Download Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 118 Hausa Novel PDF

Father of soldiers

TAKUN ƘARSHE

Tashin hankalin da ba’a sa mashi date,Wani irin kallo Sgr ke bin Uncle abusufyan dashi,just speechless,Ya ƙame a tsaye ya kasa motsa lips ɗinsa,Sam ya manta da wata yarjejeniyar aure a tsakaninsu,kamar a mafarki haka yake ganin abun,
“Rafayet!”ya ambaci sunanshi don ya lura hankalinshi baya atare dashi,firgigit Sgr yayi yana kallonshi Still bai tanka mashi ba,

“Am talking to u!nasan kaji duk abunda nace,we don’t ave time to waste,just to make it easy for you that’s why na kawo maka Paper da biro,rubutu kawai ya rage maka,nasan within minutes zaka rubuta very simple”
Gauran numfashi yaja da ƙarfi tare da runtse idanuwanshi,Da yake ba kunya ce ta ishe shi ba,Da buɗar bakinsa sai cewa yayi”Uncle,I changed my mind,I have already canceled the marriage contract,now I decided to go with her,”
Zuba mashi ido abusufyan yayi,cike da Tsantsar mamaki Yake kallonshi,
“Zan tafi da ita U.s taci gaba da yi mun aiki,”

Harara abusufyan ya wurga mashi kafin yace”aiki fa kace?me ka ɗauke ta?idan ka manta bari na tuna maka!Sehrish ƴar cikina ce,your uncle’s daughter ba house maid ba,Ni ban haifi ƴar aiki ba,”datakawa abusufyan ya ɗanyi da yin maganar yana fitar da huci,Yaji haushin maganar Sgr,Har yanzu bai daddara ba,Wato Still ƴar aiki ya ɗauketa,bai chanza ba yana nan kan bakanshi kenan,Yafi ƙarfin ya bata matsayin mata a wurinshi,daƙyar ya iya controlling  temper ɗinsa Ya ci gaba da magana”Amma rafayet baka da kunya!Har ni zaka kalli tsabar idona kace wai zaka tafi da ƴata U.s,kawai don taci gaba da yi maka aiki!ita Baiwarka ce?so kake ka ƙasƙantarmun da ƴata ne,Duk fa wani abu da kake taƙama dashi,Nima Allah ya hore mun koda bankaika ba,Also she’s ur bloodline’yana kai ƙarshen maganar,Rai a6ace Sgr ya juya tare da kai hannu ya damƙi paper ɗin da Abusufyan ya kawo mashi,Yayi tearing ɗinta,into pieces,don ma yasan ba wai zai rubuta abinda akeso ya rubuta bane,

Abun yayi mugun ɗaure ma Uncle abusufyan kai,Shi komai sai ya nuna ƙarfin iko,Ya fi ƙarfin ya miƙa wuya ya roka abashi abunda yake so ta lalama ba,jinjina kai yayi tare da cewa”Ka yage takardar ko?Ko ka manta da agreement paper ɗin dake a wurina da kuma wurin Abbanku!?
Gabansa ne yayi wani irin bugu mai sauti ji kake daram!!
“Kuma akwai signature ɗinka jikin takardar,”
Wata irin zufa ce ta soma tsatstsafo mashi,Sae kace ba yanzu ya fito daga wanka ba,
Murmushin takaici abusfyan ya ɗanyi kafin yace”As from today!Sehrish bazata ƙara zuwa part ɗinka da sunan aiki ba,Also…..”dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana duba wrist watch ɗin hannunsa,Lokaci yake kallo,
“Before 24 hours,Ina jiran Takardar sakinta,Idan kaƙi kuma hmmm kasan me zai biyo baya,”yana kai ƙarshen maganarshi,Yayi ƙwafa tare da juyawa ya fuce daga ɗakin nashi,
Wani irin jiri ne ya soma ɗibarshi,Ba arziƙi ya koma gefen gadonshi ya zauna tare da kifa kanshi saman guiwowinshi,
“Innalallahi wa’inna Ilaihi raji’un”
Wannan shine abunda yake ambato acikin Zuciyarshi,hankalinshi yayi mugun tashi,Taya zai Iya rayuwa batare da ita ba?Ta saba mashi da kanta,ta yadda bazai iya rayuwa batare da ita ba,bakomai yake tunawa ba face Romance ɗin da suka sha jiya,Yau rana ɗaya kawai ace za’a rabashi da ita,tabɗijan An taro match kuwa,Allah yasa sun tanadi filin bugata,

Kusan sau uku Marshal Omar yana kwaɗa sallama amma shiru bai amsa mashi ba,sam hankalinshi baya atare dashi,
“Rafayet”Ya ambaci sunanshi Yana shigowa cikin ɗakin,Firgit yayi tare da ɗago blue eyes ɗinsa,tamkar na wanda yasha Giya,fuskarshi tayi sharkaf da zufa,
Zama gefenshi Omar yayi”bro lafiyarka kuwa?Zaman me kake yi,Muna ta jiranka,Time ɗin sallah yayi fa”
Daƙyar ya iya buɗe baki yace”Omar,lokacin da zaka shigo kaga Uncle”?
Jinjina kai omar yayi alamar eh,
“Ashe ba mafarki bane”Ya ambaci hakan acikin zuciyarshi,
“What’s wrong with u?ko wani abu ya shiga tsakaninka dashi ne”?
girgiza kai yayi”bakomai,bari na shirya mu tafi,”yunƙurawa yayi tare da miƙewa tsaye,Daƙyar yake jan ƙafarshi,Direct ya nufi Closet ɗinshi,after some minute Ya dawo jikinshi sanye da Jallabiya,Omar ya tadda a tsaye hannunshi ruƙe da paper ɗin daya keta,Kallonshi yayi”Wannan fa?naga an yayyagata”
Yatsina fuska yayi tare da cewa”Bakomai,mu tafi,”a jere suka fita,Shiru kawai Omar yayi amma tabbas yana ji aranshi cewa wani abu ya faru dashi,Jikinshi duk yayi sanyi,downstairs suka sauko anan suka haɗu da sauran matasan gidan suka ɗunguma izuwa masallaci,

 

 

A 6angaren Sehrish kuwa,Tunda ta gudo daga part ɗinsa,Bedroom ɗin Aunty azmee ta wuce,tana shiga ta samu amrish a tsaye saman darduma ta kabbara sallah,lalla6awa tayi cikin sanɗa ta shige toilet,don ta tsarkake jikinta,ta fito ɗaure da towel ta nufi wadrobe,Da yake duk ta kwaso kayanta,Doguwar riga ta zura ajikinta orange colour,mara nauyi ƴar ta shan iska,saman dardumar ta hau,A gefen Amrish ta kabbara sallah,bayan sun kammala Sallar,ko addu’a bata samu tayi ba,Saboda yanayin da take ciki,kasala duk ta baibayeta,Saman gadonsu ta koma ta haye,ta janyo bargo ta lullu6e har kanta,duk amrish na kallonta,ta fara sanya mata ido,in dare yayi ta ɗau wanka,ta fuce daga ɗakin,tsakar dare ta dawo ko wurin asuba,Ta shiga toilet,Wani irin bacci ne ya ɗauketa mai daɗin gaske,hada minshari,

Bayan Amrish ta kammala Yin addu’ar da take yi,Komawa tayi gefen sehrish ta kwanta tana fuskantar ceilling,da alama tayi zurfin cikin tunani,

 

 

Tun wuraren ƙarfe 7 na safe,Mommy tare da Oumma suka shiga kitchen domin shirya breakfast ɗin gidan,basu jima da fara ƴan soye soye ba,Saude ta shigo kitchen ɗin tare da hajiya azeema,domin su tayasu aiki,hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba,Suna aiki suna fira,
“Naji kuna ta fira banji kuna zancen gagarumin bikin da muke dashi ba,”Hajiya azeema ce tayi maganar,.
mommy tace “Wai har mutun nawa za’a ɗaura ma aure ne?donni abbansu bai sanar dani ba,Amma yace mun in shirya tarbar surukai na,”
Aunty azeema tace”Ni kaina bansan mutun nawa za’a shafa fatihar tasu ba,Amma ina da tabbacin cewa hada abusufyan acikinsu,”da gangan tayi maganar,cike da zolaya tana satar kallon Abu,
Wata irin kunyace ta rufe ta,har ta kasa tanka mata,
“Ga kuma saude,Amaryar harrisun gwaggo,Kai gaskiya masha Allah zamu sha bikin da ba’a ta6a yin irinshi ba”abunka ga fulani ga kunya,da gudu saude ta fuce daga kitchen ɗin,
Gaba ɗaya suka fashe da dariya,
“Tunda saude ta gudu bari in dawo kan Zainabu abu,tauraruwar dake haskaka zuciyar abusufyan,Gaskiya abu ki gode ma Allah,Abusfyan ba ƙaramin Sonki yake yi ba,Ae dole ma yaso ki,Tashin farko kika haifa mashi triplet kyawawan gaske,”
Murmushi kawai abu ke saki,da alama taji daɗin maganar Aunty azeema,
Mayar da idanuwanta tayi kan mommy,
“Auntynmu,Kinsan nifa bana 6oye 6oye,nasan su Ya hossein basu sanar dake ba,”
Fuskar mommy ɗauke da murmushi tae”mekenan?
“Nima fa bani da tabbaci nadaiji ƙishin ƙishin wai cikin ƴan ukunta za’a haɗa aurensu da biyu daga cikin zaratan samarin wurinki,Amma fa bansan wanne daga cikinsu ba,”da biyu Azeema tayi maganar don taga reaction ɗinta,
Shiru Alex ta ɗanyi jimmm batare da tace komai ba,har na tsawon mintuna,azeema ta kafe ta da ido,don tasan halinta,a lokacin baya tasha faɗin cewa Ƴa’ƴanta bazasu auri baƙar fata ba,ita kanta abu ta lura da sauyawar da tayi tunda akayi mata maganar,
Lokaci guda,murmushi ya bayyana akan fuskarta,a tsanake ta soma magana”Zanfi kowa farin ciki,idan Zainab da abusufyan suka zama surukaina,Saboda na yaba da irin tarbiyar ƴa’ƴansu,suna da hankali sosai,ga girmama na gaba dasu,”
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e Aunty azeema,dama ita fargabarta karta basu matsala,
Abu kuwa taji daɗi sosai da irin yabon da Mommy tayi ma ƴa’ƴanta,

Cigaba da magana mommy tayi”Dama fa junaid ya sanar dani tun kwanakin baya,duk da na ɗanji nauyi wlh,Ya nuna yana son aure,mukuma a ƙa’ida Yaro kamar junaid ko soyayya bai isa ya fara ba,nayi tsammanin sai ya kai shekera Talatin koda biyar haka kafin ya fara zancen aure,Amma sai gashi tun yana 19 years aure yake so……”da sauri aunty azeema tace”Wannan ae ba wani abu bane,Ya hossein fa,tun yana 20years yayi aurenshi na farko,duk dashi A lokacin ya mallaki komai na rayuwa,Shi kuma junaid sakamakon tauye mashi haƙkinshi da Azeemi tayi,baisamu damar yin karatu ba,Balle aje ga maganar aiki,Amma bai kamata mu damu akan wannan ba,Still junaid yana da sauran damar da zai gyara rayuwarshi,zai cigaba da zuwa makaranta,Sannan za’a sama mashi aikin yi,tunda alhmdllh Allah ya hore mana,”
Murmushi mommy ta saki,Taji daɗin maganar azeema sosai,daga haka suka cigaba da yin firarsu suna aiki,cikin lokaci ƙanƙani suka kammala Girke girken nasu,a lokacin saude ta dawo kitchen ɗin,Atare da Oumma suka soma ɗaukar food stuffs ɗin suna kaiwa saman d-table,

READ ALSO:  Download Complete ƘANWAR MAZA Romantic Hausa Novel PDF

Bayan sun kammala jerawa,Saude tabi ɗakunansu tana tashinsu,Don su hallara a fara ɗa’amin,

Turo ƙopar ɗakin ammi tayi,Zaune tasame ta gefen gadon hannunta ruke da ƙur’ani tana karanta,Idanuwanta na sanye da glass fari,
Zuƙunnawa tayi cike da girmamawa ta gaishe da ita”Ammi ina kwana,kun tashi lafiya,Ya gajiyar tafiya,”
Murmushi ammi ta sakar mata”Lafiya lou,Gajiya tabi jiki,”
Saude tace”An kammala shirya breakfast Anan zan kawo maki,”.
“A’a,nafison nafito naci atare da jikokina,”murmushi saude ta saki kafin ta miƙe tare da juyawa zata bar ɗakin,.
“Ji mana,”ammi ce ta katse mata hanzarinta,”juyowa tayi tana kallonta,.  .
“Amm..ince ko kinyi ma su Nafisa da khadija magana”?tana magana akan ƴan matan da suka zo dasu jiya
“Ae daga ɗakinsu nake,Na same su suna shiryawa,”
Jinjina kai tayi”Masha Allah,zaki iya tafiya,”
Buɗe kopar tayi ta fuce izuwa ɗaki na gaba,

 

 

Jahad na kwance,since yesterday night bata runtsa ba,tashiga damuwa sosai akan junaid,hankalinta yaƙi kwanciya,tunda ya nuna baisanta ba,duk ta rasa natsuwarta,ita kaɗai Ce kwance saman gadon,Hosana na acikin toilet,

Kwankwasa ƙopar ɗakin akayi,Muryarta adisashe tace”Wanene”?
Muryar Hafsat ta juyo daga waje,
“Nice,”
saukowa tayi daga saman gadon taƙarasa tare da buɗe mata ƙopar,
“Aunty hafsat”Tsaye take jikinta sanye da riga da wando,ta yafa mayafi akanta,
“Jahad ce ko sehrish,”tayi tambayar ne don bata ganeta ba,
“Jahad ce,Kin tashi lafiya?Ya gajiyar tafiya”?
“Lafiyalou Alhamdullih”ta amsa mata tare da shugowa daga cikin ɗakin,
Gefen gadonsu ta zauna,kafin tace”Jahad inason magana dake,”jin haka yasa jahad ta koma gefenta ta zauna,ina sauraronki Aunty hafsat,

Calmy ta soma magana”Game da abunda Mommyna tayi maku,Ina nema mata yafiya a wurinku,dan Nasan haƙƙinku ne ke bibiyarta,Jahad tana cikin mawuyacin hali,Yanzu haka maganar da nake yi maki,ƙafarta ta ru6e ta lalace,A sakamakon wani mai mota daya bugeta A enugu,Ni bansan ma meya kaita can ba”idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar,
Hankali tashe jahad Tasoma ambaton’Innalallahi wa’inna ilaihirra’jin!”
“Wlh jahad,ta zama abun tausayi,A gefen bishiya take kwana,dare da rana tana zaune a wurin,Kona abinci bata dashi sai in ansamu na Allah ya bata sadaqa,tukunna take samun abunda zata sama cikinta,”
Jahad sarkin tausayi tuni hawaye sun wanke mata fuskarta,

Hosana dake a la6e cikin toilet tana sauraronsu,Sai 6a66aka dariya takeyi hada dafe cikinta,Don bala’e ko kuskure bakinta batayi ba,yayi dama dama da kumfa,Hannunta ruƙe da brush,
“Allah sarki aunty hafsat,wlh na tausaya mata baiwar Allah,Ni indan tani ce,Tuntuni na yafe mata,Amma meyasa ba ataimaka mata ba”?
“Jahad bamusan komai game da tafiyarta enugu ba,wayarta ma ba’a samu,Ashe tun lokacin da mai motar ya bugeta,Anan ta rasa wayarta,Shiyasa bamusan halin da take ciki ba,Amma yanzu nayiwa daddy magana,Yanzu haka tana kwance gadon asibiti acan enugun,saboda lalacewar da ƙafar tayi baza a iya ɗaukota kaitsaye ba zuwa abuja,Dole acan za’a fara yi mata aiki,Za’a cire ƙafarne…..”

Tunkan hafsat takai ƙarshen maganarta,Hosana dake ƙumshe dariya acikin toilet,ta tuntsire da wata irin mahaukaciyar dariya,
“Waye acikin toilet?Naji kamar sautin dariya”
Da sauri jahad tace”Bakowa aunty hafsat,Allah Ya bata lafiya,in sha Allah zata ji sauƙi,zamu tayata da addu’a,”
Hannu tasa tana share hawayen fuskarta,Kalaman jahad sun sanyaya mata zuciyarta,

‘Nagode sosai jahad,Yanzu saura hosana inaso na nema mata yafiyarta,”
Jahad na ƙoƙarin buɗe baki tayi magana,hosana dake acikin toilet ta ɗaga murya tare da cewa”Wlh na yafe mata,tunda an gutsire kafar,Allah ya kyauta gaba,”
Da sauri jahad ta daka mata tsawa”Hosana ya ishe ki haka,Wai meyasa baki iya magana ba,”
Hafsat kuwa murya asanyaye tace”Nagode hosana,Ni banga laifinta ba,Ai ita taja ma kanta,”tana kai ƙarshen maganar,ta nufi hanyar fita daga dakin,bayan fitarta,hosana ta futo daga cikin toilet,bakinta washe,
Harara Jahad ta jefe mata”Wawuya kawai sullu6iya,Yanzu abunda kika faɗa ma Aunty hafsat ya dace”?

Murguɗa mata baki Hosana tayi”Anje an faɗa,Allah shi ƙara in ma da ƙarin Ya ƙara,Uban dayasa ta kulle mu acikin store kamar wasu dabbobi,Wlh ni daɗi naji,wai agefen bishiya take kwana,har na hango ƙoƙwan bararta…..”fashewa ta kuma yi da dariya hada dafe ciki,jahad dai bata tanka mata ba,ido kawai tabi ta dashi,cike da takaici,
Guntun tsoki taja”Ya omar dai baiyi dacen mata ba,”
Harara hosana ta watsa mata kafin tace”eh ɗin ina ruwanki?A haka ya gani yana so,ɗan baƙin ciki sai dai ya mutu,Ni da ya Omar mutu ka raba takalmin kaza,”
Girgiza kai kawai Tayi batare da ta kuma tanka mata ba,Komawa tayi gefen gadon ta zauna,

Junaid Romeo

Har cikin ɗaki,Mommy ta shigo mashi da breakfast ɗinshi,Jiya atare dashi suka kwana,dama tunda ya fara jinya a tsakiyarsu suke sanyashi,Yanzu kuma ya fara jin sauki,Ya fara tunanin komawa bedroom ɗinshi,

A kwance ta same shi idanuwanshi na fuskantar ceilling,yayin da hawaye yake gangarowa kan fuskarsa,hakan ba ƙaramin tayar mata da hankali yayi ba,
“Junaid meke damunka ne”?tayi maganar a yayin da take ƙoƙarin zama gefenshi bayan ta ajiye mashi tray din kayan abinci saman table,
Dakyar ya iya mikewa daga kwanciyar da yayi ya zaune,hannu tasa tana goge mashi hawayen dake akan fuskarshi
“Pls tell me meyasa kake zubar da hawayenka”?ta tambaya cikin damuwa sosai,.
“Mommy,ina aunty azmee take”?
Ɗaure fuska Alex tayi”Junaid kar na sake ji,kayi mun zancenta,Yanzu azmee bata atare damu tana a prison,”
Cikin shessheƙar kuka yace”Mommy aunty azmee tana a prison why?Meyasa za’a kaita can?nifa bata cutar dani ba…..”rufe mashi baki mommy tayi da tafin hannunta”Shut up!ashe baka da hankali!duk irin cin zalun da tayi maka,amma kake faɗin bata cutar dakai ba?itace silar ciwon asthma ɗinka,sannan itace Ta mayar dakai soko ta hanaka ɗaukar karatu acikin brain ɗinka,A haka har kake cewa bata Cutar dakai ba”?shiru yayi baice komai ba,still hawaye basu daina zuba akan fuskarshi ba,
‘Why junaid?just because of azmee kake zubar da expensive tears ɗinka?kana so ka 6ata mun rai ko”?
Girgiza kai yayi”Am sorry mommy,Bazan ƙara magana akanta ba,”cikin sanyin murya yayi maganar,
Hugging ɗinshi tayi ajikinta”yawwa my baby boy,mu manta da abunda ya faru,Yakama ka mayar da hankalinka akan future ɗinka,yanzu dai bari na fara zuba maka abinci kaci ka koshi sai muyi magana mai mahimmanci akan rayuwarka,”
Janye shi tayi daga jikinta,sannan ta soma yin serving dinshi,Ta tasa shi gaba Sai da yaci ya ƙoshi tukunna suka soma magana dashi,Akan karatunshi,

 

 

Boss Bature

Wuraren ƙarfe 12 na rana,Gaba ɗaya matasan gidan suka shirya cikin kakinsu na sojoji,A jere motocinsu suka fita daga cikin gidan,babban taro su kayi a headquater ɗinsu,domin ƙarrama matasan gidan tare da ƙara masu Matsayin aikinsu,Farin ciki a wurin abbansu kamar ya zuba ruwa a ƙasa yasha,bakinshi Yaƙi rufuwa,ganin yadda ake ta yabon ƴa’ƴanshi,Manya manyan shuwagabanni na Armed forces suka halarci taron,na ƙasashe daban daban,

SEHRISH

Bata jima da fitowa daga wanka ba,Jikinta sanye da bathrobe,ta yarfo da gashin kanta ta gefen wuyanta,a takure ta samu amrish saman gadon,still taƙi sakin jikinta tayi rayuwarta kamar kowa,
“Wai meke damunki ne”?
“Babu komai”ta bata amsa a taƙaice,
“Idan kina jin kaɗaici ki fita waje mana,Ga ƴan uwa can suna ta fira a palour,”
“Bazan iya zuwa wurinsu ba,”
Tsananin tausayinta ya kamata,baiwar Allah duk ta tsani rayuwarta,ta takure kanta,

“Zanyi magana da daddy,May be idan shi yayi maki magana zaki faɗa mashi damuwarki,”
Da sauri tace”dan Allah kada kiyi mashi magana,wlh babu abunda ke damuna,rashin sabo ne nan da ɗan wani lokaci zan saba da kowa,”
Gyaɗa kai sehrish tayi tare da samun wuri gaban mirror ta zauna,
Zamanta keda wuya wayarta dake ajiye saman side drawer ta soma ringing,hannu amrish tasa ta ɗauki wayar,kafin ta sauko daga saman gadon ta miƙa mata,
Kar6ar wayar Sehrish tayi tare da kallon screen ɗin,My Boss Man ne ke kiranta,
Tayi mamakin ganin kiran Sgr,a wannan lokacin,picking call ɗin tayi tare da manna wayar a kunnanta,

“Assalamu alaikum,”
Bai amsa mata sallamarta ba,Sai cewa yayi”what are u doing now”?
“Yanzu na fito daga wanka,ina shiryawa”cikin sanyin murya ta bashi amsa,
“Its okey,before na dawo,ki shirya mun kanki,”
cike da mamaki ta amsa mashi da”Toh ”
Daga haka bai ƙara cewa komai ba,yayi rejecting kiran,tana ƙoƙarin ajiye wayar kiran Aunty azeema ya shigo wayar,murmushi ta saki dama tun jiya take ta son suyi magana da ita,
Ɗaga kiran tayi tare da manna wayar akan kunnanta,tunkafin tayi sallama hajiya azeema tace”Daughter,ki sameni a ɗakina,inason magana dake,”
Cike da zumuɗi Sehrish ta amsa mata da toh auntyna Am on my way,

READ ALSO:  Dowload Mai Dambu Hausa Novel Complete PDF

Bayan ta katse wayar ta miƙe,ta nufi wardrobe,dogon hijabi ta ɗauko ta zumbulashi ajikinta,ɗaukar wayarta dake ajiye saman mirror tayi,Amrish ta mika ma wayar”Ki yi amfani da ita,Zata ɗebe maki kewa kafin na dawo,zanje wurin auntyna ne,”
Fuskarta ɗauke da murmushi tace”Nagode,Saikin dawo,”

Da sauri ta fuce daga ɗakin,gyara kwanciya amrish tayi saman gadon,Hannunta ruƙe da wayar Sehrish,comedy din cikin wayar ta fara kallo,tun tana murmushi har ta fara tiƙar dariya,tana cikin kallon videos din Kiran ya shigo wayar,Duba sunan Mai kiran wayar tayi,

Yaya Yusif

A fili tace”yayanta ne ke kira,i won’t pick it,idan ta dawo zan faɗa mata,”har kiran ya katse bata ɗaga ba,after one minute,wani kiran nashi ya sake shigowa wayar,
Yanke shawarar ɗaga kiran tayi,A kunne ta manna wayar,Shiru tayi bata ce mashi komai ba,
“Assalamu Alaikum,Sister ya kike”?
Murmushi tasaki da yake ta ƙware wurin iya kwaikwayon muryar mutane sai cewa tayi”Lafiya lou yaya yusif,Ya kake”?
“Ina lafiya,kinyi mamakin kira na ko”?
“Eh,”ta amsa mashi,
“Na kira ne don na tambayeki,Yarinyar nan ƙawarki,i forgot her name,me irin sunanki,”
“Amrish”?tayi tambayar tana jiran jin amsarshi,
“Yeah,ita nake Nufi,naga ban cika ganinta ba,ina fata dai babu abunda ke damunta ko”?
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e amrish,ashe akwai wanda suka damu da ita acikin gidan,

“Kinyi shiru baki ce komai ba”?
Da sauri tace”Lafiyarta qalou,Yanzu haka nabarta ɗaki tana bacci,”
“Its okey,ki shafa mun kanta,idan ta tashi ki sanar da ita cewa,ina gaishe da ita,”
“Zanyi yadda kace in sha Allah,”
“Good”Yana katse kiran,ta fashe da wata irin dariya,saboda tsabar farin ciki hada yin ƙundunbale ta wutsila gefe ɗaya,Kamar anyi mata Albishir da gidan Aljanna,

A 6angaren Sehrish kuwa,Lokacin da ta shiga ɗakin hajiya Azeema a zaune ta sameta gefen gadonta,bubu gown ce ajikinta ta material,ba ƙaramin kyau yayi mata ba,
“My daughter,Zo ki zauna kusa dani,long time bamu haɗu ba,”
“Aunty ai jiya saida nazo ɗakinki,Na sameki kina bacci,sai dai na haƙura na koma,”ta ƙarasa maganar tare da samun wuri ta zauna daga gefenta,Suna fuskantar juna,
“Kinsan jiya mun kwaso gajiya,shiyasa ban samu na kiraki mun yi magana ba,Amma yanzu Alhamdullilah”
Murmushi sehrish ta saki tare da sunnar da kanta kasa tana kallon yatsun hannunta,
“Naga canji sosai attare dake,Kinyi haske kin ƙara kyau,ta ko’ina dai masha Allah,har na ƙosa naji labari me daɗi daga gare ki,”
Kunyace ta rufe sehrish da sauri ta sanya tafin hannunta asaman fuskarta ta rufe,”

dariya hajiya azeema tayi”kinfa san tsakanina dake babu kunya,Ba nace maki ki ɗauke ni tamkar ƙawarki ba”?tayi maganar tana kallonta fuskarta
Daƙyar sehrish ta iya cewa”Eh,”
“Yawwa,to cire hannunki yanzu,inaso ki faɗamun wani cigaba aka samu”?
Daƙyar ta daure ta cije cike da jin kunya ta soma bayyana mata,duk wani abu dake a tsakaninta da SGR,
Dariya sosai hajiya azeema tayi,bayan ta tsagaita da yin dariyar tace”Wonderful!My daughter u did a good job,you’re so special tunda gashi kin fara Canza mana Sgr,Naji daɗin jin hakan sosai,”ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin ta cigaba da cewa”Yanzu ya ake ciki game da tafiyarshi U.S?Yace zai tafi dake ko kuwa baiyi maki magana akan hakan ba”?
“Bani da masaniya akan wannan,bansani ba ko yana so ya tafi dani ko bayaso ya tafi dani,tunda baiyi mun magana akan hakan ba,Amma gaskiya aunty ko yace zai tafi dani ni bazan bishi ba,Saboda ba sona yake yi ba,bai ta6a furta mun kalmar so ba,”jiki asanyaye tayi maganar,

 

“Kin faɗi gaskiya,Amma inaso ki sani,Shi so ba dole sai ta kalamin baki ake furta shi ba,kowa da kalar nashi salon Soyayyar,Rafayet Baison so ba,Idan har ya kasance akanki yafara jin shi,zaiyi matuƙar wuya ya iya gane hakan,bazance ki bi shi ba,kuma bazance kada ki bi shi ba,tunda Wuƙa da nama suna a hannun abusufyan,Dole sai idan Sgr Ya soke wannan yarjejeniyar dake a tsakaninku,Ya miƙa wuya,Ya kuma amince zai rayu dake a matsayin matarshi,Uwar ƴa’ƴanshi,Idan ba haka ba,Bana tunanin Abusufyan zai bari ya tafi dake,zai nemi ya sake ki ne,”
Hankalin Sehrish ya ɗan tashi,don tasan halin Sgr,zai iya sakinta,tunda tasan ba sonta yake yi ba,A tunaninta kenan,.

“Yanzu mommy,Shikenan”
Jinjina kai hajiya azeema tayi,ƙwarai kuwa,bani da sauran shawarar da zan baki,Illa kawai mu zuba ido,muji me Abusufyan zaice,”
Sun jima suna tattaunawa kafin daga bisani,Sehrish ta baro bedroom ɗin,har wani jiri take gani acikin idanuwanta,daƙyar ta lalla6a ta koma ɗakinsu,Lokacin Amrish ta shiga toilet,saman gado ta haye tare da jan bargo ta lullu6e kanta ciki,

Fitowa amrish tayi daga cikin toilet din,tayi ɗaurin gaba da towel,ganin sehrish cikin bargo yasa ta ɗanyi mata gyaran murya tare da cewa”kin dawo kenan”?
“Eh”ta bata amsa atakaice,
“Okey,”ta ambaci hakan tare da wucewa gaban wardrobe ta buɗe ta dauko kayan da zata sanya,

Lokacin sallar magrib dakyar ta samu tayi sallah,ita kaɗai ta rage a ɗakin,Amrish ta ɗan fita waje,wurinsu Jahad,

Basu tashi dawowa cikin gidan ba,Sai wuraren ƙarfe 8 na dare,Gidan ya cika fam da manya manyan baƙi,ta ko’ina ka waiga Sojoji ne sanye cikin kakinsu,Wasu kuma Suna acikin shigarmu ta hausawa,Abun ya ƙayatar sosai,kowa na farin ciki banda mutun ɗaya SGR,domin kuwa yau ta kasance ranar baƙin ciki awurinshi,Fuskarshi kwata kwata babu annuri tunda suka fita har aka kammala taron,An karramashi shida Omar,Ga wani ƙarin  matsayin da za’a yi masu a U.S yana jiransu,Sauran matasan gidan kowanne da muƙamin da aka bashi,basu samun lokacin hutu ba,sai wuraren ƙarfe 10 lokacin Manyan bakin da suka zo,Duk sun tafi,Gidan ya rage sai mutanan cikinsu,Kowa Ya wuce bedroom ɗinshi domin hutawa,

SGR

Tun da ya shiga bedroom ɗinshi sai zarya yake yi,ya kasa samun natsuwa ko uniform ɗin jikinshi bai cire ba,Abbansu kawai yake jira Ya shigo cikin gidan suyi magana dashi,Sai kiran wayarshi yake yi,Amma bai ɗaga ba,atare dashi suka dawo,Amma bai shigo gidan ba,Yana a wurin abokinshi tafeeda a waje,komawa yayi gefen gadon ya zauna,kamar ance ya duba screen ɗin wayarshi,Sai ga text message na abusufyan,ƙin buɗe saƙon yayi don yasan cewa akan maganar sakin Sehrish ne,duk yabi ya tayar mashi da hankalinshi,duk yinin yau baisanya abinci acikinshi ba,Kamar me azumi,saboda tsabar tashin hankali,Zuciyarshi tare da agogo suke bugawa, awanni kaɗan suka rage mashi,shikaɗai yasan yadda yake ji acikin zuciyarshi,Yau da ƙishir ruwanta ya yini,yayi maraicin ganinta,duk a tunaninshi Uncle ne Ya dakatar da ita,

Yana cikin wannan mawuyacin halin,Omar Ya faɗo bedroom ɗin nashi jikinshi sanye da kaki,Yana ta faman ƙwala mashi kira”Rafayet!Rafayet”!
Daƙyar ya iya amsa mashi”Na’am,”

Ajiyar zuciya ya ɗan sauke kafin yace”Wai meke damunka ne?tunda muka fita na lura dakai,fuskarka a ɗaure tamau,babu annuri,In wani abu ne ka faɗamun mana,May be i ave the solution of it,”
Har lokacin bai motsa daga zaunan da yake ba,Gefen shi omar ya zauna tare da dafa kafaɗarsa,cikin lallami yake yi mashi magana”Pls my own bro,ka faɗamun mana,wlh duk na damu da halin da kake ciki,”
Daƙyar ya samu Sgr Ya faɗa mashi abunda ya faru tsakaninshi da Abusufyan Da asuba,”
Cike da takaici Omar yace”Ya salaam!Rafayet meke damunka ne wai?Wai meyasa komai saika nuna fin ƙarfi akanshi ne!don me zaka ce mashi haka?kana so ka tafi da ƴarshi ba don kana sonta a matsayin matarka ba,Sai don kanaso taci gaba da yi maka aiki kamar wata baiwa!?
Runtse ido sgr yayi tare da cizon pink lips ɗinsa,
“Its okey Omar,Stop shouting at me,kana cika mun kunne na,”
Rai a6ace Omar ya miƙe tare da acewa “Oh haka ma zakace!Good,wlh baka ji jiki ba,Uncle yayi mun dai dai,”juyawa yayi a fusace har yakai baƙin ƙopar ya kuma juyowa tare da kallonshi,

“Dole na fada maka gaskiya koda kuwa bakasan jinta,Rafayet ka kamu da Son Yarinyar nan!Kana tsananin sonta am advising u,tunkafin lokaci ya ƙure maka,Kayi hanzarin miƙa wuya,Idan kuma kace zaka sanya girman kai aciki,Wlh u will regret it,”yana kai ƙarshen maganarshi,ya fuce daga cikin ɗakin,bawan allah saboda yadda ya damu da sgr,a ƙopar falonshi ya tsaya sam ya kasa tafiya,tsananin tausayinshi ne ya kamashi,Sam baisan menene so ba,gashi yanzu zai fara shan wahalarshi,

READ ALSO:  Download Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 79 Hausa Novel PDF

Ya jima a haka kafin ya fito daga part ɗinsa,yana ƙoƙarin saukowa downstairs su kayi kici6us da Abbansu,da alama bene zai hau,shigowarshi kenan ko kakin jikinshi bai cire ba,
“Yawwa abba,Inason magana dakai,”
“Meya faru omar?Allah yasa dai Lafiya,Naga missed calls ɗin rafayet yana ta kirana,bansani ba saboda na sanya wayar silent”
Ruƙo hannunshi Omar yayi,Suka koma upstairs din,a tsaye suka soma magana,
“Abba,na samu rafayet cikin mawuyacin hali,dama duk yinin yau na lura dashi,ko abinci baici ba,Yanzu naje bedroom ɗinshi na tambayeshi meke damunshi,Shine yake sanar dani cewa Uncle abusufyan Ya nemi ya sakar mashi ƴarsa,”
Murmushin takaici Abba yayi kafin yace”Wata amsa ya bashi”?
“Yace shi bazai saketa ba,Ya soke yarjejeniyar auren,Maimakon yabi ta lalama,Sai cewa yayi wai zai tafi da ita U.s don taci gaba da yi mashi aiki,”
Cike da takaici,Abba ya dafe goshinshi”Ni dama nasani wlh,shiyasa tunfarko nayi ƙoƙarin in karkato hankalinshi don ya soke yarjejeniyar,Amma ya nuna mun cewa baya buƙatarta,Da zarar wata uku sun cika zai sakar mashi ƴarshi,Yanzu gashi lokaci ya cika,Ni ba abunda zan iya yi mashi Omar,nasan na isa da abusufyan amma ban isa na hana shi yin iko da ƴarshi ba,”
“Yanzu abba,Babu wani solution?Ni so nake A soke wannan auren yarjejeniyar,A barshi yayi rayuwa da matarshi,”

 

“Kasan Allah,in har rafayet bai miƙa wuya ba,Ni bazan ta6a tursasa ma abusufyan ba,Dole ya sauke jiji da kannan nashi,in har yana son yaci gaba da rayuwa da ita,Shi Yafi ƙarfin yayi biyayya ya samu abunda yakeso,Komai sai yace a dole saiya same shi,Ai bakomai ne ƙarfi da dukiya suke iya siya ma mutun ba,babban abun takaicin ma,Ya maida abusufyan tamkar tsaranshi,ko ba komai ,Shifa uncle dinsa ne,baya respecting dinshi yadda ya dace,”
jinjina kai omar yayi’Shikenan Abba,Zanyi ƙoƙari wurin ganin na fahimtar dashi,wlh banaso a wahalar mun da ɗan uwana,irin rayuwar da aka saba mashi da itane,Shiyasa ya kasance haka,”
Suna cikin maganar nan,suka jiyo takun takalmi,Alamar wani na tunkaraso,da sauri suka kai idanuwansu wurin,Bakowa bane face Abusufyan,Jikinshi na sanye da Jallabiya brown colour,ƙarasawa yayi tare da miƙa ma abba hannu suka gaisa,
Fuskarshi asake yace”Sannu da dawowa Yayana nakaina,Yanzun nan Ayaan ke sanar dani cewa ka dawo gida,”
“Eh wlh,ban jima da shigowa ba,Na nufo nan,wurin mutumin naka,”ya ƙarasa maganar da zolaya,
ta6e baki Abusufyan yayi batare da yace komai ba,
“Yanzu omar ke sanar dani abunda Ya faru atsakaninka da Sgr,Gaskiya banji daɗi ba,Rafayet bai kyauta ba,”

 

Sai lokacin abusufyan ya soma magana”Allah yaya rafayet saiya gane kuskurenshi,A ƙule nake dashi,Wai har ni zai kalli tsabar idona yace wai Ya soke yarjejeniyar aurenshi da ita,Kuma zai tafi da ita u.s,don taci gaba dayi mashi aiki?wato shi yafi ƙarfin yace yana sonta a matsayin matarshi…….”daƙyar yakai karshen maganar saboda ranshi yayi mugun 6aci,
“Dan Allah uncle kayi haƙuri,Amma ……”tunkan Omar yakai ƙarshen maganar ya dakatar dashi”kada kace komai Omar,Ka barni da rafayet kawai,Ya raina ni,Har ni zan kai mashi paper don ya rubuta mata sakinta,Yasa hannu ya ɗauki paper ya kekketata akan idona,Baiso xaman lafiya ba Allah,”
Tunda ya soma magana Abba ke kallonshi,Bai ta6a ganin abusufyan ya zuciya ba irin na yau,
Yana kai ƙarshen maganarshi,bai jira wani daga cikinsu Ya ƙara magana ba,Ya wuce part ɗin Sgr,Don yaci alwashin saiya sakar mashi ƴarshi Ayau ɗin nan,da sauri Omar da Abba suka bi bayanshi,

A lokacin sgr ya miƙe yana ta faman yin zarya acikin bedroom ɗinshi,Ba zato ba tsammani Yaji sallamar abusufyan har sai da gabanshi Ya faɗi,Yana shigowa Abba da Omar suka faɗo ɗakin,
“Rafayet!ina takardar dana ce ka rubuta mun”?
Zuba mashi ido Sgr yayi batare dayace komai ba,a hankali ya sauke idanuwanshi daga kan abusufyan ya ɗaura su kan Abbansu,jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba,ganin yadda Sgr ya koma,kamar wanda yayi zazza6i,
Har lokacin bakinshi bai mutu ba,rai a6ace Ya soma magana,
“I will never use my fingers to write her a divorce paper,sai dai duk abunda zai faru ya faru,”
A hasale Abusufyan ya kalli abba”Kaji abunda yace ko”?
Gaba ɗaya sun tashi hankalin abba,Ga gajiya daya kwaso,
“Dan Allah mubi komai a hankali,Banaso kowa yaji wannan maganar,Zansa ya sake ta,ni dakaina,”

Hankali atashe Sgr ke kallon Abbansu,
“tun farko Auren nan Anyi shine bisa yarjejeniyar zaka sakar mashi ƴarshi,Bayan wata uku cuf,A tsakanin mu ukun nan mu kayi yarjejeniyar nan,Kuma akwai shaida a hannun kowannanmu,don haka baka da wani za6i daya wuce ka sakar mashi ƴarshi kamar yarda ya buƙata,”
Girgiza kai sgr yayi”That’s impossible,”Ya ambaci hakan tare da juya masu baya,
“A matsayina na mahaifinka,Ina umartarka,daka rubuta mata takardar sakinta,Kamar yadda mahaifinta ya buƙata,Idan kuma ba haka ba,Zan yanke duk hukuncin dana ga ya dace,”
A firgice ya juyo yana kallonshi,Muryarshi na kerma yace”Abb..ba”
Fuska aɗaure abba yace”banason Jin komai daga gareka”
Wata irin zufa ce ta soma tsatstsafowa ta gefen fuskarshi,hankali tashe yake kallon Omar,Da sauri Omar ya kawar da kanshi gefe,sam baiso hakan Ya faru ba,yaso ace Sgr Ya tausasa kalamanshi,Amma yaƙi fahimtar hakan,
jikinshi har wani tsuma yake yi,gaba ɗaya sunso Sgr Ya miƙa wuya a wannan lokacin amma sai suka ji yace”Its Okey,Zan sake ta,Amma inaso a ƙara mun lokaci zuwa asuba,dakaina zan kawo takardar sakin nata,”
Kallon juna sukayi,Cike da mamakin jin yayi amanna da sakin nata,
Da sauri Omar yace”Pls,kada kuyi saurin yanke hukunci,yakamata muji ta bakin ita yarinyar,”
Girgiza kai abusufyan yayi”babu buƙatar yin hakan,Na bashi nan da asuba,Ya kawo mun takardar sakinta,”Yana kaiwa ƙarshen maganarshi,Ya juya afusace yabar bedroom ɗin,Abba ma yabi bayanshi,
Ya rage daga shi sai Omar,
“Pls bro,kada kace zaka sake ta,Nasan kana sonta wlh zaka yima zuciyarka illa ne,naso ace ka miƙa wuya tun wuri…..”
A hasale sgr ya juyo idanuwanshi sun juye,tamkar bashi ba,da wata irin murya yace”Banason ganin kowa a tare da ni,”
“Allah ya huci zuciyarka,”jiki asanyaye omar ya juya yabar mashi ɗakin,

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 12 na dare,tana zaune cikin duhu gefen gadonsu,sam batasan cewa sun dawo cikin gidan ba,saboda Baccin daya ɗauketa Mai nauyin gaske shiyasa har bata ji dirar motocinsu ba tun wurin ƙarfe goma da suka dawo,duk wannan budurin da akeyi ita bata sani ba,bata jima da farkawa ba,Amrish na kwance sai sharar baccinta takeyi hankali kwance,

Wata irin yunwa take ji,Sai faman lumshe idanuwanta takeyi don bacci bai isheta ba,gani tayi har sha biyu da rabi basu dawo ba,hakan Yasa ta ɗan kwanta gefen gadon,cikin lokaci ƙanƙanin bacci yayi awon gaba da ita,

Kwatsam!ba zato ba tsammani kamar daga sama,Taji an banko ƙopar ɗakin da suke ciki,A firgice ta miƙe zaune don ganin wanene,bata iya tantance wanda ya shigo ɗakin ba saboda sun kashe hasken ɗakin,ko’ina duhu,a tsorace takai hannu tana ƙoƙarin lalubo Fitar saman drawer don ta kunnata,Sai dai kash kafin tayi wani yunƙuri,Gaba ɗaya,ɗungurugum taji an ɗauketa sama,Tana ƙoƙarin yin ihu aka toshe mata bakinta,

FREE DOWNLOAD

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3

The most reliable and easiest way to obtain the complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 to purchase them from Jambandwaec.com (JAW)Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 inPortable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an emailcontaining the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

 

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.