Download Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 79 Hausa Novel PDF

Tofah nan fa kowa ya shiga tunanin wata hujja ce Sgr ke da ita?kanga wayar yayi a kunnansa,then Calmly ya furta”Ku ƙaraso ciki,”jin haka yasa kowa kai idanunshi kan ƙopar shigowa falon,don ganin su wanene zasu shigo ciki,

Bada jimawa ba,wata haɗaɗɗiyar Wheel chair Golden Colour mai ɗauke da wani dattijo tsoho tukuf fari tass hatta sumar kanshi furfura ce fara tass babu zaren gashi ko ɗaya daya kasance launin baƙi,hatta gashin girarsa dana idonsa fari ne tass duk furfura ta mamaye ko’ina,wani matashi ne ke ruƙe da ita yana turashi a nutse,tashin hankali ae koda Ammi tayi Arba da mutumin dake a saman wheel chair ɗin nan,hankalinta gaba ɗaya ya tashi haikam,ba ita ba Hatta su Abba dasu Gwaggo da Azeema sunyi matuƙar mamakin ganinshi,saboda a iya saninsu baya qasar,a Saudi Arabia yake da zama,amma sai gashi yau Unexpected yazo,wannan wani irin zuwan bazata ne?

Lokacin da matashin ya ƙaraso dashi ciki Ammi ta tabbatar da cewar dagaske dae shine,a kiɗime ta miƙe tsaye muryarta na in,ina ta ambaci sunan shi”Mo…moddibo”
Wani irin kallo tsohon ya wurga mata,kallon zakiyi bayani,gwaggon katsina kuwa wani irin farin ciki ne ya lullu6e ta,saboda tasan cewa tunda Modibbo ya tako da ƙafafunsa yazo Nigeria to tabbas za’a samu maslaha,saboda duk duniyar nan babu wanda ke taka ma Ammi burki in ta burkice sai Shi!mugun shakkar shi take ji,saboda shi tamkar Ubane agareta,a hannunshi ta taso,shiyasa yasan hanyoyi da dama da zai iya tankwarata,kuma duk wasu halaye nata da ɗabi’unta nashi ne sak ta ɗaukko,amma shi da ya manyanta ya ajiye wannan jin kan,’

Bayan saurayin ya tsayar da wheel chair ɗin,Modibbo ya yunƙura tare da miƙewa da sandar hannunshi,cikin sauri suka bashi wuri,ya samu wuri ya zauna a hakimce saman sofa,nan kowa ya shiga gaishe dashi suna yi mashi sannu da zuwa,fuskar nan tashi asake yake amsa masu,ba ƙaramin daɗin zuwan modibbo suka ji ba,bayan ya kammala kar6ar gaisuwarsu ɗaya bayan ɗaya,
Sannan Ammi tace”Yaya sannu da zuwa,ya gajiyar tafiya”

Fuskarshi aɗaure yace”Gajiya tabi jiki,ae ba yau nazo ba,tun shekaran jiya ina ƙasar nan,zuwa ne kawai banyi ba,kuma ba don kowa nazo ba sai don saboda ke!”
Jin haka yasa ta koma ta zauna,jiki asanyaye,

Cikin sauri Abba ya kalli su fawan tare dayi masu alamar su tashi su bar wurin,”mikewa su kayi dama Jahan a ƙagare yake daya bar wurin,duk ji yake kamar ya ɗosa mazannansa akan wuta,atare suka miƙe tare da barin wurin,Ya rage daga Gwaggon katsina,Abbansu,hajiya Azeema,General ishaq,da Cg Abbas,Uncle Abusufyan,marshal Omar da Sgr,bayan su kuma sae su Jahad dake zaune ƙasa,duk sunyi zuru rayuwarsu a hannun Allah,basu san su wanene waɗannan tsoffin ba,amma sun tsorata dasu,musamman Ammi data tayar masu da Hankali,har tana ƙoƙarin korarsu daga gidan,

Bayan su jahan sun shiga ciki,ya fashe da dariya hada dafe ciki yana faɗin”Dama ance GABA DA GABANTA ALJANI YA TAKA WUTA”💥

Junaid kuwa,bedroom ɗin Abbansu ya wuce,anan ya samu mommynsu tsaye agaban drawer,jikinta sanye da doguwar riga,tana ƙoƙarin sanya mayafi akanta,
Sam bata lura dashi ba,har saida ya ƙarasa bayanta tare da rungumota,hannu tasa tare da janyoshi ta dawo dashi ta gabanta,a shagwa6e ya ambaci sunanta”Mommy dama kina a ɗaki,bakisan meke faruwa ba a babban falo,”

Hannu tasa tare da shafa fuskarshi tace”Romeo,bani da alaƙa da abunda ke faruwa acan,yanzu faɗamun naga fuskarka kamar akwai damuwa,”
“Mommy,ba Ammi bace take son korar su Jahad daga gidan nan ba,”
“To menene damuwarka aciki don ta kore su”?

Sakin baki junaid yayi yana kallonta kafin ya ɗaure fuskarshi yace”Haba Mommy,ƴa’ƴan uncle ɗinmu fa ne,taya ba zan damu ba,uncle fa yana sonmu sosai,muma dole mu so ya’yanshi,kuma su jinin mu ne,nidai wlh banso ta koresu,kuma Allah koda ace ta koresu,wlh saina bisu…..’ya ƙarasa maganar yana zum6ura baki,
Hannu tasa taja kumatunsa”Ni kuma an gaya maka zan barka ne?zansa a ɗauke mun kaine,in kaika U.s mu cigaba da rayuwarmu acan,ko ba zaka bi mommynka bane,”
Bubbuga ƙafarsa yayi tare da cewa”I wanna fallow u Mom,amma Allah sai dai mu tafi mu duka tare dasu sehrish,jahad da hosana,”
“Dole dai saina je dasu”?

ɗaga mata kai yayi alamar eh,janyo shi tayi ta rungumeshi ajikinta,”don’t worry dear kome kakeso zanyi,indae hakan zai faranta maka rai,yanzu mu zauna ka tayani fira,inaso mu tattauna wata magana dakai mai mahimmanci,”
Komawa sukayi tare da zama daga saman gadon,suka ci gaba da tattaunawa a tsakaninsu,

Aunty Babba

Lokacin da suka faɗa cikin ɗakin suna murna ita da hayaam,tsayawa sukayi daga tsaye,suna tattaunawa,Aunty babba tace”Ae dama saida raina ya bani cewar Ammi bazata barsu su zauna a gidan nan ba!gaskiya matar nan ta burge ni wlh,yadda ta zagesu tass ta kirasu da shaggu hakan ba ƙaramin nishaɗi ya sani ba,in banda ma shashasha irin Abusufyan taya zaka kawo ƴa’ƴa daga sama kace ya’yanka ne,kuma kayi tunanin cewa kowa zai yarda dakai?Ae ni wlh tayi mun dai dai matar nan,”

Ta ƙarasa maganar tana faman sakin shu’umin murmushin nan nata,

Hayaam tace”Nima ba ƙaramin burgeni tayi ba,naci dariya lokacin data korasu suka watsa aguje suna kuka,ƴan jakar uban,yanzu sai muga ina zasu dosa,dama su kashe kansu kawai su huta muma kuma munsamu natsuwa,” cike da nishaɗi take maganar tana watsa hannu alamar ita ko ajikinta,
“Dama abunda yasa nake son Ammi ta koresu,kinga na farko zasu fita daga cikin zuri’arsu ne gaba ɗaya,babu su babu auren ɗaya daga cikin ƴa’ƴan Abba,saboda Ammi bazata bari su auri bare ba,balle kuma yaran da ta ambaci sunansu da shaggu,Secondly kuma wannan korar da tayi masu,zai hana Ishaq da Omar su tuhume ni akan tonan asirin da waccen Zararrar taso tayi mun a bainar jama’a,kinga riba biyu kenan,”

Tana kai karshen maganarta,hayaam ta ɗaura da cewar”wannan haka yake Auntyna,mu ɗin jinin nasara ne,duk abunda muka sa agaba sai munga bayanshi koma uban menene shi,”
Dariyar mugunta Aunty babba ta kuma saki kafin tace”Bazan ƙyalesu haka nan ba,saboda Omar zai iya bin bayansu don ya taimakesu,dole in samu wanda zaibi takansu da mota su mutu kawai,kowa ya huta,”
Hayaam tace”faƙat!kinga babu su a duniyarma balle ayi dasu,”

Also Download FARRAH Hausa Novel Complete Document By Maman Shuraim

…….duk wannan surutan da suke yi,Amani na la6e a ƙopar ɗakinsu wadda bata idasa rufewa ba,tana recording ɗin muryoyinsu a wayarta,don taci alwashin saita tarwatsa duk wani plan nasu,Ni boss nace kinyi mun dai dai,

Boss Bature
The genius

bari mu leƙa falo muga meke wakana,shin ansamu cigaba ko kuwa ana nan yadda ake?

Natsuwa su kayi gaba ɗayansu,wurin yayi tsit tamkar mutuwa ta gifta,kowa ya natsu ya nabba’a tamkar ɗalibai ne agaban ya sayyadi,bafa sayyadi mijin abu ba,ina nufin malami,kar ayimun wata fahimta,

“Waɗannan sune ƴan ukun Abusufyan ɗin”modibbo ne yayi maganar yayin da idanunshi ke akan Su jahad dake zaune sunyi zuru zuru,’
Har suna haɗa baki wurin cewa”Sune,”
Jinjina kai yayi tare da mayar da idanunshi kan Ammi yace”Ki kace yaran shaggu ne ko?Wata hujja gare ki na cewar bada aure ya haifesu ba?
Fuskarta aɗaure tace”Ina da hujja,saboda nice mahaifiyarshi,kuma ni bansan an ɗaura mashi aure da kowa ba,”

Girgiza kai modibbo yayi,sannan yace”hannunki ya taso ne?ko kuwa wurin ki kaɗae za’a iya ɗaura mashi aure ne”?
Shiru tayi batace masa uffan ba,cigaba da magana yayi”don haka baki da wata hujja ta cewar abusufyan yayi aure ko baiyi aure ba,ya samu ƴa’ƴa,wlh Aisha kin ban mamaki!wai har yaushe ne zaki ajiye waɗannan makaman yaƙin naki ne?ke fa yanzu ba yarinya bace,kin tara ya’ya da jikoki amma har yau bazaki ajiye wannan zafin ran naki ba,sai yaushe ne ya’yanki da kuma jikokinki zasu ji daɗin zama dake ne?yanzu ni ba misali bane agareki?ko bakisan wanene modibbo ba?kinfi kowa sanina bani da wasa ko miskala zarratin,

duk wani kangararre acikinku,keda ƴan uwanki nine nan nake tankwarashi,amma yanzu saboda na manyata,na tara ya’ya da jikoki,duk na ajiye waɗannan ɗabi’un,Na canza kaina ne ba don komai ba sai don saboda ya’yana da kuma jikokina suji daɗin zama dani,kuma suyi alfahari dani amatsayina na kakansu,bawai su dinga tsoro na ba,suna gudu na harma su dinga yi mun fatan mutuwa,kamar ke ɗin nan dai…..’yayi maganar yana nuna ta da sandar hannunshi,sunnar dakai Ammi tayi tana faman jinjina kai,

READ ALSO:  Download Complete Y'AN MATA RETURN by Hafsat Hisham Romantic Hausa Novel PDF

Canza harshe modibbo yayi izuwa harshen fulatanci,yayi hakan ne saboda kada faɗan da zaiyi mata ya zama tamkar tozarci ne agaban jikokinta,

“Gaba ɗaya kin takurawa rayuwar ya’yanki,da ta jikokinki,kin hanasu sakat,ko irin wasan dake tsakanin kaka da jikan nan bakya yi masu,kullum burinki ki ƙuntata rayuwarsu,shin menene ribarki idan kinyi hakan? Ya ɗan dakata da maganar yana kallonta,kafin yaci gaba da cewa”Yanzu jibi yaran nan ƴan wurin fatima,hakanan kika ɗaura karan tsana kika ɗaura masu sai kace ba jininki ba!in ma saboda mahaifiyarsu ne,ke kin ta6a ganin inda laifin wani ke shafar wani ne?in kuwa haka ne ae da dukkanmu mun shiga uku,saboda wancan zaiyi sata ne a ɗaura maka laifin bayan bakai ne ka aikata ba,”

Katse shi tayi cikin harshen fulatanci tace”Amma yaya modibbo ni meyasa ya’yana basu jin maganata ne?basu ɗaukeni mahaifiyarsu ba,suna yin abu gamon kansu batare da sun sanar mun ba,Hossein ya ƙetare ƙasar nan yaje yayi aure batare da sani na ba,sai dai kawai na ganshi da mata ya dawomin,matar kuma ma farar fata ba jinsun mu ba,sannan kuma Abusufyan shima yayi aure batare da sani na ba,saboda me zasuyi mun haka ne?

anzo dai dai wajen,acewar modibbo gyara zama yayi sannan yace”kin manta yadda akai kika auri salahuddeen ne?to idan kin manta bari na tuna maki,dama duk wanda ya bijire ma iyayensa ko ba daɗe ko ba jima sai shima yaga ba dai dai ba,na farko bada sa hannun iyayenmu ba,kika shiga aikin Soja,babu irin yadda ba’ayi dake ba don ana ganin bai dace dake ba,ba kaman daya kasance ke bafullatana ce,amma kika ƙeƙashe ƙasa kikace sai kinyi aikin soja,a ƙarshe da aka takura

maki,shine kika tattara kayan ki kika dawo gidana da zama saboda kina tunanin cewar ni zan goya maki baya don ki samu abunda kikeso,da kika zo wurina a lokacin na nuna cewar nima bazansa hannu na ba acikin lamarin tunda har iyayenmu sun nuna basu so,a ƙarshe sai kika gudu batare da sanin kowa ba,kika shiga aikin Soja,sae dai kwatsam muka ganki da kakin Soja ajikinki,ko ba haka akayi ba”?

Wata irin zufa ce ta shiga wankowa a fuskar Ammi sam bata ta6a tsammanin cewa wannan ƙaramin kuskuren data aikata na bijirema iyayensu,zai dinga bibiyar rayuwarta bane,
“Akan wannan aikin sojan da kika shiga,babu wanda baiyi kuka dake ba,saboda kafiya,da taurin kai irin naki,ga jinkai dake gareki,iyayenmu basu isa su baki umarni kai tsaye kiyi abu ba,sai sun biyo ta wurina saboda shakkarki da suke ji,bayan wannan kuma,baki sanar ma kowa ba game da salahuddeen lokacin da kuka fara soyayya dashi ba,sai daga baya ne muka fahimci shi ya hure maki kunne har kika bijire mana kika shiga aikin sojan,hakan kuma yasa duk muka ki amincewa da farko ki aure shi,amman da yake Allah ya kaddaro aure tsakaninku ba yadda muka iya dole muka kyale ki ko don kafewar da kika yi da kuma rabon itama Ameena anan zata samu mijin, ko ba haka akayi ba”?

Jinjina kai Ammi tashiga yi yayin da idanunta suka cicciko tab da kwalla amma bata bari sun zuba ba,
Gwaggon katsina kuwa,sae faman sakin murmushi takeyi,tana faɗin”kwarai kuwa,haka akayi,”Abban su junaid kuwa da hajiya azeema duk jikinsu yayi mugun sanyi,sae yanzu suka gane daga inda matsalar take,dama duk in mutun yaga rayuwarshi tana tafiya ba dai dai ba,kuma bai akaita wani zunubi,toWlh ya binciki kanshi!ya tuhumi kanshi ahankali zai gano dalili,

Su jahad dae suna nan tsugunne sun kasa kunne suna sauraronsu,sai dai subi bakin modibbo da kallo,daga bisani in Ammi na magana subi ta da kallo saboda basu iya fulatanci ba,haka Marshal Omar dasu ishaq duk basa jin fulatanci,haka zalika Sgr baya jin harshen nasu,dama shi ko hausa daƙyar ya koye ta,kuma har yau in yana magana da harshen hausa sai ka gane cewar ɗan koyo ne don sam hausarsa bata nuna ba shiyasa bai fiye yin magana da hausa zalla ba saiya haɗa da turanci ko spanish,amma kuma hausar tashi ba ƙaramin daɗi takeyi ma mutane ba,

Murmushi Modibbo ya ɗan saki kafin yaci gaba da cewa”ina fata yanzu kin tuna komai”?
Siraran hawayen da take 6oyewa ne suka gangaro a saman fuskarta,muryarta ƙasa ƙasa tace”Na tuna,”
Modibbo yace”Tunda kin tuna bari na ƙara ɗaura ki akan hanya,irin abunda kika aikata ne yasa shima ɗan cikinki da kika haifa yaje yayi aure batare da saninki ba,saboda gudun kada ya fara sanar dake ki hana shi yin auren,hossein ya auri Alala..kunzandariya….”kasa ƙarasa maganar yayi saboda bai iya ambaton sunanta ba,abun yaso yaba Sgr dariya,amma ya basar da ita tare da gyara mashi sunan yace”Alexandra ne sunan,”

Modibbo yace”yawwa ɗan gari,bazan dai iya Ambaton sunan nata ba,a barshi a fatima,tunda ae ta ta6a musulunta,kuma muna sa ran zata ƙara musulunta insha Allah,”
Suka ɗanyi dariya,kafin ya ɗaura da cewar”Hossein ya auri fatima batare da saninki ba,saboda yasan halinki sarai kin tsani jinsin da ba naki ba,gudun kar ya sanar dake kiƙi amince masa yasa shi yin hakan,sannan……”modibbo bai ƙarasa maganar ba,ammi ta kuma katse mashi hanzarinshi da cewa”Yaya modibbo amma ae ni harsu biyu sukayi mun haka!bayan ni,ni kaɗai ce na bijire ma iyayenmu haka,”

wannan maganar ta Ammi yasa shi yin dariya,tare da girgiza kai yace”in kikayi wata maganar kina tunamin da ƙuruciyarki wlh,dama ita irin sakayyar nan tamkar ramuwar gayya haka take,kuma ita ramuwar gayya tafi ta gayyar zafi,sakamakon abunda kika shuka ne,yasa kika girbi kyakkyawan sakamakon da ya zarta nakin,kuma tunda har kika iya ƙyale hossein bayan laifin daya aikata maki na auren bare kuma farar fata ae yaci ace kin yafe ma Abusufyan tunda shi da ƙuruciyarshi ya auri yarinyar,kuma hada sa hannun gwaggonshi,kuma kinsan wacece ita a wurinki,da mahaifinmu da nata uwa daya uba daya,kuma saboda yardar da kikayi da itane yasa kika damƙa mata

amanarshi,ita kuma ƙaunar da take yi maki ne ya shafi ɗanki da kika haifa,hakan yasa ba zataso wani abu ya cutar dashi ba,Yaro ya nuna yana son ƴar mai gadin gidansu,ke kuma kin tsani auren bare mara asali,gashi shi kuma yaron ya kwallafa rai akan yarinyar,don lokacin da ita Aminatu taso ta sanar dake game da yarinyar balbaleta kikayi da masifa,kina cewa karta kuskura ta bari alaƙarsu tayi nisa,ta raba tsakaninshi da yarinyar,a ranar saida Abusufyan ya suma jin za’a raba shi da abunda yakeso,wannan dalilin ne yasa hajiya ameenatu ta aura mashi yarinyar batare da ta sanarma kowa ba,sai ni ɗinnan da nake magana,”
ɗagowa Ammi tayi tana kallonshi cike da mamaki,

Jaddada mata maganar yayi”kwarai kuwa ta sanar dani,nasan da zancen auren,kuma aranar da aka ɗaura auren Abusufyan da zainabu abu,ina ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren batare da sanin kowa ba,ita kanta hajiya ameenatu batasan na halarci ɗaurin auren nasu ba,a iya waya kawai ta sanar dani,sae kuma akaci sa’a ina da wani taron manyan malamai da zamu halarta anan jihar kano,wannan ne babban maƙasudin daya kaini garin harna shaida wannan ɗaurin auren…..”

Ae tunkan modibbo yakai ƙarshen maganar wani irin murmushin farin ciki ya bayyana akan fuskar kowannansu,saboda yayi maganar ne cikin harshen da zasuji,wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya abusufyan ya shiga saukewa,nan take yaji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarshi,duk da yayi mamakin zuwan modibbo wurin ɗaurin auran nashi saboda bai ganshi ba,amma tunawa da irin dubban al’ummar dake a masallacin kuma ya kasance ranar juma’a ne ana kammala salla aka ɗaura auren nasu,tabbas bazai iya tantance kowa dake a wurin ba,amma ko a lokacin bayan an ɗaura auren sun koma gida sai da baba buzu ya kirashi gefe guda yake sanar dashi cewa”Wani babban malami,yayi mashi alheri bayan sun fito daga masallaci,kuma yana tunanin cewar Kamar jininsu ne saboda yaga kamannin Hajiya ameena a fuskarshi,a lokacin Abusufyan bai gane wanene ba,sai yau da modibbo yayi maganar nan kwatsam ya zancen ya faɗo mashi aranshi bayan ya shiga zurfin tunani,tabbas kuwa modibbo ne,

READ ALSO:  Download Maraici Ne Yajaa Mun Hausa Novel Complete PDF

Murmushi modibbo yayi tare da kallon Abusufyan yace”nasan zakayi mamaki,saboda nazo ɗaurin auren ka batare da sanin kowa ba,uzuri ne ke gare ni a lokacin shiyasa ban nemeka ba,don nasan muddin ka ganni a lokacin saika nace akan in tsaya,”
ya ƙarasa maganar tare da mayar da idanunshi kan Ammi,tun kafin ya kuma cewa wani abu,muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”Amma yaya kasan da maganar auren nashi shine ba’a sanar dani ba?saboda me?
“Saboda halinki”! Kai tsaye ya bata amsa,

“Tabbas naso in sanar dake ko alokacin,saboda kinsan cewa ni bana jin shakkarki,hajiya ameenace ta rokeni akan cewar karna sanar dake,saboda hakan zai iyasa ki fusata harma ki yanke ma Abusufyan hukunci mai tsanani,kuma a ƙarshe zumuncin dake tsakaninki da ita ya tarwatse,dana nace akan zan sanar dake har kuka saida tayi mun,wannan dalilin ne yasa ban sanar dake ba,kuma ana haka daga baya kwatsam naji labarin mutuwar auren Abusufyan ɗin,hada ƙarin haka yasa akabar zancen gaba ɗaya,ashe yarinya ta fita da cikinsa ta auri wani,to kinji dalilin dayasa mu kanmu bamu san da ya’yan nashi ba,har suka kai wannan girman a hannun mijin da ta aura daga baya,”

Dakatawa yayi da maganar,falon yayi shiru na wani lokaci,kafin ya mayar da idanunshi kan Sgr dake zaune,yace mashi”ka kunna mata audio din nan daka kunna mun itama ta saurare shi,”
“Okey,”ya amsa mashi tare da,daddana wayar hannunshi,ya shiga audio din tare da

kunnashi,sannan ya miƙe tare da ƙarasawa kusa da kujerar da Ammi ke zaune ya miƙa mata wayar,yatsun hannunta na kerma tasa hannu ta kar6i wayar tashi,ta ajiye asaman hannun sofa ɗin tana sauraronshi,wannan audio din na labarin da abusufyan ya bayar ne da kuma Labarin dasu sehrish suka bayar na irin ukubar da suka sha a hannun ya sayyadi,ashe ranar da abun ya faru,Sgr ya ɗauki audio na maganganun da sukayi kaf acikin wayarshi,tabbas shi ba ƙaramin jami’in Soja bane!yana Aikinsa wani lokacin tamkar jami’in sirri,Na jinjina masa,da irin baiwar da Allah yayi mashi da kuma irin kwazon dake gare shi,ta ko ina Sgr ya haɗa,shiyasa nace maku shi ɗin komai nasa Extraodinary ne~~~

Miƙewa junaid yayi tare da ruƙo hannun Mommynsu yace”Shikenan mommy tunda mun kammala discussion din,ki taso muje falo pls,kada kice baki zuwa,in ba haka ba raina zai 6aci,wlh ko abincin dare bazanci ba,indai kika ƙi zuwa gaishe da modibbo,”
Cike da mamaki tace”Modibbo?kana nufin mahaifin maryam oummunsu Omar?

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

daga mata kai yayi alamar eh,
Shiru tayi tana wani tunani,a iya saninta modibbo mutunne mai mutunci sosai,saboda shine ya taka ma Ammi burki a lokacin da taso Abba ya sake ta,tabbas bazata ta6a mantawa da halarcin da modibbo yayi mata ba,

Ganin ta miƙe yasa junaid sakin murmushi yace”mommy zaki ko”? Jinjina mashi kai tayi alamar eh,
Janyo hannunta yayi har suka ƙaraso falon,ganin hankalin mutanen dake acikin falon gaba daya yana akan Audio din da ammi ke saurare,hakan yasa itama ta samu wuri ta zauna,junaid ma ya zauna gefenta,yayin da idanunshi ke akan su sehrish,sam basu lura dashi ba saboda hankalinsu duk ya tashi,a sakamakon Audio din da aka kunna,saboda sun tsani jin labarin rayuwarsu,ko miskala zarratin,

Kowa ya natsu yana sauraron audio ɗin,lokacin da Abusufyan ya kammala bada tarihin rayuwarshi da abu,sai next audio ɗin ya shiga wanda Jahad ke bada labarin rayuwarsu,nan take hankalin AMMI yayi mugun tashi,jikinta har tsuma yakeyi,tuni wasu siraran hawaye suka shiga zarya a kuncinta,ita kanta Alexandra jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,tunda take arayuwarta bata ta6a jin tausayin wani ɗan adam ba,daga ita har ammin kamar yadda sukaji tausayin waɗannan bayin Allahn ba,Very heart touching story,wanda duk wani mai imani In ya saurareshi dole ya zubda hawaye,in ma baiyi kuka ba,

Ganin yadda hawaye ke sintiri akan fuskar AMMI yasa Omar ya cire hanky daga aljihunsa ya miƙa mata,dama kamar yasan cikin buƙatarshi take,a fuskarta ta kifa hankacif ɗin,ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai,kowa yayi mamakin yadda Ammi ke kuka,cikin shessheƙar tace”ku kashe mun audio din nan ya isa haka,kunnuwa na bazasu iya jurar jin wannan tashin hankalin ba,’
dama Audio ɗin yazo ƙarshe,junaid ne ya mike ya ɗauki wayar,tare da miƙa ma babban yayansu ita,ya kashe audio ɗin,
“Shiyasa akeso ko da yaushe mutun ya kasance mai sauƙin kai,kada ya cika tsaurara al’amurransa,yanzu da ace banzo ba,da shikenan,haka zaki kora yaran nan,ke baki tsaya kinyi bincike ba,kuma baki saurari bayani daga gurin kowannansu ba kawai kin tashi kin yanke hukunci,sai daga baya kuma kizo kina danasani”

daƙyar ammi ta iya furta”Astagfurullah Allah na tuba!ka yafe mun,rashin sani ne yasa na kirasu da shaggu,game da halin da yaran nan suka tsinci kansu,duk laifin mahaifinsu ne,shine silar komai,duk da daman Allah ya ƙaddara faruwar hakan babu wanda ya isa ya hana,amma Abusufyan bai kyauta ma rayuwarsu ba,meyasa bai sanar ma kowa ba don aɗauki mataki?saboda kawai yayi mashi barazana?

Amma dai Allah ya tsine ma fasiƙin mutumin nan,Wlh bazan barsu ba,saboda me laifin kakansu zai shafe su?wannan wata irin mugunta ce mara kan gado,?bai tsaya a iya kan ya’yan salahudeen ba,hada jikokin duka yake ɗaukar fansa akansu,?kuma shima salahudeen ɗin daya kashe mahaifinsu ae don saboda mugayen laifukan da aka kamasu dashi ne,ɗaukar fansar ta mutun ukuce suke ɗauka,mahaifinsu da kuma mahaifiyarsu,da kuma wannan ɗan koran nasu,dukkansu Allah zai toni asirinsu,’

Jinjina kai modibbo yayi yana sauraronta saida takai ƙarshen maganarta,tukunna yace”ba komai ne yasa na tako nazo ƙasar nan ba,face don abu uku,kuma ina fata zaki bani haɗin kai domin asamu maslaha atsakaninku gaba daya,saboda baza a ta6a cin nasarar gano waɗannan masu ɗaukar fansar ba,har sai ku na cikin gidan kun fara haɗa kanku,in ba haka ba,munafukan dake shirya maku zagwan ƙasa zasu samu nasarar cin galaba akanku,ta hanyar rarraba kawunanku,saboda ni inaji araina cewar masu shirya wannan maƙarƙashiyar suna ATARE DAKU!sun shiga cikinku,suna acikin rayuwarku!’

Wannan maganar ba ƙaramin jijjigasu tayi ba,don sai da kowannansu ya ɗago yana kallon fuskar modibbon,
“Nasan zakuyi mamaki amma nan gaba sannu a hankali zaku shaida maganata,yanzu dae bari inyi abunda ya kawoni,”

“AISHA” Ya ambaci sunan Ammi,muryarta asanyaye ta amsa mashi da Na’am,
“Banaso in ƙarajin wani ƙorafi akanki!wannan ne na farko kuma wannan ne na ƙarshe!idan har kinaso ki zauna lafiya,to ki gyara tsakaninki da ya’yanki!da kuma tsakaninki da Jikokinki,na uku kuma shine tsakaninki da surukarki fatima,”ya ƙarasa maganar yana nuna Alexandra da sandar hannunshi,ɗagowa ammi tayi tare da kai idonta kan Mommynsu junaid wadda itama kallon nata takeyi,kawar da kanta tayi gefe batare da tace komai ba,

Cigaba da magana modibbo yayi,”Allah ma mukanyi masa laifi kuma ya yafe mana,balle mu ƴan adam,fatima bata yi maki laifin komai ba,tun farko koda kike mata magana take mayar maki saboda kin nemi cin zarafinta ne!wanda kuma ba kowa ne zai iya jurewa ba,balle ita da take jar fata,yanayin rayuwarsu ko ince tarbiyarsu ba irin tamu bace,don da a ƙasarsu ne kikayi mata haka zata kaiki ƙara kotu ne a yanke maki hukunci,babu ruwanta da Cewar ke surukarta ce,sannan kuma bai kamata ki nuna mata ƙiyayya ba,duk maison naka ae masoyinka ne!ɗanki fa takeso,kuma saboda son da take mashi tabar iyayenta da kowa nata tazo ƙasar nan,inda bata san kowa ba,ko tsoron acutar da ita batayi ba,bakowa ne ma zai iya wannan kasadar ba,don haka yakamata ki so fatima saboda masoyiyarki ce,ba maƙiyiyarki ba,idan don ta kasance farar fata ce,damu dasu shin ba Allah bane ya halicce mu ba?ya banbanta mu ne?ko wani yafi wani ne”? Ya ɗan jinkirta da maganar yana kallonta,

Kafin ya ɗaura da cewar”Yakamata ki ajiye wannan gabar dake tsakaninki da ita,Yanzu fatima ta wuce suruka a wurinki,tamkar ƴ’a take a wurinki,tunda ta hayayyafa da ɗanki,yakamata kiyi alfahari da ita saboda itace ta haifa maki ɗaya daga cikin jikokinki wanda duniya take alfahari dasu,waɗanda suka ɗaukaka darajar mu a idon duniya,”

READ ALSO:  Download Complete A Sanadin Makwabtaka Page 54 Romantic Hausa Novel PDF

Nauyayyiyar ajiyar zuciya Ammi tasaki tare da gyaɗa kai tace”Insha Allah komai ya wuce,”
Murmushi Abba ya saki ranshi fari tass kamar an yi mashi albishir da gidan aljanna,
“Sannan kema Fatima inaso ki ajiye dukkan wasu makaman yaƙin ki,kibi surukarki tamkar mahaifiyarki,kiyi mata biyayya amatsayinta na wadda ta tsugunna ta haifi uban ya’yanki,”
Fuskarta ɗauke da murmushi tace”Nima a wurina komai ya wuce,dama saboda ƙiyayyar da take nunamin ni da ya’yana ne yasa nima nake ƙinta,amma daga yanzu insha Allah babu wanda zai ƙara jinkan mu,”

Tana kai ƙarshen maganar junaid yace”Gaskiya,wannan sulhun bai cika yadda akeson shi ba,Mommy da Ammi basu ta6a yin koda musabaha ba,yakamata yau su tashi su rungume junansu ta hakan ne zamu gane cewar sun shirya da junansu,”
Gaba ɗayansu suka saki murmushi,miƙewa Alexandra ta farayi kamin Ammi itama ta miƙe,suka ƙarasa tare da rungume juna,tafi su Abba suka shiga yi wanda hakan yaja hankalin sauran matasan gidan,har suka firfito cikin falon don suga me ke wakana,ae koda su kayi arba da Ammi da Alexandra rungume da juna,nan fa suka shiga sowa,abun ba ƙaramin farin ciki ya sanyasu ba,musamman su Fawan don sun jima suna jiran wannan ranar tazo,ashe da rabon zasu ganta da idanuwansu,
“Ki yafe mun duk abubuwan da nayi maki,kuma inaso ki sani ba don bana sonki bane yasa nayi maki hakan ba,kawai haline irin nawa,da kuma sharrin shaiɗan” Ammi ce tayi maganar ayayin da take raba jikinta daga na alexandra,fuskar kowanansu ɗauke da siraran hawaye,
Murmushi alex ta saki kafin tace”Allah ya yafe mana gaba ɗaya,inaji kamar nafi kowa farin cikin wannan ranar,”tayi maganar fuskarta ɗauke da dariya,suna cikin rahar nan sukaji ana ɗaukarsu hoto ket ket!!

Da sauri suka waiga don su ga wanene,ashe wai fawan ne ya ɗauko camera ɗinsu,yana ɗaukarsu hoto yana faɗin”yau a daily trust dole su buga wannan gagarumin labarin,zazzafan gaske,Ammin mu wato kakarmu a yau ta rungumi surukarta wadda ta kasance mahaifiyarmu bayan sun dade suna shan gwagwarmaya ,”
Dariya sosai su kayi,ganin ya sanyasu raha,yasa shi cewa”Abba mu shigo ciki a ƙarasa tattaunawar tare damu?

Fuskar Abbansu ɗauke da murmushi yace”why not,a yanzu an sasanta komai,an samu maslaha,zaku iya zuwa ku zauna,”
Jin haka yasa suka ƙaraso ciki,gaba ɗayansu ne hada su twins jabeer,khaleed irfan dasu kanal,wuri suka samu suka zazzauna a ƙasa,
Junaid yace”Yawwa Amminmu,yanzu saura Uncle ɗinmu bawan Allah,yayi missing ɗinki sosai yakamata shima ki rungumeshi,ko yaji sanyi aranshi,”ya karasa yana langa6ar da kai.
Juyawa Ammi tayi tare da kallon abusufyan wanda ke a zaune,idonshi na kallon ƙasa,
Gyaran murya ta ɗan yi mashi,ya ɗago da idonshi ya kalleta,cike da zolaya tace”So kake sai nace ka taso”?

Fashewa yayi da dariya,kafin ya miƙe da sauri ya faɗa jikinta,sosai ta rungume shi ajikinta,tana ɗan bubbuga hannunta a bayanshi tace”nayi kewarka sosai,ka sani kuka Abusufyan,fiye da tunaninka,hakanan ka tafi ka barni shekara da shekaru….”tana maganar hawaye na fita a idanunta,
ɗagowa yayi daga jikinta,idonshi na fitar da kwalla yace”Ki yafe mun Ammi,nasan ban kyauta maki ba,nayi maki abubuwa da dama wanda bakyaso,nasan cewa hada haƙƙinki ne ke bibiyar rayuwata shiyasa ma harya shafi ya’yana,….”

Hannu tasa tana share mashi hawayenshi tace”Na yafe maka abusufyan,dama ni burina shine ka dawo kusa dani,kuma Alhamdulillah,gashinan ka dawo cikin yan uwanka,naji daɗin hakan sosai,Allah ya ƙara haɗamun kanku,”
gaba ɗaya suka amsa da Ammin,
“AMMI saura su rishi,su baki rungumesu ba,kalli fa kiga yadda duk suka shiga damuwa,bayin Allah,”

junaid ne ya sake yin maganar yana raku6e fuska,alamar tausayi
Kallonsu Ammi tayi,sun cunkushe wuri guda kamar kifin gwangwani,musamman Sehrish jikinta har lokacin sae kerma yake,a hankali Ammi ta taka izuwa inda suke,ta zuƙunna agabansu,sannan takai hannunta tare da shafa fuskokinsu,kafin tace”dole in nemi yafiyarku,saboda na jefebku da mummunan kalma,bisa rashin sani,ina mai matuƙar baku Haƙuri akan abunda ya faru a rayuwarku!ba laifinku bane laifin wasu ne akeso a ɗaura maku shiyasa aka biyo ta hanyarku duk don a ƙuntata mana,amma nayi maku alƙwarin cewa ɗaya daga cikin waɗanda sukayi sanadiyar wulaƙanta rayuwarku,Wlh bazai sha ba!daga rana irin ta yau zansa a fara bincike akansu har sai Allah ya tonu asirin kowannansu,

kuma nayi maku alƙawarin cewa,zansa akawo maku wannan fasiƙin mutumin har inda kuke don ku wanke mun mummunar fuskarshi da tafukan hannayenku,”
Jin wannan maganar ta Ammi yasa Hosana fashewa da dariya,har white teeth ɗinta suka bayyana,dimples ɗin fuskarta suka lotsa,Jahad ma murmushi ne ya bayyana a fuskarta,sehrish ce kawai batayi murmushi ba,da alama kamar akwai wani abu dake damunta,duba da yanayin jikinta dake ta kerma,

Ruƙo hannayensu ammi tayi tare da miƙar dasu tsaye sannan ta haɗasu duka ta rungumesu sosai,ajikinta,
Wani irin matashin murmushi ne ya bayyana a fuskar kowannansu dake a falon,haƙika sunji daɗin wannan ranar,tsakaninsu da Allah sai godiya daya bar Modibbo a raye har zuwa wannan lokacin,saboda shine silar komai daya faru ayanzu,da bai zo ba da akasin hakan ne zai faru,
Addu’oi’ Ammi ta shiga karantowa tana tottofa masu akawunansu,a ƙarshe tace”Allah yayi maku ALBARKA,”suka amsa mata da Amin,

Komawa su kayi kowa ya zauna,itama ammin ta zauna,bayan kowa ya natsu Modibbo yace”ko akwai mai magana acikinku”?
Da sauri Abbansu junaid yace”Ina da magana,”
Modibbo yace”faɗi kai tsaye muna sauraronka,”
“Yawwa kawuna,dama akan maganar fatima ne da Abusufyan!har yanzu basu shiri a tsakaninsu,tun wani sa6ani da suka ta6a samu a lokacin baya,to har yanzu basa jituwa,yakamata aduba lamarin,’
Sunnar dakai ƙasa Abusufyan yayi,kamar yadda itama alexandran tayi,
“Ae yanzu ko banyi masu magana ba,zasu shirya kansu ne ko don zumuncin dake a tsakaninsu,da kuma ƴa’ƴayensu,”

Murmushi kowannansu,yayi abusufyan yace”Insha Allah komai ya wuce a wurina,dama can ni ban ta6a ruƙeta araina ba,nasan rashin kunyar da nakeyi mata ne a lokacin baya yasa take fushi dani har yanzu,amma ina neman afuwarta,”
Yana kai ƙarshen maganarshi,Alexandra tace”Nima komai ya wuce a wurina,Allah ya yafe mana baki ɗaya,kuma ya ƙara haɗa kawunanmu,”

Wani irin ihu junaid ya fasa,saboda tsabar farin ciki,hankalin kowa ya koma kanshi,ganin sun zuba mashi ido yasa shi sanya tafin hannunshi ya rufe fuskarshi,saboda kunyar data rufe shi,ƙasa ƙasa yake sakin dariya,bakomai ne yasa shi wannan farin cikin ba,face Shiryawar da Momnynsu tayi da Uncle ɗinsu,ko ba komai zai samu amincewarta wurin auren ɗaya daga cikinsu,💃

“Gobe da safe zan wuce damaturu,tunda naci nasarar haɗa kawunanku,ina fata zaku kasance a haka ko bayan tafiyata,” atare suka amsa mashi da cewa”Insha Allah,”
“Amma mun jima bamu haɗu ba,bazaka ƙara kwanaki ba”? Ammi ce tayi maganar,
murmushi modibbo yayi kafin yace”kada ki damu,tun da dai na shigo ƙasar zaku dinga ganina ne akai akai,insha Allah,”

Alhamdulillah,The end🥱🤣😂😅 nan bada jimawa ba,zan rubuta hakan insha Allah,nasan wasu har gabansu ya faɗi rass………

 

 

FAST DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 79

The most reliable and easiest way to obtain the complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 79 is to purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 79 in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 79 booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.