki a mace sehrish ta fice, tana cizon lips ɗinta, haƙiƙa tagama narkuwa cikin tsananin ƙaunarsa 💘

A parlor dinsa ta tsaya tana jiransa kamar yadda ya umarta, hannunta na a chest ɗinta dafe da saitin Zuciyarta, surarsa kawai idonta ke tariyo mata, Murmushi kawai take saki *Big bro* ya gama tafiya da ita, 😍

Sam bata ji fitowarsa ba, sai da ya ƙaraso ya zagayo inda royal sofa ɗin suke sannan ta ankara,

Wani sabon kallon tabi shi dashi, sleeping dress ɗinsa sunyi matuƙar yi masa kyau, koda ya ke shine yayi musu kyau, irinsu Babban yaya sune suke wa kaya kyau, wato masu sa kyau tayo kyau ko bata da kyau 😇

Riga da wando ne ƴan ƙasar indonesia masu laushin gaske, irin wanda ko mutun baijin bacci yasa su dole yaji shi, maroon colour masu zanen flowers milk colour ajikinsu, daga sama rigar bata rufe ƙirjinsa ba, dama shi bai cika sa kaya waɗanda ke covering chest ɗinsa ba, bai sanya links na rigar ba,

Cikin natsuwa ya zauna saman 3 seater, sam sehrish tagaza janye idonta akansa balle tafara saving ɗinsa har sai da taji voice ɗinsa a ears ɗinta yace “Ni zanyi saving kaina ne!? ya tambaya fuska a ɗaure,

Cikin sauri sehrish ta ɗauke ɗan bowl tare da buɗe warmer ɗin dake ɗauke da Chicken pepper soup, tasanya saving spoon ta Shaƙe masa shi, wani irin  aroma ne ke tashi daddaɗan gaske, ajiye masa tayi sannan ta zuba masa white rice acikin plate, bayan nan ta haɗa masa da drink mai sanyi,

Natsuwa tayi bayan ta kammala zuba mashi duk abinda ya dace, ta ɗan ja baya zata juya ta fice sbd tuna mgnr azmee na cewa Bayason kallo, muryarsa tasake ji ya ce “In na kammala wazai kai kayan kitchen!”? tsananin mamaki sehrish kawae take yi, ashe yana magana har haka, acewarta, muryarsa ba ƙaramin daɗi take mata ba, tayi mamakin yadda yake furta yaren hausa duk da kana ji kasan bai saba da ita ba, in ka gansa bazaka ta6a tunanin cewa zai iya magana da hausa ba, saboda yanayinsa,

Cikin hanzari tace “Ni” jinjina kansa yayi, ya ci gaba da cin kazar dake gabansa, murmushi ta ɗan saki tasamu wuri ta tsaya, da tazara tsakaninsu, amma komai yakai hannu zai ɗauko cikin sauri sehrish ke ɗauka ta zuba masa in na zubawa ne, in kuma nasha ne ta tsaiyaya masa, har ya kammala sam babban yaya baya wasa da cikinsa, yana basa haƙƙinsa yadda ya dace,

Sehrish ta tsaiyaya masa ruwa ya wanke hannunsa acikin wani bowl, sannan ta ciri tissue ta miƙa masa ya goge mouth ɗinsa dashi,

Haka tabi shi da ido harya tashi ya wuce cikin bedroom ɗinsa, ta lura bacci yake ji yadda taga yana lumshe idonsa,

Sai daga bisani ta tattare kayan ta fice tana mai jin kewarsa atare da ita, kafin zuwa gobe ta kuma sashi a idonta, cikin kitchen tamayar da kayan sai da ta wawwanke dishes ɗin acikin daren sannan ta wuce nata room ɗin tana mai cike da shauƙinsa,

Ta jima ba tayi bacci ba, su twins basu dawo cikin gidan nan ba sai around shabiyu na dare, Time ɗin ma kowa yayi bacci, cikin sanɗa su ka wuce room ɗinsu,

a cikin ƴan kwanakin nan rayuwar sehrish ta canza sosai, wani irin azababben so take mashi, wanda har ya kai ga ko sallah take yi da tunaninsa aranta, daker take samu ta dai daita natsuwarta wani sa’in,

Junaid kuwa sam ya gaza gaya mata abunda ya shirya zai sanar mata, ƙarshe azmee tace yabarta ita da kanta zata sanarwa sehrish ɗin, a yayin da sehrish ke wannan haukan sam Rafayet har yau bai ta6a ɗagowa da idonsa ba, yasa cikin nata, bae masan wanene ba ko wacece ba ke famar ɗawainiyar kai masa abinci da gyara masa part ɗinsa ba, abunda yasani shine yana samu kyakkyawar kula agurin  kowanene ma  💋

*Hafsat Bature*…………………………………………………………

………….._Katsina state_…………….

Zaune take ta haƙimce a saman 3 seater, ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, hannun ta na riƙe da remote, ta ƙura ido tana kallon faskekiyar plasman dake manne jikin bango tana facing ɗinta,

Ko kyaftawa batasan yi, dayake shirin ta ake yi, wato shirin daɗin kowa na Arewa 24, maimaici ne take kallo, sai faman washe baki take yi tana fadin “Oh koya za’a kaya tsakanin mlm na tala’a da hajiya fatima akwai bada ƙala a wurin nan,’ ta faɗi tana jinjina kai, ita kadai abunta, acikin matsakaicin parlor ya hadu iya haduwarsa ba hayaniya, ga komai cike da tsafta kwal,

Tsohuwa ce amma ba tukuf ɗin nan ba, tana da hasken fata, jikinta na sanye da riga da zani na atampa, ta coge ɗaurin dankwali, daga ganin ta kasan taji hutu ga kuma kwanciyar hankali da natsuwa,

“Saude ! Saudee !! saudatu wai ina ki ka shiga ne? kin shanya ni ina ta faman jiran ki, da alama watan barin ki agidannan ya tsaya,” 😡

tsohuwarce ta fadi tana murguda baki kamar wata yarinya,

Cikin sauri wadda aka kira da sunan saude ta fito daga kitchen hannun ta ɗauke da plate wanda naman kaza ne acikinsa jar suya

Karasowa tayi tana faɗin “dan Allah goggo ayimun afwa, wlh bata ida soyu ba ne shiyasa,’

hararar ta tayi tana yamutsa fuska tasa hannu ta kar6i plate din tana cewa “Last warning, in ki ka kara, zaki tattara kayanki ki koma can ƙauyenku aci gaba kiwon shanu baki ba ra6ar A.c ,”

Shiru saudatu tayi tana tamke fuska, ta tsani taji ance za’a maida ta ƙauyansu, gashi kullum tsohuwar cikin yi mata mita take bata gajiya,

hannu tasa ta ɗauki tsokar naman ta tusa abaki, tana tauna tana yamutsa fuska,

“Anya kuwa saude kinsa farin magi aciki kuwa,” ta tambaya tana kallonta yayin da take lasar naki,

A ƙule saude tace “bansanya ba, babban likita ya hana,!

dagowa tayi baki asake tana kallonta “saudatu ! Rashin kunya ko? Ki kalli tsabar idona ki ce babban likita ya hana ! shiya haife ni koni na haife sa dazai hanani jin daɗin rayuwa!?

Cikin ƙunkuni saudatu tace “Ke ki ka haifesa, amma ae don lafiyarki yayi hakan….’

tunkan ta idasa magana, goggon ta jefe ta da ƙashin ciyar kaza a fuska,’

Hannu saudatu tasa ta shafa wurin da ta jife ta, kafin ta kalle ta tana zumbura mata baki,

“Ke ki kiyaye ni Allah ! wato ya daure maki gindi kina iya shegen da kika ga dama ko ? Cikin sauri saude ta dafe kai cikin jin kunya tace “dan Allah goggo wannan maganar ba daɗin ji Allah, gatsar ba sakayawaa,

Baki asake goggo tace “ba shakka, yau yarinya zatayi fiffike ta koma gidan ubanta,’

Kafin Saudatu ta bata amsa, sukaji dirar motoci a cikin gidan da jiniya,

Kallon juna su kayi atare, saudatu tace “goggo meke faruwa ne, ko kinyi da wani zai zo ne ? ni naji kamar jiniyar motar ƴan sanda,”

Murmushi goggo tasaki tare da ajiye plate ɗin kazarta, kasa tana cewa

“Kin manta muna da rundunar sojoji a family ɗin mu 😇  Shiyasa nake gargaɗinki kibi ni a hankali, kiyi mun biyayya ko kin gama da duniya lafiya, cikin zolaya tayi maganar, dariya saudatu tayi,

adai~dai lokacin marshal omar ya shigo wanda dirarsa kenan,

sanye yake cikin jeans da farar t shirt mai dogon hannu tabi shape din jikinsa, surar kirjinsa ta bayyana muraran, fuskarsa na sanye da face mask, ba karamin kyau yayi ba, koda yake dama jinin kyau ne su,

tun da ya shigo baki asake saudatu ke kallonsa kamar ranar ta fara ganinsa,

Cike da wannan tafiyar tasa ta nigogi majiya karfi yake tafiya,

Tsananin farin ciki yasa goggon katsina harba plate ɗin kazarta ya watse ƙasan carpet ba tare da ta sani ba, kamar karamar yarinya haka ta watsa a guje ta rungumesa tana fadin “Wata sabon gani, mafarki nake ko gaske, Oh ni Omar,

Sakin shi tayi tana ta faman zabga murmushin jin daɗi, a hankali yasa hannu ya ɗan zame facemask ɗinsa yana kallonsa fuskarsa da fara’a ya ce “Goggo na har ynz dama baki daina wannan tsalle tsallen ba sai kin 6alla ƙafa ?

dariya tayi ta ruko hannusa tana fadin” wlh duk cikin farin ciki ne Omar, ji nake kamar in zuba ruwa a ƙasa in sha,

zama su kayi atare, sai lokacin saudatu ta samu damar gaishe shi ” sannu da zuwa ƴa’ƴa Omar,’

“yawwa” ya bata amsa without looking at her, idonsa na akan goggonsa wadda ke ta faman binsa da kallo, hannu tasa ta shafa fuskarsa tana faɗin “Oh ni Omar haka ka zama, tukunna ma dai yaushe ku kazo daga U.s ɗin? kuma ya naganka kai kaɗai ina sauran suke ? tare da matarka ku ka zo ? ta haihu yanzu ko ?

Zuru yayi yana kallonta, aransa yace  mai hali bai ta6a canzawa in banda zafin ɗumi irin na goggon katsina Yaushe yayi budurwar balle akaiga maganar aure da ƴa’ƴa?

ajiyar zuciya ya saki kafin yace “wacce amsa ki ke so na fara baki gaggona ?

Murmushi ta dan saki tare da cewa “ni ba wannan ba ma, Oh ni Omar wai kai ne ka zama haka !  kazama kamar dodo, Ka tara ƙirar karfi ba mata, kyau ace akwai inda za’a rinƙa sauke nauyin nan,…

Cikin jin kunya saudatu dake tsaye ta juya tayi cikin kitchen, domin kawo masa abun sha,

dafe kansa yayi tare da cewa “Omg !! goggo shiyasa ba kowa ke son zuwa wurinki ba, sbd in ki ka fara zuba kamar radio mai jini,’ ya faɗi yana yamutsa fuska saboda baisan hayaniya arayuwarsa,

Hannu tasa tare da rufe bakinta tace “nayi shiru tom, ka da kace zaka daina zuwa wurina bari nayi shiru,

dawowa saudatu tayi hannunta rike da tray da ta zuba masa snacks da abunsha a cup, ajiyewa tayi agabansa,

hannu yakai ya dauki lemun domin ya kur6a, muryar goggon ce ta katse sa da cewa “dole nayi magana Omar, Oh ni Jibi yadda ka tara nonuwa  a kirjinka sai kace dai za’a sa akwatin nono na mata a suturta……”

ae baisan lkcn da ya ajiye cup din ba ya miƙe tare da cewa “Ni zan tafi, kunyartar ta isa haka,”

saude dake a wurin tuni ta sulale ta gudu,sbd tayu matukar kunya ta, da sakin layin da goggon take masa,

Cikin lallami ta tashi itama tsayen tana cewa “haba ɗan shalelena, duk fa cikin murnar ganin ka ne,’

ta6e bakinsa yayi tare da cewa ” no goggo tafiya zanyi, dama bani kadai nazo ba akwai yara na dake a waje suna jira na,”

Sam bataji daɗi ba, jin zai tafi tayi tunanin zai tsaya ya kwanar mata ne, itama tasan cewa surutunta ne ya ja mata, sarai tasan cewa bayason ɗumi haka,

Cikin sanyin murya goggo tace “toh baza ka tsaya ku gaisa da Babban likita ba ? kusan kullum sai yayi mgnr yaushe zaku zo daga America,

marshal Omar ya ce ” yana ina ne ? Ko yana on duty ne ? goggo tace “Eh tun da safe ya tafi asibiti aiki,’

“Okey may be na leƙa masa bfr na wuce kaduna gobe da safe, ‘

“Yanzu omari tafiya zakayi daga zuwa,’ ?  tayi mgnr kamar zata yi kuka,

“Calm down your mind gaggo na, Captain adam da su mg Osman na nan zuwa, duk zagi gansu, nima zan dawo insha Allah, ynz akwai mahimmin aiki a gabana ne shiyasa,”

Jin sunan waɗanda zasu zo dayawa yasa ta washe daga ɗaure fuskar da tayi,

“Aiko da naji daɗi, in suka zo, zan masa a ayi musu fura, in suka zo suyi ta sha,”

Murmushi Omar yasaki ya fice yana faɗin “Zaki ga saƙona gaggo,”

Cikin jin daɗi tace “ina jira ɗan Albarka, ta ɗaga murya tana ci gaba da cewa  “Allah ya haɗa ka  da kaddarar ka acikin garin nan,’

sarai yaji ta fita yayi yana ɗan murmushi, yarasa dalilin dayasa, tsofaffin nan suke disturbing ɗinsu akan aure aure 😏

tunkan ya ƙarasa inda motocinsu su   ke, da sauri wani sergeant ya buɗe masa mota ya shiga A jere motocinsu suka fita,

sai da ya tafi sannan saude ta fito tana cewa “wlh goggo sam bakya kyauta, shikenan daga tsufa ya fara kama mutun sai yaita ƴan sambatu yana sakin layi ynx abunda ki kayiwa ƴaƴa omar kin kyauta “?

ta tambaya tana kallon goggon wadda ke zaune saman kujera, baki asake take kallon sauden,

Jinjina kai tayi tare da cewa “ba shakka raini ya shiga tsakanin mu, gobe goben nan zaki koma ƙyauyenku ni nagaji dama liƙamin ke akayi aka manna bin ba don naso ba,’ ta faɗi tana hararar ta,

Riƙe ƙugu saude tayi tare da cewa “to kisa ni ba inda zani je, koma tafiyar zanyi ƙafa ta ƙafar Babban likita ,’

“Saboda ke ki ka haife shi”? goggon ta tambaya,

Saude tace “bani na haifeshi ba, amma zaki ga yadda soyayya ke aiki……’ bata idasa ba goggo tabi ta aguje itama ta tashige ciki da sauri, dama sun saba,

 

_Husannsa & Jahad_

A 6angaren husanna dake kwance rai hannun Allah magashiyan, ba’a son inda kanta ya ke ba,

Likito ci sun gaza gane, menene matslarta, iya abunda suka sani tana da mental ilness sai asthma, bayan nan binciken su bai nuna masu komai ba,

Rashin kwanciyar hankali ne ya hana, jahad ta yi masu bayanin cewa tana da Iska, sam ta manta da wannan sbd ba natsuwa kullum cikin kuka take asibitin,

Atare suka shigo inda aka kwantar da ita, suna tattauna wa akan ciwonta, su biyu ne professional doctor ne wanda su ke kira da Babban likita (big doctor) tare da wani jami’in ɗan sanda, dr ɗin na koƙarin yi masa bayani akan yarinyar,

Sam basu lura da husanna wadda ke kwance, magashiyan sai faman fisge fisge take tana nishi, hannu tasa ta cire roban oxygen ɗin da suka sa mata, tari wurgi da shi, tana wani irin huci kamar zakanya, idanunta sun juye sun canza launi,

A haukace ta ƴunkura da ƙwarin gaske takai hannu ta zare bingidar dake soke ƙugun police man ɗin da suke magana da big doctor ba tare da saninsa ba,

sai da ta zare sannan likitan ya lura cikin tashin hankali yace “Innalallahi wa’inna ilahirrraji’un !!”

A firgice ɗan sandan ya shafa waist ɗinsa yaji ba gun ɗinsa, gaba ɗaya hankalinsu ya tashi ganin tayi sai ta su da ita, kuma ta rike maɗalllin, nan fa ido ya raina fata, lallashin ta suka shiga yi don ta ajiye bindigar amma ina, sai ma ta fisgi hanya da gudun gaske tana harba bindigar a duk inda ta samu ji ka ke daram!! Daram !! , zo ka ga yanda mutane ke gudu ba likitocin ba, ba nurses ɗin ba hatta marasa lafiyan dake kwance magashiyan neman hanyar gudu wa su ke yi, a tunanin su, ƴan bindiga daɗi ne suka kawo masu ziyara ta musamman 😂🤣😂

Jama’a gawa na tsoran rami, 😂🤣

Husanna fa ta haukace, misbehaving take yi kamar ƴar mahaukaciya,

Gashi dama ba hijabi ajikinta sun cire mata, da za’a kwantar da ita,

Wannan mahaukacin gashin, nata mai yawan gaske da tsayi ya bazo mata ta ko’ina har gaban fuskanta, tana gudu yana kara rufe mata ido ko gabanta ma bata kallo,

“Jama’a kowa ya watse, kowa ya gudu yayi takansa an samu matsala, mahaukaci ta gudo daga psychiatric hannunta riƙe da bindiga kowa yayi takansa,” 😆

Wani copral ne ke bada wannan annoucement ɗin,  don asamu kowa ya kare kansa,

Bin ta police men ɗin suke da gudu suna rokon tabasu bindigar nan, amma ina Husanna tayi nisan da bata jin kira,

Jahad ta gama rikicewa ganin bala’in da husanna ke ƙoƙarin ja, musu a guje itama take binta tana faɗin “Husanna dan Allah ki daina, kada ki kashe wani kija mana bala’i, dan Allah ki basu bindigarsu, innalallahi wa’inna ilaihirraji’un

Asibiti fa ya harmutse, kowa gudu yake yi , gashi ita husannar sai yawo take musu da hankali sai zagaye cikin asibitin suke, duk inda tabi mutane sai su watse, sai ihu ake ana zabga salati kai ka ce zombies ne suka bayyana,

Ƴan sandar sun fusata sosai ransu yayi mugun 6aci, kiris ya rage su harbe ta gudun kada tasa ayi asarar rayu ka, sbd ko’ina tasamu harbi take yi,

Abunda basu sani ba wannan ihun da ake yi shi ke ƙara haukatar da ita, bata cika son ƙara ba,

Sannan ita kanta husannar a tsorace take sbd police ɗin dake bin ta,

Tana cikin gudun nan hankalin ta atashe , gudu take amma tana waiwayon su cike da tsoronsu, cikin rashin sani kwatsam taji ta faɗa ajikin mutun,

Gam ta faɗa a faffaɗan ƙirjinsa, ta ƙankamesa, ta rungumosa sosai, a tsananin tsorace,

Nan take komai ya dakata, ji ka ke tsit kamar mutuwa ta gifta, babu mai kwakkwaran motsi acikinsu,

Gaba ɗaya duk suna tsaitsaye likitocin da nurses ɗin da wasu daga cikin marasa lpy masu ƙwarin jiki da ƴan dubiya, ga ƴan sanda , kowa dai

Saukar ajiyar zuciya kowa yake saki, ita kam jahad ta tsorata, da ganin mutumin da Husanna ta faɗama wa, duk da yasa face mask a fuskanshi, amma ƙirar karfin nan tasa, dole tasa hankali tashi,

Tsoranta karya ce zai hukunta Husanna da ta faɗa masa bagatatan,

A tare zuciyoyinsu ke bugawa, bugu bana wasa ba, ta kwanta luf ajikinsa, wato wata irin ni’ima ce atattare dashi wadda tasanya husanna dawo wa cikin hayyacinta lokaci guda, sam tagaza tashi daga jikinsa, ƙamshin turarensa ya gama kashe mata dukkan wani ƙwari na jikinta, 😌

Sai faman ajiyar zuciya take saki, hannunta ta ƙarasawa ta zagaye waist ɗinsa so tightly,

Ganin hakan yasa Soja  dake bayansa mai riƙe da mukamin major, yasa hannu ya zare gun ɗin dake hannunta , saboda ta zagayo da hannun nata a ƙugunsa ga bindigar a fili,

_NOT EDITED_

Keep sharing everywhere🫶 ❤️ Alhamdulillah ynx sai monday

*BossLady* 💋*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🌹🌹🌹Romantic Love story🌹🌹🌹*

Writer *HAFSAT BATURE* 💋

~Boss Lady~💋💋💋

*frm today, na dakata da rubutu har sai naji sauƙi insha Allah zan ci gaba, seriously bani lpy so i won’t kill my self* 😔👍

~page 71 to 72~ ✨

✨✨✨✨✨✨✨✨

Not edited, 👏

At same time heart ɗinsu ke beating da karfi, ya jima yana mamakin wata zararriya ce wannan ta faɗo masa a ƙirjinsa haka, this is d first time da mace ta faɗa masa a jikinsa, wadda ba muharramarsa ba, babban abunda ya ɗaure masa kai yadda yarinyar ta ƙanƙamesa bama Alamar zata sake shi, yana jin duk wani moving ɗinta ajikinsa, hatta numfashi ta dake fita cikin sauri sauri, kamar jinjira haka ta kwanta masa luf tana sauke ajiyar zuciya,

Mutanen dake wurin kowa yayi zuru yana kallon ikon Allah, wasu kam sai godiya suke wa Allah daya kawo masu sauƙi, har aka amshe gun ɗin dake hands ɗinta,

Jahad kam wadda ke cikin matsanancin tashin hankali, ganin bala’en da hosana ke ƙoƙarin ja musu, cikin yanayi na firgici ta ƙarasa inda hosana ke jikin bawan Allahn nan ta ruƙo hannunta da ƙarfi ta fisge ta daga jikinsa tana cewa “Dan Allah kayi Haƙuri bawan Allah, ba da sanin ta tayi hakan ba, she did it unintentionally, tana da ta6in hankali ne…..’ muryar na rawa Jahad ke kora masa bayani,

Har time ɗim bai cire face mask ɗinsa ba, kuma bai janye idonsa daga na Yarinyar ba,

“Ki rabu dani !!!!” honasa ta faɗi tare da cire hannunta daga na Jahad ta matsa wurin mutumin nan, da ta faɗa mawa ta sa hannunta cikin nasa ta riƙe kam tana kallonsa cikin muryar kuka tace “dan Allah ka rabamu da waɗannan masu baƙaƙen kayan wlh sun takurawa rayuwarmu, duk inda mu ke bin mu suke yi, wlh ba mu bane muka kashe ta ba, mun faɗa musu sunki yarda, ni dai kace su rabu ni in ba haka wlh zuciya ta bugawa zatayi na mutu kowa ya huta…..’

“Hosana !!! Ba ki da hankali ne !! Kinsan wanene shi ki !! meyasa ki ke tona mana asiri ne agaban mutane,” jahad ce tayi maganar ranta a 6ace ta janyo hosanar da karfin gaske ta dawo gefenta,

Su dae mutanen dake tsaye tare da police ɗin sun zuba ido suna sauraron su,

Rai a 6ace hosana ta sake fisge hannunta daga na Jahad cikin ƙunar rai tace “ki rabu dani, ki ƙyale ni nace !!! meyasa kowa bai son mune !!  Laifin me muka aikata, babu mai ƙaunar mu wlh Jahad ba zan koma cell ba sai dae a shigar da gawa ta, amma bani ba,’ tana gama fadar hakan ta koma wurin mutumin nan dae dake a tsaye, ta zura hannunta cikin lallausan tafin hannunsa ta rike gam, ta marairaice masa da kyawawan idanuwanta tace “Dan Allah ka tafi dani,ka da kabarni anan, bana son ganin waɗannan masu fararen kayan (wato likitocin dake tsaye da nurses ɗin dake wurin) kuma bana son waɗannan masu bakaken kayan,” ta faɗi tana nuna ƴan sandan dake tsaye baki asake suna kallonta,

kwantar da kanta tayi a damtsen hannunsa, sannan tasanya dukkan hannayenta ta rungumo nashi, (mutu ka raba kenan)

Lumshe idonsa yayi a hankali, sai lokacin kallon police men ɗin dake tsaye a wurin yace “wane irin shashanci ne yasa ku kabar yarinya harta kwaci bindiga daga wurinki!!”? Ya tambaya yana kallonsa,

Rai a6ace wani inspector yace “kaga malam ka iya bakinka, mu jami’an ƴan sanda ne munsan me muke…” tunkan ya ƙarasa major ɗin dake bayansa wanda ya fusata rai a6ace yace “Ka iya bakin ka !! Kasan wanene shi!!!”?

“maganar wanene shi bata shafe mu ba, mu dae a bakin aikin mu mu ke,” wani  inspector ne ya bashi amsa a yayn da ya fiddo da ankwa alamar zai sanya masu hosana,

Itakam ƙara kanƙameshi take yi, gaba ɗaya ta gama kashe mishi jikinsa, daurewa kawai yakeyi,

“Laifin me suka aikata”? Ya tambaya yana kallon ƴan sandar,

Wannan copral ɗin ne yayi saurin cewa “ana suspecting ɗinsu da kisan wata tsohuwa wadda take riƙonsu,”

Shiru ya ɗanyi tare da jinjina kai, kafin yace “Cancel the case (akashe case ɗin)”

ɗagowa su kayi jami’an ƴan sandan suna kallonsa cikin mamakin jin abunda yace, a fusace wannan inspector ɗin yace “malam wai wanene kai !! dame kake taƙama ne !! kaga ka kama gabanka kawai cikin salama, in ba haka ba, zamu haɗa dakai mu tafi police station…..’

Jikin major ɗin dake bayansa har tsuma ya ke yi wurin cewa,” Shut Up Stupid !!! ka iya bakin ka ƙaramin ƙwaro ko kuma nayi ƙasa ƙasa daku a wurin nan….’ cikin hanzari ya dakatar dashi tare da cewa “i did not allow u to talk again, last warn,’

Shuru major ɗin yayi sai faman huci yake yi tamkar zaki, rai a6ace ya wurgawa ƴan sandar bindigarsu ƙasa,

Matsawa Inspector ɗin yayi da nufin yasanya wa hosana ankwar dake hannunsa, amma sai mutumin ya dakatar dashi da cewa “karka kuskura !!! domin ban bada izini atafi da yarinyar nan cell ba, kamar yadda ta roƙe ni cewa bataso ta koma, daga nan ba inda zata je,”

Mamaki ne ya rufe ƴan sandan, inspector ɗin yace “idan ka cika shisshigi zamu sa bindiga mu kashe ka !! A wurin nna,”

Jinjina kai mutumin yayi tare da cewa “idan kuka kashe ni, ba hukumarku kaɗai bace zata shiga haɗari ba, gaba ɗaya sai an tada nigeria saboda raina kawai,”

Kansu fa ya gama ɗaukar zafi kowa mamakin wannan mutumin ya keyi, ganin ya toge yaki bari su ta6a yarinyar dake kwance ajikinsa yasa inspector ɗin cewa “wai dan Allah wanene kai!!”?

“Yanzu naji bayani” acewar mutumin bayan ya faɗi hakan ya zura hannunsa cikin aljihunsa ya zaro ƴar waya nokia, ya yi dialing wasu numbers da basu fi 5 digits ba ya miƙa wa, inspector ɗin wayar yace “Ka kira numbers ɗin dana sanya ka tambaye su*WANENE MARSHAL OMAR* za ka samu amsar da kake so,”

Jikin kowa yayi sanyi jin ance marshal, shi kansa inspector ɗin yana ɗan sauko, hannu yasanya ya kar6i wayar, ya danna call tare da karawa a kunnansa, one bugu on ɗauka, cike da kwarin guiwa ɗan sandar yace “WANENE MARSHAL OMAR, cikin harshen turanci yayi tambayar yana jiran amsa daga cikin wayar,

tunkan ya cire wayar a kunnansa, wasu irin jibga jibgan motoci ne suka soma antayo wa cikin asibitin aguje masu ɗauke da fusatattun sojoji zafafan gaske, runduna guda kamar a filin yaƙi, zaro ido su kayi gaba ɗayansu cikin tsananin mamaki, kowa dake kallon wannan al’amar tsantsar mamaki ne a fuskarsa,

Da gudun gaske sojojin nan suka shiga dirowa daga saman motocinsu kowanne riƙe da manyan bindigogii, da gudun gaske suka tunkaro inda Marshal omar yake sukayi masa ƙawanya, tare da buga ƙafa suka sara mashi sannan suka haɗa baki wurin cewa “We’re waiting for your command Sir  !” (Umarninka mu ke jira yalla6ai) 😳

Gaba ɗaya hankalin kowa yayi mugun tashi, sun tsorata ainin ganin sojojin ma ba na nan qasar bane, Black americans ne masu wata irin ƙira ta zakuna, kai kana ganinsu ba ɗigon Imani a fuskarsu, umarninsa kawai suke jira, koda hospital ɗinne su tada gaba ɗayansa 😳

Cikin rawar murya ɗan sandar nan wanda yaci ka zaƙe wa yace “Yalla6ai, dan Allah wanene kai”?

“dan Allah ka miƙa masa wayarsa, salin alin mu tafi,” acewar wannan copral ɗin daya gama tsorata,

Hosana ta firgita sosai, amma maimakon ta cire hannunta daga nasa, sai ma ta ƙara ƙanƙamesa sosai, duk yana jin motsin hannun yarinyar acikin nasa, ita kuwa jahad ƙiris yarage tasaki fitsari don tsabagen tsoro, gashi tayi tayi da hosana ta janye hannunta daga nashi amma taƙiyi,

Hankali fa ya tashi, kowa da ke wurin so yake yaga fuskar marshal Omar, sun jinjinawa ƙarfin ikonsa, .

“Yalla6ai! dan Allah ka karbi wayarka, wlh zamuyi biyayya akan abunda kace,” acewar wannan copral ɗin,’

sai lokacin Marshal Omar yasanya hannu cikin natsuwa, a hankali tare da zame face mask ɗinsa, Wow zo ka ga ido

Cikin wannan Cool voice ɗin tasa yace “Sunana Marshal Omar, U.s Army ni ɗane ga Chief of Army staff wato Abban sojoji,’

tunkan ya idasa maganar tasa gaba ɗaya police ɗin dake wurin suka sara masa, hatta sauran mutanen dake tsaitsaye a wurin duk suka sara mashi jin sunan daya ambata,

“Nayi muku uziri ne, saboda na lura bakusan koni wanene ba, duk da nayi mamakin hakan,”

Sauke hannayensu su kayi, Tabbas sai yanzu suka shaida shi, abunda yasa suka rikice sun san cewa Marshal Omar ɗin da su ka sani suke yawan gani tare da SGR ba anan suke zaune ba, kuma basu ta6a tunanin zasu ganshi ido da ido ba, sun saba ganinsa a kafafen sada zumunta, shiyasa su kayi tsammanin ko raina musu hankali zaiyi, gashi kuma yayi hiden face ɗinsa da mask sannan, babu uniform ajikinsa shiyasa komai ya shige musu,

“Ynz yalla6ai ya zamuyi kenan? Domim Case ɗin yaran ya kai har wurin commissioner of police, cikin week ɗin nan ma muke shirin miƙa su court don gudanar da shari’a, rashin lpyr yarinyar ne ma ya dakatar da komai,” inspector ɗinne ya kora masa bayani,

“Ku bar komai a hannu na, zan yi magana da commissioner ɗin, zaku iya tafiya,” ya basu umarni

Yayi magana tare da amsar wayarsa daga hannunsa, ba musu ƴan sandar suka kama hanya tare da barin asibitin suna masu tsananin mamakin ƙarfin ikon Marshal Omar lallai shi ba ƙaramin jan wuya bane 💪💪💪

(Yanzu shikenan an kashe case ɗin su Hosana da jahad kurmus ya mutu) 😁😬

Mutanen wurin gaba ɗaya murmushi kawai suke saki, kamar a shirin film haka suke kallon lamarin, haƙiƙa marshal Omar ya gama tafiya dasu,

Ajiyar zuciya kawai Jahad ke saki tarasa me zatayi don farin ciki, sam bakinta taƙi rufuwa (shin bana faɗa muku ba? Cewa dukkan tsanani yana tare da sauƙi? Sannan bawani yanayi na arayuwa da yake kasance wa na dundundun ba? this is an example) 💞😊

Murmushi kawai hosana ke saki, sam taƙi barin jikinsa har sai da yace “My hand” sannan ta janye jikinta, daga nasa tana zazzare masa waɗannan kyawawan idanuwan nata, sai faman murmushi take zabga mashi, shi kam binta kawai yake yi da kallo,

“Kowa ya koma bakin aikinsa!!” Marshal Omar ya faɗi yana kallon jama’ar dake wurin, cikin sauri doctors ɗin dake wurin da nurses ɗin da other peoples ɗin suka watse,

Ajiyar zuciya yasaki tare da mayar da eyes ɗinsa akan major ɗin dake bayansa yace “A tafi da twins ɗin nan, akai munsu gidan goggona, asanar da ita cewa zandawo later,”

Ya ƙare maganar da cewa “asan irin driving ɗin da za’ayi dasu,” murmushi kawai major ɗin ke saki, aransa yace “Oga fa yayi kamu da alama, Allah yasa ayi da ran mu” 😇

A fili kuma yace “Consider it done Sir!!”

Haka suka tasa ƙeyarsu hosana, waɗannan hot soldiers ɗin suka sasu agaba, har aka fice dasu marshal Omar bai dauke idonsa daga kan yarinyar ba, sai da yaji tashin motocinsu sannan,

Haka motocin nan suka fice dasu, daga asibitin, 😊

Police ɗin nan yajima yana mamaki, daga cewa wanene marshal omar sai kawai yaga rundunar sojoji, sojojin ma bana nan ba tab, lallai ba ƙaramin Jan wuya bane, 💪

Murmushi kawai babban likita ke saki wanda ya rage a wurin tsaye, sai lokacin marshal omar ya lura dashi, cikin sauri ya ƙarasa tare da hugging ɗinsa yana cewa “Am sorry ban lura dakai ba wlh,”

Babban likita yajanye jikinsa tare da cewa “Shege Omar ! Mutanen U.S wlh yau ka bani mamaki, kayi matuƙar burgeni sai naga abun kamar ashirin film, shin wai ma ni dirar yaushe ? dama ka shigo garin kenan ?

Ɗan ƙayataccen murmushi marshal omar yasaki tare da cewa “3 weeks kenan da zuwan mu, tare da Captain mu ka taho daga kd shi ya wuce zariya wurinsu ammi ni kuma na wuto nan kai tsaye, tomorrow insha Allah zan juya nima,”

Ruƙo hannunsa babban likita yayi suka tunkari office ɗinsa, domin samun damar tattaunawa dakyau, sai faman murmushi yake saki, Allah sarki ɗan uwa mai daɗi, yama rasa ina zai sa Marshal Omar saboda tsabar farin ciki,

Yana lura da nurses ɗin dake ta faman leƙensa, wato sun ƙyasa koda yake dole ne abunda ya faru ya burge kowa,

A office ɗinsa suka zauna, ga sanyin A.c komai tsaf tsaf, suka zauna suna facing juna,

“Bari nasa akawo maka abunsha,” acewar Babban likita, cikin sauri umar yace “A’a no need”

“Wai ni kam ina SGR? wato shi bazai ajiye makaman yaƙin nan ba , yazo ya kawo mana ziyara ba ko”?

ɗan murmushi omar yayi tare da cewa “rikicinsa da Ammi ne, kasan tace ita ƴa’ƴan fatima, ba jinin ta bane don haka bata buƙatar, waninsu ya sada zumunci da family ɗinta,” .

tsoki doctor yaja rai a6ace yace “wannan guyababban jarababbiyar tsohuwar bansan meke damunta ba, ƙiri~ƙiri ki tsani yara grand child ɗinki kuma? inace faɗanta da Aunty fatima ne ba da su ba, haba !!” ya ƙare mgnr cikin ƙunci

Omar yace “Abun yana damuna nima, especially yadda take nunawa su junaid tsana batasan su ƙiri-ƙiri, yanzu ni ba wannan ba game da Twins ɗin can,’ ya ɗan dakata da maganar,

Murmushi big doctor yayi tare da cewa “me kake son sani game dasu”?.

“Me ke faruwa dasu ne, kuma wacece bata lafiya acikinsu, sannan ina iyayensu ne “? Omar ya tambaya cike da son jin taƙaitaccen bayani,

Gyara zama dr ɗin yayi tare da cewa” ita wadda ta faɗa maka ajikin ka, itace bata da lpy, she has a mental illness har aiki ma an ta6ayi mata, ina ji anan asibitin ne, sannan tana da asthma, bansan dae taƙamaiman labarinsu ba, amma ita ɗayar mai hankalin munyi magana da ita, ta gayamun cewa, basu da kowa a hannun wata tsohuwa suke, so tsohuwarce ta rasu kuma bincike ya nuna cewa poison aka bata, tace mun basu ne suka kashe ta  ba, iya abunda nasani kenan,”

Shiru Omar yayi na ɗan wani lokaci kafin yace “zanyi binci ke akansu amma ba ynx ba, suna buƙatar kulawa ssae, ynx ita mara lafiyar, me take bukata,” .

“drugs  ne kawai dama ake bata, ynx ma already na rubutamusu waɗanda zata yi amfani dashi, sannan suna buƙatar abinci mai gina jiki sosai tabbas, akwai yunwa atattare dasu,’ babban likita ya kare jawabin yana kallonsa,

Shiru yayi baice komai ba, yana wani tunani,

” ynx ya zakayi da twins ɗin naji kace akaisu wurin goggonku,” babban likita ya tambaye sa, .

Ajiyar zuciya Omar yasaki tare da cewa “as frm now dukkan wani responsibilities ɗinsu ya dawo underneath ɗina ! ban damu da sanin su wanene parent ɗinsu ba ko family ɗinsu, saboda banga kowa atare dasu ba, that means anyi watsi dasu, don haka na mallakawa kaina su !!!!!

Wani irin Murnushi babban likita  yake saki yana kallonsa, wannan ƙarfin halin da ƙwarin guiwar Omar ba ƙaramin burgeshi su ke yi ba, .

Sam bakinsa ya gaza rufuwa don murna cikin tsananin farin ciki yace”haƙiƙa Omar kai na dabanne ko acikin mutane, halin ka na musamman ne, ka cancanci fiye da komai ma, Allah yasa ka maka da mafificin alkhairi, ya ci gaba da ɗaukaka ka, sakamakon wannan ceton da kayi Allah yasa ka maka da gidan Aljanna first step,”

Murmushi kawai Omar ke saki, shikam babban likita ya gaza rufe baki addu’o’i kawai yake masa, a ƙarshe yashe “Allah yasa su zama Alkhairi agare ka,”

“Ameen” ya amsa mar,

………………..SEHRISH………………….

Tsaye take tana leƙen su junaid dake buga ball a cikin filin kwallon dake a gidan ,

ta cikin window take leƙensu, tana murmushi, tashin ta kenan bayan ta koma baccin da suka kammala breakfast,

Jersey ɗin dake jikinsa ba ƙaramin kyau su kayi masa ba, abunka ga farar fata, yellow ne kayan kwallon sai faman tsalle tsalle ya keyi, dama shi indai wurin wasa ne da ci a nan yafi auki,

Tare da wasu daga cikin sojojin dake tsaron gidan suke buga ball ɗin,

dariya kawai take yi masa, ganin sai zura wa da gudu yake yana taro ball ɗin su kuma suna kwace ta,

tunano wa tayi da farkon zuwanta gidan, lokacin da motar Hajajju ta shigo da ita cikin gidan, tabbas tagansu a time ɗin suna buga wasan kwallo,

kamar yadda dae take kallonsu a yanzu, amma awancan lokacin, shi dasu twins ne da fawan suke kwallon, sa6anin ynx da masu gadin gidan suke buga wasan,

“Allah sarki junaid, ji bi yadda yake ta faman shan wahala wurin taro ball suna kwace mashi, maimakon yaji haushi amma sai faman murmushi ma yake yi, shi dae baya gaji da murmushi a face ɗinsa,”

Tayi maganar nan a lokacin da take ƙoƙarin zuge glass ɗin windon, ta janyo labulen ta rufe, tana sauke ajiyar zuciya,

tunanin ta ya koma kan Babban yaya wanda tun da safe take jiran saukowarsa, amma bai fito ba, ko breakfast bai sauko ya ci ba, hakan yasa ta cikin damuwa sosai,

“Bari dae na fita naje na tambayi aunty azmee, ko naje na tashe shi in bacci ya ke yi “?

tayi maganar a fili, cikin sauri ta ƙarasa saman bed ɗinta, ta ɗauki dogon wandonta ta zura, dama daga ita sai riga dai-dai guiwa,

Gashin bakinta kawai ta ɗauko a saman mirror, ta maƙala shi kafin ta fice daga ɗakin,

A hankali take tafiya, a main parlor ɗin ta hangi su Abbansu tare da wani Amininsa Alhajin gaske daya kawo masa ziyara,

Su biyu suna tattaunawa,

saɗaɗawa tayi ta wuce kitchen, anan ta sami aunty aunty azmee tana shirya musu drinks a tray, cikin wasu kofuna masu kyau,

“Yauwa rishi dama yanzu nake ƙoƙarin zuwa na tashe ki, kin barni da aiki ko,” ?   ta tambaya tana kallonta,

Cikin jin kunya Sehrish tace”Am sorry aunty azmee wlh, ina shiga bedroom ɗina naje na watsa ruwa, kawai sai bacci 6arawo ya ɗauke ni,”

Dariya azmee tayi azmee tayi tare da cewa “Bacci 6arawo ko? mutun yaje ya saki baki yana bacci, kuma yazo yace wa mutane wai baisan ya akai bacci ya ɗauke sa ba,’

Murmushi sehrish tayi tare da miƙa hannu ta kar6i tray ɗin da azmee ke miƙa mata,

Amsa tayi tana cewa “Aunty azmee wanene baƙon da yazo “?

“Ki je ki tambaye sa mana, ki ce wanene kai zai baki amsa,”

Dariya sehrish tayi jin amsar da azmee ta bata, ɗan zaro ido tayi tare da cewa “tab dana sha mari wlh,”

Azmee tace ” ba wani mari wlh, amsa kawai zai baki da yaren da zaki gane,”

“Ae wannan bugu kenan,” ta faɗi tana kokarin fita, har ta sa kai zata fice ta kuma juyo wa tare da cewa ” Aunty azmee babban yaya fa, bai fito daga bedroom ɗinsa ba ko lpy,”?

“Ki je part ɗinsa mana ki tambaye sa,” ta faɗi cikin zolaya, ɗan ta6e baki sehrish tayi tana jinjina kai tace “wai Allah ! ni asuwa? ɗan wake a hotel,”?

dariya azmee tayi tare da cewa “ynx dae kije ki kai musu, kin tsara surutu kamar ƴan jarida, ”

Cikin sauri sehrish ta fice  izuwa cikin main parlor ɗin, cikin natsuwa take tafiya tunkan ta isa, tajiyo muryar abokin abban dayazo yana cewa “Ae ni ba ƙaramin daɗin zuwan nan nasu  Rafayet da Omar naji ba, koba komai kafin su koma U.s zasu gyara wa wasu zama A Qasar nan,”

Abba yace “Oh damuwarka kenan, baka damu da bala’en da zai jawo mun ba, kwarama Omar shi da sauƙi, amma rafayet kana ganin last da yazo ya rinƙasa ana kawo masa ƴa’ƴan mutane har cikin gidan nan yana hukunta su, babu yadda zanyi dashi, sai dae nabishi da ido kawai, saboda yafi ƙarfi na,’

Dariyar Alhajin yayi tare da cewa “Ae samun ƴa’ƴa kamar Omar da rafayet wlh abun alfari ne, kowane Uba zai so ya mallaki ƴa’ƴa irinsu, gashi ynx asanadinsu darajarka da ta family ɗinku ta ɗaukaka sosai a faɗin duniyar nan, Kowa yabonsu ya ke yi, yakamata karinka alfahari dasu, mu gana mu nan ƴa’ƴan shaggu kamar mata, basa iya ta6akawa ƙasa komai, ga Jabeer nan har asibiti na gina masa in yadawo daga Uk ya ci gaba da kula dashi, amma yaron nan ya watsa mun ƙasa a ido, wai shi yafin karfin ya yi aiki a nigeria, Naji haushi lokacin duk mun lalacewar kasarka ae ƙasarka ce,” Cikin nuna takaici Alhajin yakewa Abban wannan bayanin

da sallama Sehrish taƙarsa cikin girmamawa ta gaishe su, suka amsa mata sannan ta miƙa musu drinks din suka ɗauka suna sa mata albarka,

bayan sun gama ta kama hanyar komawa cikin kitchen, wani irin son Babban yayan ne ya kara shiga ranta, jin yadda Abokin abban nasu ke yabonsa, murmushi kawae take saki, ynx ta kara jin ya kwanta mata luf acikin ranta,

Shiga kitchen ɗin tayi tare da ajiye tray ɗin, azmee tace “yanzu sai ki je, ki gyara masa part ɗinsa ko?  tayi maganar tana kallonta,

Sehrish tace “Yana fa ciki, kuma kince baisan atashe shi yana bacci, kuma baisan ƙara, in nayi kwaratsi fa zai ji harya farka,”

Murmushi azmee tayi tare da cewa ” to ina ruwanki da bedroom ɗinsa? Falonsa zaki fara gyara wa, kafin ya tashi sai ki gyara can ɗin ko ?

Sehrish tace “To bari nace”

tafice tana fargaba, tana jiyo muryar Aunty azmee tana cewa “Anaso ana kaiwa kasuwa,”

Ƴar dariya tayi tare da fi ce wa, kai tsaye part ɗinsa ta wuce zuciyarta na ɗar ɗar,

Kamar kullum a buɗe door ɗin parta ɗinsa take, a hankali tashiga tana sanɗa kamar 6arauniya,

Sai da tayi tsakiyar falonsa nasa tasoma tunanin wai me ma tazo yi? Saboda ko’ina agyare yake tsaf ba datti ko kaɗan, sai walwali wurin yake har yau tana jinjinawa haɗuwarsa,

Murmushi tasaki tana wani tunani aranta, wanda bazai yiyu ba, 😔

Sai da tagama zagaye falon nasa tana tunani iri iri aranta, sannan ta soma gyara sa, babu wani aiki awurin, kawai ta ɗan yi goge goge ne,

tsayawa tari riƙe da waist ɗinta, so take ta sashi a idonta,  zuciyarta ce ta bata shawara da cewa “ki ɗan leƙa sa, mana,”

“Anya? idan kuma idonsa biyu fa? In ya kama ni karairaya ni zae yi Allah,’ ta bata zuciyarta amsa,

“Ke sai ki bari ya ganki? Ae lalla6awa zakiyi a hankali sai ki dan leƙa,’

Murmushi tasaki tare da tafiya cikin sanɗa, ta tsaya a bakin ƙopan ɗakin nasa, taci sa’a kopan a bude take, curtains ɗin ta ɗan janye tana leƙensa, 👀👁️

Kwance ya ke yana sharar baccinsa, cikin natsuwa a saman Royal bed ɗinsa, kai ka ce da zallar gold aka ƙera gadon, yadda ya ke wani kyalli ajikinsa,

Half body ɗinsa yayi covering ɗinsa da lallausan blanket, hannunsa na dama, ya zagayo dashi har izuwa saitin left ear ɗinsa, yayin da hannunsa na hagu kuma ya ke a saman wide chest ɗinsa,

Bin shi take da kallo kamar kura taga nama, wannan haɗaɗɗiyar sumar tasa, ta rufe masa half face ɗinsa, dogon hancinsa kawai take hange,

Lumshe ido kawai take, ita kaɗae tasan yanayin da ta shiga,

Tana cikin wannan leƙen nasa ko ƙeftawa babu,  taji an shaqi wuyanta da ƙarfin gaske, Shaqa ba ta wasa ba,

Wani irin tsoro ne ya ziyarce ta, hankali atashe ta zazzare idanunta,

Muryarsa ce ta ratsa kunnanta da cewa “meyasa ki ke leƙe na !!”?

wata irin zufa ce ta wankowa sehrish, tsananin tashin hankali ne ya bayyana a idonta, lokacin da ta lura cewa babu shi asaman gadon nasa, yaushe har ya sauko yakuma wuce ta, ya zagayo ta bayanta,harya shaƙi wuyanta,

Wani irin fitsari ne mai zafin gaske ya kufce mata, ji kake zirrrrrrrr yana zubo mata,

Muryarsa ce ta sake karaɗe kunnanta, ” baza’a bani amsa ba” 😳😳😳😳😳😳😳

*Hafsat Bature Moh’d Boss Lady* 💋✨👏

*I Need your prayers urgently* 😔💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

_💞Extraodinary Love💞_

*Writer✍️✍️✍️✍️*

*💋HAFSAT BATURE BATURE BOSS LADY💋*

Full episode

~Page 73 -74

End of Chapter 1

*✨✨LAFAZI WRITERS ASSOCIATION* ✨✨

Not edited 😎

Jin shiru ba ta da niyar bashi amsar yasa shi harya fusata, a wani irin zuciye ya buga kanta jikin kopan da ƙarfin gaske, nan take sehrish ta fasa wata irin azababbiyar ƙara mai sauti tare da faɗuwa yaraf a sume,

Wannan sounds ɗin da sehrish ta fidda ne ya farkar dashi daga dogon baccin da ya ke yi, a hankali yake buɗe eyes ɗinsa yana yamutsa fuska agajiye blue eyes ɗinsa na facing Ceilling,

Hankali tashe sehrish ta farka daga nap ɗin daya dauke ta, sai uwar zufa ke zubowa daga cikin sumar kanta, ashe bayan ta kammala gyara masa parlor insa bacci ne ya ɗauke ta a nan kasan lallusana carpet ɗin dake shimfiɗe, sai faman zazzare kyawawan idanuwanta take, tana shasshafa jikinta don ta tabbatarwa da kanta cewa mafarki ne take ba gaskiya ba,

Ajiyar zuciya ta saki tare da faɗin “Alhamdulillah Allah na gode maka,” cikin hanzari sehrish ta miƙe tare da fice wa daga part ɗin nasa ta koma kitchen ,

Shiru tayi tana ƴan kame kame ashe tun ɗazu azmee na zaune tana jiran.dawowarta,

Tana zaune saman daya daga cikin dining chairs dake a kitchen ɗin, ga tray da ta kammala shiryawa babban yayan breakfast ɗinsa ajiye a saman table ɗin gabanta, ta zabga tagumi tana jiran Sehrish,

Bin ta tayi da kallo ganin yadda ta shigo a hargitse tana wurwurga ido,

“Sannu ko’? Shanyar da ki kayi harta bushe,” ta faɗi tana kallon ta,

Sunnar da kai sehrish tayi tana wasa da fingers ɗinta tace “Am sorry aunty azmee wlh bacci ne ya kwashe ni a falonsa without my knowing…’

tunkan ta ƙarasa azmee ta katse ta da cewa “bacci !!! A part ɗinsa!? Kin sha giyar wake ne?anya ko kinsan wanene SGR kuwa? You ave to be very careful sehrish, don’t let that happen again if not u will Explain it !!,”

Azmee ta faɗi cikin faɗa faɗa, hakan ba ƙaramin tayarwa Sehrish da hankali yayi ba, ta tsorata sosai tuni eyes ɗinta sun cicciko da kwalla,” .

“Aunty azmee tsotsai ne, ba da sani na ba nima, wlh sharrin shaiɗan ne,”

Sototo tayi da baki tana kallonta cikin takaici tace “na gane Ki  sehrish whenever u did something wrong sai ki ce sharrin shaiɗan ko? ga iya bada hakuri kamar matar aure tagari,’

duƙar da kai sehrish tayi, jikinta ya gama mutuwa jin aunty azmeenta nayi mata faɗa,

ganin halin da sehrish ta shiga yasa azmee sassautawa da murya cikin lallashi tace “Sehrish ba faɗa nake miki ba, i just wanna u to be very careful in this home, bana so asamu matsalar da zata sanya a kore ki daga aiki, Babban yaya da kike gani mutun ne mai hatsarin gaske !!!, sai kin kula,”

Cikin sauke ajiyar zuciya sehrish tace “Shikenan aunty azmee, insha Allah zan kula, i won’t let that happen zanyi komai yadda ki ke so,”

Murmushi azmee tasaki tare da cewa “yawwa my daughter, ko da yake nafiso nace ƙanwata hakan yafi mun daɗi, yanzu dae ɗauki breakfast ɗin nasa ki kai masa,”

“Tom aunty azmee,” sehrish ta faɗi tare da sa hannu ta ɗauki tray ɗin, da ƴar fara a a fuskarta ta fice daga kitchen ɗin,

A natse take tafiya, zuciyarta na bugawa especially in ta tuna abunda Aunty azmee ta sanar da ita nacewa he’s a dangerous man, hakan na kara tsoratar da ita,

tana cikin tafiya taji dirar Ball a ƙasan kafarta, ƙiris ya rage ta saki tray ɗin saboda ta tsorata, bin ball ɗin tayi da kallo kafin ta ɗago taga wanene ya jefo mata ita,

Sai faman murmushi yake ta saki, kamar gonar auduga, bawan Allah yasha wahala, kwallo kamar ibada duk zufa ajikinsa sai wanko masa face ɗinsa take,

“Junaid” ta faɗi acikin zuciyarta, a fili kuma sai cewa tayi “Sannu da dawowa”

Sam yaki mata magana, tun da yasa ta a idonsa, notikan kansa suka kwance, zallar ƙaunarta ce ke gudana a cikin zuciyarsa, karasawa yayi tare da duƙawa Yayi yakai hannu ya dauki ball ɗinsa, sannan ya ɗago tare da aza eyes ɗinsa cikin nata yace “Yunwa nake ji, ashirya mun snacks akawo mun a bedroom ɗina tare da coffeee i wll be waiting,, ya ƙare maganar yana kashe mata jiki da wannan smilling ɗin nasa,

Ita ma kanta batasan time ɗin da, ta shiga mayar masa da martani ba, na murmushinsa, tarasa dalilin dayasa take jin wani sanyi a ranta aduk lokacin da idonta suka shiga cikin na junaid (Why?)

daker ta amsa Iya amsa masa da cewa “insha Allah ynx zan kawo,”

“Ok” ya faɗi tare da bi ta gefenta ya wuce upstair duk tana, a tsaye tana kallonsa, ƙiriniyarsa na burgeta sosai,ko tafiya yake yi yana dan tsalle haka, .

Sai da junaid ya 6ace mata, sannan itama ta wuce sashen sgr ,

Time ɗin da ta karasa a bakin kopan sai da ta tsaya ta karanta addu’o’in neman tsari da sharrinsa sannan, ta shiga ciki da sallama,

Ba zato ba tsammani taji wannan sanyayyiyar muryar tasa so sexy ta amsa mata da cewa “Wa’alaikam salama,”

Wurgo ido tayi ta hangosa kishingiɗe saman royal sofa ɗin doguwa, kansa na saman hannun seater ɗinta, yayin da idonsa ke kan Laptop ɗinsa wadda ya aza ta saman stomach ɗinsa, kasancewar yana daga kwance, jikinsa na sanye da jallabiya fara, masha Allah kyau iya kyau, ba’a magana, masu sa kyau tayi kyau ba 😂

Jikinsa sai kamshin turaren imperial majesty ke tashi, wani irin daddaɗan kamshin kasancewar duk wani lotion da soap da yake using dasu bama perfumes ba kaɗae masu kamshi ne na fitar shari’a, kasancewar shi, ma’aboci son ƙamshi ga tsafta,

Lumshe ido sehrish tayi, tana jin wani irin heart beating, kamshin sa na rikitar da ita,

A hankali take tunkararsa, sai da taje dab dashi sannan murya na rawa tace “Gm sir,”  shiru bai bata amsa ba, hakan yasa ta jin fargaba,

Zuru ta ɗanyi tana tunanin kawai ta ajiye masa ta fice, har time ɗin eyes ɗinsa nakan Laptop ɗinsa yana daddanawa,

har ta ja da baya zata ajiye masa tray ɗin a samar tables ɗinsa muryarsa ta ratsa ta da cewa “Is this the right time daya dace a kawo min breakfast ɗina “?

Shiru sehrish tayi gabanta na faɗuwa, a cikin zuciyarta kuwa tsantsar tashin hankali ne, tabbas akwai matsala, saboda ita azmee ta sanar da ita cewa ba’a tashin shi daga bacci in yana yi, and now kuma yana complain ba’a kawo masa breakfast ɗinsa da wuri ba? to tayaya mutumin da ba’a tashin sa daga bacci zaisan ankawo masa breakfast ɗinsa da wuri !!!?

wannan jinkirtawar da tayi bata bashi amsa ba, ya sashi fusata, aiko tana a tsayan nan ba ta lura ba, ya ƴunƙura yasanya ƙafarsa da karfin gaske dama ga tsayi ya harba tray ɗin dake hannunta, nan take komai ya kife ƙasa, ya tarwatse food warmers ɗin da sauran tarkacen, zaro ido tayi tare da dafe ƙirji gabanta na faɗuwa, tsananin tsoro ne ya bayyana a fuskarta,

Cije lips ɗinsa kawai ya keyi, ganin koma wanene yaƙi moving, wani irin motsi taji bana wasa ba, aiko da gudun gaske ta fi ce daga falonsa, wato da ace sehrish tabari wannan motsin da taji yayi da ba ƙaramin naushi zai kai mata ba,

Kamar daga sama su ka ci karo da azmee wadda ke ƙoƙarin Fitowa daga kitchen ɗin, tana ganin sehrish gabanta ya faɗi, aranta tace “yayi tsiyar,”

Fashewa tayi da matsanancin kuka a lokacin da taganta, agaban azmee jikinta har wani jijjiga yake yi, sai kerma la66anta ke yi,

Hankali tashe azmee tace “menene sehrish me ya faru,? ta faɗi tana jiran bayani daga wurinta,

daker kukan da sehrish take yi ya tsagaita, cikin matsanancin kuka take korawa azmee bayani,

” …aunty ..azmee…baaa…ke ki ka ce ba’a tashin sa daga bacci ba….ynx fushi ya keyi ba’a kai masa breakfast ɗinsa da wuri ba..ba ki ga yadda yasa ƙafarsa ba ya harba tray ɗin abincin komai ya watse, bansan ya zanyi ba,” tana magana tana yarfa hannu, sai faman jan majina take yi, duk ta firgice,

Shiru azmee tayi saboda dama ba wannan ne karo na farko da yake faɗin cewa ba’a kaimasa breakfast ɗinsa da wuri ba, gashi mafi yawancin lokutta bacci yake yi, kuma ba uban da ya isa ya tashe shi yana bacci, saboda kamar ɗan wrestling haka yake, Naushi yake kaiwa, gaba ɗaya kannensa su fawan dasu Irfan ba wanda baije tashe shi daga bacci batare da ya naushe shi ba, shiyasa kowa yayi nesa dashi, ake barinsa sai ya kammala baccinsa ya tashi dakansa, sannan kuma ya hau jarabar ankai masa karin kumallonsa a makare,”

“Aunty azmee ba ki ce komai ba, ya zanyi? gashi can ya 6arar da abincin shima wata matsalar ne, ya za’ae abashi hakuri na samu naje na kwashe wanda ya zubar na zuba masa wani”?

ta ƙare maganar tana kallon azmee wadda tayi zuru cikin rashin sanin mafita,

yarfa hannu azmee tayi tare da cewa “wlh nima bansan menene solution ba, mutun ɗaya ne zai iya shawo kansa, kuma ba kowa bane face Junaid….”

“Naji kamar ana maganata a wurin nan,” junaid ne yayi maganar wanda ke saukowa daga saman stair ɗin, jikinsa sanye da jeans da farar t shirt,

Bin su yayi da kallo musamman sehrish wadda ke tsaye, ido luhu luhu tasha kuka, yau taga tashin hankali,

Ajiyar zuciya Azmee tasaki ganinsa cikin sauƙi,

“Junaid matsala aka samu,” azmee ta faɗi tana kallonsa,.

“Meya faru”? Ya tamvaya yana kallonsu,”

Nan azmee ta kwashe dukkan abunda ya faru ta sanar mishi, kamar yadda sehrish ta faɗa mata,”

Murmushi yasaki tare da kallon sehrish wadda ta sunnar da kanta kasa, yace “Calm down ur mind, in dai Babban yaya ne, ni ne controller ɗinsa, just wipe ur tears,” ya faɗi yana nuna tears ɗin dake zubowa daga eyes ɗinta,.

Hannu tasa tana goge su kamar yadda junaid ya bata umarnin ta share su,”

Sannan yace da aunty azmee “a shirya masa wani breakfast ɗin, ynz zan zo na karba,” yana  gama faɗan hakan ya juya tare da wuce wa izuwa upstairs part ɗin Sgr,”

“Yanzu sai kiyi murmushi, junaid da ki ke gani shine masarrafin babban yayansu, shi ke juya shi kuma ya juyu,” azmee ce tayi maganar tana kallon sehrish,

Ita dae har yanzu bata dawo cikin hayyacinta ba, ta jima tana mamakin abunda sgr yayi, yadda ya hauro da ƙafarsa ya harba tray ɗinta ya kife kasa ba ƙaramin mamakin hakan tayi ba, maimakon taji haushinsa, sai ma taƙara jin ƙaunarsa na ninkuwa azuciyarta 💋

Da sallama junaid ya shiga falonsa yana faɗin ” babban yayan mu, gani na iso, nazo na takura maka na hana ka sukuni,”

Jin Voice ɗin junaid yasa, Rafayet tashi zaune daga kishingiɗen dayake, ya mayar da laptop ɗinsa, saman desk ɗinta, a hankali ya ware idonsa akan junaid tare da cewa “sai ynx zaka so wurina? Ina ta fama da yunwa arasa wanda zai tashe ni ko”? yayi maganar yana lumshe sexy blue eyes ɗinsa,.

da murmushi junaid ya karasa yana faɗin “am so sorry babban yayanmu, kaima kasani, na damu da cikin ka sosai, shiyasa ko breakfast banyi ba tun safe, kai kawai nake jira ka farka muci atare” ya karasa maganar tare da russinawa ya rungumosa sannan ya manna masa kiss a gefen face ɗinsa,

Lumshe idonsa yayi, har cikin zuciyarsa, tsananin kaunar yaron ya keyi ba don komai ba, sai don kasancewarsaa mai tsananin biyayya ga iya magana, minti 5 yayi yawa ga junaid ya sace zuciyar mutun especially da wannan murmushin nasa, shiya sanya Hafsat bature ta kamu da tsantsar ƙaunarsa 😥

Juya wa junaid yayi ya kalli, tray ɗin da babban yayan nasu yayi watsi dashi a ƙasa, cike da daɗin baki yace “subhanallahi ya akai kayan abincin nan suka zube ƙasa, ni nasan aikin tukur ne bari na kwashe na canza wani,”

Ya karasa ya zuƙunna yana tattare kayan, duk rafayet nabinsa da ido, sai da ya kammala kwashe komai ya mayar acikin tray ɗin sannan ya ɗauka yana cewa “am coming now yayanmu,”

Sannan ya fice, ajiyar zuciya yasaki lokacin da ya fito daga part ɗin nasa, kitchen ya wuce, azmee kaɗai yasamu aciki ta kammala hada masa wani bf ɗin acikin tray,

Miƙa mata na hannunsa yayi ta karba sannan ya ɗauki wanda ta haɗa masa asaman table, ya dago yana kallonta yace “Ina Sehrish take,”? Murmushi azmee tayi kafin tace “ta tsorata ne sosai, ta koma ɗaki ynz,” .

Yace “ok amma aunty azmee yaushe zaki faɗa mata cewa nasan cewa ita maca ce ? Inaso tasani pls !” yayi maganar da shagwa6a,

Ƴar dariya azmee tayi kafin tace “insha Allah yau zuwa anjima, zan faɗa mata,”

Murmushi yasaki ya fice yana faɗin “Can’t wait to see,” dariya azmee tayi tare da cewa “Romeo kenan,”

Itama fice wa tayi daga kitchen ɗin don tajima yau tana aiki acikinsa since morning kamar enjine,

Yana zaune yana jiran junaid, sai gashi ya shigo, hannu rike da tray,  a saman table ɗin dake gabansa daga gefe ya ajiye masa shi, sannan shima yazauna gefensa tare da cewa “Babban yaya zan iya baka a baki,” ɗagowa sgr yayi yana kallonsa face ɗinsa tamkar zaiyi murmushi yana kallonsa, wannan fadancin na junaid ba karamin tafiya yake dashi ba,

Plate junaid ya ɗauka, ya shaƙe masa shi da chips har yayi sauro don yasan Babban yayan nasu baya wasa da cikinsa, akwai bama ciki haƙƙinsa 😉

Tura masa plate ɗin yayi agabansa, naɗe hannun jallabiyar jikinsa yayi, junaid ya zuba masa ruwa ya wanke hannunsa acikin bowl, sannan ya soma ya zura hannusa yana ɗibar chips ɗin yana turawa a bakinsa, in kaga yadda yake wawuro wa yana turawa a small mouth ɗinsa sai kayi mamakin tayadda akai abincin ke shiga, saboda ƙankantar bakin nasa,

Robar cool milk ya dauka ya zuba masa acikin glass cup ya tura masa a side plate nasa, ga fresh fruits ya acikin hadadden plate ya ajiye masa ga sauran delicious,”

Junaid ne yazauna yana saving nashi, bayan ya tsagaita ya zuba msihi ido yana murmushi, ɗagowa sgr yyi suka haɗa ido yace “what”

“Kyau nake kallo fuskar babban yayana,” junaid ya basa amsa,

“Duk kyau na, nakai ka junaid,”? Ya tambaya yana kallonsa, ɗan sunnar da kai junaid yayi tare da cewa “kai na musamman ne yayana, komai naka na musamman ne, haka kyan ka ma,”

dan ta6e baki sgr yayi yana kallonsa ayayin da yake mika hannu ya dauki cool milk ɗin dake acikin cup ya kurba sosai tare da mayar wa ya jiye,

Sannan cikin natsuwa yace “Ni kam tunda nake aduniyar nan, tun da Allah ya halicce ni a duniyar nan , ban ta6a ganin yaro mai shiga rai mai sace zuciya ba irin ka! junaid u are so special to me i don’t know how to explain it but I really really love u so much, just tell me whatever u want am ready to do it for u,”

daɗi kamar zai kashe junaid jin yadda babban yayan nasu ke yabonsa, sam ya gaza rufe bakinsa har sai da sgr ya maimaita cewa “ka faɗamin komai kake so nayi maka insha Allah,”

Cikin sanyin murya junaid yace “babban yaya murmushinka kawai nake so, dan Allah kayimun koda yaushe face ɗinka a daure…” ya ƙare maganar cikin shagwa6a hada ɗan bubbuga ƙafa,

Shiru sgr yayi yana tunanin wai ma ya ake murmushi aduniya, ae shi yama manta when last yayi murmushi aduniyar nan, muryar junaid ce ta ƙara katse shi”smile 4 me plsssssss..”

shiru su kayi gaba ɗayansu, zuba mishi ido junaid yayi yana jiran yaga murmushin babban yayan nasu,

ɗagowa rafayet ya ɗanyi ya kalli junaid wanda ya ƙura masa iso yana jiransa, mayar da idonsa yayi kan plate ɗin dake gabansa mai dauke da farfesun da junaid ya zuba masa,

wa’iyazubillah , A natse a hankali wani irin ƙayataccen murmushi na side face yafara bayyana a kyakkyawar fuskar sgr, Subhanallahi tabarakallahu ahsanul qalikin, wato wasu irin lotsattsun dimples ne suka bayyana a fuskarsa masu shegen kyau, dole babban yaya ya dinga rowar murmushin sa wato wani irin ruwan kyau, madarar kyau yake badawa, irin murmushin kashe zuciyar nan, irin wanda kai tsaye namiji yayiwa Mace shi duk min ji da izzarta sai ta susuce,

A susuce junaid yadinga yarfa hannu yana fadin “wow!!wow !! Oh my God yaya rafayet am just speechless wannan heart killing smile ɗin naka ya tafi dani,”

Lokaci guda kuma ya mayar da face ɗinsa yadda take, kai kace murmushi bai ta6a wanzuwa a fuskarsa ba, sannan yace “Junaid sa hannu muci abinci atare,” cikin sauri junaid ya zura hannu suka shiga ci atare abun gawanin burgewa,  💋•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

_❤‍🔥Extraordianary Love❤‍🔥_

 

*Writer*

*©️Hafsat Bature Boss Lady✍️✍️✍️*

End of chapter one

~page 75~

daga inda ku ka ga na sanya part 2, to daganan Labarin ya soma da zafi zafinsa 🔥🔥🔥

………..Sehrish……………….

Idonta na facing ceilling a yayin da take kwance tsakiyar bed ɗinta, cike da tsananin shauƙin babban yaya, tabbas ta tsorata da fusatar shi, amma hakan ba ƙaramin burgeta yayi ba, musamman yadda ya hauro da doguwar ƙafarsa yayi wurgi da tray ɗin hannunta, lumshe idonta tayi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa, ita dai sgr yayi mata ya kwanta mata aranta (nace ba Allah ya bar ƙauna)

ta jima tana juyi a saman bed ɗin nata, har sai da ta tabbatar cewa sgr ya isa ya fita ynx sannan ta tashi domin zuwa gyara masa bedroom ɗinsa,

A time ɗin junaid ya fita daga part ɗinsa ya koma nasa room ɗin, sai faman zullumi yake, tun da azmee ta sanar dashi cewa zata faɗawa sehrish cewa yasan cewa ita maca ce, zama yayi saman bedmattress ɗinsa ya lankwashe kafarsa, sae faman smilling yake yi, burinsa sehrish ta amince dashi a matsayin ɗan uwanta na jininta suyi shiri sosai, murmushi yasaki tare da yunƙura yakai hannu  daga  gefe Jikin gadon akwai side drawers ajikinsa, janyo wa yayi wato bakomai yake ajiyewa ciki ba face Chocolates,biscuits, sweet da sauransu, junaid baya rabuwa da shan zaƙi, ajinin sa yake, ledar dairy milk ya ɗauko guda biyu da snickers, ya zauna  yana gatsa yana turawa a mouth ɗinsa sai faman lasar baki ya ke yana tunanin Sehrish ɗinsa 😥

Gabanta har faɗuwa yake yi addu’arta Allah yasa sgr ya fita daga part ɗinsa, tafiya take yi cikin sanɗa, ta wuce parlor ɗinsa, adai dai kopan shiga bedroom ɗinsa suka ci karo dashi ƙiris ya rage su gabji juna,

Waro ido tayi tana kallonsa cikin tsananin tsoro, ya shirya tsaf da alama fita zaiyi, ya ɗau wankan jeans da t shirt irin na jikin junaid, ga wannan haɗaɗɗiyar sumar tasa, gyara na musamman tasha, ya daure ta abayansa, yayin da ya saki wata daga ƙasa ta ɗan zubo masa, hakan ba ƙaramin kyau yayi masa ba,

Ƙamshin turarensa sai wankar mata hanci yake yi, kai kace da ruwan turare yake wanka,

gyaran murya yayi alamar abashi hanya ya wuce, da sauri ta ɗan ja gefe, ya bi ta side ɗinta ya wuce da wannan tafiyar tashi mai jan hankali, sam tagaza ɗauke idonta akansa, wani tunanine ya faɗo mata aranta, cikin sauri tace “adawo lpy”

“yawwa” ya amsa mata a time ɗin da yake idasa fita daga falonsa, .

Saboda murna yasa sehrish ta  ɗan yi tsallen farin ciki, tare da sakin murmushi koba komai, wannan wani mataki ne, na narasa tunda yana amsa magana in akai masa, 😇

Shiga bedroom ɗinsa tayi har time ɗin tana ayyana muryarsa da yadda ya bata amsa, taci alwashin daga ynx zata dinga yi masa magana, tunda yana amsawa,

Ajiyar zuciya tasaki tare da mayar da hankalinta ga abunda ya kawo ta, bin ɗakin nasa tayi da kallo, Aljannar duniya komai tsaf a gyare, sae ƙamshi ke tashi kamar, koda yaushe tana jinjinawa haɗuwarsa da kuma dollars ɗin da aka kashe masa, nan gaba sehrish zata zayyana mana ya haɗuwarsa yake 😘

A hankali take shafa lallausan blanket ɗinsa, ta janye sa daga saman gadon ta ninke sa, tare da hugging ɗinsa a chest ɗinta tana shaƙar kamshinsa, ta jima tana lalaci a ɗakin nasa kafin ta shiga gyarasa,

………….Hosana ………….Jahad ……………

a hankali motocin nan suka shiga dasu  a katafaren gidan goggonsu, yadda motocin nan na sojojin nan suka zagaye motar da suke ciki ko shugaban ƙasa albarka,

Sunyi shiru acikin motar,ni’imtaccen sanyin a.c ne kawae ke ratsa, sassan jikinsu, tsantsar farin ciki ne a fuskarsa, ita dai jahad sai godiya take ma Allah daya kawo musu ƙarshen wahalarsu acikin zuciyarta, yayin da hosana ke ta faman zabga murmushi kamar zautacciya,

A tsakiyar gidan suka tsaida motocin, da sauri major ɗin nan dake driving ɗinsu, ya fito tare da buɗe musu kopa, riƙe da hannun juna suka fito, suna bin gidan da kallo ya haɗu masha Allah,

Major ɗinne ya shiga dasu cikin babban falon, saude ce ke ta faman goge goge, tana kakka6e kujeru, ɗagowa tayi jin anyi sallama,

Zuba ma yaran ido tayi tana kallonsu, cikin mamaki ganin tagwaye kyawawan gaske, sam ta gaza magana,

Sai da taji muryar major ɗin yana cewa “Marshal Omar ne yace akawo su nan, shima kuma yana nan shigo wa da anjima,”

yana gama faɗan hakan ya fice, zuru su kayi suna tsoron wata irin tarba za’ayi musu, don sun lura kamar baƙin jini ne dasu kowa baisan su,

ganin matashiyar ta soma sakin murmushi a fuskarta yasa su suma suka ɗan saki fuska,

Cike da zumuɗi takara inda suke kamar tasan su, ta ruƙo hannayen su tana cewa “masha Allah ku shigo ciki ku zauna, ku saki jikin ki ku,”

Haka saude ta ruƙo hannunsu, ta zaunar dasu tare da cewa “bari na kawo muku abunsha ko”?

Cikin sauri hosana tace “ƴunwa muke ji…..,” tunkan taƙarasa jahad tasa tafin hannunta ta rufe mata baki, tare da cewa “Hosana banasan wannan abun, daga zuwa gidan mutane kinsan su ne,”

murmushi saude tayi tare da cewa “ba yaya Omar bane yace akawo ku nan ba? Don haka ku saki jikin ku kamar kuna cikin jirgi mai ya ƙare” 😂

“Sannan naji kince batasan mu, ae musulmi ɗan uwan musulmi ne, akwai sanayya da ƴan uwantaka ta addinin musulunci, sannan kuma baƙon ka annabin ki, ku baƙi ne dan haka zan karramaku sosae,

Saude ta karasa maganar tare da sa hannu ta shafa kan hosana tace “kada ki damu ƙanwata, yanzu nan zan kawo miki abinci lafiyayye ki ci,”

“nima zanci,” jahad ta faɗi tare da sunnar da kai, murmushi saudat tayi tare da cewa “shikenan bari nazo ga tv nan kuyi kallo,” tayi maganar tana nuna musu plasman dakw manna a bango, sannan ta wuce kitchen,

Ajiyar zuciya suka saki atare suna ƙare wa  haɗaɗɗen falon kallo,

“Hosana dan Allah ki daina zuba, kina bani kunya sometimes, kin ci ka ɗumi daga zuwa gidan mutane sai ki fara tambayar abinci kamar mayya”?.

Harara hosana ta watsa mata tare da cewa “bani ce mayya ba kaɗai kema mayyar ce, saboda ke ma ae kince zaki ci, ” tayi maganar tana murguɗa mata baki, jinjina kai kawai jahad tayi, ba yadda zatayi da ita,

Shigowa saude tayi hannunta ɗauke da tray ta aza katuwar kula aciki, sai plate wit 2 spoon, gefe kuma jug ne mai ɗauke da juice,

Tunkan ta ƙaraso hosana, ta sauko ƙasan carpet ɗin ta zauna tana washe baki,

Ajiye musu tayi tare da cewa “yakamata ku wanke hannayen ku, bari na kawo muku wurin da zaku wanke,” ta faɗi kafin ta juya izuwa cikin kitchen ɗin,” .

Buɗe kular hosana tayi, zaro ido tayi tare da cewa “Lahh ha ilah Jahad !! Shinkafa kaza ce wlh, hada wasilla masu yawa wayyo daɗi,”  shiru jahad tayi batace mata komai ba, saboda yunwar da take ji,

Ji su kayi bazasu iya jiran saude ba, takawo musu ruwan da zasu wanke hannu ba, ai kafin saude ta fito daga kitchen ɗin tuni hosana ta ɗauke jug da plate ɗin dake saman tray ɗin ta ajiyesu on carpet ɗin , ta ɗauki kular ta zazzage musu farar shinkafar da miyar duka acikin tray ɗin, gaba ɗaya suka sa hannu suka motse ta suka shiga zubawa cikinsu, hannu baka hannu ƙurya kamar wani yace zai kwace musu abincin,

Tsaye saude tayi akansu tana kallon ikon Allah, gashi har ta ɗauko musu bottle water da bowl ɗin da zasu washing hands ɗinsu aciki, tausayinsu ne yakamata, alamu sun nuna cewa yaran na cikin mawuyacin hali na ƴunwa,

Kamar wasu kuraye haka suka dinga, zuba uwar loma suna ci, Allah sarki anjima ba’a haɗu ba, kitchen saude ta koma cups da dauko musu,

Ta dawo ta zukunna inda suke, tana tsiyaya musu ruwan bottle ɗin hannunta mai sanyi, tunkan ta gama hosana ke miƙa mata hannu tana cewa “ruwa !ruwa!!,’ wato taci taci harya shaƙe mata makoshinta,

Miƙa mata saude tayi cikin sauri ta kar6e, ta kai baki tana sha, har wani sauti throat ɗin ta ke badawa “ƙut ƙut kut,

“Hosana nima zan sha in kin gama,” jahad ce tayi maganar tana yarfa hannayenta, cikin sauri saude ta zuba mata itama a ɗayan cup ɗin ta miƙa mata, karba tayi tana faɗin “mungode,”

Zama saude tayi kamar ta samu tv tana kallonsu, yadda hosana ta dauki cinyar kaza, ta tura acikin baki kamar kura ta bata tsoro, amma abun mamaki hada ƙashin ta haɗa duka ta taune, zaro ido saude tayi cikin tsoro tana cewa “ki ci a hankali dan Allah,”

“Bazaki gane ba aunty, wlh yunwa muke ji, dan Allah in akwai sauran abincin ma akwaso mana shi duka hada ƙanzoma,” 😂

Hosana ce tayi maganar, tana ta fama lashe la66a, mouth ɗinta yayi dama dama da jar miya, kamar mayyar dae,” 😆.

Jahad dai ba baka sai kunne, sam bata gane da wane yare suke magana, bata ankare ba hosana ta ɗauke tray ɗin duka tasanya harshenta tana lasa 😅

Ita kanta saude batasan time ɗin da ta, fashe da dariya ba hada dafe ciki, sam tagaza stopping kanta, sae da tayi mai isarta, sannan ta tashi daker tana ci gaba da dariyar ta amshi tray ɗin dake hannun hosana tana cewa “bari na zubo muku alkubus da miya kuna so,”? tayi maganar tana kallonsu, ae har haɗa baki suke yi wurin cewa “eh komai ma in akwai hada ƙanzo ma azubo mana muna ci pls , mu ko ciyawa ce in dai za’a sama ta miya muna so,”  😹😹😹

Dariya kamar zata kashe saude, haka ta ɗauki tray ɗin ta wuce dashi kitchen, duk wannan budirin da akeyi goggon katsina bata sani ba, tana can haye saman gadonta,daga sauraron radio bacci ya kwashe ta,

Sai da jahad da hosana su kayi kulu wash rabu hani’an , sannan suka dawo hayyacinsu, sun ƙarar da abincin gidan duka, dole saude ta ɗaura wani girkin,

Bedroom ɗinta ta shigar dasu,bin ɗakin su kayi da kallo komae tsaf ba tarkacen hauka, sai ƙamshi ke tashi, daga bed sae wardrobe, ƴar bedside loka da sauransu,

Toilet ta nuna musu tare da cewa “nasan zaku buƙaci yin wanka, ga toilet nan, ku cire kayan jikin ku naga sun tsufa kuma sunyi datti, kusanya munsu acikin laudry basket ɗincan,” tayi maganar tana nuna inda basket ɗin yake gefen wardrobe ɗinta,

Sannan tace ” duk abinda baku gane ba kuyi mun magana, just feel free,”

“Mun gode sosae aunty,” acewar jahad, murmushi saude tasaki tace “kada ku samu damuwa, ni zan shiga ciki,” tayi maganar tare da fice wa daga ɗakin,

“Wai !! Allah hosana kin ga yadda Allah ke ikonsa ko? mun fita daga wancen kurkukun kaddarar (Next novel) ynx gashi zamu fara sabuwar rayuwa mai kyau,”

Murmushi kawai hosana ke saki, gaba ɗaya hankalinta nakan Marshal Omar duk in ta tuna yadda lamarin ɗazu ya wakana sai taga abun kamar a mafarki,” 😊

Sun jima suna shiririta, kafin jahad tafara shiga wanka, komai na toilet ɗin a tsaftace, ya ji tiles har jikin bango, shower ce ta tsaye, sai kwandon wanka, mai ɗauke da sabulu mai ƙamshi da lallausan soso,

Bakomai ya burgeta ba acikin toilet ɗinba sai shampoo da tagani jere, saman mirror, saboda gashinsu yayi dauɗa, duku-duku sai uban wari, ga ƙura,  murmushi tasaki cikin sauri ta tu6e rigar jikinta kamar tsumma, ta yi hanging ɗinta jikin towel holder,

Baƙaramin dauɗa jahad ta fidda ajikinta ba, sai da ta wanke ko’ina tayi shaving gashin under ɗinta dana armpit ɗinta da Shaving cream, dogon gashin kanta ma yasha wanki da shampoo,

Zanso ku ga yadda jahad ta fito daga toilet ɗinnan, Fesss fesss kamar wadda tayi wanka da ruwan zam zam, da daurin gaba ta fito, towel tasanya ajikinta, hannunta kuma na riƙe da rigarta, cikin laundry basket tasanya rigar kamar yadda saude ta basu umarnin,

Sakin baki jahad tayi ganin hosana nata faman sharar bacci a tsakiyar shimfidaɗen gadon saude, girgiza kai tayi tare da faɗin “basa ban ba, gida babu makwabta babu gidan miji ba tabbas” 😂

( this reminds me our class mates Allah sarki, wannan sararsu ce, wato daga anyi abu sai suce gida babu makwabta babu gidan miji ba tabbas)

Allah sarki hosana dole kiyi bacci baiwar Allah, munyi rayuwar ƙunci sosai, yanzu lokaci ne da Allah ya amshi addu’armu, zamuyi rayuwa ta jin daɗi da walwala,” jahad ce tayi wannan maganar sannan ta ƙarasa, inda hosanar take, ta ɗan russina tare da sa hannu da bubbuga ta, ” Get up hosana, bacci bazai yi maki daɗi ba, da datti ajikin ki, ki tashi pls,” a hankali hosana ke buɗe dara daran idanuwanta, tana lullumshe su, cikin kasalalliyar murya tace ” meyasa kika tashe ni dan Allah ! bakiji yadda nake ji ba, ‘

“Sorry hosana, nasan ba daɗi amma ki tashi kije ki cire dattin dake jikin ki, wlh zakiji wata irin ni’ima mai daɗin gaske na shigarki, ba ki ga yadda nayi fess ba”? tayi maganar tana jujjuya mata jikinta don tagani dakyau,’

Murmushi hosana tayi daga kwancen da take tana kallonta, miƙa mata hannunta tayi tare da cewa “pls taimakamin na tashi kasala nake Ji 🤗

*Hafsat Bature* 😎*🪄🪄🪄ABBAN SOJOJI🪄🪄🪄*

*Mallakin*

*💋Hafsat Bature Moh’d💋*

*❤‍🔥BossLady❤‍🔥*

*Junaid was the heart beats of my story not because i loved him so much, zaku shaida hakan*

~page 76-~

Murmushi hosana tayi daga kwancen da take tana kallonta, miƙa mata hannunta tayi tare da cewa “pls taimakamin na tashi kasala nake ji ajiki,”

Ruƙo hannunta jahad tayi daker ta miƙar da ita tsaye, tana faɗin “wash Allah ba dole ki ji kasala ba, kinci uban abinci kin kuma zo kin kwanta,” acewar Jahada,

Wuce wa hosana tayi tare da shigewa toilet ɗin, tana jiyo muryar jahad tana cewa “Hosana akwai shampoo ciki pls ki wanke wannan mahaukacin gashin kan naki, mara tsari nasan ki da taurin kai, bakisan wanke sumar kan ki, ko nazo na taya ki wanke wa..”? ta tambaya tana jiran amsa,

“Banso,’ ta cikin toilet ɗin tabata amsa, dafe kai jahad tayi tare da cewa “Oh God!!”  saboda tasan hosana bazata ta6a yarda ta wanke sumar kanta ba, kuma bata so wani ya wanke mata, shiyasa kullum gashin kanta a cukurkuɗe yake, gashi duk tafisu yawan gashi da cukowa, duk da kowa da yawan nasa,

jahad na zaune saman stool gaban mirror tana shafa cream ajikinta, sai ga saude tashigo da sallama, da fara’a a face ɗinta tace “wow masha Allah, tubarkallah wannan dogon gashin fa kamar na larabawa,” tayi maganar tana kallon sumar kan jahad wadda ta zubo mata har wurin waist ɗinta,

Cikin jin kunya jahad ta sunnar dakai, saude taci gaba da cewa “duk da nake bafullatana, nima ina da gashi amma bai kai ko rabin naki ba, ke wata ƙabila ce ? Jahad tace “BUXUWA,”

Saude tace “No wonder, shiyasan ya, hakan na nufin cewa ku ƴan niger ne ko?

“Mahaifiyar mu buzuwa ce ƴar niger, amma mahaifin mu bafullatani ne ɗan nan,”

saude tace “Wow wow!, haba ! ae dole kyau ya haɗu a wurin nan, dole kuyi kyau yara,” murmushi kawai jahad ke saki, ganin yadda saude ke zuzuta su duk da itama ɗin kyakkyawa ce,

Wuce wa ciki saude tayi ta buɗe wardrobe ɗinta, riguna ta ɗauko musu dogaye sun sha guga ninkakku, ta ajiye musu asaman gadon sannan tace “Gashi nan kusanya rigunana ne, duk da nasan sunyi muku tsayi sosai,”

“Mungode sosai aunty, Allah yasaka da alkairi,” saude tace “mention not pls,” sannan tafice don tabasu damar wataya wa,

“Jahad kinji yadda iska ke shiga jikina, ga wani ƙamshi dake fitowa sako da lungu na hammata ta,” hosana ce tayi maganar wadda fitowarta kenan daga toilet ɗin,

A lokacin jahad ta kammala sanya doguwar rigar da saude ta fiddo masu, na materials ne pink colour masu kyalkyali, ba karamin kyau su kayi mata ba,  cikin 6acin rai take kallon hosana

“Meyasa wai baki da hankali ne, ke shashashar ina ce? Ba sai da nace miki ki wanke sumar kanki ba,”? ta tambaya a ƙule tana kallon hosanar,

Da buɗar bakinta sai cewa tayi “Gashina ne ko Gashin ki”? Shiru jahad tayi don tasan ynx zata tada rigima har ajisu,

“Gashin ki ne hosana, zo kisanya kaya gashi nan aunty ta fiddo mana mu sanya,”  wuto wa tayi daure itama da towel ajikinta, ta zura rigar materials ɗin, tayi kyau amma gashin kanta sai uban wari ya ke yi, babu yadda jahad ta iya da ita, bayan sun kammala shiryawa, atare suka haye saman gadon suna facing ceilling, “what are u thinking about jahad”? Hosana ce ta tambaye ta, cikin sanyin murya jahad tace “SEHRISH, ke fa me kike tunani? Murmushi hosana tayi kafin tace “Wannan kyakkyawan mutumin, mai ƙarfi wanda ya ceto rayuwarmu daga shiga haɗari, daga na rufe eyes ɗina shi nake gani, lokacin da na faɗa jikinsa, bakiji ƙamshi ba wlh ya haɗu” 😇

Jahad tace “shegiya ashe kina cikin hayyacin,” 😂 dariya su kayi gaba ɗayansu

………………….SEHRISH…………………

Ta gyara komai tsaf na bedroom ɗinsa, tsayawa tayi tana kallon hoton dake jingine saman side drawer ɗinsa bayan bedside lamp, hannu takai ta ɗauki hoton tana kallo, wata mata ce acikin hoton fara tas baturiya, mai kyan gaske kai kace itace tayi kanta don kyau, jikinta sanye da uniform ɗin na sojoji, kakin ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, tsaye take tayi saluting a cikin hoton, bin sumar kanta sehrish tayi da kallo, launin gashin matar yayi yellow mai tsayin gaske, kwayar idonta kuma blue colour ce, wannan ba kowa bace face*Alexandra* Ummu Rafayet, ummun Ayan da jahan kuma ummun micheal(makel) da ROMEO 💞

Murmushi sehrish tasaki matar ta burgeta, duk da batasan kowacece ba amma kamannin fuskarta sak irin na Babban yayansu, akwai kyau, daga ganinta wayayyiya ce ajin farko,”

Hannu sehrish tasanya tare da shafa hoton a fili tace “kowacece wannan matar amma ta haɗu kuma ta burge ni, gashi tana kama da Babban yaya sosae,” ta karasa maganar tare da mayar da hoton inda yake ta ajiyesa,

Sannan ta tura kopar toilet ɗinsa ta shige 😯 uhmmm hmmmmmm, tsayawa sehrish tayi tana tunanin anya ba kuskure tayi ba, wannan ae ba toilet bane, jimmmm tayi tana ƙarewa toilet ɗin kallo, lokaci guda ta dabarbace saboda haɗuwarsa, an raba shi biyu 6angaren toilet da kuma na bathroom wurin wanka kenan, ba ƙaramin girmane dashi ba, kamar a mafarki take bin komai da kallo, shiga ciki tayi ƙamshin wurin na dakar hancinta,

ba komai yaja hankalinta ba face wurin wankansa, wato irin standing jacuzzi ɗin nan ne (kwamin wanka), wande ke zagaye cikin glass, sakin baki  sehrish tayi galala tana kallon ikon Allah, mayar da eyes ɗinta tayi kan bathroom cabinet ɗinsa, jerun wasu matsiyatan Shampoo ne, mayuka iri iri masu kyau da tsadar gaske, duk na gyaran jiki ko mace albarka wannan,

Jinjina kai kawai sehrish ke yi, haɗaɗɗen mirror ɗin dake cikin toilet ɗin mai girman gaske, ga wash basin agabansa, mai ɗauke da taps biyu na ruwa,  daga gefe kuwa soap dispenser ce,  gashi an ƙawata shi da vase a ajiye ƙasa, (Tukunyar flowers)

Zuƙunnawa sehrish tayi ƙasan hadaɗɗen tiles ɗim mai walkiya, ta zabga tagumi, aranta tana mamakin cewa wai nan toilet ne ? Idan har nan toilet ne to mukuma irin namu toilet ɗin ya sunan shi ? (Nace ba kewaye ko ki ce banɗaki) 😂

ta jima tana shirita, domin ba abun da ke buƙatar gyara a toilet ɗinsa, komai tsaf, kallo kawai ta tsaya yi daga bisani ta ɗanyi goge goge kawae ,

Fitowa sehrish tayi ta sauko down tana ko zata ganshi, basa nan ba kowa duk sun fita,

Wuce wa nata room ɗin tayi, tayo wanka, ta fito ta zura riga ta maza dai dai guiwa, ta zauna gefen gadon tana tunanin duniya, kallon sama tayi tana cewa “Oh ni yanzu wata rana nima zanyi saurayi, har nayi aure na haifi ƴa’ƴa,? When ? Ina so nima nayi shiga irin ta mata, na wataya nayi rayuwar ƴanci yaushen hakan zata faru ? 😥

Ajiyar xuciya tasaki tana tunane tunane,

Kwankwasa kopan akayi, cikin sauri tace” wanene? Azmee tace “wa kika sani yake zuwa ɗakin ki in ba ni ba,”?

Murmushi Sehrish ta saki tare da miƙewa ta buɗe mata kopan, sanye take da hijabi milk colour hannunta riƙe da Cazbaha, da murmushi a fuskarta tace “ƙanwata ina fata dae ba zaune kike hakanan ba kina tunane tunanen duniya? karfa ace bakiyin zikri? Ba istigfari da sauransu?

Sunnar da kai sehrish tayi, don kuwa batayi, ae tun ran da tasanya SGR a idonta, ta rage duk wani abu da take yi,

“Hmmm dama raina ya bani, gsky zamuyi faɗa dake muddin baxaki, daina zama hakannan ba kina sa damuwa aranki ba,

“Insha Allah aunty azmee zan rinƙa ƴi,” jinjina kai azmee tayi kafin tace “Albishirin ki,”?

Cikin mamaki sehrish tace “Goro,”

Azmee tace ” an bani sabuwar waya nabaki,”

Ɗan zaro ido sehrish tayi cikin mamaki tace “Who”? Murmushi azmee tayi tare da cewa, ” i will let u know but not now, yanzu dae da anjima bayan magrib kina da baƙo,”

Waro ido sehrish tayi tare da cewa “baƙo kuma aunty azmee ? wurin wa zai zo? Tayi maganar cikin ruɗu,

Azmee ta dafa kafadarta tare da cewa “bakowa bane , fa ce wanda nace miki, yasan cewa ke maca ce !! yau zaku haɗu, na shirya muku haɗuwa a Garden, ki same shi immediately after magrib prayer,”

Murmushi sehrish tasaki tana jujjuya ido, ta ɗan jinjina kai kafin tace “shikenan aunty azmee Allah yasa naga alkairi,” yanayin yarda tayi maganar taba azmee dariya,

“Ni zan wuce, maganar wayarki kuma, sai zuwa gobe zan baki ita, salon kuma in ga yarinya ta buɗe tiktok ko insta don na lura kan ƙanwar tawa rawa yake yi,” ta ƙarasa maganar cikin zolaya da dariya a face ɗinta,

Itama sehrish dariyar take yi, duk da batasan menene tiktok da insta ɗinba, sunan kawai ta ta6a ji ana faɗa,” .

Bayan azmee ta fita, sehrish ta daka wani uban tsalle sai saman gadonta, tsananin murna ne ya bayyana a fuskarta, rawa ta dinga yi tana tsalle tsalle asaman gadon jin an mallaka mata waya, gashi kuma zata haɗu da wanda yasan cewa ita maca ce acikin gidan, addu’a take yi Allah yasa koma wanene acikinsu yakasance mai sauƙin kai kamar hafsat bature,

😇😂

Yini tayi tana zullumi acikin ranta,wanene wannan dayasan cewa ita maca ce ba namiji ba, wayyo Allah yasa junaid ne don yafi su sauƙin kai, ko ba komai wannan wani mataki ne nasara arayuwata, ga kyautar waya kuma an bani, wayyo daɗi bisa daɗi yanzu ya’azayi na rinƙa waya da ƴan uwana? ta faɗi jiki a mace,.

Zama tayi saman gadon ta janyo pillow tare da rungumesa jiki amace, taso ace lokacin da zata riƙe  waya, ta rinƙa samun su Hosana da jahad, amma kash tun time ɗin da junaid ke ara mata wayarsa, ta daina jin ɗuriyarsu kullum switch off, sehrish ta jima tana tunanin menene yasa ba’a samun wayar tsohuwa ne ? What’s happening wit them?

 

💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

…………..AMANI……………………

tunda taji dirar motoci acikin gidanta, kuma dama Cg abbas ya sanar da ita cewa, Rafayet yace masa zai zo gidansa ya kawo masa ziyara, hakan yasa sai faman rawar kai take yi, shiri na musamman tayi, ta ɗauki wankar less maroon colour wanda akayiwa ado da stones doguwar riga ce tabi shape ɗin jikinta, ko mayafi bata sanya ba, ta zubo da gashin kanta har gadon bayanta, dama fa akwai kyau abun saiya bada Citta, kai kace ba matar aure ba, ƙanin miji zai zo an dage ana ta zabga uwar kwalliya,”

fitow tayi daga bedroom ɗinta, tana saukowa daga saman stair, cikin tafiyar rangwaɗa da yanga, dama legs ɗinta nasanye cikin highheels launin kayanta, ta fito fess abunta Balarabiya

Ƙamshin turarenta ya gama gauraye falon, tunkan ta idasa isowa ta zuba mishi ido yana a zaune saman 3 seater, ya aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya yana daddana wayar hannunsa cikin natsuwa,

gaba ɗaya ya tafi da imanin Amani, saboda tagaza janye eyes ɗinta daga nashi, daker ta iya samun natsuwa har tace mashi “sannu da zuwa Babban yaya, ashe kaine nayi mamaki wlh, ban ta6a tunanin zan ganka ba agidan namu,” tayi maganar tare da samun wuri itama tazauna suna facing ɗin juna,

Ya jima bai bata amsa ba, kusan 5 minutes sannan yace “Yawwa ya nasame ku,”?

Cikin kashe murya tace “lfy lou Alhamdulillah,’ .

shiru su kayi ba magana aranta tace “tabɗijan can ! Wai dama haka yake da miskilanci? Ko kallo babu balle magana,’? ta tambayi kanta acikin zuciyarta,

Just managed ba editing,

~HafsatBatureBossLady~

In kina so ki gode mun kiyimun share na novel ɗina, shine first novel ɗina don haka ayimun share ɗinsa ko’ina  🪄🤗

*Page 77-76*

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🪄Hafsat Bature Moh’d Boss Lady*🪄

~page 77-78~

*❤‍🔥Extraodinary Love❤‍🔥*

(Don’t forget to share it everywhere) 🪩

Miƙewa tayi tare da cewa”Bari na kawo maka snacks da abunsha,”

dakatar da ita yayi da hannunsa yace”No need thanks”

Murmushi ta ɗan yi tare da komawa ta zauna, tana ci gaba da kallon fuskarshi, kafin ta mayar da idonta kan surar jikinsa tana haɗiyar yawu,

“Banason Kallo,” ya faɗi yana ci gaba da dannar wayarsa, cikin jin kunya Amani ta janye idonta, tana mai mamakin taya akai haryasan tana kallonsa,

Cikin kashe murya tace ” Babban yaya ae dole na kalle ka, kai fa abun kallo ne, kuma ni ban ta6a ganinka ba ido da ido, shiyasan ya,’ ta ƙare maganar tana cizon pink lips ɗinta alamar ya cije ta,

shi kuwa ba ta ita yake ba, burinsa yayansa Abbas ya ƙaraso, su ga juna, yayi kewarsu sosai,

Muryarta ce ta ƙara ratsa shi “Babban yaya, ko dae baka farin ciki dani ne amatsayina na matar yayanku ishaq,’? ta yi maganar tana kallonsa,

“Why’? ya tambaya har time ɗin bai ɗago ya kalleta ba, gyara zama tayi tare da cewa “to naga u don’t even want to look at me, atlease u should put ur eyes inside mine,”

Amani ba ƙaramin takura masa tayi ba, ji yake tamkar ya tashi yabar gidan, don baisan nacin magana,

“Plsss babban yaya,”

dogon tsoki yaja tare da cewa “becareful with me,” gabanta ne taji ya faɗi jin gargaɗin da yayi mata, tabbas mace bata gabansa,

Jiki a mace Amani tabar falon, cikin bedroom ɗinta ta koma, jiki na rawa ta ɗauki phone ɗinta dake ajiye asaman pillow ta dannawa AUNTY BABBA kira,

Ringing 3 ta ɗaga kiran bayan sun gama gaisawa cikin zumuɗi Amani tace “Aunty ko kinsa cewa SGR na cikin gidan nan yanzu haka? tayi maganar da murmushi a face ɗinta,

A can 6angaren kuwa cike da mamaki aunty babba tace “Are you serious? shi da kansa kuma”?

dariya Amani tayi tare da cewa “wlh kam,baki ji yadda naji ba dana gansa duk da rashin maganarsa, yaci ka ji dakai wlh,”

Aunty babba ta fashe da dariya ta cikin wayar tare da cewa “ki barshi zai zo hannu ne yanzu dai ya maganar Ziyartar wurin bokan nan baba ibliss? kin sama mana kuɗin?

Ajiyar zuciya amani tasaki tare da cewa “tukunna dae auntyna, ina nan ina tarairayarsa, ina so nabi komai a sannu, insha Allah nan ba da jimawa ba, zaki ji daga gare ni, da kaina ma zanzo kd na kawo miki ziyara,”

Aunty babba tace “To shikenan, Allah ya kaimu lpy, shiri na musamman zamuyi, domin ganin munci nasara akan waɗannan zafafan guda biyu,”

sun jima suna waya a tsakaninsu, agame da yarda zasu ziyarcin wurin hatsabibin bokan nan Baba iblisssss 👹

A can ciki kuwa, dirar Abbas kenan fuskar nan dauke da fara’a kamar gonar auduga jin cewa Sgr ya kawo masa ziyara da kansa, sanye yake cikin kakinsa na sojoji daga headquater yake,

yana shiga falon Rafayet ya miƙe fuska a sake suka rungume juna sosae, kamar karya sake shi haka Abbas ya ji,

“Am really glad to see u bros, nayi kewarku sosae kamar kamar me,” abbas ya faɗi hakan cikin tsananin farin ciki, ruƙo hannunsa yayi suka zauna a mazauni ɗaya, suna kallon juna cike da kewa,

Cikin sanyin murya babban yaya yace”Nayi kewarku sosae, har ma bazan iya faɗa ba,”

ƴar dariya abbas yayi tare da cewa “Wake koya maka hausa ne? nayi mamakin jinta raɗau abakin ka duk da har yanzu da sauranka, last time da kazo daker kake fahimta in anyi magana,”

Jinjina kai Babban yayan yayi tare da cewa ” bana so nazo ƙasar nan ne arinƙa gulmata bana ji, that’s why na dage na koya saboda su Ammi,”

Dariya abbas yayi sosae jin abunda Rafayet yace, a wasa wasa shima ya iya zolaya in yaso , bayan abbas ya tsagaita da dariyar ne yace “Am wai baku gaisa da Amani ba? naga ko abunsha ma bata kawo maka ba,”

“No tazo mun gaisa, ni nace bana son komai shiyasa,”

Jinjina kai Abbas yayi tare da cewa “meyasa baka son shan abu ko cin abu in kazo gidan mutanene nifa ɗan uwanka ne jinin ka, shikenan  nima duk ranar da kayi aure nazo gidan ka, matarka tayi mun tayin abinci  bazan ci ba,”

wani kallo babban yayan yayi masa tare da ɗan ta6e baki kafin yace “NEVER,”  wato bashi ba aure har abada,

Murmushi abbas yayi yana kallonsa yace “hmmm haka dayawa irinka suke cewa but at the end sai ga lamarin ya sauya, irin ku ma mace tafi juya ku, sannan maza irinku da basa ra’ayin mata ko aure wlh basu iya faɗawa tarkon so ba, haukace wa suke yi idonsu ya makance lokaci guda,” .

Abbas ya ƙare maganar da zolaya yana kallon fuskar Sgr, wanda ya tamke fuska yana sauraran bayanin yayan nasa,” .

Miƙe wa yayi tare da cewa “Ni zan wuce,”

“Haba Babban yayansu, nasan magana tace tayi hurting ɗinka am sorry 4 that, it was a joke,”

Abbas ya faɗi tare da miƙewa shima ya ruko hannunsa cikin lallami,’

“Ba abunda kake tunani bane yaya abbas, time ɗin tafiyana ne yayi, saboda ko wane lokaci na rayuwata yana da amfani, kuma a ƙirge yake”

Murmushi abbas ya saki yana jinjina kai yace “kuma fa hakane, na tuna da wannan, ae nama gode ssae da ziyarar da ka kawomin, Allah yabar zumunci,” ya faɗi hakan a yayin da ya matsa suka sake hugging junansu, sannan su kayi sallama,

……………………SEHRISH……………………….

Bayan sallar La’asar wuraren ƙarfe 5 na yamma, suna kitchen ana ta faman girke girken abincin dinner, ƙamshi ya gauraye ko’ina,

tana tsaye tana yayyanka kayan lambu a saman chopping board, fuskar nan a washe abubuwa biyu na mata yawo aranta, na farko shine wanene wannan wanda xata haɗu dashi yau a garden wanda yasan cewa ita maca ce, na biyu kuma shine new phone ɗin da aunty azmee tace an bata kyauta, bakomai take ɗauki da wayarnan ba fa ce shegen son kallon fina finai dake gare ta, ga son sauraron music gata mayyar selfy kamar hafsat bature 😇

“Ji mana, ki dubamin girkin nan , ynx zanje na dawo,” azmee ce tayi maganar a yayin da take fi ce daga kitchen, ..

Cikin sauri sehrish tace “To aunty azmee,”

Ajiyar zuciya tasaki tare da cewa “ko ƙarfe nawa yanzu i ave to check the time, ina da baƙo fa,” ta faɗi cikin zumuɗi tana kallon agogon dake manna a bagon kitchen ɗin,  shida saura murmushi tasaki tana faɗin “lokacin haɗuwa ya kusa Ya Allah ka bani ƙwarin guiwar tunkarar koma wanene wanna,”

ta faɗi tana nuni da knife ɗin da ke hannunta,

Azmee kuma da ta fice bedroom ɗin junaid ta wuce,  domin ta ƙara tunasar dani haɗuwar da ta shirya musu da sehrish,”

Sai faman knocking take yi, amma sam baiji ta ba, yana tsaye riƙe da ƙugu gaban closet ɗinsa ya buɗe yana kallon jerin kayansa, yama rasa wanne zai sanya domin haɗuwa da sehrish ɗinsa for the first time, sai zabga murmushi yake yi ba magana, tun da azmee ta sanar mishi da haɗuwarsa da sehrish yarasa tsaye ya rasa zaune, sai rawar kai da zumuɗi yake, kamar sabon ango 😌

daga shi sai short ajikinsa, sai da azmee ta ɗaga murya da cewa “Junaid ka buɗe aunty azmee ce inason magana da kai,”

Ae yana shaida muryarta a kunnansa jiki na rawa, yayi hanzari zuwa ya buɗe mata kopan, yana sakar mata murmushi,

“Ango kasha ƙamshi,” azmee ta faɗi cikin zolaya,

“Ka ce ka shirya haɗuwa da amaryar taka kenan,”?

Cikin ɗan jin kunya yace “Kai aunty azmee, nifa kunya nake ji,”

yadda yayi maganar da shagwa6a yasa ta yin ƴar dariya tace “uhm junaid kenan Romeo shugaban ƴan soyayya yau zai haɗu da juliet ɗinsa akaro na farko, yakama ka rubuta wannan a diary ɗinka saboda tarihi,” .

ɗagowa yayi da dariya a fuskarsa yana kallon azmee jin abunda yace,

“Insha Allah aunty azmee, dole na rubuta wannan, saboda rana ce ta farin ciki da bazan ta6a mantawa da ita ba arayuwata,”  cikin sanyin murya junaid yayi maganar, alamar yana jin abun aransa sosae,

Azmee tace “hakan yayi kyau, ynx dae ni zuwa nayi na ƙara karfafa maka guiwa kasan kai mutumina ne, inaso ka saki jiki sosae, sbd rishi yarinya ce mai shegen tsoro, tana da wani hali dana lura dashi yanayin yadda mutun ya tarbe ta itama haka xata kar6esa, i mean yadda kasakar mata fuska haka itama zata sakar maka tata, kuma zata saki jiki da kai sosai kamar ɗan uwanta, Junaid nasan baka da ƙanwa mace, gaba ɗayanku maza ne, to inaso ka ɗauki sehrish amatsayin ƙanwarka, kai kuma ka zama tamkar yayanta mai share mata hawayenta, kuma abokin shawararta,”  natsuwa junaid yayi yana sauraran maganar azmee har cikin ransa bayaninta ya kwanta masa aransa,

Bayan ta kammala maganarta ta tace “Junaid ni zan koma kitchen, nasan gobe akwai labari mai daɗi daga wurinka, zanji ya haɗuwarka da juliat ta kasance,”

Dariya kawai junaid yake yi, yana faɗin “insha Allah aunty azmee, ngde ssae ke ce silar farin ciki na,”

Murmushi azmee tasaki tare da juyawa ta fice tana cewa “Karka manta kaifa ɗane a wurina junaid, cikina ne kawai baka zauna ba, amma ni na shayar dakai ina alfahari da hakan,”

Rufe door ɗin yayi, tare da daka uban tsalle na murna, runtse idonsa yayi tare da dunkule hannunsa yana faɗin “Can’t wait to seeeeeee you Sehrish My dreamy Girl………….

koma wa kitchen ɗin azmee rayi suka ci gaba da aiki, tana lura da sehrish cikin sauri take yin aikinta fuska ƙumshe da murmushi, ba don komai ba sai don tayi saurin taje tayi wanka ta kimtsa bayan sallar magriba ta wuce garden wurin wanda aka ce zata haɗu dashi 😘

💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕

…………..Twins………………………………

kwance su ke rungume da juna a katafaren ɗakin da suka ɗauka na hotel ya haɗu iya haɗu, da alama sun gama biyan buƙatar junansu ne bacci ya kwashe su, sam babu sutura ajikinsu zir suke manne da juna kamar tip da tyre,

Wayar Jahan ce dake saman bedside table ta soma ringing taken waƙar Shape of you ta Ed shareed,”

Almost 3 times tana ringing an rasa wanda zai ɗauka cikinsu saboda daɗin bacci,  har calling ɗin yayi rejecting, wani ya sake shigo wa da ƙarar gaske,

Ayaan ne yafarka cikin kasalalliyar murya ta wanda ke cikin shauƙi da jin bacci yace,”babe ur phone is ringing pls get up and pick the call, its disturbing my ears,” ya ƙare maganar yana bubbuga ƙafadar Jahan da hannunsa,

daker jahan ya buɗe idonsa da su kayi jawur ya kallesa da su kallon so da ƙauna yace “Honey bazaka gane bane, ko yatsana bana ji zan iya motsawa, wata irin kasala nake ji kasan fa mun jima muna yi,”

lumshe ido Ayaan yayi tare da ƴunƙurawa ya tashi shi, yakai hannu ya ɗauki wayar, jahan na cewa “Yawwa honey duba ka ga wane ɗan takurar ne, ke kira na,

natsuwa yayi yana dubawa, cikin tsananin tashin hankali yace “Jahan!!!! wlh Babban yaya ne ke kira !!!” yayi maganar da ƙarfin,

Ae tuni Jahan ya miƙe garas jin an ambaci sunan Babban yaya, jiki na rawa yasanya hannu ya karbe wayar dake hannun Ayaan yana kallon sunan da ya bayyana akan screen ɗin wayar,”

Wani irin kallo jahan ke bin Ayaan dashi cikin kashe murya ta masoya yace “Ayaan ka daina mun irin wannan abun Allah! kamin kowane irin wasa amma banda wannan,’

Tuntsirewa da dariya Ayaan yayi yana masa gwalo tare da cewa “Ni zaka cema wae kasala kake ji  ko yatsa ba ka iya motsawa, shiyasa namaka wannan wasan,”

Pillow Jahan ya wawura dake gefensa ya kifa masa a fuska, nan suka shiga wasa da junansu,

A ƙarshe suka koma suka kwanta, ba tare da sun bibiyi kiran da ake masu ba, Jahan ne ya kwanta yayin da Ayaan ya kwantar da kansa a ƙirjinsa, shi kuma jahan ɗin yana shafa masa sumar kansa, cikin sanyin murya Ayaan yace “Jahan! anya kana tunanin ranar da asirin mu zai to nu? wane hukunci za’a mana,”

“Kisa,” kaitsaye Jahan ya bashi amsa, cikin tsananin tsoro Ayaan ya janye jikinsa daga na jahan ya tashi zaune saman gadon yana kallonsa a tsorace yace “Jahan dagaske kisa ne? Kashe mu za’ayi,”?

Tashi zaune shima Jahan yayi tare da cewa “Am serious Ayaan kai fa mai ilimi ne ! Sarai kasan hukuncin waɗanda ke aikata homo a addinin musulunci,! munsan da hakan kuma muke aikatawa tabbas duk ranar da Babban yaya yasani wlh kashe mu zaiyi bazae ƙyale mu ba, duk son da yake mana hakan bazae hana yaƙiyi mana hukuncin daya dace damuba domin nema mana sauƙi wurin Allah,”

Wasu irin hawaye ne ke zuba a fuskar Ayaan cikin tsananin tsoro yace “Jahan ni banso na mutu yanzu, banso na mutu ina aikata wannan mummunan zunubin wlh banso, Jahan kullum babban yayanmu yana ja mana kunne akan mu riƙe mutuncin mu, mu ji tsoran Allah mu guji sa6a mashi domin muyi kyakkyawan ƙarshe kuma mu tsira ranar gobe ƙiyama amma meyasa zamu zama na farko da zamu karya masa zuciya duk irin soyayyar da yake nuna mana”?  cikin ƙunar rai Ayaan ke maganar yayin da idonsa ke zubar da hawaye masu raɗaɗi,

Jikin Jahan ya gama mutuwa shima idon nasa cike tab da hawaye yace “Ayaan yaya zamuyi? bamu da za6i, kaima kasan bada san ranmu muke aikatawa ba, Ayaan….kafi kowa sanin azaba da raɗaɗin da muke sha in har mu ka wuce 24 hours bamu sadu da junanmu ba,’

Cikin shesshekar kuka Jahan ke kora masa bayani, cikin sanyin murya ayaan yace “Babban yayan mu yazame mana komai arayuwa, ya sama mana rayuwar farin ciki, kullum yana ja mana kunne akan kar muja masa abun magana a family roƙonsa kenan amma mun gaza cika masa hakan, ko da yaushe dangin abbanmu suna cewa ƴa,ƴan momyn mu basu da kunya fitsararru ne, tabbas sunyi gaskiya tunda gashi nan, bamu tsoron Allah muna aikata zunubi irin wannan,…….” .

“Ya isa haka !!! Nace ya isa Ayaan , kadaina cewa bamu tsoran Allah, mu bayin Allah ne kuma masu tsananin tsoransa, Allah yana sane damu kuma asannu zai kawo mana ƙarshen matsalarmu, zai warware mana duk wata masifa dake damun mu,”

Jahan ne yayi wannan bayanin a yayin da ya komar da jikinsa ya kwanta tare da jan bedsheets a lullube jikinsa yana sharar kuka, .

Shima ayaan ya kifa kansa jikin pillow yana matsar kwalla, suna masu danasanin rayuwarsu da tazo musu a haka,” 😥

‘Shin meke damun su TWINS ne ? da son ransu suke aikata hakan ko kuwa akwai wani abu a ƙasa ne? Nifa na rikice ina buƙatar ƙarin haske game da waɗannan bayin Allah,’ . 😥

……………Sehrish…………………

Bayan sun kammala dinner ɗin, azmee tace

“Sehrish ki je ki yi sallah, bari na idasa jera dinner ɗina, sannan karki manta ki isa a lokaci dan Allah,”

Azmee ce tayi maganar a yayin da take fice wa daga kitchen hannunta riƙe da warmers cikin tray ,

“To aunty azmee ynx kam zan kimtsa,” tana gama faɗan hakan ta wuce bedroom ɗinta, bayan tayi sallar magrib tayo wanka shaf shaf tayi ta kimtsa, cikin dogon wando Jeans da riga ƴar ta maza, ta naɗe gashin kanta taturasa cikin hularta sannan ta laga mayafi daga sama, ta gyara gashin bakinta ya zauna daram,

Tsayawa tayi tana kallon kanta cikin mirror ɗin, murmushi ta ɗanyi kafin tasa kai ta fice, tana Allah Allah acikin ranta,

Babu kowa a babban falon, bi tayi ta wuce time din da  tazo harabar gidan adai dai time ɗin motocin su suka soma shigowa hada ta sgr duk ba’a tare da suke ba, amma atare suka iso gidan hadasu kanal yusif dasu irfan fawan da sauransu,

tsayawa tayi tana kallon motocinsu, firfitowa su kayi atare, kowanne cikin kakinsa, sai bayan sun fito sannan wani soja narkeke ya fito daga cikin motar Sgr ya buɗe masa ita, shima ya fito dama jeans ne da t-shirt ajikinsa, ganin sa yasa su kanal yusif ƙarasawa suna gaishe shi,

Gwanin burgewa sehrish tabisu da kallo especially mutumin ta, sai da duk suka shige ciki sannan ta wuce cikin garden ɗin gidan cike da fargabar wa zata tarass,

Ko da ta isa cikin hadaɗɗen garden ɗin sai ta boye bayan bishiya tana leƙensa

Tsaye yake cikin dress na pakistani masu kyan gaske riga dogowa ta wuce guiwarsa sai wano burgujeje irin nasu,

Rigar mai dogon hannu ce purple tasha adon sparking stones, wandon kuma light pink ne zallah ba kwalliya jikinsa , daga gefen kafaɗarsa scarf ne (mayafin da mazan pakstan ke yarfawa a shoulders ɗinsu)

Zuba mishi ido sehrish tayi tana tunanin wanene wannan ? Saboda ya juya mata baya, bazata iya shaidasa ba,

Launin fatarsa da tagani fari tass da kuma kwantacciyar sumar kansa smooth black ya tabbatar mata da cewa bazai wuce Junaid ba ko Fawan ko cikin su twins saboda sune ke da wannan hasken 6ayau,

Shiru tayi tana ƙoƙarin gano kowanene da kanta, amma sam ta kasa canka har sai da muryarsa ta ratsa kunnanta mai sanyin gaske “Sannu da zuwa,”

Murmushi sehrish ta saki tare da cewa “Yawwa sannun ka,”

Shima yace “yawwa meyasa ki ka 6oye a bayan bishiya, kina shakkar ganin kowanene ya kamata ki fito,”

ƴar dariya sehrish tayi sannan ta fito daga bayan bishiyar ta tsaya daga bayansa tace “Wanene kai,’ meyasa bazaka juyo ba mu fuskanci juna ba?

“Zan juyo amma firstly saikin fara faɗamin wanene Ni ki canka kawae,”

Wani irin daɗi ne ya rufe sehrish, natsuwa tayi tana kallon bayansa ciki da son gano ko wanene shi,

Shima shiru yayi yana jin duk wani motsinta, burinsa sehrish ta shaida shi kafin ya juyo mata da face ɗinsa,

“Am waiting 4 u Sehrish,” ya faɗi da murmushi a face ɗinsa,

Shiru sehrish tayi tana tunanin wani abu aranta,

“Idan har zanyi zurfin tunani zan iya gano wanene, na farko wannan hasken shi fari ne sol, fawan kuma hasken fatarsa mai yellow yellow ne, Ayaan da jahaan kuma nasu yayi ja haka launin fatarsu, kai wannan fa kamar junaid ne,”

Tayi maganar acikin zuciyarta, wani tunani ne ya sake zuwa mata,

Junaid shagwa6a66e ne duk yadda yayi magana ana gane wa, yanzu bari na gwada wani abu a sanina da junaid baida jumuri in ya gaji sosai yaji naƙi bashi amsa dole yayi magana da shagwa6a,

Murmushi sehrish tasaki ta tsaya riƙe da waist ɗinta tana jiransa ya hasala yayi mata magana,

Aikuwa maganar sehrish ta tabbata, da yaji shiru shiru bata bashi amsa ba kuma tayi masa shiru,

Cikin shagwa6a ya buga ƙafarsa tare da cewa” wai ba zaiki yi magana ba, so ki ke ki wahalar dani koooo.. .’  yayi maganar tamkar zaiyi kuka,

Fashewa da dariya sehrish tayi cikin tsantsar murna da farin ciki tace ” *JUNAID*!!! Wlh kaine na gano ka ,” tayi maganar da ƙarfi,

Wani irin farin ciki ne ya rufe junaid juyowa yayi fuskarnan tasa ɗauke da kyakkyawan murmushi ,

*Zubawa juna ido su kayi suna ta faman sakarwa juna murmushi, don ita sehrish hada dariya sosae Sam farin cikin ta ya gaza 6oyuwa* 😁😁😁

(Nace ba Romeo fa yau sun haɗe da juliet, don haka sai mun haɗu a next week)

Share 🪩*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

_🔥The father of soldiers🔥_

~hot novel drama~ 🌹

*Mallakin*

*Hafsat Bature Moh’d*

~BossLady~✨

Not edited

*page 79-80*

daker suka dakata daga yiwa junansu dariya, junaid yace “bismillah sister tukur ga wuri ki zuna,” yayi da maganar yana nuna garden chairs ɗin,

Murmushi sehrish tasaki cikin jin kunyar abunda junaid yace wato Sister tukur, cikin natsuwa suka zauna suna fuskantar junansu haɗaɗɗun kujeru ne irin french bishro design ɗin nan, gabansu akwai table launinsu coffee color,

Sai faman sunnar da kai sehrish take yi tana wasa da yatsun hannunta,

Yayin da junaid ya zuba mata ido,bayan masu ƴan mintina yace “Can we talk”?

“Yeah” sehrish ta bashi amsa

Junaid yace “First of all, naji daɗin ganinki as a woman, ina fata ke ma haka?

Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa “Sosae ma,” murmushi junaid yayi kafin yace “in da gaske ne, to inaso ki ɗago da idonki ki kalli cikin nawa muyi magana, sannan ki cire wannan gashin bakin da cap ɗin nan inaso na ganki da kyau,”

ɗan waro ido sehrish tayi tare da cewa “In wani ya ganni fa”?

Junaid yace “ae babu wanda zai zo nan, duk ynx suka dawo agajiye so karki ji komai,

Ajiyar zuciya tasaki tare da sa hannunta ta cire gashin bakinta, ta ajiye shi asaman table ɗin gabansu, sannan a hankali tasanya hannu, ta zame mayafin da ta naɗe hular dashi, sannan ta zame hular gaba ɗaya, ta ajiye su asaman table ɗin duka,

Lumshe ido junaid yayi yana kallonta, a yayin da sumar kanta ta soma warwarowa da kanta ta zubo mata har ƙugunta, tayi mata tamkar hijabi, kwantacciyar suma dark black very smooth,

Cikin sanyin murya ta wanda ya gama kamuwa yace “Masha Allah yanzu nan tukur ɗinmu ne ya koma haka? Ƴar kyakkyawar budurwa,”

Yayi maganar da zolaya, fashe wa da dariya sehrish tayi, sai da ta tsagaita sannan ta samun ƙwarin guiwar cewa “I want to ask you something pls,”

Junaid yace “Ina sauraron ki,”

ɗan gyara murya tayi sannan tace ” yaushe ne ka gane cewa ni maca ce? kuma sannan ya kaji aranka,”

murmushi junaid yasaki kafin yace “Na jima  da sanin hakan, but am sorry to say bazan iya faɗa miki ranar da nagane cewa ke maca ce ba, sai nan gaba, sannan maganar ya naji araina dana gane hakan, seriously i felt so happy bansan ma yanda zan misalta ba,”

Wani irin daɗi ne ya rufe sehrish sai faman satar kallonsa take tana sunnar da kai,

“I ave a question too,” junaid ya tambaya,

Cikin sauri sehrish tace “What”?

“It’s just a question pls, don’t feel anything, am… Kece ki ke mun amfani da wayata ko?  Ya tambaya yana kallonta,

Wurga ido sehrish tayi ta ɗan kalli ruwan dake gudana wurin, taƙi yarda su hada ido saboda jin kunyarsa,

ƴar dariya junaid yayi kafin yace “tun da bazaki ban amsa ba, bari ni na baki, kece ki ke mun amfani da wayata kina kiran ƴan uwanki, da farko Nasanya security ɗin wayata finger print, wato sai kika rinƙa lalla6owa while i was sleeping kina using da yatsana kina buɗe wa, afterwards dana gane ana mun using  da phone ɗinsa saina maida shi face security nan ma ki kayi kokarin ki sa a face dina don ki bude ko ? Anyi hakan ?

Ya tambaya da murmushi a face ɗinsa yana kallonta, sai faman sunnar da kai take yi tana dariya,

Junaid yaci gaba da cewa “ranar dana kama ki a bedroom ɗina, kina rarrafe zaki kin lalla6a zaki gudu, time ɗin na tashi daga bacci, muka haɗa ido dake zaki fice, kawai sai kika fashe mun da dariya ko ba haka akayi ba,’? Ya ƙare maganar tasa da tambaya,

Hannu sehrish tasanya a bakinta, tana ta faman tiƙar dariya shima kansa dariyar yake yi,

Bayan sun tsagaita da dariyar tasu junaid yace “bayan nan akwai time ɗin da kina saving ɗinmu abincin dinner, phone ɗina yayi ringing, nayi picking call ɗin kwatsam sai ki kaji muryar Sister ɗinki, wanda hakan yasanya arazane ki ka saki cup ɗin dake hannunki har ki ka 6arawa Ayaan ruwan coffee mai zafi, Anyi hakan?

Ya sake jefa mata tambayar yana yi mata kallon MAGE TA KAMA 6ERA,

Cikin jin kunya sehrish tace “Am so sorry pls,”

“why are u saying sorry to me sehrish? Ni baki mun laifin komai ba, abun ma sai ya zamar mun kamar drama, naji daɗin hakan,”  ya faɗi yana ci gaba da kallonta,

After some minutes duk sunyi shiru sai da arinƙa jefa wa juna murmushi ana satar kallon juna, rishi jin abun take tamkar a mafarki wai yau itace tare da ɗaya daga cikin ƴa’ƴan abban sojoji mai sauƙin kai haka, addu’arta shine Allah yasa sauran ma su kasance masu sauƙin kai a duk lokacin da Allah zai sa su gane cewa ita maca ce,”

Jin tayi masa shiru yasanya shi sake cewa “a matsayin me zaki ɗauke ni yanzu Aboki ko ɗan uwa”?

Sehrish tace “Da so samune duka biyun, I need both,’

Wani irin daɗi ne ya rufe junaid kamar kamar me, ji yake kamar ya rungume sehrish ajikinsa, farin cikinsa sam yagaza 6oyuwa,

Sun sha fira har wurin sallar magrib sannan suka tsagaita, sehrish ta maida gashin bakinta da hularta duka yadda suke sannan suka kama hanya atare suna ƙara tattaunawa kamar karsu rabu da juna, sai da rishi ta fara shiga ciki da jimawa, sannan junaid ya shiga saboda kar a gansu atare,

(Guys nima fa sun burgeni wlh, haɗuwarnan ta rishi da junaid ta tafi dani)💋

________________________________

*Dama nace akwai annoucement to gashi, Littafin nan littafi ne mai yawan gaske Kuma idan nace zan datse shi to tabbas zan lalata littafin daɗinshi zai ragu sosae bama zai yi tsari ba don haka Part 3 of this Novel will be paid Book, abubuwa da dama waɗanda basai na faɗa ba Ina fata zaku goyi bayana, Nasan duk ranar dana ce na dakata da rubutun littafin nan babu wanda zaiji daɗi acikin readers ɗinshi don haka muyiwa juna Adalci, Sorry 4 the late annoucement* 😔🙏

Ci gaba

_________________________

Zuba musu ido goggon katsina tayi tana kallonsu ko kyaftawa babu, kamar wadda tayi gamo da aljanu,

Zaune suke suna facing ɗinta sun matse juna cike da tsoran abunda tsohuwar zata ce musu,

Ta jima da farka wa daga bacci amma batasan dasu acikin gidan ba, saboda suna can cikin ɗakin saude suna bacci, ita kuma sauden bata sanar da ita cewa Omar ya sa an kawo wasu ƴara ba sai yanzu bayan sallar magrib ta ke sanar da ita, shine tasa ta kira mata yaran tagansu,”

“Jahad me yasa take kallon mu? bata son mu ko? Korar mu zatayi ko”? Hosana ce tayi ƙasa ƙasa da murya tana raɗawa Jahad a kunne,

Jahad tace “nima bansani ba, amma ina tsoran kartace bata son mu, in ta kore mu, ina zamu sa rayuwarmu?   Cikin raɗa suke maganar tasu, duk sai da suka gama raɗe-raɗen sannan su kaji goggon katsina ta fashe da dariya tare da cewa

“kun ta6a jin inda uwa ta guji ƴa’ƴanta !? Ku fa jinina ne, ƴa’ƴan abusufyan ae ƴa’ƴana ne halak malak,”

Kallon juna su kayi jin abunda tsohuwartace, atare suka hada baki tare da cewa “ABUSUFYAN kuma wanene shi ? mu bamu son shi ba,’

ɗaure fuska goggon katsina tayi tare da cewa “Bansan shashanci in ma zolayata ku keyi to ku daina, ni ba amun irin wannan wasan yanzu na burkice,  ku faɗamin gaskiya ku ba ƴa’ƴan abusufyan bane,?

Babu wasa a fuskarta tayi tambayar,

hankali atashe suka ce “wlh bamu son shi ba, bamu son wa kike magana akai ba, mu yau muka zo gidan nan,”

Sassauta murya goggon katsina tayi tare da cewa”kuna nufin ku ba ƴa’ƴan abusufyan bane ? Ni zaku raina wa hankali ko? Kubar ganin nafara tsufa da hankali na wlh Wannan furfurar da kuke gani akaina, bata tsufa bace ta arziƙi ce,” 😡

ta yi maganar tana hararansu, cikin tsananin tashin hankali jahad tace “wlh goggo gaskiya muke faɗa miki, bamu son shi ba, mu ba ƴa’ƴansa bane,”

Jin yadda jahad ta karyatata yasa ta fashe wa da matsanancin kuka, zaro ido su kayi ganin tsohuwar na sharar kwalla, kuka fa sosai hada jan majina tana faɗin “saboda na fara tsufa kke gudu na ko? ban ta6a tunanin ƴa’ƴan abusufyan zasu guje ni ba, wlh sai na kirasa a waya nasanar masa tashin kunyar da kukayi wa goggonsa wlh baxai ƙyale ku ba…’

tayi maganar tana shesshekar kuka abun kamar a mafarki su hosana da jahad suke kallon lamarin,

Jin kukan goggo yasa saude fitowa daga kitchen hankali a tashe karaso wa tayi tana faɗin “Subhanallahi goggonmu me nake gani haka kamar kuka a idonki,’

Ƙara fashe wa da kuka gaggon katsina tayi tare da cewa ” saudatu dan Allah waɗannan ba ƴa’ƴan abusufyan bane?  tayi maganar tana nuna su Hosana da hannunta,

Sakin baki Saude tayi galala cikin mamakin rigimar goggon katsina, girgixa kai tayi tare da cewa ” wlh narasa meke damunki goggo ! Sarai fa kinsan cewa Uncle abusufyan bai ta6a aure ba ko? wai yaushe ma yayi budurwar ballantana ma aure har akai ga ƴa’ƴa, anya goggo kina shan maganinki akai akai’?

Miƙewa tsaye goggon tayi idonta cike taf da kwalla fuskarta a damuje tasa idonta cikin na saude tace” saudatu hada ke za’a ƙaryatani ko? ke ma kallon zararriya kike mun ko? saudatu da hankali na wlh, waɗannan yaran ƴa’ƴan abunsufyan ne, Jini na ne ina ji ajiki na, dan Allah kudaina mun yawo da hankali wlh zuciyata zata iya bugawa in mutu a wurinnan,”

Goggo tayi maganar cikin ƙunar rai da jin ɗaci aranta saboda ita harga Allah ta tabbatarwa kanta cewa tagwayen nan ƴa’ƴan abusufyan ne, mutun da bai ta6a aure ba, hasalima ma ba a nigeria yake zaune ba gaba ɗaya,

Shiru saude tayi tana kallon goggo dake ta faman kuka kamar ƙaramar yarinya aranta tace “tabbas goggo fa hauka ya tashi gadan gadan, don haka a kunnan babban likita dole nasanar mishi a bincika kwakwalwarta in ba haka ba kawai daga ganin yara sai kice wai ƴa’ƴan Uncle sufyan ne, yau yau ɗinnan fa yaran nan suka fara zuwa gidan nan tab lallai akwai matsala awurin nan……..”, muryar goggonce ta katse ta da cewa

“Saudatu kinyi shuru baki ce komai ba? ƴa’ƴan abusufyan ne ko?

Yarfa hannu saude tayi saboda tama rasa amsar da zata bata,

Jinjina kai goggon katsina tayi tare da mayar da idonta kansu hosana da jahad waɗanda jikinsu keta faman kerma saboda tsoran tsohuwar don sun lura tana da ta6in hankali,

Rai a6ace tace  “Wlh ku ƴa’ƴan abusufyan ne !! Ni zakuyiwa karya don kutmar ubanku !! Kunci buhun ubanku ƴan kan uba

!!! ,

Hankali atashe su hosana ke kallonta, saude kuwa aza hannu tayi akai tana faɗin”goggo dan Allah kidaina !! Kidaina zaginsu mana akan abunda basu sani baaa……

tunkan ta ida goggon tasa hannu ta buge mata baki, dafe baki sauden tayi don taji zafin bugun,

Ci gaba da magana goggon tayi a birkice tana kuka, ” Ae dama nasani ba wanda zai goyi bayana akan magana ta, amma ni nasani wlh ku ƴa’ƴan ZAINABU ne, dama haka uwarku take kamar ku ɗinnan, shegen taurin kai da kafiyar tsiya, kunnan ta kamar na zomo, fitinanniyar yarinya ƙiri-ƙiri ta guji jini na, dama sai da nace mata cikin jikinta na Abusufyan ne amma taƙi yarda ae dama nace mata jiki magayi amma taƙii ji, kunnan ƙashi ko ae ynx nasan taji jiki bawan Allah bai mata komai ba amma taƙisa, wlh cikinsa ne ku ƴa’ƴansa ne amma kunƙaryata ni, ga falo falon kunnuwanku nan irin na abusufyan shima dayake baijin maganata kangararre ne yaƙi jin magana ae gashi nan……

Zuba kawae goggon katsina  takeyi ba ƙaƙƙautawa kai kace radiyon da bata da saiti, notikan kanta sun kwance sai faman zazzaga musu bala’e take yi, tana yi musu magana akan mutanen da basu san da zamansu ba,

tashi su kayi atare su ka tsaya suna kallonta haƙika sun tsorata da tsohuwar tuni idonsu ya cicciko da kwalla,

Goggon katsina bata dakata da surutun ba har sai da Saude tace “goggon kiyi hakuri dan Allah, nima na yarda cewa su ƴa’ƴan Uncle sufyan ne, sai yanzu na ƙara lura da kamannin nasu dagaske ne abunda kika faɗa,

saude na gama faɗan maganar ta kalli su hosana tayi musu alamar su amince suma da maganarta don asamu ta lafa,

Cikin sauri suka zube saman guiwowinsu agabanta tare da cewa “Dan Allah kiyi haƙuri goggonmu, munyi miki laifi, tabbas mu jininki ne mu ƴa’ƴan abusufyan ɗinki ne, ki yafe mana munsa kin zubda hawayenki,”

Sanyi goggo taji aranta dama ita burinta kawai su amince cewa su ya’yansa ne, hannu tasa tana share hawayenta, bayan ta kammala ta miƙa hannayenta tare da ruko nasu ta tsayar dasu tsaye fuskarta da murmushi sai kace ba wadda tagama sharbar kuka tace ”  Alhamdulillah har hankali na ya kwanta ynx, amma fa kun wahalar da gaggonku sosae kun sani ina ta faman zubda hawaye na, da ace abusufyan na nan kuma yasan abunda ku kayi ma goggonsa tabbas sai ya muku dukan tsiya” ,

Sunnar da kai su kayi tare da cewa “ayi mana afuwa goggonmu, bazamu ƙara ba insha Allah,”

Murmushi tasaki tare da cewa ” ku koma kuzauna ƴa’ƴana, yanzun nan zan kira mahaifinku a waya ku gaisa,”   🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️

BossLady❤️ Inaso naji ta bakin ku game da annoucement ɗina nasan kowa ya karanta, sannan comment akan page ɗin yau 👏👏👏

*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ

ﺭﺍﻓﻴﺖ🌹❤️

*Mallakin*

*🌹Hafsat Bature Moh’d*🌹

~BossLady~💋

Page 81-82 part 2

*Meaning of name sehrish is an arabic name, ma’anar sa kuma Glamorous Personality* 🌹

Har haɗa baki suke yi wurin cewa “mahifinmu kuma ! A waya !?.

Da ƴar dariya a fuskarta tace”Eh mana, ae kullum sai ya kira ni mungaisa,’  tayi maganar ayayin da ta kama hanyar zuwa bedroom ɗinta don ta ɗauko wayarta,

Hannu suka aza akai alamar sun shiga uku,  ita kanta saude tama rasa me zatayi abun ya ɗaure mata kai, lamarin goggo sai addu’a tsufanta da rigima yazo mata,

“Kada ku damu kunji kawai, ku kwantar da hankalin ku, in ta kawo muku wayar ku amsa ku gaisa dashi amatsayin mahaifinku, Uncle sufyan ya riga da yasan rigimar Goggonmu wayayye ne shi zai fahimce ku,”

Saude ce tayi musu wannan bayanin, jiki amace suka amsa mata da cewa “Toh,”

Sannan ta juya ta koma kitchen saboda tabar girki saman gas,

Zuru su kayi suna jiran zuwan gaggon katsina da waya, babban tashin hankalinsu yarda zasuyi waya da mutumin da goggo ta ƙaƙaba musu a matsayin mahaifinsu wanda basu ta6a gani ba kuma basu san kowanene shi ba,”

suna nan zaune zuciyarsu nata bugawa sai ga goggo ta fito daga ɗakinta, hannunta riƙe da waya sai faman zabga murmushi take yi,

Koda su ka ganta gabansu ne ya faɗi rass don su a tsorace suke,

Miƙa musu wayar tayi tare da cewa “Maza ga mahaifinku nan akan layi kuyi masa magana,”

Kamar bazasu kar6a ba haka su kayi daker Jahad tasa hannu ta karbi wayar goggon tare da karawa a kunnanta tace ,”Assalamu alaikum,”

daga can 6angaren taji wata natsattsiyar murya ta amsa mata da cewa “Wa’alaikum salam,”

sai da jahad tayi jimmmm kafin ta daure ta cije tace “Abba Jahad ce ɗiyarka, ina fata kana cikin koshin lpy,”

Abusufyan ya amsa mata da cewa “lpy lou Alhamdulillah My daughter, kin yi missing ɗin abbanki kuwa,”? Yanda yayi maganar ba  ƙaramin kashe ma jahad jiki yayi ba, sai kawai taji hawaye na ƙokarin zubo mata,

Murya na rawa tace “Nayi missing ɗinka sosae abbana, ina kewarka,” tayi maganar  ayayin da take dab da fashe wa da kuka, cikin sauri tace “Abbana ga hosana ku gaisa, itama tayi kewarka sosae,”

“Okey bata wayar,” ya umarce ta,

Miƙawa hosana wayar tayi jikinta na kerma, hannu hosana tasanya ta karbi wayar tare da karawa a kunnata, duk goggo na tsaye tana kallonsu sai faman murmushi take yi, (ta haɗa Bomb)

Tashi jahad tayi cikin sauri ta wuce bedroom ɗin saude tana shesshekar kuka tana idasa shiga ɗakin  ta faɗa saman gado tare da fashe wa da matsanancin kuka, bakomai bane ya karya mata zuciya ba face tunda suke arayuwa basu ta6a sanin daɗin soyayyar mahaifi ba ga Uban amma bai da amfani,”

A can kuwa tun da hosana tasanya wayar a kunnanta tace “Abbana dagaske kaine mahaifin mu kamar yadda goggo ta faɗa,”

On the other hand abusufyan yace “My daughter are u doubting abt ur father? nasan kinyi kewata ne shiyasanya kike kokwanto akaina,”

aikuwa jin ya tabbatar mata da cewa shi mahaifinsu ne yasanya ta fashe masa da kuka tare da cewa “dama nasani kaine mahaifinmu, ba wancen mugun ba, sai da nace ma Oumma mu bamu kama dashi mummunane shi mai baƙar zuciya amma taƙi yarda, ni nasani ba abban mu bane, babu uban da zaiyi wa ƴa’ƴansa haka, kaine mahaifinmu,……”

Katseta yayi tare da cewa “Silent pls, sorry my daughter bana fahimtar zancen ki i was busy now, zan kira anjima,’

yana gama faɗan hakan ya kashe wayar saboda baisan inda zancen nata ya dosa ba, shi dai kawae ya amsa kira ne kamar yadda goggonsu ta sanar dashi cewa ƴa,ƴanshi sun zo, sarai yasan rigimarta shiyasa yabisu a hakan,

Ganin ya katse kiran yasa hosana fashewa da kuka, wurgi tayi da wayar goggon saman kujerar sannan itama ta miƙe tana ci gaba kuka ta wuce ɗakin saude,

Jikin goggo yayi sanyi, ita a tunaninta abusufyan bai kula da  yaransa shiyasa suke kuka, don haka taci alwashin zata sashi dole saiya zo nigeria ya ɗauki ƴa’ƴansa ya koma dasu can qasar da yake zaune, a ranta tana cewa “in banda shiririta irin ta abusufyan ka kama hanya ka tafi ƙasar Turƙiya kabar yara cikin damuwa, gashi nan sai faman kuka suke yi, Allah ni da kai ne, saina sanar wa AMMI halin da ake ciki,

Ta idasa maganar tata tare da sa hannu ta ɗauki wayarta ta wuce dakinta tana ci gaba da surfa bala’e akan rashin adalcin abusufyan,

……………………………………..SEHRISH…………………….

tun da suka koma ciki take jin zuciyarta wasai, hankalinta kuma ya ƙara kwanciya yanzu,

Gaba ɗaya matasan gidan sun kammala dinner ɗinsu kowa ya koma bedroom ɗinsa,

Babu kowa ita kaɗae ya rage ta kai wa Babban yayansu dinner ɗinsa, shine kaiwa bai sauko yaci ba, dama azmee tace sometimes kai masa ake a part ɗinsa,

Tsoranta kar yayi mata abunda yayi mata da safe, wato da yayi watsi da tray ɗin hannunta,

A natse take tafiya zuciyarta na ɗar ɗar hai ta haye upstairs ta wuce part ɗinsa da sallama ta shiga babu kowa aciki, agyare yake tsaf haske ta ko’ina ga ni’ima acikin palor insa,

A hankali tasanya kafa tashiga ta ƙarasa gaban table ɗinsa ta ajiye tray ɗin ta tsaya riqe da ƙugu tana jiran fitowarsa bin ko’ina take da kallo tana ƙara jinjinawa haɗuwarsaa, .

bakomai ke fisgarta ba fa ce sanyayyan ƙamshin dake tashi tana burin wata rana ta samu damar da za ta ɗan miƙe ƙafa a saman 3 seater ɗinsa ta kwanta, 😌😒

Sauko ƙafarsa yayi fara tass babu takalmi a kafar jikinsa na sanye da sleeping dress red color masu laushin gaske, jikinsu akwai zanene flowers masu kyau, riga da wando ne abunka ga handsome stylish man ga kira sun bi shape ɗin jikinsa kai kace don shi akayi kayan, kyau kam ba’a magana ku kun sani ae,

tana cikin wannan kalle kallen idonta ya hango mata shi to fa nan take ta rasa duk wani karsashi na jikinta, bin shi kawai take da kallo, cike da wannan tafiyar tasa ta nigogin basawa ya karaso hannunsa ɗaya na cikin aljihun wandonsa, halittar kyawunsa ta kara fitowa sosai daga saman rigar ƙirjinsa a buɗe yake farar fatar sa ta bayyana muraran,

Sai kamshi jikinsa yake kamar wanda aka tsamo daga kogin turare,

Ga sumar nan tasha gyara sai salƙi take tana ɗaukar ido,

Zama yayi yana naɗe hannun rigarsa,

Sai da rishi ta dai dai natsuwarta sannan tace “Barka da fitowa Babban yaya,”

“Yawwa,” ya bata amsa a takaice,

Har cikin ranta jin daɗin muryarsa take saboda yanayin yadda hausarshi ke fita irin ta wanda bai ƙware ba,

Cikin girmamawa sehrish ta sake cewa “Me kake buƙata na zuba maka,’?

ta tamabaya saboda kartayi ba dai-dai ba,

“Abun da ya dace,” ya bata amsa,

Murmushi tasaki tana kallon face ɗinsi musamman gashin girarshi da eye lashes ɗinsa,

Hannu tasa ta buɗe plate ɗinda ke ɗauke da friend meat (tsiran nama) yasha kayan ƙamsi yaji mai yaji komai,

tura mishi tayi agabansa sannan ta ɗauki bottle milk ta zuba mishi a glass cup ta ajiye masa,

bayan ta gama ta ɗan ja da baya tana ƙare masa kallo, yanayin yadda yake ɗaukar tsiren yana turawa a bakinsa ba ƙaramin kyau yayi mata, ji take ina ma da hali ta bashi abaki saboda ta sauƙaƙe mishi wahalar ,😒

Wayar sa ce dake ajiye cikin bedroom ɗinsa  ta soma ringing da sautin gaske taken wakar nan ta  Imran khan (Satisfya) wadda yake cewa “am rider,provider, bring the heat girl i will bring the fire,”

gyaran murya yayi tare da cewa “My phone,” cikin sauri sehrish ta wuce bedroom ɗinsa asaman pillow ta samu wayar ɗauka tayi jiki na rawa kamar ta riƙe bomb haka take ji, ta riƙe wayar manya ba,

Fitowa tayi da sauri taje ta miƙa masa, sai da ya fara cirar tissue ya goge hannunsa sannan ya sake tearing ɗin wani acikin hannunsa sannan ya miƙa hannu ya karbi wayar  tare da picking call ɗin ya kara a kunnansa,

Zuru sehrish tayi tana jira taji mai zai tattauna acikin wayar, sai dai kash cikin harshen spanish yake magana kalma ɗaya ce sehrish ta tsinta, da taji yace “Mom,”

Jinjina kai tayi aranta tace “Ina ji da mamansa yake waya, ashe mahaifiyarsu na nan, ko tana ina ne ita?

ta, tambayi kanta ba amsa,

babban burinta yanzu shine su haɗa ido dashi atlease yasan da zamanta sam bata tunanin hakan zai iya janyo mata matsala acikin gidan,

A tunanin sehrish SGR bai ta6a kallota ba, tabbas hakane amma rana ta farko da tayi masa 6arin fruits a bedroom ɗinsa, ya hangeta ta cikin mirror ya ganta a matsayin namiji tsaye cikin fargaba a time ɗin, duk da bai shaida kamannin fuskarba amma yasan cewa namiji ne mai kula dashi wato ɗan aikinsu,’

Kammala wayar yayi tare da mayar da wayar ya ajiye gefensa, yaci gaba da cin dinner ɗinsa sehrish na saving ɗinshi in ya kammala da wannan ta zuba mishi wancan haka suke abun nasu,

Goya hannayenta tayi a ƙirjinta tana kallon sumar kanshi ba ƙaramin jan hankalinta Sgr yake yi ba, hakan yasa bata gajiya da tsayuwarda take yi na saving ɗinshi tamkar mirror haka ya koma mata, tana cikin masa wannan kallon muryarsa ta ratsa ta da cewa “Kallon ya isa haka, ko saina shaƙe ne,”

Cikin sauri da jin kunya sehrish ta mayar da idonta ƙasa tana mai mamakin yarda akai Sgr yasan cewa tana kallonsaa murmushi tasaki saboda jin daɗin mgnarsa tabbas tana ji aranta cewa yana da sauƙin kai he’s not arrogant kamar yaddda ta ɗauka,

…………………. ..,,……………………………….

A tsiyace ya shigo da motar layin gidan a dai dai gate ɗin gidan ya dakatar da ita, ya shiga buga uban horn kamar zai tada motar gaba ɗaya saboda karar da take yi,

“Kai!! uban waye ke mana horn haka,”? ɗaya daga cikin sojojin dake gadin gidan ne ya tambaya da ɗaga murya, akwai yasamu amsa dai dai dashi sai ji yayi ance “Ubanka ne kazo ka duba,”

Abun ya basu mamaki aiko afusace sojojin nan suka tunkaro motar kamar wasu zakuna har haɗa hannu suke wurin buga glass ɗin motar tare da cewa “Come out !! ,”

“Ae basai kunbar umarnin na fito ba, ɗan tasha ne ni dai dai daku,”

Zuge glass ɗin motar yayi tare da sa hannu ya cire ƙumeman glass ɗin dake manne a face ɗinsa yace “Akwai magana,”?

Shiru su kayi dama ransu ya basu cewa shegen ne, ae duk duniya ba mai musu haka sai shi tantirin ɗan duniya,

Bama cikin hayyacinsa yake ba ae mafi yawancin lokaci a buge yake yasha yasha har takai masa karo,”

dogon tsoki ya buga tare da cewa “abani hanya na wuce kona bi takan mutun ba ruwana, kuma in na kashe mutun na kashe banza abanzance,”

Ransu yayi mugun 6aci a dole suka matsa mishi ya shige babban gate ɗin gidan da motarsa yana raira waƙa,”

Parking ɗin motarsa yayi sannan ya fito hannunsa riƙe da kwalbar giya, jikinsa na sanye da t-shirt baƙa sai wando crazy jeans ɗinnan ne, wani irin ɗan iskan aski ne akansa na shaiɗanu jigunannun ƴan duniya gefe da gefe an aske sumar kan, tsakiya kuma an mikar da wata tsaye ba ladabi, wuyansa na sanye da sarƙa yayin da kunnansa ke manna da earrings kai kace ba musulmi ba, saboda kwata kwata bai kama da musulmai ma, don kyau fa akwai kyau kana ganinsa ka ga bafullatani sak, duk da ba fari bane sosai amma yana da hasken fata mai kyau, yana da tsaga ta fulani agefen fuskarsa,

daker yaja ƙafarsa izuwa cikin babban falon gidan babu kowa aciki wayam, ɗaga murya yayi yadda kowa zaiji sa yace “NADAWO !!!! Hhhhhhhhh Woooo !!  Yaro ya dawo gidan Ubansa !!! Abba !! Gani fa nadawo !! ɗanka HAROON ya iso dira ta kenan na ƙaro sabon wulaƙanci buhu buhu hhhh,

Gaba ɗaya hayaniyarsa ta cika musu kunne kamar zararre haka yadinga sambatu,

Ba arziƙi suka soma fitowa kowa jikinsa sanye da kayan bacci kanal yousouf ne yafara fito wa yana buga tsoki sai Khaleed da jabeer da irfan kowa ido cike da jin bacci ya katse musu baccinsu, atare twins suka sauko daga upstairs hannunsu cikin na juna sai hamma suke yi,,

Abba ma tare da junaid suka fito sanye cikin phyjamas hannunsu cikin na juna, kowa sai faman buga tsoki yake yi a ƙuntace, tun da suka ga Commender haroon gabansu ya faɗi hankalinsu ya tashi ainin, sam babu mai farin ciki da zuwanshi duk da kasancewarshi ɗan uwansu na jininsu amma munanan ɗabi’unsa da halayyarsa tasa sun tsane shi sbd mugune na bugawa ajarida,

Cike da takaici suke kallonsa kwashewa ya sake yi da dariya tare da cewa” ƙananin ƴan iska sun bayyana ga kuma fararen balbelu,” yayi maganar yana nuna su Twins da fawan da hannu ɗaure fuska su kayi har time ɗin ba wanda ya tanka masa binsa kawai suke da ido,

“Kutmelisiiii! Ni kuka maida shashasha ina magana kowa ya zubamin ido wato ga zautacce ko?baku farin ciki da zuwana ne, ae nayi tunanin ina zuwa zaku watso aguje kamar karnuka  ku rungumeni ku sunbace ni muuuaaah a baki na,’ cike da futsara Haroon ke musu magana baya jin kunyar Abbansu,

Gaba ɗaya duk wannan suratan da Haroon yake yi a kunnansa kaf ya gama fusata yagama hasala, aiko a harzuƙe ya ƴunkura tamkar zaki yabi ta gefen Sehrish ya wuce ita kanta ta tsorata sosai ganin yadda Sgr ya fusata,

A wani irin slow sauri sauri yake tattakowa izuwa downstairs ɗin, yana idasa sauko wa kai tsaye inda haroon yake tsaye riqe da beer a hannunsa ya tunkara,

Kanal yousouf ne kawai ya lura dashi wani shu’umin murmushi yasoma saki saboda yasan mai zai faru,

Haroon na cikin wannan sambatun baiyi wani aune ba yaji saukar wasu zafafan maruka ajere saman kuncinsa,

 

Sai gashi ƙasa baje saman tiles idonsa na facing sama, wato wasu irin black stars yagani a ƙwayar idonsa masu wutsiya, kowa dake wurin bakinsa kumshe da dariya,

Sgr kuwa kara naɗe hannun rigarsa yake yi,

daker haroon ke kallonsa muryarsa na rawa yace “Ya Allah ka yafemun in zunubi nayi ka haɗani da wannan Ifritun minal jinnin, wlh danasan cewa kana acikin gidan da ba abunda zai kawo ni, Abba mai yasa baka sanar dani cewa Babban yaya na cikin gidan nan ba…? Yayi tambaye agalabaice har lokacin bai samu ya miƙe ba yana daka kwancen yake sambatun nasa idonsa na kallon ceilling,

mayar da hannu Sgr yayi ya damƙi wuyan rigar haroon da hannu guda ya ɗago shi tare da Buga shi ƙasa ya ƙife a susuce, shin wai ina kwalbar giyar dake hannun haroon ae tuni tayi gefe guda ta tarwatse,

Ganin Sgr na ƙoƙarin sake kai hannu yakaiwa haroon wani naushin yasanya abban su cikin sauri ya riƙo hannusa yana cewa “Ya isa haka pls rabu dashi ae yaji jiki,”

Jinjina kai Babban yayan yayi yana cije lips ɗinsa da ace abba yabarsa wannan naushin da yaso yakaiwa haroon da to tabbas sai yayi jinya a gadon asibiti,

ɗagowa haroon yayi ido luhu luhu yana kallon babban yayan nasu murya na rawa yace “Yanzu babban yayan mu don rashin imani ka daddage ka dunkule wannan hannun naka ƙirar samudawa da adawa bakaji komai ba ka jibge ni agaban ƙanne na,”? yayi maganar akasalance yana kallonsa,

Wato bai daddara ba rae abace sgr yace “kai wai waye ya kawo wannan ɗan iskan acikin gidan nan !?

“Da ƙafafuna nazo,” haroon ya bashi amsa a raunane, mayar da idonsa yayi akan haroon yana huci in ya biyewa haroon to tabbas zai iya halaka shi a wurin nan, don shi bakinsa bai mutuwa ana bugunsa yana magana sai dae akashe shi,

In kina so ki gode mun kiyimun share na novel ɗina 🪩 Kar a Manta da Comment 👍👏🤝*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ

ﺭﺍﻓﻴﺖ❤️💋

*Episode 83-84*

*Hafsat Bature Moh’d*

Meaning of Name Rafayet, arabic name ne, kuma sunane na Mace da Namiji both suna amfani dashi, Ma’anarshi  *Ur highness*👑,*sublimity*high rank*,

*power*💪

Dariya kawai junaid ke saki bama shi kadae ba hadasu irfan da sauransu in ka cire Kanal yusif da fuskarsa ke adaure shida babban yayansu,

duk wanda abun dake faruwa a kunnan sehrish tun da babban yayan nasu ya fito itama tabiyo bayansa, tana 6oye abayansa shi kansa baisan da mutun ba, sai dae ta leƙo ta saci kallon haroon dake baje yana sambatu ta takoma ta boye kanta, hakanan taji bai burgeta ba tunda taga fuskarsa taji bai kwanta mata arai ba,

junaid ne kawai ya lura da ita, amma ita bata ganshi ba, sai yi mata alama yake yi da hannunsa alamar ta matsa daga bayan babban yayan nasu, saboda gudun idan zai juyo kar yayi wurgi da ita, amma ita sam bata lura ba,

“Dad pls kabarni na koyawa bastard ɗinnan hankali,” ya faɗi yana kallonsa a ƙule

Haroon yace “hankali kuma na yaushe babban yayan mu ? ae tun ranar da ka fara aza tafin hannunka a kunci ne na zama cikakken mai hankali,”

ƙokari fa Rafayet yake na ya janye  hannunsa daga na abbansu yakai wa haroon bugu, amma abban ya hana hakan saboda tsoran karya naƙasa shi,

Sam bazai  iya jure kallon haroon ba a fusace ya zame hannunsa daga na abbansu tunkan ya juya junaid yayi hanzarin riƙo hannun sehrish ya janye ta, ita kanta ta tsorata da ganin yadda sgr ya juyo tabbas da baƙaramin buguwa zatayi ba, cikin hanzari ya haye upstairs azazafe yake tattaka steps ɗin benen ya wuce part ɗinsa,

“Kowa ya koma bedroom ɗinsa ya kwanta,” kanal yusif ne ya basu umarni duk suka juya shima ya wuce nasa ɗakin,

Ya rage daga Abbansu sai junaid sai sehrish dake gefe boye bayan junaid tunda ya janyota gabanta ke faɗuwa,

Kallonsu yake fuskarsa kamar zai fashe da kuka yace “Abba akan idonka yaran nan duk sun raina ni, ba wanda yayimun tarbar arziki shikenan ba komai ni daga nan zan koma inda na fito,”

yayi maganar yana ƙoƙarin tashi cikin sauri junaid ya ƙarasa inda haroon ɗin yake gaba ɗaya yasa hannu ya rungumosa cikin sanyayyiyar muryarsa yace “Yaya haroon ni ina farinciki da zuwanka sosai, i missed u so much ka tambayi Abba kaji kullum saina ce mashi yaushe yaya haroon ɗina zai dawo, (Allah sarki junaid wato shi na musamman ne, kowa nasa ne baya gudun kowa, baya son ganin kowa cikin damuwa burinsa koda zai rasa nasa farin cikin indae hakan zai farantawa wani to tabbas zai rasa nashi,)

hannu haroon yasa ya ƙara ƙanƙame Junaid tare da cewa “Dama nasani junaid kai kana sona sosai, kai kaɗae ne ka damu dani, Allah sarki ɗan uwa mai daɗi,”

“Nima ina farin ciki da zuwanka haroon, ka ta6a ganin inda uba ya guji ɗansa ? najima ina jiran ranar da zaka dawo saboda nayi kewarka sosae,” acewar abbansu,

Farin ciki ne ya lullu6e haroon cikin hanzari ya miƙe bayan sun rabu da junaid  ya rungume abbansu yana cewa “nasani Abba kaima kana farin ciki da zuwana,”

Juya junaid yayi ya kalle sehrish wadda take tsaye kamar gunki alama yayi mata na cewa itama ta gaishe da yayan nasu haroon,

Murya na rawa tace ” Sannu da zuwa yaya haroon, nima ina farin ciki da zuwanka,”

tun da muryar rishi ta ratsa kunnansa a wani irin yanayi ya ɗago da idonsa ya kalle ta, sai taji gabanta yayi wani irin mugun bugu har ta ɗan firgita a bayyane,

A wayance haroon ya saki murmushi tare da cewa “Wow junaid wanene wannan ko friend ɗinka ne,”? Ya tambaya yana kallonta,

Junaid yace “a’a mai aikin mu ne tukur bai jima da fara aiki a gidan nan ba,”

Lumshe ido Haroon yayi yana kallonta duk tsigar jikinta ya tashi saboda kallon da haroon yake yi mata ba irin kallon da namiji keyi wa ɗan uwansa namiji bane, wani irin kallo ne dake nuna cewa akwai wani abu a ƙasa,

daker ya janye idonsa daga face ɗin sehrish yana ci gaba da sakin wani shu’umin murmushi,

“My son ya kamata kaje ka huta a brdroom ɗinka dare yayi ssae, gobe zamu tattauna mu ƙara gaisawa ko,’?

abba ya tambaya yana kallonsa, haroon yace “hakane dad, but ina buƙatar abunda zan sawa ciki na, a sanya wannan mai aikin tukur yake da suna ko wama ya kawo mun abinci naci,” ya kare maganar yana yatsina fuska,

Cikin sauri sehrish tace “shikenan bari naje na kawo maka,” a tunaninta a nan zai ci saman dining,

Amma sai muryarsa ta katse ta da cewa “a bedroom  ɗina nake so akawomin junaid ka nuna masa ɗakina pls,” ya faɗi hakan tare da wuce wa yana cewa Abban nasu “Good nyt abbana,”

Abban ya amsa masa da cewa “Sleep well my son,”

ji tayi zuciyarta na bugawa, tunda ta haɗa ido da haroon taji tashin zuciya, wuce wa abbansu yayi shima bedroom ɗinsa yana barwa Junaid sakon ya same shi acan ɗaki su kwanta,”

Tsayawa su kayi suna kallon juna murmushi junaid ya sakar mata tare da cewa “Muje kitchen ko? ki haɗa wa yaya haroon abincinsa,’

itama murmushin tasakar mata tare da cewa “toh, amma babban yaya fa? inaso naje na idasa saving ɗinshi abinci,

“Shikenan kije wurin babban yayan namu, ni bari naje kitchen na shirya masa abincin nakai masa,”

Wani daɗi ne ya rufe rishi dama batason zuwa wurin wancan baƙuwar fuskar da ta gani yau a gidan,

“nagode junaid,” ta faɗi cikin sanyin murya,

Junaid yace “Never mind ina yinki sosai,” wuce wa su kayi ita takama hanyar upstairs shi kuma ya miƙi hanyar zuwa kitchen suna tafiya suna waiwayon juna,

Time ɗin da ta shiga part ɗin babban yayanmu samun shi, samu tayi babu shi a falon nasa alamar ya kammala cin abincin nasa kenan,

tunanin kwashe kayan abincin tayi amma sam tagaza samun natsuwa burinta atlease tasan wane hali yake ciki don ta lura da yadda ya fusata akan wancen baƙuwar fuskar da taji sun kira da haroon, hakan yasa ma taji bai kwanta mata a ranta ba,

tana cikin wannan tunanin tajiyo muryarsa yana faɗin “who’s there,”

Cikin sauri tace “Tukur ne mai aiki,”

“Ok brings my phone, i left it there on seater,”  yana acikin bedroom ɗinsa yake magana,

Murmushi sehrish tasaki cike da rawar kai tasanya hannu a saman 3 seater ɗin, ta dauki wayar tashi bin ta kawai take da kallo waya sai kacw wadda aka ƙera da zallar diamond saboda tsantsar kyau, juya bayan wayar tayi tana kallon sunan dake a jiki karantawa tayi a fili (SGR)

Jinjina kai tayi tare da cewa full meaning ɗinsa na nufin SURGEON GENERAL RAFAYET, kamar yadda aunty azmee na faɗa,

da sallama sehrish ta shiga room ɗin nasa ae tana ɗagowa wa’iya zubillah cikin sauri ta sunnar da kanta jiki na kerma, tsaye yake daga shi sai shorts ajikinsa babu riga wannan surar tashi mai rikitarwa ta bayyana muraran, sehrish taga abunda yafi ƙarfinta dole ta kawar da ido,

Da alama daga toilet ya fito don ga danshin ruwa nan ajikinsa, sai faman lumshe blue eyes ɗinsa yake alamar bacci yake ji sosae,

Ƙarasawa tayi zuciyarta na bubbugawa kamar zata fito waje saboda tsoransa,

Miƙa masa tayi hannunta nata faman kerma tamkar wayar zata faɗi, har time ɗin fa sgr baisan ya idonsa akan na sehrish ba, itama kuma saboda shegen tsoransa har yau bata bari idonta ya shiga cikin nashi ba, duk da bata da burin daya wuce ta haɗa ido da shi~~~

A ƙoƙarin ya sanya hannunsa ya kar6i wayar hannunsa ya gogi nata, wayyo zo gaka yadda sehrish ƙanƙame idonta ruff ta cije lips ɗinta saboda shock ɗin da taji,

Tamkar tayi hugging ɗin sgr harka take ji saboda wani irin ƙamshi dake fesowa daga jikinsa,

muryarsa ce ta shige ta da cewa “thanks,” bayan ya karbi wayar ya furta hakan batare da ya sa idonsa ba akanta,

Tsaye tayi tana kallonsa har ya wuce izuwa saman shimfiɗeɗen round bed ɗinsa mai ɗauke da wata irin haɗaɗɗiyar mattress irin wadda kai tsaye mutun na hawa zata lomatse dashi ga wasu irin lumtsa lumbutsan matasssan kai a jere dayawa, idan muka zo kan Blanket ɗinsa kuwa wayyo just speechless wani irin lallausan bargone nama rasa yadda zan kwatantashi, jibgege ne mai gashi gashi ajikinsa irin wanda mutun na shiga cikinsa ko baiyi niyar yin bacci ba nan take zaiji sa,

Sehrish fa bata bar room ɗin nasa ba kai kace tare zasu kwana ne,

Shikansa mamaki yake na ganin alamar cewa har yanzu fa house boy ɗinnan bai bar masa part ɗinsa ba, kawai zubawa sarautar Allah ido yayi yaga iya ƙarshen abun,

A natse a hankali ya kwanta tare da miƙer da dogayen kafafunsa harya so ya wuce gadon ma don Allah yayi sa da tsayi ga kuma ƙira abunsa duk shi kaɗai,

Zira ziran yatsun hannunsa yasanya tare da janyo blanket ɗinsa ya rufe har iya ƙirjinsa, sannan ya ɗan lumshe idonsa yana sauke ajiyar zuciya,

sam tagaza janye idonta akanshi komai nasa burgeta yakeyi yana yin komai a natse ba hayaniya,

Har bacci ya ɗauke sa sehrish bata fita ba leƙen beautiful face ɗinsa take,

matsawa tayi a hankali dab da bed ɗin nasa sannan ta ɗan jinkirta ta shiga yi masa addu’a daga tsayen da take, addu’o’i sosae sehrish tayi wa Sgr batare da sanin shi ba don yayi nisa a cikin baccin nasa,

Bayan ta kammala ta juya ta fice tana mai jin sanyi aranta har cikin ranta Sgr ya kwanta mata sosai,

Cike da wannan shauƙin sehrish ta wuce nata room ɗin ta haye saman gadonta fuskar nan da murmushi, abu biyu take tunawa haɗuwarsu ta yau da junaid sai kuma Babban yayanmu, duk in ta rufe idonta shi kawai take gani sai juyi take cikin bargo cikin nishaɗi,

(Allah sarki na tausayawa sehrish sosae domin ta faɗa tarkon so, son ma wanda ba son maso wani ba wannan son ya zarce hakan domin ta faɗa tarkon son wanda sam bai ra’ayin mace arayuwarshi bai da burin yin aure har abada)

________________________________________________hafsat Bature

A hankali motocinsa suka shiga cikin gidan yana zaune a back seat a hakimce ana driving ɗinsa,

Bayan sunyi parking ɗin motocin cikin sauri major ɗin nan ya fito ya buɗe masa mota,

Fitowa marshal Omar yayi yana sauke ajiyar zuciya bakomai idonsa ke marmarin gani ba face wannan Zararriyar yarinyar da ta faɗa masa a chest ɗinsa da ita ya yini a zuciyar shi,

Ba shi kaɗae bane tare da Babban likita suka dawo gidan, saboda dama nan ne makwancinsa,

Bayan sun shiga cikin main palor ɗin agajiye babban likita ya wuce side ɗinsa, yayin da Marshal Omar ya samu wuri saman 2 seater,

Shigowa major ɗin nan yayi hannunsa ɗauke da laptop ɗinsa ya miƙa masa,

Kar6a Omar yayi tare da furta “thanks,” sannan major ɗin ya sara masa kafin ya fice,

Tsit bakowa sai shikadae a falon, aza laptop ɗin yyi saman table  ɗin dake a gabansa sannan ya zaro wayarsa daga trouser pocket ɗinsa,

Zubawa wayar ido yayi yana tunanin wa zai kira ma domin a kira msa yaran yana son ganinsu kafin ya kwanta, bai son kiran goggon katsina don yasan halinta da rigima, gashi bai da numbar saude

Zama.yayi shiru yana tunanin mafita, kamar daga sama sai ga jahad  ta fito cikin sanɗa ashe batayi bacci ba komai ya fito da ita Oho,

“Ke zo nan,”

Daram !! Taji gabanta ya faɗi rass jin muryar mutumin nan tsaya wa tayi a hankali tana kallonsa,

Kafin ta tunkaresa zuciyarta na ɗar ɗar ta samu wuri ƙasa tazauna tare da lankwashe ƙafa ta gashe shi “Ina wuni,”

Bai amsa mata wannan ba sai ce mata yayi “where’s your sister”?

Jahad tace “Bacci take yi,”

“Je ki tasarmun ita, ina son ganinta,”

Mamaki ne ya kama jahad alamu sun nuna cewa marshal Omar fa yana iya banbance su tunda gashi ya nemi ta kira masa yar uwarta wato wadda ta faɗa masa ajikinsa,

Kallo guda yayiwa jahad ya gane cewa ba ita bace wadda ta faɗa masa a ƙirjinsa ba, kaji masu aiki da kwakwalwa,

farat ɗaya ya karanci wani abu a tsakaninsu daga ɗazu a asibiti zuwa yanzu,

tashi jahad tayi cikin sauri ta shiga ɗakin kamar yadda tabar hosana haka ta same ta kwance a tsakiyar gadon ta lumbutse abunta, baki wangame sai sharar bacci take.tana hura hanci kamar SA,

ɗan bubbugata Jahad tayi tare da cewa “Hosana !! Hosana ki tashi,”

Tsoki taja tare da juya mata baya “Leave me alone,”

a ƙule jahad tace “wai baxaki tashi ba,”

“Eh baxan tashi ba, in kinji haushi ki ɗauke ni mana,”

murmushi jahad tayi tare da cewa ” to shikenan bari naje na ce masa kince baki zuwa,”

jin abunda jahad tace yasa ta yin wani irin juyi ta ƴunƙura cike da zumuɗi tace “Wa,?

ƴar dariya Jahad tayi tare da cewa”mutuminki mai ƙarfi,” 💪

Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskar hosana, tasowa tayi daga saman gadon tana gaggyara rigar jikinta, hannu tasa ta ɗauki mayafinta dake anan saman gadon ta yafa,

Sannan suka fito atare ita da jahad ɗin, ƙarasawa su kayi gabansa riƙe da hannun junansu,

ɗagowa Omar yayi ya kallesu atare ya sauke idonsa kan Hosana wadda ke ta faman zabga mishi murmushi kamar gonar auduga,

“Have a seat,” ya umarce su

Zama su kayi saman 2 seater ɗin dake facing ɗinshi,

“What’s Ur names,’? Ya tambaya yana ci gaba da danna laptop ɗinsa,

Cike da zumuɗi hosana tace “Ni sunana Hosana ita kuma sunan ta Jahad,”

Jinjina kai Omar yayi kafin ya kuma cewa “Wacece mai ta6in hankali acikin ku,”? Ya tambaya tamkar bai gane ta ba,

Cikin sauri hosana tace “Ni ce,’

Murmushi kawai jahad ke yi shiriritar hosana nabata headache,

“Au kece kenan,? Ya tambaya yana ɗan kallonta,

Hosana tace “Eh nice bani da hankali but not always ynx ina cikin hankali na,

ɗan ta6e lips ɗinsa yayi kafin ya kuma cewa “Ina iyayen ku suke,”?

Shiru sukayi saboda sun rasa amsar da zasu bashi sai can hosana tace “Bamu da kowa, bamu son kowa ba, mu kawai muke rayuwarmu….’

tunkan taƙarasa ya dakatar da ita tayi shiru , ci gaba da danna laptop ɗin dake gabansa yayi kusan 15 mins bai sake cewa komai ba sai dai ya ɗan ɗago da idonsa ya kalle su ya mayar,

“A matsayin me zaku ɗauke “?

ya tambaya yana kallonsu har haɗa baki sukeyi wurin cewa “Yayanmu,’

Jinjina kansa yayi tare da cewa “Good, as frm now na zama yayanku, a shirye nake dana ɗauki dukkan wata ɗawainiya taku daga yanzu kun dawo ƙarƙashin kulawa ta, komai kke so just feel free ku sanar mun ko wani abu na damunku haka, sa’annan ku shirya tafiya gobe domin ba’a nan zaku zauna ba, zan mayar daku kaduna state gidan ƴaƴana, zaku samu kulawa sosae acan,

Har haɗa baki suke yi wurin yi masa godiya,

“No bana son wannan, bana son ana min gdy, zaku iya tafiya gobe ku tashi da shirin tafiya,

Miƙewa su kayi atare har sun ɗanyi nisa sai kuma suka juyo suna kallon shi atare suka haɗa baki wurin cewa “Sai Allah ya kaimu yaya Omar,”

Ba ƙaramin daɗin sunan yaji ba, jinjina musu kai kawai yayi sannan suka shige, shima tashi yayi ya wuce can cikin part ɗin big doctor domin dama acan suke kwana in sun zo,”

“Hosana ya kika ji muryar mutumin nan na ɗazu wanda goggon nan ta bamu mu gaisa dashi a matsayin mahaifin mu?

Jahad ce tayi wa hosana wannan tambayar ayayin da suke kwance su biyu saman gadon suna fuskantar junansu,

“A time ɗin naji shine tamkar mahaifina Jahad banso ya kashe mun waya ba kuma yace zai kira da anjima amma bai kira ba,”

Ajiyar zuciya jahad tasaki kafin tace “Nima haka Hosana, tun da naji voice ɗinshi naji zuciyata ta karye, shiyasanya na miƙa miki wayar sbd kukan da yazo mun,”

Hosana tace “dama ace shine mahaifinmu ko?

jahad tace “how that can be possible, we already ave our own father hosana, so stop expecting that pls,”

Shiru hosana tayi suka zuba ma juna ido na wani lokaci kafin Jahad tace “Allah Sarki Sehrish nayi kewarta sosae kullum tunani ya rayuwarta take, yaushe zamu sake sanyata a idonmu duk in na tuna hakan sai naji tsananin ƙunci da baƙin ciki araina, sehrish tasha wahala akan mu, tayi mana irin sadaukarwar da uwa ke yiwa ƴa’ƴanta, duk da kasancewar ko a wurin haihuwarmu Oumma ta faɗamin cewa sai da muka fara zuwa duniya da minti 30 sannan sehrish ta fito Allah sarki mai kyakkyawar zuciya insha Allah rayuwarki zatayi kyau Sehrish no matter what the situation is I wll neva stop praying 4 u,

ta daka da maganar a yayin da hawaye ke zubo mata daga eyes ɗinta izuwa saman pillow ɗin da take kwance,

Jikin hosana ne yayi mugun sanyi itama murya akarye tace “duk nice Sila jahad da ace ban jefa wayar nan ba, da yanzu muna nan muna waya da ita har ma yaya Omar yakaimu wurinta……..’

Kuka ne yaci ƙarfinta har ta kasa ƙarasa maganar da take yi,

“Oumma ta faɗa min cewa mu ba ƴan uku bane ta haifa, amma Abba ya kwashe sauran ya siyar dasu saboda shegen son kuɗinsa, narasa wani irin uba ne shi ya azabtar da rayuwar mahaifiyarmu da kuma rayuwarmu Allah ya isa bazamu ta6a yafe mishi ba har abada……….

cikin kuka take magana itama hosanar kukan take yi domin komai ya faru arayuwarsu in suka tuna sai zuciyarsu ta karaya, mummunan Labari mara daɗin Ji

Matsawa su kayi jikin juna suka rungume junansu suna ta faman shesshekar kuka Allah sarki kowa da irin tasa kaddarar, 😥

___________________________________________Hafsat Bature Moh’d

“Junaid menene haka wai”? Abbansu ne ke yi masa magana da bacci a idonsa, junaid dake saman chair ɗin dake gaban mirror sai faman zabga murmushi yake ya juyo ya kalli abban nasu dake kwance saman gadonsu yace “Abba u will not understand it, Abba kasan yadda so ke shiga ? Yayi tambayar yana kallon Abban nasu,

Cike da takaici yace “Junaid taso kazo ka kwanta kayi bacci tunkan  raina ya 6aci,’

“Hmmmm dad  kenan ka ta6a ganin inda Romeo yayi bacci ayayin da yake tunanin Juliet ɗinsa,”

shiru Abban yayi yana kallon ikon Allah lamarin junaid ya fara bashi tsoro, shi burin shi ya taso su kwanta amma  junaid ya ƙiya, gashi in baiyi bacci da wuri ba daker ake tashin shi bacci wurin sallar asuba,

Hannu Abban yasa ya daki katifar gadon da ƙarfi yace” Zaka taso ko bazaka taso ba”

Fari junaid yayi wa Abban nasu da ido, irin farin da mata keyi na ido yace” Daddy kaima kayi tunanin mommy mana, Nima nayi tunanin juliet ɗita,

*BossLady* 💋 in kinaso ki saka mun kawai kimun share na novel ɗina 🪩🪩🪩 sannan In zakuyimun comment pls ba thanks nakeso naji mutun yace mun ba, kawai kimun comment da abunda ya burgeki ko wanda ya baki haushi, komai dae 👏🤝*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🔥the father Soldiers🔥*

*mallakin*

*🌹Hafsat Bature Moh’d🌹*

*Episode 85-86-87*

◻ “To rasa kunya 6eran tanka zaka fara mun tsokanar taka ko,”?

◻ junaid yace “ae gaskiya na faɗa Abba, kallon ka kawai nake yi kai ta shan ƙamshi kamar baka son momynmu alhalin ko rannan kana bacci cikin mafarki naji kana cewa bana ji bana gani ni makaho ne agame da sonki Momyn junaid in bake ba sai rijiya in na rasa ki zan rungumi transformer akanki zan iya tunkararrrr

◻ bai idasa ba saboda jin saukar pillow din da abban nasu ya wurgo mashi, tabbas junaid ya bawa abban nasu dariya sosai

◻ “Kai ko? Yaushe akai hakan junaid Ƙaraya kke mun,” ya faɗi yana kara janyo Wani pillow ya wurga masa, hannu junaid yasanya ya ca6e pillow ɗin da Abban nasu ya wurgo masa a ƙinjinsa ya rungumesa yana faɗin “thank u Abbana dole na gode maka domin gashi da hannunka ka miƙo mun juliet ɗita,” ya faɗi hakan yana shafa filon dake ƙirjinsa yayin da yake kallon fuskarshi cikin madubin gabansa,

◻ Jin shiru Abban nasu bai sake cewa komai ba, yasanya junaid juyowa da kallonsa, samun sa yayi zaune tsakiyar gadon kansa na kallon ƙasa Allamar da damuwa a fuskarshi,

◻ tasowa junaid yayi jiki asanyayye ya haye saman gadon in da abban nasu yake yace “Abbana meya faru naga kashiga wani yanayi na damuwa,”?

◻ ɗagowa Abban yayi ya kallesa cikin sanyin murya yace “Junaid momynku ! kasan bana 6oye maka komai kaine abokin sirrina, babu wanda ke fahimtar zuciyata kamar kai,” ya dakata da maganar yana dan jinjina kai,

◻ “Dad pls tell me may be i ave the solution of it,”

◻ “Junaid mom ɗinku ta azabtar dani da soyayyarta, junaid ita tace tana so na tun kafin na fara sonta, amma kalli ynx ta kama hanya da aure na akanta ta koma australlia da zama, junaid ya zanyi?

◻ gyara zama junaid yayi suna fuskantar juna kamar zaiyi maganar arziki sai cewa “Abba dole sai ita? Ga zankaɗa zankaɗan mata nan ƴan goma shatakwas ƴan shila kyawawan gaske masu neman sugar daddy irinka wlh abba har rububinka zasu yi ka share ta kawai ka auri wata,” in serious matter junaid yake magana,

◻ Takaici ya hana abban magana a tunaninsa junaid zai bashi shawara akan yadda zasuyi mom ɗinsu ta dawo wurinsu da zama, amma sai ga akasin hakan, in banda sangartaccen irin junaid waye zaiso ayiwa uwarsa kishiya”

◻ “Abba u didnt say anything, shawarata batayi bane,?.

◻ “Eh junaid batayi ba, ashe baka da hankali in rasa wa zanyiwa kishiya sae momynku, bakasan halinta bane, duk da bamu tare da ita amma tayimun gargaɗin cewa muddin na ƙara aure sai ta dasa Bomb acikin gidan kowa ma ya rasa,”

◻ Fashewa da dariya junaid yayi, abban nasu yaci gaba da cewa “kuma in banda abunka wani magidanci ne mai ƴa’ƴa irinsu Sgr da Marshal Omar zai kara aure, auren ma ƴar shekara sha takwas ae wlh a ranar da ta sa ƙafarta acikin gidan nan aranar zasu balla ta gutsi gutsi

◻ Dariya kawai junaid yake kwasa wato ta ko’ina ba sauƙi, ita mommy tace zata dasa bomb su kuma su Babban yaya in an kawo ta gidan 6arar gyaɗa zasu yi mata,.

◻ “Enough junaid dariyar ta isa haka, zan baka lokaci daga yau zuwa gobe kayi tunanin shawarar da zaka bani akan yadda zamu shawo kan momynku ta dawo nan da zama,”

◻ “Kana nufin muyi mata wayau abba,”?

◻ ɗan zaro ido abban yayi tare da cewa “kai ! wannan matar mai ɗan banzan wayau kamar dila tab ae banta6a ganin dakakkiyar mata ba irin momynku ae wannan ba wanda ya isa ya yayi mata wayau,

◻ Dariya su kayi gaba ɗayansu sun jima suna fira kafin su kwanta tare Abban yayi musu addu’a yabi ya shafe su duka,

◻ _____________________________________________

◻ ƙaramar yarinya ce wadda bazata gaza shekara 12 ba ke tafama gudun saman titi sai faman kuka takeyi tana ambaton sunan “Oumma !! Oumma !!! ba tare da ta lura ba wata ƙatuwar motar ƙirar range rover tayi awon gaba da ita, nan take kanta ya fashe jini ya soma kwaranyo wa ta ko’ina

◻ A firgice sehrish ta farka daga mummunan mafarkin da take yi murya na rawa ta furta “Innalallahi wa’ina ilaihirraji’un,” ta faɗi tana cusa hannunta cikin sumar kanta idonta sunyi jawur hawaye na bulbulowa daga cikinsu, tabbas ta tsorata da mafarkin da tayi,

◻ Jiki a mace ta tashi ta wuce toilet saboda lokacin sallama yayi, sai da ta watsa ruwa sannan ta ɗaura alwala ta fito tana ta faman sauke ajiyar zuciya,

◻ Wardrobe ta buɗe ta dauko hijab ɗinta ta shimfiɗa sallaya ta kabbara sallah, bayan ta kammala ta zauna saman sallayar ta ɗaga hannayenta tana addu’o’i,

◻ Bayan ta kammala komawa tayi ta kwanta saman bed batare da ta cire hijab ɗin ba, haƙiƙa mafarkin ɗazu da tayi ya tuna mata wani abu mummuna daya ta6a faruwa makamancinsa,

◻ Ta jima hawaye na gangarowa daga eyes ɗinta kafin wani baccin ya sake ɗauke ta, ba ita ta farka ba har sae wurin ƙarfe tara, jiki na rawa ta shirya kamar kullum ta wuce kitchen,

◻ tsayawa tayi tana zazzare ido ganin har azmee ta kammala breakfast ɗin, wanda zata je ta jera a dining kawai take shiryawa,

◻ “Ina kwana aunty azmee,” tayi maganar tana ƴa kame kame, murmushi azmee tayi tare da cewa “Lafiya lou reesh, fatan kin tashi lpy,”

◻ “Aunty azmee ai mun afwa ban fito da wuri ba,”

◻ “Bakomai sehrish nifa da so samu ne ki koma kawai room ɗinki na kawo miki breakfast ɗinki ki ci acan ba sai kinyi wani aiki ba,”

◻ murmushi sehrish tayi tare da cewa “hakan bazaiyiyu ba auntyna, nima bana so nabar miki aiki dayawa ke kaɗai,

◻ Sehrish tayi maganar tare da ƙarasawa ciki domin ta taya azmee shirya abincin da zasu jera,

◻ Kamar daga sama ya faɗo kitchen ɗin daga shi sai shorts ajikinsa ba riga,

◻ gaba ɗayansu sai da gabansu ya faɗi ganinsa kwatsam haka ba sallama,

◻ daker azmee ta iya cewa “wata sabon gani haroon yaushe ka dawo ne ? Amma dae saukar dare kayi ko,”? Ta tambaya tana kallon shi

◻ idasa shiga yayi yana sakin murmushi yace “Eh jiya da daddare na iso, nayi mamaki da banganki ba auntyna gaskiya i really missed u, nayi kewar delicious ɗinnan naki,

◻ da ƴar dariya a fuska azmee tace” ae yanzu tunda ka dawo sai ka dasa daga inda ka tsaya, halan yanzu ma yunwace ta koro ka,?

◻ “Eh auntyna fruits nake so da coffee haka ko tea, pls a shirya mun sannan abawa wannan mai aikin yakawo mun,” yayi magana yana kallon sehrish wadda tunda ya shigo gabanta ke faɗuwa tarasa dalilin hakan,

◻ “Shikenan yanzu zan bashi ya kawo maka,”

◻ Murmushi ya saki tare da juyawa ya fuce daga kitchen ɗin,

◻ “Wanene wannan aunty azmee”? Sehrish ta tambaya domin neman ƙarin bayani akansa,

◻ Azmee tace “Wannan haroon kenan, ki saki jiki dashi bai da wata matsala a iya sani na, shima ɗayane daga cikin matasan gidan nan,”

◻ ɗan ta6e baki sehrish tayi tare da jinjina kai tace ” Allah yasa bai da wata matsala,” aranta kuma tace “sam ni baiyi mun kama da sauran ba, hasalima duk sun fishi kyau da natsuwa,”

◻ Ba da son ranta ba azmee ta shirya mata fruit a tray da cup na coffee takai masa,

◻ sai da tabi kwatancen da azmee tayi mata sannan ta gano room ɗinsa a nan down yake kusa dana kanal yusif,”

◻ a bude tasamu kopan sallama ta kwala masa daga ciki taji ance “Come in,”

◻ Shiga ciki tayi gabanta na faɗuwa rass rass, daga kwance yake saman haɗaɗɗen gadonsa ya taso zaune yana ƙare mata kallo,

◻ Cike da girmamawa sehrish tace “Gm sir,”

◻ bai amsa mata ba har ta ajiye masa fruits ɗin asaman table ɗin dake a front ɗinsa,

◻ Cikin sauri tajuya zata fita muryarsa ta katse ta”na sallame ka ne,”? Jiki a mace ta dawo ta tsaya daga tsaye tare da sunnar dakai tana kallon yatsun hanunta da take wasa dasu,

◻ Jin shiru yasa ta ɗan dago ta kallesa samun shi tayi yana bin jikinta da wani irin matsiyacin kallo tundaga kan yatsun ƙafarta har izuwa ƙirjinta,

◻ Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, ita burinta ya sallame ta tawuce taje wurin dining don ta taya aunty azmee ga kuma son sanya Babban yaya da take yi a idonta,

◻ Ganin ya tsayar da idonsa a gaban wandon jikinta yasanya tsigar jikinta tashi,

◻ da buɗar bakinsa sai cewa yayi “ina Ak47 ɗinka take, don ni banga alamarta ba anan,”?

◻ Cike da rashin farintar me yake nufi sehrish tace “bangane me kke nufi ba,”

◻ Wani shu’umin murnushi haroon ya saki tare da kai hannu cikin tray ɗin da takawo masa ya ɗauko damin Banana ya cire guda tare da sa hannu yana 6are bawon ayabar yace “Ina nufin wannan,” yayi nuni da ayabar dake hannunsa,.

◻ Jigum sehrish tayi sam tagaza fahimtar me haroon ke nufi, ganin bata da niyar bashi amsa yasa shi cewa “ina nufin abu na maza wannan,” yayi maganar yana ruƙo abunsa dake cikin shorts ɗin jikinsa,.

◻ Zaro ido sehrish tayi gabanta na faɗuwa zuciyarta tayi mugun tashi ganin abunda yake nuna mata sai lokacin ta gane me yake nufi ma,

◻ Shiru tayi idonta na kallon ƙasa gabanta na faɗuwa

◻ “A cire mun wando inaso nagani na shaida,”

◻ Ya faɗi ayayin da yake kai ayabar hannunsaa cikin bakinsa yana gatsa yana ci,

◻ Ji tayi gaba ɗaya komai ya tsaya mata tsak, tabbas ta tsorata da haroon sosae tun da take aiki a gidan bawanda ya ta6a lura da hakan farat ɗaya sai shi,

◻ “Baza a cire ba,!? ya tambaya a fusace

◻ Cikin en ena sehrish tace “kayi hkr dan Allah ! amma baxan iya yin abunda kke so ba……,” kafin ta idasa maganar tuni yasanya hanunshi yaja zariyar wandonta nan take wandon ya tafi suuuuuuuuuu zai sabule jiki na rawa ta cafko shi tayi saurin maidashi ta ɗaure abunta a yayin da zufa ke wanko mata,

◻ Dariya haroon yayi kafin ya tsagaita yace “Ke !!! nifa tun jiya dana ganki nasan cewa Ke maca ce ba namiji ba !!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!

◻ ɗagowa da ido sehrish tayi a firgice tana kallonsa tamkar a mafarki take jin kalaman haroon .

◻ Ƙara jaddada mata yayi da cewa “Ke maca ce ba namiji ba !! ki faɗamin uban miyasa kikayi shigar namiji kika zo gidannan? Da kwai wata manufa aranki ko !!?

◻ Muryar na rawa sehrish tace “innalallahi wa’inna ilaihirraji’una!! taya akai ka gane cewa Ni maca ce farat ɗaya!?

◻ Dariya haroon yayi tare da cewa “saboda ni Shu’umi ne ! Kuma cikakken ɗan duniya wanda idonsa ya buɗe a harkar barikanci ! ba wani abu da mutun zai 6oye mun batare dana gano sa ba,”

◻ “Shikenan nashiga ukuna !! dan Allah ka rufemun asiri karka ce zaka tona cewa ni maca ce pls!!

◻ Ajiye ayabar dake hannunsa yayi cikin tray ɗin sannan yace “Okey, i won’t expose ur secret but under one condition!!?.

◻ Ya faɗi yana kallonta a raunane sehrish tace “koma meye zanyi nidai karka tona mun asiri,” tuni idonta ya ciko tab da kwalla,

◻ Har wani lumshe ido haroon yake yi yana kallonta ” share hawayenki baby, bani da matsala muddin za’a biyamun buƙatata,’

◻ shiru sehrish tayi tana sauraron shi

◻ “Zamuyi magana anjima yanzu zaki iya tafiya naga kuna cikin aiki ne,”

◻ tunkan ya idasa mgnr sehrish ta fuce tana shasshekar kuka ,

◻ sai da ta dakata bayan ta fita ta tsaya ta share hawayenta tare da dai dai ta natsuwarta sannan ta sauka ƙasa, anan ta samu ma Aunty azmeen tana jera musu breakfast ɗin a dining,

◻ Karasawa tayi suka ji gaba da jerawa atare,

◻ Kallonta azmee tayi tare da cewa “Naga kin jima ! Lapiya dae ko?

◻ “Eh,” ta bata amsa atakaice, ita kaɗae tasan yadda take ji aranta, brain ɗinta ta gama shiga ruɗu tashiga tashin hankali mamakinta taya akai farat ɗaya haroon ya gane cewa ita maca ce !? how many days ta share a gidan amma ba wanda ya ta6a lura in aka cire junaid sai shi wanda jiya jiyan nan yazo da daddare, tabbas abun ya ɗaure mata kai, kuma tasa mishi alamar tambaya, (?) Anya ba Aljani bane

◻ gaba ɗaya ta tafi duniyar tunani har batasan cewa masu gidan duk sun fito ba, domin yin breakfast, yawancinsu duk jallabiya ce ajikinsu,

◻ Fawan da twins ne suka fara hallara suka zauna a kusa da juna, sai Irfan da jabeer bayansu sai khaleed da kanal yusif, duk suka gaishe da Azmee ta amsa musu kafin ta ci gaba da saving ɗinsu,

◻ Har time ɗin sehrish bata cikin hayyacinta tana tsaye kamar gunki tana tunane tunane iri iri aranta, sam azmee bata lura da halin da take ciki ba,

◻ A tare Abbansu ya fito da baby junaid hannunsu cikin na juna, fuskar nan tasa a washe tun da idonsa su kayi Arba da sehrish ɗinsa, tunkan ya ƙaraso ya lura da cewa ta tafi duniyar tunani,

◻ Ganin Abbansu yasa suka haɗa baki wurin gaishe shi “Barka da safiya Abba, kun tashi lafiya,”

◻ “Alhamdulillah My Sons ina fata kuma kuna lafiya,”

◻ da fara’ a fuskan kowannansu suka amsa mishi,

◻ Bayan sun zauna cike da tsokana junaid yace

◻ “Ni bazaku gaishe ni ba”? ya faɗi yana kallonsu,

◻ Tsoki fawan yaja tare da cewa “kabari sai ka fara ajiye gemu da ƴa’ƴa tukunna,

◻ “Wai junaid da gemu ba rana ba wata, don gsky ban ga alamar junaid zai yi gemu ba ko nan gaba,’

◻ Acewar Jahan,

◻ Abbansu yace “Talle zatai wa audu gori, ka fara duba fuskarka tukunna, muddin junaid bazaiyi gashin baki ba ko na gemu to kaima haka baza ta6a yi ba,”

◻ dariya su kayi gaba ɗayansu kanal yousuf yace “Wai ina Haroon ne ? Shi bazai fito bane?

◻ Abba yace “taya zai fito bayan abunda ku kayi masa jiya, sam banji daɗi ba, tun da ya dawo ya kamata ku tarbi ɗan uwanku hannu bibbiyu, in baku ja shi ajiki ba taya zai shiryu ? Yayi maganar cike da nuna 6acin rai akan abunda su kayi jiya,

◻ “Abba amma ba ka ga irin yadda yake mana magana ba har agabanka batare da jin komai ba? Acewar Irfan,

◻ Ajiye cokalin dake hannunsa yayi tare da cewa ” in da sabo ae ya isa ace kun saba da halinsa, addu’a kawai zaku bishi da ita Allah ya shirye shi,” yana kai karshen maganar ya ɗauki spoon ɗin yaci gaba da cin abincin dake gabansa,

◻ Jinjina kai su kayi kawai shikam fawan ta6e baki yayi tare da cewa “Ashe dagaske yazo, ae ni nayi tunanin duk mafarki ne zuwan nasa jiya,”

◻ Harararsa khaleed yayi “dole kace haka dama bakwa good time dashi ae,”

◻ tun da suka ambaci sunan HAROON hankalin sehrish ya dawo jikinta, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi ga zufa na wanko mata,

aza idonta tayi akan junaid wanda ke ta faman satar kallonta yana mata murmushi

◻ Murmushi itama tasakar mishi,

◻ So yake yayi mata magana amma ba hali sai dae daga inda yake ya rinƙa yi mata alama da bakinsa batare da sauti ya fita ba yace “Sehrish kin tashi lafiya,”

◻ tagane me yake cewa don haka itama tayi kamar yadda yayi tace “lafiya lou junaid ina fata kaima haka,”

◻ ɗaga mata kai yayi alamar eh, duk abunda junaid keyi akan idon Abbansu mamaki yake menene tsakanin junaid da mai aikin nan tukur, kodae sun ƙulla abota ne, ɗan murmushi ya saki domin yaji daɗin hakan, sbd duk wani abu da zai sanya shalelensa farin ciki son shi yake,

◻ “Ga babban yaya nan fa kowa ya shiga taitayinsa” fawan ne yayi maganar a yayin da yake cunkusa kebab abakinsa,

◻ Yadda fawan yayi maganar yasanya abbansu yin dariya, wai ga babban yayanan kowa yashiga taitayinsa, Kanal yusif yace “wato kaine annoucer duk in big bro zai fito sai kace kowa ya shiga taitayinsa, nawa ake biyanka salary ne ?

◻ Dariya sukayi gaba ɗayansu cikin nishaɗi in ka cire Twins dake ta faman jin bugun zuciya,

◻ A tare suka fito su biyu shi yana saukowa daga saman stairs yayin da shi kuma Haroon ke fitowa daga part ɗinsu dake a nan down,

◻ Jikinsa na sanye da tank top riga ce kamar singlet haka take fara, sai wando jeans, sumar nan tasha gyara,

◻ Shi kuma Haroon shirt ce da gajeran wando ajikinsa, ga uban gashin jiki da Allah yayi masa don ma Allah yasa kwantacce ne amma duk da haka ba kyan gani,

◻ Ganin Sgr yasa shi fara yi mashi kirari “Barka da Fitowa Babban yayanmu Namijin Zaki Uban dawa, mai mulkar ƙananun ƴan iska kai ɗaya tak kake tada runduna, gabanka Bullet bayanka Bomb ka ga Ingarmar Namiji ƙasaitacce takawarka lafiya Namijin duniya,’

◻ wannan kirarin na haroon yasa su Yousouf dariya, shi kuwa Sgr ko kallo haroon bai ishe shi ba,

◻ A tare suka ƙarasa ya zauna a empty chair ɗin dake kusa da Junaid, haroon ma yasamu wuri ya zauna,

◻ “Barka da safiya Abbana abun alfaharina,”

◻ Murmushi Abba yayi tare da cewa “Yawwa barka dae Haroon ya gajiyar tafiya ?

◻ “Abba ae ta washe tun jiya, yanzu garass nake jina,”

◻ Jinjina kai Abba yayi tare da cewa “Naji kace ka ƙaro wulaƙanci dagaske ne?

◻ Cikin sauri haroon ya saci kallon Babban yayan nasu yace “Bana cikin hayyacina ne, shiyasanya nayi maganar,”

◻ Murmushi su kayi gaba ɗayansu,bayan nan suka shiga gaishe da babban yayan nasu, bai amsa ba sai dai ya rinƙa yi musu alamar yaji da kansa, gyaran murya abbansu yayi hakan yasa Sgr ɗagowa ya kallesa cikin sanyin murya yace “Gm Dad,”

ta6e baki Abba yayi tare da cewa “sai ynx ka ganni? Ni fa narasa ganewa, nan gaba ina ga sai na rinƙa gaishe ka dakaina da alama,

“Insha Allah hakan bazata ta6a faruwa,” sgr yayi maganar ayayin da yaɗauke idonsa daga nakan Abban, Murmushi Abban yayi, yarasa dalilin dayasanya yake jinshi sosae aransa ko dan yana kama da Momynsa alexandra,

Sehrish kuwa

◻ Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta time ɗin da tayi arba da kyakkyawar fuskar Sgr duk da a firgice take ganin yadda haroon ke satar kallonta,

◻ tunkan azmee tayi yunkurin zuba mishi breakfast ɗinsa sehrish ta riga ta, plate ta ɗauka ta zuba mishi Chips ta shake mashi shi, sannan ta tura mishi agabansa ta kuma haɗa masa da hot coffee a acikin cup,

◻ “Mlm tukur ni baza’a zuba min bane”? Haroon ne yayi mata maganar yana binta da wani irin shu’umin kallo,

◻ Jiki na rawa sehrish ta ɗauki plate hannunta har kerma yake yi, tama rasa me zata zuba mishi,

◻ Muryarshi ce ta katse ta da cewa “Snacks nake so”,

Cikin sauri sauri ta zuba mishi snacks ɗin sannan ta haɗa masa da lemu a cup ta tura mishi,

◻ “Yawwa Good Job,” ya faɗi yana kai hannunsa cikin plate ɗin ya ɗauki donuts yakai bakinsa,’

◻ matsawa tayi daga bayan sgr ta tsaya saboda ta

◻ samu damar da zata rinƙa kallon sumar kanshi da kyau, tana shakar turaren shi,

◻ Ji take tamkar takai hannunta ta shafi sumar nan tashi, tun da ta tsaya abayan sgr bata motsa ba, duk wanda ya faɗi yana buƙatar wani abu sai dae azmee ta zuba mishi, ita kawai Babban yaya take saving abunda yake so,

◻ ɗagowa junaid yayi da idonsa ya ɗan kalle ta dayake tana tsaye daga bayansu, mamaki ne ya kamashi ganin yadda sehrish ke ta faman kallon Babban yayan nasu ko kyaftawa batayi, sam bai kawo wa ransa komai ba game da kallon nata kawai yasanwa ransa cewa wata’ƙil respecting ne yasanya sehrish tsayawa abayan, kallonsa kuma da take yi may be burgeta yayi ne, amma yaso ace shi sehrish take ma wannan kallon dayaji daɗi, mayar da kansa yayi jikinsa a sanyaye yaci gaba da shan farfesun naman dake gabansa cikin plate,

◻ Sun jima suna ɗawainiyar zuba musu breakfast ɗinsu kafin daga bisani kowa ya fuce, banda junaid da haroon suna acikin gidan, Sgr sun fita tare da abbansu headquater

_______________________________________________

A 6angaren su Hosana kuwa Tun da asuba da saude ta tashe su su kayi salla, suka koma tare da shimfiɗa wani sabon baccin kamar matattu haka suka dingi sharar bacci, dole kuyi bacci Allah, zaman cell ba daɗi anjima ana cikin tashin hankali, ga sauƙi yazo daga Lillahi,

Koma wa kitchen saude tayi ta shiga harhaɗa kayan breakfast da zatayi amfani dashi, shaf shaf ta fere dankali turawa bayan ta kammala ta yanka shi slide sannan ta shiga soya shi a saman frying fan,

Muryar goggo ce ta katse ta da cewa “umm agogo sarkin aiki nace ya akai banga yaran nan ba? Kodai mafarki nayi jiya?

Fuska ɗauke da dariya saude tace “Su wa kike nufi kenan”?

Watsa hannu tayi tare da cewa “Ƴa’ƴan Abusufyan mana? waɗannan tagwayen ?

ta tambaya tana neman jin ƙarin bayani,

Bin ta da kallo saude tayi jikinta na sanye da kayan baccin nan ƴan gado, sun yamutse sun tsufa riga da wando kwalar rigar ta sukurkuce, gasu Over size sun mata yawa kamar agwagwa haka ta koma acikinsu, taƙi ta janza wasu koda yaushe akayi mata magana akan ta sauya wasu kayan baccin sai tace tafi son waɗannan saboda ƴan ƙasar turƙiya ne irin wanda Zehra ke sanya abarmata abunta, wato ta cikin tarkon kauna, Abusufyan ne yayi mata tsarabar su tun last year dayazo nageria,

Gashi ta ƙife ɗan kwalin atamfa akanta abundae ba’ace wa komai,

“Saude kinyi shiru baki ce mun komai,”

daker saude ta iya cewa “Suna nan mana, ba mafarki kikayi ba goggo, suna can suna sharar bacci ɗakina,

Washe baki goggon katsina tayi tare da cewa “Yawwa madalla har hankali na ya kwanta,” ta faɗi tana shafa saitin zuciyarta, hakan ba ƙaramin sa saude dariya yyi ba,

goggo taci gaba da cewa “Saude so nake ki shirya musu karin kumallonsu mai daɗin gaske, a shaƙe musu tray, sannan a hada musu farfesun kaji dan Allah naga ƙasusuwan wuyansu kamar an jera ƙarafuna suna fama da yunwa, so nake kafin Abusufyan yadawo daga ƙasar turƙiya ko ina na jikinsu ya cicciko suyi kyau ƴan dumur-mur,’ tayi maganar tana kwatanta yadda take so su koma da hannunta,

Dariya kawai saude ke saki jin abunda goggon tace wato ƙashin wuyansu kamar an jera ƙarafuna, har dafe ciki take yi,

“Bansan iya shege wa kike wa dariya? Saude kin raina ni ko ina magana kina mun dariya, idan kika fusata ni, yau yau ɗinnan zakiyi fiffige ki koma rugarku acigaba da kiwon shanu,”

Tsuke fuska saude tayi jin abunda goggo tace rai abace tace”shikenan tun da haka kke so bari naje na shirya kayana yau dai na tafi na huta da gori,”    tayi maganar tare da kama hanya zata bar kitchen ɗin, .

Da sauri goggo ta ruƙo hannunta fuska dauke da murmushi cikin lallami tace “haba ƴar saude ta ke ko bakisan wasa ba, in kika tafi wa zai haɗawa ƴa’ƴan abusufyan ɗina breakfast ɗinsu,”

Murmushi saude tasaki ganin yadda goggo ke lallashinta yau, ita tasan saboda twins ɗincan tasamu wannan kulawar,

Koma cikin kitchen ɗin tayi tana cewa ” shikenan na fasa, amma goggo gsky ki barni nayi aikina mana, kinzo sai katse ni kike yi,”

Juyawa goggo tayi ta fi ce tana cewa “To natafi Allah baki haƙuri, ayi aiki lafiya,

Sai da goggon katsina ta wuce ɗakin saude ta tura kopan ɗakin ta hangi su Hosana da Jahad suna bacci sannan hankalinta ya kwanta hada jinjina kai da cewa “Masha Allah, ƴa’ƴan abusufyan ɗina kusha baccin ku ku more ƴan gatana abinci na nan yana jiran ku,” ta kammala sambatun nata sannan ta koma falo ta kunna kallo ta samu wuri ta zauna saman 3 seater tana cewa “Oh ko yaushe suke maimaicin shirin Omaru da zahra, aiko bari waɗancan yaran su tashi daga bacci in nuna musu ƙasar da mahaifinsu ke zaune, ni nasan ma ba’a rasa ganin shi acikin film ɗin wata’kil ko yazo giftawa aciki Camera man ya hasko dashi,”

Haka ta runka sambatu ita kadae abunta, sam bakinta bai zama hakannan batare da tace wani abu,

Bayan saude ta kammala breakfast ɗin, acikin katon tray ta jera warmers ɗin da sauran food stuffs ɗin ta shigo falon dasu,

Tunkan ta karaso goggo tace “Yawwa saude na maza ajiye shi anan gabana, sannan kije ki tasomun ƴa’ƴan Abusufyan ɗina, bayin Allah suna can suna fama da yunwa, bacci bai da imani baisan in kana jin yunwa ba ya ƙyale ka ba,”

Fashewa da dariya saude tayi aranta tana cewa wato da ace goggo ƴar comedy ce ba ƙaramin nishaɗantarwa zatayi ba,

Ajiye tray ɗin tayi asaman carpet ɗin geben ƙafar goggon kamar yadda tae commanding ɗinta, sannan ta wuce room.ɗin ta don ta tayar dasu Hosana da Jahad,

Duk wannan abun dake faruwa Goggo da saude basusan cewa Omar da Babban likita suna cikin gidan ba, saboda dama jiya bayan sunyi bacci suka dawo, Su hosana ne kawai suka sani saboda sunyi magana dashi,

duk in taga yaran wani farin ciki take ji aranta, sai faman sharar baccinsu suke, addu’arta Allah yasa Yaya Omar yabar musu twins ɗin su zauna agidan koba komai zata samu abokan fira,

Ƙarasawa tayi gaban gadon ta sanya hannunta ta ɗan bubbugi ƙafafunsu a hankali kamar wadda zata tasar da Jarirai,

Farkawa su kayi kowa na faman yin hamma, atare suka tashi zaune suna kallonta, lokacin da jahad ta shaida ta cikin sauri tace “ina kwana Aunty,” murmushi saude tasaki tare da cewa “Lpy lou my sisters fatan kun tashi cikin ƙoshin lpy,”

Jahad tace “Alhamdulillah aunty, munji daɗi sosai da kulawarnan,

“Aunty nidai Yunwa nake ji, da yunwa natashi kamar na cinye ƴan hanjin ciki na,” hosana ce tayi maganar, fashewa da dariya saude tayi hada jahad ɗin, murya a ƙule Jahad tace “waike baki da kawaici ne? Ko gaishe ta bakiyi ba sai magana akan yunwa yunwa,”

Murmushi saude tayi tare da cewa”kwantar da hankalin ki, special breakfast na nan nayi maku reserving ɗinshi a palor, kuma goggonku na nan tana jiran ku, sai tambaya take ina ƴa’ƴan abusufyan ɗinta,”

Jin hakan yasa su yin murmushi tare da kallon juna, kafin jahad tace”Aunty saude dama ina so na faɗamiki jiya yaya Omar yazo munyi magana dashi har yace mana, mu shirya yau zai wuce damu kaduna gidan yayan shi, gsky mun fi so muzauna anan,” ta ƙarasa magar tana kallon sauden,

dafe ƙirji saude tayi tare da cewa “Wai dagaske abunda ya faɗamaku kenan ! Hakan na nufin bazai bar mana ku nan ba, mu zauna atare ya Allah,’   sam bataji daɗin hakan ba, har cikin ranta, babban tashin hankalin ma da taji Jahad tace zai kaisu kd gidan Yaya ishaq,

Aranta tace “tabɗijan gidan wannan shu’wa arab ɗin jarababbiya, sam bana fata akai yaran nan can saboda bazata ƙyalesu ba, sai ta azabtar dasu waiyo Allah na, ya zanyi yaya omar yabar mana su anan su zauna, wlh aunty babba bata da mutunci ga Hafsat kuma yadda yarinyar nan ta tsani talaka aikom yaya omar zaiyi gangancin jefa rayuwarku cikin hadari,’

“Aunty baki ce komai ba? dan Allah kice masa yabarmu anan muzauna daku munfi jin daɗi,” jahad ce ta katse mata tunanin da take yi,

Jiki a mace saude tace “i dont know wat to do, yaya omar in yayi niyar yin abu no body can stops him, kuyi addu’a kawai Allah yasa goggo ta hana shi tafiya daku, amma muddin aka kaiku gidan yaya Ishaq kun shiga uku,”

Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda saude tace, murya na rawa jahad tace “aunty meyasa kika ce haka”?

Saude tace “hmmm abar zancen kawai, ku tashi ynx ga breakfast can na jiranku, ga goggo kuma nasan ganinku, ni ynx kitchen zan koma na shiryawa su yaya Omar nasu, pls kusan yadda zakuyi kar yaya Omar yabar gidan nan daku,” tana gama faɗan hakan ta fice izuwa kitchen zuciyarta nayi mata ba daɗi saboda tausayin yaran duk da batasa su wanene su ba amma tasan basu da gata, yaya Omar kuma dama shi mutun ne mai son taimakai wata’kil wani wuri yagansu a wahalce yake son taimakon rayuwarsu, da wannan tunanin Saude ta shige kitchen,

Kallon juna su kayi cikin tsananin tsoran inda za’a kaisu, atare suka tashi haryanzu doguwar rigar material ɗinnan ce ajikinsu, mayafi kawai suka ɗaura akansu sannan suka fito,

Goggo naganinsu ta soma washe baki tana cewa “masha Allah ƴa’ƴan abusufyan ɗina maza ku matso ku kwashi albarka wurin gaggonku, ga kuma abincinku na jiranku,”

Da fara’a suka karasa atare suka zauna suna gaishe ta “barka da safiya goggonmu fatan kun tashi lafiya,”

“Lafiya lou Alhamdulillah, har mafarkin ku saida nayi jira, tsorona kar na farka na taras da bakwanan agidan bansan ya zanyi ba, in banga ƴa’ƴan abusufyan ɗina ba,”

fuskarsu cike da tsantsar farin ciki ga kaunar goggon katsina data shiga ransu daga jiya izuwa yau,”

“Yawwa maza ga shinan kuci ku ƙoshi, in ma bai isa ba aƙaro maku,”

Cike da zumuɗi hosana ta ɗauki plate ta bude warmer ɗin dake ɗauke da soyayyan dankalin turawa ta shake plate ɗin dashi, sannan ta bude ƙaramar kular jar miya  ta lafta asama, ta motse ta shiga da turama cikinta,

Jahad kuwa Wainar kwai ta rinƙa haɗawa da slide bread tana cunkusawa abakinta, hannu goggo tasanya ta ɗauki flask ɗin dake ɗauke da ruwan liptop, ta tsaiyaya musu a cup kowa da nasa sannan tace “ga madara nan leda kowa ya zuba yadda zata ishe shi,”

Zame hannu hosana tayi daga irishi ɗin da take ji don haɗama, ta ɗauki milk ɗin ta zazzafa acikin ruwn tea ɗin mai uban yawa, tana jin jahad na cewa “banza kaɗan zaki zuba,”

Harara ta watsa mata tare da cewa “ina ruwanki ! ki ci abunda ke gabanki,” sai da taga ruwan tea ɗin yayi kauri yaji uwar madara sannan ta tsagaita ta sanya sugar,” ta hada tana sipping ɗinshi,

girgiza kai kawai jahad tayi  tare da haɗa nata tea ɗin tashiga kurbarshi tana ci da bread ɗin,”

Kamar kura haka ta lamushe abunda ta zuma sannan ta bude warmer ɗin dake dauke da chicken pper soup,  ganin lafiyayyiyar kaza yasa hosana gyara zama, anjima ba’a haɗuwa hannunta har kerma yake yi wurin daukar cinyar kazar tana turawa abakinta, gwanin daɗi kunnanta har rawa sukeyi,

Goggo sai murmushi takeyi tana kallonsu tsananin ƙaunar yaran take ji har cikin ranta,

Jahad kam kunyar abunda hosana keyi take ji kamar ta shaƙo ta take ji, sai faman licking hands ɗinta take kamar mayya,

Ƙasa ƙasa da murya tayi cike da jan faɗa tace “su hosana basaban ba, gida babu makwabta babu gidan miji ba tabbas, banza tasamu sai wankarta ake ba baka sai kunne,”

Fashewa da dariya su kayi gaba ɗayansu, ashe goggo na jinsu sai cewa tayi “Inji wa ya faɗi maki cewa gida babu, tab Ke ko kinsan katafaren gidan da abusufyan yake rayuwa acikinsa acan ƙasar Turƙiya? Kinsan irin daukar dayake ciki ? ae wannan bakomai bane, hmmm lokacin da naje turƙiya nakai masa ziyara, in zan ci abinci saiya sa an jera mun kayan maƙwalashe cike da dining tabur ae masu aiki gare shi sun iya girki sosai in sukayi abinci kamar abincin Aljanna don daɗi,”  ta ƙare maganar tana jaddada musu mgnrta

Tsagaitawa da cin abincin su kayi suna sauraronta baki asake, sukam wai wanene wannan abusufyan ɗin da Goggon katsina ke ta faman labarta musu zancen shi?

Kallon juna su kayi alamar neman karin bayani, goggo tace “ae ku kwantar da hankalinku, ni da kaina zansa abusufyan yazo nigeria ƙafarsa ƙafarku baxan ƙara bari ya tafi yabar yaransa cikin wahala ba,”

Sunnar dakansu su kayi ga dariya na cinsu, jin yadda goggo ke ƙaƙaba musu mutumin da basu san da Existing ɗinsa ba a duniya,

Atare Omar ya fito shi da babban likita sun shirya tsaf,

Goggon na ganinsu tace “Kai dirar yaushe ? ta ina kuka shigo cikin gidan,”

Murmushi Omar yasaki tare da cewa “goggona ke nan, ae jiya muka dawo tare da mutumina, mun same ku kuna bacci,”

Babban likita yace “Barkanka da safiya Mommyna fatan kun tashi lpy’ yayi maganar ayayin da yake zama saman 2 seater, shi kuma marshal Omar ya samu wuri gefen gaggo yazauna saboda ya samu damar gaisawa dasu Hosana dakyau,

Atare suka haɗa baki wurin cewa “Barka da safiya yaya Omar dafatan ka tashi lpy,” .

“Lafiya Alhamdulillah,” ya amsa musu yana mai ƙara azan idonshi akansu,” ba ƙaramin daɗi yaji ba ganinsu suna cin abinci,”

Duk kunya ta kama jahad har takasa idasa cin abincin, ita kuwa hosana bakin nan nata dama dama da jar miya, kuma a haka take kallonsa tana sakar mashi murmushi,

Bayan sun gaggaisa da goggo tace “daɗa sai naga ƴa’ƴan abusufyan jiya, ance wai kai ka kawo su naita mamaki nace yanzu har yaran nan sunyi girma haka amma ba’a ta6a nuna musu gidan goggonsu ba sunzo sun gaishe ni,’? Tayi tambayar rai a ɗan 6ace tana kallon Omar,

Jim omar yayi yana kallonta cikin mamaki yace “Suwa kenan”? Goggo ta nuna su hosana tare da cewa “gasu nan mana,”

ɗan murmushi yayi tare da kallon babban likita wanda shima murmushin ne a fuskarshi, sarai sunsan rigimarta, in ba haka ba yaushe Uncle Abusufyan ya ta6a aure balle har aje ga maganar aure,

Babban likita yace “Mommyna ayi mana afwan laifin mu ne, da bamu kawo su ba, kuma hada ƙarin makaranta sukeyi ne boarding school shiyasanya,”

ta6e baki goggo tayi tare da cewa “amma dae nikam ba’a kyautamun ba Allah, yara har sun isa aure amma ban ta6a sasu a idona ba! koda yake ba laifinku bane laifin Sufyanu ɗinne zan hadu dashi sai yayimun bayanin yadda ya hana ni jinina,

babban likita yace “Mommyna kenan, ina fata kina shan maganinki da na baki akai akai? Yayi maganar yana kallonta,

Yamutsa fuska tayi tare da cewa “kai ni na manta da wasu magunguna, suna nan cikin kwandon shara nake zuba su, ai naji sauƙi ynx,”

dariya su kayi gaba ɗayansu hada su hosana, Omar yace “goggo ina fa sauƙi a nan? U need a medicine 4 ur health,”

“Ae narasa meke damun mommyna, magani mai tsada kike zubawa cikin dustbin, gsky bana jin daɗi,”

Tsuke fuska goggo tayi tare da cewa “nifa bansan Iya shege, lafiyata ce ko lafiyarku ? ta tambaya tana harararsu

babban likita yace “lafiyarki ae tamuce mommyna, samun lafiyarki ae shine kwanciyar hankalin mu,”

Omar yace “maganarka gsky ne bro, goggonmu ataimaka adaina zuba magani a dustbin pls yakamata kina sha,”

Murmushi tasaki jin yadda suka damu da ita tace “shikenan, naji zan rinƙa sha daga ynx,”

Bayan sun ɗan tsagaita na wani lokaci Omar yace “goggo ina fata sun sanar dake cewa atare yau zan wuce dasu kaduna gidan yaya ishaq,”

Zumbur goggo tayi ta miƙe hankali atashe tace “bangane me kke nufi ba Omar? dama ba abusufyan bane yace akawo munsu nan ba su zauna wurina ? Bansan shegentaka fa ? Rabani zakuyi dasu ?

shiru Omar yayi just speechless ya ma rasa amsar da zai bata,

Babban likita ne yace “goggo go back to ur seat, lemme explain to u”

tsoki taja tare da cewa “Nifa bana gane ko wane yare a yanzu, in zakayimun magana da hausa kamun,” tayi maganar tare komawa ta zauna don sarai taji mai yace, tsohuwar ƴar boko ce ,”

ƴar dariya dr haris yayi kafin yace “mommyna kin gane, yaran nan school suke yi acan, kuma exam suke zana wa, shiyasan ya muke so mu maida su makaranta kar asamu matsala,”

juya masa ƙeya goggo tayi tare da cewa “In ansan exam sukeyi a makaranta maiyasa to aka kawo munsu ? Don aja mun rai ! I hate nonsense wlh,’

Yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya ta basu ba gaba ɗayansu, hatta saude dake tsaye a ƙopan kitchen tana sauraran firar tasu sai da ta dara, jikinta duk yayi sanyi Allah Allah take aranta Allah yasa kada goggo ta amince akai yaran nan kaduna gidan Aunty Babba,”

Atare da Omar suka shiga lallashinta don ta amince, sam taƙi yarda har sai da dr Haris babban likita yace “mommyna i promise u da sun samu hutun school zansa akawo mana su nan, su zauna wurinki ko ba haka ba Omar? Yayi maganar yana kallon omar,

Marshal Omar yace “Yeah hakane, dakaina zansa akawo su goggona,”

jiki asanyaye gaggo tace “shikenan na amince amma karku sa6a Alƙwari da zarar ansamu hutu akawominsu in ba haka ba zan sanarwa Abusufyan ɗina,”

Murmushi suka saki atare kafin Omar yace “insha Allah, ‘ sannan ya kalli su hosana ganin sun kammala cin abincin harsun wanke hannayansu yasa shi cewa “Kuje ku shirya,”

Atare suka miƙe sam basu so zasu rabu da gaggon su da aunty saude,  har sun fara tafiya jahad ta dawo zata ɗauki kayan abincin da suka ci Marshal Omar yace “just leave it, bari saude tazo ta kwashe,”

Juyawa tayi suka wuce bedroom ɗin saude suna shesshekar kuka, har cikin ransu basu son rabuwa da gaggonsu da aunty saude jiya izuwa yau sunji tsananin ƙaunar kasancewa dasu,”

Shaf shaf jahad ta fara yin wanka sannan hosana tayi, dukansu suna ɗaure da towel suna shafa mai ajikinsu,”

Hannu tasa da sauri jin hawaye a idonta, goge su tayi da sauri, sannan ta gyara natsuwarta, ta shirya musu breakfast ɗinsu ta shigo da shi palor,

Bin ta kallo dr haris yayi tare da cewa “Omar ga fa future wife ɗina danake baka labari,” .

ɗan kallonta Omar yayi tare da cewa “Oh dama ita ce kenan, ni bansan ta ba,”

Dr haris yace “taya xa’ae kasanta, daga rugar fulani nazo da ita, amatsayin wadda zan aura don na nunawa goggonku amma goggo ta maida mun mata ƴar aiki, ”

murmushi omar yayi batare da cewa komai ba, goggon kam tuni ta wuce ɗakinta saboda rashin jin daɗi za’a tafi da ƴa’ƴan abusufyan ɗinta

Saude jiki amace ta gaishe su, suka amsa sannan ta ajiye musu tray ɗin, sannan ta juya ta kwashe kayan abincin da su hosana suka kammala dashi ta zuba a tray ɗin ta wuce kitchen, bayan ta ajiye kayan ta koma ɗakinta wurin su hosana, ko ido batasan ta haɗa dasu saboda kukan da take ji, saboda turken wawa,

Wardrobe ta buɗe ta ɗauko musu kayan da zasu sanya, jahad tabata riga da skirt na atampa da mayafi, sannan ita kuma hosana doguwar riga ce ta larabawa, baka sai ƴar guntuwar hijab fara, ba ƙaramin kyau su kayi ba,

Bayan sun shirya tsaf, ta haɗasu duka ta rungume ajikinta, gaba ɗayansu sukaji kuka yazo.musu nan suka shiga yinsa, sun jima kafin su fito,

daker aka samu goggon katsina tafito tayi musu sallama tasanya musu albarka idonta cike tab da hawaye, bayan sun kammala yi musu bankwana suka fito waje,

a jere motocin marshal Omar suke a harabar gidan, dakanshi ya buɗe musu motar da zasu zauna ciki suka shiga atare, sannan shima ya shiga motar dake bayan tasu ya zauna,

a natse ake driving ɗinsu har motocin suka fice daga gidan, suka miƙi hanya har suka fi ce daga welcome To katsina,

(* New destiny has started), 😥*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*page 88-89*

wuce azmee tayi dakinta agajiye saboda ta samu ta huta, yayin da tabar sehrish tana faman kwashe dishes ɗin izuwa kitchen, bayan ta kammala wanke komai ta mayar dasu inda suke ta jera,

Sannan ta kama hanyar futowa daga kitchen ɗin, sam bata lura dashi ba sai dae taganshi agabanta kamar Aljani,

Tsorone ya kamata jikinta ya shiga kerma, dariya haroon yayi tare da cewa “Ina son ganinki baby da yaushe zamu haɗu ne,”? Ya tambaya yana kashe mata ido,

Murya na rawa sehrish tace ” Zuwa anjima yanzu agajiye nake, inaso na huta,”

Jinjina kai yayi tare da cewa “Okey, ki tabbatar kin kawomin kanki ɗakina, zan jira ki anjiman,”

“Insha Allah,” ta faɗi tare da bi ta gefenshi ta wuce hankali atashe, tuni hawaye sun soma zarya a kuncin ta ,

tana shiga bedroom ɗinta ta shiga yarfa hannu tana safa da marwa, damuwa iri iri daga nan sai wancan, babban tashin hankalinta a yanzu batasan da wata manufa haroon ke nemanta ba, runtse ido tayi tare da faɗin “Ya Allah ka tsare ni daga sharrin wannan bawan naka, Ya ilahi ni ynx bansan ya zanyi ba, gashi yace nakai mashi kaina ɗakinsa,” ta ƙare maganar tana mai jin bugun zuciya da fargabansa,

Daker ta tsagaita da zagaye zagayen da take yi a ɗakin nata,

gefen bed ɗinta ta hau ta ɗan kwanta eyes ɗinta na facing ceilling thinking abt many things, a haka har bacci 6arawo yayi awon gaba da ita, tasha bacci Ssae, dama ga weather ɗin is so comport,

Ba ita tafarka ba sai around ƙarfe 2 da mintuna har time ɗin sallah ya haura, tashi tayi tana dafe ƙirji domin kuwa har mafarkin haroon sai da tayi wai yace zai tona mata asiri wurin babban yayansu, da ta tabbatar da cewa mafarkine sai ta sauke ajiye zuciya tare da furta “Thank God it was a dream,”

Da hanzari ta shiga toilet tayi wanka ta ɗauro alwala, sannan ta fito ta nufi wardrobe tayi dressing kanta cikin riga da wando, sannan ta ɗauki hijab ta sanya, ta janyo sallaya ɗinta dake a saman murfin wardrobe ɗin dama nan take hanging ɗinta sometimes hada hijabin sallanta,

Shimfiɗawa tayi sannan ta kabbara sallah, a natse take yin ibadarta ta, bayan ta kammala  sallar ta zauna saman carpet ɗin ta lankwashe ƙafarta, ta ɗaga hannayenta  ta shiga jero addu’a, ta jima hada hawayenta domin tabbas tana ji aranta akwai wasu ƙalubalen da zata fuskanta acikin watan nan, tana roƙon Allah ya bata ikon cinye koma wata irin jarabawace sannan yabata damar tsallake duk wani ƙalubalen da zata fuskanta,” 😥

Bayan ta kammala ta miƙe tare da naɗe sallayar ta ninke ta sannan ta cire hijabin ta ninke ta itama ta tura su cikin wardrobe dukansu,

Hayaniya taji daga harabar gidan alamar ana buga ball daga wajen murmushi tasaki tabbas tasan su junaid ne ke wannan,  wasan,

Ji tayi tana marmarin itama ta kalli wasan ball ɗin nasu wataƙil ta rage ƙuncin da take ji a zuciyarta,

Da azama ta ƙarasa jikin window ɗinta ta naɗe curtains ɗin sannan ta zuge glass ɗin ta tsaya tana leƙensu,

Su 6 ne acikin ragar filin ball ɗin dake acikin gidan , shi da wasu daga cikin soldiers ɗin dake tsaren gidan,

time ɗin da ta aza idonta akan  junaid sai da taji zuciyar ta ta buga, sanye yake cikin kayan kallonsa riga da gajeran wando dai dai guiwarsa kana ganin waɗannan fararen ƙafafun nasa na rainon madara abun ba’ace wa komai,

launin kayan nasa red colour ne, wayyo ruwan kyau white in red dress na pyjamas, abayan rigar tashi an rubuta (ROMEO) No 10,

gaba ɗaya yazama tamkar tauraro acikin su sai faman tsalle tsalle yake ga kwantacciyar sumarnan tashi sai faman yarfo masa take saboda akwai Iska sosai a wurin,  hakan ba ƙaramin kyau ta ƙara mashi ba,

Natsuwa sehrish tayi tana kallonshi daga inda take tsananin tausayin shi take ji ganin sai faman cin shi suke, in yasha wahalar cafke ball ɗin su kwace, ji take kamar tayi fiffike taje ta shigar mishi duk da bata ta6a jaraba buga ball ba,

Ransa ne ya basa cewa Sehrish na kallonsa saboda abun a  jininsa yake muddin reeesh na a wurin sai yaji a heart ɗinsa sometimes heart beat ɗinsa ke canzawa,

daga inda yake ya shiga waiwayon ta ina zai ganta aikuwa cikin sa’a ya hange ta jikin window ta leƙensu, murmushi ya saki na jin daɗi aransa yana cewa ashe sehrish tana kallonsa kenan may be ma ba yau ta fara ganinsu suna buga ball ba aiko dole ya ƙara himma wurin wasan nasa yasamu yaci don ya burgeta sosai,

Bata lura da cewa junaid ya ganta ba saboda akwai tazara sosai a tsakaninsu,

Da gudu junaid ya shige cikin su yasamu nasarar kwace ball ɗin cikin sa’a sai gashi yaci, aiko gaba ɗayansu suka sanya sowa suna jinjina mashi, yau yayi abun arziƙi,

Ita kanta sehrish dake leƙensu kamar ta diro ta window ɗin taje inda suke ball ɗin don murnar junaid ɗinta yaci ball,.

Abun ya matuƙar basu mamaki ganin yadda junaid ke ta cinsu ball har 5 times, alhalin bai ta6a cim nasara akansu ba even one time, yau kam kamar ansa masa battery haka yake abun nasa, fuskar nan tashi ɗauke da murmushin nasara don yasan dole sehrish taji daɗi ssae,

A hankali motocin SGR suka shigo cikin gidan a jere dawowarsa kenan shi da wani abokinsu,

Bayan motocin sun dakata da sauri wani black american army mafi kusanci dashi mai suna Armstrong ya buɗe masu mota, A natse ya zuro ƙafarsa masu sanye cikin haɗaɗɗun takalma na maza, yana sanye da Army trouser, sai t shirt fara, kyau kam ba’a magana, sun bi shape ɗin jikin shi ta ko’ina ya bada ma’ana kuma ya bada Citta,

Sumar kannan kamar kullum tasha gyara ya daureta ta zubo mishi har gadon bayan shi,

Sai faman lumshe shining blue eyes ɗinshi yake alamar agajiye yake da bacci a idonsa,

Abokin nashi da suka zo tare shima yana sanye cikin army trouser da shirt, akwai kyau natsattse dashi ɗan giant ba fari bane yana da duhun fata amma ya haɗu,

Murmushi kawai sehrish ke saki ganin shi, wani irin sanyi taji azuciyarta, sam batayi tsammanin zasu dawo yanzu ba, murna a wurinta ba’a magana, har tafara tunanin ta hanzarta taje kitchen ta shirya mishi abunda zai sama cikin shi,”

Murmushi adams yayi tare da cewa “Kamar junaid nake gani fa, dama junaid na wasan ball ne har haka”? ya tambaya yana kallon Sgr ayayin da suke ɗan tattakawa suna tafiya atare,

“Shine mana,” ya bashi amsa a takaice,

Adams yace “kai gsky fa yaron nan yayi girma sosai zanyi wa daughter ɗina kamu,”

Sgr yace “So u get ready to pay for the price?

Dariya adams yayi tare da cewa “In dae za’a mallaka mana Junaid ae ko nawa ne farashinsa zamu biya,”

Jinjina kai sgr yayi batare da yace komai ba,

Junaid kam dake buga ball tun da ya hango babban yayan nasu yabar musu filin kwallon ya fito a guje kamar ƙaramin yaro bai tsaya ko’ina ba sai a bayan babban yayan nasu ya rungumeshi ƙam,

tsayawa da tafiya sgr yayi jin yadda junaid ya rumgumoshi ta baya,

“oh junaid ni baka ganni bane wato babban yayan naku kawai ka sani ko”? adams ya faɗi yana kallon shi,

Janye jikin shi yayi daga na Sgr, cikin jin kunya yace “a’a yaya adams ba haka bane,” ya faɗi tare da matsawa yayi hugging ɗinsa “ko kaifa yanzu naji bayani, nayi tunanin wariyar launin fata za’a nuna mini,” dariya su kayi atare jin abunda yace, shi kanshi sgr sai da ya ɗan so yayi murmushi,

“Yaya adams wane ni na isama, kafi ƙarfin wannan Allah, tukunna ma meyasa baka zuwa kawomun ziyara, ko dan Babban yaya baya ƙasar ne? Dama kullum ba’a ganin ka sai in Babban yayan mu yazo sannan kke zuwa ko? Ya tambaya yana kallon shi irin kallon na kama mai laifi ɗinnan,

Adams yace “junaid ba haka bane aiyuka ne sun min yawa, nima ae bana ƙasar ban jima da dawo daga Norway ba,”

Junaid yace “tom shikenan ina tsarabata “?

yayi maganar hada riqe ƙugunshi, hakan ba ƙaramin dariya ya ba Adams ba, hatta shi babban yayan nasu dake kallonsu abun ba ƙaramin nishaɗartar dashi yayi ba, especially yadda junaid ke magana, komai nasa burgeshi yake yi, junaid young bro ɗinshi ne kuma crush ɗinsa ne,

“In dae kana son tsaraba to kazo gidana ka amsa da anjima,”

ɗan zaro ido junaid yayi tare da cewa “tab !!” sannan Ya kalli babban yayan nasu tare da cewa “zaka barni inje ?”

Fashewa da dariya adams yayi yana kallon ikon Allah, wato sgr shine ke sarrafa shi,

Sgr yace   “Why not but not today zuwa tomorrow ko jibi zan sa akawo maka shi har gida,”

Ya ƙare maganar tare da cewa “am tired of standing, Lets go in,”

Atare suka jera junaid na tsakiyarsu ya ruƙo hannun kowannansu fuskar nan ɗauke da murmushi a haka suka shiga ciki,

Wuce wa upstairs su kayi, a part ɗinsa adams ya zauna saman 3 seater, shi kuma sgr ya wuce bedroom ɗinsa don ya rage kayan jikinsa,

“Bari nazo yaya adams,”  junaid ne ya faɗi tare da tashi ya fice cikin sauri don yaje ya shirya masu abunda zasu sha,

Fitowa yayi sanye da shorts a jikinsa sai ƴar singlet fara, hannunsa ɗauke da phone ɗinsa ya ƙaraso ya zauna On royal sofa ɗin da Adams ke zaune amma akwai tazara a tsakaninsu saboda mai zaman mutun ukuce,”

Kallonshi adam yayi tare da cewa “Surgeon ka fa tara abubuwa da dama, ina so na tattauna wani abu dakai mana,”

Sgr yace “ina sauraron ka,”

Adams ya gyara zama tare da cewa “yanzu fisabilillahi kalli kanka da kyau,”

Cikin mamaki sgr yabi jikinshi da kallo kamar yadda Adams yace sannan ya ɗago ya kallesa yace “what u mean”?

Murmushi adams yayi kafin yace “Haba sgr ka mallaki kowane abu da ake buƙata ajikin ɗa Namiji harma ka wuce, kalli fa in kyau ne da anzo gunka anzo ƙarshe kai kankat ne, in arziki ne da anzo gunka anzo ƙarshe, in Ilmi ne na addini dana zamani da anzo gun ka anzo ƙarshe, baiwa iri iri Allah ya baka to maiya rage maka a yanzu “?

Tun da Adams yaso ma bayanin Sgr ya ke bin shi da wani irin kallo saboda ya gano inda ya dosa,

Duk cikin friends ɗinshi babu mai mishi katsalandan irin adams, saboda kusan halinsu ɗaya, adams ne kawai ya ware daban acikinsu,

Ci gaba da magana adams yayi ” da ace ni na mallaki waɗannan abubuwan daka tara, wlh da yanzu na ajiye mata har 4 Cuf, yadda kke da farin jinin nan ta ko’ina binka ake don asamu shiga, Amma sam ka haramta ma kanka mace duk wannan Hadaɗɗiyar Surar taka sai dae suyi ta kallo suna haɗiye yawu’

Shiru sgr yayi yana kallon fuskan adams daya daddage yana kora masa bayani,

Jinjina kai adams yayi tare da cewa “ae dama nasani, u wll not say anything kabarni ina ta zuba kamar radion da bata da saiti,”

Lumshe ido sgr yayi tare da cewe “me kke so nace”?

ta6e baki adams yayi tare da cewa “abunda ka iya kenan, nasha wahalar koro maka bayani amma u ar asking me me nakeso kace,” yayi maganar hada ɗaure fuska yana kallonshi,

hakan yasa sgr saki wani ɗan kayataccen murmushi batare da lips ɗinshi sun motsa ba, dimples ɗinsa ne kawai suka bayyana alamar murmushi yyi,’

adams yace ” ka ga wannan murmushin naka, wanda ko namiji ya kalla sai gabansa ya faɗi, duk in kayi shi nasan da wata manufa,”

sai lokacin sgr yace “ka kammala bayanin naka”?

Adams yace “a’a ban idasa b

a, i just start it now,” yayi maganar yana tsuke fuska

“Ok Go ahead in ka kammala zan baka amsa a dunƙule,” sgr ya faɗi tare da ci gaba da dannar wayarsa kunnansa na akan Adams,”

Adams yace “haba jama’a kaga ƙato har ƙato amma ba zancen mace a ransa, zuciyarsa kaman ta dutse,’

Aransa kuma yace “kwarama da ba macen aransa, tab yadda yake da ƙirar nan da kyawun nan da ace ɗan iskane shi da Allah kaɗai yasan matan da zaiyi disvirgin ɗinsu, mata fa zasu sallawanta sosai yadda suke haukanshi suna kawo mashi kansu, tun ranar da matata tayi arba dashi shegiyar har yau kullum sai tace mun ina friend ɗin nan naka mai blue eyes shi bazai kawo mana ziyara ba,

Sam ya tafi tunani har sai da muryar sgr ta katse shi da cewa “are u gossiping me in your heart”?

Dariya adams yayi tare da cewa “ya akai kasan ina gulmarka bayan acikin zuciyata nake magana,”

“Naji araina” ya faɗi yana ɗan harararsa,

murmushi kawai adams yayi masa tare da cewa “nima bari na danni wayata, da na zauna naita zuba nikaɗae,’  yana maganar yana sa hannunsa cikin aljihunsa ya zaro wayarsa yaci gaba da danna shima, falon yazama shiru,

___________________________________

Time ɗin da junaid yaje ƙopan kitchen ɗin domin ya shirya musu abunda zasu sha, Sehrish yasamu aciki ta kammala jera Fancy cups masu ɗauke da Coffee aciki sai plate mai ɗauke da snacks acikin tray, sam bata lura da junaid ba, shima tun da yazo ya tsaya yana ta faman kallonta fuskarnan ɗauke da murmushi har kullum ƙara burge shi tayi,

Gyaran murya yayi, hakan yasanya Reesh ɗagowa a ɗan firgice a tunaninta Haroon ne ashe junaid ne, tana ganin sa ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin “junaid sannunka,”

“Yawwa sehrish na jima a tsaye ina kallon ki, wa kika shiryama wannan ne,’ yayi maganar tare da idasa shiga ciki yana nuna tray ɗin dake saman table,

Sehrish tace “babban yaya nagama hada abokinsa suka zo”

Junaid yace “yawwa Good girl kin hutasshe ni, dama nima zuwa nayi na shirya musu sai naganki,”

Murmushi tasaki tana faman sunnar dakai,

“Bari naje ciki inaso na yi wanka, sannan pls in kina da free time mu haɗu a garden mana”? ya tambaya yana kallonta,

Cike da zumuɗi sehrish tace “Shikenan wurin ƙarfe nawa”?

“After magrib prayer yyi maki”?

“Eh” ta amsa mashi kafin yasa kai ya fice daga kitchen ɗin Izuwa br ɗinsa, dama a ƙagare yake daya cire kayan ball ɗinsa,

bakomai yasa ta ɗoki ba fa ce tana tsananin son garden ɗin gidan ya haɗu sosai dama ita ma’abociyar son kayataccen wuri ce mai shufke shufken flowers da ruwa mai gudana,

A hannu ta ɗauki tray ɗin ta fuce dashi izuwa upstairs part ɗin babban yaya, sai da ta ɗan jinkirta da ta iso ƙopan shiga, tasama ma kanta Calmness, Sannan tayi sallama a natse “Assalamu Alaikum,”

Ta jira aka amsa mata sannan ta shiga A hankali take tafiya kamar wadda ta ɗauko  Kwai a hannunta,

Kowannansu wayace a hands ɗinshi, sai da taje gabansu tace “ina wunin ku,” sannan adams ya ɗago yana kallonta yace “yawwa fine boy, drinks ne aka kawo mana,” yayi maganar tare da sa hannu ya ɗauki one cup, matsawa tayi ta miƙawa sgr tana kallon shi sam bai ɗago ba har sai da tace “ga shi,” sannan yasa hannu ya ɗauka, ta ajiye musu tray ɗin a saman table,

kamar karta fuce haka take ji, wani irin sanyi take ji in tana kallonsa, yayi wani fresh abunsa cikin singlet da shorts,

“Ji mana,” adams ne yayi mata magana cikin sauri ta juya ta kallesa tare da cewa “Na’am”

“Amma kai sabon mai aiki ne ko? Ina aunty azmee ne?

ya tambaya yana neman jin ƙarin bayani

Sehrish tace “Eh sabone, aunty azmee tana nan,”

Jinjina kansa yayi kafin ya kuma cewa “Suna fa”?

Rishi tace”Tukur,”

Abun mamaki sai taga yana mata dariya gashi kuma yana bin ƙafafunta da kallo abun ya ɗan bata tsoro,

Tsagaitawa da dariyar yayi tare da cewa “Wow good wasan kwaikwayon fa yayi kyau sosai,” sam Bata gane me yake nufi ba duk ta dabarbace, duk wannan maganganun nasu a kunnan sgr,

“u can go mr Tukur,” adams ya umarce ta yana mai ci gaba da ɗan murmusawa,

Jiki asanyaye sehrish ta fuce tana mai mamakin wannan abokin na Sgr, komai yake nufi da dariyarsa Oho, ta faɗi tana yarfa hannayenta,

Kurbar coffee ɗin yayi yana cewa “Sgr ina kuka samu ɗan aiki ne?

“Don’t know,” ya bashi amsa,

Adams yace “Wannan fa maca ce tayi shigar maza wlh, amma fa ta iya shiririta,”

ɗan kallonsa sgr yayi tare da cewa “Wa kenan?

“House boy ɗin nan mana, daya kawo mana drinks yanzun nan,”

Sgr yace “Are u serious ?

Adams yace “Of course baka ta6a lura bane?

Sgr yace “taya zan lura, bayan ko face ɗin mai aikin bansani ba,’

Adams yace “No wonder that’s y baka lura da hakan ba, amma fa maca ce wannan hada sa gashin baki, ‘ ya ƙare maganar yana dariya don kam ba ƙaramin nishaɗi abun ya bashi ba, shigar yarinyar amatsayin namiji kamar ɗan chali chali,

“Amma ko meyasa tayi hakan”? Adams ya tambaya yana kallonshi,”

Ajiye cup ɗin dake hannunsa yayi tare da cewa “Zan bincika, koma  wa ya turo ta, zan sani ne, zasuyi bayani,” Acewar sgr,

“Gsky kam, u ave to investigate about it, kasan mugun mutun bakasan da wata siga zai shigo rayuwarka ba, especially yadda kke da suna haka ba’a rasa enemies masu son kawo muku hari ta bayan fage, ya kamata ka miƙe tsaye akan lamarin wannan mai aikin tukur, kasan da wata manufa yazo domin kuwa wlh maca ce ba namiji ba,”

Adams ne yake kora masa bayani yana ƙara jaddada masa akan mai aikin Don ayi saurin dakatar da shi daga abunda yake ƙoƙarin aikatawa, 😳

Sehrish fa batasan wainar da ake toyawa ba, Ashe watan cin uban wata yayi acikin gidan nan 😂

bedroom ɗinta ta koma tana safa da marwa, cike da tunanin dariyar da taga abokin sgr nayi mata aranta tace wata’ƙil shigar mazan da nayice ta bashi dariya Allah saki,

__________________________________

A hankali motocin marshal Omar suke shiga cikin katafaren gidan General Ishaq wanda ke a Unguwar rimi,

Hamshaƙin gidan wanda sojoji ke tsare dashi ta ko’ina, jahad sai faman bin gidan take da kallo ganin haɗuwarsa ta cikin glass ɗin motar, jinjina kanta tayi aranta tace “Aljannar duniya,”

Juyawa tayi ta kalli hosana wadda ta kwantar da kanta a kafaɗar Jahad ɗin sai faman bacci take shararawa murmushi jahad tasaki tare da cewa “Nasan hosana in taga wannan haɗaɗɗen gidan dole ta susuce,’

Mayar da idonta tayi kan glass ɗin tana ƙarewa gidan kallo aranta tace “Allah yasa kamar yadda gidan nan yake da kyau mutanen gidan ma zuciyarsu ta kasance mai kyau ce kamar haka, Ya Allah kasa kasancewar mu acikin gidan nan yasa ƙarshen wahalar mu kenan, Allah yasa  mutanen gidan suyi marhaban da zuwan mu kuma su tarbemu hannu bibbiyu kamar yadda goggon katsina tayi mana,” ta ƙare maganar tana mai jin wani sabon yanayi atattare da ita,

A jere motocin suka tsaya, sajan ɗin dake driving ɗinsu ya fito ya buɗe musu mota,

fitow jahad tayi tana faɗin “Hosana ki tashi mun iso fa,”

daker hosana ta buɗe idonta da sukayi luhu luhu tana bin jahad dake mata magana da ido, daker ta iya sa ƙafa ta futo daga motar tana murje idanunta don taƙara tabbatarwa kanta cewa dagaske ne hamshaƙin gidan da take ganinsu aciki ba mafarki ba, aiko ta shaida hakan,

Fitowa Marshal Omar yayi daga tashi motar, yana sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kalli su hosana yace ” ku biyo ni,”

Bin bayansa su kayi atare suka shiga hadaɗɗen jigunannan babban falon Aunty babba, wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa ta cikinsa abunka ga ƴan maiduguri dama an shaidasu akan hakan,

Wasu irin haɗaɗɗun Sofas ne masu Numfashi sets guda, launinsu Maroon colour, ga sofa tables ɗinsu launinsu,

Falon yasha ado da decorative object ga vase ajiye (tukunyar flower) ga wata irin faskekiyar plasma manne a wall ɗin kai komai fa yaji ya haɗu,

Babu kowa a falon sai sanyin A.c dake ratsa sassan jikin mutun,

“Have a seat,” umar ya umarce su sai faman bin ko’ina suke da kallo , a tare suka zauna saman 2 seater suka takure junansu tsoransu dawa zasu fara cin karo,

Shima yasamu wuri saman 3 seater ya zauna yana facing ɗinsu idon shi nakan hosana wadda ke ta faman lumshe ido saboda baccin da takeji ga yunwa,

Phone ɗinsa ya zaro daga trouser pocket ɗinshi ya danna numbar aunty Babba ya buga mata Calling,

Da ƙarfi wayarta ƙirar Iphone 13 pro max ta soma ringing tana ajiye saman bedside drawer gefen lamp,

Hajiyar na hakimce tana sharar bacci Saman haɗadɗen gadon nata, jikinta na sanye da riga da wando masu kyan gaske ga laushi kamar sleeping dress haka suke,

takurar da ringing ɗin yayi mata ne yasa ta buga uban tsoki a ƙule cikin bacci take cewa “Mtsww Wai wanene ne yake son takuramin ina tsaka da jin daɗin baccina,” ta ƙarasa maganar tana buga Uban tsoki rai a bace ta tashi zaune fuskarnan kamar Alkubus a kumbure take don ma Allah yasa akwai kyau da haske ssae da ba ƙaramin muni zatayi ba,

Hannu tasa ta fisgi wayar ta duba ta ga wanene, sunan (Marshal Omar ) ne ya bayyana akan screen ɗin wayar, ae tuni ta wartsake daga baccin da take yi, jiki na rawa ta ɗaga tare da karawa a kunnanta tace “salamun Alaikum,” bai amsa mata ba sai cewa yayi “Muna a palor muna jira,”

Cikin sauri tace “oh to gani nan zuwa,”

Ta ajiye wayar tare da miƙewa tasa hannu ta ɗauki mayafin kayan jikinta dake ajiye saman gadon, ɗaure shi tayi akanta maimakon tayafa shi a jikinta, sumar kannan nata tasha ƙananun kitson kalaba,

 

A hankali take tattaka steps ɗin benen tana saukowa down, tun da suka ji takon takalmi suka ɗago suna kallonta haƙiƙa sun tsorata da kyawun matar ga yanayinta na  marasa son mutane da hayaniya haka,

Jinjina kai su kayi tare da kallon juna lokaci guda suka mayar dakansu ƙasa,

A second to the last steps na stairs ɗin ta tsaya Curus ! tana kallon tagwayen matan da tagani zaune saman kujerunta sai taga abun kamar a mafarki gadai marshal omar zaune to su waɗannan isassun da suka zauna matan saman kujerunta su wanene ta tambayi kanta, har hannu take sawa tana murza idanunta don ta tabbatar cewa ba mafarki take yi ba,

Idasa saukowa tayi har time ɗin bata sauke idonta ba daga nasu Hosana wani irin kallo take binsu dashi kallon neman ƙarin bayani,

Muryar Omar ce ta katse ta da cewa “barka da fitowa aunty, fatan na same ku lafiya,”

Lokaci guda ta saki fuskarta ta ƙarasa ta zauna saman 1 seater tana cewa ” Yawwa Omar saukar yaushe? wlh bacci ne ya kwashe ni nasan dae ka ce mun zaka zo nan bfr ka wuce abuja,”

Omar yace “Eh hakane, ina yaya ishaq ne?

“Ae bayan kabar nan, shima yayi tafiya,”

Ta faɗi tana kallonsu hosana da jahad, wadanda suka sha jinin jikinsu tuntuni musamman da suka gaisheta sai tayi kamar batagansu ba,

Miƙewa tayi tare da cewa “bari na kawo muku abun ta6awa,”

tayi mgnr tare da wuce wa kitchen, tana shiga ta tsaya riƙe da qugu tana sake sake iri iri aranta.

“Su wanene waɗancan twins ɗin da Omar ya kawomin a gida? hankali na fa bazai kwantaba har Sai nasan su wanene da kuma matsayinsu a wurinsa,”

ta ƙarasa tunanin nata tare da shigewa ciki tana shirya musu  Abunsha dana ci,”

 

Su hosana da jahad kam sunfa shiga taitayinsu tundaga irin kallon da Aunty Babba tayi musu,

“Bacci kike ji ne har yanzu”?

Jahad ce tayiwa hosana tambayar, a kasalance hosana tace “sosai ma ga yunwa ina ji,”

“Wacece ke jin bacci”? Marshal Omar ya tambaya don yaji firar tasu,

Hosama tace “Ni ce, kuma hada yunwa nake ji ma,” tayi maganar tana ɗan turo baki,

Murmushi gefen fuska yasaki yana ɗan kallonta yanayin yadda tayi maganar ba ƙaramin tafiya tayi dashi ba,

” ok ki bari ki fara cin abincin sai ki yi wanka inyaso daga baya sai kiyi baccin ko? ya faɗi yana kallonta, hosana tace “to shikenan,”

Ya jinjina kansa

Shigowa Aunty Babba tayi hannunta ɗauke da tray tinkis tinkis take tafiya, har ta ƙaraso ta ajiye musu shi a saman table ɗin dake kusa da Marshal Omar,

“ki miƙa musu, ni bana buƙatar komai ynx,” ya faɗi yana kallon wayar dake hannunsa dayake dannawa,

daurewa kawai aunty babba takeyi, matsar musu da table ɗin tayi gabansu tace “gashi nan ƴan mata,”

Har haɗa baki sukeyi wurin cewa “mungode,”

Jiki na rawa hosana ta ɗauki coke mai sanyi ta buɗe tashiga ɗaɗɗakar lemun har ta kusa shanyewa duka,  jahad kuwa jiki asanyaye ta ɗauki robar swan tana sha,

Jinjina kai aunty Babba tayi ganin yadda yarinyar take ta faman kerma jikinta na rawa taga abunci aranta tace “To fa !

Bayan ta koma ta zauna ta kalli marshal Omar tare da cewa “har yanzu bakayimun bayanin waɗannan twins ɗin ba dana ganku atare,”?

gyara zama Omar yayi cikin natsuwa yasoma magana “Babu buƙatar dogon bayani, na kawosu ne zasu zauna nan atare daku na wani lokaci…….’

Yadda aunty babba ta zabura tsaye yasa shi dakatawa da bayanin yana kallonta yace “lafiya”?

A susuce ta koma tazauna tana cewa “babu komai ci gaba da bayani,”

Ajiyar zuciya yasaku tare da cewa ” zasu zauna anan, kamar yadda nace bana buƙatar kowa ya kashe ko sisin shi akansu, komai suke buƙata lissafi kawai za’a yimun na turo,’

Murmushin yaƙe aunty babba tayi tare da cewa “wannan ae mai sauƙi ne Omar, zasu samu kulawa sosai amma abunda nakeso nasani shin su wanene su?

“Ba buƙatar sani Aunty Laila, kawai a kulamun dasu yadda ya dace,” ya faɗi yana kallonta,

Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa “shikenan za’ayi kamar yadda kace insha Allah,”

Ya amsa da “Okey ynx zan wuce masallaci kafin nadawo pls abasu bedroom ɗin da zasu zauna su huta,”

Ya faɗi tare da miƙewa yasa kai ya fice,

Maida idonta tayi kansu Hosana da jahad fuskarnan a murtuke,

Hosana sai faman cin fried rice ɗin da ta shaƙe a plate takeyi tana korawa da lemu a cup, ko lura da kallon da Aunty babba keyi musu batayi ba,

Sai jahad ce ta ankara da hakan har tayi saurin ajiye spoon ɗin dake hannunta cikin plate gabanta na faɗuwa,

Muryarta ce ta katse su da cewa “kai !! Su wanene ku? ƴa’ƴan waye ku a dangin Su Omar?

dakatawa da cin abincin hosana tayi tana kallonta, murya na rawa jahad tace ” Mu bamusan kowa a dangin shi ba, taimakon mu yayi saboda ya tsince mu cikin wani hali,’

Fashewa da dariya aunty babba tayi har saida suka razana, hannu tashiga tafawa tare da cewa “Wlh kun shiga uku !! meyasa baku bashi shawarar yakai ku Orphanage Home ba? Sai gidana za’a kawomin tsintattu, to bari kuji in faɗa muku Omar yayi gangancin jefa rayuwarku cikin haɗari domin ni bani da Imani wlh,’ ta faɗi a faɗace tana kallonsu

Gabansu ne yayi mugun faɗuwa just now suka zo gidan amma gashi matar gidan ta bayyana musu halinta tabbas akwai matsala,

Shewa tayi “Ahayyye !!! wai ni za’a kawo wa tsintattu na riƙe ae wlh kun shiga uku kuna cikin masifa domin Laila bata da mutunci ,

Sam sun gaza ci gaba da cin abincin jikinsu sai kerma yake yi saboda tsoran wannan matar da ta kira kanta da Mara imani, mara mutunci,

jinkirtawa tayi tana kallonsu tana yatsina fuska kafin tace “me kuka tsaya kuna kallone? Kuci gaba da cin abincin ku domin daga inda Omar yasa ƙafa yabar gidan nan kuda ganin Abinci sai dae kuji ƙamshin sa Wlh,”  ta faɗi tare da miƙewa ta wuce room ɗinta dake asaman upstairs,

Tuni hawaye sun soma zubo ma jahad masu zafin gaske har taji ta tsani abincin da take ci ma, ita kuwa hosana jikinta yagama mutuwa jin abunda matar tace wato su da ganin abinci sai dae su ji ƙamshinsa, tuna wannan yasa ta fashe wa da kuka,

Haƙiƙa suna cikin tashin hankali kuwa,

Cikin kuka hosana tace “jahad Mun shiga uku,dama yaya Omar yabarmu gidan goggon mu da aunty saude,’ tayi maganar tana lashe hannunta ga hawaye sha6a sha6a,

Cikin shesshekar kuka jahad tace “hosana duk yadda za’ae karmu bari yaya Omar ya tafi yabarmu agidan nan, wlh kashe mu zatayi tace bata da Imani, kuma xata mana Horon yunwa innalallahi mun yi gudun gara mun faɗa gidan Zago 😭

Jikinsu duk ya gama mutuwa ga gajiyar tafiya gashi suna son suyi sallah su ɗan kishin giɗa amma ba halin hakan,

Murya na rawa jahad tace “Hosana ki ci gaba da cin abincin, kwara muci ko na yau ne tunda tace daga yaya Omar yabar gidan sai dae muji ƙamshinsa,

Hannu suka sa Hannu suka ci gaba da cin abincin ba ƙaƙƙautawa, hannu baka hannu ƙurya suna ci suna matsar kwalla,

Sai da suka kammala da komai sannan suka jinkirta suka zauna jiki a mace,

Jin ƙarar shigowar motocin Omar yasanya Aunty babban yin saurin fitowa daga room ɗinta ta sauko down jiki na rawa ta kallesu tare da cewa “Maza ku share hawayen nan dake a fuskarku, wlh muddin ku ga ja Omar ya gane cewa wani abu ya faru saina Murƙusaku a wurin nan, Dallah ni ku taso ku biyoni,

Jiki na kerma suka bi bayanta cikin hanzari takai su wani room ya hadu sosai ba hayani komai simple,

Shiga ciki su kayi rai a6ace tace “ku shiga toilet ku gyara jikin ku, ko da gigin wasa kar na kuskura naga wata ta leƙo d daga ɗakin nan balle ma ta fito!”

Tana gama faɗin hakan ta fuce tana sakin murmushi mugunta,

Falon ta koma ta tattare kayan abincin da sukayi Amfani dashi ta wuce dasu kitchen, tana a cikin kitchen ɗin tajiyo shigowarsa,

Fitowa tayi tana faman sakin murmushi taƙarasa tana faɗin “harka dawo kenan,”

Ya amsa mata da cewa “Eh ina yaran suke,” ya faɗi a yayin da yake zama saman seater,

itama ta zauna tana faɗin “Ae tunda kasa kai ka fuce, bayan sun kammala cin abinci na nuna musu ɗaki ynx haka sun kammala wanka sunyi sallah ynx bacci ma suke yi,”

lumshe ido Omar yayi alamar jin daɗi aransa sannan yace “naso ace na nasake gaisawa dasu don yanzu zan wuce abuja,”

cikin sauri tace “gsky kam, amma fa sunyi nisa a baccin nasu, bai kamata atashe su ba,

Omar yace “hakane kuma, Ni yanzu zan wuce,” ya faɗi tare da miƙewa

Aunty babba tace “Toh Omar agaishe mana da mutanen gidan Allah ya tsare hanya,”

Su hosana dake cikin ɗaki suna faman safa da marwa duk maganar da Omar yake yi da aunty babba a kunnansu yake yi, bayin Allah suna so su fito suce mashi karya tafi yabarsu a hannun wannan matar amma ba hali don ta tsawatar musu akan karsu Kuskura Su fito, hawaye kawai ke zuba daga idanuwansu domin suna leƙen Omar ta Window ɗin ɗakin, a yayin da yajuya baya ya soma tafiya shi kanshi hakanan ya dinga jin babu daɗi jikinshi atlease yaso ya sanyasu acikin idonshi kafin ya tafi tunda baisan ranar dawowarshi ba,

Har yakai bakin kopan fita daga falon ya juyo ya kalli aunty babba dake tsaye yace “AMANATA ki kulamin pls,”

Murmushi tasaki tare da cewa “Baka da matsala dani ƙanin Miji na, insha Allah zan kula maka dasu sosai,’

Jinjina kansa yayi tare da juyawa yasa kai ya fice,”

Su Hosana najin tashin Motocin shi, nan take suka fashe da wani irin matsananin kuka mai cin rai suka rungune junansu😭

 

 

*BossLady*

Keep sharing my Novel everwhere

,*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🔥the father of soldiers🔥*

Story by *Hafsat Bature*

~BossLady~

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ

ﺭﺍﻓﻴﺖ💓💞

*Episode 90-91* 💘

*🔔🔔🔔daga ynx ranakun da zaku samu posting na abban sojoji 3 days ne a week sbd ina busy ssae, amma zan ƙara muku yawan pages, days ɗin danayi Choosing sune Monday Tuesday da kuma wednesday daga zarar wadannan kwanakin sun zo daraina da lafiyata zaku samu posting da sassafe* 👏🙏

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~SEHRISH

Jin knocking yasa ta tayin saurin miƙewa daga zaunan da take saman gadonta , ƙarasawa tayi jikin ƙopan tare da cewa “Wanene”?

“Aunty azmee ce” ta bata amsa daga waje,

Ajiyar zuciya sehrish tasaki tare da buɗe mata ƙopan, shigowa azmee tayi jikinta na sanye da Doguwar riga sai babban mayafin da ta yafa,

“Ƙanwata me kke yi yanzu ne? halan kina nan zaune cikin damuwa ko? ko irin kiyi tunanin kin gaji da zaman kaɗaici ki kawomin Ziyara a bedroom ɗina bakya yi ko?

 

tayi maganar tana kallonta, cikin jin kunya sehrish tace “Aunty azmee bana so na taƙura maki ne, shiyasa bana zuwa ɗakin ki,”

Murmushi Azmee tasaki tare da cewa ” babu wani batun takura anan, kawai bakya son zuwane, nima kaina gajiye nake da zama wani sa’in duk atukure mutun kamar maye shikaɗai a ɗaki haba,”

azmee tayi maganar tare da shigewa cikin ɗakin sehrish tasamu wuri ta zauna gefen gadon, itama sehrish ɗin wuri tasamu gefen azmee tana fuskantarta,

Kallon juna su kayi lokaci guda suka sakarwa kansu murmushi, Azmee tace “Naji shiru baki tambaye ni game da sabuwar wayar da nace an baki ba”?

Sehrish tace “jira kawai nake, in kin bani in kar6a,”

Jinjina kai azmee tayi tare da cewa ” kiyi hkr sai zuwa gobe wayar zata iso,”

“Babu komai aunty azmee zanjira ni da za’a taimaka mawa abani kyauta, amma aunty azmee wanene ya siyamun wayar”?

ta tambaya tana kallonta,

“Ba abani iznin in faɗa ba, sai nan gaba zaki ji koma wanene,’

Murmushu sehrish tayi tare da cewa “Allah yakaimu time ɗin da rai da lpy

“Ameen” azmee ta amsa mata sun ɗan yi shiru na ɗan wani lokaci, kafin sehrish ta ce “Aunty azmee wai su Babban yaya Ina mahaifiyarsu take ko ta rasu ne? ta tambaya tana kallonta ,

“tana nan mana, tana zaune a sydney ƙasar Australlia,’

Jinjina kai sehrish tayi kafin ta kuma cewa “Amma mommynsu ita ba ƴar nigeria bace ko?

“Kin ga hotanta ne”? Azmee ta tambaya

Murmushi sehrish tayi tare da cewa “ban shaida ba, amma naga hoton wata mata Mai kyau baturiya mai sanye da kakin Soja a bedroom ɗin Babban yaya saman bedside drawer aka ajiye hoton,

Azmeee tace “dawa tayi miki kama acikin su”?

Sehrish tace “Babban yaya sunyi kama ssae hada blue eyes ɗinsu ma, sai kuma su twins da fawan, amma dae aunty Azmee dukansu ba uwarsu ɗaya ba ko? Ta ƙarasa maganar tata da tambaya,

Azmee tace “eh su Twins da fawan da Babban yayansu da junaid uwarsu ɗaya, suma su Kanal Yusif mahaifiyarsu daban’

Jinjina kai Sehrish tayi tare da cewa “Su mommynsu ƴar wata ƙasa ce aunty azmeee?

Cikin zolaya Azmee tace “Kice yau kin shirya son sanin wacece surikarki da alama naga kina ta jefamun tambayoyi akanta ko ba haka ba”?

Sunnar da kai sehrish tayi tana kallon yatsun hannunta cikin jin kunya

Azmee taci gaba da cewa “Sunan ta *Fatima ita ƴar America ce amma tana zaune a Australlia,”

ɗan shiru tayi na wani lokaci kafin ta sake cewa “Aunty azmee Yaushe zata zo nigeria ne? ita bazata zauna nan ba ko Abba ya sake ta ne?

Dariya azmee tayi tare da cewa “Wasa wasa sehrish kema fa kin iya surutu na lura wurine baki samu ba shiyasa kike noƙewa kamar bakyason magana,” tayi magana tana ɗan kallonta,

“In har aka tashi aurenki da babban yayansu ae dole tazo asha biki da ita,”

Jin wannan maganar ta aunty azmee yasa Sehrish ɗan zaro ido hada dafe ƙirji aranta tana cewa “tab ! Wannan matar ta cikin hoto anya xata barni in zama surukarta daga gani zatayi zafi Allah,

Murmushi kawai azmee takeyi tana kallon Sehrish dake faman sake sake aranta,

Ita kanta Azmeen  zolaya take mata amma tasan cewa sarai Alexandra bazata ta6a bari Sgr ya auri bakar fata ba,

Sun jima suna fira har wurin sallar la’asar sannan azmee tayi mata sallama ta fuce izuwa nata ɗakin,

 

tashi tayi itama ta shiga ta ɗauro alwala tayi sallah, bayan tagama ta shirya zuwa kitchen don tasan da wuri zasu fara preparing dinner,”

time ɗin da tafito babu kowa wayam falon kai tsaye kitchen ta wuce, azmee bata iso ba don haka tafara fiddo abubuwan da zasu yi amfani dashi, tafara aikin kafin ita tazo,  Aiki take amma hankalinta natashe tarasa dalilin dayasa take jin wani irin ɗaci aranta, wanda hakan alama ce dake nuna cewa waninsu nacikin matsala, Ita ko suna hosana

Har azmee ta shiga sam sehrish bata ankara ba har sai da tace “Good girl haka nakeso kina aiki da azama,” murmushi sehrish tasaki tare da kallonta tace “Aunty azmee ae dama baki fito ba ni namiki aikin duka,’

ɗan harararta Azmee tayi tare da cewa “Ki zubamin detergent aciki a matsayin gishiri?

Dariya sehrish tayi jin abunda tace “No aunty azmee bazan sake wannan mistakes ɗim ba,’

Azmee tace “Hmmmm zamu gani ae,’

Shiga ciki tayi suka kama aiki cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala, basu jera abincin a dining ba sun bari sai after magriba prayer,”

Cike da zumuɗi ta shiga tayo wanka, ta kimtsa kamar kullum, hada alwalarta jira kawai take Yi a kira sallar magrib taje su haɗu da junaid cos she’s so eager to see him,’

_________________________________

Fitowa daga wanka junaid yayi fuskarnan a washe zai haɗu da sehrish ɗinsa, daga shi sai shorts ajikinsa, shaf shaf ya shirya cikin shirt ash colour mai dogon hannu sai dogon wando black colour, wow baƙaramin kyau kayan su kayi mashi ba, ya feshe jikin shi da turaren spice bomb sannan ya zura shoes a ƙafansa launin wandonsa,

Hannun nan nasa na manne da wrist watch ta diamond mai kyan gaske,  ya fito fess abunshi,

Time ɗin da ya fito ana cikin kiran sallar ne, don haka yayi deciding zuwa yayi sallah in ya dawo direct zai wuce garden,

Sehrish

Bayan tayi sallah ta fito don ta wuce wurin haɗuwar tasu a hanyar fita kwatsam suka ci karo da Haroon wanda shigowarsa kenan,

Ji tayi gabanta ya faɗi rass, murmushi yasakar mata tare da cewa “ta kwana gidan sauƙi, dama don ke nashigo ciki don haka ki haɗomon Tea ki kawomin yanzu a bedroom ɗina i wll be waiting,” yana faɗin hakan ya wuce part ɗinsu,

Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, ga junaid tasan already now he is waiting for her and now ga haroon na jiran takai masa Tea, kuma batasan me yake son ce mata ba,

Addu’a kawai takeyi acikin zuciyarta, juyawa tayi ta shiga kitchen ɗin, ta haɗo masa tea ɗin sannan ta fito ɗauke da cup ɗin a ɗan plate ɗinsa,’

Tsayawa tayi a bakin door room ɗin nasa ta yi masa sallama muryarsa taji ta ciki yana cewa”Antayo kawai,”

Wato bama sai ya amsa sallamar ba, zuciyarta na ɗar ɗar ta shiga, yanayin da taganshi yasa hankalin ta tashi matuƙa, ya cire kayan jikin shi daga shi sai shorts, jikin nan nashi duk hairs fitowarsa kenan daga bathroom yana ganin ta ya tsaya yana bin ta da kallo, ”

Murya na rawa tace “Ga tea ɗin,” da buɗar bakinsa sai cewa yayi “Ni ba tea nake buƙata ba wadda takawomin tea ɗin nake buƙata,’

Baki asake sehrish ta tsaya tana kallonsa, bi yayi ta gefenta ya isa izuwa kopan ɗakin ya datse shi don kar wani ya faɗo ciki,”

Hankalin sehrish fa ba ƙaramin tashi yayi ba kallonsa kawai take yi jikinta na kerma,

Dawowa yayi inda take yasanya hannun shi ya kar6i kayan tea ɗin ya ajiye su asaman bedside table ɗinshi,

Sannan ya ɗago yana sakar mata wani irin shu’umin murmushi, matsawa yayi kusa da ita cikin tsananin tsoro sehrish ke ja da baya har sai da ya ƙure ta,

Cikin tsananin tashin hankali tace “Wai me kake so ne !? Why u closed the door pls ‘? tamkar zatayi kuka tayi maganar,

“So nake ki shayar dani that’s what i want,”

Zaro ido sehrish tayi tana girgiza mishi kai tace “bangane ba nashiga uku !!!,”

dariya haroon yayi kafin ya ɗaure fuska yace ” Feeding ɗina zakiyi kamar yarda uwa take shayar da jaririnta nono, shine abunda nakeso in kuma kika bijire mun, Hmmm kin shiga Uku !!! don kuwa zan tona miki asirine kowa yaji cewa ke maca ce, da zarar hakan ta faru kin mutu yarinya,

Fashewa da kuka sehrish tayi lokaci guda, tsawa haroon ya daka mata tare da cewa “Ke!! Yi mun shiru, ko da yake ci gaba da kukan idan wani yaji ya tambayi jin ba’asi zan sanar mishi cewa ke macace !!.

“Dan Allah ka yi hkr ka kyaleni in tafi, bazan iya aikata abunda kake so ba, meyasa zaka neme ni da fasikanci kaifa musulmi ne kaji tsoran Allah………..

Tsawar da haroon ya daka mata ne yasata yin shiru, matsawa yayi ya matse ta jikin bango har numfashinsu na harhaɗuwa,

Wata irin Zufa ce ke wanko mata mai zafin gaske ta jikinta, haroon ya matseta daker take numfashi,

Cikin shesshekar kuka tace “dan Allah  …….’ bata ƙarasa ba taji shigar harshen shi acikin bakinta duk yadda taso ta kwace kanta ta buge haroon ta gudu amma hakan ya faskara, yadda yasa dukan hannayensa yana shafa jikinta, ƙoƙarin cire mata rigar jikinta yake yi ma, har time ɗin bai janye tongue ɗinshi daga nata ba sai faman sucking lips ɗinta yake yi,

Kuka takeyi kamar ranta zai fita wani irin raɗaɗi mai ɗacin gaske take ji aranta, 😥

Ayayin da sehrish ke cikin wannan tashin hankalin, shi kuma junaid bawan Allah yana a garden yana jiran zuwanta, sai faman dube dube yake yi yana tunanin kota ina Sehrish ɗinsa xata 6ullo, amma shiru ga yunwa yana ji ssae, amma yayi alƙwarin bazai ta6a barin garden ɗin ba har sae sehrish tazo sun ga juna , 😥

Ringing ɗin wayarsa ne ya shigo da ƙarfin gaske hakan yasa yasaki sehrish da sauri domin dama there’s important call da yake jira wanda baxae bari yayi missing ɗinshi ba,

Cikin sauri ya isa inda wayar take saman gadonsa, hakan yaba sehrish damar watsa wa da gudun gaske daker tasamu ta buɗe kopan room ɗin nasa ta fuce tana shesshekar kuka,

In da Allah yasota babu kowa a main palor ɗin , da gudun gaske ta wuce bedroom ɗinta kai tsaye ta faɗa saman gadonta, jikinta na wani irin kerma ga uwar zufa, wani irin ƙyanƙyamin tadinga ji wanda hakan ya haifar mata da jin amai, nan take tafara yunƙurin aman jiki na rawa ta miƙe daga kan gadon ta faɗa toilet haka ta rinƙa kwarara aman kamar kamar me, bayan ta kammala tasanya ruwa sosai ta korasa, sannan ta shiga wanke mouth ɗinta, ji take haroon najasa ya goga mata,

Sai da tayi brush ta gurje bakinta har sae da le6enta ya fashe sannan tasamu salama azuciyarta,

Tasha kuka kamar kamar me, taji tsananin tsanar Haroon a zuciyarta, domin duk namijin dayayi attempting touching some part of her body, tsanar shi take yi gaba ɗaya,

Fitowa tayi jiki asanyaye ta haye saman gadon tayi covering jikinta da bargo tana ci gaba da kuka kamar ranta zai fita, sam ta manta da maganar gaɗuwarsu da Junaid,

Haroon ko baiso kiran nan yayi interrupting ɗinsa ba, yaso ace ya idasa nufinsa ga yarinyar, sae faman huci yakeyi gaba ɗaya ya kwaɗaituwa da son kasancewa da yarinyar domin bai ta6a jin macen da lokaci ɗaya ta tayar mishi da sha’awarsa gaba ɗayaba ba irin yarinyar, yaci alwashin sai ya ci gaba da yi mata barazanar zai tona mata asiri in ba tayi masa abunda yake so ba ,

___________________________________

Sam ya gaza manta fuskar twins ɗin, tsananin kewarsu ce ke ɗawainiya dashi, bakomai yake tunawa ba face yadda hosana ta faɗo mishi ajikinsa a asibitin nan, haƙiƙi wannan wani yanayi ne da bazai ta6a mantawa arayuwarshi ba,

Bakowa bane yake wannan tunanin ba fa ce marshal omar, wanda ke a hakimce cikin haɗaɗɗiyar motarsa mai lumfashi ana driving ɗinsa, ya jima da shigowa abuja batare da yasanar da kowa ba, ya fara biya wa guest house ɗinshi ya huta ssae sannan ya shirya shigowa cikin gidan nasu,

A dai dai time ɗin da motocin shi ke shiga cikin gidan, suka haɗe dana su Sgr, da su kanal yusif duka a lokaci ɗaya suka jero izuwa cikin gidan kowa ya dawon kenan,

Kusan tare duk su kayi parking ɗin motocin nasu, fitowa Omar yayi fuskarshi ɗauke da murmushi ganin mutuminsa ɗan uwansa rabin ransa wato Rafayet, wanda shima fitowarshi kenan daga motarsa,

gaba ɗaya su kanal yusif suka firfito shi da sauran dukansu fawan twins, Jabeer irfan da khaleed farin cikine ƙarara A fuskansu ganin Yayan nasu yadawo sunyi missing ɗinshi sosai,

Ƙarasawa su kayi inda yake suka shiga rungumarsa ɗaya bayan ɗaya,

Har haɗa baki suke yi wurin cewa “yaya Omar munyi kewarka ssai, bamusan yau zaka dawo ba kayi mana zuwan bazata,”

Murmushi Omar yasaki tare da cewa “I miss u 2 guys hope nasame ku lpy ?

Suka amsa mishi da ” muna lfy Alhamdulillah,”

“Good” ya faɗi tare da matsawa inda Sgr yake jikin mota jingine yana kallonsa, fushi yake dashi dama bada son ranshi ba ya tafi,

ganin ya tunkaro shi yasa shi dakatar dashi tare da cewa “kada ka kuskura kace zaka zomin nan, i don’t wanna see u bansan ka ba,”

Da dariya a fuskar Omar ya ƙarasa yana faɗin “haba lion in nazo ka kashe ni, amma nikam sai na rungumi sanyin idaniyata,”

Yana faɗin hakan yasanya hannu zaiyi hugging ɗinsa, sgr yajanye jikinsa tare da kai masa punch a ƙirjinsa, aikuwa omar ya daddage shima yakai mashi naushi,

Zuba ido su kanal yusif su kayi suna kallon ikon Allah dama haka suke da wasa da wasa su jibgi junansu abun ajininsu yake sun saba,

kamar afilin dambe suka shiga kaiwa juna naushi a ƙarshe kuwa sgr ya janyoshi tare da rungume shi ajikinshi ssae yace “Tiger I missed u so much, ka tafi kabarni,”

dariya Omar yayi tare da cewa “Wato shiyasanya ka nannaushe ni saboda ka huce haushinka ko?

“Eh mana,” ya bashi amsa ayayin da Omar ke janye jikinshi daga na sgr yace “mu shiga ciki Har ynx akwai gajiya atare da ni, ”

.. Jerewa sukayi suna tafiya yayin da su yusif ke bayansu,

“Abubuwa dayawa sun faru a tafiyar danayi, omar yafaɗi a lokacin da suke shugewa palor ɗin,

“Haba kamar me”? Sgr ya tambaya,

Omar yace “Idan na huta zuwa gobe zaka sha story bro,” .

Jinjina kai Sgr yayi tare da cewa “Okey,”

Sai da sgr yakai Omar har izuwa bedroom ɗinsa dake a upstairs sannan ya wuce nashi,

Rage kayan jikinsa yayi sannan ya shiga towel yayi wanka ya fito ɗaure da towel a waist ɗinshi, gaba ɗaya jinsa yake cikin nishaɗi musamman da yaji shi acikin gidansu cikin ƴan uwansa, duk da tunanin twins ɗin nan na ɗawainiya dashi, yaso ya kira yaji ya suke bayan daya barsu amma yyi deciding ya bari sai da safe ya kira Aunty babba ta basu wayar,

Dressing kan shi yyi cikin sleeping dress riga da wando masu kyan gaske milk colour zo kaga ruwan kyau, Omar fa na musamman ne, feshe jikinsa yayi da turare sannan yasa hannu ya ɗauki wayarsa da ya ajiye a gaban mirror,

Missed call ya gani na Abban su murmushi yasaki tare da cewa “Abbana kenan baka mantawa da ƴaƴanka duk yawanmu,”

Zama yayi a bedside sannan ya danna wa Abban nasu kira bugu ɗaya yyi picking thats means jiransa yake ya kira dama,

tunkan yayi sallama Abban yasoma magana “Omar ka shigo Abujan ne? nayi trying number ɗinka baka ɗaga ba why ‘

Cikin natsuwa yace “Abbana nasanya wayata silent so bansan ka kira ba am sorry for that, ynx haka ina a cikin gida,

“Alhamdulillah Omar naji daɗi sosai, da Allah ya mai domin kai lafiya, kayi wanka ka ci abinci ko”?

wannan magnar tasa Omar jin tsananin ƙaunar Abban tasu haka yake duk da girmansu in ya kirasu a phone sai ya tambayesu sun ci abinci sunyi wanka, Soyayyar mahaifi kenan

“Abbana nayi abinci ne kawai zan nema yanzu, yaushe zaka shigo gida ne “? Omar ya tambaya,

“Akwai abunda ya tsaida ni ne, amma insha Allah wurin ƙarfe 12 zan shigo,”

Omar yace “Allah ya shigo dakai lpy, my dad i will be waiting to ave ur hug,”

Sun jima suna waya, daga bisani omar ya ajiye wayar gefensa, da murmushi a face ɗinsa, kulawar da abbansu yake basu na matuƙar ƙara musu jinshi azuciyarsu

( Allah sarki yayin da wasu basu da Uban wasu kuma akwai uban amma baisan ya kula dasu koya damu dasu haka ba)

Azmee ce kaɗai ta fito ta wuce kitchen domin shirya abincin, ita kanta tayi late wurin zuwa shirya musu dinner ɗin, hakan yasa bata tsaya neman sehrish ba, ta wuce kitchen ta shiga kwaso warmers ɗin acikin tray tana kaiwa saman dining table,

tunkan ta idasa jerawa ma, suka fara fitowa kowa sae hamma yake a yunwace suke da alama,

“Aunty azmee 2 times kenan ina leƙowa daga bedroom ɗina in ga in an shirya dinner amma ina ganin ba komai,”  fawan ne yayi maganar yana shafa ciki,

Murmushi azmee tasaki tare da cewa “kuyi hkr dan Allah, wlh bacci ne ya ɗan kwashe ni,”

“Ai kina ma ƙoƙari Allah, girka wa ƙattai abinci, ɗawainiya da tazurai ae is not a simple ɗin wlh,’    ɗagowa su kayi gaba ɗaya dan suka wanene me maganar haroon ne wanda shima fitowarsa kenan,

kawar dakai kowa yyi cike da jin haushin maganarsa, zama kowannansu yayi, twins na kusa da junansu sai fawan, su irfan da jabeer da khaleed suna facing ɗinsu,

Sai haroon daya iso shima yasamu wuri ya zauna yana faɗin “don ƙaniyarku bazaku gaishe ni ba? wai me kka maidani ne sai kace ba yayanku ba, yayi maganar yana kallonsu,

banza su kayi dashi sai fawan ne yace “babu kyau ana cin abinci ana surutu,”

“To fitsararre iya magana dama ae ammi ta faɗi cewa bakujin magana kamar uwaku,”

Rai a6ace suke kallo shi abunda suka tsana kuma basa so, ganin sun ji haushi yasa shi ci gaba da cewa “Ƙarya nayi ne? Ammi tace ƴa’ƴan fatima fitsararru ne masu jan kunne ƙarya tayi ne”? ya tambaya yana kallonsu,

Rai a6ace khaleed yace “yaya Haroon ka daina menene haka wai? taya zaka rinƙa cin mutuncin ƴan uwanmu agaban mu?

Azmee dake a tsaye hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, gashi bata da ikon dakatar dasu ƙa’idar aikinta kenan,

“Ta ina suka zama ƴan uwanku? uba kawai kuka haɗa dasu bayan nan sai me? uwa kowa da tashi, kun manta irin tsanar da Uwarsu take yi maku ? Ita batasan baƙar fata,

A zafafe Jahan yace “Kai ya isa wlh, kabar ganinka yayanmu wlh zanci maka mutunci a wurin nan,

“Dama ae baku da mutunci gashi ka faɗa da bakin ka, ae gadonsa kayi wurin uwarku,”

Ruƙe hannun jahan Ayaan yayi ganin yana ƙoƙarin tashi yakaiwa haroon bugu, shima fawan ƴunƙurin yayi amma irfan ya dakatar dashi,

duk wannan maganganun na Haroon a kunnan Marshal Omar wanda ke tsaye saman stairs yana sauraronsu, babu wanda yasan cewa ya fito,

Haroon yaci gaba da cewa “Ae da kunbarsu Allah jiki magayi in ma yara……..’

Shaƙar da Marshal yayi masa ce ta bayansa yasan shi dakatawa, da karfin gaske ya ruƙo kwalar rigar haroon gaba ɗaya ya wuntsilo dashi ta bayan daga saman kujerar sai gashi ƙasa baje

Wani irin sanyi suka Ji aransu, dama ya hanasu sakat ya hanasu cin abincin ga yunwa suna ji,

Wani irin biji biji haroon ya rinƙa gani murya na rawa yace “Ya Allah ka nuna min annabi kamar yadda naga wannan bawan naka zahiran a idona,”

Damƙoso Omar yayi tare da ɗagosa ya buga shi ƙasa da karfi sai ga haroon asusuce kamar wanda aka zarewa lakar jikinsa sam ya fita hayyacinsa agigice yake faɗin ” Innalallahi wa’inna ilahirraji’un akashe ni kawai a huta,”

su fawan sai faman murmushi suka saki ita kanta azmee ba ƙaramin daɗi taji ba, ci gaba da saving ɗinsu tayi, ta zuzzubama kowannansu, cikin nishaɗi suke cin abincin nasu suna kallon yadda Yaya Omar ke jibgar haroon,’

“Bazaka min shiru ba don ubanka,” marshal ya faɗi a fusace

“Ae wlh sai dae akashe ni,” agalabaice haroon yayi maganar,

Miƙar dashi tsaye Marshal yayi a lokacin so yayi ko hannunsa ne ya gota masa wata’ƙil yashiga taitayinsa,  cikin sauri kanal yusif ya iso yana faɗin “Yaya Omar ae masa afwa ya jibgu ae,”

Tsoki Omar yaja tare da yin wurgi da haroon kamar kayan wanki haka ya gangara saman tiles ɗin yana faɗin ” sakayya na wurin ubangiji, sai mun haɗe a ƙiyama kowa zaiyi bayani,”

Fashewa da dariya su fawan su kayi, shikansa marshal abun yaso ya bashi dariya, wato shi bakinsa bai ta6a mutuwa sai dae akashe shi kamar yadda ya faɗa,

Wuce wa Omar yayi shida Kanal yusif suka zauna,

Cikin girmamawa ya gaishe da azmeee, murmushi tasaki tare da cewa “Omar saukar yaushe? ashe ka dawo,

“Ban jima da shigowa ba,” ya bata amsa,

“Ya gajiyar tafiya “? ta tambaya tana kallonsa,

“Alhamdulillah gajiya tabi jiki,” ya faɗi ayayin da yake kai kofin Tea ɗin da azmee ta zuba mishi abakinsa yana sha,

Muryar haroon suka ji yana cewa “ae dole gajiya tabi jiki yaya omar tun da anjibgi ƙato kamata agaban ƙanne na,’  Yyi mgnr tare da miƙewa  yana harararsu Su twins da fawan saboda jin haushinsu da yake yi, yana baƙin ciki dasu, kullum gani yake yi Abbansu yafi son su ƴa’ƴan Mommy alexandra akansu, kullum da wannan baƙin cikin yake kwana, kuma yaci alwashin in bai yi sanadiyar Mutuwarsu ba saiya naƙasa su !!!!!!!!!!!

Fasa cin abincin yayi ya wuce bedroom ɗinsa yana huci,

Natsuwa su kayi suna cin abinci kowannansu ya lura babu junaid amma sai ransu yabasu cewa yana a bedroom ɗinsa yana bacci, hakan yasa basu damu ba,

Bayan sun kammala kowa ya wuce ɗakinsa domin baccin da suke ji ssae,

Junaid fa har time ɗin yana a garden ƙanƙame da jikinsa saboda sanyi, ko’ Ina  Na jikinsa rawa yake yi  amma yagaza tashi yabar garden ɗin saboda sunyi da sehrish zata same shi acan, bawan Allah gashi athmatic, That’s the secrets Of true Love

Sehrish kuwa kamar matatta haka take kwance idonta luhu luhu, wasu siraran hawaye ne masu xafi ke saukar mata daga eyes ɗinta, haroon ya ƙuntata mata yasa ta tsani jikinta, ko’ina ƙyanƙyaminsa take ji,

Ga wani matsanancin ciwon kai da take fama dashi saboda kukan da tasha, ga zazza6i duk ita ɗaya, duk wannan bai hanata tunanin Sgr ba, shin yaci dinner ɗinsa kuwa, so take ta tashi taje ta dubasa amma tsoran karta haɗuwa da haroon ya hana ta fita,

Aunty azmee itace takai masa dinner ɗinsa a part ɗinsa, har ɗagowa yayi ya kalleta a tunaninsa mai aikin nan ne da akace masa maca ne, wanda yake so yakama hannu dumu dumu,

Wannan ke nan 👍

Keeep sharing everywhere, kar a manta da comment 🤨*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

~🔥Father Of soldiers🔥~

 

*Page 92-93*

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ

ﺭﺍﻓﻴﺖ💞😍

*✨Hafsat Bature*✨

~BossLady~

*Na canza days na sanya littafin abban sojoji, Ya koma Monday Tuesday da kuma friday*👏🤝

🔔🔔🔔

_This novel part 2 will be paid book,  a next post zan faɗi nawa ne payment ɗin_🤨

______

A 6angaren su Hosana kuwa, tun da suka samu su kayi wanka suka yi alwala da sallah, basu yi kuskuren fitowa daga ɗakin ba, tsoransu kar wannan matar ta shigo basu son dame zata fara musu ba,

Yinin ranar cikin fargaba su kayi shi, suna ta faman zagaye zagaye a ɗakin, sallah ce kawai ke tsaida su,

Daga bisa ni  bayan sallar Magrib ne bacci ya kwashe su a saman shimfiɗeɗen gadon dake ɗakin, sun sha gajiyar tafiya hakan yasa sukai ta sharar bacci kamar matattu,

A tsiyace Ta shigo da motarta acikin gidan, tayi parking ɗinta a wurin ajiye motocinsu, sannan ta harba murfin motar da ƙafarta don bala’i ta bude sannan ta fito,

Jikinta na sanye da less tsadadden gaske blue colour yasha adon duwatsu, less mai tsada amma an wulakanta shi wurin ɗinkinsa,

Riga da skirt ne rigar ta matse ta ƙam kamar zata tsage, wuyan rigar yayi girma sosai tamkar boob ɗinta zasu fito dukansu,

Skirt ɗin kuwa ya ɗameta over, ga wata uwar tsaga da akayi mashi tun daga guiwarta tsagar ta fara har ƙasan ƙafarta, kuma daga ciki batasa komai ba,

Hannunta na sanye da knuckle rings, mai kyan gaske Hancinta ma nasanye da Nose ring,

tana riƙe da  purse A hannunta launin kayanta,

fuskarnan na sanye da Makeup hada eye lashes tasa na kanti tayi fixing,

bakin nan nata yasha uban jan baki red colour  Sai faman taunar cingam take yi a tsiyace,

ɗaurin ɗan kwalin kanta kadae ya isa ya tabbatar maka da cewa bata da sauƙi,

Cike da yauƙi tashiga tafiya kwas kwas saboda ƙafarta na sanye da wasu matsiyatan high heels masu tsinin gaske,

Kai tsaye ta wuce bedroom ɗinta, hannu tasa ta turo kopan tana faɗin “am so tired ina buƙatar watsa ruwa naci abinci nayi wan……..’

Bata idasa ba saboda abunda tagani kamar a mafarki Yan mata saman gadonta suna bacci,

Hannunta tasa ta murza idonta donta tabbatarwa kanta abunda take gani aikuwa ta sheda hakan

A fili tace “Bura’ubancan !!! Yau akeyin ta wlh,”

Wurga purse ɗinta tayi saman gadon sannan ta fuce waje a tsiyace take kwalawa Aunty Babba kira

“Mom!! Mom!! Mommyyyyyy !!

A razane aunty babba ta fito daga bedroom ɗinta ta sauko down tana faɗin “Hafsat meya faru haka kke kwalamun kira haka ? yaushe kika shigo ne?

ta tambaya tana kallonta,

Uban tsoki taja tare da cewa “Mom duk ba wannan ba! Suwanene waɗancan yaran isassu dana gani kwance asaman bed ɗina? a faɗace tayi maganar tana riƙe qugu,

Aunty babba ta yatsina fuska tare da cewa “ni wlh sam nama manta dasu, wlh Omar ne ya kawomana tsintattun yara tagwaye wai su zauna tare damu acikin gidan nan na wani lokaci……….’

Zaro ido hafsat tayi tare da cewa “Jakar uban can kayyasa !!  sai kika amince ke kuma !?

Babu respect hafsat take magana da mahaifiyarta koda yake dama ance magaji mafiyi,

Yarfa hannu aunty babba tayi tare da cewa “To ya kike so nayi !? Omar fa ne ! Na isa na hana shi yin iko da gidan yayansa ?

Jinjina kai hafsat tayi tare da cewa “aiko zasu ci ubansu wlh ! they’ll regret being here in this home !

“Ae bama sai kin faɗa ba, ynx dai am sorry my daughter nakai miki su bedroom ɗinki, nayi hakan saboda Omar yana nan ne shiyasa nayi musu amma ynx wancan Tsohon Store ɗin zan maidasu da zama ciki,”

Jinjina kai hafsat tayi tare dace “Can yafi dacewa dasu yanzu dae muje a fitar mun dasu daga bedroom ɗina, ni saina ma Canza bedsheet Allah, sannan ina jin yunwa hope kin shiryamin abinci na Mommy,” tayi maganar tana shafa ciki

Aunty babba tace “dolena ne wannan, yanzu muje ɗakin mu fitar dasu, kisamu kiyi wanka na shirya miki abinci kici,

Atare da aunty babba suka shiga cikin ɗakin, su hosana bayin Allah na kwance suna sharar bacci

hafsat tace “Eyyehh !! Banza tasamu an haye mun gadona ana sharar bacci, wlh nasan maganinsu,’

Tana faɗin hakan ta juya ta fita daga ɗakin izuwa parlor in da freezer take,

Murmushi aunty babba tayi don tasan me hafsat zata ɗauko,

Aikuwa sai gata hannunta ɗauke da Cool water har yasoma ice acikinsa cikin ƙatuwar bottle,

Dariya aunty babba ta fashe da ita, tana faɗin “Good my daughter hakan yayimun wlh,”

Cire murfin robar tayi batare da tausayi ba ta zazzaga musu ruwan mai matuƙar sanyi a jikinsu,

A firce jahad da hosana suka farka jin dirar ruwa mai sanyi ajikinsu, jahad na faɗin “innalallahi wa’inna ilahirrajin’un, muryarta tamkar zatayi kuka ita kuwa hosana fashe wa tayi da matsanancin kuka saboda bata son sanyi balle ita mai asthma, jikinta har wani irin kerma yake yi,

Ido luhu luhu yayi jawur daker suke kallon Aunty Babba da hafsat dake tsaye suna kallonsu,.

Hafsat tayi mamakin kamannin su iri ɗaya sak aranta tace “Ashe har ynx ana yin twins masu kama da juna haka, ba laifi suna da kyau,”

A fili kuma ta daka musu tsawa har sai da suka firgita Hosana ta ƙanƙame jahad don batason sauti mai ƙarfi,

“GET UP !!!! Maza a tasarmun daga gado na, ku sauko Mun haka nan ankawo mana mutane tsintattu cikin gida,’   tayi maganar tana yi musu alama da hannu na su sauko,

Jiki na rawa suka miƙe tare da saukowa daga saman gadon jikinsu na rawar ɗari saboda sanyin A.c ne ya haɗu da sanyin ruwan da Hafsat ta watsa musu,

Tsayawa su kayi a tsananin tsorace suna faman shessheƙar kuka,

Tsoki aunty babba tayi tare da cewa “ku biyo ni,”

Bin bayanta su kayi ta fuce dasu daga ɗakin, sunyi mamakin ganin suna ta faman tafiya acikin wata Corner na gidan,

Adai dai ƙopan wani Room ta tsayar dasu, hannu tasa ta riƙe handle ɗin kopar tare da buɗewa tace “To ƴan matan mama ga fa makwancin ku daga yau,’

Hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba domin kuwa, wani tsohon store ne na ajiyar kayan abinci, tarkace ne kamar hauka, jarkoki da galon aciki na manja dana mai da akai amfani dasu awargaje, Sun tsufa sunyi ƙura, ga buhun hunan Shinkafa dana gero dana fulawa duk gasunan, ƙasa kuwa sunkin doyoyoyi ne ajere da dankalin hausa dana turawa, da gunduwa gunduwar Albasa, babban tashin hankalin ɗakin ko fanka babu duk ƙura ga yanar girgizo har jikin bango, ga ƙwari kuma a ƙasan suna shawagi, Ga manyan drawers waɗan da ke a datse jikin bango da alama na ajiyar tarkace ne,’

“Uban me kuka tsaya kuna kallo kushi ga mana! Ko saina shigar daku ne !?

Basu yi mata musu ba jahad ta ruƙe hannun hosana suka shiga cikin store ɗin sannan aunty babba ta ƙara da cewa “daga yanzu nan ne wurin kwanan ku   Kuma wurin zamanku, saboda baku da gurbi acikin gidan nan,”

ta faɗi hakan tare da turo kopan kuma tasanya Key ɗin dake ajiki tayi Locking ɗinta, ba damar fita kenan, ko taya mutun zai iya kwakkwaran Numfashi a ɗakin nan !? 😰

____________________________________________*ABBAN SOJOJI*

*Story by Hafsat Bature*

*BossLady*💞💞💞

Around 12 Abban su ya dawo cikin gidan time ɗin duk sunyi bacci, bai wuce ɗakinsa ba sai da ya fara zuwa part ɗin Marshal Omar domin yaga ɗansa kafin ya wuce nasa ɗakin, lokacin daya tura kopan part ɗinsa shima nashi sak irin na Sgr ne, akwai hamshaƙin ƙayataccen palor aciki sai bedroom aciki,

Wuce wa bedroom ɗinsa yayi ya shiga Ciki samun shi yayi saman shimfiɗeɗen gadonsa ya lullu6e da lallausan blanket ɗinsa,

Murmushi Abbansu yayi tare da cewa “Yawwa haka nakeso my son asha bacci lafiya,” juyawa yayi zai fita Muryar Omar ta ratsa shi da cewa “Abbana idona biyu fa, i ave told u that i wll be waiting to ave ur hug, that’s why i stayed awake,’

Omar ne yayi maganar a yayin da yasanya hannunsa yana janye Bargonsa ya miƙe zaune da murmushi a face ɗinsa,”

Ƙarasawa Abban yayi Omar ya tashi tsaye suka rungume juna ssae,

“Nayi missing ɗin Tiger ɗina ssae, ” ya faɗi yana bubbuga bayansa, Omar yace “Abbana nima haka, ina fata nasame ka lpy,”

“Lpy lou Alhamdulillah Omar,” ya yi maganar tare da janye jikinsa daga na Omar yana cewa “Ka koma ka kwanta Omar nima zan wuce ɗaki ynx,”

“Shikenan Abba, Mu tashi lpy,”

Sallama su kayi abban ya fice,  kwanciya Omar yayi amma yana jin there’s something missing a heart ɗinsa tabbas akwai wanda baisa a idonsa ba, tun da ya dawo cikin gidan ba kowa bane face “Junaid,” ya bari ne kawai sae gobe ya neme shi su gaisa cos yyi missing ɗinshi,”

Sehrish fa sam ta gaza runtse eyes ɗinta tayi bacci, duk ta takure kanta ta tsani jikin ta, ta6awar da haroon yayi mata ji take tamkar raping ɗinta yayi, tana saman gadon daga kwance ta tashi zaune tsakiyar gadon, ta matse kanta baiwar Allah,

___________________________/___/

Time ɗin da Abban su ya shiga ɗakinsa, yayi tunanin zai ga junaid a kwance yana sharar bacci, amma sai yaga wayam daga blanket sai pillow asaman gadon, abun ya ɗaure masa kansa, aransa ya ce “meyasa Junaid bai zo ya kwanta bane wai, ko dae yana a bedroom ɗinsa bara dae na canza kaya naje na duba sa,”

Shaf shaf ya cire kakin dake jikinsa, ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ya zura jallabiya fara, sannan ya fice daga room ɗinsa izuwa na junaid dake a upstairs,

Yana isa ya tura kopan ɗakinsa abun mamaki babu junaid babu alamarsa, har toilet ɗinsa ya duba babu Shi saboda tsabar ruɗu har cikin Laundry basket ɗinsa ya duba da cikin Wardrobe ɗinsa don yaga ko ya 6uya aciki 😂

Amma babu shi, aikuwa hankali atashe abban su ya fito ya wuce part ɗin sgr, ya shiga har ɗakinsa ya bubbuga masa jikin ƙoparsa,

Sgr dake kwance natse saman gadonsa yaji knocing ɗin da abban ke masa,

Janye bargon jikinsa yayi, sannan ya tashi zaune yana kallon Abban nasu daker yake buɗe Eyes ɗinsa saboda bacci,

A sanyaye yace “Abba me ya faru ne? Kai ne da kanka?

“Ina fa lafiya babu junaid fa acikin gidan nan”! Jin hakan yasa sgr yin saurin haurowa ya sauko daga saman gadon, jikinsa na sanye da night dress riga ce dai dai guiwarsa ta tsaya babu dogon wando sai dai shorts acan ciki,

Cikin ruɗu yace “Abba kamarya? How za’ace junaid baya cikin gidan nan!!!? ya tmby yana kallon abban nasu dake a tsaye,

“Nima bansani ba, dawowa ta kenan, gsky akwai matsala,’

Fito wa su kayi atare shida abban suka bi sauran bedrooms ɗin sauran saboda su duba su gani ko ya kwana a ɗakin sauran saboda yana yin haka in rigimarshi ta tashi sai ya za6i inda yake so ya kwana ko ɗakin waye kuma dole abarsa ya kwanta,

Duk wanda akayi wa knocing ya buɗe daga yaji cewa Junaid ake nema sai kaga ya wartsake daga baccin da yake yi, hankalin kowa ya tashi matuƙa,

Gaba ɗayansu duk suka hallara a babban falon in ka cire Marshal saboda basu tashe shi ba tunda shi ranar ya dawo baisan wainar da ake toyawa ba Sai haroon,

Duk sukayi tsaye cirko cirko sai faman hammar bacci suke yi,

“A cikin ku wayasan inda Junaid yaje !!? Abban su ne ya tambaye su,

Kowa sai faman murxa ido yake yana hammar bacci,

Haɗa baki su kayi wurin cewa “Abban bamu San inda yake ba wlh,”

Tsawa sgr ya daka musu har sai da suka ɗan firgita yace “wannan wane irin shashanci ne ace junaid yabar gidan nan batare da kun sani ba har yakai wannan time ɗin a waje baku lura ba,!”?

Murya na rawa Su twins suka haɗa baki wurin cewa “Junaid fa baya zuwa ko’ina kowa yasani yana cikin gida kullum sai dae wani abun daban,”

“Nima a iya sani na kenan gsky akwai matsala* acewar fawan

Jabeer da Irfan suka ce “mun fa lura baya cikin gidan nan, amma gaba ɗayanmu munyi tunanin yana ɗakin Abba yana bacci shiyasa mukayi shiru,”

Bin su da kallo kawai sgr yake yi suma kallon shi suke yi suna kora bayani,

“Yakamata ajaraba kiran layinsa mana aji inda yake” acewar Khaleed, cikin sauri kanal yusif ya zaro wayarsa dake cikin aljihun wandon baccinsa,

Contact ya shiga ya dubo numbar junaid wadda yayi saving da *Last Born* Ya danna masa kira ta soma ringing,

Gaba ɗaya koya ya saurara yana jiran amsa kira daga junaid, 3 times tana ringing junaid bai ɗaga ba,

Hakan yasa kanal yusif yin amfani da wayarsa wurin duba location ɗin Inda wayar take,

Gaba ɗaya kowa na jiran tsammani, kanal yusif yace “kai ! Location ɗin fa ya nuna cewa wayar tana acikin gidan nan that means junaid yana acikin gidan kenan ko yabar wayar tashi a bedroom ɗinsa ne,

cikin hanzari su fawan suka haye upstars shi da su twins domin su duba ɗakin junaid koyana nan,

A tsiyace suka tura ƙopan ɗakin suka shiga cike da tsammanin ganinsa amma sai suka ga wayam, sae wayarsa dake ajiye saman Pillow bisa gadonsa, hakan na nufin gida yabarta,

Duk basu ji daɗin hakan ba, jiki amace suka sauko down ɗin har haɗa baki suke keyi wurin tambayar Su ina junaid ɗin ? Suka amsa musu da cewa basu ganshi ba sai dae wayar shi kawai,

“I know u will not see him cos i ave checked his bedroom already ya Ilahi,” acewar Abbansu ya faɗi cikin tsananin damuwa,

Hankalin kowa fa ya tashi, bazaman lpy ba Romeo ba junaid ba last born, ba shagwa6a boy Ba dole kowa ya rasa natsuwa,

“nasan inda yake ni,”

Atare suka ɗago don suga wanene haroon ne wanda fitowarsa kenan daga shi sai gajeran wando ajikinsa,

Har haɗa baki suke yi wurin cewa “Yana Ina!?

“Abada cin hanci a ɗauko muku shi,” kai kana ganinsa kasan yasha ya bugu idon nan sunyi jawur kamar na mujiya sai tangyaɗi yake yi,

Tsoki suka ja atare,

Abbansu ya daka mishi tsawa “Haroon kadaina mun wannan wasan kasan inda yake ne ko baka Sani ba _”!!!

Haroon yace “Billahil Azeemu na tsarance da rabbus sama’wati wal’ard nasan inda junaid yake, in ku kayi haƙuri kuka sa salama azuciyarku yanzun nan zan ɗauko muku shi,”

gaba ɗaya mamaki ne ya kamasu su kace shikenan “Muna jira,”

Juyawa haroon yayi ya nufi hanyar ɗakinsa yana faɗin “saboda wannan ɗan shilan duk kun bi kun tashe mutane Fil laili……….

Shigewa bedroom ɗinsa yayi yana ƙunƙuni,

Su kuwa zama su kayi suna ta faman jiran haroon ya fito musu da junaid,”

Jimmm kaɗan sai gashi ya fito hannun shi ruƙe da Pillow yana tangal tangal,

Zuba ido su kayi suna kallon ikon Allah, haroon na ƙarasowa ya shiga ƙoƙarin tu6e rigar pillown yana cewa “Yawwwa ynx zaku ga shegen ya faɗo daga cikin pillown ae nan cikin ya 6uya ja’irin,’

Rai a6ace har haɗa hannu suka yi  Babban yaya da Abbansu suka sharara mashi zafafan maruka , daga shi har filon kowa yayi ƙasa baje,

Ihu haroon yasaki tare da cewa “Eeeeeeee !!!huuu!!!huuuu !!! waman ƙadarallahu haƙƙa ƙadrihi yanzu abba daga abun arxiki zan nuna muku inda junaid ya 6oye sai kawai naji saukar maruka? Yaron nan fa akan idona ya shige cikin rigar filon nan ya 6uya amma shikenan bakomai,’

Abun haushi abun takaici, banza kowa yayi dashi suka shiga tattauna yarda za’a yi a nemo junaid,

Kanal yusif yace “ina ga bari naje na sanarwa Azmee wata’ƙil tasan inda yake,

“A’a bana tunanin hakan, kwarama wannan mai aikin tukur raina yana bani cewa suna shiri sosai da junaid wata’ƙil shi yasan inda yake tunda kusan shine tsaransa,” acewar Abban su

yace hakan ne saboda abunda yagani wato da Junaid yyai ma sehrish magana ƙasa ƙasa lokacin da suna Cin abinci dama abbansu shine ya lura da hakan,

Cikin sauri Fawan yace “Bari naje na tambayesa,’

Yakama hanya da sauri ya nufi wurin ɗakin azmee don yana da tabbacin ɗakin tukur yana kusa dana Azmeee

Sehrish na zaune idanu duk sun kumbura, taji bugun ƙopa da ƙarfi jiki na rawa tace “Wanene,” a tsorace ta tambaya,

Muryar fawan taji yana faɗin “Fawan ne, Fito maza ina son magana da kai,”

Cikin sauri sehrish ta kimtsa ta mayar da gashin bakinta, ta gyara ɗaurin kanta,

Sannan ta taso ta buɗe ƙopan cike da mamakin ganin fawan tabbas kam akwai matsala,

“Gani,” ta faɗi a raunane,

Fawan yace “Kana da masaniyar inda JUNAID ! Yaje !?

Zaro ido tayi gabanta na faɗuwa aranta tace “Ina junaid yaje har daren ne bai dawo ba ake nemansa,’

Cikin sauri tace “a’a gsky ban da masaniya akan hakan,”

“Ka tabbata’?

“Eh wlh,” ta bashi amsa

jiki a mace fawan ya wuce izuwa falon,

Shigewa cikin ɗakin tayi gabanta na faɗuwa sai lokacin ta tuno da cewa ɗazu junaid ya sanar mata da cewa su haɗu a garden After magrib,

.   “to kodai yana can ? May be ya jira ni ne yaji shiru banzo ba bacci ya kwashe shi Acan, kai anya kuwa !? taya ma zai zauna tun bayan magrib zaman jira na har yanzu kusan ƙarfe 1:00 na dare bai shigo ba, gsky bana tunanin hakan,

Haka sehrish ta rinƙa tunane tunane aranta, har ta samu wuri gefen gadon ta tazauna zuciyarta ta saƙa mata cewa “Junaid fa rigimamme ne zai iya yiyuwa yana can ya dage akan in banzo ba ba zai bar garden ɗin ba, kai gsky fa haka nake tunani hankali na bazae kwanta ba har sai naje na duba garden ɗin can, tana faɗin hakan ta miƙe ………………………………………….

Wannan kenan 🙌

Keep sharing it everywhere pls 🙏

Boss Lady 💝

Masu son yi mun Comment ba hali ga Phone no ɗina Only message kuma mata kaɗai (08103884440)*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

*🔥The Father Of Soldiers🔥*

*Na*

*Hafsat Bature Moh’d*

~BossLady~

🔔🔔🔔

_nataƙaita littafin Abban sojoji yanzu yakoma part one and part two only duk mun yawansa zai ƙare a part 2, namai dashi yanzu muna a part 1 sai ya kai 100 pages cuf, sannan part 2 zai shiga, sannan kuma yanzu free pages ne_💔👌

 

Page 94-95

a hankali ta buɗe kopan ta fito cikin sanɗa, gabanta ne ya faɗi da ta hango su gaba ɗaya sun hallara a babban palorn cikin tashin hankalin rashin junaid, har sun fara yanke sha’warar fara kiran friends ɗinsa da sauran ƴan uwa aji koya je can,

Dafe zuciya sehrish tayi tabbas kuwa in tabi ta entry ɗin main palor zasu tambaye ta jin ba’asin ina xataje, don haka tayi deciding ta canza hanya cos there’s many doors acikin gidan da zaka iya fita compound ɗin gidan,

Ja da baya tayi a hankali dama slippers ne a ƙafarta marasa sauti, cikin sanɗa ta lallaba, ta miƙi doguwar hanyar da zata sada ta da backyard ɗin gidan,

Taci sa’a akwai Key ajikin ƙopan jikinta na kerma tasanya hannu ta murɗa key ɗin kopan ta buɗe, ahankali ta zura ƙafa ta fuce,

tsoranta kada security guard ɗin dake strolling acikin gidan su ganta a daren nan tana shawagi tabbas sai sun tuhume ta, gashi ko’ina na gidan Haske ne 6ayau kamar rana saboda fitilun kwan da aka ƙawata shi dasu masu hasken da kyan gaske kamar rana,

A hankali sehrish ke tafiya kamar 6arauniya, har Allah ya shigar da ita cikin garden ɗin kai tsaye wurin da garden chairs ɗin suke ta tunkara,

tunkan ta ƙarasa ta Hango mutun a ƙanƙame saman kujera ya kifa kansa saman table ɗin gabansa, gaba ɗaya jikinsa sai kermar sanyi yake na tashin hankali,

Zaro ido sehrish tayi cikin tsananin tashin hankali ta watsa aguje inda yake gabanta na faɗuwa, tabbas kuwa Junaid ne, dafe kanta tayi tare da cewa “Innalallahi wa’inna ilaihirraji’un !!! Nashiga Ukuna ! Junaid meyasa !!!!!

Cikin tashin hankali tayi maganar tuni hawaye sunzo mata shar a face ɗinta,

Matsawa tayi dab dashi tasa hannu ta bubbuga table ɗin dake gabansa murya a mace take ambaton sunan shi “Junaid…junaid…,’

Wani irin dogon numfashi yaja hatta yatsun hannayansa kerma suke yi, ko eyes ɗinsa bai iya buɗewa tabbas yaji Muryar sehrish amma sam yagaza bata amsa, so yake yayi mata magana taje ta sanar da wani daga cikin gidan yazo ya taimaka mishi ya tashi amma ya gaza, saboda sautin muryarsa baya fita, Lips ɗin ma nasa rawa suke yi kaf kaf,

Bin ziraran yatsun hannun shi tayi da kallo ganin suna kerma kaf ! kaf !! Hakan ya tabbatar mata da cewa Junaid idonshi biyu, sanyi ne yakamashi ssae,.

Cikin sauri sehrish ta cire mayafin da take naɗe gashin kanta dashi ta rufa ma junaid abayansa, duk da mayafin bai da wani kaurin da zai masa magani,

Zubewa tayi saman guiwarta agaban table ɗin, saitin fuskarshi dake kwance saman table ɗin tace “Junaid meyasa? Why pls? meyasa zaka cutar da kanka har haka? dan Allah ka buɗe idonka junaid, ka tashi mu tafi,’

Daker numfashinsa ke fita sam sehrish batayi tunanin tana 6ata lokaci ba wurin agaza masa,

So yake ya buɗe idonsa ya kalle ta amma sam ya gaza, sai kerma eye lids ɗinsa suke yi,

Hawaye ne kawae ke fita a idon Reesh, tana cikin wannan zuƙunnan karaf idonta suka sauka akan Hancinsa da Jini ke ɗigo wa,

Waro ido tayi waje a firgice ta fashe da kuka tare da faɗin “Junaidd…!!! innalallahi wa’inna ilaihirraji’un nashiga ukuna Wayyo Allah !!!

A zabure ta miƙe ta juya da gudu don taje ta sanarwa Aunty azmee wata’ƙil ta taimaka wurin sanar dasu halin da Romeo yake ciki don azo ataimake shi karya mutu,

Har  Tayi nisa da gudun nata muryar shi ta ratsa kunnan ta “Sehrishhhhhhhh,” cikin wata irin matacciyar murya wadda ta galabaita yyi maganar,

A razane ta dakata tare da juyo tana kallon shi, samun shi tayi ya buɗe idonshi waɗanda suka rune jawur daker yake ƴunƙurin tayar da jikinsa da dukkan sauran ƙarfinsa,

Cikin tsananin tausayi sehrish ta koma da gudu wurinsa tana faɗin “junaid,’  tashi yayi zaune yana fidda numfashi a hargitse muryarsa na rawa yace “ki taimaka mun numfashi na zai iya ɗauke wa, ki goyani ki kaini wurin Abbana,’

ɗan zaro ido tayi tana kallonsa can kuma tayi tunanin ae junaid bazaiyi nauyi ba, ba wani girman jiki gare shi ba, duka nawa yake

daddagewa sehrish tayi ta tsugunna masa tare da cewa “hau muje,” daker junaid ya sauko ya faɗo bayanta tare da ƙanƙameta yana numfashi a sama sama,

Jigumm sehrish tayi saboda wani abu da taji ya yi mata yawo ajikinta,

“Ki tashi mana so kike na mutu ko,” junaid ne yayi maganar daker cikin shagwa6a, bawan Allah,

Da iya ƙarfinta na ƙarshe, daker sehrish ta miƙe tana tangal tangal zata faɗi amma ta hana hakan, ta dake ta cije ta miƙi hanyar fita daga garden ɗin da junaid goye abayanta kamar wani ƙaramin yaro, ya lafe abayan sehrish ɗinsa, tana jin numfashinsa a gefen wuyanta saboda nan hancinsa yake, tana jin yarda junaid ya ƙanƙame mata stomach ɗinta saboda ta nan ya zagayo da hannayensa,

Cikin sa’a ta fuce dashi daga garden ɗin kuma ba wanda ya ganta har ta shige dashi cikin ƙopan da ta fito, yanzu tunaninta shine yarda za’ae ta haɗa junaid da ƴan uwansa batare da wani ya ganta ba, tsayawa tayi tana wannan tunanin aikuwa junaid ya fashe mata da kuka mai sautin gaske yana cewa “wai bazaki shiga dani ba so kike na mutu ko,’ duk yarda sehrish taso ta hana junaid magana abun ya faskara sai ma ya ƙara sautin kukan wanda hakan ya janyo hankalin Mutanen gidan dake a falo,

.    gaba ɗayansu sunji kukan junaid da muryarsa, har haɗa baki suke yi wurin cewa “Kai wannan ae kukan junaid ne !!,’

gaba ɗayansu suka nufi hanyar da suka jiyo muryar junaid yana kuka yana yima sehrish faɗa akan taƙi ta motsa takai shi ɗakinsu,

Jin takon takalmansu alaman sun tunkaro wurin yasa sehrish shiga tashin hankalin, gashi ta cire mayafinta, hular kanta ta karkace dogon gashin kanta duk ya barbazo waje, ae kuwa a firgice ta saki Junaid ya faɗi ƙasa tumm !tayi saurin zame mayafinta dake jikinsa, kamar aljana tayi Wuff ta boye a wani saƙo hannunta dafe da saitin zuciyarta,

Junaid kuwa ganin sehrish ta jefar dashi ƙasa ta gudu yasa shi ƙara sautin kukan nashi ya karaɗe ko’ina yadinga burgima a ƙasa yana faɗin “wayyo Allah na, ta jefar ni !! bazaki zo ki goyani ba ki maida ni wurin Abbana ba, Wlh saina tona miki asiri tunda kikai mun hakan…….’ sam junaid fa baya cikin hayyacinsa yake waɗannan maganganun, sehrish kuwa saboda ruɗin abunda junaid yace, tuni futsari ya kufce mata ta cikin wandonta ya soma zuba zirrrrrrrrrr ! Mai zafin gaske cije le6enta tayi tare da runtse idanunta,

 

Isowa su kayi gaba ɗayansu sunyi mamakin ganin junaid baje a ƙasa yana burgima sai faman sambatu yakeyi yana faɗin “wlh saina tona miki asiri kowa ma yasani Allah,’ cikin kuka da shagwa6a yake maganar,

Atare suka haɗa baki suna cewa “Junaid ! ina ka shiga muna ta nemanka? Kai da wanene ? Ta ina ka shigo,’

Jin muryoyinsu yasa shi dakatawa yana kallonsu idonshi biji biji sam bai gane su wanene akanshi,

Murya na kerma yace “ita ce ta shigo dani, ta goyani kuma ta jefar dani ƙasa ta boye acan wurin,’ yayi maganar yana nuna inda sehrish ta 6oye,

Tuni temperature ɗin jikin sehrish ya ɗau wani irin mahaukacin zafi, nan take wani futsarin ya sake zubo mata na tashin hankali, tuni zufa ta gama wanko mata sharkaf wandon jikinta kuwa ya jiƙe sharr,

Babu abunda take furtawa Acikin zuciyarta fa ce “La’ila ha illah anta subhanaka inni kuntu minal Zalimin,’

Gaba ɗaya idonsu ya kai inda junaid ya nuna musu,

“Ah Wannan Fa aikin shaiɗanun aljanu ne kubarmin kawai A ya neh nayi maganin ƴan Iskan,” acewar haroon

Yana maganar ya nufin wurin,

Sgr bai tsaya jin bayanansu ba, hannu kawai yasa ya ɗago junaid dake kwance, ya ɗauke sa kamar wani ƙaramin yaro ya aza shi a ƙafaɗarsa, ya juya batare da ce musu komai ba ya wuce dashi part ɗinsa,

Shi dae abbansu ajiyar zuciya kawai yake saki tunda Allah ya dawo masa da Baby junaid ɗinsa lafiya, kallon sauran yayi tare da cewa “Kowa yaje ya kwanta, koma mekenan gobe zamu duba,”

Juyawa su kayi gaba ɗayansu kowa na faman sauke ajiyar zuciya suka wuce rooms ɗinsu, ban da haroon wanda ke faman sakin murmushin mugunta, domin kuwa ya hango ƙafafun sehrish masu sanye da wannan slippers ɗin nata na ƴan gado,

Bayan kowa ya bar wurin, sehrish tayi tunanin ta lalla6a ta wuce ɗakinta, dama idonta na runtse a hankali ta buɗesu gaf taga fuskar haroon a kusa da tata, wage baki tayi zatayi Ihu yayi saurin sanya hannunsa ya toshe mata baki yana faɗin “Ƴar shila, ae dama nasan kece ja’ira, na hango waɗan nan ƙafafuwan naki masu kama dana Zabbi,’

Tsananin bakin ciki ne ya cika sehrish ganin mutumin da ta tsana,

A faɗace tasanya hannunta tare da Buge nasa, da gudun gaske ta wuce shi ta faɗa bedroom ɗinta tana shessheƙar kuka, datse ƙopan tayi gudun kada haroon yasamu damar faɗo mata,

Jingina jikinta tayi jikin ƙopan bayan ta rufe, tana kuka mai cin rai, ta ƙara jin tsanar haroon a ranta hada shine yaja mata barin junaid yayi ta faman jiran ta a garden gashi hakan yayi masa Illah ssae, duk inta tuna ɗigon jinin junaid da tagani daga hancinsa, sai taji wani irin ba daɗi aranta,

Ta jima jikin kopan kafin daga bisani ta wuce toilet ta tu6e wandon daya jiƙe sharkaf da futsari tasa shi a bucket ta wanke sa, sannan ta shanya shi a siririyar rigiyar dake a toilet ɗin, wadda akayi ta domin shanya panties, da hanging ɗin kaya, bayan ta kammala tayo wanka sannan ta fito ta canza wasu kayan riga da wando

daga bisani ta haye saman gadonta tana sauke ajiyar zuciya, shigewa tayi cikin bargo tana dariya lokaci guda da ta tuna abunda junaid yaso yayi mata a yau da ta shiga uku kuwa, daker bacci 6arawo yayi awon gaba da ita,

A hankali Babban yaya ya kwantar da junaid saman shimfiɗeɗan gadonsa, har lokacin junaid fa bai dae na sambatu ba akan abunda sehrish tayi masa, sai da yaji yatsun sgr a bakinsa, sannan ya ware idonsa da kyau yana kallonsa, yayi tsit daga maganar da yake yi,

Tashi yayi ya kashe a.c ɗin ɗakin gaba ɗaya, sannan ya kunna masa Room heater (na’urar dake ɗumama ɗaki ta zafi) nan take bedroom ɗin ya ɗumama da wani irin ɗumi mai daɗin gaske, hakan yasanya junaid fara dawowa cikin hayyacinsa, sanyin jikinsa ya soma ragewa ssae,

Bayan ya kunna masa, ya fice daga ɗakin izuwa medication room ɗinsu, inda suke ajiyar magunguna,

Abunka ga professional surgeon doctor within minutes sai ga junaid yadawo cikin sense ɗinshi, bayan babban yayan nasu ya bashi medicine ɗinshi yasha,

Sannan yace “Bazan ƙyale ka Ba junaid, u must explain to me where did u go in this night, ka tanadi amsar da zaka bani before tomorrow, Kana mun wasa da lafiyarka ko?” sgr ya faɗi yana kallonsa A yayin da suke daga zaune saman gadon,’

narai narai junaid yayi da ido yana kallonsa, aiko hakan ya fusata sgr rai a6ace yace “zaka kwanta kayi bacci ko saina murƙusaka a wurin nan”?   Koma wa  junaid yayi tare da jan bargo ya lullu6e hada fuskarshi duka, bawan Allah yana so yace ma Babban yayan nasu Yunwa yake ji, amma ya gaza saboda ganin yadda ya fusata dashi,

Kwanciya shima sgr ɗin yayi yaja bargon ya lulu6e jikinsa har wurin neck ɗinsa sannan bacci ya kwashe su, su duka,

(Bacci da Yunwa😥)

________________________________________________________________

A 6angaren su hosana kuwa, tun da suka shiga cikin wannan tsohon store ɗin da Aunty babba ta turasu, Sam sun gaza samun sukuni, daker numfashin su ke fita saboda ƙura ga ko ina a tsohe ba windows,

Sun jima a tsaye cikin tashin hankali ga wani yin bacci da suke ji,

Jiki a mace hosana tace “nidae bacci nake ji, zan kwanta ko,a ƙasan ne,” ta faɗi tare da tattarewa zata kwanta ƙasa, ruƙo hannunta jahad tayi tare da cewa “A’a hosana in ki ka kwanta ƙasan nan wlh ƙwarin nan shigar miki cikin kunne zasuyi suyi miki illah,’ ta faɗi tana kallonta cikin karayar zuciya,

Muryar tamkar zatayi kuka hosana tace “to ya kike so nayi jahad ! A tsaye zamuyi baccin ne !!,

Jahad tace “a’a bari ki ga dabaran da zanyi mana mu kwanta,” tayi maganar tare da sakin hannun hosana ta wuce inda jarkokin nan suke burjiki, tasa hannu tashiga ɗauko su tana kwantar dasu ƙasa a jere, kusan jarka Goma sha biyu ne, ta rabasu shida shida biyu na jikin biyu su ka ɗanyi faɗi, sannan ta ta ɗauki tsumman dake a ƙasan ledar ɗakin tashiga kakka6esu saboda sunyi ƙura ssae ga matattun girgizo asaman su, daker tasamu suka ɗanyi haske sannan ta wurgar da tsumman, ta cire mayafin jikinta wanda saude tabata, ta shimfiɗa musu asaman jarkokin,

murmushi hosana tayi na jin daɗi ganin irin dabarar jahad, gashi ta mayar da Jarkoki sun zama kamar single bed,

Itama jahad ɗin murmushi tasaki tare da juyawa ta kalli hosana tace “To ya kika gani yanzu?

“Yayi kyau ssae jahad ,” ta bata amsa da murna a fuskarta,

“Zoki kwanta to,”  jahad ta faɗi tana Yi mata alamar tazo ta kwanta,

Wuce wa hosana tayi tare da hayewa saman jarkokin ta kwanta, sannan itama jahad ta hau a hankali ta kwanta suna fuskantar junan su,

tace “mu kuma haka rayuwarmu zata ƙare Ko jahad? ko munyi addu’a Allah baya kar6a……

Cikin sauri jahad tace “Waya faɗa miki? Karna sake jin kince haka, Allah shi ya halicce mu, kuma yana sane damu, yana jarabtarmu ne ba don baya sonmu, face donya jaraba ƙarfin imanin mu, in har muka cinye jarabawar nan, zamu kasance masu nasara arayuwa,’

Hosana tace “Yaushe jarabawar zata ƙare jahad? Ae anyi mana dayawa yakamata suma wasu a ɗandana musu jarabawar mukuma mu huta,’

Murmushin takaici jahad tayi kafin tace “Allah shine mafi sani hosana, mu ci gaba da addu’a kawai kada mu daina, domin Allah yana fushi da duk wanda baya rokonsa,’

Cikin sanyin murya hosana tace “Insha Allah bazamu fasa Yin addu’a ba, muna kai kukan mu wurin  Allah ba, har sai ranar da muka koma gare sa,

Murmushi jahad tayi tare da cewa “Hakane hosana,”

A haka har wani wahalallan bacci ya kwashe su, tsakar dare wani uban zafi ya fargar dasu, wata irin zufa ce ke zazzafowa daga jikinsu,

Hosana duk ta razana sai kuka take ta faman yi saboda bata da juriya duba da halin da take ciki ga ciwo ga ta6in hankali,

Daker jahad ta shawo kanta, da cewa ta kwanta ita zatayi mata fifita, cikin kuka tace “dame zakiyimun fifitar,”?

Jahad tace “Hijab ɗin jikin ki, zaki bani,” hannu hosana tasanya ta cire guntun hijab ɗin dake ajikinta wanda saude tabata, ta miƙawa jahad, Sannan ta kwanta saman jarkokin,

A haka Jahad ta shiga yi ma hosana fifita tana kore mata saurayen dake shawagi asama, nan take bacci ya ɗauki Hosana mai nauyin gaske,

Baiwar Allah Jahad idonta sunyi jawur saboda jin bacci, amma sam tagaza runtsawa saboda fifitar da take yima Hosana, tana tsananin tausayinta ssae, tana jin son ƴar uwarta bazata so wani abu ya kuma cutar da ita ba,

Tana Hamma tana yi mata fifita idonta na rurrufewa saboda bacci Amma haka ta jure ta tsayar da kanta don hosana tasamu isasshen bacci 😥 wani sa’in in tana gyangyaɗi har kusan faɗama Hosana take ta galabaita ssae,

Rayuwa kenan wasu mutanen basu da ɗigon imani aransu, basa tuna dame aka haliccesu, basa tuna ta yadda suka zo duniya, Son zuciya kawai, Ynx duk girman gidan general ishaq a ƙalla ba’a rasa bedrooms sama da shida, ga palor Amma a rasa inda za’a ba rai ya kwanta don baƙar mugunta da zalunci sai Store ɗin ajiye tarkacen buhunhuna da jarkoki? Wasu mutanen dae ba tausayi aransu,😿

Masu gidan na can suna shan ra6ar a.c a haɗaɗɗun bedrooms ɗinsu yayin da sukuma suke nan suna fama da Uban zafi, haƙiƙa su hosana sunyi dana sanin zuwansu gidan nan , sai suka ji dama Yaya Omar ya barsu gidan Goggon katsina da aunty saude, Allah sarki ƙaddara ta riga fata 😖

 

****

_ku gyara zama domin kuwa yanzu hot pages suka fara, da zafi zafinsu hada hayaƙi ma🔥😅 Sannan kada maganar payment ta sagar muku da guiwa zanyi muku sauƙi ssae, kuma ku shaidane akan littafin nan in yayi daɗi ma kunsani ba asara zakuyi ba_ 🤝💋

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.