BINTU DIYAR BAYICE 3
Writing by
Abdul qadir Ahmed Narago
Gameson complete book 3 din yaimin magana t WhatsApp number na dake wajan naira 200 kawai zaku biya a tura miku.
. Chapter Bintu karki tafi kibarni pls Bintu kitsaya kiji ina sonki ina kaunarki Bintu wallahi idan kika barni zan iya rasa Raina bud’an bakin Bintu saitace Aisar uncle waishin kamanta nidin baiwace cikin daka mata tsawa Aisar yace ya’isa ya’isa haka Bintu.
Kisani nisanda nake miki natsakani da Allah ne baruwana dake baiwace ta yuwu wasu mutane kallonki suke amatsayin baiwa ammani awajena kinfi duk wata yar sarki a wajena kara matsaya Aisar yayi gaban Bintun.
Dur kusawa yayi ido cikin ido suke kallon junanansu Aisar yafara magana yace please Bintu kisoni koda rabin yadda nake sonkine Bintu nima bansan nakamu da kaunar kiba Saida kika tafi kika barni a ecolo Bintu kice eh kina sona nikuma zan rikeki da gaskiya hartsawan rayuwata.
Yana kaiwa nan kuka yakwace masa itama Bintu ganin Aisar nakuka yasa nata kukan da take dan newa yakwace mata jada baya tafarayi tana girgiza kai ganin haka yasa Aisar mikewa.
Yana cewa Bintu karki tafi dan mesama narokeki Bintu juyawa tayi tafara gudun da batasan inda zata ba shima Aisar bayanta yabi da gudu yana kiran sunanta ko juyowa Bintu batayiba bare tatsaya gudu kawai suke a cikin wannan taf keken filin meciki da tsinre kala kala cak Bintu taja tatsaya saboda ganin mutum a gabanta.
Shiko Aisar betsaya ba saida yaje yashiga gabanta kallon mutumin yakeyi koze ganeshi amma beganeshi wannan mutumin ne yak’arasa wajan Bintun.
Kafin Aisar ya ankara mutumin tuni yadafa kafa dun Bintu sunbace sama da k’asa kasa basu firgigit Aisar yafarka daga mummunan mafarkin da yakeyi bakinsa dauke da ina lillahi wa’Inna ilaihirra ju’un shine abinda Aisar yaketa mai maitawa a fili ganin hasken da gari yayine.
Yasashi tashi da sauri yashiga toilet dan yasan yamakara dayin sallan asubahi bayan ya idar da sallan ne addu’a kawai yaketa jerowa akansu shida Bintu taneman zabin Allah.
Wani tunani ne yazoma Aisar bayan yagama addu’ar cewa lallai dole gobe yatafi masarautar sa’ayrasa domin yaga halinda Bintu take ciki hankalinsa bazai taba kwanciya inhar bazuwa yayi suka hadu ba dan zuwa yanzu yaga yarda yana matukar kaunar Bintu diyar bayi bari kawai yaje yasanar da mahaifinsa.
Yana kaiwa nan a tunaninsa kawai yamike ko tsayawa nade sallayan beyiba saboda sauri yana fitowa part din mahaifin nasa yawuce a falo yatadda gaddafi Nur wato president na jamboriyar Nijar din baki daya kuma mahaifinsa.
Koda Aisar yakarasa falon taraddashi yayi yana shan bakin shayinsa kamar yadda yasaba sha a kullin kwanan duniya yana ganin dan nasa Aisar yashigo yafadada murmushin dake kan fuskarsa kusada mahaifin nasa Aisar yazauna bayan sun gaisa shirune yabiyo baya inda Aisar yakeson yin magana amma yak’asa.
READ ALSO:
- Download Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 10 Romantic Hausa Novel PDF
- Download Complete Matar Damisa Book 1 Chapter 9 Romantic Hausa Novel PDF
- Download Complete MATAR DAMUSA by MALLAKIN ASMEETAH Romantic Hausa Novel PDF
- Download Complete SONE KO K’IYAYYA (32) by Mommyn Fareesa Romantic Hausa Novel PDF
- Download Complete Y’AN MATA RETURN by Hafsat Hisham Romantic Hausa Novel PDF
Saboda waswasin da yake aransa nayafadi karya ne ko yafadi gaskiya kafin yayanke abinda zaice dinne mahaifiyar tasu Haj Barakat tashigo dauke da sallama abakinta suka amsa mata atare kamar hadin baki ganin Aisar da safennan kuma kusada mahaifinsa.
Yasa Hajiya cewa lallai yau tunda naga Aisar anan da sassafen nan to tabbar nasan cewa akwai abinda yakenema dariya presidant yayi tare da fadin nima tunda naganshi a wannan lokacin nasan akwai abinda yakeso amma kuma har yanzu bece komai ba haj data zauna yanzunne ta kalli Aisar tace to fada mana duk abinda kakeso kaji zamuyi maka indai befi karfin muba.
Murmushi mekama da dariya Aisar yayi kamin yace no hajiya kawai dai zanje taya friend dina Sahid murnar birthday din sane president daya gama karantar dan nasane yai saurin cewa dama wannan ne kakeson fada shine tundazu kayi shiru.
To kaje kishirya katafi just you can take your time awajan har sai sanda yayi maka sai kadawo okey Dad nagode bari da yaje nashirya hajiyar mu kuma mom dinmu sai nadawo cikin sakin fuska yayi maganan dan harda dariyarsa bejira mezata ceba yafice.
Murmushi kawai tayi tareda kallon mijin nata tace his excellence amma ko kagane cewa Aisar karya yafad’a eh nasani kuma na yaddane dan nasan baze taba aikata wani mugun abuba to amma inane yakeson zuwa da bayason mu iyayensa musani cewar Hajiya.
Allah masani cewar president yak’ara da cewa Hajiya ki kwantar da hankalinki kawai kimasa addu’ar Allah yatsare shi aduk inda zaije Haj barakat shiru kawai tayi batajin zata iya cewa komai shiko Aisar yana fita dakinsa yakoma toilet yashiga yayi wanka yafito amma sai yakisa kaya kawai kwanciya.
Yayi akan shinfideden bed dinsa dagashi sai towel farin cikine fal aransa saboda yau zaiga Bintun sa farin cikin sa karuwa kawai yakeyi Allah Allah yake karfe goma 10 tayi yakeyi dan yashirya yaje wajan Bintu.
Masarautar Fabarusa
Bayan sallan isha wajan 8:30 Bintu ce zaune a room dinta but tarasa meke damunta dan tunda Barde yaturo Bakar number aka sanar da ita cewa yau Barde yana kan hanyarsa tazuwa wajanta hakane yasa tarasa sukuni gakuma yawan tunanin Aisar da yawan mafar kinsa da takeyi.
Maman changwai ce tashi dakin ta zauwa gefenta mamakin halin da Bintu ke cikin maman Cangwai takeyi firgigit Bintu tadawo natsuwar ta saka makon tabata da taji anyi ganin maman Cangwai ce yasa Bintu sakin dogon ajiyar zuciya.
Magana maman Cangwai tafara yata kidaukeni a matsayin mahaifiya agareki kisanar dani matsalarki tayuwu inada shawarar dazan baki wanda zata cireki daga halin da kike cikin Bintu kallonta tayi amma saita kasa sanar da ita komai cen kuma saita tsinci kanta da fadin taya ake gane soyayya ko mutun yakamu da ita.
Maman Cangwai taja tasaki shiru tayi na wasu secords cen tace to nidai a iya nawa sanin babban alama da mutun ke yane yakamu da son wani shine zai dinga yanwan tunanin mutum sannan koda sunansa aka kira gabanka zaringa bugawa da sauri da sauri sai farin ciki da zarar yaganshi kojin sunansa.
Sannan abuna karshe dana sani shine zakaji aduk fadin duniya bakada burin da wuce ganinshi iya dan abinda nasani kenan akanso amma akwai abu daya kudena yawan tunanin cewa yawan tara samari shine zaisa kiyi aure wallahi ba haka bane hasalima saidai kirasa damarki ta auran miji nagari.
Wallahi babu namiji indai nagari ne da zaizo wajan macen da takeda wayan samari kunsan meyasa dalilin shine namiji mekishin kansa tofa yana kishin duk wani abunda yakeso.
Shiyasa bazai juri ganin budirwansa da wasu samarin ba hakane zaisa yatafi yabarki indan ko irin mazajen yanzu ne bama susan meye sodin ba kuma basa kishin kansu to belle kuma suyi kishin abinda suke so sudai kawai sutara yam mata suma a haka suke rasa damarsu tasamun mace tagari saboda sunki tsayawa.
Susan meye soyayya kuma wallahi dama so d’aya take zuwa sai kayi mugun sa,ane zata zomaka sau biyu dan haka wallahi ku natsu sosai kafin kukori masoyanku kuyi tunani kafin kuci mutuncin wanda yace yana sonku karku kalla dan kuna da yawan samari.
Ko kunada kyau hakan yasa ku wulak’an ta wani kodan inada yawan yam mata ko farin jini hakan yasa naci zarafin wata dan tana sona to akwai lokacin karewar farin jinin yam matan duk subarka alhakin matan dakasa bakin ciki yakamaka sai kahadu da wanda zata baka wahala koda ka aureta farin cikin ka na yan kwana kine bakin cikin yafiyawa kuma wani ikon Allah.
Saika kasa sakinta saboda kana matukar sonta sasai kema bakin cikin wani hakan zai miki dan wallahi Allah baya taba yafe hakkin wani akan wani sai ku kula tunkan kurasa damarku.
Maman Cangwai tana zuwanan azancen taja dogon ajiyar zuciya Bintu ko kallonta kawai takeyi dan zancen yayi matukar zatsa Bintu aranta tafara tunanin kenan tunda dadewa takamu da soyayyar Aisar.
Maman Cangwai ce takatse mata tunanin da takeyi da cewa Bintu tashi kije kishirya kinsan Barde yakusa zuwa nasa angama gyara ko ina ke kadai yarage kishirya wata tsanar Barde ne taji yadira mata a cikin zuciyarta cikin hade fuskar tace mekuma zaizo min anan ni bana bukatarsa a yau.
Cikin mamakin ta maman Cangwai tace gimbiya Fatima meye kike cewane haka bafah ayima miji haka miji Bintu tamai maita fuska a yatsine niban daukeshi a matsayin mijija ba koda ko ace narana d’aya ne to yaushe ma akayi daren bare garin yawaye kawai ni nariga da nagama magana ta.
Banason ganinsa a yau idan shi yamanta da cin mutun cin da yamin niban mantaba tana kaiwa nan tamike tsaye kayan jikinta tarage sannan tadawo ta kwanta tunda Bintu tafara fada maman Cangwai takafe ta da ido tana mamakin yaushe Bintu tazama haka salin alim maman Cangwai tafita.
Tare da rufe mata k’ofan shiko ango Barde yau a cikin farin ciki yawuni abu kadan saiya ringa murmushi shikadai Allah Allah kawai yake dare yayi Bakar number ne yashigo cikin girmama wa yazube gaban Barde dake zaune a falonsa a saman tik’a tik’an kujeru yana nishadi shika dai.
Kirari yafara jeroma Barde Allah yajada ran babban Barde kowa Kai karo dashi buhun k’aya kake kafi karfin dauka sai kallo Barde kake angon gimbiya Fatima yau ranar takace gimbiya Fatima tana maraba da zuwan ka cikin matukar ji da Isa ya murmusa kamar baze magana ba sai kuma yace wankan yau na masan manne domin daren yau yafi ko wanne matsayi a wajena.
Acen gefe d’aya kuma yarima Sadauki ne zaune a wani garden dake cikin masarautar tare da mabiyan sa kwance yake ya lumshe idanunsa bakomai yake tunawa ba illa matar kaninsa wato Bintu yadda surar jikinta ke juyawa idan tana tafita kawai yake gani a idansa sha’awar ta k’ara karuwa take a cikin ransa yakuma rasa taya zai sameta.
Wani wanda ake kirada Mugu ne yashigo cikin garden din gaban yarima Sadauki yazube yaname yimasa kirari kala kala kamin daga karshe yace Allah yak’ara tsawon kwana yarima Sadauki.
Kamar yadda kace a yimaka bincike akan matar yarima Barde nayi binciken amma sedai bansami komai ba sai abu daya Sadauki da idaninsa suke rufene yabude su sunyi jajaye na jaraba cikin sonjin abinda aka samu yace meyeshi abinda kasamo kai Mugu yasaukar k’asa tare da jinjina hannunsa da yake rufe yace.
Naje masarautar Sa’ayrasa nasami labarin komai gameda gimbiya Fatima sannan nasami labarin su biyu aka haifa a wannan lokacin saidai sunada banban ci banban cin nasu shine daya baiwar gidan sarkin.
Sa’ayrasa ce ta haifeta d’ayar kuma matar sarkin ne ta haifeta dukkan su yaran sunan su dayane amma sun banban ta wajan kiran sunan diyar sarkin Binta suke cemata yar gidan bayin kuma Bintu kuma itace baiwar gimbiya Binta wato Fatima
Abin tam bayan anan shine meyasa iyayen Bintu zasu bargari dan za’ayi amren yar sarki Binta bud’an bakin Sadauki sai yace sedai in idan akwai makir cin da aka shirya akai nima nayi wannan tunanin cewar Mugu.
Shiyasa nayi tunanin neman cikakkan labarin ata bangaran mutanen dake shiga cikin gidan Sarkin Sa’ayrasa na tam bayi mutane da dama amma sunce basu san komai ba.
Sedai natam bayi jakadiya indai labarin masarautar nakeso to fah saidai natam bayeta dan itace kawai zata fadamin duk wani abu dake faruwa gameda gidan sarki amma fah zata fadane kawai idan har anbata tarin dukiya masu yawa yana kawa nan yasauke a jiyar zuciya kamin yaci gaba da fadin to shiyasa nadawo dan naji yaza’ayi wannan ba abinda damuwa bane cewar Sadauki.
Kallo d’aya Sadauki yayima wani daga cikin mukar rabansa juyawa yayi yatafi sai gashi yadawo da kudi masu yawa sosai yazube su a gaban Mugu izinin diba Sadauki yabashi cikin sauri Mugu yakwashe kudin zetafi muryar Sadauki ce tatsayar dashi inda yace Mugu kasani karka yarda kadawo min nan bada wani lavari mekyau ba zansa a kashe ka.
To……. Lefin dadi dai karewa Dan haka anan zan tsaya a cikin littafin BINTU DIYAR BAYI CE book 3 Kuma chapter 31/40
Dan haka nagode bisa nuna min goyan bayanku akan wannan labarin
Yauwa g hanya mafi sauki dan samin ci gaban littafin BINTU DIYAR BAYI CE dama dai sauran littafai na dake rubutawa
Hanyar itace zaku ringa samun littafai nane a duk bayan kwana bakwai 7 zanyi posting akan group dina na Facebook dama sauran Hausa novel groups
idan kuma ta WhatsApp ne zan ringa posting ne a kullin a cikin group dinmu me suna
NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY.