Download Complete Duk Karfin Izzata By Star Lady Romantic Hausa Novel PDF

Duk Karfin Izzata

By
Star Lady

Page 50

 

A yaune su Ammi suka bar hotel ɗin gaba ɗayan su suka koma gidan bgs,in da aka fara kwantar da hiyana
gidan Part uku kowani part yana da babban palon kasa mai ɗauke da ɗakin barci uku sai katon kitchen da table ɗin cin abinci sai sama shima komai irin na kasan ne palo ɗaya bedroom uku kowani bedroom da katafaren toilet ciki da dressing room
Abba da Ammi da Ummi suka ɗauki Part ɗaya na gidan Yusuf Khalid Fahad suka ɗaki part ɗaya amma iya kasa kawai su Aunty farida Aunty mardiya Aunty salma suka ɗauki sama na part ɗin su Yusuf bgs Aryan suka ɗauki Part ɗaya Aryan na kasa bgs na sama yaso su wuce da hiyana amma taki ta gudu tabi Ammi ita kuwa Ammi ta goya mata baya ta bata wajen zama a ɗakin ta su amrat kam kowa na manne da mijin ita diyana itace oga tana manne da yaya Aryan ɗin ta gwanin ban sha’awa suna.
10pm kwance yake saman katafaren gadon sa ya kasa barci sai tunanin ta yake mikewa yayi zaune a saman gadon ba abun da yake gani a face nashi face kyakkyawar face nata lokacin da ya shigo hotel nan ya same ta tana hira da murmushi ita da su Zahra kasa kasa yace”my Eshat gaskiya kinyi wa yaya Prince illa daki ka ki biyoni”wayar sa ya jawo ya kira layin ta a kashe kai tsaye ya kira layin Ammi lokacin da kiran ya shigo wayar Ammi na zaune saman tsakiyar gadon ta,hiyana ta tada kai da cinyar ta Ammi na mata natsiha akan zaman Aure sai hawaye take dan natsihar Ammi na ratsa ta har cikin jikin ta tana kuka tana tana tunanin kyakkyawan face ɗin kyakkyawar mijin ta lokacin da ya ɗogo habarta a hotel yayi kyau sosai lokacin
ganin kiran bgs yasa Ammi ta miƙawa hiyana wayar dan tasan bgs ba zai kirata awan nan time ɗin ba idan ba da hiyana yake son yin magana ba mamaki ne ya kama hiyana lokacin da taga sunan da Ammi tayi saving number bgs my first love wani mugun kunyan Ammi ne ya kara kamata cikin ranta ta fara nadamar cewa Ammi da tayi bata son bgs ashe ashe Ammi na bala’i son bgs kawai dannewa take tabi bayan hiyana dan ta kwatanta adalci gaskiya Ammi mutuniyar kirki ce.
da bata so ɗaukar wayar ba amma ganin sunan da Ammi ta sa masa yasa tayi picking ɗin a ranta tana faɗin “daga yau ba zan sake cewa bana son wani abun da ya shafi yaya Prince ba ko dan kaunar da Ammi ta nuna min”shiru tayi bata yi magana ba dan kunyar Ammi da take ji kasa kasa da murya kamar mai raɗa yace”barka da dare my Ammi”murmushi ne ya suɓuce mata ji yadda magana cikin kaunar Ammi da girmamawa jin muryan sa yasa ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya tayi shiru ta kasa magana dan Kunyar Ammi take ji sosai,jin ajiyar zuciya ta yasa ya gane ba Ammi bace dan haka sai yace”my Eshat kema kina kewata ko?”shiru tayi bata masa magana ba”why kika ki bin mijin ki kin san dole zanyi tunanin ki ko?
“ganin taki yin magana yasa Ammi ta jawo pillow ta kwantar mata da kan ta ta mike ta sauka gadon ta nufi palo tana faɗin”ina zuwa humaira”jin abun da Ammi tace yasa bgs yace”kunyar Ammi kike ji ko?to yanzu ta tafi pls kiyi magana””yaya prince ina wuni?meyasa ka kirani?” “dan naji muryan matata mana”cool murmushi ta saki tare da juyawa ta gyara kwanciyar ta da kyau”murmushi na miki kyau sosai my Eshat” “waya ce maka murmushi nake” “zuciya tace ta faɗa min”shiru tayi tana tunanin ko dai yasa camera ne a ɗakin”ki dai na wahalar min da kanki wajen tunani ni ban sa camera a ɗakin ba bana sa camera a bedroom sai palo bedroom sirrin mai ɗaki ne bai kamata aga sirrin mutun ba domin Annabi ya hana ka bibiyi sirrin ɗan uwanka”
“ni ban yarda ba dole kasa camera idan ba haka ba ya akayi kasan nayi murmushin?sanna ya akayi kasan ina tunani” “kenan karya zan miki Eshat?rai a ɗan bace yayi maganar cikin sauri tace”a’a kayi hakuri kawai mamaki nake”shiru ya ɗan yi kafin yace”muyi video call?”da sauri ta girgiza kai tana faɗin”aa”dan ita har yanzu tsoron ganin sa take”why har yanzu kike tsoro na bakin son kallon face na kai tsaye sai dai ki rinƙa satar kallona?”
waro ido waje tayi ko yaushe yasan tana satar kallon sa oho mutun kamar wani aljani ɗaure fuska tayi a kule tace”ni bana satar kallon ka kuma me zan gani a fuskar ka baya fuskar mu iri ɗaya”girgiza kai kawai yayi dan har ga Allah da kyar yake maganar nan da ita kwata kwata arayuwar sa bai san yawan magana idan yayi magana ya wuce 5mins kan sa har ciwo yake masa to amma ba yadda zai yi dole yayi magana da ita dan sauraron voice nata ne kawai zai iya sa yayi barci,jin yayi shiru yasa tace”yaya Prince sai da safe” “ke kika kira ne?”gurgiza kai tayi tana faɗin”a’a

FAST DOWNLOAD

READ ALSO:  Download SONE KO K'IYAYYA Hausa Novel Complete PDF

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

How To Get Complete Duk Karfin Izzata

The most reliable and easiest way to obtain the complete Duk Karfin Izzata is to purchase them from Jambandwaec.com (JAW) Novel Store, because we remain the best in delivering the true novels you will definitely enjoy.

You can get the complete Duk Karfin Izzata in Portable Document Format (PDF) for just ₦1,000.

JAW remains the best, reliable and most credible resources you will find online as it is also well Arranged in PDF.

To get your own copy of the complete MURMUSHIN ALKAWARI By SNazir Adam Salih booklet, follow these simple steps:

Step 1: Visit the DOWNLOAD LINK to make a payment.

Step 2: Fill in the form with the right information including emails, and title of novel.

Step 3: Make payment for the booklet using your preferred payment method.

Step 4: Once payment is confirmed, you will receive an email containing the PDF of the novel you want.

DOWNLOAD COMPLETE PDF HERE

 

NEED a guide, update, or answer on something? You can spend just #1000 to get professional answers and guides. Click here to request Mr. Samuel's INSTANT REPLY. 

Leave a Comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.